23) Sūrat Al-Mu'uminūna

Printed format

23)

Qad 'Aflaĥa Al-Mu'uminūna 023-001 Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.
Al-Ladhīna Hum Fī Şalātihim Khāshi`ūna 023-002 Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne.
Wa Al-Ladhīna Hum `Ani Al-Laghwi Mu`rūna 023-003 Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.
Wa Al-Ladhīna Hum Lilzzakāati Fā`ilūna 023-004 Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne.
Wa Al-Ladhīna Hum Lifurūjihim Ĥāfižūna 023-005 Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne.
'Illā `Alá 'Azwājihim 'W Mā Malakat 'Aymānuhum Fa'innahum Ghayru Malūmīna 023-006 Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne.
Famani Abtaghá Warā'a Dhālika Fa'ūlā'ika Humu Al-`Ādūna 023-007 Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi.
Wa Al-Ladhīna Hum Li'mānātihim Wa `Ahdihim Rā`ūna 023-008 Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
Wa Al-Ladhīna Hum `Alá Şalawātihim Yuĥāfižūna 023-009 Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa.
'Ūlā'ika Humu Al-Wārithūna 023-010 Waɗannan, sũ ne magãda.
Al-Ladhīna Yarithūna Al-Firdawsa Hum Fīhā Khālidūna 023-011 Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne.
Wa Laqad Khalaq Al-'Insāna Min Sulālatin Min Ţīnin 023-012 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka.
Thumma Ja`alnāhu Nuţfatan Fī Qarārin Makīnin 023-013 Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.
Thumma Khalaq An-Nuţfata `Alaqatan Fakhalaq Al-`Alaqata Muđghatan Fakhalaq Al-Muđghata `Ižāmāan Fakasawnā Al-`Ižāma Laĥmāan Thumma 'Ansha'nāhu Khalqāan 'Ākhara  ۚ  Fatabāraka Al-Lahu 'Aĥsanu Al-Khāliqīna 023-014 Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa.  ۚ 
Thumma 'Innakum Ba`da Dhālika Lamayyitūna 023-015 Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.
Thumma 'Innakum Yawma Al-Qiyāmati Tub`athūna 023-016 Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar ¡iyãma, za a iãyar da ku,
Wa Laqad Khalaqnā Fawqakum Sab`a Ţarā'iqa Wa Mā Kunnā `Ani Al-Khalqi Ghāfilīna 023-017 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba.
Wa 'Anzalnā Mina As-Samā'i Mā'an Biqadarin Fa'askannāhu Fī Al-'Arđi  ۖ  Wa 'Innā `Alá Dhahābin Bihi Laqādirūna 023-018 Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne.  ۖ 
Fa'ansha'nā Lakum Bihi Jannātin Min Nakhīlin Wa 'A`nābin Lakum Fīhā Fawākihu Kathīratun Wa Minhā Ta'kulūna 023-019 Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci.
Wa Shajaratan Takhruju Min Ţūri Saynā'a Tanbutu Bid-Duhni Wa Şibghin Lil'ākilīna 023-020 Da wata itãciya, tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ.
Wa 'Inna Lakum Al-'An`āmi La`ibratan  ۖ  Nusqīkum Mimmā Fī Buţūnihā Wa Lakum Fīhā Manāfi`u Kathīratun Wa Minhā Ta'kulūna 023-021 Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ  ۖ 
Wa `Alayhā Wa `Alá Al-Fulki Tuĥmalūna 023-022 Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku.
Wa Laqad 'Arsalnā Nūĥāan 'Ilá Qawmihi Faqāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu  ۖ  'Afalā Tattaqūna 023-023 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba?" ~  ۖ 
Faqāla Al-Mala'u Al-Ladhīna Kafarū Min Qawmihi Mā Hādhā 'Illā Basharun Mithlukum Yurīdu 'An Yatafađđala `Alaykum Wa Law Shā'a Al-Lahu La'anzala Malā'ikatan Mā Sami`nā Bihadhā Fī 'Ābā'inā Al-'Awwalīna 023-024 Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme)ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko."
