30) Sūrat Ar-Rūm

Printed format

30)

'Alif-Lām-Mīm 030-001 A. L̃. M̃. --
Ghulibati Ar-Rūmu 030-002 An rinjãyi Rũmawa.
Fī 'Adná Al-'Arđi Wa Hum Min Ba`di Ghalabihim Sayaghlibūna 030-003 A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya.
Fī Biđ`i Sinīna  ۗ  Lillahi Al-'Amru Min Qablu Wa Min Ba`du  ۚ  Wa Yawma'idhin Yafraĥu Al-Mu'uminūna 030-004 A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki.  ۗ   ۚ 
Binaşri Al-Lahi  ۚ  Yanşuru Man Yashā'u  ۖ  Wa Huwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 030-005 Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.  ۚ   ۖ 
Wa`da Al-Lahi  ۖ  Lā Yukhlifu Al-Lahu Wa`dahu Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna 030-006 Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.  ۖ 
Ya`lamūna Žāhirāan Mina Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Hum `Ani Al-'Ākhirati Hum Ghāfilūna 030-007 Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira.
'Awalam Yatafakkarū Fī 'Anfusihim  ۗ  Mā Khalaqa Al-Lahu As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā 'Illā Bil-Ĥaqqi Wa 'Ajalin Musammáan  ۗ  Wa 'Inna Kathīrāan Mina An-Nāsi Biliqā'i Rabbihim Lakāfirūna 030-008 Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu?  ۗ   ۗ 
'Awalam Yasīrū Fī Al-'Arđi Fayanžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  Kānū 'Ashadda Minhum Qūwatan Wa 'Athārū Al-'Arđa Wa `Amarūhā 'Akthara Mimmā `Amarūhā Wa Jā'at/hum Rusuluhum Bil-Bayyināti  ۖ  Famā Kāna Al-Lahu Liyažlimahum Wa Lakin Kānū 'Anfusahum Yažlimūna 030-009 Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.  ۚ   ۖ 
Thumma Kāna `Āqibata Al-Ladhīna 'Asā'ū As-Sū'á 'An Kadhdhabū Bi'āyāti Al-Lahi Wa Kānū Bihā Yastahzi'ūn 030-010 Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su.
Al-Lahu Yabda'u Al-Khalqa Thumma Yu`īduhu Thumma 'Ilayhi Turja`ūna 030-011 Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku.
Wa Yawma Taqūmu As-Sā`atu Yublisu Al-Mujrimūna 030-012 Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana.
Wa Lam Yakun Lahum Min Shurakā'ihim Shufa`ā'u Wa Kānū Bishurakā'ihim Kāfirīna 030-013 Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu kãfircẽwadaga abũbuwan shirkinsu.
Wa Yawma Taqūmu As-Sā`atu Yawma'idhin Yatafarraqūna 030-014 Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mutãne ke farraba.
Fa'ammā Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Fahum Fī Rawđatin Yuĥbarūna 030-015 To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu.
Wa 'Ammā Al-Ladhīna Kafarū Wa Kadhdhabū Bi'āyātinā Wa Liqā'i Al-'Ākhirati Fa'ūlā'ika Fī Al-`Adhābi Muĥđarūna 030-016 Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba.
Fasubĥāna Al-Lahi Ĥīna Tumsūna Wa Ĥīna Tuşbiĥūna 030-017 Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya.
Wa Lahu Al-Ĥamdu Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa `Ashīyāan Wa Ĥīna Tužhirūna 030-018 Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli.
