22) Sūrat Al-Ĥaj

Printed format

22)

Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Attaqū Rabbakum 'Inna Zalzalata As-Sā`ati Shay'un `Ažīmun 022-001 Yã ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma.
Yawma Tarawnahā Tadh/halu Kullu Murđi`atin `Ammā 'Arđa`at Wa Tađa`u Kullu Dhāti Ĥamlin Ĥamlahā Wa Tará An-Nāsa Sukārá Wa Mā Hum Bisukārá Wa Lakinna `Adhāba Al-Lahi Shadīdun 022-002 A rãnar da kuke ganin ta dukan mai shãyar da mãma tanã shagala daga abin da ta shãyar, kuma dukan mai ciki tanã haihuwar cikinta, kuma kanã ganin mutãne sunã mãsu mãyẽ alhãli kuwa su bã mãsu mãye ba, amma azãbar Allah ce mai tsanani.
Wa Mina An-Nāsi Man Yujādilu Fī Al-Lahi Bighayri `Ilmin Wa Yattabi`u Kulla Shayţānin Marīdin 022-003 Akwai daga mutãne wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bã da wani ilmi ba, kuma yanã biyar kõwane Shaiɗan mai taurin kai.
Kutiba `Alayhi 'Annahu Man Tawallāhu Fa'annahu Yuđilluhu Wa Yahdīhi 'Ilá `Adhābi As-Sa`īri 022-004 An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azãbar sa'ĩr. ~
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu 'In Kuntum Fī Raybin Mina Al-Ba`thi Fa'innā Khalaqnākum Min Turābin Thumma Min Nuţfatin Thumma Min `Alaqatin Thumma Min Muđghatin Mukhallaqatin Wa Ghayri Mukhallaqatin Linubayyina Lakum  ۚ  Wa Nuqirru Fī Al-'Arĥāmi Mā Nashā'u 'Ilá 'Ajalin Musammáan Thumma Nukhrijukum Ţiflāan Thumma Litablughū 'Ashuddakum  ۖ  Wa Minkum Man Yutawaffá Wa Minkum Man Yuraddu 'Ilá 'Ardhali Al-`Umuri Likaylā Ya`lama Min Ba`di `Ilmin Shay'āan  ۚ  Wa Tará Al-'Arđa Hāmidatan Fa'idhā 'Anzalnā `Alayhā Al-Mā'a Ahtazzat Wa Rabat Wa 'Anbatat Min Kulli Zawjin Bahījin 022-005 Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tãshin ¡iyãma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga taõka wadda ake halittãwa da wadda ba a halittawa dõmin, Mu bayyana muku. Kuma Munã tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Munã fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan kuma dõmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kanã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa.  ۚ   ۖ   ۚ 
Dhālika Bi'anna Al-Laha Huwa Al-Ĥaqqu Wa 'Annahu Yuĥyī Al-Mawtá Wa 'Annahu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 022-006 Wancan ne dõmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rãyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kõme.
Wa 'Anna As-Sā`ata 'Ātiyatun Lā Rayba Fīhā Wa 'Anna Al-Laha Yab`athu Man Al-Qubūri 022-007 Kuma lalle ne Sa'ar Tãshin ¡iyãma mai zuwa ce, bãbu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yanã tãyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura.
Wa Mina An-Nāsi Man Yujādilu Fī Al-Lahi Bighayri `Ilmin Wa Lā Hudáan Wa Lā Kitābin Munīrin 022-008 Kuma daga mutãne akwai mai yin musu ga Allah bã da wani ilmi ba kuma bã da wata shiriya ba, kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba.
Thāniya `Iţfihi Liyuđilla `An Sabīli Al-Lahi  ۖ  Lahu Fī Ad-DunKhizyun  ۖ  Wa Nudhīquhu Yawma Al-Qiyāmati `Adhāba Al-Ĥarīqi 022-009 Yanã mai karkatar da sãshensa dõmin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yanã da wani wulãkanci a dũniya, kuma Munã ɗanɗana masa azãbar gõbara a Rãnar ¡iyãma.  ۖ   ۖ 
Dhālika Bimā Qaddamat Yadāka Wa 'Anna Al-Laha Laysa Bižallāmin Lil`abīdi 022-010 (A ce masa): "Wancan azaba sabõda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zãlunci ga bãyinSa ba."
