40) Sūrat Ghāfir

Printed format

40) سُورَة غَافِر

Ĥā-Mīm َ040-001 Ḥ. M̃. حَا-مِيم
Tanzīlu Al-Kitābi Mina Al-Lahi Al-`Azīzi Al-`Alīmi َ040-002 Saukar da Littãfi daga Allah ne, Mabuwãyi, Masani. تَنزِيلُ الْكِتَابِ مِنَ اللَّهِ الْعَزِيزِ الْعَلِيمِ
Ghāfiri Adh-Dhanbi Wa Qābili At-Tawbi Shadīdi Al-`Iqābi Dhī Aţ-Ţawli  ۖ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  'Ilayhi Al-Maşīru َ040-003 Mai gãfarta zunubi kuma Mai karɓar tũba Mai tsananin azãba, Mai wadãtarwa bãbu abin bautawa fãce Shi, zuwa gare Shi makõma take. غَافِرِ الذَّنْبِ وَقَابِلِ التَّوْبِ شَدِيدِ الْعِقَابِ ذِي الطَّوْلِ  ۖ  لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ  ۖ  إِلَيْهِ الْمَصِيرُ
Mā Yujādilu Fī 'Āyāti Al-Lahi 'Illā Al-Ladhīna Kafarū Falā Yaghrurka Taqallubuhum Al-Bilādi َ040-004 Bãbu mai jãyayya a cikin ãyõyin Allah, fãce waɗanda suka kãfirta. Sabõda haka kada jũyãwarsu a cikin garũruwa ta rũɗe ka مَا يُجَادِلُ فِي آيَاتِ اللَّهِ إِلاَّ الَّذِينَ كَفَرُوا فَلاَ يَغْرُرْكَ تَقَلُّبُهُمْ فِي الْبِلاَدِ
Kadhdhabat Qablahum Qawmu Nūĥin Wa Al-'Aĥzābu Min Ba`dihim  ۖ  Wa Hammat Kullu 'Ummatin Birasūlihim Liya'khudhūhu  ۖ  Wa Jādalū Bil-Bāţili Liyudĥiđū Bihi Al-Ĥaqqa Fa'akhadhtuhum  ۖ  Fakayfa Kāna `Iqābi َ040-005 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata a gabãninsu, da ƙungiyõyin da suke a bãyansu, kuma kõwace al'umma tã yi nufi game da Manzonsu, dõmin su kãmã shi. Kuma suka yi jãyayya da ƙarya dõmin su gusar da gaskiya da ita. Sai Na kãmã su. To, yãya azãbãTa take? كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوح ٍ وَالأَحْزَابُ مِنْ بَعْدِهِمْ  ۖ  وَهَمَّتْ كُلُّ أُمَّة ٍ بِرَسُولِهِمْ لِيَأْخُذُوه ُُ  ۖ  وَجَادَلُوا بِالْبَاطِلِ لِيُدْحِضُوا بِهِ الْحَقَّ فَأَخَذْتُهُمْ  ۖ  فَكَيْفَ كَانَ عِقَابِ
Wa Kadhalika Ĥaqqat Kalimatu Rabbika `Alá Al-Ladhīna Kafarū 'Annahum 'Aşĥābu An-Nāri َ040-006 Kuma kamar haka kalmar Ubangijinka ta wajaba a kan waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ 'yan wutã ne. وَكَذَلِكَ حَقَّتْ كَلِمَةُ رَبِّكَ عَلَى الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّهُمْ أَصْحَابُ النَّارِ
Al-Ladhīna Yaĥmilūna Al-`Arsha Wa Man Ĥawlahu Yusabbiĥūna Biĥamdi Rabbihim Wa Yu'uminūna Bihi Wa Yastaghfirūna Lilladhīna 'Āmanū Rabbanā Wasi`ta Kulla Shay'in Raĥmatan Wa `Ilmāanghfir Lilladhīna Tābū Wa Attaba`ū Sabīlaka Wa Qihim `Adhāba Al-Jaĥīmi َ040-007 Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), "Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azãbar Jahĩm." الَّذِينَ يَحْمِلُونَ الْعَرْشَ وَمَنْ حَوْلَه ُُ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَيُؤْمِنُونَ بِه ِِ وَيَسْتَغْفِرُونَ لِلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا وَسِعْتَ كُلَّ شَيْء ٍ رَحْمَة ً وَعِلْما ً فَاغْفِرْ لِلَّذِينَ تَابُوا وَاتَّبَعُوا سَبِيلَكَ وَقِهِمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ
Rabbanā Wa 'Adkhilhum Jannāti `Adnin Allatī Wa`adtahum Wa Man Şalaĥa Min 'Ābā'ihim Wa 'Azwājihim Wa Dhurrīyātihim  ۚ  'Innaka 'Anta Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ040-008 "Ya Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su a gidãjen Aljannar zama, wannan da Ka yi musu wa'adi, sũ da wanda ya kyautatu daga ubanninsu da mãtan aurensu da zurriyarsu. Lalle Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima." رَبَّنَا وَأَدْخِلْهُمْ جَنَّاتِ عَدْن ٍ الَّتِي وَعَدْتَهُم وَمَنْ صَلَحَ مِنْ آبَائِهِمْ وَأَزْوَاجِهِمْ وَذُرِّيَّاتِهِمْ  ۚ  إِنَّكَ أَنْتَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Wa Qihimu As-Sayyi'āti  ۚ  Wa Man Taqī As-Sayyi'āti Yawma'idhin Faqad Raĥimtahu  ۚ  Wa Dhalika Huwa Al-Fawzu Al-`Ažīmu َ040-009 "Kuma Ka tsare su daga mũnãnan ayyuka, kuma wanda Ka tsare shi daga mũnãnan ayyuka a rãnarnan, to, lalle, Ka yi masa rahama kuma wancan shi ne babban rabo mai girma." وَقِهِمُ السَّيِّئَاتِ  ۚ  وَمَنْ تَقِي السَّيِّئَاتِ يَوْمَئِذ ٍ فَقَدْ رَحِمْتَه ُُ  ۚ  وَذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Yunādawna Lamaqtu Al-Lahi 'Akbaru Min Maqtikum 'Anfusakum 'Idh Tud`awna 'Ilá Al-'Īmāni Fatakfurūna َ040-010 Lalle waɗanda suka kãfirta, anã kiran su, "Haƙĩƙa, ƙin Allah (a gare ku) shĩ ne mafi girma daga ƙinku ga kanku a lõkacin da ake kiran ku zuwa ga ĩmãni, sai kunã ta kãfircẽwa." إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا يُنَادَوْنَ لَمَقْتُ اللَّهِ أَكْبَرُ مِنْ مَقْتِكُمْ أَنْفُسَكُمْ إِذْ تُدْعَوْنَ إِلَى الإِيمَانِ فَتَكْفُرُونَ