'In Huwa 'Illā Rajulun Bihi Jinnatun Fatarabbaşū Bihi Ĥattá Ĥīnin 023-025 "Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci."
Qāla Rabbi Anşurnī Bimā Kadhdhabūni 023-026 Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimakeni sabõda sun ƙaryatani."
Fa'awĥaynā 'Ilayhi 'Ani Aşna`i Al-Fulka Bi'a`yuninā Wa Waĥyinā Fa'idhā Jā'a 'Amrunā Wa Fāra At-Tannūru  ۙ  Fāsluk Fīhā Min Kullin Zawjayni Athnayni Wa 'Ahlaka 'Illā Man Sabaqa `Alayhi Al-Qawlu Minhum  ۖ  Wa Lā Tukhāţibnī Fī Al-Ladhīna Žalamū  ۖ  'Innahum Mughraqūna 023-027 Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne.  ۙ   ۖ   ۖ 
Fa'idhā Astawayta 'Anta Wa Man Ma`aka `Alá Al-Fulki Faquli Al-Ĥamdu Lillahi Al-Ladhī Najjānā Mina Al-Qawmi Až-Žālimīna 023-028 "Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai."
Wa Qul Rabbi 'Anzilnī Munzalāan Mubārakāan Wa 'Anta Khayru Al-Munzilīna 023-029 "Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'"
'Inna Fī Dhālika La'āyātin Wa 'In Kunnā Lamubtalīna 023-030 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu jarrabãwa.
Thumma 'Ansha'nā Min Ba`dihim Qarnāan 'Ākharīna 023-031 Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu.
Fa'arsalnā Fīhim Rasūlāan Minhum 'Ani A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu  ۖ  'Afalā Tattaqūna 023-032 Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba?" ~  ۖ 
Wa Qāla Al-Mala'u Min Qawmihi Al-Ladhīna Kafarū Wa Kadhdhabū Biliqā'i Al-'Ākhirati Wa 'Atrafnāhum Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Mā Hādhā 'Illā Basharun Mithlukum Ya'kulu Mimmā Ta'kulūna Minhu Wa Yashrabu Mimmā Tashrabūna 023-033 Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã."
Wa La'in 'Aţa`tum Basharāan Mithlakum 'Innakum 'Idhāan Lakhāsirūna 023-034 "Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne."
'Aya`idukum 'Annakum 'Idhā Mittum Wa Kuntum Turābāan Wa `Ižāmāan 'Annakum Mukhrajūna 023-035 "Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?"
Hayhāta Hayhāta Limā Tū`adūna 023-036 "Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi."
'In Hiya 'Illā Ĥayātunā Ad-Dunyā Namūtu Wa Naĥyā Wa Mā Naĥnu Bimabthīna 023-037 "Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
'In Huwa 'Illā Rajulun Aftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan Wa Mā Naĥnu Lahu Bimu'uminīna 023-038 "Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba."
Qāla Rabbi Anşurnī Bimā Kadhdhabūni 023-039 Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni."
Qāla `Ammā Qalīlin Layuşbiĥunna Nādimīna 023-040 Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma."
Fa'akhadhat/humu Aş-Şayĥatu Bil-Ĥaqqi Faja`alnāhum Ghuthā'an  ۚ  Fabu`dāan Lilqawmi Až-Žālimīna 023-041 Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai!  ۚ 
Thumma 'Ansha'nā Min Ba`dihim Qurūnāan 'Ākharīna 023-042 Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu.
Mā Tasbiqu Min 'Ummatin 'Ajalahā Wa Mā Yasta'khirūna 023-043 Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
Thumma 'Arsalnā Rusulanā Tatrā  ۖ  Kulla Mā Jā'a 'Ummatan Rasūluhā Kadhdhabūhu  ۚ  Fa'atba`nā Ba`đahum Ba`đāan Wa Ja`alnāhum 'Aĥādītha  ۚ  Fabu`dāan Liqawmin Lā Yu'uminūna 023-044 Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni!  ۖ   ۚ   ۚ 
Thumma 'Arsalnā Mūsá Wa 'Akhāhu Hārūna Bi'āyātinā Wa Sulţānin Mubīnin 023-045 Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli bayyananne.
