27) Sūrat An-Naml

Printed format

27) سُورَة النَّمل

Ţā-Sīn Tilka 'Āyātu Al-Qur'āni Wa Kitābin Mubīnin َ027-001 ¦.S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa. طَا-سِين تِلْكَ آيَاتُ الْقُرْآنِ وَكِتَاب ٍ مُبِين ٍ
Hudáan Wa Bushrá Lilmu'uminīna َ027-002 Shiriya ce da bushãra ga mũminai. هُدى ً وَبُشْرَى لِلْمُؤْمِنِينَ
Al-Ladhīna Yuqīmūna Aş-Şalāata Wa Yu'utūna Az-Zakāata Wa Hum Bil-'Ākhirati Hum Yūqinūna َ027-003 Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ,sunã yin yaƙĩni. الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلاَةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ بِالآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ
'Inna Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati Zayyannā Lahum 'A`mālahum Fahum Ya`mahūna َ027-004 Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa. إِنَّ الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ زَيَّنَّا لَهُمْ أَعْمَالَهُمْ فَهُمْ يَعْمَهُونَ
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Lahum Sū'u Al-`Adhābi Wa Hum Al-'Ākhirati Humu Al-'Akhsarūna َ027-005 Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra. أُوْلَائِكَ الَّذِينَ لَهُمْ سُوءُ الْعَذَابِ وَهُمْ فِي الآخِرَةِ هُمُ الأَخْسَرُونَ
Wa 'Innaka Latulaqqá Al-Qur'āna Min Ladun Ĥakīmin `Alīmin َ027-006 Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani. وَإِنَّكَ لَتُلَقَّى الْقُرْآنَ مِنْ لَدُنْ حَكِيمٍ عَلِيم ٍ
'Idh Qāla Mūsá Li'hlihi 'Innī 'Ānastu Nārāan Sa'ātīkum Minhā Bikhabarin 'Aw 'Ātīkum Bishihābin Qabasin La`allakum Taşţalūna َ027-007 A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi." إِذْ قَالَ مُوسَى لِأهْلِهِ~ِ إِنِّي آنَسْتُ نَارا ً سَآتِيكُمْ مِنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ آتِيكُمْ بِشِهَاب ٍ قَبَس ٍ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ
Falammā Jā'ahā Nūdiya 'Anrika Man An-Nāri Wa Man Ĥawlahā Wa Subĥāna Al-Lahi Rabbi Al-`Ālamīna َ027-008 To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu." فَلَمَّا جَاءَهَا نُودِيَ أَنْ بُورِكَ مَنْ فِي النَّارِ وَمَنْ حَوْلَهَا وَسُبْحَانَ اللَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Yā Mūsá 'Innahu 'Anā Al-Lahu Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ027-009 "Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima." يَا مُوسَى إِنَّهُ~ُ أَنَا اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Wa 'Alqi `Aşāka  ۚ  Falammā Ra'āhā Tahtazzu Ka'annahā Jānnun Wallá Mudbirāan Wa Lam Yu`aqqib  ۚ  Yā Mūsá Lā Takhaf 'Innī Lā Yakhāfu Ladayya Al-Mursalūna َ027-010 "Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa." وَأَلْقِ عَصَاكَ  ۚ  فَلَمَّا رَآهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَانّ ٌ وَلَّى مُدْبِرا ً وَلَمْ يُعَقِّبْ  ۚ  يَا مُوسَى لاَ تَخَفْ إِنِّي لاَ يَخَافُ لَدَيَّ الْمُرْسَلُونَ
'Illā Man Žalama Thumma Baddala Ĥusnāan Ba`da Sū'in Fa'innī Ghafūrun Raĥīmun َ027-011 "Sai wanda ya yi zãlunci, sa'an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." إِلاَّ مَنْ ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسْنا ً بَعْدَ سُوء ٍ فَإِنِّي غَفُور ٌ رَحِيم ٌ
Wa 'Adkhil Yadaka Fī Jaybika Takhruj Bayđā'a Min Ghayri Sū'in  ۖ  Fī Tis`i 'Āyātin 'Ilá Fir`awna Wa Qawmihi  ۚ  'Innahum Kānū Qawmāan Fāsiqīna َ027-012 "Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai." وَأَدْخِلْ يَدَكَ فِي جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَاءَ مِنْ غَيْرِ سُوء ٍ  ۖ  فِي تِسْعِ آيَات ٍ إِلَى فِرْعَوْنَ وَقَوْمِهِ~ِ  ۚ  إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْما ً فَاسِقِينَ
Falammā Jā'at/hum 'Āyātunā Mubşiratan Qālū Hādhā Siĥrun Mubīnun َ027-013 To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne. فَلَمَّا جَاءَتْهُمْ آيَاتُنَا مُبْصِرَة ً قَالُوا هَذَا سِحْر ٌ مُبِين ٌ
