24) Sūrat An-Nūr

Printed format

24)

Sūratun 'Anzalnāhā Wa Farađnāhā Wa 'Anzalnā Fīhā 'Āyātin Bayyinātin La`allakum Tadhakkarūna 024-001 (Wannan) sũra ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da ãyõyi bayyanannu a cikinta, dõmin ku riƙa tunãwa.
Az-Zāniyatu Wa Az-Zānī Fājlidū Kulla Wāĥidin Minhumā Miā'ata Jaldatin  ۖ  Wa Lā Ta'khudhkum Bihimā Ra'fatun Fī Dīni Al-Lahi 'In Kuntum Tu'uminūna Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri  ۖ  Wa Līash/had `Adhābahumā Ţā'ifatun Mina Al-Mu'uminīna 024-002 Mazinãciya da mazinãci, to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu.  ۖ   ۖ 
Az-Zānī Lā Yankiĥu 'Illā Zāniyatan 'Aw Mushrikatan Wa Az-Zāniyatu Lā Yankiĥuhā 'Illā Zānin 'Aw Mushrikun  ۚ  Wa Ĥurrima Dhālika `Alá Al-Mu'uminīna 024-003 Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna Yarmūna Al-Muĥşanāti Thumma Lam Ya'tū Bi'arba`ati Shuhadā'a Fājlidūhum Thamānīna Jaldatan Wa Lā Taqbalū Lahum Shahādatan  ۚ  'Abadāan Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Fāsiqūna 024-004 Kuma waɗanda ke jĩfar mãtã masu kãmun kai, sa'an nan kuma ba su jẽ da shaidu huɗu ba to, ku yi musu bũlãla, bũlãla tamãnin, kuma kada ku karɓi wata shaida tãsu, har abada. Waɗancan su ne fãsiƙai.  ۚ 
'Illā Al-Ladhīna Tābū Min Ba`di Dhālika Wa 'Aşlaĥū Fa'inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 024-005 Fãce waɗanda suka tũbadaga bãyan wannan, kuma suka gyãru, to lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Wa Al-Ladhīna Yarmūna 'Azwājahum Wa Lam Yakun Lahum Shuhadā'u 'Illā 'Anfusuhum Fashahādatu 'Aĥadihim 'Arba`u Shahādātin  ۙ  Bil-Lahi 'Innahu Lamina Aş-Şādiqīna 024-006 Kuma waɗanda ke jĩfar mãtan aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su ba, fãce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga magasganta.'  ۙ 
Wa Al-Khāmisatu 'Anna La`nata Al-Lahi `Alayhi 'In Kāna Mina Al-Kādhibīna 024-007 Kuma ta biyar cẽwa 'La'anar Allah ta tabbata a kansa, idan ya kasance daga maƙaryata.'
Wa Yadra'u `Anhā Al-`Adhāba 'An Tash/hada 'Arba`a Shahādātin Bil-Lahi  ۙ  'Innahu Lamina Al-Kādhibīna 024-008 Kuma yanã tunkuɗe mata azãba ta yi shaida, shaida huɗu da Allah, 'Lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga maƙaryata.'  ۙ 
Wa Al-Khāmisata 'Anna Ghađaba Al-Lahi `Alayhā 'In Kāna Mina Aş-Şādiqīna 024-009 Kuma tã biyar cẽwa 'Hushin Allah ya tabbata a kanta idan ya kasance daga magasganta.'
Wa Lawlā Fađlu Al-Lahi `Alaykum Wa Raĥmatuhu Wa 'Anna Al-Laha Tawwābun Ĥakīmun 024-010 Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku, da rahamarSa, kuma cẽwa Allah Mai karɓar tũba ne, Mai hikima!