Wa Mina An-Nāsi Man Ya`budu Al-Laha `Alá Ĥarfin  ۖ  Fa'in 'Aşābahu Khayrun Aţma'anna Bihi  ۖ  Wa 'In 'Aşābat/hu Fitnatun Anqalaba `Alá Wajhihi Khasira Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirata Dhālika  ۚ  Huwa Al-Khusrānu Al-Mubīnu 022-011 Kuma daga mutãne akwai mai bauta wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alhẽri ya sãme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta sãme shi, sai ya jũya bãya a kan fuskarsa. Yã yi hasãrar dũniya da Lãhira. Waccan ita ce hasãra bayyananna.  ۖ   ۖ   ۚ 
Yad`ū Min Dūni Al-Lahi Mā Lā Yađurruhu Wa Mā Lā Yanfa`uhu  ۚ  Dhālika Huwa Ađ-Đalālu Al-Ba`īdu 022-012 Yanã kiran baicin Allah, abin da bã ya cũtarsa da abin da bã ya amfãninsa! waccan ita ce ɓata mai nĩsa.  ۚ 
Yad`ū Laman Đarruhu 'Aqrabu Min Naf`ihi  ۚ  Labi'sa Al-Mawlá Wa Labi'sa Al-`Ashīru 022-013 Yanã kiran wanda yake lalle cũtarwarsa ce mafi kusa daga amfãninsa! Lalle ne, tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abõkin zama! ~  ۚ 
'Inna Al-Laha Yudkhilu Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru  ۚ  'Inna Al-Laha Yaf`alu Mā Yurīdu 022-014 Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake nufi.  ۚ 
Man Kāna Yažunnu 'An Lan Yanşurahu Al-Lahu Fī Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati Falyamdud Bisababin 'Ilá As-Samā'i Thumma Liyaqţa` Falyanžur Hal Yudh/hibanna Kayduhu Mā Yaghīžu 022-015 Wanda ya kasance yanã zaton cẽwa Allah bã zai taimake shi ba a cikin dũniya da Lãhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici?
Wa Kadhalika 'Anzalnāhu 'Āyātin Bayyinātin Wa 'Anna Al-Laha Yahdī Man Yurīdu 022-016 Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ãni) yanã ãyõyi bayyanannu. Kuma lalle ne Allah Yanã shiryar da wanda Yake nufi.
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Al-Ladhīna Hādū Wa Aş-Şābi'īna Wa An-Naşārá Wa Al-Majūsa Wa Al-Ladhīna 'Ashrakū 'Inna Al-Laha Yafşilu Baynahum Yawma Al-Qiyāmati  ۚ  'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Shahīdun 022-017 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda suka tũba (Yahũdu) da waɗanda suka karkace (Saba'ãwa) da Nasãra da Majũsãwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Ranãr ¡iyãma.Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kõme.  ۚ 
'Alam Tará 'Anna Al-Laha Yasjudu Lahu Man As-Samāwāti Wa Man Al-'Arđi Wa Ash-Shamsu Wa Al-Qamaru Wa An-Nujūmu Wa Al-Jibālu Wa Ash-Shajaru Wa Ad-Dawābbu Wa Kathīrun Mina An-Nāsi  ۖ  Wa Kathīrun Ĥaqqa `Alayhi Al-`Adhābu  ۗ  Wa Man Yuhini Al-Lahu Famā Lahu Min Mukrimin  ۚ  'Inna Al-Laha Yaf`alu Mā Yashā'u 022-018 Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa yanã yin sujada a gare shi, da kuma rãna da watã da taurãri da duwãtsu da itãce da dabbõbi, da kuma mãsu yawa daga mutãne? Kuma waɗansu mãsu yawa azãba tã tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulãkantar, to, bã ya da wani mai girmamãwa. Kuma Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake so.  ۖ   ۗ   ۚ 
Hadhāni Khaşmāni Akhtaşamū Fī Rabbihim  ۖ  Fa-Al-Ladhīna Kafarū Quţţi`at Lahum Thiyābun Min Nārin Yuşabbu Min Fawqi Ru'ūsihimu Al-Ĥamīmu 022-019 waɗannan ƙungiyõyi biyu ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu.  ۖ 
Yuşharu Bihi Mā Fī Buţūnihim Wa Al-Julūdu 022-020 Da shĩ ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fãtun jikinsu.
