26) Sūrat Ash-Shu`arā'

Printed format

26)

Ţā-Sīn-Mīm 026-001 . S̃. M̃. --
Tilka 'Āyātu Al-Kitābi Al-Mubīni 026-002 Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
La`allaka Bākhi`un Nafsaka 'Allā Yakūnū Mu'uminīna 026-003 Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!
'In Nasha' Nunazzil `Alayhim Mina As-Samā'i 'Āyatan Fažallat 'A`nāquhum Lahā Khāđi`īna 026-004 Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
Wa Mā Ya'tīhim Min Dhikrin Mina Ar-Raĥmāni Muĥdathin 'Illā Kānū `Anhu Mu`rīna 026-005 Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
Faqad Kadhdhabū Fasaya'tīhim 'Anbā'u Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn 026-006 To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.
'Awalam Yaraw 'Ilá Al-'Arđi Kam 'Anbatnā Fīhā Min Kulli Zawjin Karīmin 026-007 Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?
'Inna Fī Dhālika La'āyatan  ۖ  Wa Mā Kāna 'Aktharuhum Mu'uminīna 026-008 Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.  ۖ 
Wa 'Inna Rabbaka Lahuwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 026-009 Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
Wa 'Idh Nādá Rabbuka Mūsá 'Ani A'ti Al-Qawma Až-Žālimīna 026-010 Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
Qawma Fir`awna  ۚ  'Alā Yattaqūna 026-011 "Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"  ۚ 
Qāla Rabbi 'Innī 'Akhāfu 'An Yukadhdhibūni 026-012 Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
Wa Yađīqu Şadrī Wa Lā Yanţaliqu Lisānī Fa'arsil 'Ilá Hārūna 026-013 "Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.
Wa Lahum `Alayya Dhanbun Fa'akhāfu 'An Yaqtulūni 026-014 "Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."
Qāla Kallā  ۖ  Fādh/habā Bi'āyātinā  ۖ  'Innā Ma`akum Mustami`ūna 026-015 Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."  ۖ   ۖ 
Fa'tiyā Fir`awna Faqūlā 'Innā Rasūlu Rabbi Al-`Ālamīna 026-016 "Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."
'An 'Arsil Ma`anā Banī 'Isrā'īla 026-017 "Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."
Qāla 'Alam Nurabbika Fīnā Walīdāan Wa Labithta Fīnā Min `Umurika Sinīna 026-018 Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
Wa Fa`alta Fa`lataka Allatī Fa`alta Wa 'Anta Mina Al-Kāfirīna 026-019 "Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"
Qāla Fa`altuhā 'Idhāan Wa 'Anā Mina Ađ-Đāllīn 026-020 Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi."
Fafarartu Minkum Lammā Khiftukum Fawahaba Lī Rabbī Ĥukmāan Wa Ja`alanī Mina Al-Mursalīna 026-021 "Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."
Wa Tilka Ni`matun Tamunnuhā `Alayya 'An `Abbadta Banī 'Isrā'īla 026-022 "Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."
Qāla Fir`awnu Wa Mā Rabbu Al-`Ālamīna 026-023 Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"
Qāla Rabbu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā  ۖ  'In Kuntum Mūqinīna 026-024 Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."  ۖ 
Qāla Liman Ĥawlahu 'Alā Tastami`ūna 026-025 Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?" ~
Qāla Rabbukum Wa Rabbu 'Ābā'ikumu Al-'Awwalīna 026-026 Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
Qāla 'Inna Rasūlakumu Al-Ladhī 'Ursila 'Ilaykum Lamajnūnun 026-027 Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."
Qāla Rabbu Al-Mashriqi Wa Al-Maghribi Wa Mā Baynahumā  ۖ  'In Kuntum Ta`qilūna 026-028 Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."  ۖ 
Qāla La'ini Attakhadhta 'Ilahāan Ghayrī La'aj`alannaka Mina Al-Masjūnīna 026-029 Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."
Qāla 'Awalaw Ji'tuka Bishay'in Mubīnin 026-030 Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"
Qāla Fa'ti Bihi 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna 026-031 Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya." ~
Fa'alqá `Aşāhu Fa'idhā Hiya Thu`bānun Mubīnun 026-032 Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.
Wa Naza`a Yadahu Fa'idhā Hiya Bayđā'u Lilnnāžirīna 026-033 Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
Qāla Lilmala'i Ĥawlahu 'Inna Hādhā Lasāĥirun `Alīmun 026-034 (Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi! ~
Yurīdu 'An Yukhrijakum Min 'Arđikum Bisiĥrihi Famādhā Ta'murūna 026-035 "Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?"