Qālū Rabbanā 'Amattanā Athnatayni Wa 'Aĥyaytanā Athnatayni Fā`tarafnā Bidhunūbinā Fahal 'Ilá Khurūjin Min Sabīlin َ040-011 Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Kã matar da mu sau biyu, kuma Kã rãyar da mu sau biyu, sabõda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita?" قَالُوا رَبَّنَا أَمَتَّنَا اثْنَتَيْنِ وَأَحْيَيْتَنَا اثْنَتَيْنِ فَاعْتَرَفْنَا بِذُنُوبِنَا فَهَلْ إِلَى خُرُوج ٍ مِنْ سَبِيل ٍ
Dhālikum Bi'annahu 'Idhā Du`iya Al-Lahu Waĥdahu Kafartum  ۖ  Wa 'In Yushrak Bihi Tu'uminū  ۚ  Fālĥukmu Lillahi Al-`Alīyi Al-Kabīri َ040-012 Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirãyi Allah Shi kaɗai, sai ku kãfirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi ĩmãni. To, hukuncin fa, na Allah Maɗaukaki, Mai girma ne. ذَلِكُمْ بِأَنَّهُ~ُ إِذَا دُعِيَ اللَّهُ وَحْدَه ُُ كَفَرْتُمْ  ۖ  وَإِنْ يُشْرَكْ بِه ِِ تُؤْمِنُوا  ۚ  فَالْحُكْمُ لِلَّهِ الْعَلِيِّ الْكَبِيرِ
Huwa Al-Ladhī Yurīkum 'Āyātihi Wa Yunazzilu Lakum Mina As-Samā'i Rizqāan  ۚ  Wa Mā Yatadhakkaru 'Illā Man Yunību َ040-013 Shĩ ne Wanda ke nũna muku ãyõyinSa, kuma Ya saukar da arziki daga sama sabõda ku, kuma bãbu mai yin tunãni fãce mai mayar da al'amari ga Allah. هُوَ الَّذِي يُرِيكُمْ آيَاتِه ِِ وَيُنَزِّلُ لَكُمْ مِنَ السَّمَاءِ رِزْقا ً  ۚ  وَمَا يَتَذَكَّرُ إِلاَّ مَنْ يُنِيبُ
d Al-Laha Mukhlişīna Lahu Ad-Dīna Wa Law Kariha Al-Kāfirūna َ040-014 Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi. فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ
Rafī`u Ad-Darajāti Dhū Al-`Arshi Yulqī Ar-Rūĥa Min 'Amrihi `Alá Man Yashā'u Min `Ibādihi Liyundhira Yawma At-Talāqi َ040-015 Mai ɗaukaka darajõji (dõmin mũminai), Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar gamuwa. رَفِيعُ الدَّرَجَاتِ ذُو الْعَرْشِ يُلْقِي الرُّوحَ مِنْ أَمْرِه ِِ عَلَى مَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِه ِِ لِيُنْذِرَ يَوْمَ التَّلاَقِ
Yawma Humrizūna  ۖ  Lā Yakhfá `Alá Al-Lahi Minhum Shay'un  ۚ  Limani Al-Mulku Al-Yawma  ۖ  Lillahi Al-Wāĥidi Al-Qahhāri َ040-016 Rãnar da suke bayyanannu, bãbu wani abu daga gare su wanda yake iya bõyuwa ga Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa. يَوْمَ هُمْ بَارِزُونَ  ۖ  لاَ يَخْفَى عَلَى اللَّهِ مِنْهُمْ شَيْء ٌ  ۚ  لِمَنِ الْمُلْكُ الْيَوْمَ  ۖ  لِلَّهِ الْوَاحِدِ الْقَهَّارِ
Al-Yawma Tujzá Kullu Nafsin Bimā Kasabat  ۚ  Lā Žulma Al-Yawma  ۚ  'Inna Al-Laha Sarī`u Al-Ĥisābi َ040-017 Yau anã sãka wa kõwane rai a game da abin da ya aikata, bãbu zãlunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisãbi ne. الْيَوْمَ تُجْزَى كُلُّ نَفْس ٍ بِمَا كَسَبَتْ  ۚ  لاَ ظُلْمَ الْيَوْمَ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ
Wa 'Andhirhum Yawma Al-'Āzifati 'Idhi Al-Qulūbu Ladá Al-Ĥanājiri Kāžimīna  ۚ  Mā Lilžžālimīna Min Ĥamīmin Wa Lā Shafī`in Yuţā`u َ040-018 Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar (Sã'a) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu). وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ الآزِفَةِ إِذِ الْقُلُوبُ لَدَى الْحَنَاجِرِ كَاظِمِينَ  ۚ  مَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ حَمِيم ٍ وَلاَ شَفِيع ٍ يُطَاعُ
Ya`lamu Khā'inata Al-'A`yuni Wa Mā Tukh Aş-Şudūru َ040-019 (Allah) Ya san yaudarar idãnu da abin da ƙirãza ke ɓõyẽwa. يَعْلَمُ خَائِنَةَ الأَعْيُنِ وَمَا تُخْفِي الصُّدُورُ
Wa Allāhu Yaqđī  ۖ  Bil-Ĥaqqi Wa Al-Ladhīna Yad`ūna Min Dūnihi Lā Yaqđūna  ۗ  Bishay'in 'Inna Al-Laha Huwa As-Samī`u Al-Başīru َ040-020 Kuma Allah Shĩ ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, waninSa,bã su yin hukunci da kõme. Lalle Allah, Shĩ ne Mai ji, Mai gani. وَاللَّهُ يَقْضِي بِالْحَقِّ  ۖ  وَالَّذِينَ يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ لاَ يَقْضُونَ بِشَيْء ٍ  ۗ  إِنَّ اللَّهَ هُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ
'Awa Lam Yasīrū Fī Al-'Arđi Fayanžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Ladhīna Kānū Min  ۚ  Qablihim Kānū Hum 'Ashadda Minhum Qūwatan Wa 'Āthārāan Al-'Arđi Fa'akhadhahumu Al-Lahu Bidhunūbihim Wa Mā Kāna Lahum Mini Al-Lahi Min Wāqin َ040-021 Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu. Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah. أَوَ لَمْ يَسِيرُوا فِي الأَرْضِ فَيَنظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ كَانُوا مِنْ  ۚ  قَبْلِهِمْ كَانُوا هُمْ أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّة ً وَآثَارا ً فِي الأَرْضِ فَأَخَذَهُمُ اللَّهُ بِذُنُوبِهِمْ وَمَا كَانَ لَهُمْ مِنِ اللَّهِ مِنْ وَاق ٍ