Wa Lahum Maqāmi`u Min Ĥadīdin 022-021 Kuma sunã da waɗansu gwalmõmin dũka na baƙin ƙarfe.
Kullamā 'Arādū 'An Yakhrujū Minhā Min Ghammin 'U`īdū Fīhā Wa Dhūqū `Adhāba Al-Ĥarīqi 022-022 A kõyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu) "Ku ɗanɗani azãbar gõbara."
'Inna Al-Laha Yudkhilu Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Yuĥallawna Fīhā Min 'Asāwira Min Dhahabin Wa Lu'ulu'uāan  ۖ  Wa Libāsuhum Fīhā Ĥarīrun 022-023 Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, anã ƙawãta su, a cikinsu, da waɗansu mundãye na zĩnãri da lu'u-lu'u. Kuma tufãfinsu a cikinsu alharĩni ne.  ۖ 
Wa Hudū 'Ilá Aţ-Ţayyibi Mina Al-Qawli Wa Hudū 'Ilá Şirāţi Al-Ĥamīdi 022-024 Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga, hanyar wanda ake gode wa.
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Wa Yaşuddūna `An Sabīli Al-Lahi Wa Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Al-Ladhī Ja`alnāhu Lilnnāsi Sawā'an Al-`Ākifu Fīhi Wa Al-Bādi  ۚ  Wa Man Yurid Fīhi Bi'ilĥādin Bižulmin Nudhiqhu Min `Adhābin 'Alīmin 022-025 Lalle ne waɗanda suka kãfirta kuma suka taushe (mutãne) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutãne alhãli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar da gaskiya a cikinsa da zãlunci zã Mu ɗanɗana masa daga wata azãba mai raɗadi.  ۚ 
Wa 'Idh Bawwa'nā Li'ibrāhīma Makāna Al-Bayti 'An Lā Tushrik Bī Shay'āan Wa Ţahhir Baytiya Lilţţā'ifīna Wa Al-Qā'imīna Wa Ar-Rukka`i As-Sujūdi 022-026 Kuma a lõkacin da Muka iyãkance wa Ibrãhim wurin akin (Muka ce masa), "Kada ka haɗa kõme da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu tsayuwa da mãsu ruku'u da mãsu sujada.
Wa 'Adhdhin An-Nāsi Bil-Ĥajji Ya'tūka Rijālāan Wa `Alá Kulli Đāmirin Ya'tīna Min Kulli Fajjin `Amīqin 022-027 "Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi."
Liyash/hadū Manāfi`a Lahum Wa Yadhkurū Asma Al-Lahi Fī 'Ayyāmin Ma`lūmātin `Alá Mā Razaqahum Min Bahīmati Al-'An`ām  ۖ  Fakulū Minhā Wa 'Aţ`imū Al-Bā'isa Al-Faqīra 022-028 "Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci."  ۖ 
Thumma Liyaqđū Tafathahum Wa Līūfū Nudhūrahum Wa Līaţţawwafū Bil-Bayti Al-`Atīqi 022-029 "Sa'an nan kuma sai su ƙãre ibãdarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawãfi (sunã gẽwaya) ga ãkin nin 'yantacce."