Qālū 'Arjihi Wa 'Akhāhu Wa Ab`ath Al-Madā'ini Ĥāshirīna 026-036 Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne."
Ya'tūka Bikulli Saĥĥārin `Alīmin 026-037 "Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."
Fajumi`a As-Saĥaratu Limīqāti Yawmin Ma`lūmin 026-038 Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.
Wa Qīla Lilnnāsi Hal 'Antum Mujtami`ūna 026-039 Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?
La`allanā Nattabi`u As-Saĥarata 'In Kānū Humu Al-Ghālibīna 026-040 "Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya."
Falammā Jā'a As-Saĥaratu Qālū Lifir`awna 'A'inna Lanā La'ajrāan 'In Kunnā Naĥnu Al-Ghālibīna 026-041 To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?"
Qāla Na`am Wa 'Innakum 'Idhāan Lamina Al-Muqarrabīna 026-042 Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai."
Qāla Lahum Mūsá 'Alqū Mā 'Antum Mulqūna 026-043 Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa."
Fa'alqaw Ĥibālahum Wa `Işīyahum Wa Qālū Bi`izzati Fir`awna 'Innā Lanaĥnu Al-Ghālibūna 026-044 Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya."
Fa'alqá Mūsá `Aşāhu Fa'idhā Hiya Talqafu Mā Ya'fikūna 026-045 Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.
Fa'ulqiya As-Saĥaratu Sājidīna 026-046 Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.
Qālū 'Āmannā Birabbi Al-`Ālamīna 026-047 Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta."
Rabbi Mūsá Wa Hārūna 026-048 "Ubangijin Mũsa da Hãrũna."
Qāla 'Āmantum Lahu Qabla 'An 'Ādhana Lakum  ۖ  'Innahu Lakabīrukumu Al-Ladhī `Allamakumu As-Siĥra Falasawfa Ta`lamūna  ۚ  La'uqaţţi`anna 'Aydiyakum Wa 'Arjulakum Min Khilāfin Wa La'uşallibannakum 'Ajma`īna 026-049 Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa,zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya."  ۖ   ۚ 
Qālū Lā Đayra  ۖ  'Innā 'Ilá Rabbinā Munqalibūna 026-050 Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu."  ۖ 
'Innā Naţma`u 'An Yaghfira Lanā Rabbunā Khaţāyānā 'An Kunnā 'Awwala Al-Mu'uminīna 026-051 "Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni."
Wa 'Awĥaynā 'Ilá Mūsá 'An 'Asri Bi`ibādī 'Innakum Muttaba`ūna 026-052 Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ne.
Fa'arsala Fir`awnu Fī Al-Madā'ini Ĥāshirīna 026-053 Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.
'Inna Hā'uulā' Lashirdhimatun Qalīlūna 026-054 "Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan."
Wa 'Innahum Lanā Laghā'ižūna 026-055 "Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne."
Wa 'Innā Lajamī`un Ĥādhirūna 026-056 "Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne."
Fa'akhrajnāhum Min Jannātin Wa `Uyūnin 026-057 Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.
Wa Kunūzin Wa Maqāmin Karīmin 026-058 Da taskõki da mazauni mai kyau.
Kadhālika Wa 'Awrathnāhā Banī 'Isrā'īla 026-059 Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.
Fa'atba`ūhum Mushriqīna 026-060 Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.
Falammā Tarā'á Al-Jam`āni Qāla 'Aşĥābu Mūsá 'Innā Lamudrakūna 026-061 Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."
Qāla Kallā  ۖ  'Inna Ma`iya Rabbī Sayahdīni 026-062 Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."  ۖ 
Fa'awĥaynā 'Ilá Mūsá 'Ani Ađrib Bi`aşāka Al-Baĥra  ۖ  Fānfalaqa Fakāna Kullu Firqin Kālţţawdi Al-`Ažīmi 026-063 Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.  ۖ 
Wa 'Azlafnā Thamma Al-'Ākharīna 026-064 Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.
Wa 'Anjaynā Mūsá Wa Man Ma`ahu 'Ajma`īna 026-065 Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya. ~
Thumma 'Aghraq Al-'Ākharīna 026-066 Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.
'Inna Fī Dhālika La'āyatan  ۖ  Wa Mā Kāna 'Aktharuhum Mu'uminīna 026-067 Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.  ۖ 
Wa 'Inna Rabbaka Lahuwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 026-068 Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.