Dhālika Bi'annahum Kānat Ta'tīhim Rusuluhum Bil-Bayyināti Fakafarū Fa'akhadhahumu Al-Lahu  ۚ  'Innahu Qawīyun Shadīdu Al-`Iqābi َ040-022 Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azãba. ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ كَانَتْ تَأْتِيهِمْ رُسُلُهُمْ بِالْبَيِّنَاتِ فَكَفَرُوا فَأَخَذَهُمُ اللَّهُ  ۚ  إِنَّه ُُ قَوِيّ ٌ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Wa Laqad 'Arsalnā Mūsá Bi'āyātinā Wa Sulţānin Mubīnin َ040-023 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã a game da ãyõyinMu da wani dalĩli bayyananne. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَى بِآيَاتِنَا وَسُلْطَان ٍ مُبِين ٍ
'Ilá Fir`awna Wa Hāmāna Wa Qārūna Faqālū Sāĥirun Kadhdhābun َ040-024 Zuwa ga Fir'auna da Hãmãna da Kãrũna, sai suka ce: "Mai sihiri ne, maƙaryaci." إِلَى فِرْعَوْنَ وَهَامَانَ وَقَارُونَ فَقَالُوا سَاحِر ٌ كَذَّاب ٌ
Falammā Jā'ahum Bil-Ĥaqqi Min `Indinā Qālū Aqtulū 'Abnā'a Al-Ladhīna 'Āmanū Ma`ahu Wa Astaĥyū Nisā'ahum  ۚ  Wa Mā Kaydu Al-Kāfirīna 'Illā Fī Đalālin َ040-025 Sa'an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: "Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu." Kuma mugun shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata. فَلَمَّا جَاءَهُمْ بِالْحَقِّ مِنْ عِنْدِنَا قَالُوا اقْتُلُوا أَبْنَاءَ الَّذِينَ آمَنُوا مَعَه ُُ وَاسْتَحْيُوا نِسَاءَهُمْ  ۚ  وَمَا كَيْدُ الْكَافِرِينَ إِلاَّ فِي ضَلاَل ٍ
Wa Qāla Fir`awnu Dharūnī 'Aqtul Mūsá Wa Līad`u Rabbahu  ۖ  'Innī 'Akhāfu 'An Yubaddila Dīnakum 'Aw 'An Yužhira Fī Al-'Arđi Al-Fasāda َ040-026 Kuma Fir'auna ya ce: "Ku bar ni in kashe Mũsã, kuma shĩ, ya kirãyi Ubangijinsa. Lalle ne nĩ, inã tsõron ya musanya addininku, kõ kuwa ya bayyana ɓarna a cikin kasã." وَقَالَ فِرْعَوْنُ ذَرُونِي أَقْتُلْ مُوسَى وَلْيَدْعُ رَبَّهُ~ُ  ۖ  إِنِّي أَخَافُ أَنْ يُبَدِّلَ دِينَكُمْ أَوْ أَنْ يُظْهِرَ فِي الأَرْضِ الْفَسَادَ
Wa Qāla Mūsá 'Innī `Udhtu Birabbī Wa Rabbikum Min Kulli Mutakabbirin Lā Yu'uminu Biyawmi Al-Ĥisābi َ040-027 Kuma Mũsã ya ce: "Lalle nĩ, nã nẽmi tsari da Ubangijĩna kuma Ubangijinku, daga dukan makangari, wanda bã ya ĩmani da rãnar Hisãbi." وَقَالَ مُوسَى إِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ مِنْ كُلِّ مُتَكَبِّر ٍ لاَ يُؤْمِنُ بِيَوْمِ الْحِسَابِ
Wa Qāla Rajulun Mu'uminun Min 'Āli Fir`awna Yaktumu 'Īmānahu 'Ataqtulūna Rajulāan 'An Yaqūla Rabbiya Al-Lahu Wa Qad Jā'akum Bil-Bayyināti Min Rabbikum  ۖ  Wa 'In Yaku Kādhibāan Fa`alayhi Kadhibuhu  ۖ  Wa 'In Yaku Şādiqāan Yuşibkum Ba`đu Al-Ladhī Ya`idukum  ۖ  'Inna Al-Laha Lā Yahdī Man Huwa Musrifun Kadhdhābun َ040-028 Kuma wani namiji mũmini daga dangin Fir'auna, yanã bõye ĩmãninsa, ya ce: "Ashe, za ku kashe mutum dõmin ya ce Ubangijina Allah ne, alhãli kuwa haƙĩƙa ya zo muku da hujjõji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan yã kasance maƙaryaci ne, to, ƙaryarsa na kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sãshen abin da yake yi muku wa'adi zai sãme ku. Lalle ne Allah bã Ya shiryar da wanda yake mai barna, mai yawan ƙarya." وَقَالَ رَجُل ٌ مُؤْمِن ٌ مِنْ آلِ فِرْعَوْنَ يَكْتُمُ إِيمَانَهُ~ُ أَتَقْتُلُونَ رَجُلاً أَنْ يَقُولَ رَبِّيَ اللَّهُ وَقَدْ جَاءَكُمْ بِالْبَيِّنَاتِ مِنْ رَبِّكُمْ  ۖ  وَإِنْ يَكُ كَاذِبا ً فَعَلَيْهِ كَذِبُه ُُ  ۖ  وَإِنْ يَكُ صَادِقا ً يُصِبْكُمْ بَعْضُ الَّذِي يَعِدُكُمْ  ۖ  إِنَّ اللَّهَ لاَ يَهْدِي مَنْ هُوَ مُسْرِف ٌ كَذَّاب ٌ
Yā Qawmi Lakumu Al-Mulku Al-Yawma Žāhirīna Fī Al-'Arđi Faman Yanşurunā Min Ba'si Al-Lahi 'In Jā'anā  ۚ  Qāla Fir`awnu Mā 'Urīkum 'Illā Mā 'Ará Wa Mā 'Ahdīkum 'Illā Sabīla Ar-Rashādi َ040-029 "Yã kũ mutãnẽna! Kunã da mulki a yau, kuma kũ ne marinjãya a cikin kasã to wãne ne zai taimake mu daga azãbar Allah idan ta zo mana?" Fir'auna ya ce: "Bã ni nũnamuku kõme face abin da na gani, kuma ba ni shiryar da ku, sai ga hanyar shiryuwa." يَاقَوْمِ لَكُمُ الْمُلْكُ الْيَوْمَ ظَاهِرِينَ فِي الأَرْضِ فَمَنْ يَنصُرُنَا مِنْ بَأْسِ اللَّهِ إِنْ جَاءَنَا قَالَ  ۚ  فِرْعَوْنُ مَا أُرِيكُمْ إِلاَّ مَا أَرَى وَمَا أَهْدِيكُمْ إِلاَّ سَبِيلَ الرَّشَادِ
Wa Qāla Al-Ladhī 'Āmana Yā Qawmi 'Innī 'Akhāfu `Alaykum Mithla Yawmi Al-'Aĥzābi َ040-030 Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽnã! Lallene, nĩ, inã yi muku tsõron kwatankwacin rãnar ƙungiyõyi." وَقَالَ الَّذِي آمَنَ يَاقَوْمِ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ مِثْلَ يَوْمِ الأَحْزَابِ
Mithla Da'bi Qawmi Nūĥin Wa `Ādin Wa Thamūda Wa Al-Ladhīna Min Ba`dihim  ۚ  Wa Mā Al-Lahu Yurīdu Žulmāan Lil`ibādi َ040-031 "Kwatankwacin al'adar mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da waɗanda ke a bãyansu. Kuma Allah bã Ya nufin zãlunci ga bãyinSa." مِثْلَ دَأْبِ قَوْمِ نُوح ٍ وَعَاد ٍ وَثَمُودَ وَالَّذِينَ مِنْ بَعْدِهِمْ  ۚ  وَمَا اللَّهُ يُرِيدُ ظُلْما ً لِلْعِبَادِ
