29) Sūrat Al-`Ankabūt

Printed format

29) سُورَة العَنكَبُوت

'Alif-Lām-Mīm َ029-001 A. L̃. M̃. أَلِف-لَام-مِيم
'Aĥasiba An-Nāsu 'An Yutrakū 'An Yaqūlū 'Āmannā Wa Hum Lā Yuftanūna َ029-002 Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmãni," alhãli kuwa bã zã a fitine su ba?" أَحَسِبَ النَّاسُ أَنْ يُتْرَكُوا أَنْ يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لاَ يُفْتَنُونَ
Wa Laqad Fatannā Al-Ladhīna Min Qablihim  ۖ  Falaya`lamanna Al-Lahu Al-Ladhīna Şadaqū Wa Laya`lamanna Al-Kādhibīna َ029-003 Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata. وَلَقَدْ فَتَنَّا الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ  ۖ  فَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ صَدَقُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْكَاذِبِينَ
'Am Ĥasiba Al-Ladhīna Ya`malūna As-Sayyi'āti 'An Yasbiqūnā  ۚ  Sā'a Mā Yaĥkumūna َ029-004 Kõ waɗanda ke aikata miyãgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntãwa ya mũnana. أَمْ حَسِبَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ أَنْ يَسْبِقُونَا  ۚ  سَاءَ مَا يَحْكُمُونَ
Man Kāna Yarjū Liqā'a Al-Lahi Fa'inna 'Ajala Al-Lahi La'ātin  ۚ  Wa Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu َ029-005 Wanda ya kasance yanã fãtan gamuwa da Al1ah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma (Allah) Shĩ ne Mai ji, Masani. مَنْ كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ اللَّهِ فَإِنَّ أَجَلَ اللَّهِ لَآت ٍ  ۚ  وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Wa Man Jāhada Fa'innamā Yujāhidu Linafsihi  ۚ  'Inna Al-Laha Laghanīyun `Ani Al-`Ālamīna َ029-006 Kuma wanda ya yi jihãdi, to, yanã yin jihãdin ne dõmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa waɗatacce ne daga barin tãlikai. وَمَنْ جَاهَدَ فَإِنَّمَا يُجَاهِدُ لِنَفْسِهِ~ِ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ لَغَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lanukaffiranna `Anhum Sayyi'ātihim Wa Lanajziyannahum 'Aĥsana Al-Ladhī Kānū Ya`malūna َ029-007 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã kankare musu miyãgun ayyukansu, kuma lalle Munã sãka musu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa. وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَحْسَنَ الَّذِي كَانُوا يَعْمَلُونَ
Wa Waşşaynā Al-'Insāna Biwālidayhi Ĥusnāan  ۖ  Wa 'In Jāhadāka Litushrika Bī Mā Laysa Laka Bihi `Ilmun Falā Tuţi`humā  ۚ  'Ilayya Marji`ukum Fa'unabbi'ukum Bimā Kuntum Ta`malūna َ029-008 Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatãwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta maka dõmin ka yi shirki da Ni game da abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'ã. Zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa. وَوَصَّيْنَا الإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ حُسْنا ً  ۖ  وَإِنْ جَاهَدَاكَ لِتُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِه ِِ عِلْم ٌ فَلاَ تُطِعْهُمَا  ۚ  إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lanudkhilannahum Aş-Şāliĥīna َ029-009 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã shigar da su a cikin mutãnen kirki. وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُدْخِلَنَّهُمْ فِي الصَّالِحِينَ
Wa Mina An-Nāsi Man Yaqūlu 'Āmannā Bil-Lahi Fa'idhā 'Ūdhiya Fī Al-Lahi Ja`ala Fitnata An-Nāsi Ka`adhābi Al-Lahi Wa La'in Jā'a Naşrun Min Rabbika Layaqūlunna 'Innā Kunnā Ma`akum  ۚ  'Awalaysa Al-Lahu Bi'a`lama Bimā Fī Şudūri Al-`Ālamīna َ029-010 Kuma daga cikin mutãne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmãni da Allah" sa'an nan idan aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutãne kamar azãbar Allah kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: "Lalle mũ mun kasance tãre da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin ƙirãzan halittunSa? وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَقُولُ آمَنَّا بِاللَّهِ فَإِذَا أُوذِيَ فِي اللَّهِ جَعَلَ فِتْنَةَ النَّاسِ كَعَذَابِ اللَّهِ وَلَئِنْ جَاءَ نَصْر ٌ مِنْ رَبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمْ  ۚ  أَوَلَيْسَ اللَّهُ بِأَعْلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ الْعَالَمِينَ