Wa Jaĥadū Bihā Wa Astayqanat/hā 'Anfusuhum Žulmāan Wa `Ulūwāan  ۚ  Fānžur Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mufsidīna َ027-014 Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance. وَجَحَدُوا بِهَا وَاسْتَيْقَنَتْهَا أَنْفُسُهُمْ ظُلْما ً وَعُلُوّا ً  ۚ  فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ
Wa Laqad 'Ātaynā Dāwūda Wa Sulaymāna `Ilmāan  ۖ  Wa Qālā Al-Ĥamdu Lillahi Al-Ladhī Fađđalanā `Alá Kathīrin Min `Ibādihi Al-Mu'uminīna َ027-015 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai." وَلَقَدْ آتَيْنَا دَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ عِلْما ً  ۖ  وَقَالاَ الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي فَضَّلَنَا عَلَى كَثِير ٍ مِنْ عِبَادِهِ الْمُؤْمِنِينَ
Wa Waritha Sulaymānu Dāwūda  ۖ  Wa Qāla Yā 'Ayyuhā An-Nāsu `Ullimnā Manţiqa Aţ-Ţayri Wa 'Ūtīnā Min Kulli Shay'in  ۖ  'Inna Hādhā Lahuwa Al-Fađlu Al-Mubīnu َ027-016 Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: "Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna." وَوَرِثَ سُلَيْمَانُ دَاوُودَ  ۖ  وَقَالَ يَاأَيُّهَا النَّاسُ عُلِّمْنَا مَنطِقَ الطَّيْرِ وَأُوتِينَا مِنْ كُلِّ شَيْء ٍ إِنَّ  ۖ  هَذَا لَهُوَ الْفَضْلُ الْمُبِينُ
Wa Ĥushira Lisulaymāna Junūduhu Mina Al-Jinni Wa Al-'Insi Wa Aţ-Ţayri Fahum Yūza`ūna َ027-017 Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya). وَحُشِرَ لِسُلَيْمَانَ جُنُودُه ُُ مِنَ الْجِنِّ وَالإِنْسِ وَالطَّيْرِ فَهُمْ يُوزَعُونَ
Ĥattá 'Idhā 'Ataw `Alá Wādī An-Namli Qālat Namlatun Yā 'Ayyuhā An-Namlu Adkhulū Masākinakum Lā Yaĥţimannakum Sulaymānu Wa Junūduhu Wa Hum Lā Yash`urūna َ027-018 Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba." حَتَّى إِذَا أَتَوْا عَلَى وَادِي النَّمْلِ قَالَتْ نَمْلَة ٌ يَاأَيُّهَا النَّمْلُ ادْخُلُوا مَسَاكِنَكُمْ لاَ يَحْطِمَنَّكُمْ سُلَيْمَانُ وَجُنُودُه ُُ وَهُمْ لاَ يَشْعُرُونَ
Fatabassama Đāĥikāan Min Qawlihā Wa Qāla Rabbi 'Awzi`nī 'An 'Ashkura Ni`mataka Allatī 'An`amta `Alayya Wa `Alá Wa A-Dayya Wa 'An 'A`mala Şāliĥāan Tarđāhu Wa 'Adkhilnī Biraĥmatika Fī `Ibādika Aş-Şāliĥīna َ027-019 Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai." فَتَبَسَّمَ ضَاحِكا ً مِنْ قَوْلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَى وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَالِحا ً تَرْضَاه ُُ وَأَدْخِلْنِي بِرَحْمَتِكَ فِي عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ
Wa Tafaqqada Aţ-Ţayra Faqāla Mā Lī Lā 'Ará Al-Hud/huda 'Am Kāna Mina Al-Ghā'ibīna َ027-020 Kuma ya binciki tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?" وَتَفَقَّدَ الطَّيْرَ فَقَالَ مَا لِي لاَ أَرَى الْهُدْهُدَ أَمْ كَانَ مِنَ الْغَائِبِينَ
La'u`adhdhibannahu `Adhābāan Shadīdāan 'Aw La'adhbaĥannahu 'Aw Laya'tiyanī Bisulţānin Mubīnin َ027-021 "Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne." لَأُعَذِّبَنَّه ُُ عَذَابا ً شَدِيداً أَوْ لَأَذْبَحَنَّهُ~ُ أَوْ لَيَأْتِيَنِي بِسُلْطَان ٍ مُبِين ٍ
Famakatha Ghayra Ba`īdin Faqāla 'Aĥaţtu Bimā Lam Tuĥiţ Bihi Wa Ji'tuka Min Saba'iin Binaba'iin Yaqīnin َ027-022 Sai ya zauna bã nẽsa ba, sa'an nan ya ce: "Nã san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba da wani lãbari tabbatacce." فَمَكَثَ غَيْرَ بَعِيد ٍ فَقَالَ أَحَطتُ بِمَا لَمْ تُحِطْ بِه ِِ وَجِئْتُكَ مِنْ سَبَإ ٍ بِنَبَإ ٍ يَقِين ٍ
'Innī Wa Jadttu Amra'atan Tamlikuhum Wa 'Ūtiyat Min Kulli Shay'in Wa Lahā `Arshun `Ažīmun َ027-023 "Lalle ni nã sãmi wata mace wadda tanã mulkinsu kuma an bã ta daga dukkan kõme, kuma tanã da gadon sarauta mai girma. إِنِّي وَجَدتُّ امْرَأَة ً تَمْلِكُهُمْ وَأُوتِيَتْ مِنْ كُلِّ شَيْء ٍ وَلَهَا عَرْشٌ عَظِيم ٌ
Wa Jadtuhā Wa Qawmahā Yasjudūna Lilshshamsi Min Dūni Al-Lahi Wa Zayyana Lahumu Ash-Shayţānu 'A`mālahum Faşaddahum `Ani As-Sabīli Fahum Lā Yahtadūna َ027-024 "Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa." وَجَدْتُهَا وَقَوْمَهَا يَسْجُدُونَ لِلشَّمْسِ مِنْ دُونِ اللَّهِ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ فَهُمْ لاَ يَهْتَدُونَ
