21) Sūrat Al-'Anbyā'

Printed format

21) سُورَة الأَنبيَاء

Aqtaraba Lilnnāsi Ĥisābuhum Wa HumGhaflatin Mu`rūna َ021-001 Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa. اقْتَرَبَ لِلنَّاسِ حِسَابُهُمْ وَهُمْ فِي غَفْلَة ٍ مُعْرِضُونَ
Mā Ya'tīhim Min Dhikrin Min Rabbihim Muĥdathin 'Illā Astama`ūhu Wa Hum Yal`abūna َ021-002 Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa. مَا يَأْتِيهِمْ مِنْ ذِكْر ٍ مِنْ رَبِّهِمْ مُحْدَث ٍ إِلاَّ اسْتَمَعُوه ُُ وَهُمْ يَلْعَبُونَ
Lāhiyatan Qulūbuhum  ۗ  Wa 'Asarrū An-Naj Al-Ladhīna Žalamū Hal Hādhā 'Illā Basharun Mithlukum  ۖ  'Afata'tūna As-Siĥra Wa 'Antum Tubşirūna َ021-003 Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?" لاَهِيَة ً قُلُوبُهُمْ  ۗ  وَأَسَرُّوا النَّجْوَى الَّذِينَ ظَلَمُوا هَلْ هَذَا إِلاَّ بَشَر ٌ مِثْلُكُمْ  ۖ  أَفَتَأْتُونَ السِّحْرَ وَأَنْتُمْ تُبْصِرُونَ
Qāla Rabbī Ya`lamu Al-Qawla Fī As-Samā'i Wa Al-'Arđi  ۖ  Wa Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu َ021-004 Ya ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani." قَالَ رَبِّي يَعْلَمُ الْقَوْلَ فِي السَّمَاءِ وَالأَرْضِ  ۖ  وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Bal Qālū 'Ađghāthu 'Aĥlāmin Bal Aftarāhu Bal Huwa Shā`irun Falya'tinā Bi'āyatin Kamā 'Ursila Al-'Awwalūna َ021-005 Ã'a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko." بَلْ قَالُوا أَضْغَاثُ أَحْلاَم ٍ بَلْ افْتَرَاه ُُ بَلْ هُوَ شَاعِر ٌ فَلْيَأْتِنَا بِآيَة ٍ كَمَا أُرْسِلَ الأَوَّلُونَ
Mā 'Āmanat Qablahum Min Qaryatin 'Ahlaknāhā  ۖ  'Afahum Yu'uminūna َ021-006 Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni? مَا آمَنَتْ قَبْلَهُمْ مِنْ قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا  ۖ  أَفَهُمْ يُؤْمِنُونَ
Wa Mā 'Arsalnā Qablaka 'Illā Rijālāan Nūĥī 'Ilayhim  ۖ  Fās'alū 'Ahla Adh-Dhikri 'In Kuntum Lā Ta`lamūna َ021-007 Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato idan kun kasance ba ku sani ba. وَمَا أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ إِلاَّ رِجَالا ً نُوحِي إِلَيْهِمْ  ۖ  فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنتُمْ لاَ تَعْلَمُونَ
Wa Mā Ja`alnāhum Jasadāan Lā Ya'kulūna Aţ-Ţa`āma Wa Mā Kānū Khālidīna َ021-008 Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba. وَمَا جَعَلْنَاهُمْ جَسَدا ً لاَ يَأْكُلُونَ الطَّعَامَ وَمَا كَانُوا خَالِدِينَ
Thumma Şadaqnāhumu Al-Wa`da Fa'anjaynāhum Wa Man Nashā'u Wa 'Ahlaknā Al-Musrifīna َ021-009 Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa. ثُمَّ صَدَقْنَاهُمُ الْوَعْدَ فَأَنجَيْنَاهُمْ وَمَنْ نَشَاءُ وَأَهْلَكْنَا الْمُسْرِفِينَ
Laqad 'Anzalnā 'Ilaykum Kitābāan Fīhi Dhikrukum  ۖ  'Afalā Ta`qilūna َ021-010 Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku, a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta? لَقَدْ أَنزَلْنَا إِلَيْكُمْ كِتَابا ً فِيه ِِ ذِكْرُكُمْ  ۖ  أَفَلاَ تَعْقِلُونَ
Wa Kam Qaşamnā Min Qaryatin Kānat Žālimatan Wa 'Ansha'nā Ba`dahā Qawmāan 'Ākharīna َ021-011 Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta. وَكَمْ قَصَمْنَا مِنْ قَرْيَة ٍ كَانَتْ ظَالِمَة ً وَأَنشَأْنَا بَعْدَهَا قَوْما ً آخَرِينَ
Falammā 'Aĥassū Ba'sanā 'Idhā Hum Minhā Yarkuđūna َ021-012 Sai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta. فَلَمَّا أَحَسُّوا بَأْسَنَا إِذَا هُمْ مِنْهَا يَرْكُضُونَ
Lā Tarkuđū Wa Arji`ū 'Ilá Mā 'Utriftum Fīhi Wa Masākinikum La`allakum Tus'alūna َ021-013 "Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku." لاَ تَرْكُضُوا وَارْجِعُوا إِلَى مَا أُتْرِفْتُمْ فِيه ِِ وَمَسَاكِنِكُمْ لَعَلَّكُمْ تُسْأَلُونَ
Qālū Yā Waylanā 'Innā Kunnā Žālimīna َ021-014 Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci." قَالُوا يَاوَيْلَنَا إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ
Famā Zālat Tilka Da`wāhum Ĥattá Ja`alnāhum Ĥaşīdāan Khāmidīna َ021-015 Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu. فَمَا زَالَتْ تِلْكَ دَعْوَاهُمْ حَتَّى جَعَلْنَاهُمْ حَصِيداً خَامِدِينَ