Yukhriju Al-Ĥayya Mina Al-Mayyiti Wa Yukhriju Al-Mayyita Mina Al-Ĥayyi Wa Yuĥyī Al-'Arđa Ba`da Mawtihā  ۚ  Wa Kadhalika Tukhrajūna 030-019 Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku.  ۚ 
Wa Min 'Āyātihi 'An Khalaqakum Min Turābin Thumma 'Idhā 'Antum Basharun Tantashirūna 030-020 Kuma akwai daga ãyõyinSa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa. ~
Wa Min 'Āyātihi 'An Khalaqa Lakum Min 'Anfusikum 'Azwājāan Litaskunū 'Ilayhā Wa Ja`ala Baynakum Mawaddatan Wa Raĥmatan  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yatafakkarūna 030-021 Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni. ~  ۚ 
Wa Min 'Āyātihi Khalqu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Akhtilāfu 'Alsinatikum Wa 'Alwānikum  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Lil`ālimīna 030-022 Kuma akwai daga ãyõyinSa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi.  ۚ 
Wa Min 'Āyātihi Manāmukum Bil-Layli Wa An-Nahāri Wa Abtighā'uukum Min Fađlihi  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yasma`ūna 030-023 Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa. ~  ۚ 
Wa Min 'Āyātihi Yurīkumu Al-Barqa Khawfāan Wa Ţama`āan Wa Yunazzilu Mina As-Samā'i Mā'an Fayuĥyī Bihi Al-'Arđa Ba`da Mawtihā  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Ya`qilūna 030-024 Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.  ۚ 
Wa Min 'Āyātihi 'An Taqūma As-Samā'u Wa Al-'Arđu Bi'amrihi  ۚ  Thumma 'Idhā Da`ākum Da`watan Mina Al-'Arđi 'Idhā 'Antum Takhrujūna 030-025 Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita. ~  ۚ 
Wa Lahu Man As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Kullun Lahu Qānitūna 030-026 Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a gare Shi.  ۖ 
Wa Huwa Al-Ladhī Yabda'u Al-Khalqa Thumma Yu`īduhu Wa Huwa 'Ahwanu `Alayhi  ۚ  Wa Lahu Al-Mathalu Al-'A`lá Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu 030-027 Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.  ۚ   ۚ 
Đaraba Lakum Mathalāan Min 'Anfusikum  ۖ  Hal Lakum Min Mā Malakat 'Aymānukum Min Shurakā'a Fī Mā Razaqnākum Fa'antum Fīhi Sawā'un Takhāfūnahum Kakhīfatikum 'Anfusakum  ۚ  Kadhālika Nufaşşilu Al-'Āyāti Liqawmin Ya`qilūna 030-028 Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltawa.  ۖ   ۚ 
Bal Attaba`a Al-Ladhīna Žalamū 'Ahwā'ahum Bighayri `Ilmin  ۖ  Faman Yahdī Man 'Ađalla Al-Lahu  ۖ  Wa Mā Lahum Min Nāşirīna 030-029 Ã'aha! waɗanda suka yi zã1unci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba. To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?  ۖ   ۖ 
Fa'aqim Wajhaka Lilddīni Ĥanīfāan Fiţrata  ۚ  Al-Lahi Allatī Faţara An-Nāsa `Alayhā Lā  ۚ  Tabdīla Likhalqi Al-Lahi Dhālika  ۚ  Ad-Dīnu Al-Qayyimu Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna 030-030 Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah, wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.  ۚ   ۚ   ۚ 
Munībīna 'Ilayhi Wa Attaqūhu Wa 'Aqīmū Aş-Şalāata Wa Lā Takūnū Mina Al-Mushrikīna 030-031 Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai.
Mina Al-Ladhīna Farraqū Dīnahum Wa Kānū Shiya`āan  ۖ  Kullu Ĥizbin Bimā Ladayhim Farūna 030-032 Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.  ۖ 
Wa 'Idhā Massa An-Nāsa Đurrun Da`aw Rabbahum Munībīna 'Ilayhi Thumma 'Idhā 'Adhāqahum Minhu Raĥmatan 'Idhā Farīqun Minhum Birabbihim Yushrikūna 030-033 Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu.
Liyakfurū Bimā 'Ātaynāhum  ۚ  Fatamatta`ū Fasawfa Ta`lamūna 030-034 Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku, sani.  ۚ 
'Am 'Anzalnā `Alayhim Sulţānāan Fahuwa Yatakallamu Bimā Kānū Bihi Yushrikūna 030-035 Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka kasance sunã shirkin da shi?