Dhālika Wa Man Yu`ažžim Ĥurumāti Al-Lahi Fahuwa Khayrun Lahu `Inda Rabbihi  ۗ  Wa 'Uĥillat Lakumu Al-'An`ām 'Illā Mā Yutlá `Alaykum  ۖ  Fājtanibū Ar-Rijsa Mina Al-'Awthāni Wa Ajtanibū Qawla Az-Zūri 022-030 Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbõbin ni'ima fãce abin da ake karantãwa a kanku. Sabõda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumãka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur.  ۗ   ۖ 
Ĥunafā'a Lillahi Ghayra Mushrikīna Bihi  ۚ  Wa Man Yushrik Bil-Lahi Faka'annamā Kharra Mina As-Samā'i Fatakhţafuhu Aţ-Ţayru 'Aw Tahwī Bihi Ar-Rīĥu Fī Makānin Saĥīqin 022-031 Kuna mãsu tsayuwa ga gaskiya dõmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yanã kamar abin da ya fãɗo daga sama, sa'an nan tsuntsãye su cafe shi, ko iska ta fãɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa.  ۚ 
Dhālika Wa Man Yu`ažžim Sha`ā'ira Al-Lahi Fa'innahā Min Taq Al-Qulūbi 022-032 Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda.
Lakum Fīhā Manāfi`u 'Ilá 'Ajalin Musammáan Thumma Maĥilluhā 'Ilá Al-Bayti Al-`Atīqi 022-033 Kuna da waɗansu abũbuwan amfãni a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattãta zuwa ga ãkin 'yantacce ne.
Wa Likulli 'Ummatin Ja`alnā Mansakāan Liyadhkurū Asma Al-Lahi `Alá Mā Razaqahum Min Bahīmati Al-'An`āmi  ۗ  Fa'ilahukum 'Ilahun Wāĥidun Falahu 'Aslimū  ۗ  Wa Bashshiri Al-Mukhbitīna 022-034 Kuma ga kõwace al'umma Mun sanya ibãdar yanka, dõmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbõbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushãra ga mãsu ƙanƙantar da kai.  ۗ  ~  ۗ 
Al-Ladhīna 'Idhā Dhukira Al-Lahu Wajilat Qulūbuhum Wa Aş-Şābirīna `Alá Mā 'Aşābahum Wa Al-Muqīmī Aş-Şalāati Wa Mimmā Razaqnāhum Yunfiqūna 022-035 Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukãtansu su firgita, da mãsu haƙuri a kan abin da ya sãme su, da mãsu tsayar da salla, kuma sunã ciyarwa daga abin da Muka azurta su.
Wa Al-Budna Ja`alnāhā Lakum Min Sha`ā'iri Al-Lahi Lakum Fīhā  ۖ  Khayrundhkurū Asma Al-Lahi `Alayhā  ۖ  Şawāffa Fa'idhā Wajabat Junūbuhā Fakulū Minhā Wa 'Aţ`imū Al-Qāni`a Wa  ۚ  Al-Mu`tarra Kadhālika Sakhkharnāhā Lakum La`allakum Tashkurūna 022-036 Kuma rãƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibãdõjin Allah. Kunã da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sunã tsaye a kan ƙafãfu uku. Sa'an nan idan sãsanninsu suka fãɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hõre muku su, tsammãninku kunã gõdẽwa.  ۖ   ۖ   ۚ 
Lan Yanāla Al-Laha Luĥūmuhā Wa Lā Dimā'uuhā Wa Lakin Yanāluhu At-Taqwá Minkum  ۚ  Kadhālika Sakhkharahā Lakum Litukabbirū Al-Laha `Alá Mā Hadākum  ۗ  Wa Bashshiri Al-Muĥsinīna 022-037 Nãmõminsu bã za su sãmi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tanã, sãmun Sa. Kamar haka Ya hõre su sabõda ku dõmin ku girmama Allah sabõda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushãra ga mãsu kyautata yi.  ۚ   ۗ 
'Inna Al-Laha Yudāfi`u `Ani Al-Ladhīna 'Āmanū  ۗ  'Inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Kulla Khawwānin Kafūrin 022-038 Lalle ne, Allah Yanã yin faɗa sabõda waɗanda suka yi ĩmãni. Lalle ne Allah bã Ya son dukkan mayaudari, mai yawan kãfirci.  ۗ 
