20) Sūrat Ţāhā

Printed format

20) سُورَة طَاهَا

Ţāhā َ020-001 ¦. H. طَاهَا
Mā 'Anzalnā `Alayka Al-Qur'āna Litash َ020-002 Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba. مَا أَنْزَلْنَا عَلَيْكَ الْقُرْآنَ لِتَشْقَى
'Illā Tadhkiratan Liman Yakhshá َ020-003 Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah. إِلاَّ تَذْكِرَة ً لِمَنْ يَخْشَى
Tanzīlāan Mimman Khalaqa Al-'Arđa Wa As-Samāwāti Al-`Ulā َ020-004 (An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka. تَنزِيلا ً مِمَّنْ خَلَقَ الأَرْضَ وَالسَّمَاوَاتِ الْعُلاَ
Ar-Raĥmānu `Alá Al-`Arshi Astawá َ020-005 Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'arshi. الرَّحْمَنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى
Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā Wa Mā Taĥta Ath-Thará َ020-006 Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya. لَه ُُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَمَا تَحْتَ الثَّرَى
Wa 'In Tajhar Bil-Qawli Fa'innahu Ya`lamu As-Sirra Wa 'Akh َ020-007 Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa. وَإِنْ تَجْهَرْ بِالْقَوْلِ فَإِنَّه ُُ يَعْلَمُ السِّرَّ وَأَخْفَى
Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  Lahu Al-'Asmā'u Al-Ĥusná َ020-008 Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau. اللَّهُ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ  ۖ  لَهُ الأَسْمَاءُ الْحُسْنَى
Wa Hal 'Atāka Ĥadīthu Mūsá َ020-009 Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka? وَهَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَى
'Idh Ra'á Nārāan Faqāla Li'hlihi Amkuthū 'Innī 'Ānastu Nārāan La`allī 'Ātīkum Minhā Biqabasin 'Aw 'Ajidu `Alá An-Nāri Hudáan َ020-010 A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar." إِذْ رَأَى نَارا ً فَقَالَ لِأهْلِهِ امْكُثُوا إِنِّي آنَسْتُ نَارا ً لَعَلِّي آتِيكُمْ مِنْهَا بِقَبَسٍ أَوْ أَجِدُ عَلَى النَّارِ هُدى ً
Falammā 'Atāhā Nūdī Yā Mūsá َ020-011 Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!" فَلَمَّا أَتَاهَا نُودِي يَامُوسَى
'Innī 'Anā Rabbuka Fākhla` Na`layka  ۖ  'Innaka Bil-Wādi Al-Muqaddasi Ţūáan َ020-012 "Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa." إِنِّي أَنَا رَبُّكَ فَاخْلَعْ نَعْلَيْكَ  ۖ  إِنَّكَ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوى ً
Wa 'Anā Akhtartuka Fāstami` Limā Yūĥá َ020-013 "Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi." وَأَنَا اخْتَرْتُكَ فَاسْتَمِعْ لِمَا يُوحَى
'Innanī 'Anā Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā 'Anā Fā`budnī Wa 'Aqimi Aş-Şalāata Lidhikrī َ020-014 "Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni." إِنَّنِي أَنَا اللَّهُ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ أَنَا فَاعْبُدْنِي وَأَقِمِ الصَّلاَةَ لِذِكْرِي
