28) Sūrat Al-Qaşaş

Printed format

28)

Ţā-Sīn-Mīm 028-001 . S̃. M̃. --
Tilka 'Āyātu Al-Kitābi Al-Mubīni 028-002 Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
Natlū `Alayka Min Naba'i Mūsá Wa Fir`awna Bil-Ĥaqqi Liqawmin Yu'uminūna 028-003 Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
'Inna Fir`awna `Alā Fī Al-'Arđi Wa Ja`ala 'Ahlahā Shiya`āan Yastađ`ifu Ţā'ifatan Minhum Yudhabbiĥu 'Abnā'ahum Wa Yastaĥyī Nisā'ahum  ۚ  'Innahu Kāna Mina Al-Mufsidīna 028-004 Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.  ۚ 
Wa Nurīdu 'An Namunna `Alá Al-Ladhīna Astuđ`ifū Fī Al-'Arđi Wa Naj`alahum 'A'immatan Wa Naj`alahumu Al-Wārithīna 028-005 Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.
Wa Numakkina Lahum Al-'Arđi Wa Nuriya Fir`awna Wa Hāmāna Wa Junūdahumā Minhum Mā Kānū Yaĥdharūna 028-006 Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su.
Wa 'Awĥaynā 'Ilá 'Ummi Mūsá 'An 'Arđi`īhi  ۖ  Fa'idhā Khifti `Alayhi Fa'alqīhi Fī Al-Yammi Wa Lā Takhāfī Wa Lā Taĥzanī  ۖ  'Innā Rāddūhu 'Ilayki Wa Jā`ilūhu Mina Al-Mursalīna 028-007 Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi,kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni  ۖ   ۖ  ~
Fāltaqaţahu 'Ālu Fir`awna Liyakūna Lahum `Adūwāan Wa Ĥazanāan  ۗ  'Inna Fir`awna Wa Hāmāna Wa Junūdahumā Kānū Khāţi'īna 028-008 Sai mutãnen Fir'auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci.  ۗ 
Wa Qālat Amra'atu Fir`awna Qurratu `Aynin Lī Wa Laka  ۖ  Lā Taqtulūhu `Asá 'An Yanfa`anā 'Aw Nattakhidhahu Waladāan Wa Hum Lā Yash`urūna 028-009 Kuma matar Fir'auna ta ce ("Ka bar shi yanã) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã," alhãli kuwa sũ ba su sansance ba.  ۖ 
Wa 'Aşbaĥa Fu'uādu 'Ummi Mūsá Fārighāan  ۖ  'In Kādat Latubdī Bihi Lawlā 'An Rabaţnā `Alá Qalbihā Litakūna Mina Al-Mu'uminīna 028-010 Kuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta. Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai.  ۖ 
Wa Qālat Li'khtihi Quşşīhi  ۖ  Fabaşurat Bihi `An Junubin Wa Hum Lā Yash`urūna 028-011 Kuma ta ce wa 'yar'uwarsa, "Ki bĩ shi." Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba.  ۖ 
Wa Ĥarramnā `Alayhi Al-Marāđi`a Min Qablu Faqālat Hal 'Adullukum `Alá 'Ahli Baytin Yakfulūnahu Lakum Wa Hum Lahu Nāşiĥūna 028-012 Kuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: "Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi?"
Faradadnāhu 'Ilá 'Ummihi Kay Taqarra `Aynuhā Wa Lā Taĥzana Wa Lita`lama 'Anna Wa`da Al-Lahi Ĥaqqun Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna 028-013 Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba. ~
Wa Lammā Balagha 'Ashuddahu Wa Astawá 'Ātaynāhu Ĥukmāan Wa `Ilmāan  ۚ  Wa Kadhalika Naj Al-Muĥsinīna 028-014 Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.  ۚ 
Wa Dakhala Al-Madīnata `Alá Ĥīni Ghaflatin Min 'Ahlihā Fawajada Fīhā Rajulayni Yaqtatilāni Hādhā Min Shī`atihi Wa Hadhā Min `Adūwihi  ۖ  Fāstaghāthahu Al-Ladhī Min Shī`atihi `Alá Al-Ladhī Min `Adūwihi Fawakazahu Mūsá Faqađá `Alayhi  ۖ  Qāla Hādhā Min `Amali Ash-Shayţāni  ۖ  'Innahu `Adūwun Muđillun Mubīnun 028-015 Kuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: "Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne!"  ۖ   ۖ   ۖ 
Qāla Rabbi 'Innī Žalamtu Nafsī Fāghfir Lī Faghafara Lahu  ۚ  'Innahu Huwa Al-Ghafūru Ar-Raĥīmu 028-016 Ya ce: "Ya Uhangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara." Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai. ~  ۚ 
Qāla Rabbi Bimā 'An`amta `Alayya Falan 'Akūna Žahīrāan Lilmujrimīna 028-017 Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Dõmin abin da Ka ni'imta shi a kaina, sahõda haka bã zan kasance mai taimako ga mãsu laifi ba."