'Allā Yasjudū Lillahi Al-Ladhī Yukhriju Al-Khab'a Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Ya`lamu Mā Tukhfūna Wa Mā Tu`linūna َ027-025 "Ga su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa." أَلاَّ يَسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي يُخْرِجُ الْخَبْءَ فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا تُخْفُونَ وَمَا تُعْلِنُونَ
Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Rabbu Al-`Arshi Al-`Ažīmi َ027-026 "Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin Al'arshi, mai girma." اللَّهُ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ
Qāla Sananžuru 'Aşadaqta 'Am Kunta Mina Al-Kādhibīna َ027-027 Ya ce: "Za mu dũba shin kã yi gaskiya ne, kõ kuwa kã kasance daga maƙaryata?" قَالَ سَنَنظُرُ أَصَدَقْتَ أَمْ كُنتَ مِنَ الْكَاذِبِينَ
Adh/hab Bikitābī Hādhā Fa'alqih 'Ilayhim Thumma Tawalla `Anhumnžur Mādhā Yarji`ūna َ027-028 "Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa." اذْهَب بِكِتَابِي هَذَا فَأَلْقِه إِلَيْهِمْ ثُمَّ تَوَلَّ عَنْهُمْ فَانظُرْ مَاذَا يَرْجِعُونَ
Qālat Yā 'Ayyuhā Al-Mala'u 'Innī 'Ulqiya 'Ilayya Kitābun Karīmun َ027-029 Ta ce: "Yã kũ mashawarta! Lalle ne, an jẽfo, zuwa gareni, wata takarda mai girma." قَالَتْ يَا أَيُّهَا المَلَأُ إِنِّي أُلْقِيَ إِلَيَّ كِتَاب ٌ كَرِيم ٌ
'Innahu Min Sulaymāna Wa 'Innahu Bismi Al-Lahi Ar-Raĥmāni Ar-Raĥīmi َ027-030 "Lalle ita daga Sulaiman take, kuma lalle ita da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai ne." إِنَّه ُُ مِنْ سُلَيْمَانَ وَإِنَّه ُُ بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
'Allā Ta`lū `Alayya Wa 'Tūnī Muslimīna َ027-031 "Kada ku yi girman kai a gare ni, kuma ku zo mini kunã mãsu sallamãwa." أَلاَّ تَعْلُوا عَلَيَّ وَأْتُونِي مُسْلِمِينَ
Qālat Yā 'Ayyuhā Al-Mala'u 'Aftūnī Fī 'Amrī Mā Kuntu Qāţi`atan 'Amrāan Ĥattá Tash/hadūni َ027-032 Ta ce: "Yã ku mashawarta ! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta." قَالَتْ يَاأَيُّهَا المَلَأُ أَفْتُونِي فِي أَمْرِي مَا كُنتُ قَاطِعَةً أَمْراً حَتَّى تَشْهَدُونِ
Qālū Naĥnu 'Ūlū Qūwatin Wa 'Ūlū Ba'sin Shadīdin Wa Al-'Amru 'Ilayki Fānžurī Mādhā Ta'murīna َ027-033 Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da shi)?" قَالُوا نَحْنُ أُوْلُوا قُوَّة ٍ وَأُولُوا بَأْس ٍ شَدِيد ٍ وَالأَمْرُ إِلَيْكِ فَانظُرِي مَاذَا تَأْمُرِينَ
Qālat 'Inna Al-Mulūka 'Idhā Dakhalū Qaryatan 'Afsadūhā Wa Ja`alū 'A`izzata 'Ahlihā 'Adhillatan  ۖ  Wa Kadhalika Yaf`alūna َ027-034 Ta ce: "Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa." قَالَتْ إِنَّ الْمُلُوكَ إِذَا دَخَلُوا قَرْيَةً أَفْسَدُوهَا وَجَعَلُوا أَعِزَّةَ أَهْلِهَا أَذِلَّة ً  ۖ  وَكَذَلِكَ يَفْعَلُونَ
Wa 'Innī Mursilatun 'Ilayhim Bihadīyatin Fanāžiratun Bima Yarji`u Al-Mursalūna َ027-035 "Kuma lalle nĩ mai aikãwa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dũbawa ce: Da me manzannin zã su kõmo." وَإِنِّي مُرْسِلَة ٌ إِلَيْهِمْ بِهَدِيَّة ٍ فَنَاظِرَة ٌ بِمَ يَرْجِعُ الْمُرْسَلُونَ
Falammā Jā'a Sulaymāna Qāla 'Atumiddūnani Bimālin Famā 'Ātāniya Al-Lahu Khayrun Mimmā 'Ātākum Bal 'Antum Bihadīyatikum Tafraĥūna َ027-036 To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: "Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To, abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke yin farin ciki da kyautarku." فَلَمَّا جَاءَ سُلَيْمَانَ قَالَ أَتُمِدُّونَنِ بِمَال ٍ فَمَا آتَانِيَ اللَّهُ خَيْر ٌ مِمَّا آتَاكُمْ بَلْ أَنْتُمْ بِهَدِيَّتِكُمْ تَفْرَحُونَ
Arji` 'Ilayhim Falana'tiyannahum Bijunūdin Lā Qibala Lahum Bihā Wa Lanukhrijannahum Minhā 'Adhillatan Wa Hum Şāghirūna َ027-037 "Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu." ارْجِعْ إِلَيْهِمْ فَلَنَأْتِيَنَّهُمْ بِجُنُود ٍ لاَ قِبَلَ لَهُمْ بِهَا وَلَنُخْرِجَنَّهُمْ مِنْهَا أَذِلَّة ً وَهُمْ صَاغِرُونَ
Qāla Yā 'Ayyuhā Al-Mala'u 'Ayyukum Ya'tīnī Bi`arshihā Qabla 'An Ya'tūnī Muslimīna َ027-038 Ya ce: "Yã ku mashãwarta! Wannenku zai zo mini da gadonta a gabãnin su zo, sunã mãsu sallamãwa?" قَالَ يَاأَيُّهَا المَلَأُ أَيُّكُمْ يَأْتِينِي بِعَرْشِهَا قَبْلَ أَنْ يَأْتُونِي مُسْلِمِينَ