Wa 'Idhā 'Adhaq An-Nāsa Raĥmatan Fariĥū Bihā  ۖ  Wa 'In Tuşibhum Sayyi'atun Bimā Qaddamat 'Aydīhim 'Idhā Hum Yaqnaţūna 030-036 Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã yanke ƙauna,  ۖ 
'Awalam Yaraw 'Anna Al-Laha Yabsuţu Ar-Rizqa Liman Yashā'u Wa Yaqdiru  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yu'uminūna 030-037 Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni.  ۚ 
Fa'āti Dhā Al-Qurbá Ĥaqqahu Wa Al-Miskīna Wa Abna As-Sabīli  ۚ  Dhālika Khayrun Lilladhīna Yurīdūna Wajha Al-Lahi Wa 'Ūlā'ika  ۖ  Humu Al-Mufliĥūna 030-038 Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo.  ۚ   ۖ 
Wa Mā 'Ātaytum Min Ribāan Liyarbuwā Fī 'Amwāli An-Nāsi Falā Yarbū `Inda Al-Lahi  ۖ  Wa Mā 'Ātaytum Min Zakāatin Turīdūna Wajha Al-Lahi Fa'ūlā'ika Humu Al-Muđ`ifūna 030-039 Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu).  ۖ 
Al-Lahu Al-Ladhī Khalaqakum Thumma Razaqakum Thumma Yumītukum Thumma Yuĥyīkum  ۖ  Hal Min Shurakā'ikum Man Yaf`alu Min Dhālikum Min Shay'in  ۚ  Subĥānahu Wa Ta`ālá `Ammā Yushrikūna 030-040 Allah ne Wanda Ya halitta ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki.  ۖ   ۚ 
Žahara Al-Fasādu Fī Al-Barri Wa Al-Baĥri Bimā Kasabat 'Aydī An-Nāsi Liyudhīqahum Ba`đa Al-Ladhī `Amilū La`allahum Yarji`ūna 030-041 arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su kõmo.
Qul Sīrū Fī Al-'Arđi Fānžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Ladhīna Min Qablu  ۚ  Kāna 'Aktharuhum Mushrikīna 030-042 Ka ce: "Ku tafi a cikin ƙasã sa'an nan ku dũbi yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance mãsu yin shirki."  ۚ 
Fa'aqim Wajhaka Lilddīni Al-Qayyimi Min Qabli 'An Ya'tiya Yawmun Lā Maradda Lahu Mina Al-Lahi Yawma'idhin  ۖ  Yaşşadda`ūna 030-043 Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa (su rabu biyu).  ۖ 
Man Kafara Fa`alayhi Kufruhu  ۖ  Wa Man `Amila Şāliĥāan Fali'anfusihim Yamhadūna 030-044 Wanda ya kãfirta,to,kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa.  ۖ 
Liyajziya Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Min Fađlihi  ۚ  'Innahu Lā Yuĥibbu Al-Kāfirīna 030-045 Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai. ~  ۚ 
Wa Min 'Āyātihi 'An Yursila Ar-Riyāĥa Mubashshirātin Wa Liyudhīqakum Min Raĥmatihi Wa Litajriya Al-Fulku Bi'amrihi Wa Litabtaghū Min Fađlihi Wa La`allakum Tashkurūna 030-046 Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, fãtanku zã ku gode. ~
Wa Laqad 'Arsalnā Min Qablika Rusulāan 'Ilá Qawmihim Fajā'ūhum Bil-Bayyināti Fāntaqamnā Mina Al-Ladhīna 'Ajramū  ۖ  Wa Kāna Ĥaqqāan `Alaynā Naşru Al-Mu'uminīna 030-047 Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi, kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu.  ۖ 
Al-Lahu Al-Ladhī Yursilu Ar-Riyāĥa Fatuthīru Saĥābāan Fayabsuţuhu Fī As-Samā'i Kayfa Yashā'u Wa Yaj`aluhu Kisafāan Fatará Al-Wadqa Yakhruju Min Khilālihi  ۖ  Fa'idhā 'Aşāba Bihi Man Yashā'u Min `Ibādihi 'Idhā Hum Yastabshirūna 030-048 Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi.  ۖ  ~
Wa 'In Kānū Min Qabli 'An Yunazzala `Alayhim Min Qablihi Lamublisīna 030-049 Kuma kõ da sun kasance a gabãnin a saukar da shi a kansu, kusa-kusa, sunã baƙin ciki hai bã su iya magana.