Fa'aşbaĥa Fī Al-Madīnati Khā'ifāan Yataraqqabu Fa'idhā Al-Ladhī Astanşarahu Bil-'Amsi Yastaşrikhuhu  ۚ  Qāla Lahu Mūsá 'Innaka Laghawīyun Mubīnun 028-018 Sai ya wãyi gari a cikin birnin yanã mai tsõro, yanã sauna. Sai ga wanda ya nẽmi taimako daga gare shi a jiya, yanã nẽman ãgajinsa. Mũsã ya ce masa, "Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne."  ۚ 
Falammā 'An 'Arāda 'An Yabţisha Bial-Ladhī Huwa `Adūwun Lahumā Qāla Yā Mūsá 'Aturīdu 'An Taqtulanī Kamā Qatalta Nafsāan Bil-'Amsi  ۖ  'In Turīdu 'Illā 'An Takūna Jabbārāan Al-'Arđi Wa Mā Turīdu 'An Takūna Mina Al-Muşliĥīna 028-019 To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce, "Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa."  ۖ 
Wa Jā'a Rajulun Min 'Aqşá Al-Madīnati Yas`á Qāla Yā Mūsá 'Inna Al-Mala'a Ya'tamirūna Bika Liyaqtulūka Fākhruj 'Innī Laka Mina An-Nāşiĥīna 028-020 Kuma wani mutum ya zo daga mafi nĩsan birnin yanã taliya da gaggãwa, ya ce: "Ya Mũsã! Lalle mashãwarta sunã shãwara game da kai dõmin su kashe ka sabõda haka ka fita. Lalle nĩ, mai nasĩha ne a gare ka."
Fakharaja Minhā Khā'ifāan Yataraqqabu  ۖ  Qāla Rabbi Najjinī Mina Al-Qawmi Až-Žālimīna 028-021 Sai ya fita daga gare ta, yanã mai jin tsõro yanã sauna. Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Kã tsẽrar da ni daga mutãne azzãlumai."  ۖ 
Wa Lammā Tawajjaha Tilqā'a Madyana Qāla `Asá Rabbī 'An Yahdiyanī Sawā'a As-Sabīl 028-022 Kuma a lõkacin da ya fuskanci wajen Madyana, ya ce: "Inã fatan Ubangijĩna Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya."
Wa Lammā Warada Mā'a Madyana Wajada `Alayhi 'Ummatan Mina An-Nāsi Yasqūna Wa Wajada Min Dūnihimu Amra'tayni Tadhūdāni  ۖ  Qāla Mā Khaţbukumā  ۖ  Qālatā Lā Nasqī Ĥattá Yuşdira Ar-Ri`ā'u  ۖ  Wa 'Abūnā Shaykhun Kabīrun 028-023 Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho ne mai daraja."  ۖ   ۖ   ۖ 
Fasaqá Lahumā Thumma Tawallá 'Ilá Až-Žilli Faqāla Rabbi 'Innī Limā 'Anzalta 'Ilayya Min Khayrin Faqīrun 028-024 Sai ya shãyar musu, sa'an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne."