Qāla `Ifrytun Mina Al-Jinni 'Anā 'Ātīka Bihi Qabla 'An Taqūma Min Maqāmika  ۖ  Wa 'Innī `Alayhi Laqawīyun 'Amīnun َ027-039 Wani mai ƙarfi daga aljannu ya ce: "Nĩ inã zo maka da shi a gabãnin ka tãshi daga matsayinka. Kuma llale nĩ a gare shi, haƙĩƙa, mai ƙarfi ne amintacce." قَالَ عِفْريت ٌ مِنَ الْجِنِّ أَنَا آتِيكَ بِه ِِ قَبْلَ أَنْ تَقُومَ مِنْ مَقَامِكَ  ۖ  وَإِنِّي عَلَيْهِ لَقَوِيٌّ أَمِين ٌ
Qāla Al-Ladhī `Indahu `Ilmun Mina Al-Kitābi 'Anā 'Ātīka Bihi Qabla 'An Yartadda 'Ilayka Ţarfuka  ۚ  Falammā Ra'āhu Mustaqirrāan `Indahu Qāla Hādhā Min Fađli Rabbī Liyabluwanī 'A'ashkuru 'Am 'Akfuru  ۖ  Wa Man Shakara Fa'innamā Yashkuru Linafsihi  ۖ  Wa Man Kafara Fa'inna Rabbī Ghanīyun Karīmun َ027-040 Wanda yake a wurinsa akwai wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi." قَالَ الَّذِي عِنْدَه ُُ عِلْم ٌ مِنَ الْكِتَابِ أَنَا آتِيكَ بِه ِِ قَبْلَ أَنْ يَرْتَدَّ إِلَيْكَ طَرْفُكَ  ۚ  فَلَمَّا رَآهُ مُسْتَقِرّاً عِنْدَه ُُ قَالَ هَذَا مِنْ فَضْلِ رَبِّي لِيَبْلُوَنِي أَأَشْكُرُ أَمْ أَكْفُرُ  ۖ  وَمَنْ شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِه ِِ  ۖ  وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيّ ٌ كَرِيم ٌ
Qāla Nakkirū Lahā `Arshahā Nanžur 'Atahtadī 'Am Takūnu Mina Al-Ladhīna Lā Yahtadūna َ027-041 Ya ce: "Ku canza kamar gadonta gare ta, mu gani, shin zã ta shiryu, kõ kuwa tanã kasancẽwa daga waɗanda bã su shiryuwa." قَالَ نَكِّرُوا لَهَا عَرْشَهَا نَنظُرْ أَتَهْتَدِي أَمْ تَكُونُ مِنَ الَّذِينَ لاَ يَهْتَدُونَ
Falammā Jā'at Qīla 'Ahakadhā `Arshuki  ۖ  Qālat Ka'annahu Huwa  ۚ  Wa 'Ūtīnā Al-`Ilma Min Qablihā Wa Kunnā Muslimīna َ027-042 To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce: "Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu sallamãwar (al'amari ga Allah)." فَلَمَّا جَاءَتْ قِيلَ أَهَكَذَا عَرْشُكِ  ۖ  قَالَتْ كَأَنَّه ُُ هُوَ  ۚ  وَأُوتِينَا الْعِلْمَ مِنْ قَبْلِهَا وَكُنَّا مُسْلِمِينَ
Wa Şaddahā Mā Kānat Ta`budu Min Dūni Al-Lahi  ۖ  'Innahā Kānat Min Qawmin Kāfirīna َ027-043 Kuma abin da ta kasance tanã bautãwa, baicin Allah, ya kange ta. Lalle ita, tã kasance daga mutãne kãfirai. وَصَدَّهَا مَا كَانَتْ تَعْبُدُ مِنْ دُونِ اللَّهِ  ۖ  إِنَّهَا كَانَتْ مِنْ قَوْم ٍ كَافِرِينَ
Qīla Lahā Adkhulī Aş-Şarĥa  ۖ  Falammā Ra'at/hu Ĥasibat/hu Lujjatan Wa Kashafat `An Sāqayhā  ۚ  Qāla 'Innahu Şarĥun Mumarradun Min Qawārīra  ۗ  Qālat Rabbi 'Innī Žalamtu Nafsī Wa 'Aslamtu Ma`a Sulaymāna Lillahi Rabbi Al-`Ālamīna َ027-044 Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu." قِيلَ لَهَا ادْخُلِي الصَّرْحَ  ۖ  فَلَمَّا رَأَتْهُ حَسِبَتْهُ لُجَّة ً وَكَشَفَتْ عَنْ سَاقَيْهَا  ۚ  قَالَ إِنَّه ُُ صَرْح ٌ مُمَرَّد ٌ مِنْ قَوَارِيرَ  ۗ  قَالَتْ رَبِّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي وَأَسْلَمْتُ مَعَ سُلَيْمَانَ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Wa Laqad 'Arsalnā 'Ilá Thamūda 'Akhāhum Şāliĥāan 'Ani A`budū Al-Laha Fa'idhā Hum Farīqāni Yakhtaşimūna َ027-045 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, mun aika zuwa Samũdãwa da ɗan'uwansu, Salihu (ya ce), "Ku bauta wa Allah." Sai gã su ƙungiyõyi biyu sunã ta husũma. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَى ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحاً أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ فَإِذَا هُمْ فَرِيقَانِ يَخْتَصِمُونَ
Qāla Yā Qawmi Lima Tasta`jilūna Bis-Sayyi'ati Qabla Al-Ĥasanati  ۖ  Lawlā Tastaghfirūna Al-Laha La`allakum Turĥamūna َ027-046 Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?" قَالَ يَاقَوْمِ لِمَ تَسْتَعْجِلُونَ بِالسَّيِّئَةِ قَبْلَ الْحَسَنَةِ لَوْلاَ  ۖ  تَسْتَغْفِرُونَ اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Qālū Aţţayyarnā Bika Wa Biman Ma`aka  ۚ  Qāla Ţā'irukum `Inda Al-Lahi  ۖ  Bal 'Antum Qawmun Tuftanūna َ027-047 Suka ce: "Munã shu'umci da kai, kuma da wanda ke tãre da kai." Ya ce: "Shu'umcinku a wurin Allah yake. Ã'a, kũ mutãne ne, anã fitinar ku." قَالُوا اطَّيَّرْنَا بِكَ وَبِمَنْ مَعَكَ  ۚ  قَالَ طَائِرُكُمْ عِنْدَ اللَّهِ  ۖ  بَلْ أَنْتُمْ قَوْم ٌ تُفْتَنُونَ