Wa Laya`lamanna Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Laya`lamanna Al-Munāfiqīna َ029-011 Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi ĩmãni kuma lalle Yanã sanin munfukai. وَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْمُنَافِقِينَ
Wa Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lilladhīna 'Āmanū Attabi`ū Sabīlanā Wa Lnaĥmil Khaţāyākum Wa Mā Hum Biĥāmilīna Min Khaţāyāhum Min Shay'in  ۖ  'Innahum Lakādhibūna َ029-012 Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Ku bi hanyarmu, kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhãli kõwa ba su zamo mãsu ɗauka da a kõme ba daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne. وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا اتَّبِعُوا سَبِيلَنَا وَلْنَحْمِلْ خَطَايَاكُمْ وَمَا هُمْ بِحَامِلِينَ مِنْ خَطَايَاهُمْ مِنْ شَيْء ٍ  ۖ  إِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ
Wa Layaĥmilunna 'Athqālahum Wa 'Athqālāan Ma`a 'Athqālihim  ۖ  Wa Layus'alunna Yawma Al-Qiyāmati `Ammā Kānū Yaftarūna َ029-013 Kuma lalle sunã ɗaukar kãyan nauyinsu da waɗansu nauyãyan kãya tãre da kãyan nauyinsu, kuma lalle zã a tambaye su a Rãnar ¡iyama game da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya. وَلَيَحْمِلُنَّ أَثْقَالَهُمْ وَأَثْقَالا ً مَعَ أَثْقَالِهِمْ  ۖ  وَلَيُسْأَلُنَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَمَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Wa Laqad 'Arsalnā Nūĥāan 'Ilá Qawmihi Falabitha Fīhim 'Alfa Sanatin 'Illā Khamsīna `Āmāan Fa'akhadhahumu Aţ-Ţūfānu Wa Hum Žālimūn َ029-014 Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu fãce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfãna) ta kãmã su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحا ً إِلَى قَوْمِه ِِ فَلَبِثَ فِيهِمْ أَلْفَ سَنَة ٍ إِلاَّ خَمْسِينَ عَاما ً فَأَخَذَهُمُ الطُّوفَانُ وَهُمْ ظَالِمُون
Fa'anjaynāhu Wa 'Aşĥāba As-Safīnati Wa Ja`alnāhā 'Āyatan Lil`ālamīna َ029-015 Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutãnen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata ãyã ga tãlikai. فَأَنجَيْنَاه ُُ وَأَصْحَابَ السَّفِينَةِ وَجَعَلْنَاهَا آيَة ً لِلْعَالَمِينَ
Wa 'Ibrāhīma 'Idh Qāla Liqawmihi A`budū Al-Laha Wa Attaqūhu  ۖ  Dhālikum Khayrun Lakum 'In Kuntum Ta`lamūna َ029-016 Da Ibrãhĩm a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ku bautã wa Allah ku bĩ Shi da taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani. وَإِبْرَاهِيمَ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاتَّقُوه ُُ  ۖ  ذَلِكُمْ خَيْر ٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ
'Innamā Ta`budūna Min Dūni Al-Lahi 'Awthānāan Wa Takhluqūna 'Ifkāan  ۚ  'Inna Al-Ladhīna Ta`budūna Min Dūni Al-Lahi Lā Yamlikūna Lakum Rizqāanbtaghū `Inda Al-Lahi Ar-Rizqa Wa A`budūhu Wa Ashkurū Lahu  ۖ  'Ilayhi Turja`ūna َ029-017 "Abin da dai kuke bautãwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bã su mallakã muku arziki. Sabõda haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gõdiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku. إِنَّمَا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَوْثَانا ً وَتَخْلُقُونَ إِفْكا ً  ۚ  إِنَّ الَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ لاَ يَمْلِكُونَ لَكُمْ رِزْقا ً فَابْتَغُوا عِنْدَ اللَّهِ الرِّزْقَ وَاعْبُدُوه ُُ وَاشْكُرُوا لَهُ~ُ  ۖ  إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Wa 'In Tukadhdhibū Faqad Kadhdhaba 'Umamun Min Qablikum  ۖ  Wa Mā `Alá Ar-Rasūli 'Illā Al-Balāghu Al-Mubīnu َ029-018 "Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummõmi a gabãninku sun ƙaryata, kuma bãbu abin da ke kan Manzo, fãce iyar da manzanci, iyarwa bayyananna." وَإِنْ تُكَذِّبُوا فَقَدْ كَذَّبَ أُمَم ٌ مِنْ قَبْلِكُمْ  ۖ  وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلاَّ الْبَلاَغُ الْمُبِينُ