Wa Mā Khalaq As-Samā'a Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā Lā`ibīna َ021-016 Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba. وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاءَ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لاَعِبِينَ
Law 'Aradnā 'An Nattakhidha Lahwan Lāttakhadhnāhu Min Ladunnā 'In Kunnā Fā`ilīna َ021-017 Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa. لَوْ أَرَدْنَا أَنْ نَتَّخِذَ لَهْوا ً لاَتَّخَذْنَاه ُُ مِنْ لَدُنَّا إِنْ كُنَّا فَاعِلِينَ
Bal Naqdhifu Bil-Ĥaqqi `Alá Al-Bāţili Fayadmaghuhu Fa'idhā Huwa Zāhiqun  ۚ  Wa Lakumu Al-Waylu Mimmā Taşifūna َ021-018 Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa. بَلْ نَقْذِفُ بِالْحَقِّ عَلَى الْبَاطِلِ فَيَدْمَغُه ُُ فَإِذَا هُوَ زَاهِق ٌ  ۚ  وَلَكُمُ الْوَيْلُ مِمَّا تَصِفُونَ
Wa Lahu Man As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Wa Man `Indahu Lā Yastakbirūna `An `Ibādatihi Wa Lā Yastaĥsirūna َ021-019 Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurinSa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya. وَلَه ُُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۚ  وَمَنْ عِنْدَهُ لاَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِه ِِ وَلاَ يَسْتَحْسِرُونَ
Yusabbiĥūna Al-Layla Wa An-Nahāra Lā Yafturūna َ021-020 Sunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni. يُسَبِّحُونَ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ لاَ يَفْتُرُونَ
'Am Attakhadhū 'Ālihatan Mina Al-'Arđi Hum Yunshirūna َ021-021 Kõ (kãfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa (gare su)? أَمْ اتَّخَذُوا آلِهَة ً مِنَ الأَرْضِ هُمْ يُنشِرُونَ
Law Kāna Fīhimā 'Ālihatun 'Illā Al-Lahu Lafasadatā  ۚ  Fasubĥāna Al-Lahi Rabbi Al-`Arshi `Ammā Yaşifūna َ021-022 Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa. لَوْ كَانَ فِيهِمَا آلِهَة ٌ إِلاَّ اللَّهُ لَفَسَدَتَا  ۚ  فَسُبْحَانَ اللَّهِ رَبِّ الْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَ
Lā Yus'alu `Ammā Yaf`alu Wa Hum Yus'alūna َ021-023 Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su. لاَ يُسْأَلُ عَمَّا يَفْعَلُ وَهُمْ يُسْأَلُونَ
'Am Attakhadhū Min Dūnihi 'Ālihatan  ۖ  Qul Hātū Burhānakum  ۖ  Hādhā Dhikru Man Ma`iya Wa Dhikru Man Qablī  ۗ  Bal 'Aktharuhum Lā Ya`lamūna Al-Ĥaqqa  ۖ  Fahum Mu`rūna َ021-024 Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne." أَمْ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِهِ آلِهَة ً  ۖ  قُلْ هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ  ۖ  هَذَا ذِكْرُ مَنْ مَعِيَ وَذِكْرُ مَنْ قَبْلِي  ۗ  بَلْ أَكْثَرُهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ الْحَقَّ  ۖ  فَهُمْ مُعْرِضُونَ
Wa Mā 'Arsalnā Min Qablika Min Rasūl 'Iinillā Nūĥī 'Ilayhi 'Annahu Lā 'Ilāha 'Illā 'Anā Fā`budūni َ021-025 Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini." وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رَسُول إٍِلاَّ نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ أَنَا فَاعْبُدُونِ
Wa Qālū Attakhadha Ar-Raĥmānu Waladāan  ۗ  Subĥānahu  ۚ  Bal `Ibādun Mukramūna َ021-026 Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja. وَقَالُوا اتَّخَذَ الرَّحْمَنُ وَلَدا ً  ۗ  سُبْحَانَه ُُ  ۚ  بَلْ عِبَاد ٌ مُكْرَمُونَ
Lā Yasbiqūnahu Bil-Qawli Wa Hum Bi'amrihi Ya`malūna َ021-027 Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki. لاَ يَسْبِقُونَه ُُ بِالْقَوْلِ وَهُمْ بِأَمْرِه ِِ يَعْمَلُونَ
Ya`lamu Mā Bayna 'Aydīhim Wa Mā Khalfahum Wa Lā Yashfa`ūna 'Illā Limani Artađá Wa Hum Min Khashyatihi Mushfiqūna َ021-028 Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõronSa. يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يَشْفَعُونَ إِلاَّ لِمَنِ ارْتَضَى وَهُمْ مِنْ خَشْيَتِه ِِ مُشْفِقُونَ
Wa Man Yaqul Minhum 'Innī 'Ilahun Min Dūnihi Fadhālika Najzīhi Jahannama  ۚ  Kadhālika Naj Až-Žālimīna َ021-029 Kuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa," to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai. وَمَنْ يَقُلْ مِنْهُمْ إِنِّي إِلَه ٌ ٌ مِنْ دُونِه ِِ فَذَلِكَ نَجْزِيه ِِ جَهَنَّمَ  ۚ  كَذَلِكَ نَجْزِي الظَّالِمِينَ