'Udhina Lilladhīna Yuqātalūna Bi'annahum Žulimū  ۚ  Wa 'Inna Al-Laha `Alá Naşrihim Laqadīrun 022-039 An yi izni ga waɗanda ake yãƙar su da cẽwa lalle an zãlunce su, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa,Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu.  ۚ 
Al-Ladhīna 'Ukhrijū Min Diyārihim Bighayri Ĥaqqin 'Illā 'An Yaqūlū Rabbunā Al-Lahu  ۗ  Wa Lawlā Daf`u Al-Lahi An-Nāsa Ba`đahum Biba`đin Lahuddimat Şawāmi`u Wa Biya`un Wa Şalawātun Wa Masājidu Yudhkaru Fīhā Asmu Al-Lahi Kathīrāan  ۗ  Wa Layanşuranna Al-Lahu Man Yanşuruhu  ۗ  'Inna Al-Laha Laqawīyun `Azīzun 022-040 Waɗanda aka fitina daga gidajensu bã da wani hakki ba fãce sunã cẽwa, Ubangijinmu Allah ne."Kuma ba dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne ba, sãshensu da sãshe, haƙĩƙa, da an rũsa sauma'õ'in (Ruhbãnãwa) dã majãmi'õ'in Nasãra da gidãjen ibãdar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yanã taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne haƙĩƙa Mai ƙarfi Mabuwãyi.  ۗ   ۗ  ~  ۗ 
Al-Ladhīna 'In Makkannāhum Al-'Arđi 'Aqāmū Aş-Şalāata Wa 'Ātaw Az-Zakāata Wa 'Amarū Bil-Ma`rūfi Wa Nahaw `Ani Al-Munkari  ۗ  Wa Lillahi `Āqibatu Al-'Umūri 022-041 Waɗanda suke idan Muka bã su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani, kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma ãƙibar al'amura ga Allah take.  ۗ 
Wa 'In Yukadhdhibūka Faqad Kadhdhabat Qablahum Qawmu Nūĥin Wa `Ādun Wa Thamūdu 022-042 Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙĩƙa, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa, sun ƙaryata a gabaninsu.
Wa Qawmu 'Ibrāhīma Wa Qawmu Lūţin 022-043 Da mutãnen Ibrahim da mutãnen Lũɗu.
Wa 'Aşĥābu Madyana  ۖ  Wa Kudhdhiba Mūsá Fa'amlaytu Lilkāfirīna Thumma 'Akhadhtuhum  ۖ  Fakayfa Kāna Nakīri 022-044 Da mãsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsã. Sai Na jinkirtawa kãfiran, sa'an nan kuma Na kãma su. To, yãya musũNa (gare su) ya kasance?  ۖ   ۖ 
Faka'ayyin Min Qaryatin 'Ahlaknāhā Wa Hiya Žālimatun Fahiya Khāwiyatun `Alá `Urūshihā Wa Bi'rin Mu`aţţalatin Wa Qaşrin Mashīdin 022-045 Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhãli kuwa tanã mai zalũnci sai ta zama fãɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wõfintar, da kuma gidãjen sarauta maɗaukaka.
'Afalam Yasīrū Fī Al-'Arđi Fatakūna Lahum Qulūbun Ya`qilūna Bihā 'Aw 'Ādhānun Yasma`ūna Bihā  ۖ  Fa'innahā Lā Ta`má Al-'Abşāru Wa Lakin Ta`má Al-Qulūbu Allatī Fī Aş-Şudūri 022-046 Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dõmin zukãta waɗanda zã su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurãre da su su kasance a gare su? Dõmin lalle ne idãnun ba su makanta, amma zukãta waɗanda ke a cikin ƙirãza sũ ke makanta.  ۖ 
Wa Yasta`jilūnaka Bil-`Adhābi Wa Lan Yukhlifa Al-Lahu Wa`dahu  ۚ  Wa 'Inna Yawmāan `Inda Rabbika Ka'alfi Sanatin Mimmā Ta`uddūna 022-047 Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa.  ۚ 
Wa Ka'ayyin Min Qaryatin 'Amlaytu Lahā Wa Hiya Žālimatun Thumma 'Akhadhtuhā Wa 'Ilayya Al-Maşīru 022-048 Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azãba gare ta (da laifinta) sa'an nan Na kãma ta, kuma zuwa gare Ni makõma take.