'Awalam Yaraw Kayfa Yubdi'u Al-Lahu Al-Khalqa Thumma Yu`īduhu  ۚ  'Inna Dhālika `Alá Al-Lahi Yasīrun َ029-019 Shin, ba su ga yadda Allah ke fãra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah. أَوَلَمْ يَرَوْا كَيْفَ يُبْدِئُ اللَّهُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ~ُ  ۚ  إِنَّ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِير ٌ
Qul Sīrū Fī Al-'Arđi Fānžurū Kayfa Bada'a Al-Khalqa  ۚ  Thumma Al-Lahu Yunshi'u An-Nash'ata Al-'Ākhirata  ۚ  'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ029-020 Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yanã ƙãga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kõme. قُلْ سِيرُوا فِي الأَرْضِ فَانْظُرُوا كَيْفَ بَدَأَ الْخَلْقَ  ۚ  ثُمَّ اللَّهُ يُنشِئُ النَّشْأَةَ الآخِرَةَ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Yu`adhdhibu Man Yashā'u Wa Yarĥamu Man Yashā'u  ۖ  Wa 'Ilayhi Tuqlabūna َ029-021 "Yanã azabta wanda Ya so, kuma Yanã jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku." يُعَذِّبُ مَنْ يَشَاءُ وَيَرْحَمُ مَنْ يَشَاءُ  ۖ  وَإِلَيْهِ تُقْلَبُونَ
Wa Mā 'Antum Bimu`jizīna Fī Al-'Arđi Wa Lā Fī As-Samā'i  ۖ  Wa Mā Lakum Min Dūni Al-Lahi Min Wa Līyin Wa Lā Naşīrin َ029-022 "Kuma ba ku zamo mãsu buwãya ba a cikin ƙasã, kuma haka a cikin sama kuma bã ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki." وَمَا أَنْتُمْ بِمُعْجِزِينَ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ  ۖ  وَمَا لَكُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ مِنْ وَلِيّ ٍ وَلاَ نَصِير ٍ
Wa Al-Ladhīna Kafarū Bi'āyāti Al-Lahi Wa Liqā'ihi 'Ūlā'ika Ya'isū Min Raĥmatī Wa 'Ūlā'ika Lahum `Adhābun 'Alīmun َ029-023 Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sunã da wata azãba mai raɗaɗi. وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ اللَّهِ وَلِقَائِهِ~ِ أُوْلَائِكَ يَئِسُوا مِنْ رَحْمَتِي وَأُوْلَائِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Famā Kāna Jawāba Qawmihi 'Illā 'An Qālū Aqtulūhu 'Aw Ĥarriqūhu Fa'anjāhu Al-Lahu Mina An-Nāri  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yu'uminūna َ029-024 Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa (Ibrãhĩm) fãce dai suka ce: "Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni. فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ~ِ إِلاَّ أَنْ قَالُوا اقْتُلُوهُ~ُ أَوْ حَرِّقُوه ُُ فَأَنجَاهُ اللَّهُ مِنَ النَّارِ  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِقَوْم ٍ يُؤْمِنُونَ
Wa Qāla 'Innamā Attakhadhtum Min Dūni Al-Lahi 'Awthānāan Mawaddata Baynikum Al-Ĥayāati Ad-Dunyā  ۖ  Thumma Yawma Al-Qiyāmati Yakfuru Ba`đukum Biba`đin Wa Yal`anu Ba`đukum Ba`đāan Wa Ma'wākumu An-Nāru Wa Mā Lakum Min Nāşirīna َ029-025 Kuma Ibrahĩm ya ce "Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar ¡iyãma sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu mataimaka." وَقَالَ إِنَّمَا اتَّخَذْتُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَوْثَانا ً مَوَدَّةَ بَيْنِكُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا  ۖ  ثُمَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكْفُرُ بَعْضُكُمْ بِبَعْض ٍ وَيَلْعَنُ بَعْضُكُمْ بَعْضا ً وَمَأْوَاكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُمْ مِنْ نَاصِرِينَ
Fa'āmana Lahu Lūţun  ۘ  Wa Qāla 'Innī Muhājirun 'Ilá Rabbī  ۖ  'Innahu Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ029-026 Sai Lũɗu ya yi ĩmãni da shi. Kuma Ibrãhĩm ya ce: "Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima." فَآمَنَ لَه ُُ لُوط ٌ  ۘ  وَقَالَ إِنِّي مُهَاجِر ٌ إِلَى رَبِّي  ۖ  إِنَّه ُُ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Wa Wahabnā Lahu 'Isĥāqa Wa Ya`qūba Wa Ja`alnā Fī Dhurrīyatihi An-Nubūwata Wa Al-Kitāba Wa 'Ātaynāhu 'Ajrahu Fī Ad-Dunyā  ۖ  Wa 'Innahu Fī Al-'Ākhirati Lamina Aş-Şāliĥīn َ029-027 Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira, tabbas, yanã a cikin sãlihai. وَوَهَبْنَا لَهُ~ُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَجَعَلْنَا فِي ذُرِّيَّتِهِ النُّبُوَّةَ وَالْكِتَابَ وَآتَيْنَاهُ~ُ أَجْرَه ُُ فِي الدُّنْيَا  ۖ  وَإِنَّه ُُ فِي الآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِين
Wa Lūţāan 'Idh Qāla Liqawmihi 'Innakum Lata'tūna Al-Fāĥishata Mā Sabaqakum Bihā Min 'Aĥadin Mina Al-`Ālamīna َ029-028 Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa, "Lalle kũ, haƙĩƙa kunã jẽ wa alfãsha wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba. وَلُوطا ً إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ~ِ إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ مَا سَبَقَكُمْ بِهَا مِنْ أَحَد ٍ مِنَ الْعَالَمِينَ
'A'innakum Lata'tūna Ar-Rijāla Wa Taqţa`ūna As-Sabīla Wa Ta'tūna Fī Nādīkumu Al-Munkara  ۖ  Famā Kāna Jawāba Qawmihi 'Illā 'An Qālū A'tinā Bi`adhābi Al-Lahi 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna َ029-029 "Ashe, lalle kũ kunã je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da bã shi da kyau? To, jawãbin mutãnensa bai kasance ba fãce dai sun ce: 'Ka zo mana da azãbar Allah, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.'" أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ وَتَقْطَعُونَ السَّبِيلَ وَتَأْتُونَ فِي نَادِيكُمُ الْمُنكَرَ  ۖ  فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ~ِ إِلاَّ أَنْ قَالُوا ائْتِنَا بِعَذَابِ اللَّهِ إِنْ كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Qāla Rabbi Anşurnī `Alá Al-Qawmi Al-Mufsidīna َ029-030 Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutãnen nan maɓarnata." قَالَ رَبِّ انصُرْنِي عَلَى الْقَوْمِ الْمُفْسِدِينَ
Wa Lammā Jā'at Rusulunā 'Ibrāhīma Bil-Bushrá Qālū 'Innā Muhlikū 'Ahli Hadhihi Al-Qaryati  ۖ  'Inna 'Ahlahā Kānū Žālimīna َ029-031 Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka jẽ wa Ibrãhĩm da bushãra suka ce: "Lalle mu mãsu halaka mutãnen, wannan alƙarya ne. Lalle mutãnenta sun kasance mãsu zãlunci." وَلَمَّا جَاءَتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيمَ بِالْبُشْرَى قَالُوا إِنَّا مُهْلِكُو أَهْلِ هَذِهِ الْقَرْيَةِ  ۖ  إِنَّ أَهْلَهَا كَانُوا ظَالِمِينَ
Qāla 'Inna Fīhā Lūţāan  ۚ  Qālū Naĥnu 'A`lamu Biman Fīhā  ۖ  Lanunajjiyannahu Wa 'Ahlahu 'Illā Amra'atahu Kānat Mina Al-Ghābirīn َ029-032 Ya ce: "Lalle akwai Lũɗu a cikinta!" Suka ce: "Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle munã tsĩrar da shi da mutãnensa, fãce fa mãtarsa ta kasance a cikin mãsu wanzuwa." قَالَ إِنَّ فِيهَا لُوطا ً  ۚ  قَالُوا نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَنْ فِيهَا  ۖ  لَنُنَجِّيَنَّه ُُ وَأَهْلَهُ~ُ إِلاَّ امْرَأَتَه ُُ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِين
Wa Lammā 'An Jā'at Rusulunā Lūţāan Sī'a Bihim Wa Đāqa Bihim Dhar`āan Wa Qālū Lā Takhaf Wa Lā Taĥzan  ۖ  'Innā Munajjūka Wa 'Ahlaka 'Illā Amra'ataka Kānat Mina Al-Ghābirīna َ029-033 Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka je wa Lũɗu ya ɓãta rai sabõda su, kuma yã ƙuntata ga kirji sabõda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsõro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mũ mãsu tsĩrar da kai ne da iyãlanka, fãce dai matarka ta kasance daga mãsu wanzuwa. وَلَمَّا أَنْ جَاءَتْ رُسُلُنَا لُوطا ً سِيءَ بِهِمْ وَضَاقَ بِهِمْ ذَرْعا ً وَقَالُوا لاَ تَخَفْ وَلاَ تَحْزَنْ  ۖ  إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهْلَكَ إِلاَّ امْرَأَتَكَ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ
'Innā Munzilūna `Alá 'Ahli Hadhihi Al-Qaryati Rijzāan Mina As-Samā'i Bimā Kānū Yafsuqūna َ029-034 "Lalle mũ, mãsu saukar da azãba ne daga sama a kan mutãnen wannan alƙarya sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci." إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَى أَهْلِ هَذِهِ الْقَرْيَةِ رِجْزا ً مِنَ السَّمَاءِ بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ
Wa Laqad Taraknā Minhā 'Āyatan Bayyinatan Liqawmin Ya`qilūna َ029-035 Kuma lalle Mun bar wata ãyã bayyananna daga gare ta ga mutãne mãsu hankalta. وَلَقَد تَرَكْنَا مِنْهَا آيَة ً بَيِّنَة ً لِقَوْم ٍ يَعْقِلُونَ
Wa 'Ilá Madyana 'Akhāhum Shu`aybāan Faqāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Wa Arjū Al-Yawma Al-'Ākhira Wa Lā Ta`thaw Fī Al-'Arđi Mufsidīn َ029-036 Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rãnar Lãhira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasã, alhãli kuwa kunã mãsu lãlãtarwa." وَإِلَى مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبا ً فَقَالَ يَاقَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَارْجُوا الْيَوْمَ الآخِرَ وَلاَ تَعْثَوْا فِي الأَرْضِ مُفْسِدِين
Fakadhdhabūhu Fa'akhadhat/humu Ar-Rajfatu Fa'aşbaĥū Fī Dārihimthimīna َ029-037 Sai suka ƙaryata shi, sabõda haka tsãwa ta kãmã su, dõmin haka suka wãyi gari sunã guggurfãne. فَكَذَّبُوه ُُ فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ
Wa `Ādāan Wa Thamūda Wa Qad Tabayyana Lakum Min Masākinihim  ۖ  Wa Zayyana Lahumu Ash-Shayţānu 'A`mālahum Faşaddahum `Ani As-Sabīli Wa Kānū Mustabşirīna َ029-038 Da Ãdawa da Samũdãwa alhãli kuwa lalle alãmun azãba sun bayyana a gare su daga gidãjensu kuma Shaiɗan ya ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance mãsu basĩra! وَعَادا ً وَثَمُودَ وَقَدْ تَبَيَّنَ لَكُمْ مِنْ مَسَاكِنِهِمْ  ۖ  وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَكَانُوا مُسْتَبْصِرِينَ
Wa Qārūna Wa Fir`awna Wa Hāmāna  ۖ  Wa Laqad Jā'ahum Mūsá Bil-Bayyināti Fāstakbarū Fī Al-'Arđi Wa Mā Kānū Sābiqīna َ029-039 Kuma ¡ãrũna da Fir'auna da Hãmãna, kuma lalle Mũsaya je musu da hujjõji, sai suka yi girman kai a cikin ƙasã kuma ba su kasance mãsu tsẽrẽwa ba. وَقَارُونَ وَفِرْعَوْنَ وَهَامَانَ  ۖ  وَلَقَدْ جَاءَهُمْ مُوسَى بِالْبَيِّنَاتِ فَاسْتَكْبَرُوا فِي الأَرْضِ وَمَا كَانُوا سَابِقِينَ
Fakullāan 'Akhadhnā Bidhanbihi  ۖ  Faminhum Man 'Arsalnā `Alayhi Ĥāşibāan Wa Minhum Man 'Akhadhat/hu Aş-Şayĥatu Wa Minhum Man Khasafnā Bihi Al-'Arđa Wa Minhum Man 'Aghraqnā  ۚ  Wa Mā Kāna Al-Lahu Liyažlimahum Wa Lakin Kānū 'Anfusahum Yažlimūna َ029-040 Sabõda haka kõwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsãwa ta kãmã, kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasã da shi kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Bã ya yiwuwa ga Allah Ya zãlunce su, amma sun kasance kansu suke zãlunta. فَكُلّاً أَخَذْنَا بِذَنْبِه ِِ  ۖ  فَمِنْهُمْ مَنْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِ حَاصِبا ً وَمِنْهُمْ مَنْ أَخَذَتْهُ الصَّيْحَةُ وَمِنْهُمْ مَنْ خَسَفْنَا بِهِ الأَرْضَ وَمِنْهُمْ مَنْ أَغْرَقْنَا  ۚ  وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَكِنْ كَانُوا أَنْفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Mathalu Al-Ladhīna Attakhadhū Min Dūni Al-Lahi 'Awliyā'a Kamathali Al-`Ankabūti Attakhadhat Baytāan  ۖ  Wa 'Inna 'Awhana Al-Buyūti Labaytu Al-`Ankabūti  ۖ  Law Kānū Ya`lamūna َ029-041 Misãlin waɗanda suka riƙi waɗansu masõya waɗanda bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa lalle mafi raunin gidãje, shĩ ne gidan gizogizo, dã sun kasance sunã sane. مَثَلُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِ اللَّهِ أَوْلِيَاءَ كَمَثَلِ الْعَنكَبُوتِ اتَّخَذَتْ بَيْتا ً  ۖ  وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنْكَبُوتِ  ۖ  لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
'Inna Al-Laha Ya`lamu Mā Yad`ūna Min Dūnihi Min Shay'in  ۚ  Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ029-042 Lalle Allah Yanã sane da abin da suke kira wanda bã Shi ba na wani abu duka kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. إِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا يَدْعُونَ مِنْ دُونِه ِِ مِنْ شَيْء ٍ  ۚ  وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Wa Tilka Al-'Amthālu Nađribuhā Lilnnāsi  ۖ  Wa Mā Ya`qiluhā 'Illā Al-`Ālimūna َ029-043 Kuma waɗancan misãlan Munã bayyana su ga mutãne kuma bãbu mai hankalta da su sai mãsu ilmi. وَتِلْكَ الأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ  ۖ  وَمَا يَعْقِلُهَا إِلاَّ الْعَالِمُونَ