Wa Atlu `Alayhim Naba'a 'Ibrāhīma 026-069 Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.
'Idh Qāla Li'abīhi Wa Qawmihi Mā Ta`budūna 026-070 A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"
Qālū Na`budu 'Aşnāmāan Fanažallu Lahā `Ākifīna 026-071 Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."
Qāla Hal Yasma`ūnakum 'Idh Tad`ūna 026-072 Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"
'Aw Yanfa`ūnakum 'Aw Yađurrūna 026-073 "Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"
Qālū Bal Wajadnā 'Ābā'anā Kadhālika Yaf`alūna 026-074 Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."
Qāla 'Afara'aytum Mā Kuntum Ta`budūna 026-075 Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"
'Antum Wa 'Ābā'uukumu Al-'Aqdamūna 026-076 "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"
Fa'innahum `Adūwun Lī 'Illā Rabba Al-`Ālamīna 026-077 "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."
Al-Ladhī Khalaqanī Fahuwa Yahdīni 026-078 "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."
Wa Al-Ladhī Huwa Yuţ`imunī Wa Yasqīni 026-079 "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."
Wa 'Idhā Mariđtu Fahuwa Yashfīni 026-080 "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."
Wa Al-Ladhī Yumītunī Thumma Yuĥyīni 026-081 "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."
Wa Al-Ladhī 'Aţma`u 'An Yaghfira Lī Khī'atī Yawma Ad-Dīni 026-082 "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."
Rabbi Hab Lī Ĥukmāan Wa 'Alĥiqnī Biş-Şāliĥīna 026-083 "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
Wa Aj`al Lī Lisāna Şidqin Al-'Ākhirīna 026-084 "Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya a cikin mutãnen ƙarshe."
Wa Aj`alnī Min Warathati Jannati An-Na`īmi 026-085 "Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."
Wa Aghfir Li'abī 'Innahu Kāna Mina Ađ-Đāllīna 026-086 "Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."
Wa Lā Tukhzinī Yawma Yub`athūna 026-087 "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."
Yawma Lā Yanfa`u Mālun Wa Lā Banūna 026-088 "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."
'Illā Man 'Atá Al-Laha Biqalbin Salīmin 026-089 "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."
Wa 'Uzlifati Al-Jannatu Lilmuttaqīna 026-090 Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.
Wa Burrizati Al-Jaĥīmu Lilghāwīna 026-091 Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.
Wa Qīla Lahum 'Ayna Mā Kuntum Ta`budūna 026-092 Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"
Min Dūni Al-Lahi Hal Yanşurūnakum 'Aw Yantaşirūna 026-093 "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"
Fakubkibū Fīhā Hum Wa Al-Ghāwūna 026-094 Sai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun.
Wa Junūdu 'Iblīsa 'Ajma`ūna 026-095 Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.
Qālū Wa Hum Fīhā Yakhtaşimūna 026-096 Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,
Ta-Allāhi 'In Kunnā Lafī Đalālin Mubīnin 026-097 "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."
'Idh Nusawwīkum Birabbi Al-`Ālamīna 026-098 "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.
Wa Mā 'Ađallanā 'Illā Al-Mujrimūna 026-099 "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."
Famā Lanā Min Shāfi`īna 026-100 "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."
Wa Lā Şadīqin Ĥamīmin 026-101 "Kuma bã mu da abõki, masõyi."
Falaw 'Anna Lanā Karratan Fanakūna Mina Al-Mu'uminīna 026-102 "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"
'Inna Fī Dhālika La'āyatan  ۖ  Wa Mā Kāna 'Aktharuhum Mu'uminīna 026-103 Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.  ۖ 
Wa 'Inna Rabbaka Lahuwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 026-104 Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Kadhdhabat Qawmu Nūĥin Al-Mursalīna 026-105 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.
'Idh Qāla Lahum 'Akhūhum Nūĥun 'Alā Tattaqūna 026-106 A lõkacin da ɗan'uwansu, Nũhu, ya ce musu, "Shin, bã zã ku yi taƙawa ba?"
'Innī Lakum Rasūlun 'Amīnun 026-107 "Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."
Fāttaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni 026-108 "To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Wa Mā 'As'alukum `Alayhi Min 'Ajrin  ۖ  'In 'Ajrī 'Illā `Alá Rabbi Al-`Ālamīna 026-109 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."  ۖ 
Fāttaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni 026-110 "Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Qālū 'Anu'uminu Laka Wa Attaba`aka Al-'Ardhalūna 026-111 Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?"