'Inna Al-Ladhīna Jā'ū Bil-'Ifki `Uşbatun Minkum  ۚ  Lā Taĥsabūhu Sharrāan Lakum  ۖ  Bal Huwa Khayrun Lakum  ۚ  Likulli Amri'in MinhumAktasaba Mina Al-'Ithmi Wa  ۚ  Al-Ladhī Tawallá Kibrahu Minhum Lahu `Adhābun `Ažīmun 024-011 Lalle ne waɗanda suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma.  ۚ   ۖ   ۚ   ۚ 
Lawlā 'Idh Sami`tumūhu Žanna Al-Mu'uminūna Wa Al-Mu'uminātu Bi'anfusihim Khayrāan Wa Qālū Hādhā 'Ifkun Mubīnun 024-012 Don me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce: "Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?"
Lawlā Jā'ū `Alayhi Bi'arba`ati Shuhadā'a  ۚ  Fa'idh Lam Ya'tū Bish-Shuhadā'i Fa'ūlā'ika `Inda Al-Lahi Humu Al-Kādhibūna 024-013 Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata.  ۚ 
Wa Lawlā Fađlu Al-Lahi `Alaykum Wa Raĥmatuhu Fī Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati Lamassakum Fī Mā 'Afađtum Fīhi `Adhābun `Ažīmun 024-014 Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne,dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa.
'Idh Talaqqawnahu Bi'alsinatikum Wa Taqūlūna Bi'afwāhikum Mā Laysa Lakum Bihi `Ilmun Wa Taĥsabūnahu Hayyināan Wa Huwa `Inda Al-Lahi `Ažīmun 024-015 A lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a wurin Allah, babba ne.
Wa Lawlā 'Idh Sami`tumūhu Qultum Mā Yakūnu Lanā 'An Natakallama Bihadhā Subĥānaka Hādhā Buhtānun `Ažīmun 024-016 Kuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, "Bã ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma"?
Ya`ižukumu Al-Lahu 'An Ta`ūdū Limithlihi 'Abadāan 'In Kuntum Mu'uminīna 024-017 Allah Yanã yi muku wa'azi, kada ku kõma ga irinsa, har abada, idan kun kasance mũminai. ~
Wa Yubayyinu Al-Lahu Lakumu Al-'Āyāti Wa  ۚ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 024-018 Kuma Allah Yanã bayyana muku ãyõyinSa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Yuĥibbūna 'An Tashī`a Al-Fāĥishatu Fī Al-Ladhīna 'Āmanū Lahum `Adhābun 'Alīmun Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati Wa  ۚ  Allāhu Ya`lamu Wa 'Antum Lā Ta`lamūna 024-019 Lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ ba ku sani ba.  ۚ 
Wa Lawlā Fađlu Al-Lahi `Alaykum Wa Raĥmatuhu Wa 'Anna Al-Laha Ra'ūfun Raĥīm 024-020 Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa. Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai!
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tattabi`ū Khuţuwāti Ash-Shayţāni  ۚ  Wa Man Yattabi` Khuţuwāti Ash-Shayţāni Fa'innahu Ya'muru Bil-Faĥshā'i Wa Al-Munkari  ۚ  Wa Lawlā Fađlu Al-Lahi `Alaykum Wa Raĥmatuhu Mā Zakā Minkum Min 'Aĥadin 'Abadāan Wa Lakinna Al-Laha Yuzakkī Man Yashā'u Wa  ۗ  Allāhu Samī`un `Alīmun 024-021 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni, kada ku bi hanyõyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin hanyõyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yanã umurni da yin alfãsha da abin da ba a sani ba, kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, bãbu wani mutum daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yanã tsarkake wanda Yake so kuma Allah Mai ji ne, Masani.  ۚ   ۚ   ۗ 
Wa Lā Ya'tali 'Ū Al-Fađli Minkum Wa As-Sa`ati 'An Yu'utū 'Ū Al-Qurbá Wa Al-Masākīna Wa Al-Muhājirīna Fī Sabīli Al-Lahi  ۖ  Wa Līa`fū Wa Līaşfaĥū  ۗ  'Alā Tuĥibbūna 'An Yaghfira Al-Lahu Lakum Wa  ۗ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 024-022 Kuma kada ma'abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?  ۖ   ۗ   ۗ 
'Inna Al-Ladhīna Yarmūna Al-Muĥşanāti Al-Ghāfilāti Al-Mu'umināti Lu`inū Fī Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati Wa Lahum `Adhābun `Ažīmun 024-023 Lalle ne waɗannan da suke jĩfar mãtã mãsu kãmun kai gãfilai mũminai, an la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma sunãda azãba mai girma.