'Ilá Fir`awna Wa Mala'ihi Fāstakbarū Wa Kānū Qawmāan `Ālīna 023-046 Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya.
Faqālū 'Anu'uminu Libasharayni Mithlinā Wa Qawmuhumā Lanā `Ābidūna 023-047 Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne."
Fakadhdhabūhumā Fakānū Mina Al-Muhlakīna 023-048 Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku.
Wa Laqad 'Ātaynā Mūsá Al-Kitāba La`allahum Yahtadūna 023-049 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu zã su shiryu.
Wa Ja`alnā Abna Maryama Wa 'Ummahu 'Āyatan Wa 'Āwaynāhumā 'Ilá Rabwatin Dhāti Qarārin Wa Ma`īnin 023-050 Kuma Mun sanya an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.
Yā 'Ayyuhā Ar-Rusulu Kulū Mina Aţ-Ţayyibāti Wa A`malū Şāliĥāan  ۖ  'Innī Bimā Ta`malūna `Alīmun 023-051 Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.  ۖ 
Wa 'Inna Hadhihi 'Ummatukum 'Ummatan Wāĥidatan Wa 'Anā Rabbukum Fa Attaqūni 023-052 Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa. ~
Fataqaţţa`ū 'Amrahum Baynahum Zuburāan  ۖ  Kullu Ĥizbin Bimā Ladayhim Farūna 023-053 Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.  ۖ 
FadharhumGhamratihim Ĥattá Ĥīnin 023-054 To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci.
'Ayaĥsabūna 'Annamā Numidduhum Bihi Min Mālin Wa Banīna 023-055 Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya,
Nusāri`u Lahum Al-Khayrāti  ۚ  Bal Lā Yash`urūna 023-056 Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri?  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Hum Min Khashyati Rabbihim Mushfiqūna 023-057 Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu,
Wa Al-Ladhīna Hum Bi'āyāti Rabbihim Yu'uminūna 023-058 Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni,
Wa Al-Ladhīna Hum Birabbihim Lā Yushrikūna 023-059 Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki,
Wa Al-Ladhīna Yu'utūna Mā 'Ātaw Wa Qulūbuhum Wa Jilatun 'Annahum 'Ilá Rabbihim Rāji`ūna 023-060 Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu,
'Ūlā'ika Yusāri`ūna Fī Al-Khayrāti Wa Hum Lahā Sābiqūna 023-061 Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri).
Wa Lā Nukallifu Nafsāan 'Illā Wus`ahā  ۖ  Wa Ladaynā Kitābun Yanţiqu Bil-Ĥaqqi  ۚ  Wa Hum Lā Yužlamūn 023-062 Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su.  ۖ   ۚ 
Bal QulūbuhumGhamratin Min Hādhā Wa Lahum 'A`mālun Min Dūni Dhālika Hum Lahā `Āmilūna 023-063 Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su,mãsu aikatãwa ne.
Ĥattá 'Idhā 'Akhadhnā Mutrafīhim Bil-`Adhābi 'Idhā Hum Yaj'arūna 023-064 Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa.
Lā Taj'arū Al-Yawma  ۖ  'Innakum Minnā Lā Tunşarūna 023-065 Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku.  ۖ 
Qad Kānat 'Āyātī Tutlá `Alaykum Fakuntum `Alá 'A`qābikum Tankişūna 023-066 Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya.
Mustakbirīna Bihi Sāmirāan Tahjurūna 023-067 Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha.
'Afalam Yaddabbarū Al-Qawla 'Am Jā'ahum Mā Lam Ya'ti 'Ābā'ahumu Al-'Awwalīna 023-068 Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu?
'Am Lam Ya`rifū Rasūlahum Fahum Lahu Munkirūna 023-069 Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi?