Wa Kāna Fī Al-Madīnati Tis`atu Rahţin Yufsidūna Fī Al-'Arđi Wa Lā Yuşliĥūna َ027-048 Kuma waɗansu jama'a tara sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa, shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'." وَكَانَ فِي الْمَدِينَةِ تِسْعَةُ رَهْط ٍ يُفْسِدُونَ فِي الأَرْضِ وَلاَ يُصْلِحُونَ
Qālū Taqāsamū Bil-Lahi Lanubayyitannahu Wa 'Ahlahu Thumma Lanaqūlanna Liwalīyihi Mā Shahidnā Mahlika 'Ahlihi Wa 'Innā Laşādiqūna َ027-049 Kuma suka ƙulla mãkirci, kuma Muka ƙulla sakamakon mãkirci, alhãli sũ ba su sani ba. قَالُوا تَقَاسَمُوا بِاللَّهِ لَنُبَيِّتَنَّه ُُ وَأَهْلَه ُُ ثُمَّ لَنَقُولَنَّ لِوَلِيِّه ِِ مَا شَهِدْنَا مَهْلِكَ أَهْلِه ِِ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ
Wa Makarū Makrāan Wa Makarnā Makrāan Wa Hum Lā Yash`urūna َ027-050 Ka dũba yadda ãƙibar mãkircinsu ta kasance lalle Mũ Mun darkãke su da mutãnensu, gabã ɗaya. وَمَكَرُوا مَكْرا ً وَمَكَرْنَا مَكْرا ً وَهُمْ لاَ يَشْعُرُونَ
nžur Kayfa Kāna `Āqibatu Makrihim 'Annā Dammarnāhum Wa Qawmahum 'Ajma`īna َ027-051 Waɗancan, gidãjensu ne, wõfintattu sabõda zãluncin da suka yi, lalle ne a wancan akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke sani. فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ مَكْرِهِمْ أَنَّا دَمَّرْنَاهُمْ وَقَوْمَهُمْ أَجْمَعِينَ
Fatilka Buyūtuhum Khāwiyatan Bimā Žalamū  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Liqawmin Ya`lamūna َ027-052 Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sun kasance sunã taƙawa. فَتِلْكَ بُيُوتُهُمْ خَاوِيَة ً بِمَا ظَلَمُوا  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِقَوْم ٍ يَعْلَمُونَ
Wa 'Anjaynā Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Kānū Yattaqūna َ027-053 Da Lũdu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Shin kunã jẽ wa alfasha ne, alhãli, kuwa kunã gani?" وَأَنجَيْنَا الَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ
Wa Lūţāan 'Idh Qāla Liqawmihi 'Ata'tūna Al-Fāĥishata Wa 'Antum Tubşirūna َ027-054 "Shin lalle kũ haƙĩƙa kunã je wa maza da sha'awa baicin mãtã? Ã'a, kũ wasu irin mutãne ne kuna aikin jãhilci." وَلُوطا ً إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ~ِ أَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ وَأَنْتُمْ تُبْصِرُونَ
'A'innakum Lata'tūna Ar-Rijāla Shahwatan Min Dūni An-Nisā'  ۚ  Bal 'Antum Qawmun Tajhalūna َ027-055 49. أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ شَهْوَة ً مِنْ دُونِ النِسَاء  ۚ  بَلْ أَنْتُمْ قَوْم ٌ تَجْهَلُونَ
Famā Kāna Jawāba Qawmihi 'Illā 'An Qālū 'Akhrijū 'Āla Lūţin Min Qaryatikum  ۖ  'Innahum 'Unāsun Yataţahharūna َ027-056 Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce "Ku fitar da mutãnen Lũɗu daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki." فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ~ِ إِلاَّ أَنْ قَالُوا أَخْرِجُوا آلَ لُوط ٍ مِنْ قَرْيَتِكُمْ  ۖ  إِنَّهُمْ أُنَاس ٌ يَتَطَهَّرُونَ
Fa'anjaynāhu Wa 'Ahlahu 'Illā Amra'atahu Qaddarnāhā Mina Al-Ghābirīna َ027-057 Sai Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa, fãce mãtarsa, Mun ƙaddara ta a cikin mãsu wanzuwa. فَأَنجَيْنَاه ُُ وَأَهْلَهُ~ُ إِلاَّ امْرَأَتَه ُُ قَدَّرْنَاهَا مِنَ الْغَابِرِينَ
Wa 'Amţarnā `Alayhim Maţarāan  ۖ  Fasā'a Maţaru Al-Mundharīna َ027-058 Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa. To, ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana. وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ مَطَرا ً  ۖ  فَسَاءَ مَطَرُ الْمُنذَرِينَ
Quli Al-Ĥamdu Lillahi Wa Salāmun `Alá `Ibādihi Al-Ladhīna Aşţafá  ۗ  'Āālllahu Khayrun 'Ammā Yushrikūna َ027-059 Ka ce: "Godiya ta tabbata ga A1lah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa." Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi? قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ وَسَلاَمٌ عَلَى عِبَادِهِ الَّذِينَ اصْطَفَى  ۗ  آاللَّهُ خَيْرٌ أَمَّا يُشْرِكُونَ