Yawma Tash/hadu `Alayhim 'Alsinatuhum Wa 'Aydīhim Wa 'Arjuluhum Bimā Kānū Ya`malūna 024-024 A rãnar da harsunansu da hannãyensu, da ƙafãfunsu suke bãyar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Yawma'idhin Yuwaffīhimu Al-Lahu Dīnahumu Al-Ĥaqqa Wa Ya`lamūna 'Anna Al-Laha Huwa Al-Ĥaqqu Al-Mubīnu 024-025 a rãnar dl Allah Yake cika musu sakamakonsu tabbatacce kuma sunã sanin (cẽwa) lalle Allah, Shi ne Gaskiya bayyananna.
Al-Khabīthātu Lilkhabīthīna Wa Al-Khabīthūna Lilkhabīthāti Wa  ۖ  Aţ-Ţayyibātu Lilţţayyibīna Wa Aţ-Ţayyibūna Lilţţayyibāti  ۚ  'Ūlā'ika Mubarra'ūna Mimmā Yaqūlūna  ۖ  Lahum Maghfiratun Wa Rizqun Karīmun 024-026 Miyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantãwa daga abin da (mãsu ƙazafi) suke faɗa kuma sunã da gãfara da arziki na karimci.  ۖ   ۚ   ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tadkhulū Buyūtāan Ghayra Buyūtikum Ĥattá Tasta'nisū Wa Tusallimū `Alá 'Ahlihā  ۚ  Dhālikum Khayrun Lakum La`allakum Tadhakkarūna 024-027 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna.  ۚ 
Fa'in Lam Tajidū Fīhā 'Aĥadāan Falā Tadkhulūhā Ĥattá Yu'udhana Lakum  ۖ  Wa 'In Qīla Lakum Arji`ū Fārji`ū  ۖ  Huwa 'Azká Lakum Wa  ۚ  Allāhu Bimā Ta`malūna `Alīmun 024-028 To, idan ba ku sãmi kõwa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku izni. Kuma idan an ce muku, "Ku kõma." Sai ku kõma, shi ne mafi tsarkaka a gare ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatãwa, Masani ne.  ۖ   ۖ   ۚ 
Laysa `Alaykum Junāĥun 'An Tadkhulū Buyūtāan Ghayra Maskūnatin Fīhā Matā`un Lakum Wa  ۚ  Allāhu Ya`lamu Mā Tubdūna Wa Mā Taktumūna 024-029 Bãbu laifi a kanku, ga ku shiga gidãje waɗanda bã zaunannu ba, a cikinsu akwai waɗansu kãya nãku. Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke nũnãwa, da abin dakuke ɓãyẽwa.  ۚ 
Qul Lilmu'uminīna Yaghuđđū Min 'Abşārihim Wa Yaĥfažū Furūjahum  ۚ  Dhālika 'Azká Lahum  ۗ  'Inna Al-Laha Khabīrun Bimā Yaşna`ūna 024-030 Ka ce wa mũminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjõjinsu. wannan shĩ ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã'antãwa.  ۚ   ۗ 
Wa Qul Lilmu'umināti Yaghđuđna Min 'Abşārihinna Wa Yaĥfažna Furūjahunna Wa Lā Yubdīna Zīnatahunna 'Illā Mā Žahara Minhā  ۖ  Wa Līađribna Bikhumurihinna `Alá Juyūbihinna  ۖ  Wa Lā Yubdīna Zīnatahunna 'Illā Libu`ūlatihinna 'Aw 'Ābā'ihinna 'Aw 'Ābā'i Bu`ūlatihinna 'Aw 'Abnā'ihinna 'Aw 'Abnā'i Bu`ūlatihinna 'Aw 'Ikhwānihinna 'Aw Banī 'Ikhwānihinna 'Aw Banī 'Akhawātihinna 'Aw Nisā'ihinna 'Aw Mā Malakat 'Aymānuhunna 'Awi At-Tābi`īna Ghayri 'Ū Al-'Irbati Mina Ar-Rijāli 'Awi Aţ-Ţifli Al-Ladhīna Lam Yažharū `Alá `Awrāti An-Nisā'  ۖ  Wa Lā Yađribna Bi'arjulihinna Liyu`lama Mā Yukhfīna Min Zīnatihinna  ۚ  Wa Tūbū 'Ilá Al-Lahi Jamī`āan 'Ayyuhā Al-Mu'uminūna La`allakum Tufliĥūna 024-031 Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu.Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo.  ۖ   ۖ   ۖ   ۚ 