'Inna As-Sā`ata 'Ātiyatun 'Akādu 'Ukhfīhā Litujzá Kullu Nafsin Bimā Tas`á َ020-015 "Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa." إِنَّ السَّاعَةَ آتِيَةٌ أَكَادُ أُخْفِيهَا لِتُجْزَى كُلُّ نَفْس ٍ بِمَا تَسْعَى
Falā Yaşuddannaka `Anhā Man Lā Yu'uminu Bihā Wa Attaba`a Hawāhu Fatardá َ020-016 "Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka." فَلاَ يَصُدَّنَّكَ عَنْهَا مَنْ لاَ يُؤْمِنُ بِهَا وَاتَّبَعَ هَوَاه ُُ فَتَرْدَى
Wa Mā Tilka Biyamīnika Yā Mūsá َ020-017 "Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!" وَمَا تِلْكَ بِيَمِينِكَ يَامُوسَى
Qāla Hiya `Aşāya 'Atawakka'u `Alayhā Wa 'Ahushshu Bihā `Alá Ghanamī Wa Liya Fīhā Ma'āribu 'Ukh َ020-018 Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci na dabam a gare ta." قَالَ هِيَ عَصَايَ أَتَوَكَّأُ عَلَيْهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَى غَنَمِي وَلِيَ فِيهَا مَآرِبُ أُخْرَى
Qāla 'Alqihā Yā Mūsá َ020-019 Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!" قَالَ أَلْقِهَا يَامُوسَى
Fa'alqāhā Fa'idhā Hiya Ĥayyatun Tas`á َ020-020 Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa. فَأَلْقَاهَا فَإِذَا هِيَ حَيَّة ٌ تَسْعَى
Qāla Khudh/hā Wa Lā Takhaf  ۖ  Sanu`īduhā Sīratahā Al-'Ū َ020-021 Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko." قَالَ خُذْهَا وَلاَ تَخَفْ  ۖ  سَنُعِيدُهَا سِيرَتَهَا الأُولَى
Wa Ađmum Yadaka 'Ilá Janāĥika Takhruj Bayđā'a Min Ghayri Sū'in 'Āyatan 'Ukh َ020-022 "Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam." وَاضْمُمْ يَدَكَ إِلَى جَنَاحِكَ تَخْرُجْ بَيْضَاءَ مِنْ غَيْرِ سُوء ٍ آيَةً أُخْرَى
Linuriyaka Min 'Āyātinā Al-Kub َ020-023 "Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya." لِنُرِيَكَ مِنْ آيَاتِنَا الْكُبْرَى
Adh/hab 'Ilá Fir`awna 'Innahu Ţaghá َ020-024 "Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)." اذْهَبْ إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّه ُُ طَغَى
Qāla Rabbi Ashraĥ Lī Şadrī َ020-025 Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa mini, ƙirjĩna. قَالَ رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي
Wa Yassir Lī 'Amrī َ020-026 "Kuma ka sauƙaƙe mini al'amarĩna." وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي
Wa Aĥlul `Uqdatan Min Lisānī َ020-027 "Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna." وَاحْلُلْ عُقْدَة ً مِنْ لِسَانِي
Yafqahū Qawlī َ020-028 "Su fahimci maganãta." يَفْقَهُوا قَوْلِي
Wa Aj`al Lī Wazīrāan Min 'Ahlī َ020-029 "Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena." وَاجْعَلْ لِي وَزِيرا ً مِنْ أَهْلِي
Hārūna 'Akhī َ020-030 "Hãrũna ɗan'uwana." هَارُونَ أَخِي
Ashdud Bihi 'Azrī َ020-031 "Ka ƙarfafa halittata da shi." اشْدُدْ بِهِ~ِ أَزْرِي
Wa 'Ashrik/hu Fī 'Amrī َ020-032 "Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina." وَأَشْرِكْهُ فِي أَمْرِي
Kay Nusabbiĥaka Kathīrāan َ020-033 "Dõmin mu tsarkake Ka da yawa." كَيْ نُسَبِّحَكَ كَثِيرا ً