'Awalam Yará Al-Ladhīna Kafarū 'Anna As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Kānatā Ratqāan Fafataqnāhumā  ۖ  Wa Ja`alnā Mina Al-Mā'i Kulla Shay'in Ĥayyin  ۖ  'Afalā Yu'uminūna َ021-030 Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke, sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba? أَوَلَمْ يَرَى الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ كَانَتَا رَتْقا ً فَفَتَقْنَاهُمَا  ۖ  وَجَعَلْنَا مِنَ الْمَاءِ كُلَّ شَيْءٍ حَيٍّ  ۖ  أَفَلاَ يُؤْمِنُونَ
Wa Ja`alnā Fī Al-'Arđi Rawāsiya 'An Tamīda Bihim Wa Ja`alnā Fīhā Fijājāan Subulāan La`allahum Yahtadūna َ021-031 Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa. وَجَعَلْنَا فِي الأَرْضِ رَوَاسِيَ أَنْ تَمِيدَ بِهِمْ وَجَعَلْنَا فِيهَا فِجَاجا ً سُبُلا ً لَعَلَّهُمْ يَهْتَدُونَ
Wa Ja`alnā As-Samā'a Saqfāan Maĥfūžāan  ۖ  Wa Hum `An 'Āyātihā Mu`rūna َ021-032 Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirẽwa ne. وَجَعَلْنَا السَّمَاءَ سَقْفا ً مَحْفُوظا ً  ۖ  وَهُمْ عَنْ آيَاتِهَا مُعْرِضُونَ
Wa Huwa Al-Ladhī Khalaqa Al-Layla Wa An-Nahāra Wa Ash-Shamsa Wa Al-Qamara  ۖ  Kullun Fī Falakin Yasbaĥūna َ021-033 Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu a cikin wani sarari suKe iyo. وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ  ۖ  كُلّ ٌ فِي فَلَك ٍ يَسْبَحُونَ
Wa Mā Ja`alnā Libasharin Min Qablika Al-Khulda  ۖ  'Afa'īn Mitta Fahumu Al-Khālidūna َ021-034 Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama? وَمَا جَعَلْنَا لِبَشَر ٍ مِنْ قَبْلِكَ الْخُلْدَ  ۖ  أَفَإِيْنْ مِتَّ فَهُمُ الْخَالِدُونَ
Kullu Nafsin Dhā'iqatu Al-Mawti  ۗ  Wa Nablūkum Bish-Sharri Wa Al-Khayri Fitnatan  ۖ  Wa 'Ilaynā Turja`ūna َ021-035 Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku. كُلُّ نَفْس ٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ  ۗ  وَنَبْلُوكُمْ بِالشَّرِّ وَالْخَيْرِ فِتْنَة ً  ۖ  وَإِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
Wa 'Idhā Ra'āka Al-Ladhīna Kafarū 'In Yattakhidhūnaka 'Illā Huzuwan 'Ahadhā Al-Ladhī Yadhkuru 'Ālihatakum Wa Hum Bidhikri Ar-Raĥmāni Hum Kāfirūna َ021-036 Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta ne. وَإِذَا رَآكَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنْ يَتَّخِذُونَكَ إِلاَّ هُزُواً أَهَذَا الَّذِي يَذْكُرُ آلِهَتَكُمْ وَهُمْ بِذِكْرِ الرَّحْمَنِ هُمْ كَافِرُونَ
Khuliqa Al-'Insānu Min `Ajalin  ۚ  Sa'urīkum 'Āyātī Falā Tasta`jilūni َ021-037 An halitta mutum daga gaggãwa, zan nũna muku ãyõyiNa. Sabõda haka kada ku nẽmiyin gaggãwa. خُلِقَ الإِنسَانُ مِنْ عَجَل ٍ  ۚ  سَأُرِيكُمْ آيَاتِي فَلاَ تَسْتَعْجِلُونِ
Wa Yaqūlūna Matá Hādhā Al-Wa`du 'In Kuntum Şādiqīna َ021-038 Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai tabbata, idan kun kasance mãsu gaskiya?" وَيَقُولُونَ مَتَى هَذَا الْوَعْدُ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ
Law Ya`lamu Al-Ladhīna Kafarū Ĥīna Lā Yakuffūna `An Wujūhihimu An-Nāra Wa Lā `An Žuhūrihim Wa Lā Hum Yunşarūna َ021-039 Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba. لَوْ يَعْلَمُ الَّذِينَ كَفَرُوا حِينَ لاَ يَكُفُّونَ عَنْ وُجُوهِهِمُ النَّارَ وَلاَ عَنْ ظُهُورِهِمْ وَلاَ هُمْ يُنْصَرُونَ
Bal Ta'tīhim Baghtatan Fatabhatuhum Falā Yastaţī`ūna Raddahā Wa Lā Hum Yunžarūna َ021-040 Ã'a, tanã jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba. بَلْ تَأْتِيهِمْ بَغْتَة ً فَتَبْهَتُهُمْ فَلاَ يَسْتَطِيعُونَ رَدَّهَا وَلاَ هُمْ يُنظَرُونَ
Wa Laqadi Astuhzi'a Birusulin Min Qablika Faĥāqa Bial-Ladhīna Sakhirū Minhum Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn َ021-041 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su. وَلَقَدِ اسْتُهْزِئَ بِرُسُل ٍ مِنْ قَبْلِكَ فَحَاقَ بِالَّذِينَ سَخِرُوا مِنْهُمْ مَا كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُون
Qul Man Yakla'uukum Bil-Layli Wa An-Nahāri Mina Ar-Raĥmāni  ۗ  Bal Hum `An Dhikri Rabbihim Mu`rūna َ021-042 Ka ce: "Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" Ã'a, sũ mãsu bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu. قُلْ مَنْ يَكْلَؤُكُمْ بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ مِنَ الرَّحْمَنِ  ۗ  بَلْ هُمْ عَنْ ذِكْرِ رَبِّهِمْ مُعْرِضُونَ
'Am Lahum 'Ālihatun Tamna`uhum Min Dūninā  ۚ  Lā Yastaţī`ūna Naşra 'Anfusihim Wa Lā Hum Minnā Yuşĥabūna َ021-043 Ko kuwa sunã da waɗansu abũbuwan bautãwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bã su iya taimakon kansu kuma ba su kasance anã abũtar su ba daga gareMu. أَمْ لَهُمْ آلِهَة ٌ تَمْنَعُهُمْ مِنْ دُونِنَا  ۚ  لاَ يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَ أَنفُسِهِمْ وَلاَ هُمْ مِنَّا يُصْحَبُونَ
Bal Matta`nā Hā'uulā' Wa 'Ābā'ahum Ĥattá Ţāla `Alayhimu Al-`Umuru  ۗ  'Afalā Yarawna 'Annā Na'tī Al-'Arđa Nanquşuhā Min 'Aţrāfihā  ۚ  'Afahumu Al-Ghālibūna َ021-044 Ã'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a kansu. Shin, to, bã su ganin cẽwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage ta daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya? بَلْ مَتَّعْنَا هَاؤُلاَء وَآبَاءَهُمْ حَتَّى طَالَ عَلَيْهِمُ الْعُمُرُ  ۗ  أَفَلاَ يَرَوْنَ أَنَّا نَأْتِي الأَرْضَ نَنقُصُهَا مِنْ أَطْرَافِهَا  ۚ  أَفَهُمُ الْغَالِبُونَ
Qul 'Innamā 'Undhirukum Bil-Waĥyi  ۚ  Wa Lā Yasma`u Aş-Şummu Ad-Du`ā'a 'Idhā Mā Yundharūna َ021-045 Ka ce: "Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi. قُلْ إِنَّمَا أُنذِرُكُمْ بِالْوَحْيِ  ۚ  وَلاَ يَسْمَعُ الصُّمُّ الدُّعَاءَ إِذَا مَا يُنذَرُونَ
Wa La'in Massat/hum Nafĥatun Min `Adhābi Rabbika Layaqūlunna Yā Waylanā 'Innā Kunnā Žālimīna َ021-046 Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, "Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci." وَلَئِنْ مَسَّتْهُمْ نَفْحَة ٌ مِنْ عَذَابِ رَبِّكَ لَيَقُولُنَّ يَاوَيْلَنَا إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ
Wa Nađa`u Al-Mawāzīna Al-Qisţa Liyawmi Al-Qiyāmati Falā Tužlamu Nafsun Shay'āan  ۖ  Wa 'In Kāna Mithqāla Ĥabbatin Min Khardalin 'Ataynā Bihā  ۗ  Wa Kafá Binā Ĥāsibīna َ021-047 Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi. وَنَضَعُ الْمَوَازِينَ الْقِسْطَ لِيَوْمِ الْقِيَامَةِ فَلاَ تُظْلَمُ نَفْس ٌ شَيْئا ً  ۖ  وَإِنْ كَانَ مِثْقَالَ حَبَّة ٍ مِنْ خَرْدَلٍ أَتَيْنَا بِهَا  ۗ  وَكَفَى بِنَا حَاسِبِينَ
Wa Laqad 'Ātaynā Mūsá Wa Hārūna Al-Furqāna Wa Điyā'an Wa Dhikrāan Lilmuttaqīna َ021-048 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa. وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى وَهَارُونَ الْفُرْقَانَ وَضِيَاء ً وَذِكْرا ً لِلْمُتَّقِينَ
Al-Ladhīna Yakhshawna Rabbahum Bil-Ghaybi Wa Hum Mina As-Sā`ati Mushfiqūna َ021-049 Waɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa'a. الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ بِالْغَيْبِ وَهُمْ مِنَ السَّاعَةِ مُشْفِقُونَ
Wa Hadhā Dhikrun Mubārakun 'Anzalnāhu  ۚ  'Afa'antum Lahu Munkirūna َ021-050 Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi? وَهَذَا ذِكْر ٌ مُبَارَكٌ أَنزَلْنَاهُ~ُ  ۚ  أَفَأَنْتُمْ لَه ُُ مُنكِرُونَ
Wa Laqad 'Ātaynā 'Ibrāhīma Rushdahu Min Qablu Wa Kunnā Bihi `Ālimīna َ021-051 Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi. وَلَقَدْ آتَيْنَا إِبْرَاهِيمَ رُشْدَه ُُ مِنْ قَبْلُ وَكُنَّا بِه ِِ عَالِمِينَ
'Idh Qāla Li'abīhi Wa Qawmihi Mā Hadhihi At-Tamāthīlu Allatī 'Antum Lahā `Ākifūna َ021-052 Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?" إِذْ قَالَ لِأَبِيه ِِ وَقَوْمِه ِِ مَا هَذِهِ التَّمَاثِيلُ الَّتِي أَنْتُمْ لَهَا عَاكِفُونَ
Qālū Wajadnā 'Ābā'anā Lahā `Ābidīna َ021-053 Suka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu." قَالُوا وَجَدْنَا آبَاءَنَا لَهَا عَابِدِينَ
Qāla Laqad Kuntum 'Antum Wa 'Ābā'uukum Fī Đalālin Mubīnin َ021-054 Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna." قَالَ لَقَدْ كُنتُمْ أَنْتُمْ وَآبَاؤُكُمْ فِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ
Qālū 'Aji'tanā Bil-Ĥaqqi 'Am 'Anta Mina Al-Lā`ibīna َ021-055 Suka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãSu wãsã ne?" قَالُوا أَجِئْتَنَا بِالْحَقِّ أَمْ أَنْتَ مِنَ اللاَّعِبِينَ
Qāla Bal Rabbukum Rabbu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Al-Ladhī Faţarahunna Wa 'Anā `Alá Dhālikum Mina Ash-Shāhidīna َ021-056 Ya ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka." قَالَ بَل رَبُّكُمْ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ الَّذِي فَطَرَهُنَّ وَأَنَا عَلَى ذَلِكُمْ مِنَ الشَّاهِدِينَ
Wa Tālllahi La'akīdanna 'Aşnāmakum Ba`da 'An Tuwallū Mudbirīna َ021-057 "Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya." وَتَاللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصْنَامَكُمْ بَعْدَ أَنْ تُوَلُّوا مُدْبِرِينَ
Faja`alahum Judhādhāan 'Illā Kabīrāan Lahum La`allahum 'Ilayhi Yarji`ūna َ021-058 Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi. فَجَعَلَهُمْ جُذَاذا ً إِلاَّ كَبِيرا ً لَهُمْ لَعَلَّهُمْ إِلَيْهِ يَرْجِعُونَ
Qālū Man Fa`ala Hādhā Bi'ālihatinā 'Innahu Lamina Až-Žālimīna َ021-059 Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai." قَالُوا مَنْ فَعَلَ هَذَا بِآلِهَتِنَا إِنَّه ُُ لَمِنَ الظَّالِمِينَ
Qālū Sami`nā Fatáan Yadhkuruhum Yuqālu Lahu 'Ibrāhīmu َ021-060 Suka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm." قَالُوا سَمِعْنَا فَتى ً يَذْكُرُهُمْ يُقَالُ لَهُ~ُ إِبْرَاهِيمُ
Qālū Fa'tū Bihi `Alá 'A`yuni An-Nāsi La`allahum Yash/hadūna َ021-061 Suka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida." قَالُوا فَأْتُوا بِه ِِ عَلَى أَعْيُنِ النَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَشْهَدُونَ
Qālū 'A'anta Fa`alta Hādhā Bi'ālihatinā Yā 'Ibrāhīmu َ021-062 Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!" قَالُوا أَأَنْتَ فَعَلْتَ هَذَا بِآلِهَتِنَا يَاإِبْرَاهِيمُ
Qāla Bal Fa`alahu Kabīruhumdhā Fās'alūhum 'In Kānū Yanţiqūna َ021-063 Ya ce: "Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana." قَالَ بَلْ فَعَلَه ُُ كَبِيرُهُمْ هَذَا فَاسْأَلُوهُمْ إِنْ كَانُوا يَنطِقُونَ
Faraja`ū 'Ilá 'Anfusihim Faqālū 'Innakum 'Antumu Až-Žālimūna َ021-064 Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai." فَرَجَعُوا إِلَى أَنفُسِهِمْ فَقَالُوا إِنَّكُمْ أَنْتُمُ الظَّالِمُونَ
Thumma Nukisū `Alá Ru'ūsihim Laqad `Alimta Mā Hā'uulā' Yanţiqūna َ021-065 Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana." ثُمَّ نُكِسُوا عَلَى رُءُوسِهِمْ لَقَدْ عَلِمْتَ مَا هَاؤُلاَء يَنطِقُونَ
Qāla 'Afata`budūna Min Dūni Al-Lahi Mā Lā Yanfa`ukum Shay'āan Wa Lā Yađurrukum َ021-066 Ya ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?" قَالَ أَفَتَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لاَ يَنفَعُكُمْ شَيْئا ً وَلاَ يَضُرُّكُمْ
'Uffin Lakum Wa Limā Ta`budūna Min Dūni Al-Lahi  ۖ  'Afalā Ta`qilūna َ021-067 "Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?" أُفّ ٍ لَكُمْ وَلِمَا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ  ۖ  أَفَلاَ تَعْقِلُونَ
Qālū Ĥarriqūhu Wa Anşurū 'Ālihatakum 'In Kuntum Fā`ilīna َ021-068 Suka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa." قَالُوا حَرِّقُوه ُُ وَانصُرُوا آلِهَتَكُمْ إِنْ كُنتُمْ فَاعِلِينَ
Qulnā Yā Nāru Kūnī Bardāan Wa Salāmāan `Alá 'Ibrāhīma َ021-069 Muka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm." قُلْنَا يَا نَارُ كُونِي بَرْدا ً وَسَلاَماً عَلَى إِبْرَاهِيمَ
Wa 'Arādū Bihi Kaydāan Faja`alnāhumu Al-'Akhsarīna َ021-070 Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra. وَأَرَادُوا بِه ِِ كَيْدا ً فَجَعَلْنَاهُمُ الأَخْسَرِينَ
Wa Najjaynāhu Wa Lūţāan 'Ilá Al-'Arđi Allatī Bāraknā Fīhā Lil`ālamīna َ021-071 Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai. وَنَجَّيْنَاه ُُ وَلُوطا ً إِلَى الأَرْضِ الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا لِلْعَالَمِينَ