Wa Yāqawmi 'Innī 'Akhāfu `Alaykum Yawma At-Tanādi َ040-032 "Kuma ya mutãnẽna! Lallenĩ, inã yi muku tsõron rãnar kiran jũna." وَيَاقَوْمِ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ يَوْمَ التَّنَادِ
Yawma Tuwallūna Mudbirīna Mā Lakum Mina Al-Lahi Min `Āşimin  ۗ  Wa Man Yuđlili Al-Lahu Famā Lahu Min Hādin َ040-033 "A rãnar da zã ku jũya, kunã mãsu bãyar da bãya (gudãne) bã ku da wani mai tsaro daga Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa." يَوْمَ تُوَلُّونَ مُدْبِرِينَ مَا لَكُمْ مِنَ اللَّهِ مِنْ عَاصِم ٍ  ۗ  وَمَنْ يُضْلِلِ اللَّهُ فَمَا لَه ُُ مِنْ هَاد ٍ
Wa Laqad Jā'akum Yūsufu Min Qablu Bil-Bayyināti Famā ZiltumShakkin Mimmā Jā'akum Bihi  ۖ  Ĥattá 'Idhā Halaka Qultum Lan Yab`atha Al-Lahu Min Ba`dihi Rasūlāan  ۚ  Kadhālika Yuđillu Al-Lahu Man Huwa Musrifun Murtābun َ040-034 "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da ya halaka kuka ce, 'Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa.' Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka." وَلَقَدْ جَاءَكُمْ يُوسُفُ مِنْ قَبْلُ بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا زِلْتُمْ فِي شَكّ ٍ مِمَّا جَاءَكُمْ بِه ِِ  ۖ  حَتَّى إِذَا هَلَكَ قُلْتُمْ لَنْ يَبْعَثَ اللَّهُ مِنْ بَعْدِه ِِ رَسُولا ً  ۚ  كَذَلِكَ يُضِلُّ اللَّهُ مَنْ هُوَ مُسْرِف ٌ مُرْتَاب ٌ
Al-Ladhīna Yujādilūna Fī 'Āyāti Al-Lahi Bighayri Sulţānin 'Atāhum  ۖ  Kabura Maqtāan `Inda Al-Lahi Wa `Inda Al-Ladhīna 'Āmanū  ۚ  Kadhālika Yaţba`u Al-Lahu `Alá Kulli Qalbi Mutakabbirin Jabbārin َ040-035 "Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai tĩlastãwa." الَّذِينَ يُجَادِلُونَ فِي آيَاتِ اللَّهِ بِغَيْرِ سُلْطَانٍ أَتَاهُمْ  ۖ  كَبُرَ مَقْتاً عِنْدَ اللَّهِ وَعِنْدَ الَّذِينَ آمَنُوا  ۚ  كَذَلِكَ يَطْبَعُ اللَّهُ عَلَى كُلِّ قَلْبِ مُتَكَبِّر ٍ جَبَّار ٍ
Wa Qāla Fir`awnu Yā Hāmānu Abni Lī Şarĥāan La`allī 'Ablughu Al-'Asbāba َ040-036 Kuma Fir'auna ye ce, "Yã Hãmana! Ka gina mini bẽne, dammãnĩna zã ni isa ga ƙõfõfi." وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَا هَامَانُ ابْنِ لِي صَرْحا ً لَعَلِّي أَبْلُغُ الأَسْبَابَ
'Asbāba As-Samāwāti Fa'aţţali`a 'Ilá 'Ilahi Mūsá Wa 'Innī La'ažunnuhu Kādhibāan  ۚ  Wa Kadhalika Zuyyina Lifir`awna Sū'u `Amalihi Wa Şudda `Ani As-Sabīli  ۚ  Wa Mā Kaydu Fir`awna 'Illā Fī Tabābin َ040-037 "¡õfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci." Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir'auna mũnãnan aikinsakuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama ba fãce yanã a cikin hasãra." أَسْبَابَ السَّمَاوَاتِ فَأَطَّلِعَ إِلَى إِلَه ِِ مُوسَى وَإِنِّي لَأَظُنُّه ُُ كَاذِبا ً  ۚ  وَكَذَلِكَ زُيِّنَ لِفِرْعَوْنَ سُوءُ عَمَلِه ِِ وَصُدَّ عَنِ السَّبِيلِ  ۚ  وَمَا كَيْدُ فِرْعَوْنَ إِلاَّ فِي تَبَاب ٍ
Wa Qāla Al-Ladhī 'Āmana Yā Qawmi Attabi`ūnī 'Ahdikum Sabīla Ar-Rashādi َ040-038 Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bĩ ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa." وَقَالَ الَّذِي آمَنَ يَاقَوْمِ اتَّبِعُونِي أَهْدِكُمْ سَبِيلَ الرَّشَادِ
Yā Qawmi 'Innamā Hadhihi Al-Ĥayā Atu Ad-Dunyā Matā`un Wa 'Inna Al-'Ākhirata Hiya Dāru Al-Qarāri َ040-039 "Kuma ya mutãnẽna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata." يَاقَوْمِ إِنَّمَا هَذِهِ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا مَتَاع ٌ وَإِنَّ الآخِرَةَ هِيَ دَارُ الْقَرَارِ
Man `Amila Sayyi'atan Falā Yujzá 'Illā Mithlahā  ۖ  Wa Man `Amila Şāliĥāan Min Dhakarin 'Aw 'Unthá Wa Huwa Mu'uminun Fa'ūlā'ika Yadkhulūna Al-Jannata Yurzaqūna Fīhā Bighayri Ĥisābin َ040-040 "Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba." مَنْ عَمِلَ سَيِّئَة ً فَلاَ يُجْزَى إِلاَّ مِثْلَهَا  ۖ  وَمَنْ عَمِلَ صَالِحا ً مِنْ ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَى وَهُوَ مُؤْمِن ٌ فَأُوْلَائِكَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ يُرْزَقُونَ فِيهَا بِغَيْرِ حِسَاب ٍ
Wa Yāqawmi Mā Lī 'Ad`ūkum 'Ilá An-Najāati Wa Tad`ūnanī 'Ilá An-Nāri َ040-041 "Kuma ya mutãnẽna! Me ya sãme ni, inã kiran ku zuwa ga tsĩra, kuma kunã kira na zuwa ga wutã?" وَيَاقَوْمِ مَا لِي أَدْعُوكُمْ إِلَى النَّجَاةِ وَتَدْعُونَنِي إِلَى النَّارِ
Tad`ūnanī Li'kfura Bil-Lahi Wa 'Ushrika Bihi Mā Laysa Lī Bihi `Ilmun Wa 'Anā 'Ad`ūkum 'Ilá Al-`Azīzi Al-Ghaffāri َ040-042 "Kuna kira na zuwa ga in kãfirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da abin da bãbu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni inã kiran ku zuwa ga Mabuwãyi, Mai gãfara." تَدْعُونَنِي لِأكْفُرَ بِاللَّهِ وَأُشْرِكَ بِه ِِ مَا لَيْسَ لِي بِه ِِ عِلْم ٌ وَأَنَا أَدْعُوكُمْ إِلَى الْعَزِيزِ الْغَفَّارِ