Qul Yā 'Ayyuhā An-Nāsu 'Innamā 'Anā Lakum Nadhīrun Mubīnun 022-049 Ka ce: "Ya ku mutãne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa."
Fa-Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lahum Maghfiratun Wa Rizqun Karīmun 022-050 To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sunã da gãfara da arziki na karimci.
Wa Al-Ladhīna Sa`aw Fī 'Āyātinā Mu`ājizīna 'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Jaĥīmi 022-051 Kuma waɗanda suka yi aikin ɓãtãwa a cikin ayõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahĩm ne.
Wa Mā 'Arsalnā Min Qablika Min Rasūlin Wa Lā Nabīyin 'Illā 'Idhā Tamanná 'Alqá Ash-Shayţānu Fī 'Umnīyatihi Fayansakhu Al-Lahu Mā Yulqī Ash-Shayţānu Thumma Yuĥkimu Al-Lahu 'Āyātihi Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 022-052 Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri, sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyinSa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.  ۗ 
Liyaj`ala Mā Yulqī Ash-Shayţānu Fitnatan Lilladhīna Fī Qulūbihim Marađun Wa Al-Qāsiyati Qulūbuhum  ۗ  Wa 'Inna Až-Žālimīna Lafī Shiqāqin Ba`īdin 022-053 Dõmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfãwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukãtansu akwai cũta, da mãsu ƙẽƙasassun zukãtansu. Kuma lalle ne azzãlumai haƙĩƙa, sunã a cikin sãɓãnimai nĩsa.  ۗ 
Wa Liya`lama Al-Ladhīna 'Ū Al-`Ilma 'Annahu Al-Ĥaqqu Min Rabbika Fayu'uminū Bihi Fatukhbita Lahu Qulūbuhum  ۗ  Wa 'Inna Al-Laha Lahādi Al-Ladhīna 'Āmanū 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin 022-054 Kuma dõmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka dõmin su yi ĩmãni da shi sabõda zukãtansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmãni ne zuwa ga hanya madaidaiciya.  ۗ 
Wa Lā Yazālu Al-Ladhīna Kafarū Fī Miryatin Minhu Ĥattá Ta'tiyahumu As-Sā`atu Baghtatan 'Aw Ya'tiyahum `Adhābu Yawmin `Aqīmin 022-055 Kuma waɗanda suka kãfirta bã zã su gushe ba sunã a cikin shakka daga gare shi, har Sa'a ta jẽ musu bisa ga abke, kõ kuwa azãbar wani yini bakarãre ta jẽ musu.
Al-Mulku Yawma'idhin Lillahi Yaĥkumu Baynahum  ۚ  Fa-Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Fī Jannāti An-Na`īmi 022-056 Mulki a rãnar nan ga Allah yake, Yanã hukunci a tsakãninsu. To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã a cikin gidãjen Aljannar ni'ima.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna Kafarū Wa Kadhdhabū Bi'āyātinā Fa'ūlā'ika Lahum `Adhābun Muhīnun 022-057 Kuma waɗandra suka kãfirta kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, to, waɗannan sunã da azãba mai wulãkantarwa.
Wa Al-Ladhīna Hājarū Fī Sabīli Al-Lahi Thumma Qutilū 'Aw Mātū Layarzuqannahumu Al-Lahu Rizqāan  ۚ  Ĥasanāan Wa 'Inna Al-Laha Lahuwa Khayru Ar-Rāziqīna 022-058 Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, kõ suka mutu, lalle ne Allah Yanã azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu azurtãwa.  ۚ 
Layudkhilannahum Mudkhalāan Yarđawnahu  ۗ  Wa 'Inna Al-Laha La`alīmun Ĥalīmun 022-059 Lalle ne, Yanã shigar da su a wata mashiga wadda zã su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri.  ۗ 
Dhālika Wa Man `Āqaba Bimithli Mā `Ūqiba Bihi Thumma Bughiya `Alayhi Layanşurannahu Al-Lahu  ۗ  'Inna Al-Laha La`afūwun Ghafūrun 022-060 Wancan! Kuma wanda ya rãma azãba da misãlin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zãlunce shi, lalle ne Allah Yanã taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.  ۗ 
Dhālika Bi'anna Al-Laha Yūliju Al-Layla Fī An-Nahāri Wa Yūliju An-Nahāra Fī Al-Layli Wa 'Anna Al-Laha Samī`un Başīrun 022-061 Wancan! sabõda Allah Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne,Mai gani.