Wa 'Ankiĥū Al-'Ayāmá Minkum Wa Aş-Şāliĥīna Min `Ibādikum Wa 'Imā'ikum  ۚ  'In Yakūnū Fuqarā'a Yughnihimu Al-Lahu Min Fađlihi Wa  ۗ  Allāhu Wāsi`un `Alīmun 024-032 Kuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku, da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani.  ۚ   ۗ 
Wa Līasta`fifi Al-Ladhīna Lā Yajidūna Nikāĥāan Ĥattá Yughniyahumu Al-Lahu Min Fađlihi Wa  ۗ  Al-Ladhīna Yabtaghūna Al-Kitāba Mimmā Malakat 'Aymānukum Fakātibūhum 'In `Alimtum Fīhim Khayrāan  ۖ  Wa 'Ātūhum Min Māli Al-Lahi Al-Ladhī 'Ātākum  ۚ  Wa Lā Tukrihū Fatayātikum `Alá Al-Bighā'i 'In 'Aradna Taĥaşşunāan Litabtaghū `Arađa Al-Ĥayāati Ad-Dunyā  ۚ  Wa Man Yukrihhunna Fa'inna Al-Laha Min Ba`di 'Ikrāhihinna Ghafūrun Raĥīmun 024-033 Kuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu, dõmin ku nẽmi rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۗ   ۖ   ۚ   ۚ 
Wa Laqad 'Anzalnā 'Ilaykum 'Āyātin Mubayyinātin Wa Mathalāan Mina Al-Ladhīna Khalaw Min Qablikum Wa Maw`ižatan Lilmuttaqīna 024-034 Kuma lalle ne Mun saukar zuwa gare ku, ãyõyi mãsu bayyanãwa, da misãli daga waɗanda suka shige daga gabãninku, da wa'azi ga mãsu taƙawa.
Al-Lahu Nūru As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Mathalu Nūrihi Kamishkāatin Fīhā Mişbāĥun  ۖ  Al-Mişbāĥu Fī Zujājatin  ۖ  Az-Zujājatu Ka'annahā Kawkabun Durrīyun Yūqadu Min Shajaratin Mubārakatin ZaytūniatinSharqīyatin Wa Lā Gharbīyatin Yakādu Zaytuhā Yuđī'u Wa Law Lam Tamsas/hu Nārun  ۚ  Nūrun `Alá Nūrin  ۗ  Yahdī Al-Lahu Linūrihi Man Yashā'u  ۚ  Wa Yađribu Al-Lahu Al-'Amthāla Lilnnāsi Wa  ۗ  Allāhu Bikulli Shay'in `Alīmun 024-035 Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misãlin HaskenSa, kamar tãgã, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurãro ne mai tsananin haske, anã kunna shi daga wata itãciya mai albarka, ta zaitũni, bã bagabashiya ba kuma bã bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kõ wuta ba ta shãfe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misãlai ga mutãne, kuma Allah game da dukan kõme, Masani ne.  ۚ   ۖ   ۖ   ۚ   ۗ   ۚ   ۗ 
Fī Buyūtin 'Adhina Al-Lahu 'An Turfa`a Wa Yudhkara Fīhā Asmuhu Yusabbiĥu Lahu Fīhā Bil-Ghudūwi Wa Al-'Āşāli 024-036 A cikin waɗansu gidãje waɗanda Allah Yã yi umurnin a ɗaukaka kuma a ambaci sũnansa a cikinsu, sunã yin tasbĩhi a gare Shi a cikinsu, sãfe da maraice.