Fajā'at/hu 'Iĥdāhumā Tamshī `Alá Astiĥyā'in Qālat 'Inna 'Abī Yad`ūka Liyajziyaka 'Ajra Mā Saqayta Lanā  ۚ  Falammā Jā'ahu Wa Qaşşa `Alayhi Al-Qaşaşa Qāla Lā Takhaf  ۖ  Najawta Mina Al-Qawmi Až-Žālimīna 028-025 Sai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, "Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu." To, a lõkacin da ya je masa,ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: "Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai."  ۚ   ۖ 
Qālat 'Iĥdāhumā Yā 'Abati Asta'jirhu  ۖ  'Inna Khayra Mani Asta'jarta Al-Qawīyu Al-'Amīnu 028-026 ayarsu ta ce, "Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi amintacce."  ۖ 
Qāla 'Innī 'Urīdu 'An 'Unkiĥaka 'Iĥdá Abnatayya Hātayni `Alá 'An Ta'juranī Thamāniyata Ĥijajin  ۖ  Fa'in 'Atmamta `Ashrāan Famin `Indika  ۖ  Wa Mā 'Urīdu 'An 'Ashuqqa `Alayka  ۚ  Satajidunī 'In Shā'a Al-Lahu Mina Aş-Şāliĥīna 028-027 Ya ce: "Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan 'yã'yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai."  ۖ   ۖ   ۚ 
Qāla Dhālika Baynī Wa Baynaka  ۖ  'Ayyamā Al-'Ajalayni Qađaytu Falā `Udwāna `Alayya Wa  ۖ  Allāhu `Alá Mā Naqūlu Wa Kīlun 028-028 Ya ce: "Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa."  ۖ   ۖ 
Falammā Qađá Mūsá Al-'Ajala Wa Sāra Bi'ahlihi 'Ānasa Min Jānibi Aţūri Nārāan Qāla Li'hlihi Amkuthū 'Innī 'Ānastu Nārāan La`allī 'Ātīkum Minhā Bikhabarin 'Aw Jadhwatin Mina An-Nāri La`allakum Taşţalūna 028-029 To, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (ũr). Ya cewa iyãlinsa, "Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi."
Falammā 'Atāhā Nūdī Min Shāţi'i Al-Wādī Al-'Aymani Fī Al-Buq`ati Al-Mubārakati Mina Ash-Shajarati 'An Yā Mūsá 'Innī 'Anā Al-Lahu Rabbu Al-`Ālamīna 028-030 To, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) "Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu."
Wa 'An 'Alqi `Aşāka  ۖ  Falammā Ra'āhā Tahtazzu Ka'annahā Jānnun Wallá Mudbirāan Wa Lam Yu`aqqib  ۚ  Yā Mūsá 'Aqbil Wa Lā Takhaf  ۖ  'Innaka Mina Al-'Āminīna 028-031 "Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya,bai kõma ba. "Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu."  ۖ   ۚ   ۖ 
Asluk Yadaka Fī Jaybika Takhruj Bayđā'a Min Ghayri Sū'in Wa Ađmum 'Ilayka Janāĥaka Mina Ar-Rahbi  ۖ  Fadhānika Burhānāni Min Rabbika 'Ilá Fir`awna Wa Mala'ihi  ۚ  'Innahum Kānū Qawmāan Fāsiqīna 028-032 "Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai."  ۖ  ~  ۚ 
Qāla Rabbi 'Innī Qataltu Minhum Nafsāan Fa'akhāfu 'An Yaqtulūni 028-033 Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle nã kashe wani rai daga gare su, dõmin haka inã tsõron kada su kashe ni."
Wa 'Akhī Hārūnu Huwa 'Afşaĥu Minnī Lisānāan Fa'arsilhu Ma`iya Rid'āan Yuşaddiqunī  ۖ  'Innī 'Akhāfu 'An Yukadhdhibūni 028-034 "Kuma ɗan'uwana Hãrũna shĩ ne mafi fasãha daga gareni, ga harshe, sabõda haka Ka aika shi tãre da ni, yanã mai taimako, yanã gaskata ni, lalle ne inã tsõron su ƙaryata ni."  ۖ 
Qāla Sanashuddu `Ađudaka Bi'akhīka Wa Naj`alu Lakumā Sulţānāan Falā Yaşilūna 'Ilaykumā  ۚ  Bi'āyātinā 'Antumā Wa Mani Attaba`akumā Al-Ghālibūna 028-035 Ya ce: "Zã Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan'uwanka kuma Mu sanya muku wani dalĩli, sabõda haka bã zã su sãdu zuwa gareku ba, tãre da ãyõyinMu, kũ da waɗanda suka bĩ ku ne marinjãya."  ۚ 
Falammā Jā'ahum Mūsá Bi'āyātinā Bayyinātin Qālū Mā Hādhā 'Illā Siĥrun Muftaráan Wa Mā Sami`nā Bihadhā Fī 'Ābā'inā Al-'Awwalīna 028-036 To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko."