Dhālika Bi'anna Al-Laha Huwa Al-Ĥaqqu Wa 'Anna Mā Yad`ūna Min Dūnihi Huwa Al-Bāţilu Wa 'Anna Al-Laha Huwa Al-`Alīyu Al-Kabīru 022-062 Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.
'Alam Tará 'Anna Al-Laha 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an Fatuşbiĥu Al-'Arđu Mukhđarratan  ۗ  'Inna Al-Laha Laţīfun Khabīrun 022-063 Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sai ƙasa ta wãyi gari kõriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa.  ۗ 
Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۗ  Wa 'Inna Al-Laha Lahuwa Al-Ghanīyu Al-Ĥamīdu 022-064 Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa,Shi ne wadatacce, Gõdadde.  ۗ 
'Alam Tará 'Anna Al-Laha Sakhkhara Lakum Mā Fī Al-'Arđi Wa Al-Fulka Tajrī Fī Al-Baĥri Bi'amrihi Wa Yumsiku As-Samā'a 'An Taqa`a `Alá Al-'Arđi 'Illā Bi'idhnihi  ۗ  'Inna Al-Laha Bin-Nāsi Lara'ūfun Raĥīmun 022-065 Shin ba ka gani ba, lalle ne Allah Ya hõre muku abin da yake a cikin ƙasa, kuma jirãge sunã gudãna a cikin tẽku, da umurninSa kuma Yanã riƙe sama dõmin kada ta fãɗi a kan ƙasa fãce da izninsa? Lalle ne Allah ga mutãne haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai. ~  ۗ 
Wa Huwa Al-Ladhī 'Aĥyākum Thumma Yumītukum Thumma Yuĥyīkum  ۗ  'Inna Al-'Insāna Lakafūrun 022-066 Kuma shĩ ne wanda Ya rãya ku, sa'an nan kuma Yanã matar da ku, sa'an nan kuma Yanã rãyar da ku. Lalle mutum, haƙĩƙa, mai kãfirci ne.  ۗ 
Likulli 'Ummatin Ja`alnā Mansakāan Hum Nāsikūhu  ۖ  Falā Yunāzi`unnaka Fī Al-'Amri  ۚ  Wa Ad`u 'Ilá Rabbika  ۖ  'Innaka La`alá Hudáan Mustaqīmin 022-067 Ga kõwace al'umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare Shi, sabõda haka, kada su yi maka jãyayya a cikin al'amarin (hadaya). Kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka lalle kai kana a kan shiriya madaidaiciya.  ۖ   ۚ   ۖ 
Wa 'In Jādalūka Faquli Al-Lahu 'A`lamu Bimā Ta`malūna 022-068 Kuma idan sun yi maka jidãli, sai ka ce: "Allah ne Mafi sani game da abin da kuke aikatãwa."
Al-Lahu Yaĥkumu Baynakum Yawma Al-Qiyāmati Fīmā Kuntum Fīhi Takhtalifūna 022-069 "Allah ne zai yi hukunci a tsakãninku, a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da kuka kasance a cikinsa kunã sãɓawa jũna."