Qāla Wa Mā `Ilmī Bimā Kānū Ya`malūna 026-112 Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."
'In Ĥisābuhum 'Illā `Alá Rabbī  ۖ  Law Tash`urūna 026-113 "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."  ۖ 
Wa Mā 'Anā Biţāridi Al-Mu'uminīna 026-114 "Ban zama mai kõre mũminai ba."
'In 'Anā 'Illā Nadhīrun Mubīnun 026-115 "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."
Qālū La'in Lam Tantahi Yā Nūĥu Latakūnanna Mina Al-Marjūmīna 026-116 Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"
Qāla Rabbi 'Inna Qawmī Kadhdhabūni 026-117 Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."
Fāftaĥ Baynī Wa Baynahum Fatĥāan Wa Najjinī Wa Man Ma`ī Mina Al-Mu'uminīna 026-118 "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."
Fa'anjaynāhu Wa Man Ma`ahu Fī Al-Fulki Al-Mashĥūni 026-119 Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.
Thumma 'Aghraqnā Ba`du Al-Bāqīna 026-120 Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.
'Inna Fī Dhālika La'āyatan  ۖ  Wa Mā Kāna 'Aktharuhum Mu'uminīna 026-121 Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.  ۖ 
Wa 'Inna Rabbaka Lahuwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 026-122 Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.
Kadhdhabat `Ādun Al-Mursalīna 026-123 Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni.
'Idh Qāla Lahum 'Akhūhum Hūdun 'Alā Tattaqūna 026-124 A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
'Innī Lakum Rasūlun 'Amīnun 026-125 "Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."
Fāttaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni 026-126 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Wa Mā 'As'alukum `Alayhi Min 'Ajrin  ۖ  'In 'Ajrī 'Illā `Alá Rabbi Al-`Ālamīna 026-127 "Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."  ۖ 
'Atabnūna Bikulli Rī`in 'Āyatan Ta`bathūna 026-128 "Shin, kunã yin ginin sitadiyo a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"
Wa Tattakhidhūna Maşāni`a La`allakum Takhludūna 026-129 "Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?"
Wa 'Idhā Baţashtum Baţashtum Jabbārīna 026-130 "Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."
Fāttaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni 026-131 "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Wa Attaqū Al-Ladhī 'Amaddakum Bimā Ta`lamūna 026-132 "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."
'Amaddakum Bi'an`āmin Wa Banīna 026-133 "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."
Wa Jannātin Wa `Uyūnin 026-134 "Da gõnaki da marẽmari."
'Innī 'Akhāfu `Alaykum `Adhāba Yawmin `Ažīmin 026-135 "Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."
Qālū Sawā'un `Alaynā 'Awa`ažta 'Am Lam Takun Mina Al-Wā`ižīna 026-136 Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."
'In Hādhā 'Illā Khuluqu Al-'Awwalīna 026-137 "Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen mutãnen farko."
Wa Mā Naĥnu Bimu`adhdhabīna 026-138 "Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."
Fakadhdhabūhu Fa'ahlaknāhum  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan  ۖ  Wa Mā Kāna 'Aktharuhum Mu'uminīna 026-139 Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ.Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.  ۗ   ۖ 
Wa 'Inna Rabbaka Lahuwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 026-140 Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Kadhdhabat Thamūdu Al-Mursalīna 026-141 Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni.
'Idh Qāla Lahum 'Akhūhum Şāliĥun 'Alā Tattaqūna 026-142 A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?"
'Innī Lakum Rasūlun 'Amīnun 026-143 "Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce."
Fāttaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni 026-144 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.
Wa Mā 'As'alukum `Alayhi Min 'Ajrin  ۖ  'In 'Ajriya 'Illā `Alá Rabbi Al-`Ālamīna 026-145 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu."  ۖ 
'Atutrakūna Fī Mā Hāhunā 'Āminīna 026-146 "Shin, anã barin ku a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?"
Fī Jannātin Wa `Uyūnin 026-147 "A cikin gõnaki da marẽmari."
Wa Zurū`in Wa Nakhlin Ţal`uhā Hađīmun 026-148 "Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi mãsu narkẽwa a ciki?"
Wa Tanĥitūna Mina Al-Jibāli Buyūtāanrihīna 026-149 "Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?"
Fāttaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni 026-150 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Wa Lā Tuţī`ū 'Amra Al-Musrifīna 026-151 "Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata."
Al-Ladhīna Yufsidūna Fī Al-'Arđi Wa Lā Yuşliĥūna 026-152 "Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa."