'Amman Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa 'Anzala Lakum Mina As-Samā'i Mā'an Fa'anbatnā Bihi Ĥadā'iqa Dhāta Bahjatin Mā Kāna Lakum 'An Tunbitū Shajarahā  ۗ  'A'ilahun Ma`a Al-Lahi  ۚ  Bal Hum Qawmun Ya`dilūna َ027-060 Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa (Allah da wani). أَمَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَأَنزَلَ لَكُمْ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَأَنْبَتْنَا بِه ِِ حَدَائِقَ ذَاتَ بَهْجَة ٍ مَا كَانَ لَكُمْ أَنْ تُنْبِتُوا شَجَرَهَا  ۗ  أَءِلَه ٌ ٌ مَعَ اللَّهِ  ۚ  بَلْ هُمْ قَوْم ٌ يَعْدِلُونَ
'Amman Ja`ala Al-'Arđa Qarārāan Wa Ja`ala Khilālahā 'Anhārāan Wa Ja`ala Lahā Rawāsiya Wa Ja`ala Bayna Al-Baĥrayni Ĥājizāan  ۗ  'A'ilahun Ma`a Al-Lahi  ۚ  Bal 'Aktharuhum Lā Ya`lamūna َ027-061 Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba. أَمَّنْ جَعَلَ الأَرْضَ قَرَارا ً وَجَعَلَ خِلاَلَهَا أَنْهَارا ً وَجَعَلَ لَهَا رَوَاسِيَ وَجَعَلَ بَيْنَ الْبَحْرَيْنِ حَاجِزاً  ۗ  أَءِلَه ٌ ٌ مَعَ اللَّهِ  ۚ  بَلْ أَكْثَرُهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ
'Amman Yujību Al-Muđţarra 'Idhā Da`āhu Wa Yakshifu As-Sū'a Wa Yaj`alukum Khulafā'a Al-'Arđi  ۗ  'A'ilahun Ma`a Al-Lahi  ۚ  Qalīlāan Mā Tadhakkarūna َ027-062 Kõ wãne ne yake karɓã , kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni. أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضطَرَّ إِذَا دَعَاه ُُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَاءَ الأَرْضِ  ۗ  أَءِلَه ٌ ٌ مَعَ اللَّهِ  ۚ  قَلِيلا ً مَا تَذَكَّرُونَ
'Amman Yahdīkum Fī Žulumāti Al-Barri Wa Al-Baĥri Wa Man Yursilu Ar-Riyāĥa Bushrāan Bayna Yaday Raĥmatihi  ۗ  'A'ilahun Ma`a Al-Lahi  ۚ  Ta`ālá Al-Lahu `Ammā Yushrikūna َ027-063 Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku,kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi. أَمَّنْ يَهْدِيكُمْ فِي ظُلُمَاتِ الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَمَنْ يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرا ً بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ~ِ  ۗ  أَءِلَه ٌ ٌ مَعَ اللَّهِ  ۚ  تَعَالَى اللَّهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ
'Amman Yabda'u Al-Khalqa Thumma Yu`īduhu Wa Man Yarzuqukum Mina As-Samā'i Wa Al-'Arđi  ۗ  'A'ilahun Ma`a Al-Lahi  ۚ  Qul Hātū Burhānakum 'In Kuntum Şādiqīna َ027-064 Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita,kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: "Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya." أَمَّنْ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُه ُُ وَمَنْ يَرْزُقُكُمْ مِنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ  ۗ  أَءِلَه ٌ ٌ مَعَ اللَّهِ  ۚ  قُلْ هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ
Qul Lā Ya`lamu Man As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Al-Ghayba 'Illā Al-Lahu  ۚ  Wa Mā Yash`urūna 'Ayyāna Yub`athūna َ027-065 Ka ce: "Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su." قُلْ لاَ يَعْلَمُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ الْغَيْبَ إِلاَّ اللَّهُ  ۚ  وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
Bal Addāraka `Ilmuhum Al-'Ākhirati  ۚ  Bal HumShakkin Minhā  ۖ  Bal Hum Minhā `Amūna َ027-066 Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne. بَلْ ادَّارَكَ عِلْمُهُمْ فِي الآخِرَةِ  ۚ  بَلْ هُمْ فِي شَكّ ٍ مِنْهَا  ۖ  بَلْ هُمْ مِنْهَا عَمُونَ
Wa Qāla Al-Ladhīna Kafarū 'A'idhā Kunnā Turābāan Wa 'Ābā'uunā 'A'innā Lamukhrajūna َ027-067 Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne?" وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَئِذَا كُنَّا تُرَابا ً وَآبَاؤُنَا أَئِنَّا لَمُخْرَجُونَ