Wa Qāla Mūsá Rabbī 'A`lamu Biman Jā'a Bil-Hudá Min `Indihi Wa Man Takūnu Lahu `Āqibatu Ad-Dāri  ۖ  'Innahu Lā Yufliĥu Až-Žālimūna 028-037 Kuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara."  ۖ 
Wa Qāla Fir`awnu Yā 'Ayyuhā Al-Mala'u Mā `Alimtu Lakum Min 'Ilahin Ghayrī Fa'awqid Lī Yā Hāmānu `Alá Aţīni Fāj`al Lī Şarĥāan La`allī 'Aţţali`u 'Ilá 'Ilahi Mūsá Wa 'Innī La'ažunnuhu Mina Al-Kādhibīna 028-038 Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."
Wa Astakbara Huwa Wa Junūduhu Fī Al-'Arđi Bighayri Al-Ĥaqqi Wa Žannū 'Annahum 'Ilaynā Lā Yurja`ūna 028-039 Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba.
Fa'akhadhnāhu Wa Junūdahu Fanabadhnāhum Al-Yammi  ۖ  Fānžur Kayfa Kāna `Āqibatu Až-Žālimīna 028-040 Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance.  ۖ 
Wa Ja`alnāhum 'A'immatan Yad`ūna 'Ilá An-Nāri  ۖ  Wa Yawma Al-Qiyāmati Lā Yunşarūna 028-041 Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta,kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba.  ۖ 
Wa 'Atba`nāhum Fī Hadhihi Ad-Dunyā La`natan  ۖ  Wa Yawma Al-Qiyāmati Hum Mina Al-Maqbūĥīna 028-042 Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu.  ۖ 
Wa Laqad 'Ātaynā Mūsá Al-Kitāba Min Ba`di Mā 'Ahlaknā Al-Qurūna Al-'Ūlá Başā'ira Lilnnāsi Wa Hudáan Wa Raĥmatan La`allahum Yatadhakkarūna 028-043 Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa.
Wa Mā Kunta Bijānibi Al-Gharbīyi 'Idh Qađaynā 'Ilá Mūsá Al-'Amra Wa Mā Kunta Mina Ash-Shāhidīn 028-044 Kuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba.
Wa Lakinnā 'Ansha'nā Qurūnāan Fataţāwala `Alayhimu Al-`Umuru  ۚ  Wa Mā Kunta Thāwīāan Fī 'Ahli Madyana Tatlū `Alayhim 'Āyātinā Wa Lakinnā Kunnā Mursilīna 028-045 Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game da waɗancan lãbarai).  ۚ 
Wa Mā Kunta Bijānibi Aţūri 'Idh Nādaynā Wa Lakin Raĥmatan Min Rabbika Litundhira Qawmāan Mā 'Atāhum Min Nadhīrin Min Qablika La`allahum Yatadhakkarūna 028-046 Kuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa.
Wa Lawlā 'An Tuşībahum Muşībatun Bimā Qaddamat 'Aydīhim Fayaqūlū Rabbanā Lawlā 'Arsalta 'Ilaynā Rasūlāan Fanattabi`a 'Āyātika Wa Nakūna Mina Al-Mu'uminīna 028-047 Kuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: "Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa,kuma mu kasance daga mũminai?"
Falammā Jā'ahumu Al-Ĥaqqu Min `Indinā Qālū Lawlā 'Ūtiya Mithla Mā 'Ūtiya Mūsá  ۚ  'Awalam Yakfurū Bimā 'Ūtiya Mūsá Min Qablu  ۖ  Qālū Siĥrāni Tažāharā Wa Qālū 'Innā Bikullin Kāfirūna 028-048 Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurinMu, suka ce: "Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba?" Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin (wannan)? suka ce: "Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna," kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu?"  ۚ   ۖ 
Qul Fa'tū Bikitābin Min `Indi Al-Lahi Huwa 'Ahdá Minhumā 'Attabi`hu 'In Kuntum Şādiqīna 028-049 Ka ce: "To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya."
Fa'in Lam Yastajībū Laka Fā`lam 'Annamā Yattabi`ūna 'Ahwā'ahum  ۚ  Wa Man 'Ađallu Mimmani Attaba`a Hawāhu Bighayri Hudáan Mina Al-Lahi  ۚ  'Inna Al-Laha Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna 028-050 To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai.  ۚ   ۚ 
Wa Laqad Waşşalnā Lahumu Al-Qawla La`allahum Yatadhakkarūna 028-051 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sãdar da magana sabõda su, tsammãninsu, suna tunãni.