Wa Nadhkuraka Kathīrāan َ020-034 "Kuma mu tuna Ka da yawa." وَنَذْكُرَكَ كَثِيرا ً
'Innaka Kunta Binā Başīrāan َ020-035 "Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu." إِنَّكَ كُنْتَ بِنَا بَصِيرا ً
Qāla Qad 'Ūtīta Su'ulaka Yā Mūsá َ020-036 Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!" قَالَ قَدْ أُوتِيتَ سُؤْلَكَ يَامُوسَى
Wa Laqad Manannā `Alayka Marratan 'Ukh َ020-037 "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam." وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَيْكَ مَرَّةً أُخْرَى
'Idh 'Awĥaynā 'Ilá 'Ummika Mā Yūĥá َ020-038 "A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka." إِذْ أَوْحَيْنَا إِلَى أُمِّكَ مَا يُوحَى
'Ani Aqdhifīhi Fī At-Tābūti Fāqdhifīhi Fī Al-Yammi Falyulqihi Al-Yammu Bis-Sāĥili Ya'khudh/hu `Adūwun Lī Wa`adūwun Lahu  ۚ  Wa 'Alqaytu `Alayka Maĥabbatan Minnī Wa Lituşna`a `Alá `Ayni َ020-039 "Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan ganiNa." أَنِ اقْذِفِيه ِِ فِي التَّابُوتِ فَاقْذِفِيه ِِ فِي الْيَمِّ فَلْيُلْقِهِ الْيَمُّ بِالسَّاحِلِ يَأْخُذْهُ عَدُوّ ٌ لِي وَعَدُوّ ٌ لَه ُُ  ۚ  وَأَلْقَيْتُ عَلَيْكَ مَحَبَّة ً مِنِّي وَلِتُصْنَعَ عَلَى عَيْنِ
'Idh Tamshī 'Ukhtuka Fataqūlu Hal 'Adullukum `Alá Man Yakfuluhu  ۖ  Faraja`nāka 'Ilá 'Ummika Kay Taqarra `Aynuhā Wa Lā Taĥzana  ۚ  Wa Qatalta Nafsāan Fanajjaynāka Mina Al-Ghammi Wa Fatannāka Futūnāan  ۚ  Falabithta Sinīna Fī 'Ahli Madyana Thumma Ji'ta `Alá Qadarin Yā Mūsá َ020-040 "A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã! إِذْ تَمْشِي أُخْتُكَ فَتَقُولُ هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَى مَنْ يَكْفُلُه ُُ  ۖ  فَرَجَعْنَاكَ إِلَى أُمِّكَ كَيْ تَقَرَّ عَيْنُهَا وَلاَ تَحْزَنَ  ۚ  وَقَتَلْتَ نَفْسا ً فَنَجَّيْنَاكَ مِنَ الْغَمِّ وَفَتَنَّاكَ فُتُونا ً  ۚ  فَلَبِثْتَ سِنِينَ فِي أَهْلِ مَدْيَنَ ثُمَّ جِئْتَ عَلَى قَدَر ٍ يَامُوسَى
Wa Aşţana`tuka Linafsī َ020-041 "Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina." وَاصْطَنَعْتُكَ لِنَفْسِي
Adh/hab 'Anta Wa 'Akhūka Bi'āyātī Wa Lā Taniyā Fī Dhikrī َ020-042 "Ka tafi kai da ɗan'uwanka game da ãyõyiNa, kuma kada ku yi rauni ga ambatõNa." اذْهَبْ أَنْتَ وَأَخُوكَ بِآيَاتِي وَلاَ تَنِيَا فِي ذِكْرِي
Adh/habā 'Ilá Fir`awna 'Innahu Ţaghá َ020-043 "Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai)." اذْهَبَا إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّه ُُ طَغَى
Faqūlā Lahu Qawlāan Layyināan La`allahu Yatadhakkaru 'Aw Yakhshá َ020-044 "Sai ku gaya masa magana mai laushi, tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji tsõro." فَقُولاَ لَه ُُ قَوْلا ً لَيِّنا ً لَعَلَّه ُُ يَتَذَكَّرُ أَوْ يَخْشَى
Qālā Rabbanā 'Innanā Nakhāfu 'An Yafruţa `Alaynā 'Aw 'An Yaţghá َ020-045 Su biyu suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne munã tsõron ya yi gaggawa a kanmu, kõ ya ƙẽtare haddi." قَالاَ رَبَّنَا إِنَّنَا نَخَافُ أَنْ يَفْرُطَ عَلَيْنَا أَوْ أَنْ يَطْغَى