Khalaqa Al-Lahu As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Bil-Ĥaqqi  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Lilmu'uminīna َ029-044 Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai ãyã ga mũminai. خَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِالْحَقِّ  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِلْمُؤْمِنِينَ
Atlu Mā 'Ūĥiya 'Ilayka Mina Al-Kitābi Wa 'Aqimu Aş-Şalāata  ۖ  'Inna Aş-Şalāata Tanhá `Ani Al-Faĥshā'i Wa Al-Munkari  ۗ  Wa Ladhikru Al-Lahi 'Akbaru Wa  ۗ  Allāhu Ya`lamu Mā Taşna`ūna َ029-045 Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa. اتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ وَأَقِمُ الصَّلاَةَ  ۖ  إِنَّ الصَّلاَةَ تَنْهَى عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ  ۗ  وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ  ۗ  وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ
Wa Lā Tujādilū 'Ahla Al-Kitābi 'Illā Bi-Atī Hiya 'Aĥsanu 'Illā Al-Ladhīna Žalamū Minhum  ۖ  Wa Qūlū 'Āmannā Bial-Ladhī 'Unzila 'Ilaynā Wa 'Unzila 'Ilaykum Wa 'Ilahunā Wa 'Ilahukum Wāĥidun Wa Naĥnu Lahu Muslimūna َ029-046 Kada ku yi jayayya da mazowa Littãfi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, kuma ku ce, "Mun yi ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautãwarmu da Abin bautãwarku Guda ne, kama mũ mãsu sallamãwa ne a gare shi." وَلاَ تُجَادِلُوا أَهْلَ الْكِتَابِ إِلاَّ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِلاَّ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْهُمْ  ۖ  وَقُولُوا آمَنَّا بِالَّذِي أُنْزِلَ إِلَيْنَا وَأُنْزِلَ إِلَيْكُمْ وَإِلَهُنَا وَإِلَهُكُمْ وَاحِد ٌ وَنَحْنُ لَه ُُ مُسْلِمُونَ
Wa Kadhalika 'Anzalnā 'Ilayka Al-Kitāba  ۚ  Fa-Al-Ladhīna 'Ātaynāhumu Al-Kitāba Yu'uminūna Bihi  ۖ  Wa Min Hā'uulā' Man Yu'uminu Bihi  ۚ  Wa Mā Yajĥadu Bi'āyātinā 'Illā Al-Kāfirūna َ029-047 Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa Littãfi sanã ĩmãni da shi, daga cikin wãɗannan akwai mai ĩmãni da shi, kuma bãbu mai musun ãyõyinMu, fãce kãfirai. وَكَذَلِكَ أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ  ۚ  فَالَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يُؤْمِنُونَ بِه ِِ  ۖ  وَمِنْ هَاؤُلاَء مَنْ يُؤْمِنُ بِه ِِ  ۚ  وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلاَّ الْكَافِرُونَ
Wa Mā Kunta Tatlū Min Qablihi Min Kitābin Wa Lā Takhuţţuhu Biyamīnika  ۖ  'Idhāan Lārtāba Al-Mubţilūna َ029-048 Kuma ba ka kasance kana karãtun wani littãfi ba a gabãninsa, kuma bã ka rubũtunsa da dãmanka dã haka yã auku, dã mãsu ɓarnã sun yi shakka. وَمَا كُنْتَ تَتْلُو مِنْ قَبْلِه ِِ مِنْ كِتَاب ٍ وَلاَ تَخُطُّه ُُ بِيَمِينِكَ  ۖ  إِذا ً لاَرْتَابَ الْمُبْطِلُونَ
Bal Huwa 'Āyātun Bayyinātun Fī Şudūri Al-Ladhīna 'Ū Al-`Ilma  ۚ  Wa Mā Yajĥadu Bi'āyātinā 'Illā Až-Žālimūna َ029-049 Ã'a, shĩ ãyõyi ne bayyanannu a cikin ƙirãzan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce azzãlumai. بَلْ هُوَ آيَات ٌ بَيِّنَات ٌ فِي صُدُورِ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ  ۚ  وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلاَّ الظَّالِمُونَ
Wa Qālū Lawlā 'Unzila `Alayhi 'Āyātun Min Rabbihi  ۖ  Qul 'Innamā Al-'Āyātu `Inda Al-Lahi Wa 'Innamā 'Anā Nadhīrun Mubīnun َ029-050 Kuma suka ce: "Don me ba a saukar masa da ãyõi ba daga Ubangijinsa? "Ka ce: "Su ãyõyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa." وَقَالُوا لَوْلاَ أُنْزِلَ عَلَيْهِ آيَات ٌ مِنْ رَبِّه ِِ  ۖ  قُلْ إِنَّمَا الآيَاتُ عِنْدَ اللَّهِ وَإِنَّمَا أَنَا نَذِير ٌ مُبِين ٌ