'Am Yaqūlūna Bihi Jinnatun  ۚ  Bal Jā'ahum Bil-Ĥaqqi Wa 'Aktharuhum Lilĥaqqi Kārihūna 023-070 Kõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne.  ۚ 
Wa Lawi Attaba`a Al-Ĥaqqu 'Ahwā'ahum Lafasadati As-Samāwātu Wa Al-'Arđu Wa Man Fīhinna  ۚ  Bal 'Ataynāhum Bidhikrihim Fahum `An Dhikrihim Mu`rūna 023-071 Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa.  ۚ 
'Am Tas'aluhum Kharjāan Fakharāju Rabbika Khayrun  ۖ  Wa Huwa Khayru Ar-Rāziqīna 023-072 Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa.  ۖ 
Wa 'Innaka Latad`ūhum 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin 023-073 Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya.
Wa 'Inna Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati `Ani Aş-Şirāţi Lanākibūna 023-074 Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne.
Wa Law Raĥimnāhum Wa Kashafnā Mā Bihim Min Đurrin Lalajjū Fī Ţughyānihim Ya`mahūna 023-075 Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa.
Wa Laqad 'Akhadhnāhum Bil-`Adhābi Famā Astakānū Lirabbihim Wa Mā Yatađarra`ūna 023-076 Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u.
Ĥattá 'Idhā Fataĥnā `Alayhim Bābāan Dhā `Adhābin Shadīdin 'Idhā Hum Fīhi Mublisūna 023-077 Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi.
Wa Huwa Al-Ladhī 'Ansha'a Lakumu As-Sam`a Wa Al-'Abşāra Wa Al-'Af'idata  ۚ  Qalīlāan Mā Tashkurūna 023-078 Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.  ۚ 
Wa Huwa Al-Ladhī Dhara'akum Al-'Arđi Wa 'Ilayhi Tuĥsharūna 023-079 Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku.
Wa Huwa Al-Ladhī Yuĥyī Wa Yumītu Wa Lahu Akhtilāfu Al-Layli Wa An-Nahāri  ۚ  'Afalā Ta`qilūna 023-080 Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba?  ۚ 
Bal Qālū Mithla Mā Qāla Al-'Awwalūna 023-081 Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa.
Qālū 'A'idhā Mitnā Wa Kunnā Turābāan Wa `Ižāmāan 'A'innā Lamabthūna 023-082 Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lal1e ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne?
Laqad Wu`idnā Naĥnu Wa 'Ābā'uunā Hādhā Min Qablu 'In Hādhā 'Illā 'Asāţīru Al-'Awwalīna 023-083 "Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko."
Qul Limani Al-'Arđu Wa Man Fīhā 'In Kuntum Ta`lamūna 023-084 Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani?"
Sayaqūlūna Lillahi  ۚ  Qul 'Afalā Tadhakkarūna 023-085 Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?"  ۚ 
Qul Man Rabbu As-Samāwāti As-Sab`i Wa Rabbu Al-`Arshi Al-`Ažīmi 023-086 Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?"
Sayaqūlūna Lillahi  ۚ  Qul 'Afalā Tattaqūna 023-087 Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?"  ۚ 
Qul Man Biyadihi Malakūtu Kulli Shay'in Wa Huwa Yujīru Wa Lā Yujāru `Alayhi 'In Kuntum Ta`lamūn 023-088 Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?"
Sayaqūlūna Lillahi  ۚ  Qul Fa'annā Tusĥarūna 023-089 Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku?"  ۚ 
Bal 'Ataynāhum Bil-Ĥaqqi Wa 'Innahum Lakādhibūna 023-090 Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
Attakhadha Al-Lahu Min Waladin Wa Mā Kāna Ma`ahu Min 'Ilahin  ۚ  'Idhāan Ladhahaba Kullu 'Ilahin Bimā Khalaqa Wa La`alā Ba`đuhum `Alá Ba`đin  ۚ  Subĥāna Al-Lahi `Ammā Yaşifūna 023-091 Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa. ~  ۚ   ۚ 
`Ālimi Al-Ghaybi Wa Ash-Shahādati Fata`ālá `Ammā Yushrikūna 023-092 Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
Qul Rabbi 'Immā Turiyannī Mā Yū`adūna 023-093 Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi."
Rabbi Falā Taj`alnī Fī Al-Qawmi Až-Žālimīna 023-094 "Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai."