Al-Ladhīna 'Ātaynāhumu Al-Kitāba Min Qablihi Hum Bihi Yu'uminūna 028-052 Waɗanda Muka bã su littãfi daga gabãninsa (Alƙur'ãni), su mãsu ĩmãni ne da shi.
Wa 'Idhā Yutlá `Alayhim Qālū 'Āmannā Bihi 'Innahu Al-Ĥaqqu Min Rabbinā 'Innā Kunnā Min Qablihi Muslimīna 028-053 Kuma idan anã karanta shi a kansu, sai su ce: "Mun yi ĩmãni da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mũ, mun kasance a gabãninsa masu sallamãwa." ~
'Ūlā'ika Yu'utawna 'Ajrahum Marratayni Bimā Şabarū Wa Yadra'ūna Bil-Ĥasanati As-Sayyi'ata Wa Mimmā Razaqnāhum Yunfiqūna 028-054 Waɗancan anã ba su lãdarsu sau biyu, sabõda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatãwa suna tunkuɗewar mũnanãwa kuma daga abin da Muka azũrtã susunã ciyarwa.
Wa 'Idhā Sami`ū Al-Laghwa 'A`rađū `Anhu Wa Qālū Lanā 'A`mālunā Wa Lakum 'A`mālukum Salāmun `Alaykum Lā Nabtaghī Al-Jāhilīna 028-055 Kuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, "Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai (da husũma)."
'Innaka Lā Tahdī Man 'Aĥbabta Wa Lakinna Al-Laha Yahdī Man Yashā'u  ۚ  Wa Huwa 'A`lamu Bil-Muhtadīna 028-056 Lalle ne kai bã ka shiryar da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa.  ۚ 
Wa Qālū 'In Nattabi`i Al-Hudá Ma`aka Nutakhaţţaf Min 'Arđinā  ۚ  'Awalam Numakkin Lahum Ĥaramāan 'Āmināan Yujbá 'Ilayhi Thamarātu Kulli Shay'in Rizqāan Min Ladunnā Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna 028-057 Kuma suka ce: "Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu daga ƙasamiu." Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.  ۚ 
Wa Kam 'Ahlaknā Min Qaryatin Baţirat Ma`īshatahā  ۖ  Fatilka Masākinuhum Lam Tuskan Min Ba`dihim 'Illā Qalīlāan  ۖ  Wa Kunnā Naĥnu Al-Wārithīna 028-058 Kuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rãyuwarta. To, waɗancan gidãjensu ne, ba a zaune su ba, a bãyansu, fãce kaɗan. Kuma mun kasance Mũ ne Magãda.  ۖ   ۖ 
Wa Mā Kāna Rabbuka Muhlika Al-Qurá Ĥattá Yab`atha Fī 'Ummihā Rasūlāan Yatlū `Alayhim 'Āyātinā  ۚ  Wa Mā Kunnā Muhlikī Al-Qurá 'Illā Wa 'Ahluhā Žālimūna 028-059 Kuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yanã karanta ãyõyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Mãsu halaka alƙaryu ba, fãce mutanensu sun kasance mãsu zãlunci.  ۚ 
Wa Mā 'Ūtītum Min Shay'in Famatā`u Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Zīnatuhā  ۚ  Wa Mā `Inda Al-Lahi Khayrun Wa 'Abqá  ۚ  'Afalā Ta`qilūna 028-060 Kuma abin da aka bã su daga kõme, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shĩ ne mafi alhẽri, knma mafi wanzuwa. Shin bã ku hankalta?  ۚ   ۚ 
'Afaman Wa`adnāhu Wa`dāan Ĥasanāan Fahuwa Lāqīhi Kaman Matta`nāhu Matā`a Al-Ĥayāati Ad-DunThumma Huwa Yawma Al-Qiyāmati Mina Al-Muĥđarīna 028-061 Shin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa'an nan shi a Rãnar ¡iyãma yanã daga mãsu shiga wuta?
Wa Yawma Yunādīhim Fayaqūlu 'Ayna Shurakā'iya Al-Ladhīna Kuntum Taz`umūna 028-062 Kuma rãnar da (Allah) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?"