Qāla Lā Takhāfā  ۖ  'Innanī Ma`akumā 'Asma`u Wa 'Ará َ020-046 Ya ce: "Kada ku ji tsõro. Lalle Nĩ, Inã tãre da ku, Inaji, kuma Inã gani." قَالَ لاَ تَخَافَا  ۖ  إِنَّنِي مَعَكُمَا أَسْمَعُ وَأَرَى
Fa'tiyāhu Faqūlā 'Innā Rasūlā Rabbika Fa'arsil Ma`anā Banī 'Isrā'īla Wa Lā Tu`adhdhibhum  ۖ  Qad Ji'nāka Bi'āyatin Min Rabbika Wa  ۖ  As-Salāmu `Alá Mani Attaba`a Al-Hudá َ020-047 "Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya." فَأْتِيَاه ُُ فَقُولاَ إِنَّا رَسُولاَ رَبِّكَ فَأَرْسِلْ مَعَنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ وَلاَ تُعَذِّبْهُمْ  ۖ  قَدْ جِئْنَاكَ بِآيَة ٍ مِنْ رَبِّكَ  ۖ  وَالسَّلاَمُ عَلَى مَنِ اتَّبَعَ الْهُدَى
'Innā Qad 'Ūĥiya 'Ilaynā 'Anna Al-`Adhāba `Alá Man Kadhdhaba Wa Tawallá َ020-048 "Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwaazãba tanã a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya." إِنَّا قَدْ أُوحِيَ إِلَيْنَا أَنَّ الْعَذَابَ عَلَى مَنْ كَذَّبَ وَتَوَلَّى
Qāla Faman Rabbukumā Yā Mūsá َ020-049 Ya ce: "To, wãne ne Ubangijinku? Ya Mũsã!" قَالَ فَمَنْ رَبُّكُمَا يَامُوسَى
Qāla Rabbunā Al-Ladhī 'A`ţá Kulla Shay'in Khalqahu Thumma Hadá َ020-050 Ya ce: "Ubangijinmu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kõme halittarsa, sa'an nan Ya shiryar." قَالَ رَبُّنَا الَّذِي أَعْطَى كُلَّ شَيْءٍ خَلْقَه ُُ ثُمَّ هَدَى
Qāla Famā Bālu Al-Qurūni Al-'Ū َ020-051 Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko?" قَالَ فَمَا بَالُ الْقُرُونِ الأُولَى
Qāla `Ilmuhā `Inda Rabbī Fī Kitābin  ۖ  Lā Yađillu Rabbī Wa Lā Yan َ020-052 Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa." قَالَ عِلْمُهَا عِنْدَ رَبِّي فِي كِتَاب ٍ  ۖ  لاَ يَضِلُّ رَبِّي وَلاَ يَنسَى
Al-Ladhī Ja`ala Lakumu Al-'Arđa Mahdāan Wa Salaka Lakum Fīhā Subulāan Wa 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an Fa'akhrajnā Bihi 'Azwājāan Min Nabātin Shattá َ020-053 "Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam. الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأَرْضَ مَهْدا ً وَسَلَكَ لَكُمْ فِيهَا سُبُلا ً وَأَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَأَخْرَجْنَا بِهِ~ِ أَزْوَاجا ً مِنْ نَبَات ٍ شَتَّى
Kulū Wa Ar`aw 'An`āmakum  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Li'wlī An-Nuhá َ020-054 Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali. كُلُوا وَارْعَوْا أَنْعَامَكُمْ  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِأوْلِي النُّهَى
Minhā Khalaqnākum Wa Fīhā Nu`īdukum Wa Minhā Nukhrijukum Tāratan 'Ukh َ020-055 Daga gare ta Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam. مِنْهَا خَلَقْنَاكُمْ وَفِيهَا نُعِيدُكُمْ وَمِنْهَا نُخْرِجُكُمْ تَارَةً أُخْرَى
Wa Laqad 'Araynāhu 'Āyātinā Kullahā Fakadhdhaba Wa 'Abá َ020-056 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya! وَلَقَدْ أَرَيْنَاهُ آيَاتِنَا كُلَّهَا فَكَذَّبَ وَأَبَى