'Alam Ta`lam 'Anna Al-Laha Ya`lamu Mā Fī As-Samā'i Wa Al-'Arđi  ۗ  'Inna Dhālika Fī Kitābin  ۚ  'Inna Dhālika `Alá Al-Lahi Yasīrun 022-070 Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.  ۗ   ۚ 
Wa Ya`budūna Min Dūni Al-Lahi Mā Lam Yunazzil Bihi Sulţānāan Wa Mā Laysa Lahum Bihi `Ilmun  ۗ  Wa Mā Lilžžālimīna Min Naşīrin 022-071 Kuma sunã bautãwa baicin Allah, abin da (Allah) bai saukar da wani dalili ba game da shi, kuma abin da bã su da wani ilmi game da shi, kuma bãbu wani mai taimako ga azzãlumai.  ۗ 
Wa 'Idhā Tutlá `Alayhim 'Āyātunā Bayyinātin Ta`rifu Fī Wujūhi Al-Ladhīna Kafarū Al-Munkara  ۖ  Yakādūna Yasţūna Bial-Ladhīna Yatlūna `Alayhim 'Āyātinā  ۗ  Qul 'Afa'unabbi'ukum Bisharrin Min Dhalikumu  ۗ  An-Nāru Wa`adahā Al-Lahu Al-Ladhīna Kafarū  ۖ  Wa Bi'sa Al-Maşīru 022-072 Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu kanã sanin abin ƙyãma a cikin fuskõkin waɗanda suka kãfirta sunã kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karãtun ayõyinMu a kansu. Ka ce: "Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga wannan? (Ita ce) Wuta." Allah Yã yi alkawarinta ga waɗanda suka kãfirta. Kuma makõmarsu ta mũnana.  ۖ   ۗ   ۗ   ۖ 
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Đuriba Mathalun Fāstami`ū Lahu  ۚ  'Inna Al-Ladhīna Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi Lan Yakhluqū Dhubābāan Wa Lawi Ajtama`ū Lahu  ۖ  Wa 'In Yaslubhumu Adh-Dhubābu Shay'āan Lā Yastanqidhūhu Minhu  ۚ  Đa`ufa Aţ-Ţālibu Wa Al-Maţlūbu 022-073 "Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana." ~  ۚ   ۖ   ۚ 
Mā Qadarū Al-Laha Ĥaqqa Qadrihi  ۗ  'Inna Al-Laha Laqawīyun `Azīzun 022-074 Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi. ~  ۗ 
Al-Lahu Yaşţafī Mina Al-Malā'ikati Rusulāan Wa Mina An-Nāsi  ۚ  'Inna Al-Laha Samī`un Başīrun 022-075 Allah nã zãɓen Manzanni daga malã'iku kuma daga mutãne. Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani.  ۚ 
Ya`lamu Mā Bayna 'Aydīhim Wa Mā Khalfahum  ۗ  Wa 'Ilá Al-Lahi Turja`u Al-'Umūru 022-076 Yanã sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura.  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Arka`ū Wa Asjudū Wa A`budū Rabbakum Wa Af`alū Al-Khayra La`allakum Tufliĥūna 022-077 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammãninku, ku sami babban rabo.
Wa Jāhidū Fī Al-Lahi Ĥaqqa Jihādihi  ۚ  Huwa Ajtabākum Wa Mā Ja`ala `Alaykum Ad-Dīni Min Ĥarajin  ۚ  Millata 'Abīkum 'Ibrāhīma  ۚ  Huwa Sammākumu Al-Muslimyna Min Qablu Wa Fī Hādhā Liyakūna Ar-Rasūlu Shahīdāan `Alaykum Wa Takūnū Shuhadā'a `Alá An-Nāsi  ۚ  Fa'aqīmū Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata Wa A`taşimū Bil-Lahi Huwa Mawlākum  ۖ  Fani`ma Al-Mawlá Wa Ni`ma An-Naşīru 022-078 Kuma ku yi jihãdi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihãdinSa. shĩ ne Ya zãɓe ku alhãli kuwa bai sanya wani ƙunci ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrãhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi daga gabãnin haka. Kuma a cikin wannan (Littãfi ya yi muku sũna Musulmi), dõmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemãsu shaida a kan mutãne. Sabõda haka ku tsayar da salla kuma ku bãyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Sãbõda haka mãdalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mãdalla da Shi ya zama Mai taimako.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۖ 
Next Sūrah