Rijālun Lā Tulhīhim Tijāratun Wa Lā Bay`un `An Dhikri Al-Lahi Wa 'Iqāmi Aş-Şalāati Wa 'Ītā'i Az-Zakāati  ۙ  Yakhāfūna Yawmāan Tataqallabu Fīhi Al-Qulūbu Wa Al-'Abşāru 024-037 Waɗansu maza, waɗanda wani fatauci bã ya shagaltar da su, kuma sayarwa bã ta shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da bãyar da zakka, sunã tsõron wani yini wanda zukãta sunã bibbirkita a cikinsa, da gannai.  ۙ 
Liyajziyahumu Al-Lahu 'Aĥsana Mā `Amilū Wa Yazīdahum Min Fađlihi Wa  ۗ  Allāhu Yarzuqu Man Yashā'u Bighayri Ĥisābin 024-038 Dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Ya ƙãra musu daga falalarsa. Kuma Allah Yanã azurta wanda Yake so, bã da lissafi ba.  ۗ 
Wa Al-Ladhīna Kafarū 'A`māluhum Kasarābin Biqī`atin Yaĥsabuhu Až-Žam'ānu Mā'an Ĥattá 'Idhā Jā'ahu Lam Yajid/hu Shay'āan Wa Wajada Al-Laha `Indahu Fawaffāhu  ۗ  Ĥisābahu Wa Allāhu Sarī`u Al-Ĥisābi 024-039 Kuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya sãmi Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne.  ۗ 
'Aw Kažulumātin Fī Baĥrin Lujjīyin Yaghshāhu Mawjun Min Fawqihi Mawjun Min Fawqihi Saĥābun  ۚ  Žulumātun Ba`đuhā Fawqa Ba`đin 'Idhā 'Akhraja Yadahu Lam Yakad Yarāhā  ۗ  Wa Man Lam Yaj`ali Al-Lahu Lahu Nūrāan Famā Lahu Min Nūrin 024-040 Kõ kuwa kamar duffai a cikin tẽku mai zurfi, tãguwar ruwa tanã rufe da shi, daga bisansa akwai wata tãguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sãshensu a bisa sãshe, idan ya fitar da tãfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to, bã ya da wani haske.  ۚ   ۗ 
'Alam Tará 'Anna Al-Laha Yusabbiĥu Lahu Man As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Aţ-Ţayru Şāffātin  ۖ  Kullun Qad `Alima Şalātahu Wa Tasbīĥahu Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Bimā Yaf`alūna 024-041 Shin, ba ka gani ba (cẽwa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa sunã yi Masa tasbĩhi, kuma tsuntsaye sunã mãsu sanwa, kõwane lalle ya san sallarsa da tasbĩhinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa?  ۖ   ۗ 
Wa Lillahi Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Wa 'Ilá Al-Lahi Al-Maşīru 024-042 Mulkin sammai da ƙasa ga Allah kawai yake, kuma zuwa ga Allah makõma take.  ۖ 