Lā Jarama 'Annamā Tad`ūnanī 'Ilayhi Laysa Lahu Da`watun Ad-Dunyā Wa Lā Fī Al-'Ākhirati Wa 'Anna Maraddanā 'Ilá Al-Lahi Wa 'Anna Al-Musrifīna Hum 'Aşĥābu An-Nāri َ040-043 "Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, bã ya da wani kira a cikin dũniya, kuma bã shi da shi a Lãhira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take, kuma lalle mabarnata sũ ne 'yan wutã." لاَ جَرَمَ أَنَّمَا تَدْعُونَنِي إِلَيْهِ لَيْسَ لَه ُُ دَعْوَة ٌ فِي الدُّنْيَا وَلاَ فِي الآخِرَةِ وَأَنَّ مَرَدَّنَا إِلَى اللَّهِ وَأَنَّ الْمُسْرِفِينَ هُمْ أَصْحَابُ النَّارِ
Fasatadhkurūna Mā 'Aqūlu Lakum  ۚ  Wa 'Ufawwiđu 'Amrī 'Ilá Al-Lahi  ۚ  'Inna Al-Laha Başīrun Bil-`Ibādi َ040-044 "To zã ku ambaci abin da nake gaya muku, kuma inã fawwala al'amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai gani ne ga bãyinSa." فَسَتَذْكُرُونَ مَا أَقُولُ لَكُمْ  ۚ  وَأُفَوِّضُ أَمْرِي إِلَى اللَّهِ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ بَصِير ٌ بِالْعِبَادِ
Fawaqāhu Al-Lahu Sayyi'āti Mā Makarū  ۖ  Wa Ĥāqa Bi'āli Fir`awna Sū'u Al-`Adhābi َ040-045 Sai Allah Ya tsare shi daga mũnãnan abũbuwa da suka yi na mãkirci, kuma mummunar azãba ta wajaba ga mutãnen Fir'auna. فَوَقَاهُ اللَّهُ سَيِّئَاتِ مَا مَكَرُوا  ۖ  وَحَاقَ بِآلِ فِرْعَوْنَ سُوءُ الْعَذَابِ
An-Nāru Yu`rađūna `Alayhā Ghudūwāan Wa `Ashīyāan  ۖ  Wa Yawma Taqūmu As-Sā`atu 'Adkhilū 'Āla Fir`awna 'Ashadda Al-`Adhābi َ040-046 Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, "Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba." النَّارُ يُعْرَضُونَ عَلَيْهَا غُدُوّا ً وَعَشِيّا ً  ۖ  وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ أَدْخِلُوا آلَ فِرْعَوْنَ أَشَدَّ الْعَذَابِ
Wa 'Idh Yataĥājjūna Fī An-Nāri Fayaqūlu Ađ-Đu`afā'u Lilladhīna Astakbarū 'Innā Kunnā Lakum Taba`āan Fahal 'Antum Mughnūna `Annā Naşībāan Mina An-Nāri َ040-047 Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna (mabiya) su ce wa waɗanda suka kangara (shugabanni), "Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to, shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã?" وَإِذْ يَتَحَاجُّونَ فِي النَّارِ فَيَقُولُ الضُّعَفَاءُ لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا إِنَّا كُنَّا لَكُمْ تَبَعا ً فَهَلْ أَنْتُمْ مُغْنُونَ عَنَّا نَصِيبا ً مِنَ النَّارِ
Qāla Al-Ladhīna Astakbarū 'Innā Kullun Fīhā 'Inna Al-Laha Qad Ĥakama Bayna Al-`Ibādi َ040-048 Waɗanda suka kangara suka ce: "Lalle mũ duka munã a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakãnin bãyinSa." قَالَ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا إِنَّا كُلّ ٌ فِيهَا إِنَّ اللَّهَ قَدْ حَكَمَ بَيْنَ الْعِبَادِ
Wa Qāla Al-Ladhīna Fī An-Nāri Likhazanati Jahannama Ad`ū Rabbakum Yukhaffif `Annā Yawmāan Mina Al-`Adhābi َ040-049 Kuma waɗanda suke a cikin wutã suka ce wa matsaran Jahannama, "Ku rõki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana ,a yini ɗaya, daga azãba." وَقَالَ الَّذِينَ فِي النَّارِ لِخَزَنَةِ جَهَنَّمَ ادْعُوا رَبَّكُمْ يُخَفِّفْ عَنَّا يَوْما ً مِنَ الْعَذَابِ
Qālū 'Awa Lam Taku Ta'tīkum Rusulukum  ۖ  Bil-Bayyināti Qālū  ۚ  Balá Qālū  ۗ  Fād`ū Wa Mā Du`ā'u Al-Kāfirīna 'Illā Fī Đalālin َ040-050 Suka ce: "Ashe, Manzanninku ba su jẽ muku da hujjõji bayyanannu ba?" Suka ce: "Na'am, sun jẽ!" Suka ce: "To, ku rõƙa." Kuma rõƙon kãfirai bai zamo ba fãce a cikin ɓata. قَالُوا أَوَ لَمْ تَكُ تَأْتِيكُمْ رُسُلُكُمْ  ۖ  بِالْبَيِّنَاتِ قَالُوا  ۚ  بَلَى قَالُوا  ۗ  فَادْعُوا وَمَا دُعَاءُ الْكَافِرِينَ إِلاَّ فِي ضَلاَل ٍ
'Innā Lananşuru Rusulanā Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Fī Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Yawma Yaqūmu Al-'Ash/hādu َ040-051 Lalle Mũ, hakĩka, Munã taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, a cikin rãyuwar dũniya da rãnar da shaidu ke tsayãwa. إِنَّا لَنَنصُرُ رُسُلَنَا وَالَّذِينَ آمَنُوا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَيَوْمَ يَقُومُ الأَشْهَادُ
Yawma Lā Yanfa`u Až-Žālimīna Ma`dhiratuhum  ۖ  Wa Lahumu Al-La`natu Wa Lahum Sū'u Ad-Dāri َ040-052 Rãnar da uzurin azzãlumai bã ya amfãninsu, kuma sunã da la'ana, kuma sunã da mũnin gida. يَوْمَ لاَ يَنفَعُ الظَّالِمِينَ مَعْذِرَتُهُمْ  ۖ  وَلَهُمُ اللَّعْنَةُ وَلَهُمْ سُوءُ الدَّارِ
Wa Laqad 'Ātaynā Mūsá Al-Hudá Wa 'Awrathnā Banī 'Isrā'īla Al-Kitāba َ040-053 Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã shiriya, kuma Mun gãdar da Banĩ Isrã'ĩla Littãfi. وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْهُدَى وَأَوْرَثْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ الْكِتَابَ