Qālū 'Innamā 'Anta Mina Al-Musaĥĥarīna 026-153 Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake."
Mā 'Anta 'Illā Basharun Mithlunā Fa'ti Bi'āyatin 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna 026-154 "Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Qāla Hadhihi Nāqatun Lahā Shirbun Wa Lakum Shirbu Yawmin Ma`lūmin 026-155 Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan yini, kuma kunã da shan yini sasanne."
Wa Lā Tamassūhā Bisū'in Faya'khudhakum `Adhābu Yawmin `Ažīmin 026-156 "Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku."
Fa`aqarūhā Fa'aşbaĥū Nādimīna 026-157 Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma.
Fa'akhadhahumu Al-`Adhābu  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan  ۖ  Wa Mā Kāna 'Aktharuhum Mu'uminīna 026-158 Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.  ۗ   ۖ 
Wa 'Inna Rabbaka Lahuwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 026-159 Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai.
Kadhdhabat Qawmu Lūţin Al-Mursalīna 026-160 Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.
'Idh Qāla Lahum 'Akhūhum Lūţun 'Alā Tattaqūna 026-161 A lõkacin da ɗan'uwansu, Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
'Innī Lakum Rasūlun 'Amīnun 026-162 "Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."
Fāttaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni 026-163 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Wa Mā 'As'alukum `Alayhi Min 'Ajrin  ۖ  'In 'Ajriya 'Illā `Alá Rabbi Al-`Ālamīna 026-164 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."  ۖ 
'Ata'tūna Adh-Dhukrāna Mina Al-`Ālamīna 026-165 "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"
Wa Tadharūna Mā Khalaqa Lakum Rabbukum Min 'Azwājikum  ۚ  Bal 'Antum Qawmun `Ādūna 026-166 "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"  ۚ 
Qālū La'in Lam Tantahi Yā Lūţu Latakūnanna Mina Al-Mukhrajīna 026-167 Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."
Qāla 'Innī Li`amalikum Mina Al-Qālīna 026-168 Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."
Rabbi Najjinī Wa 'Ahlī Mimmā Ya`malūna 026-169 "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."
Fanajjaynāhu Wa 'Ahlahu 'Ajma`īna 026-170 Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya. ~
'Illā `Ajūzāan Al-Ghābirīna 026-171 Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.
Thumma Dammarnā Al-'Ākharīna 026-172 Sa'an nan kuma Muka darkãke wasu.
Wa 'Amţarnā `Alayhim Maţarāan  ۖ  Fasā'a Maţaru Al-Mundharīna 026-173 Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.  ۖ 
'Inna Fī Dhālika La'āyatan  ۖ  Wa Mā Kāna 'Aktharuhum Mu'uminīna 026-174 Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.  ۖ 
Wa 'Inna Rabbaka Lahuwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 026-175 Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Kadhdhaba 'Aşĥābu Al-'Aykati Al-Mursalīna 026-176 Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.
'Idh Qāla Lahum Shu`aybun 'Alā Tattaqūna 026-177 A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
'Innī Lakum Rasūlun 'Amīnun 026-178 "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."
Fāttaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni 026-179 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."
Wa Mā 'As'alukum `Alayhi Min 'Ajrin  ۖ  'In 'Ajriya 'Illā `Alá Rabbi Al-`Ālamīna 026-180 "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."  ۖ 
'Awfū Al-Kayla Wa Lā Takūnū Mina Al-Mukhsirīna 026-181 "Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."
Wa Zinū Bil-Qisţāsi Al-Mustaqīmi 026-182 "Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."
Wa Lā Tabkhasū An-Nāsa 'Ashyā'ahum Wa Lā Ta`thaw Fī Al-'Arđi Mufsidīna 026-183 "Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."
Wa Attaqū Al-Ladhī Khalaqakum Wa Al-Jibillata Al-'Awwalīna 026-184 "Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko."
Qālū 'Innamā 'Anta Mina Al-Musaĥĥarīna 026-185 Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne."
Wa Mā 'Anta 'Illā Basharun Mithlunā Wa 'In Nažunnuka Lamina Al-Kādhibīna 026-186 "Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata."
Fa'asqiţ `Alaynā Kisafāan Mina As-Samā'i 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna 026-187 "To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya."
Qāla Rabbī 'A`lamu Bimā Ta`malūna 026-188 Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa."