'Alam Tará 'Anna Al-Laha Yuzjī Saĥābāan Thumma Yu'uallifu Baynahu Thumma Yaj`aluhu Rukāmāan Fatará Al-Wadqa Yakhruju Min Khilālihi Wa Yunazzilu Mina As-Samā'i Min Jibālin Fīhā Min Baradin Fayuşību Bihi Man Yashā'u Wa Yaşrifuhu `An Man Yashā'u  ۖ  Yakādu Sanā Barqihi Yadh/habu Bil-'Abşāri 024-043 Ashe, ba ka ganĩ ba, lalle ne Allah Yanã kõra girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a tsakãninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar jũna? Sai ka ga ruwa yanã fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwãtsu a cikinsa na ƙanƙarã daga sama, sai ya sãmu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yanã kusa ya tafi da gannai.  ۖ 
Yuqallibu Al-Lahu Al-Layla Wa An-Nahāra  ۚ  'Inna Fī Dhālika La`ibratan Li'wlī Al-'Abşāri 024-044 Allah Yanã jũyar da dare da yini. Lalle ne a cikin wannan akwai abin kula ga ma'abũta gannai.  ۚ 
Wa Allāhu Khalaqa Kulla Dābbatin Min  ۖ  Mā'in Faminhum Man Yamshī `Alá Baţnihi Wa Minhum Man Yamshī `Alá Rijlayni Wa Minhum Man Yamshī `Alá  ۚ  'Arba`in Yakhluqu Al-Lahu Mā  ۚ  Yashā'u 'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 024-045 Kuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafãfu biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yãna halitta abin da Yake so, lalle Allah, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne.  ۖ   ۚ   ۚ 
Laqad 'Anzalnā 'Āyātin Mubayyinātin Wa  ۚ  Allāhu Yahdī Man Yashā'u 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin 024-046 Lalle ne haƙĩƙa Mun saukar da ãyõyi, mãsu bayyanãwa. Kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya.  ۚ 
Wa Yaqūlūna 'Āmannā Bil-Lahi Wa Bir-Rasūli Wa 'Aţa`nā Thumma Yatawallá Farīqun Minhum Min Ba`di Dhālika  ۚ  Wa Mā 'Ūlā'ika Bil-Mu'uminīna 024-047 Kuma sunã cẽwa, "Mun yi ĩmãni da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗã'ã." Sa'an nan kuma wata ƙungiya daga gare su,su jũya daga bãyan wancan. Kuma waɗancan ba mũminai ba ne.  ۚ 
Wa 'Idhā Du`ū 'Ilá Al-Lahi Wa Rasūlihi Liyaĥkuma Baynahum 'Idhā Farīqun Minhum Mu`rūna 024-048 Kuma idan aka kirã su zuwa ga Allah da ManzonSa, dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu, sai gã wata ƙnngiya daga gare su sunã mãsu bijirewa.
Wa 'In Yakun Lahumu Al-Ĥaqqu Ya'tū 'Ilayhi Mudh`inīna 024-049 Kuma idan hakki ya kasance a gare su, zã su jẽ zuwa gare shi, snnã mãsu mĩƙa wuya.