Qāla 'Aji'tanā Litukhrijanā Min 'Arđinā Bisiĥrika Yā Mūsá َ020-057 Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã?" قَالَ أَجِئْتَنَا لِتُخْرِجَنَا مِنْ أَرْضِنَا بِسِحْرِكَ يَامُوسَى
Falana'tiyannaka Bisiĥrin Mithlihi Fāj`al Baynanā Wa Baynaka Maw`idāan Lā Nukhlifuhu Naĥnu Wa Lā 'Anta Makānāan Sūáan َ020-058 "To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa." فَلَنَأْتِيَنَّكَ بِسِحْر ٍ مِثْلِه ِِ فَاجْعَلْ بَيْنَنَا وَبَيْنَكَ مَوْعِدا ً لاَ نُخْلِفُه ُُ نَحْنُ وَلاَ أَنْتَ مَكَانا ً سُوى ً
Qāla Maw`idukum Yawmu Az-Zīnati Wa 'An Yuĥshara An-Nāsu Đuĥáan َ020-059 Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi." قَالَ مَوْعِدُكُمْ يَوْمُ الزِّينَةِ وَأَنْ يُحْشَرَ النَّاسُ ضُحى ً
Fatawallá Fir`awnu Fajama`a Kaydahu Thumma 'Atá َ020-060 Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo. فَتَوَلَّى فِرْعَوْنُ فَجَمَعَ كَيْدَه ُُ ثُمَّ أَتَى
Qāla Lahum Mūsá Waylakum Lā Taftarū `Alá Al-Lahi Kadhibāan Fayusĥitakum Bi`adhābin  ۖ  Wa Qad Khāba Mani Aftará َ020-061 Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe." قَالَ لَهُمْ مُوسَى وَيْلَكُمْ لاَ تَفْتَرُوا عَلَى اللَّهِ كَذِبا ً فَيُسْحِتَكُمْ بِعَذَاب ٍ  ۖ  وَقَدْ خَابَ مَنِ افْتَرَى
Fatanāza`ū 'Amrahum Baynahum Wa 'Asarrū An-Naj َ020-062 Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãninsu kuma suka asirta gãnawa. فَتَنَازَعُوا أَمْرَهُمْ بَيْنَهُمْ وَأَسَرُّوا النَّجْوَى
Qālū 'In Hadhāni Lasāĥirāni Yurīdāni 'An Yukhrijākum Min 'Arđikum Bisiĥrihimā Wa Yadh/habā Biţarīqatikumu Al-Muth َ020-063 Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya." قَالُوا إِنْ هَذَانِ لَسَاحِرَانِ يُرِيدَانِ أَنْ يُخْرِجَاكُمْ مِنْ أَرْضِكُمْ بِسِحْرِهِمَا وَيَذْهَبَا بِطَرِيقَتِكُمُ الْمُثْلَى
Fa'ajmi`ū Kaydakum Thumma A'tū Şaffāan  ۚ  Wa Qad 'Aflaĥa Al-Yawma Mani Asta`lá َ020-064 "Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta." فَأَجْمِعُوا كَيْدَكُمْ ثُمَّ ائْتُوا صَفّا ً  ۚ  وَقَدْ أَفْلَحَ الْيَوْمَ مَنِ اسْتَعْلَى
Qālū Yā Mūsá 'Immā 'An Tulqiya Wa 'Immā 'An Nakūna 'Awwala Man 'Alqá َ020-065 Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa." قَالُوا يَامُوسَى إِمَّا أَنْ تُلْقِيَ وَإِمَّا أَنْ نَكُونَ أَوَّلَ مَنْ أَلْقَى
Qāla Bal 'Alqū  ۖ  Fa'idhā Ĥibāluhum Wa `Işīyuhum Yukhayyalu 'Ilayhi Min Siĥrihim 'Annahā Tas`á َ020-066 Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri. قَالَ بَلْ أَلْقُوا  ۖ  فَإِذَا حِبَالُهُمْ وَعِصِيُّهُمْ يُخَيَّلُ إِلَيْهِ مِنْ سِحْرِهِمْ أَنَّهَا تَسْعَى
Fa'awjasa Fī Nafsihi Khīfatan Mūsá َ020-067 Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa. فَأَوْجَسَ فِي نَفْسِه ِِ خِيفَة ً مُوسَى
Qulnā Lā Takhaf 'Innaka 'Anta Al-'A`lá َ020-068 Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka." قُلْنَا لاَ تَخَفْ إِنَّكَ أَنْتَ الأَعْلَى