Laqad Wu`idnā Hādhā Naĥnu Wa 'Ābā'uunā Min Qablu 'In Hādhā 'Illā 'Asāţīru Al-'Awwalīna َ027-068 "Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko." لَقَدْ وُعِدْنَا هَذَا نَحْنُ وَآبَاؤُنَا مِنْ قَبْلُ إِنْ هَذَا إِلاَّ أَسَاطِيرُ الأَوَّلِينَ
Qul Sīrū Fī Al-'Arđi Fānžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mujrimīna َ027-069 Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take?" قُلْ سِيرُوا فِي الأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُجْرِمِينَ
Wa Lā Taĥzan `Alayhim Wa Lā Takun Fī Đayqin Mimmā Yamkurūna َ027-070 Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci. وَلاَ تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلاَ تَكُنْ فِي ضَيْق ٍ مِمَّا يَمْكُرُونَ
Wa Yaqūlūna Matá Hādhā Al-Wa`du 'In Kuntum Şādiqīna َ027-071 Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi (zai auku), idan kun kasance mãsu gaskiya?" وَيَقُولُونَ مَتَى هَذَا الْوَعْدُ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ
Qul `Asá 'An Yakūna Radifa Lakum Ba`đu Al-Ladhī Tasta`jilūna َ027-072 Ka ce: "Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta a gare ku." قُلْ عَسَى أَنْ يَكُونَ رَدِفَ لَكُمْ بَعْضُ الَّذِي تَسْتَعْجِلُونَ
Wa 'Inna Rabbaka Ladhū Fađlin `Alá An-Nāsi Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Yashkurūna َ027-073 Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kanmutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa. وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى النَّاسِ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَشْكُرُونَ
Wa 'Inna Rabbaka Laya`lamu Mā Tukinnu Şudūruhum Wa Mā Yu`linūna َ027-074 Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa. وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ
Wa Mā Min Ghā'ibatin As-Samā'i Wa Al-'Arđi 'Illā Fī Kitābin Mubīnin َ027-075 Kuma bãbu wata (mas'ala) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne. وَمَا مِنْ غَائِبَة ٍ فِي السَّمَاءِ وَالأَرْضِ إِلاَّ فِي كِتَاب ٍ مُبِين ٍ
'Inna Hādhā Al-Qur'āna Yaquşşu `Alá Banī 'Isrā'īla 'Akthara Al-Ladhī Hum Fīhi Yakhtalifūna َ027-076 Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki. إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَقُصُّ عَلَى بَنِي إِسْرَائِيلَ أَكْثَرَ الَّذِي هُمْ فِيه ِِ يَخْتَلِفُونَ
Wa 'Innahu Lahudáan Wa Raĥmatun Lilmu'uminīna َ027-077 Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai. وَإِنَّه ُُ لَهُدى ً وَرَحْمَة ٌ لِلْمُؤْمِنِينَ
'Inna Rabbaka Yaqđī Baynahum Biĥukmihi  ۚ  Wa Huwa Al-`Azīzu Al-`Alīmu َ027-078 "Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani." إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُمْ بِحُكْمِه ِِ  ۚ  وَهُوَ الْعَزِيزُ الْعَلِيمُ
Fatawakkal `Alá Al-Lahi  ۖ  'Innaka `Alá Al-Ĥaqqi Al-Mubīni َ027-079 Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya. فَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ  ۖ  إِنَّكَ عَلَى الْحَقِّ الْمُبِينِ
'Innaka Lā Tusmi`u Al-Mawtá Wa Lā Tusmi`u Aş-Şumma Ad-Du`ā'a 'Idhā Wa Llaw Mudbirīna َ027-080 Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya. إِنَّكَ لاَ تُسْمِعُ الْمَوْتَى وَلاَ تُسْمِعُ الصُّمَّ الدُّعَاءَ إِذَا وَلَّوْا مُدْبِرِينَ
Wa Mā 'Anta Bihādī Al-`Umyi `An Đalālatihim  ۖ  'In Tusmi`u 'Illā Man Yu'uminu Bi'āyātinā Fahum Muslimūna َ027-081 Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga Allah). وَمَا أَنْتَ بِهَادِي الْعُمْيِ عَنْ ضَلاَلَتِهِمْ  ۖ  إِنْ تُسْمِعُ إِلاَّ مَنْ يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا فَهُمْ مُسْلِمُونَ
Wa 'Idhā Waqa`a Al-Qawlu `Alayhim 'Akhrajnā Lahum Dābbatan Mina Al-'Arđi Tukallimuhum 'Anna An-Nāsa Kānū Bi'āyātinā Lā Yūqinūna َ027-082 Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni." وَإِذَا وَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِمْ أَخْرَجْنَا لَهُمْ دَابَّة ً مِنَ الأَرْضِ تُكَلِّمُهُمْ أَنَّ النَّاسَ كَانُوا بِآيَاتِنَا لاَ يُوقِنُونَ