'Afī Qulūbihim Marađun 'Am Artābū 'Am Yakhāfūna 'An Yaĥīfa Al-Lahu `Alayhim Wa Rasūluhu  ۚ  Bal 'Ūlā'ika Humu Až-Žālimūn 024-050 Shin, a cikin zukãtansu akwai cũta ne, ko kuwa sunã tsõron Allah Ya yi zãlunci a kansu da ManzonSa? Ã'a, waɗancan sũ ne azzãlumai.  ۚ 
'Innamā Kāna Qawla Al-Mu'uminīna 'Idhā Du`ū 'Ilá Al-Lahi Wa Rasūlihi Liyaĥkuma Baynahum 'An Yaqūlū Sami`nā Wa 'Aţa`nā  ۚ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna 024-051 Maganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu takan kasance kawai su ce "Mun ji, kuma mun yi ɗã'ã, Kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara."  ۚ 
Wa Man Yuţi`i Al-Laha Wa Rasūlahu Wa Yakhsha Al-Laha Wa Yattaqhi Fa'ūlā'ika Humu Al-Fā'izūna 024-052 Kuma wanda ya yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsõron Allah, ya kuma bĩ Shi da taƙawa to waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
Wa 'Aqsamū Bil-Lahi Jahda 'Aymānihim La'in 'Amartahum Layakhrujunna  ۖ  Qul Lā Tuqsimū  ۖ  Ţā`atun Ma`rūfatun  ۚ  'Inna Al-Laha Khabīrun Bimā Ta`malūna 024-053 Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙĩƙa sunã fita.' Ka ce, "Kada ku rantse, ɗã'ã sananna ce! Lalle ne, Allah Mai ƙididdigewã ne ga abin da kuke aikatãwã."  ۖ   ۖ   ۚ 
Qul 'Aţī`ū Al-Laha Wa 'Aţī`ū Ar-Rasūla  ۖ  Fa'in Tawallaw Fa'innamā `Alayhi Mā Ĥummila Wa `Alaykum Mā Ĥummiltum  ۖ  Wa 'In Tuţī`ūhu Tahtadū  ۚ  Wa Mā `Alá Ar-Rasūli 'Illā Al-Balāghu Al-Mubīnu 024-054 Ka ce: "Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu. Kuma bãbu abin da yake a kan Manzo fãce iyarwa bayyananna."  ۖ   ۖ   ۚ 
Wa`ada Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Minkum Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Layastakhlifannahum Al-'Arđi Kamā Astakhlafa Al-Ladhīna Min Qablihim Wa Layumakkinanna Lahum Dīnahumu Al-Ladhī Artađá Lahum Wa Layubaddilannahum Min Ba`di Khawfihim 'Amnāan  ۚ  Ya`budūnanī Lā Yushrikūna Bī Shay'āan  ۚ  Wa Man Kafara Ba`da Dhālika Fa'ūlā'ika Humu Al-Fāsiqūna 024-055 Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai.  ۚ   ۚ 
Wa 'Aqīmū Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata Wa 'Aţī`ū Ar-Rasūla La`allakum Turĥamūna 024-056 Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo, tsammãninku a yi muku rahama.
Lā Taĥsabanna Al-Ladhīna Kafarū Mu`jizīna Fī Al-'Arđi  ۚ  Wa Ma'wāhumu An-Nāru  ۖ  Wa Labi'sa Al-Maşīru 024-057 Kada lalle ka yi zaton waɗanda suka kãfirta zã su buwãya a cikin ƙasa, kuma makõmarsu wuta ce, kuma lalle ne makomar tã mũnana.  ۚ   ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Liyasta'dhinkumu Al-Ladhīna Malakat 'Aymānukum Wa Al-Ladhīna Lam Yablughū Al-Ĥuluma Minkum Thalātha Marrātin  ۚ  Min Qabli Şalāati Al-Fajri Wa Ĥīna Tađa`ūna Thiyā Bakum Mina Až-Žahīrati Wa Min Ba`di Şalāati  ۚ  Al-`Ishā'i Thalāthu `Awrātin  ۚ  Lakum Laysa `Alaykum Wa Lā `Alayhim Junāĥun  ۚ  Ba`dahunna Ţawwāfūna `Alaykum Ba`đukum `Alá  ۚ  Ba`đin Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu Lakumu  ۗ  Al-'Āyā Ti Wa Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 024-058 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۗ 