Hudáan Wa Dhikrá Li'wlī Al-'Albābi َ040-054 Shiryarwa da tunãwa ga ma'abũta hankali. هُدى ً وَذِكْرَى لِأولِي الأَلْبَابِ
Fāşbir 'Inna Wa`da Al-Lahi Ĥaqqun Wa Astaghfir Lidhanbika Wa Sabbiĥ Biĥamdi Rabbika Bil-`Ashīyi Wa Al-'Ibkāri َ040-055 Sabõda haka, ka yi haƙuri, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nẽmi gãfara ga zunubinka, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, maraice da kuma wãyẽwar sãfiya. فَاصْبِرْ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقّ ٌ وَاسْتَغْفِرْ لِذَنْبِكَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ بِالْعَشِيِّ وَالإِبْكَارِ
'Inna Al-Ladhīna Yujādilūna Fī 'Āyāti Al-Lahi Bighayri Sulţānin 'Atāhum  ۙ  'In Fī Şudūrihim 'Illā Kibrun Mā Hum Bibālighīhi  ۚ  Fāsta`idh Bil-Lahi  ۖ  'Innahu Huwa As-Samī`u Al-Başīru َ040-056 Lalle waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, bã game da wani dalĩli wanda ya jẽ musu ba, bãbu kõme a cikin kirãzansu, fãce girman kai, ba su zama mãsu isa ga gũrinsu ba, sabõda haka ka nẽmi tsari daga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Mai gani. إِنَّ الَّذِينَ يُجَادِلُونَ فِي آيَاتِ اللَّهِ بِغَيْرِ سُلْطَانٍ أَتَاهُمْ  ۙ  إِنْ فِي صُدُورِهِمْ إِلاَّ كِبْر ٌ مَا هُمْ بِبَالِغِيه ِِ  ۚ  فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ  ۖ  إِنَّه ُُ هُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ
Lakhalqu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi 'Akbaru Min Khalqi An-Nāsi Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna َ040-057 Lalle halittar sammai da ƙasã, ita ce mafi girma daga halittar mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. لَخَلْقُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ أَكْبَرُ مِنْ خَلْقِ النَّاسِ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ
Wa Mā Yastawī Al-'A`má Wa Al-Başīru Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Wa Lā Al-Musī'u  ۚ  Qalīlāan Mā Tatadhakkarūna َ040-058 Kuma makãho da mai gani bã su daidaita kuma waɗanda suka yi ĩmãni suka, aikata ayyukan ƙwarai da mai mũnanãwa bã su daidaita. Kaɗan ƙwarai, kuke yin tunãni. وَمَا يَسْتَوِي الأَعْمَى وَالْبَصِيرُ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَلاَ الْمُسِيءُ  ۚ  قَلِيلا ً مَا تَتَذَكَّرُونَ
'Inna As-Sā`ata La'ātiyatun Lā Rayba Fīhā Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Yu'uminūna َ040-059 Lalle Sa'a, haƙĩƙa mai zuwa ce, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni. إِنَّ السَّاعَةَ لَآتِيَة ٌ لاَ رَيْبَ فِيهَا وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يُؤْمِنُونَ
Wa Qāla Rabbukum Ad`ūnī 'Astajib Lakum  ۚ  'Inna Al-Ladhīna Yastakbirūna `An `Ibādatī Sayadkhulūna Jahannama Dākhirīna َ040-060 Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu." وَقَالَ رَبُّكُمْ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ  ۚ  إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ
Al-Lahu Al-Ladhī Ja`ala Lakumu Al-Layla Litaskunū Fīhi Wa An-Nahāra Mubşirāan  ۚ  'Inna Al-Laha Ladhū Fađlin `Alá An-Nāsi Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Yashkurūna َ040-061 Allah ne Wanda Ya sanya muku dare dõmin ku natsu a cikinsa, da rãna mai gãnarwa. Lalle Allah, haƙĩƙa, Ma'abũcin falala ne a kan mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa. اللَّهُ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ اللَّيْلَ لِتَسْكُنُوا فِيه ِِ وَالنَّهَارَ مُبْصِرا ً  ۚ  إِنَّ اللَّهَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى النَّاسِ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَشْكُرُونَ
Dhalikumu Al-Lahu Rabbukum Khāliqu Kulli Shay'in Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  Fa'annā Tu'ufakūna َ040-062 Wancan shine Allah Ubangijinku, Mahaliccin dukan kõme, bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku? ذَلِكُمُ اللَّهُ رَبُّكُمْ خَالِقُ كُلِّ شَيْء ٍ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ  ۖ  فَأَنَّا تُؤْفَكُونَ
Kadhālika Yu'ufaku Al-Ladhīna Kānū Bi'āyāti Al-Lahi Yajĥadūna َ040-063 Kamar haka ake karkatar da waɗanda suka kasance sunã jãyayya game da ãyõyin Allah. كَذَلِكَ يُؤْفَكُ الَّذِينَ كَانُوا بِآيَاتِ اللَّهِ يَجْحَدُونَ
Al-Lahu Al-Ladhī Ja`ala Lakumu Al-'Arđa Qarārāan Wa As-Samā'a Binā'an Wa Şawwarakum Fa'aĥsana Şuwarakum Wa Razaqakum Mina Aţ-Ţayyibāti  ۚ  Dhalikumu Al-Lahu Rabbukum  ۖ  Fatabāraka Al-Lahu Rabbu Al-`Ālamīna َ040-064 Allah ne Ya sanya muku kasã tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku,, kuma Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana. اللَّهُ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأَرْضَ قَرَارا ً وَالسَّمَاءَ بِنَاء ً وَصَوَّرَكُمْ فَأَحْسَنَ صُوَرَكُمْ وَرَزَقَكُمْ مِنَ الطَّيِّبَاتِ  ۚ  ذَلِكُمُ اللَّهُ رَبُّكُمْ  ۖ  فَتَبَارَكَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ
Huwa Al-Ĥayyu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Fād`ūhu Mukhlişīna Lahu Ad-Dīna  ۗ  Al-Ĥamdu Lillahi Rabbi Al-`Ālamīna َ040-065 Shĩ ne Mai rai, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Sabõda haka ku kira Shi, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi. Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. هُوَ الْحَيُّ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ فَادْعُوه ُُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ  ۗ  الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Qul 'Innī Nuhītu 'An 'A`buda Al-Ladhīna Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi Lammā Jā'aniya Al-Bayyinātu Min Rabbī Wa 'Umirtu 'An 'Uslima Lirabbi Al-`Ālamīna َ040-066 Ka ce: "Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu." قُلْ إِنِّي نُهِيتُ أَنْ أَعْبُدَ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ لَمَّا جَاءَنِيَ الْبَيِّنَاتُ مِنْ رَبِّي وَأُمِرْتُ أَنْ أُسْلِمَ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ
Huwa Al-Ladhī Khalaqakum Min Turābin Thumma Min Nuţfatin Thumma Min `Alaqatin Thumma Yukhrijukum Ţiflāan Thumma Litablughū 'Ashuddakum Thumma Litakūnū Shuyūkhāan  ۚ  Wa Minkum Man Yutawaffá Min Qablu  ۖ  Wa Litablughū 'Ajalāan Musammáan Wa La`allakum Ta`qilūna َ040-067 Shĩ ne Wanda Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga maniyyi, sa'an nan daga sãren jini, sa'an nan Ya fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan dõmin ku isa ga cikar ƙarfinku sa'an nan dõmin ku kasance tsõfaffi, kuma daga cikinku, akwai wanda ake karɓar ransa a gabãnin haka, kuma dõmin ku isa ga ajali ambatacce, kuma dammãninku ko zã ku hankalta. هُوَ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ تُرَاب ٍ ثُمَّ مِنْ نُطْفَة ٍ ثُمَّ مِنْ عَلَقَة ٍ ثُمَّ يُخْرِجُكُمْ طِفْلا ً ثُمَّ لِتَبْلُغُوا أَشُدَّكُمْ ثُمَّ لِتَكُونُوا شُيُوخا ً  ۚ  وَمِنْكُمْ مَنْ يُتَوَفَّى مِنْ قَبْلُ  ۖ  وَلِتَبْلُغُوا أَجَلا ً مُسَمّى ً وَلَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ
Huwa Al-Ladhī Yuĥyī Wa Yumītu  ۖ  Fa'idhā Qađá 'Amrāan Fa'innamā Yaqūlu Lahu Kun Fayakūnu َ040-068 Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukunta wani al'amari, to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance sai yana kasancewa (kamar yadda ake bukatar sa.) هُوَ الَّذِي يُحْيِي وَيُمِيتُ  ۖ  فَإِذَا قَضَى أَمْرا ً فَإِنَّمَا يَقُولُ لَه ُُ كُنْ فَيَكُونُ
'Alam Tará 'Ilá Al-Ladhīna Yujādilūna Fī 'Āyāti Al-Lahi 'Anná Yuşrafūna َ040-069 Ashe, ba ka gani ba ga waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, yadda ake karkatar da su? أَلَمْ تَرَى إِلَى الَّذِينَ يُجَادِلُونَ فِي آيَاتِ اللَّهِ أَنَّى يُصْرَفُونَ
Al-Ladhīna Kadhdhabū Bil-Kitābi Wa Bimā 'Arsalnā Bihi Rusulanā  ۖ  Fasawfa Ya`lamūna َ040-070 Waɗanda suka ƙaryata, game da Littãfin, kuma da abin da Muka aika Manzanninmu da shi. To, za su sani. الَّذِينَ كَذَّبُوا بِالْكِتَابِ وَبِمَا أَرْسَلْنَا بِه ِِ رُسُلَنَا  ۖ  فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
'Idhi Al-'Aghlālu Fī 'A`nāqihim Wa As-Salāsilu Yusĥabūna َ040-071 A lõkacin da ƙuƙumma suke a cikin wuyõyinsu, da sarƙõƙi anã jan su. إِذِ الأَغْلاَلُ فِي أَعْنَاقِهِمْ وَالسَّلاَسِلُ يُسْحَبُونَ
Al-Ĥamīmi Thumma Fī An-Nāri Yusjarūna َ040-072 A cikin ruwan zãfi, sa'an nan a cikin wutã anã babbaka su. فِي الْحَمِيمِ ثُمَّ فِي النَّارِ يُسْجَرُونَ
Thumma Qīla Lahum 'Ayna Mā Kuntum Tushrikūna َ040-073 Sa'an nan a ce musu, "Ina abin da kuka kasance kunã shirki da shi" ثُمَّ قِيلَ لَهُمْ أَيْنَ مَا كُنْتُمْ تُشْرِكُونَ
Min Dūni Al-Lahi  ۖ  Qālū Đallū `Annā Bal Lam Nakun Nad`ū Min Qablu Shay'āan  ۚ  Kadhālika Yuđillu Al-Lahu Al-Kāfirīna َ040-074 "Wanin Allah?" Suka ce: "Sun ɓace mana. Ã'a, ba mu kasance munã kiran kõme ba a gabani."Kamar wancan ne Allah Yake ɓatar da kãfirai. مِنْ دُونِ اللَّهِ  ۖ  قَالُوا ضَلُّوا عَنَّا بَلْ لَمْ نَكُنْ نَدْعُو مِنْ قَبْلُ شَيْئا ً  ۚ  كَذَلِكَ يُضِلُّ اللَّهُ الْكَافِرِينَ
Dhālikum Bimā Kuntum Tafraĥūna Fī Al-'Arđi Bighayri Al-Ĥaqqi Wa Bimā Kuntum Tamraĥūna َ040-075 Wancan dõmin abin da kuka kasance ne kunã farin ciki da shi, a cikin ƙasã, bã da hakki ba, kuma da abin da kuka kasance kunã yi na nishãɗi. ذَلِكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَفْرَحُونَ فِي الأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَبِمَا كُنْتُمْ تَمْرَحُونَ