Wa Yawma Naĥshuru Min Kulli 'Ummatin Fawjāan Mimman Yukadhdhibu Bi'āyātinā Fahum Yūza`ūna َ027-083 Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. (ga kõra) وَيَوْمَ نَحْشُرُ مِنْ كُلِّ أُمَّة ٍ فَوْجا ً مِمَّنْ يُكَذِّبُ بِآيَاتِنَا فَهُمْ يُوزَعُونَ
Ĥattá 'Idhā Jā'ū Qāla 'Akadhdhabtum Bi'āyātī Wa Lam Tuĥīţū Bihā `Ilmāan 'Ammādhā Kuntum Ta`malūna َ027-084 Har idan sun zo, (Allah) zai ce, "Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa?" حَتَّى إِذَا جَاءُوا قَالَ أَكَذَّبْتُمْ بِآيَاتِي وَلَمْ تُحِيطُوا بِهَا عِلْماً أَمَّاذَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Wa Waqa`a Al-Qawlu `Alayhim Bimā Žalamū Fahum Lā Yanţiqūna َ027-085 Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta cẽwa. وَوَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِمْ بِمَا ظَلَمُوا فَهُمْ لاَ يَنطِقُونَ
'Alam Yaraw 'Annā Ja`alnā Al-Layla Liyaskunū Fīhi Wa An-Nahāra Mubşirāan  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yu'uminūna َ027-086 Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni. أَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا اللَّيْلَ لِيَسْكُنُوا فِيه ِِ وَالنَّهَارَ مُبْصِرا ً  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِقَوْم ٍ يُؤْمِنُونَ
Wa Yawma Yunfakhu Fī Aş-Şūri Fafazi`a Man As-Samāwāti Wa Man Al-'Arđi 'Illā Man Shā'a Al-Lahu  ۚ  Wa Kullun 'Atawhu Dākhirīna َ027-087 Kuma da rãnar da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu. وَيَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَفَزِعَ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَمَنْ فِي الأَرْضِ إِلاَّ مَنْ شَاءَ اللَّهُ  ۚ  وَكُلٌّ أَتَوْهُ دَاخِرِينَ
Wa Tará Al-Jibāla Taĥsabuhā Jāmidatan Wa Hiya Tamurru Marra As-Saĥābi  ۚ  Şun`a Al-Lahi Al-Ladhī 'Atqana Kulla Shay'in  ۚ  'Innahu Khabīrun Bimā Taf`alūna َ027-088 Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa. وَتَرَى الْجِبَالَ تَحْسَبُهَا جَامِدَة ً وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ السَّحَابِ  ۚ  صُنْعَ اللَّهِ الَّذِي أَتْقَنَ كُلَّ شَيْء ٍ  ۚ  إِنَّه ُُ خَبِير ٌ بِمَا تَفْعَلُونَ
Man Jā'a Bil-Ĥasanati Falahu Khayrun Minhā Wa Hum Min Faza`in Yawma'idhin 'Āminūna َ027-089 Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita, a yinin nan, amintattu ne. مَنْ جَاءَ بِالْحَسَنَةِ فَلَه ُُ خَيْر ٌ مِنْهَا وَهُمْ مِنْ فَزَع ٍ يَوْمَئِذ ٍ آمِنُونَ
Wa Man Jā'a Bis-Sayyi'ati Fakubbat Wujūhuhum An-Nāri Hal Tujzawna 'Illā Mā Kuntum Ta`malūna َ027-090 Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa? وَمَنْ جَاءَ بِالسَّيِّئَةِ فَكُبَّتْ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ هَلْ تُجْزَوْنَ إِلاَّ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
'Innamā 'Umirtu 'An 'A`buda Rabba Hadhihi Al-Baldati Al-Ladhī Ĥarramahā Wa Lahu Kullu Shay'in  ۖ  Wa 'Umirtu 'An 'Akūna Mina Al-Muslimīna َ027-091 (Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa." إِنَّمَا أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ رَبَّ هَذِهِ الْبَلْدَةِ الَّذِي حَرَّمَهَا وَلَه ُُ كُلُّ شَيْء ٍ  ۖ  وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُسْلِمِينَ
Wa 'An 'Atluwa Al-Qur'āna  ۖ  Famani Ahtadá Fa'innamā Yahtadī Linafsihi  ۖ  Wa Man Đalla Faqul 'Innamā 'Anā Mina Al-Mundhirīna َ027-092 "Kuma inã karanta Alƙur'ãni." To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: "Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake." وَأَنْ أَتْلُوَ الْقُرْآنَ  ۖ  فَمَنِ اهْتَدَى فَإِنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِه ِِ  ۖ  وَمَنْ ضَلَّ فَقُلْ إِنَّمَا أَنَا مِنَ الْمُنذِرِينَ
Wa Quli Al-Ĥamdu Lillahi Sayurīkum 'Āyātihi Fata`rifūnahā  ۚ  Wa Mā Rabbuka Bighāfilin `Ammā Ta`malūna َ027-093 Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu." Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba. وَقُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ سَيُرِيكُمْ آيَاتِه ِِ فَتَعْرِفُونَهَا  ۚ  وَمَا رَبُّكَ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ
Next Sūrah