Wa 'Alqi Mā Fī Yamīnika Talqaf Mā Şana`ū  ۖ  'Innamā Şana`ū Kaydu Sāĥirin  ۖ  Wa Lā Yufliĥu As-Sāĥiru Ĥaythu 'Atá َ020-069 "Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je." وَأَلْقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلْقَفْ مَا صَنَعُوا  ۖ  إِنَّمَا صَنَعُوا كَيْدُ سَاحِر ٍ  ۖ  وَلاَ يُفْلِحُ السَّاحِرُ حَيْثُ أَتَى
Fa'ulqiya As-Saĥaratu Sujjadāan Qālū 'Āmannā Birabbi Hārūna Wa Mūsá َ020-070 Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin Hãrũna da Mũsã." فَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سُجَّدا ً قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ هَارُونَ وَمُوسَى
Qāla 'Āmantum Lahu Qabla 'An 'Ādhana Lakum  ۖ  'Innahu Lakabīrukumu Al-Ladhī `Allamakumu As-Siĥra  ۖ  Fala'uqaţţi`anna 'Aydiyakum Wa 'Arjulakum Min Khilāfin Wa La'uşallibannakum Fī Judhū`i An-Nakhli Wa Lata`lamunna 'Ayyunā 'Ashaddu `Adhābāan Wa 'Ab َ020-071 Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno, kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar (azãba)." قَالَ آمَنْتُمْ لَه ُُ قَبْلَ أَنْ آذَنَ لَكُمْ  ۖ  إِنَّه ُُ لَكَبِيرُكُمُ الَّذِي عَلَّمَكُمُ السِّحْرَ  ۖ  فَلَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ مِنْ خِلاَف ٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ فِي جُذُوعِ النَّخْلِ وَلَتَعْلَمُنَّ أَيُّنَا أَشَدُّ عَذَابا ً وَأَبْقَى
Qālū Lan Nu'uthiraka `Alá Mā Jā'anā Mina Al-Bayyināti Wa Al-Ladhī Faţaranā  ۖ  Fāqđi Mā 'Anta Qāđin  ۖ  'Innamā Taqđī Hadhihi Al-Ĥayāata Ad-Dun َ020-072 Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa, ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne." قَالُوا لَنْ نُؤْثِرَكَ عَلَى مَا جَاءَنَا مِنَ الْبَيِّنَاتِ وَالَّذِي فَطَرَنَا  ۖ  فَاقْضِ مَا أَنْتَ قَاض ٍ  ۖ  إِنَّمَا تَقْضِي هَذِهِ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا
'Innā 'Āmannā Birabbinā Liyaghfira Lanā Khaţāyānā Wa Mā 'Akrahtanā `Alayhi Mina As-Siĥri Wa  ۗ  Allāhu Khayrun Wa 'Ab َ020-073 "Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kumaMafi wanzuwa." إِنَّا آمَنَّا بِرَبِّنَا لِيَغْفِرَ لَنَا خَطَايَانَا وَمَا أَكْرَهْتَنَا عَلَيْهِ مِنَ السِّحْرِ  ۗ  وَاللَّهُ خَيْر ٌ وَأَبْقَى
'Innahu Man Ya'ti Rabbahu Mujrimāan Fa'inna Lahu Jahannama Lā Yamūtu Fīhā Wa Lā Yaĥyā َ020-074 Lalle shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa. إِنَّه ُُ مَنْ يَأْتِ رَبَّه ُُ مُجْرِما ً فَإِنَّ لَه ُُ جَهَنَّمَ لاَ يَمُوتُ فِيهَا وَلاَ يَحْيَا
Wa Man Ya'tihi Mu'umināan Qad `Amila Aş-Şāliĥāti Fa'ūlā'ika Lahumu Ad-Darajātu Al-`Ulā َ020-075 Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka. وَمَنْ يَأْتِه ِِ مُؤْمِنا ً قَدْ عَمِلَ الصَّالِحَاتِ فَأُوْلَائِكَ لَهُمُ الدَّرَجَاتُ الْعُلاَ
Jannātu `Adnin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā  ۚ  Wa Dhalika Jazā'u Man Tazakká َ020-076 Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku. جَنَّاتُ عَدْن ٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا  ۚ  وَذَلِكَ جَزَاءُ مَنْ تَزَكَّى