Qāla Al-Ladhīna Ĥaqqa `Alayhimu Al-Qawlu Rabbanā Hā'uulā' Al-Ladhīna 'Aghwaynā 'Aghwaynāhum Kamā Ghawaynā  ۖ  Tabarra'nā 'Ilayka  ۖ  Mā Kānū 'Īyānā Ya`budūna 028-063 Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba."  ۖ   ۖ 
Wa Qīla AdShurakā'akum Fada`awhum Falam Yastajībū Lahum Wa Ra'aw Al-`Adhāba  ۚ  Law 'Annahum Kānū Yahtadūna 028-064 Kuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa !  ۚ 
Wa Yawma Yunādīhim Fayaqūlu Mādhā 'Ajabtumu Al-Mursalīna 028-065 Kuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: "Mẽne nekuka karɓa wa Mananni?"
Fa`amiyat `Alayhimu Al-'Anbā'u Yawma'idhin Fahum Lā Yatasā'alūna 028-066 Sai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnaosu ba.
Fa'ammā Man Tāba Wa 'Āmana Wa `Amila Şāliĥāan Fa`asá 'An Yakūna Mina Al-Mufliĥīna 028-067 To, amma wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni' ya aikata aiki na ƙwarai, to, akwai fãtan su kasance daga mãsu cin nasara.
Wa Rabbuka Yakhluqu Mā Yashā'u Wa Yakhtāru  ۗ  Mā Kāna Lahumu Al-Khiyaratu  ۚ  Subĥāna Al-Lahi Wa Ta`ālá `Ammā Yushrikūna 028-068 Kuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba.Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.  ۗ   ۚ 
Wa Rabbuka Ya`lamu Mā Tukinnu Şudūruhum Wa Mā Yu`linūna 028-069 Kuma Ubangijinka Yanã sanin abin da zukãtansu ke ɓõyẽwa, da abin da suke bayyanãwa.
Wa Huwa Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  Lahu Al-Ĥamdu Fī Al-'Ūlá Wa Al-'Ākhirati  ۖ  Wa Lahu Al-Ĥukmu Wa 'Ilayhi Turja`ūna 028-070 Kuma Shĩ ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kuma Shi ne abin gõdiya a cikin ta farko (dũniya), da ta ƙarshe (Lãhira). Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. ~  ۖ   ۖ 
Qul 'Ara'aytum 'In Ja`ala Al-Lahu `Alaykumu Al-Layla Sarmadāan 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati Man 'Ilahun Ghayru Al-Lahi Ya'tīkum Biđiyā'in  ۖ  'Afalā Tasma`ūna 028-071 Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji?"  ۖ 
Qul 'Ara'aytum 'In Ja`ala Al-Lahu `Alaykumu An-Nahāra Sarmadāan 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati Man 'Ilahun Ghayru Al-Lahi Ya'tīkum Bilaylin Taskunūna Fīhi  ۖ  'Afalā Tubşirūna 028-072 Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani?" ~  ۖ 
Wa Min Raĥmatihi Ja`ala Lakumu Al-Layla Wa An-Nahāra Litaskunū Fīhi Wa Litabtaghū Min Fađlihi Wa La`allakum Tashkurūna 028-073 "Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde."
Wa Yawma Yunādīhim Fayaqūlu 'Ayna Shurakā'iya Al-Ladhīna Kuntum Taz`umūna 028-074 Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: "Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa"
Wa Naza`nā Min Kulli 'Ummatin Shahīdāan Faqulnā Hātū Burhānakum Fa`alimū 'Anna Al-Ĥaqqa Lillahi Wa Đalla `Anhum Mā Kānū Yaftarūna 028-075 Kuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: "Ku kãwo dalilinku." Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu.