Wa Wahabnā Lahu 'Isĥāqa Wa Ya`qūba Nāfilatan  ۖ  Wa Kullāan Ja`alnā Şāliĥīna َ021-072 Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai. وَوَهَبْنَا لَهُ~ُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ نَافِلَة ً  ۖ  وَكُلاّ ً جَعَلْنَا صَالِحِينَ
Wa Ja`alnāhum 'A'immatan Yahdūna Bi'amrinā Wa 'Awĥaynā 'Ilayhim Fi`la Al-Khayrāti Wa 'Iqāma Aş-Şalāati Wa 'Ītā'a Az-Zakāati  ۖ  Wa Kānū Lanā `Ābidīna َ021-073 Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu. وَجَعَلْنَاهُمْ أَئِمَّة ً يَهْدُونَ بِأَمْرِنَا وَأَوْحَيْنَا إِلَيْهِمْ فِعْلَ الْخَيْرَاتِ وَإِقَامَ الصَّلاَةِ وَإِيتَاءَ الزَّكَاةِ  ۖ  وَكَانُوا لَنَا عَابِدِينَ
Wa Lūţāan 'Ātaynāhu Ĥukmāan Wa `Ilmāan Wa Najjaynāhu Mina Al-Qaryati Allatī Kānat Ta`malu Al-Khabā'itha  ۗ  'Innahum Kānū Qawma Saw'in Fāsiqīna َ021-074 Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai. وَلُوطا ً آتَيْنَاه ُُ حُكْما ً وَعِلْما ً وَنَجَّيْنَاه ُُ مِنَ الْقَرْيَةِ الَّتِي كَانَتْ تَعْمَلُ الْخَبَائِثَ  ۗ  إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمَ سَوْء ٍ فَاسِقِينَ
Wa 'Adkhalnāhu Fī Raĥmatinā  ۖ  'Innahu Mina Aş-Şāliĥīna َ021-075 Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai. وَأَدْخَلْنَاه ُُ فِي رَحْمَتِنَا  ۖ  إِنَّه ُُ مِنَ الصَّالِحِينَ
Wa Nūĥāan 'Idh Nādá Min Qablu Fāstajabnā Lahu Fanajjaynāhu Wa 'Ahlahu Mina Al-Karbi Al-`Ažīmi َ021-076 Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma. وَنُوحا ً إِذْ نَادَى مِنْ قَبْلُ فَاسْتَجَبْنَا لَه ُُ فَنَجَّيْنَاه ُُ وَأَهْلَه ُُ مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ
Wa Naşarnāhu Mina Al-Qawmi Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā  ۚ  'Innahum Kānū Qawma Saw'in Fa'aghraqnāhum 'Ajma`īna َ021-077 Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya. وَنَصَرْنَاه ُُ مِنَ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا  ۚ  إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمَ سَوْء ٍ فَأَغْرَقْنَاهُمْ أَجْمَعِينَ
Wa Dāwūda Wa Sulaymāna 'Idh Yaĥkumāni Fī Al-Ĥarthi 'Idh Nafashat Fīhi Ghanamu Al-Qawmi Wa Kunnā Liĥukmihim Shāhidīna َ021-078 Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu. وَدَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ إِذْ يَحْكُمَانِ فِي الْحَرْثِ إِذْ نَفَشَتْ فِيه ِِ غَنَمُ الْقَوْمِ وَكُنَّا لِحُكْمِهِمْ شَاهِدِينَ
Fafahhamnāhā Sulaymāna  ۚ  Wa Kullāan 'Ātaynā Ĥukmāan Wa `Ilmāan  ۚ  Wa Sakhkharnā Ma`a Dāwūda Al-Jibāla Yusabbiĥna Wa Aţ-Ţayra  ۚ  Wa Kunnā Fā`ilīna َ021-079 Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa. فَفَهَّمْنَاهَا سُلَيْمَانَ  ۚ  وَكُلاّ ً آتَيْنَا حُكْما ً وَعِلْما ً  ۚ  وَسَخَّرْنَا مَعَ دَاوُودَ الْجِبَالَ يُسَبِّحْنَ وَالطَّيْرَ  ۚ  وَكُنَّا فَاعِلِينَ
Wa `Allamnāhu Şan`ata Labūsin Lakum Lituĥşinakum Min Ba'sikum  ۖ  Fahal 'Antum Shākirūna َ021-080 Kuma Muka sanar da shi sana'ar wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne? وَعَلَّمْنَاه ُُ صَنْعَةَ لَبُوس ٍ لَكُمْ لِتُحْصِنَكُمْ مِنْ بَأْسِكُمْ  ۖ  فَهَلْ أَنْتُمْ شَاكِرُونَ
Wa Lisulaymāna Ar-Rīĥa `Āşifatan Tajrī Bi'amrihi 'Ilá Al-'Arđi Allatī Bāraknā Fīhā  ۚ  Wa Kunnā Bikulli Shay'in `Ālimīna َ021-081 Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme. وَلِسُلَيْمَانَ الرِّيحَ عَاصِفَة ً تَجْرِي بِأَمْرِهِ~ِ إِلَى الأَرْضِ الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا  ۚ  وَكُنَّا بِكُلِّ شَيْءٍ عَالِمِينَ
Wa Mina Ash-Shayāţīni Man Yaghūşūna Lahu Wa Ya`malūna `Amalāan Dūna Dhālika  ۖ  Wa Kunnā Lahum Ĥāfižīna َ021-082 Kuma daga Shaiɗannu (Mun hõre) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su. وَمِنَ الشَّيَاطِينِ مَنْ يَغُوصُونَ لَه ُُ وَيَعْمَلُونَ عَمَلا ً دُونَ ذَلِكَ  ۖ  وَكُنَّا لَهُمْ حَافِظِينَ
Wa 'Ayyūba 'Idh Nādá Rabbahu 'Annī Massanī Ađ-Đurru Wa 'Anta 'Arĥamu Ar-Rāĥimīna َ021-083 Kuma da Ayyũba a sã'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama." وَأَيُّوبَ إِذْ نَادَى رَبَّهُ~ُ أَنِّي مَسَّنِي الضُّرُّ وَأَنْتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ
Fāstajabnā Lahu Fakashafnā Mā Bihi Min Đurrin  ۖ  Wa 'Ātaynāhu 'Ahlahu Wa Mithlahum Ma`ahum Raĥmatan Min `Indinā Wa Dhikrá Lil`ābidīna َ021-084 Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunãtarwa ga mãsu ibãda. فَاسْتَجَبْنَا لَه ُُ فَكَشَفْنَا مَا بِه ِِ مِنْ ضُرّ ٍ  ۖ  وَآتَيْنَاهُ~ُ أَهْلَه ُُ وَمِثْلَهُمْ مَعَهُمْ رَحْمَة ً مِنْ عِنْدِنَا وَذِكْرَى لِلْعَابِدِينَ
Wa 'Ismā`īla Wa 'Idrīsa Wa Dhā Al-Kifli  ۖ  Kullun Mina Aş-Şābirīna َ021-085 Kuma da Ismãĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sunã daga mãsu haƙuri. وَإِسْمَاعِيلَ وَإِدْرِيسَ وَذَا الْكِفْلِ  ۖ  كُلّ ٌ مِنَ الصَّابِرِينَ
Wa 'Adkhalnāhum Fī Raĥmatinā  ۖ  'Innahum Mina Aş-Şāliĥīna َ021-086 Kuma Muka shigar da su a cikin rahamarMu. Lalle ne, sunã daga sãlihai. وَأَدْخَلْنَاهُمْ فِي رَحْمَتِنَا  ۖ  إِنَّهُمْ مِنَ الصَّالِحِينَ
Wa Dhā An-Nūni 'Idh Dhahaba Mughāđibāan Fažanna 'An Lan Naqdira `Alayhi Fanādá Fī Až-Žulumāti 'An Lā 'Ilāha 'Illā 'Anta Subĥānaka 'Innī Kuntu Mina Až-Žālimīna َ021-087 Kuma mai kifi a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai." وَذَا النُّونِ إِذْ ذَهَبَ مُغَاضِبا ً فَظَنَّ أَنْ لَنْ نَقْدِرَ عَلَيْهِ فَنَادَى فِي الظُّلُمَاتِ أَنْ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ الظَّالِمِينَ
Fāstajabnā Lahu Wa Najjaynāhu Mina Al-Ghammi  ۚ  Wa Kadhalika Nun Al-Mu'uminīna َ021-088 Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni. فَاسْتَجَبْنَا لَه ُُ وَنَجَّيْنَاه ُُ مِنَ الْغَمِّ  ۚ  وَكَذَلِكَ نُنْجِي الْمُؤْمِنِينَ
Wa Zakarīyā 'Idh Nādá Rabbahu Rabbi Lā Tadharnī Fardāan Wa 'Anta Khayru Al-Wārithīna َ021-089 Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo." وَزَكَرِيَّا إِذْ نَادَى رَبَّه ُُ رَبِّ لاَ تَذَرْنِي فَرْدا ً وَأَنْتَ خَيْرُ الْوَارِثِينَ
Fāstajabnā Lahu Wa Wahabnā Lahu Yaĥyá Wa 'Aşlaĥnā Lahu Zawjahu  ۚ  'Innahum Kānū Yusāri`ūna Fī Al-Khayrāti Wa Yad`ūnanā Raghabāan Wa Rahabāan  ۖ  Wa Kānū Lanā Khāshi`īna َ021-090 Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu. فَاسْتَجَبْنَا لَه ُُ وَوَهَبْنَا لَه ُُ يَحْيَى وَأَصْلَحْنَا لَه ُُ زَوْجَهُ~ُ  ۚ  إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبا ً وَرَهَبا ً  ۖ  وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ
Wa A-Atī 'Aĥşanat Farjahā Fanafakhnā Fīhā Min Rūĥinā Wa Ja`alnāhā Wa Abnahā 'Āyatan Lil`ālamīna َ021-091 Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu. Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya. وَالَّتِي أَحْصَنَتْ فَرْجَهَا فَنَفَخْنَا فِيهَا مِنْ رُوحِنَا وَجَعَلْنَاهَا وَابْنَهَا آيَة ً لِلْعَالَمِينَ
'Inna Hadhihi 'Ummatukum 'Ummatan Wāĥidatan Wa 'Anā Rabbukum Fā`budūni َ021-092 Lalle ne wannan ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini. إِنَّ هَذِهِ~ِ أُمَّتُكُمْ أُمَّة ً وَاحِدَة ً وَأَنَا رَبُّكُمْ فَاعْبُدُونِ
Wa Taqaţţa`ū 'Amrahum Baynahum  ۖ  Kullun 'Ilaynā Rāji`ūna َ021-093 Kuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni وَتَقَطَّعُوا أَمْرَهُمْ بَيْنَهُمْ  ۖ  كُلّ ٌ إِلَيْنَا رَاجِعُونَ
Faman Ya`mal Mina Aş-Şāliĥāti Wa Huwa Mu'uminun Falā Kufrāna Lisa`yihi Wa 'Innā Lahu Kātibūna َ021-094 Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne. فَمَنْ يَعْمَلْ مِنَ الصَّالِحَاتِ وَهُوَ مُؤْمِن ٌ فَلاَ كُفْرَانَ لِسَعْيِه ِِ وَإِنَّا لَه ُُ كَاتِبُونَ
Wa Ĥarāmun `Alá Qaryatin 'Ahlaknāhā 'Annahum Lā Yarji`ūna َ021-095 Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa. وَحَرَامٌ عَلَى قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا أَنَّهُمْ لاَ يَرْجِعُونَ
Ĥattá 'Idhā Futiĥat Ya'jūju Wa Ma'jūju Wa Hum Min Kulli Ĥadabin Yansilūna َ021-096 Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa. حَتَّى إِذَا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ وَهُمْ مِنْ كُلِّ حَدَب ٍ يَنسِلُونَ
qtaraba Al-Wa`du Al-Ĥaqqu Fa'idhā Hiya Shākhişatun 'Abşāru Al-Ladhīna Kafarū Yā Waylanā Qad Kunnā Fī Ghaflatin Min Hādhā Bal Kunnā Žālimīna َ021-097 Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!" وَاقْتَرَبَ الْوَعْدُ الْحَقُّ فَإِذَا هِيَ شَاخِصَةٌ أَبْصَارُ الَّذِينَ كَفَرُوا يَاوَيْلَنَا قَدْ كُنَّا فِي غَفْلَة ٍ مِنْ هَذَا بَلْ كُنَّا ظَالِمِينَ