Wa 'Idhā Balagha Al-'Aţfālu Minkumu Al-Ĥuluma Falyasta'dhinū Kamā Asta'dhana Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu Lakum 'Āyātihi Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 024-059 Kuma idan yãra daga cikinku suka isa mafarki to su nẽmi izni, kamar yadda waɗanda suke a gabãninsu suka nẽmi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.  ۚ   ۗ 
Wa Al-Qawā`idu Mina An-Nisā' Al-Lātī Lā Yarjūna Nikāĥāan Falaysa `Alayhinna Junāĥun 'An Yađa`na Thiyābahunna Ghayra Mutabarrijātin  ۖ  Bizīnatin Wa 'An Yasta`fifna Khayrun  ۗ  Lahunna Wa Allāhu Samī`un `Alīmun 024-060 Kuma tsõfaffi daga mãtã, waɗanda bã su fatan wani aure to, bãbu laifi a kansu su ajiye tufãfinsu, bã sunã mãsu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shĩ ne mafi alhẽri a gare su. Kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.  ۖ   ۗ 
Laysa `Alá Al-'A`má Ĥarajun Wa Lā `Alá Al-'A`raji Ĥarajun Wa Lā `Alá Al-Marīđi Ĥarajun Wa Lā `Alá 'Anfusikum 'An Ta'kulū Min Buyūtikum 'Aw Buyūti 'Ābā'ikum 'Aw Buyūti 'Ummahātikum 'Aw Buyūti 'Ikhwānikum 'Aw Buyūti 'Akhawātikum 'Aw Buyūti 'A`māmikum 'Aw Buyūti `Ammātikum 'Aw Buyūti 'Akhwālikum 'Aw Buyūti Khālātikum 'Aw Mā Malaktum Mafātiĥahu 'Aw Şadīqikum  ۚ  Laysa `Alaykum Junāĥun 'An Ta'kulū Jamī`āan 'Aw 'Ashtātāan  ۚ  Fa'idhā Dakhaltum Buyūtāan Fasallimū `Alá 'Anfusikum Taĥīyatan Min `Indi Al-Lahi Mubārakatan Ţayyibatan  ۚ  Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu Lakumu Al-'Āyāti La`allakum Ta`qilūna 024-061 Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku, gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali. ~  ۚ   ۚ   ۚ 
'Innamā Al-Mu'uminūna Al-Ladhīna 'Āmanū Bil-Lahi Wa Rasūlihi Wa 'Idhā Kānū Ma`ahu `Alá 'Amrin Jāmi`in Lam Yadh/habū Ĥattá Yasta'dhinūhu  ۚ  'Inna Al-Ladhīna Yasta'dhinūnaka 'Ūlā'ika Al-Ladhīna Yu'uminūna Bil-Lahi Wa Rasūlihi  ۚ  Fa'idhā Asta'dhanūka Liba`đi Sha'nihim Fa'dhan Liman Shi'ta Minhum Wa Astaghfir Lahumu Al-Laha  ۚ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 024-062 Waɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai . ~  ۚ   ۚ   ۚ 
Lā Taj`alū Du`ā'a Ar-Rasūli Baynakum Kadu`ā'i Ba`đikum Ba`đāan  ۚ  Qad Ya`lamu Al-Lahu Al-Ladhīna Yatasallalūna Minkum Liwādhāan  ۚ  Falyaĥdhari Al-Ladhīna Yukhālifūna `An 'Amrihi 'An Tuşībahum Fitnatun 'Aw Yuşībahum `Adhābun 'Alīmun 024-063 Kada ku sanya kiran Manzo a tsakãninku kamar kiran sãshenku ga sãshe. Lalle ne Allah Yanã sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗãɗe. To, waɗanda suke sãɓãwa daga umurninSa, su yi saunar wata fitina ta sãme su, kõ kuwa wata azãba mai raɗãɗi ta sãme su.  ۚ   ۚ  ~
'Alā 'Inna Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Qad Ya`lamu Mā 'Antum `Alayhi Wa Yawma Yurja`ūna 'Ilayhi Fayunabbi'uhum Bimā `Amilū Wa  ۗ  Allāhu Bikulli Shay'in `Alīmun 024-064 To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa, Yanã sanin abin da kuke a kansa kuma a rãnar da ake mayar da su zuwa gare shi, sai Yanã bã su lãbãri game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kõme, Masani ne.  ۖ   ۗ 
Next Sūrah