Fakadhdhabūhu Fa'akhadhahum `Adhābu Yawmi Až-Žullati  ۚ  'Innahu Kāna `Adhāba Yawmin `Ažīmin 026-189 Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.  ۚ 
'Inna Fī Dhālika La'āyatan  ۖ  Wa Mā Kāna 'Aktharuhum Mu'uminīna 026-190 Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.  ۖ 
Wa 'Inna Rabbaka Lahuwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu 026-191 Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Wa 'Innahu Latanzīlu Rabbi Al-`Ālamīna 026-192 Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne.
Nazala Bihi Ar-Rūĥu Al-'Amīnu 026-193 Rũhi amintacce ne ya sauka da shi.
`Alá Qalbika Litakūna Mina Al-Mundhirīna 026-194 A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi.
Bilisānin `Arabīyin Mubīnin 026-195 Da harshe na Larabci mai bayãni.
Wa 'Innahu Lafī Zuburi Al-'Awwalīna 026-196 Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko.
'Awalam Yakun Lahum 'Āyatan 'An Ya`lamahu `Ulamā'u Banī 'Isrā'īla 026-197 Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?
Wa Law Nazzalnāhu `Alá Ba`đi Al-'A`jamīna 026-198 Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,
Faqara'ahu `Alayhim Mā Kānū Bihi Mu'uminīna 026-199 Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba.
Kadhālika Salaknāhu Fī Qulūbi Al-Mujrimīna 026-200 Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.
Lā Yu'uminūna Bihi Ĥattá Yaraw Al-`Adhāba Al-'Alīma 026-201 Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi.
Faya'tiyahum Baghtatan Wa Hum Lā Yash`urūna 026-202 Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba.
Fayaqūlū Hal Naĥnu Munžarūna 026-203 Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?"
'Afabi`adhābinā Yasta`jilūna 026-204 Ashe, to, da azãbarMu suke nẽman gaggãwa?
'Afara'ayta 'In Matta`nāhum Sinīna 026-205 Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,
Thumma Jā'ahum Mā Kānū Yū`adūna 026-206 Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu,
Mā 'Aghná `Anhum Mā Kānū Yumatta`ūna 026-207 Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare su.
Wa Mā 'Ahlaknā Min Qaryatin 'Illā Lahā Mundhirūna 026-208 Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi.
Dhikrá Wa Mā Kunnā Žālimīna 026-209 Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba.
Wa Mā Tanazzalat Bihi Ash-Shayāţīnu 026-210 Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba.
Wa Mā Yanbaghī Lahum Wa Mā Yastaţī`ūna 026-211 Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa.
'Innahum `Ani As-Sam`i Lama`zūlūna 026-212 Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne.
Falā Tad`u Ma`a Al-Lahi 'Ilahāan 'Ākhara Fatakūna Mina Al-Mu`adhdhabīna 026-213 Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba.
Wa 'Andhir `Ashīrataka Al-'Aqrabīna 026-214 Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci.
Wa Akhfiđ Janāĥaka Limani Attaba`aka Mina Al-Mu'uminīna 026-215 Kuma ka sassauta fikãfikanka ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.
Fa'in `Aşawka Faqul 'Innī Barī'un Mimmā Ta`malūna 026-216 Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa."
Wa Tawakkal `Alá Al-`Azīzi Ar-Raĥīmi 026-217 Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Al-Ladhī Yarāka Ĥīna Taqūmu 026-218 Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye.
Wa Taqallubaka Fī As-Sājidīna 026-219 Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada.
'Innahu Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu 026-220 Lalle Shi, Shi ne Mai ji,Masani.
Hal 'Unabbi'ukum `Alá Man Tanazzalu Ash-Shayāţīnu 026-221 Shin, (kunã so) in gaya muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?
Tanazzalu `Alá Kulli 'Affākin 'Athīmin 026-222 Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi.
Yulqūna As-Sam`a Wa 'Aktharuhumdhibūna 026-223 Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne.
Wa Ash-Shu`arā'u Yattabi`uhumu Al-Ghāwūna 026-224 Kuma mawãƙa halakakku ne ke bin su.
'Alam Tará 'Annahum Fī Kulli Wādin Yahīmūna 026-225 Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba?
Wa 'Annahum Yaqūlūna Mā Lā Yaf`alūna 026-226 Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?
'Illā Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Wa Dhakarū Al-Laha Kathīrāan Wa Antaşarū Min Ba`di Mā Žulimū  ۗ  Wa Saya`lamu Al-Ladhīna Žalamū 'Ayya Munqalabin Yanqalibūna 026-227 Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.  ۗ 
Next Sūrah