nžur 'Ilá 'Āthāri Raĥmati Al-Lahi Kayfa Yuĥyī Al-'Arđa Ba`da Mawtihā  ۚ  'Inna Dhālika Lamuĥyī Al-Mawtá  ۖ  Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 030-050 Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kõme.  ۚ   ۖ 
Wa La'in 'Arsalnā Rīĥāan Fara'awhu Muşfarrāan Lažallū Min Ba`dihi Yakfurūna 030-051 Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle zã su yini a bãyansa sunã kãfirta.
Fa'innaka Lā Tusmi`u Al-Mawtá Wa Lā Tusmi`u Aş-Şumma Ad-Du`ā'a 'Idhā Wa Llaw Mudbirīna 030-052 Sabõda haka, kai, bã ka jiyar da matattu kira, kuma bã ka jiyar da kurãme kira idan sun jũya bãya sunã gudu.
Wa Mā 'Anta Bihādī Al-`Umyi `An Đalālatihim  ۖ  'In Tusmi`u 'Illā Man Yu'uminu Bi'āyātinā Fahum Muslimūn 030-053 Kuma ba ka zamo mai shiryar da makãfi ba daga ɓatarsu, bã ka jiyarwa fãce wanda ke yin ĩmãni da ãyõyinMu, watau sũ ne mãsu mĩƙa wuya, su sallama.  ۖ 
Al-Lahu Al-Ladhī Khalaqakum Min Đa`fin Thumma Ja`ala Min Ba`di Đa`fin Qūwatan Thumma Ja`ala Min Ba`di Qūwatin Đa`fāan Wa Shaybatan  ۚ  Yakhluqu Mā Yashā'u  ۖ  Wa Huwa Al-`Alīmu Al-Qadīru 030-054 Allah ne Ya halitta ku daga rauni, sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi,  ۚ   ۖ 
Wa Yawma Taqūmu As-Sā`atu Yuqsimu Al-Mujrimūna Mā Labithū Ghayra Sā`atin  ۚ  Kadhālika Kānū Yu'ufakūna 030-055 Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su.  ۚ 
Wa Qāla Al-Ladhīna 'Ū Al-`Ilma Wa Al-'Īmāna Laqad Labithtum Fī Kitābi Al-Lahi 'Ilá Yawmi Al-Ba`thi  ۖ  Fahadhā Yawmu Al-Ba`thi Wa Lakinnakum Kuntum Lā Ta`lamūna 030-056 Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar, kuma amma kũ, kun kasance ba ku sani ba."  ۖ 
Fayawma'idhin Lā Yanfa`u Al-Ladhīna Žalamū Ma`dhiratuhum Wa Lā Hum Yusta`tabūna 030-057 To, a rãnar da uzurin waɗanda suka yi zãlunci bã ya amfaninsu, kuma bã a neman yardarsu.
Wa Laqad Đarabnā Lilnnāsi Fī Hādhā Al-Qur'āni Min Kulli Mathalin  ۚ  Wa La'in Ji'tahum Bi'āyatin Layaqūlanna Al-Ladhīna Kafarū 'In 'Antum 'Illā Mubţilūna 030-058 Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta zã su ce "Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua."  ۚ 
Kadhālika Yaţba`u Al-Lahu `Alá Qulūbi Al-Ladhīna Lā Ya`lamūna 030-059 Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba.
Fāşbir 'Inna Wa`da Al-Lahi Ĥaqqun  ۖ  Wa Lā Yastakhiffannaka Al-Ladhīna Lā Yūqinūna 030-060 Sabõda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda bã su da yaƙĩni su sassabce maka hankali.  ۖ 
Next Sūrah