Wa Laqad 'Awĥaynā 'Ilá Mūsá 'An 'Asri Bi`ibādī Fāđrib Lahum Ţarīqāan Al-Baĥri Yabasāan Lā Takhāfu Darakāan Wa Lā Takhshá َ020-077 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa." وَلَقَدْ أَوْحَيْنَا إِلَى مُوسَى أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِي فَاضْرِبْ لَهُمْ طَرِيقا ً فِي الْبَحْرِ يَبَسا ً لاَ تَخَافُ دَرَكا ً وَلاَ تَخْشَى
Fa'atba`ahum Fir`awnu Bijunūdihi Faghashiyahum Mina Al-Yammi Mā Ghashiyahum َ020-078 Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su. فَأَتْبَعَهُمْ فِرْعَوْنُ بِجُنُودِه ِِ فَغَشِيَهُمْ مِنَ الْيَمِّ مَا غَشِيَهُمْ
Wa 'Ađalla Fir`awnu Qawmahu Wa Mā Hadá َ020-079 Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar(dasu) ba. وَأَضَلَّ فِرْعَوْنُ قَوْمَه ُُ وَمَا هَدَى
Yā Banī 'Isrā'īla Qad 'Anjaynākum Min `Adūwikum Wa Wā`adnākum Jāniba Aţūri Al-'Aymana Wa Nazzalnā `Alaykumu Al-Manna Wa As-Salwá َ020-080 Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku. يَابَنِي إِسْرَائِيلَ قَدْ أَنجَيْنَاكُمْ مِنْ عَدُوِّكُمْ وَوَاعَدْنَاكُمْ جَانِبَ الطُّورِ الأَيْمَنَ وَنَزَّلْنَا عَلَيْكُمُ الْمَنَّ وَالسَّلْوَى
Kulū Min Ţayyibāti Mā Razaqnākum Wa Lā Taţghaw Fīhi Fayaĥilla `Alaykum Ghađabī  ۖ  Wa Man Yaĥlil `Alayhi Ghađabī Faqad Hawá َ020-081 Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi. كُلُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ وَلاَ تَطْغَوْا فِيه ِِ فَيَحِلَّ عَلَيْكُمْ غَضَبِي  ۖ  وَمَنْ يَحْلِلْ عَلَيْهِ غَضَبِي فَقَدْ هَوَى
Wa 'Innī Laghaffārun Liman Tāba Wa 'Āmana Wa `Amila Şāliĥāan Thumma Ahtadá َ020-082 Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa. وَإِنِّي لَغَفَّار ٌ لِمَنْ تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحا ً ثُمَّ اهْتَدَى
Wa Mā 'A`jalaka `An Qawmika Yā Mūsá َ020-083 "Kuma mẽne ne ya gaggautar da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!" وَمَا أَعْجَلَكَ عَنْ قَوْمِكَ يَامُوسَى
Qāla Hum 'Ūlā'i `Alá 'Atharī Wa `Ajiltu 'Ilayka Rabbi Litarđá َ020-084 Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda." قَالَ هُمْ أُولاَءِ عَلَى أَثَرِي وَعَجِلْتُ إِلَيْكَ رَبِّ لِتَرْضَى
Qāla Fa'innā Qad Fatannā Qawmaka Min Ba`dika Wa 'Ađallahumu As-Sāmirīyu َ020-085 Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su." قَالَ فَإِنَّا قَدْ فَتَنَّا قَوْمَكَ مِنْ بَعْدِكَ وَأَضَلَّهُمُ السَّامِرِيُّ
Faraja`a Mūsá 'Ilá Qawmihi Ghađbāna 'Asifāan  ۚ  Qāla Yā Qawmi 'Alam Ya`idkum Rabbukum Wa`dāan Ĥasanāan  ۚ  'Afaţāla `Alaykumu Al-`Ahdu 'Am 'Aradtum 'An Yaĥilla `Alaykum Ghađabun Min Rabbikum Fa'akhlaftum Maw`idī َ020-086 Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna?" فَرَجَعَ مُوسَى إِلَى قَوْمِه ِِ غَضْبَانَ أَسِفا ً  ۚ  قَالَ يَاقَوْمِ أَلَمْ يَعِدْكُمْ رَبُّكُمْ وَعْداً حَسَناً أَفَطَالَ  ۚ  عَلَيْكُمُ الْعَهْدُ أَمْ أَرَدْتُمْ أَنْ يَحِلَّ عَلَيْكُمْ غَضَب ٌ مِنْ رَبِّكُمْ فَأَخْلَفْتُمْ مَوْعِدِي