Wa 'Innā `Alá 'An Nuriyaka Mā Na`iduhum Laqādirūna 023-095 Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi.
Adfa` Bi-Atī Hiya 'Aĥsanu As-Sayyi'ata  ۚ  Naĥnu 'A`lamu Bimā Yaşifūna 023-096 Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ neMafi sani game da abin da suke siffantãwa.  ۚ 
Wa Qul Rabbi 'A`ūdhu Bika Min Hamazāti Ash-Shayāţīni 023-097 Ka ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu."
Wa 'A`ūdhu Bika Rabbi 'An Yaĥđurūni 023-098 "Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni, "
Ĥattá 'Idhā Jā'a 'Aĥadahumu Al-Mawtu Qāla Rabbi Arji`ūni 023-099 Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya)."
La`allī 'A`malu Şāliĥāan Fīmā Taraktu  ۚ  Kallā  ۚ  'Innahā Kalimatun Huwa Qā'iluhā  ۖ  Wa Min Warā'ihim Barzakhun 'Ilá Yawmi Yub`athūna 023-100 "Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su.  ۚ   ۚ   ۖ 
Fa'idhā Nufikha Fī Aş-Şūri Falā 'Ansāba Baynahum Yawma'idhin Wa Lā Yatasā'alūna 023-101 Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba.
Faman Thaqulat Mawāzīnuhu Fa'ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna 023-102 To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
Wa Man Khaffat Mawāzīnuhu Fa'ūlā'ika Al-Ladhīna Khasirū 'Anfusahum Fī Jahannama Khālidūna 023-103 Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama.
Talfaĥu Wujūhahumu An-Nāru Wa Hum Fīhā Kāliĥūna 023-104 Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne.
'Alam Takun 'Āyātī Tutlá `Alaykum Fakuntum Bihā Tukadhdhibūna 023-105 "Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa?"
Qālū Rabbanā Ghalabat `Alaynā Shiqwatunā Wa Kunnā Qawmāan Đāllīna 023-106 Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu."
Rabbanā 'Akhrijnā Minhā Fa'in `Udnā Fa'innā Žālimūna 023-107 "Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci."
Qāla Akhsa'ū Fīhā Wa Lā Tukallimūni 023-108 Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana."
'Innahu Kāna Farīqun Min `Ibādī Yaqūlūna Rabbanā 'Āmannā Fāghfir Lanā Wa Arĥamnā Wa 'Anta Khayru Ar-Rāĥimīna 023-109 Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi."
Fāttakhadhtumūhum Sikhrīyāan Ĥattá 'Ansawkum Dhikrī Wa Kuntum Minhum Tađĥakūna 023-110 Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya.
'Innī Jazaytuhumu Al-Yawma Bimā Şabarū 'Annahum Humu Al-Fā'izūna 023-111 Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
Qāla Kam Labithtum Al-'Arđi `Adada Sinīna 023-112 Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru?"
Qālū Labithnā Yawmāan 'Aw Ba`đa Yawmin Fās'ali Al-`Āddīna 023-113 Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa."
Qāla 'In Labithtum 'Illā Qalīlāan  ۖ  Law 'Annakum Kuntum Ta`lamūna 023-114 Ya ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani."  ۖ 
'Afaĥasibtum 'Annamā Khalaqnākum `Abathāan Wa 'Annakum 'Ilaynā Lā Turja`ūna 023-115 "Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba?"
Fata`ālá Al-Lahu Al-Maliku Al-Ĥaqqu  ۖ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Rabbu Al-`Arshi Al-Karīmi 023-116 Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja.  ۖ  ~
Wa Man Yad`u Ma`a Al-Lahi 'Ilahāan 'Ākhara Lā Burhāna Lahu Bihi Fa'innamā Ĥisābuhu `Inda Rabbihi  ۚ  'Innahu Lā Yufliĥu Al-Kāfirūna 023-117 Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara. ~  ۚ 
Wa Qul Rabbi Aghfir Wa Arĥam Wa 'Anta Khayru Ar-Rāĥimīna 023-118 Kuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama."
Next Sūrah