'Inna Qārūna Kāna Min Qawmi Mūsá Fabaghá `Alayhim  ۖ  Wa 'Ātaynāhu Mina Al-Kunūzi Mā 'Inna Mafātiĥahu Latanū'u Bil-`Uşbati 'Ū Al-Qūwati 'Idh Qāla Lahu Qawmuhu Lā Tafraĥ  ۖ  'Inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Al-Farīna 028-076 Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa."  ۖ   ۖ 
Wa Abtaghi Fīmā 'Ātāka Al-Lahu Ad-Dāra Al-'Ākhirata  ۖ  Wa Lā Tansa Naşībaka Mina Ad-Dunyā  ۖ  Wa 'Aĥsin Kamā 'Aĥsana Al-Lahu 'Ilayka  ۖ  Wa Lā Tabghi Al-Fasāda Fī Al-'Arđi  ۖ  'Inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Al-Mufsidīna 028-077 "Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna."  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ 
Qāla 'Innamā 'Ūtītuhu `Alá `Ilmin `Indī  ۚ  'Awalam Ya`lam 'Anna Al-Laha Qad 'Ahlaka Min Qablihi Mina Al-Qurūni Man Huwa 'Ashaddu Minhu Qūwatan Wa 'Aktharu Jam`āan  ۚ  Wa Lā Yus'alu `An Dhunūbihimu Al-Mujrimūna 028-078 Ya ce: "An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba?  ۚ   ۚ 
Fakharaja `Alá Qawmihi Fī Zīnatihi  ۖ  Qāla Al-Ladhīna Yurīdūna Al-Ĥayāata Ad-Dunyā Yālayta Lanā Mithla Mā 'Ūtiya Qārūnu 'Innahu Ladhū Ĥažžin `Ažīmin 028-079 Sai (¡ãrũna) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: "Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa ¡ãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne."  ۖ 
Wa Qāla Al-Ladhīna 'Ū Al-`Ilma Waylakum Thawābu Al-Lahi Khayrun Liman 'Āmana Wa `Amila Şāliĥāan Wa Lā Yulaqqāhā 'Illā Aş-Şābirūna 028-080 Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai ha ƙuri."
Fakhasafnā Bihi Wa Bidārihi Al-'Arđa Famā Kāna Lahu Min Fi'atin Yanşurūnahu Min Dūni Al-Lahi Wa Mā Kāna Mina Al-Muntaşirīna 028-081 Sai Muka shãfe ƙasa da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.
Wa 'Aşbaĥa Al-Ladhīna Tamannaw Makānahu Bil-'Amsi Yaqūlūna Wayka'anna Al-Laha Yabsuţu Ar-Rizqa Liman Yashā'u Min `Ibādihi Wa Yaqdiru  ۖ  Lawlā 'An Manna Al-Lahu `Alaynā Lakhasafa Binā  ۖ  Wayka'annahu Lā Yufliĥu Al-Kāfirūna 028-082 Kuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, "Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara."  ۖ   ۖ 
Tilka Ad-Dāru Al-'Ākhiratu Naj`aluhā Lilladhīna Lā Yurīdūna `Ulūwāan Al-'Arđi Wa Lā Fasādāan Wa  ۚ  Al-`Āqibatu Lilmuttaqīna 028-083 Wancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take.  ۚ 
Man Jā'a Bil-Ĥasanati Falahu Khayrun Minhā  ۖ  Wa Man Jā'a Bis-Sayyi'ati Falā Yuj Al-Ladhīna `Amilū As-Sayyi'āti 'Illā Mā Kānū Ya`malūna 028-084 Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.  ۖ 
'Inna Al-Ladhī Farađa `Alayka Al-Qur'āna Larādduka 'Ilá Ma`ādin  ۚ  Qul Rabbī 'A`lamu Man Jā'a Bil-Hudá Wa Man Huwa Fī Đalālin Mubīnin 028-085 Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananna."  ۚ 
Wa Mā Kunta Tarjū 'An Yulqá 'Ilayka Al-Kitābu 'Illā Raĥmatan Min Rabbika  ۖ  Falā Takūnanna Žahīrāan Lilkāfirīna 028-086 Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako ga kãfirai.  ۖ 
Wa Lā Yaşuddunnaka `An 'Āyāti Al-Lahi Ba`da 'Idh 'Unzilat 'Ilayka  ۖ  Wa Ad`u 'Ilá Rabbika  ۖ  Wa Lā Takūnanna Mina Al-Mushrikīna 028-087 Kuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ãyõyin Allah, a bãyãn har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga mãsu shirka.  ۖ   ۖ 
Wa Lā Tad`u Ma`a Al-Lahi 'Ilahāan 'Ākhara  ۘ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۚ  Kullu Shay'in Hālikun 'Illā Wajhahu Lahu  ۚ  Al-Ĥukmu Wa 'Ilayhi Turja`ūna 028-088 Kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kõwane abu mai halaka ne fãce fuskarSa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.  ۘ  ~  ۚ   ۚ 
Next Sūrah