'Awalam Yakfihim 'Annā 'Anzalnā `Alayka Al-Kitāba Yutlá `Alayhim  ۚ  'Inna Fī Dhālika Laraĥmatan Wa Dhikrá Liqawmin Yu'uminūna َ029-051 Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littãfin akanka, anã karanta shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunãtawa ga mutanen da ke yin ĩmãni. أَوَلَمْ يَكْفِهِمْ أَنَّا أَنْزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ يُتْلَى عَلَيْهِمْ  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَرَحْمَة ً وَذِكْرَى لِقَوْم ٍ يُؤْمِنُونَ
Qul Kafá Bil-Lahi Baynī Wa Baynakum Shahīdāan  ۖ  Ya`lamu Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa  ۗ  Al-Ladhīna 'Āmanū Bil-Bāţili Wa Kafarū Bil-Lahi 'Ūlā'ika Humu Al-Khāsirūna َ029-052 Ka ce: "Allah Yã isa shaida a tsakãnĩna da tsakãnĩnku Yanã sane da abin da ke a cikin sammai da ƙasã, kuma waɗanda suka yi ĩmãni da ɗarya kuma suka kãfirta da Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra." قُلْ كَفَى بِاللَّهِ بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ شَهِيدا ً  ۖ  يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۗ  وَالَّذِينَ آمَنُوا بِالْبَاطِلِ وَكَفَرُوا بِاللَّهِ أُوْلَائِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Wa Yasta`jilūnaka Bil-`Adhābi  ۚ  Wa Lawlā 'Ajalun Musammáan Lajā'ahumu Al-`Adhābu Wa Laya'tiyannahum Baghtatan Wa Hum Lā Yash`urūna َ029-053 Kuma suna nẽman ka da gaggauta azãba, to, bã dõmin ajali ƙayyadadde ba, dã azãba ta jẽ musu kuma lalle dã tanã iske su bisa ia abke, alhãli kuwa sũ ba su sani ba. وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ  ۚ  وَلَوْلاَ أَجَل ٌ مُسَمّى ً لَجَاءَهُمُ الْعَذَابُ وَلَيَأْتِيَنَّهُمْ بَغْتَة ً وَهُمْ لاَ يَشْعُرُونَ
Yasta`jilūnaka Bil-`Adhābi Wa 'Inna Jahannama Lamuĥīţatun Bil-Kāfirīna َ029-054 Sunã nẽman ka da gaggauta azãba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kẽwayewa ce gakãfirai. يَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَة ٌ بِالْكَافِرِينَ
Yawma Yaghshāhumu Al-`Adhābu Min Fawqihim Wa Min Taĥti 'Arjulihim Wa Yaqūlu Dhūqū Mā Kuntum Ta`malūna َ029-055 Rãnar da azãba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya ce: "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa." يَوْمَ يَغْشَاهُمُ الْعَذَابُ مِنْ فَوْقِهِمْ وَمِنْ تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ وَيَقُولُ ذُوقُوا مَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ
Yā `Ibādiya Al-Ladhīna 'Āmanū 'Inna 'Arđī Wāsi`atun Fa'īyāya Fā`budūni َ029-056 Yã bãyiNa, waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle fa ƙasãTa mai yalwã ce, sabãda haka ku bauta Mini. يَاعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ أَرْضِي وَاسِعَة ٌ فَإِيَّايَ فَاعْبُدُونِ
Kullu Nafsin Dhā'iqatu Al-Mawti  ۖ  Thumma 'Ilaynā Turja`ūna َ029-057 Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku. كُلُّ نَفْس ٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ  ۖ  ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lanubawwi'annahum Mina Al-Jannati Ghurafāan Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna  ۚ  Fīhā Ni`ma 'Ajru Al-`Āmilīna َ029-058 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zã Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidãjen bẽne, ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon mãsu aikin ƙwarai. وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُبَوِّئَنَّهُمْ مِنَ الْجَنَّةِ غُرَفا ً تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا  ۚ  نِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ
Al-Ladhīna Şabarū Wa `Alá Rabbihim Yatawakkalūna َ029-059 Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu kawai. الَّذِينَ صَبَرُوا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Wa Ka'ayyin Min Dābbatin Lā Taĥmilu Rizqahā Al-Lahu Yarzuquhā Wa 'Īyākum  ۚ  Wa Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu َ029-060 Kuma da yawa dabba wadda bã ta ɗaukar abincinta Allah Yanã ciyar da ita tãre da ku, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai ilmi. وَكَأَيِّن مِنْ دَابَّة ٍ لاَ تَحْمِلُ رِزْقَهَا اللَّهُ يَرْزُقُهَا وَإِيَّاكُمْ  ۚ  وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Wa La'in Sa'altahum Man Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Sakhkhara Ash-Shamsa Wa Al-Qamara Layaqūlunna Al-Lahu  ۖ  Fa'annā Yu'ufakūna َ029-061 Lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasã kuma ya hõre rãnã da watã?" Lalle sunã cẽwa Allah ne. TO, yãya ake karkatar da su ? وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ  ۖ  فَأَنَّا يُؤْفَكُونَ
Al-Lahu Yabsuţu Ar-Rizqa Liman Yashā'u Min `Ibādihi Wa Yaqdiru Lahu  ۚ  'Inna Al-Laha Bikulli Shay'in `Alīmun َ029-062 A1lah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin bãyinsa kuma Yanã ƙuntãtãwa ga (wanda, Yake so). Lalle Allah, Masani ne ga dukan kõme. اللَّهُ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِه ِِ وَيَقْدِرُ لَهُ~ُ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيم ٌ
Wa La'in Sa'altahum Man Nazzala Mina As-Samā'i Mā'an Fa'aĥyā Bihi Al-'Arđa Min Ba`di Mawtihā Layaqūlunna Al-Lahu  ۚ  Quli Al-Ĥamdu Lillahi  ۚ  Bal 'Aktharuhum Lā Ya`qilūna َ029-063 Kuma lalle idan ka tambaye su. "Wãne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta?" Lalle sunã cẽwa, "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya tã tabbata ga Allah." Ã'a, mafi yawansu bã su hankalta. وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ نَزَّلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَأَحْيَا بِهِ الأَرْضَ مِنْ بَعْدِ مَوْتِهَا لَيَقُولُنَّ اللَّهُ  ۚ  قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ  ۚ  بَلْ أَكْثَرُهُمْ لاَ يَعْقِلُونَ
Wa Mā Hadhihi Al-Ĥayāatu Ad-Dunyā 'Illā Lahwun Wa La`ibun  ۚ  Wa 'Inna Ad-Dāra Al-'Ākhirata Lahiya Al-Ĥayawānu  ۚ  Law Kānū Ya`lamūna َ029-064 Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani. وَمَا هَذِهِ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلاَّ لَهْو ٌ وَلَعِب ٌ  ۚ  وَإِنَّ الدَّارَ الآخِرَةَ لَهِيَ الْحَيَوَانُ  ۚ  لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
Fa'idhā Rakibū Fī Al-Fulki Da`aw Al-Laha Mukhlişīna Lahu Ad-Dīna Falammā Najjāhum 'Ilá Al-Barri 'Idhā Hum Yushrikūna َ029-065 To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki. فَإِذَا رَكِبُوا فِي الْفُلْكِ دَعَوْا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُونَ
Liyakfurū Bimā 'Ātaynāhum Wa Liyatamatta`ū  ۖ  Fasawfa Ya`lamūna َ029-066 Dõmin su kãfirce wa abin da Muka bã su kuma dõmin su ji dãɗi sa'an nan kuma zã su sani. لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ وَلِيَتَمَتَّعُوا  ۖ  فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
'Awalam Yaraw 'Annā Ja`alnā Ĥaramāan 'Āmināan Wa Yutakhaţţafu An-Nāsu Min Ĥawlihim  ۚ  'Afabiālbāţili Yu'uminūna Wa Bini`mati Al-Lahi Yakfurūna َ029-067 Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhãli kuwa anã fisge mutãne a gẽfensu? Shin, da ɓãtaccen abu suke ĩmãni kuma da ni'imarAllah suka kãfirta? أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا حَرَما ً آمِنا ً وَيُتَخَطَّفُ النَّاسُ مِنْ حَوْلِهِمْ  ۚ  أَفَبِالْبَاطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَةِ اللَّهِ يَكْفُرُونَ
Wa Man 'Ažlamu Mimmani Aftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan 'Aw Kadhdhaba Bil-Ĥaqqi Lammā Jā'ahu  ۚ  'Alaysa Fī Jahannama Mathwáan Lilkāfirīna َ029-068 Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai? وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِباً أَوْ كَذَّبَ بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُ~ُ  ۚ  أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوى ً لِلْكَافِرِينَ
Wa Al-Ladhīna Jāhadū Fīnā Lanahdiyannahum  ۚ  Subulanā Wa 'Inna Al-Laha Lama`a Al-Muĥsinīna َ029-069 Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga addĩninsu). وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا  ۚ  وَإِنَّ اللَّهَ لَمَعَ الْمُحْسِنِينَ
Next Sūrah