Adkhulū 'Abwāba Jahannama Khālidīna Fīhā  ۖ  Fabi'sa Math Al-Mutakabbirīna َ040-076 Ku shiga kofõfin Jahannama kunã madawwama a cikinta. To, mazaunin mãsu girman kai yã mũnana. ادْخُلُوا أَبْوَابَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا  ۖ  فَبِئْسَ مَثْوَى الْمُتَكَبِّرِينَ
Fāşbir 'Inna Wa`da Al-Lahi Ĥaqqun  ۚ  Fa'immā Nuriyannaka Ba`đa Al-Ladhī Na`iduhum 'Aw Natawaffayannaka Fa'ilaynā Yurja`ūna َ040-077 Sabõda haka ka yi haƙuri. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. To, kõ dai lalle Mu nũna maka sãshen abin da Muka yi musu wa'adi da shi kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu ake mayar da su. فَاصْبِرْ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقّ ٌ  ۚ  فَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعْضَ الَّذِي نَعِدُهُمْ أَوْ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيْنَا يُرْجَعُونَ
Wa Laqad 'Arsalnā Rusulāan Min Qablika Minhum Man Qaşaşnā `Alayka Wa Minhum Man Lam Naqşuş `Alayka  ۗ  Wa Mā Kāna Lirasūlin 'An Ya'tiya Bi'āyatin 'Illā Bi'idhni Al-Lahi  ۚ  Fa'idhā Jā'a 'Amru Al-Lahi Quđiya Bil-Ĥaqqi Wa Khasira Hunālika Al-Mubţilūna َ040-078 Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka. Bã ya yiwuwa ga wani Manzo ya jẽ da wata ãyar mu'ujiza fãce da iznin Allah. Sa'an nan idan umurnin Allah ya jẽ, sai a yi hukunci da gaskiya, mãsu ɓãtãwa sun yi hasara a can. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلا ً مِنْ قَبْلِكَ مِنْهُمْ مَنْ قَصَصْنَا عَلَيْكَ وَمِنْهُمْ مَنْ لَمْ نَقْصُصْ عَلَيْكَ  ۗ  وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَنْ يَأْتِيَ بِآيَة ٍ إِلاَّ بِإِذْنِ اللَّهِ  ۚ  فَإِذَا جَاءَ أَمْرُ اللَّهِ قُضِيَ بِالْحَقِّ وَخَسِرَ هُنَالِكَ الْمُبْطِلُونَ
Al-Lahu Al-Ladhī Ja`ala Lakumu Al-'An`ām Litarkabū Minhā Wa Minhā Ta'kulūna َ040-079 Allah ne Wanda Ya sanya muku dabbõbi dõmin ku hau daga gare su, kuma daga gare su kuke ci. اللَّهُ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأَنعَام لِتَرْكَبُوا مِنْهَا وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
Wa Lakum Fīhā Manāfi`u Wa Litablughū `Alayhā Ĥājatan Fī Şudūrikum Wa `Alayhā Wa `Alá Al-Fulki Tuĥmalūna َ040-080 Kuma kunã da abũbuwan amfãni a cikinsu, kuma dõmin ku isar da wata buƙãta, a cikin ƙirãzanku a kansu kuma a kansu da a kan jirãge ake, ɗaukar ku. وَلَكُمْ فِيهَا مَنَافِعُ وَلِتَبْلُغُوا عَلَيْهَا حَاجَة ً فِي صُدُورِكُمْ وَعَلَيْهَا وَعَلَى الْفُلْكِ تُحْمَلُونَ
Wa Yurīkum 'Āyātihi Fa'ayya 'Āyāti Al-Lahi Tunkirūna َ040-081 Kuma Ya nũna muku ayõyinSa. To, wane ãyõyin Allah kuke musu? وَيُرِيكُمْ آيَاتِه ِِ فَأَيَّ آيَاتِ اللَّهِ تُنكِرُونَ
'Afalam Yasīrū Fī Al-'Arđi Fayanžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  Kānū 'Akthara Minhum Wa 'Ashadda Qūwatan Wa 'Āthārāan Al-'Arđi Famā 'Aghná `Anhum Mā Kānū Yaksibūna َ040-082 Ashe fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasã ba, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafi yawa daga gare su. Kuma sun fi tsananin ƙarfi, da (yawan) gurãbun sanã'õ'i a cikin ƙasã. To, abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su ba. أَفَلَمْ يَسِيرُوا فِي الأَرْضِ فَيَنظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ  ۚ  كَانُوا أَكْثَرَ مِنْهُمْ وَأَشَدَّ قُوَّة ً وَآثَارا ً فِي الأَرْضِ فَمَا أَغْنَى عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Falammā Jā'at/hum Rusuluhum Bil-Bayyināti Fariĥū Bimā `Indahum Mina Al-`Ilmi Wa Ĥāqa Bihim Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn َ040-083 A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu. فَلَمَّا جَاءَتْهُمْ رُسُلُهُمْ بِالْبَيِّنَاتِ فَرِحُوا بِمَا عِنْدَهُمْ مِنَ الْعِلْمِ وَحَاقَ بِهِمْ مَا كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُون
Falammā Ra'aw Ba'sanā Qālū 'Āmannā Bil-Lahi Waĥdahu Wa Kafarnā Bimā Kunnā Bihi Mushrikīna َ040-084 Sa'an nan a lõkacin da suka ga azãbarMu, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, Shi kaɗai, kuma mun kãfirta da abin da muka kasance munã shirki da shi." فَلَمَّا رَأَوْا بَأْسَنَا قَالُوا آمَنَّا بِاللَّهِ وَحْدَه ُُ وَكَفَرْنَا بِمَا كُنَّا بِه ِِ مُشْرِكِينَ
Falam Yaku Yanfa`uhum 'Īmānuhum Lammā Ra'aw Ba'sanā  ۖ  Sunnata Al-Lahi Allatī Qad Khalat Fī `Ibādihi  ۖ  Wa Khasira Hunālika Al-Kāfirūna َ040-085 To ĩmaninsu bai kasance yanã amfaninsu ba a lõkacin da suka ga azãbarMu. Hanyar Allah wadda ta gabãta a cikin bãyinSa. Kuma kãfirai sun yi hasãra a can. فَلَمْ يَكُ يَنْفَعُهُمْ إِيمَانُهُمْ لَمَّا رَأَوْا بَأْسَنَا  ۖ  سُنَّةَ اللَّهِ الَّتِي قَدْ خَلَتْ فِي عِبَادِه ِِ  ۖ  وَخَسِرَ هُنَالِكَ الْكَافِرُونَ
Next Sūrah