'Innakum Wa Mā Ta`budūna Min Dūni Al-Lahi Ĥaşabu Jahannama 'Antum Lahā Wa Aridūna َ021-098 (A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne." إِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنْتُمْ لَهَا وَارِدُونَ
Law Kāna Hā'uulā' 'Ālihatan Mā Waradūhā  ۖ  Wa Kullun Fīhā Khālidūna َ021-099 Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne. لَوْ كَانَ هَاؤُلاَء آلِهَة ً مَا وَرَدُوهَا  ۖ  وَكُلّ ٌ فِيهَا خَالِدُونَ
Lahum Fīhā Zafīrun Wa Hum Fīhā Lā Yasma`ūna َ021-100 Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme. لَهُمْ فِيهَا زَفِير ٌ وَهُمْ فِيهَا لاَ يَسْمَعُونَ
'Inna Al-Ladhīna Sabaqat Lahum Minnā Al-Ĥusná 'Ūlā'ika `Anhā Mub`adūna َ021-101 Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne. إِنَّ الَّذِينَ سَبَقَتْ لَهُمْ مِنَّا الْحُسْنَى أُوْلَائِكَ عَنْهَا مُبْعَدُونَ
Lā Yasma`ūna Ĥasīsahā  ۖ  Wa Hum Fī Mā Ashtahat 'Anfusuhum Khālidūna َ021-102 Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa. لاَ يَسْمَعُونَ حَسِيسَهَا  ۖ  وَهُمْ فِي مَا اشْتَهَتْ أَنفُسُهُمْ خَالِدُونَ
Lā Yaĥzunuhumu Al-Faza`u Al-'Akbaru Wa Tatalaqqāhumu Al-Malā'ikatu Hādhā Yawmukumu Al-Ladhī Kuntum Tū`adūna َ021-103 Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) "Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi." لاَ يَحْزُنُهُمُ الْفَزَعُ الأَكْبَرُ وَتَتَلَقَّاهُمُ الْمَلاَئِكَةُ هَذَا يَوْمُكُمُ الَّذِي كُنتُمْ تُوعَدُونَ
Yawma Naţ As-Samā'a Kaţayyi As-Sijilli Lilkutubi  ۚ  Kamā Bada'nā 'Awwala Khalqin Nu`īduhu  ۚ  Wa`dāan `Alaynā  ۚ  'Innā Kunnā Fā`ilīna َ021-104 A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa. يَوْمَ نَطْوِي السَّمَاءَ كَطَيِّ السِّجِلِّ لِلْكُتُبِ  ۚ  كَمَا بَدَأْنَا أَوَّلَ خَلْق ٍ نُعِيدُه ُُ  ۚ  وَعْداً عَلَيْنَا  ۚ  إِنَّا كُنَّا فَاعِلِينَ
Wa Laqad Katabnā Fī Az-Zabūri Min Ba`di Adh-Dhikri 'Anna Al-'Arđa Yarithuhā `Ibādiya Aş-Şāliĥūna َ021-105 Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩNa sãlihai, sunã gãdonta. وَلَقَدْ كَتَبْنَا فِي الزَّبُورِ مِنْ بَعْدِ الذِّكْرِ أَنَّ الأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ الصَّالِحُونَ
'Inna Fī Hādhā Labalāghāan Liqawmin `Ābidīna َ021-106 Lalle ne a cikin wannan (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta ga waɗansu mutãne mãsu ibãda. إِنَّ فِي هَذَا لَبَلاَغا ً لِقَوْمٍ عَابِدِينَ
Wa Mā 'Arsalnāka 'Illā Raĥmatan Lil`ālamīna َ021-107 Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai. وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلاَّ رَحْمَة ً لِلْعَالَمِينَ
Qul 'Innamā Yūĥá 'Ilayya 'Annamā 'Ilahukum 'Ilahun Wāĥidun  ۖ  Fahal 'Antum Muslimūna َ021-108 Ka ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne?" قُلْ إِنَّمَا يُوحَى إِلَيَّ أَنَّمَا إِلَهُكُمْ إِلَه ٌ ٌ وَاحِد ٌ  ۖ  فَهَلْ أَنْتُمْ مُسْلِمُونَ
Fa'in Tawallaw Faqul 'Ādhantukum `Alá Sawā'in  ۖ  Wa 'In 'Adrī 'Aqarībun 'Am Ba`īdun Mā Tū`adūna َ021-109 Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci?" فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُلْ آذَنْتُكُمْ عَلَى سَوَاء ٍ  ۖ  وَإِنْ أَدْرِي أَقَرِيبٌ أَمْ بَعِيد ٌ مَا تُوعَدُونَ
'Innahu Ya`lamu Al-Jahra Mina Al-Qawli Wa Ya`lamu Mā Taktumūna َ021-110 "Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa. إِنَّه ُُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ مِنَ الْقَوْلِ وَيَعْلَمُ مَا تَكْتُمُونَ
Wa 'In 'Adrī La`allahu Fitnatun Lakum Wa Matā`un 'Ilá Ĥīnin َ021-111 "Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci." وَإِنْ أَدْرِي لَعَلَّه ُُ فِتْنَة ٌ لَكُمْ وَمَتَاع ٌ إِلَى حِين ٍ
Qāla Rabbi Aĥkum Bil-Ĥaqqi  ۗ  Wa Rabbunā Ar-Raĥmānu Al-Musta`ānu `Alá Mā Taşifūna َ021-112 Ya ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa." قَالَ رَبِّ احْكُمْ بِالْحَقِّ  ۗ  وَرَبُّنَا الرَّحْمَنُ الْمُسْتَعَانُ عَلَى مَا تَصِفُونَ
Next Sūrah