Qālū Mā 'Akhlafnā Maw`idaka Bimalkinā Wa Lakinnā Ĥummilnā 'Awzārāan Min Zīnati Al-Qawmi Faqadhafnāhā Fakadhalika 'Alqá As-Sāmirīyu َ020-087 Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa." قَالُوا مَا أَخْلَفْنَا مَوْعِدَكَ بِمَلْكِنَا وَلَكِنَّا حُمِّلْنَا أَوْزَارا ً مِنْ زِينَةِ الْقَوْمِ فَقَذَفْنَاهَا فَكَذَلِكَ أَلْقَى السَّامِرِيُّ
Fa'akhraja Lahum `Ijlāan Jasadāan Lahu Khuwārun Faqālū Hādhā 'Ilahukum Wa 'Ilahu Mūsá Fanasiya َ020-088 "Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta." فَأَخْرَجَ لَهُمْ عِجْلا ً جَسَدا ً لَه ُُ خُوَار ٌ فَقَالُوا هَذَا إِلَهُكُمْ وَإِلَه ُُ مُوسَى فَنَسِيَ
'Afalā Yarawna 'Allā Yarji`u 'Ilayhim Qawlāan Wa Lā Yamliku Lahum Đarrāan Wa Lā Naf`āan َ020-089 Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni? أَفَلاَ يَرَوْنَ أَلاَّ يَرْجِعُ إِلَيْهِمْ قَوْلا ً وَلاَ يَمْلِكُ لَهُمْ ضَرّا ً وَلاَ نَفْعا ً
Wa Laqad Qāla Lahum Hārūnu Min Qablu Yā Qawmi 'Innamā Futintum Bihi  ۖ  Wa 'Inna Rabbakumu Ar-Raĥmānu Fa Attabi`ūnī Wa 'Aţī`ū 'Amrī َ020-090 Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umurnĩna." وَلَقَدْ قَالَ لَهُمْ هَارُونُ مِنْ قَبْلُ يَاقَوْمِ إِنَّمَا فُتِنتُمْ بِه ِِ وَإِنَّ  ۖ  رَبَّكُمُ الرَّحْمَنُ فَاتَّبِعُونِي وَأَطِيعُوا أَمْرِي
Qālū Lan Nabraĥa `Alayhi `Ākifīna Ĥattá Yarji`a 'Ilaynā Mūsá َ020-091 Suka ce: "Ba zã mu gushe ba faufau a kansa munã mãsu lazimta, sai Mũsã ya kõmo zuwa gare mu." قَالُوا لَنْ نَبْرَحَ عَلَيْهِ عَاكِفِينَ حَتَّى يَرْجِعَ إِلَيْنَا مُوسَى
Qāla Yā Hārūnu Mā Mana`aka 'Idh Ra'aytahum Đallū َ020-092 (Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace." قَالَ يَاهَارُونُ مَا مَنَعَكَ إِذْ رَأَيْتَهُمْ ضَلُّوا
'Allā Tattabi`anī  ۖ  'Afa`aşayta 'Amrī َ020-093 "Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne?" أَلاَّ تَتَّبِعَنِي  ۖ  أَفَعَصَيْتَ أَمْرِي
Qāla Yabna'uumma Lā Ta'khudh Biliĥyatī Wa Lā Bira'sī 'Innī Khashītu  ۖ  'An Taqūla Farraqta Bayna Banī 'Isrā'īla Wa Lam Tarqub Qawlī َ020-094 (Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba." قَالَ يَبْنَؤُمَّ لاَ تَأْخُذْ بِلِحْيَتِي وَلاَ بِرَأْسِي إِنِّي خَشِيتُ  ۖ  أَنْ تَقُولَ فَرَّقْتَ بَيْنَ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَلَمْ تَرْقُبْ قَوْلِي
Qāla Famā Khaţbuka Yā Sāmirīyu َ020-095 (Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Ya Sãmiri!" قَالَ فَمَا خَطْبُكَ يَاسَامِرِيُّ
Qāla Başurtu Bimā Lam Yabşurū Bihi Faqabađtu Qabđatan Min 'Athari Ar-Rasūli Fanabadhtuhā Wa Kadhalika Sawwalat Lī Nafsī َ020-096 (Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini." قَالَ بَصُرْتُ بِمَا لَمْ يَبْصُرُوا بِه ِِ فَقَبَضْتُ قَبْضَة ً مِنْ أَثَرِ الرَّسُولِ فَنَبَذْتُهَا وَكَذَلِكَ سَوَّلَتْ لِي نَفْسِي
Qāla Fādh/hab Fa'inna Laka Fī Al-Ĥayāati 'An Taqūla Lā Misāsa  ۖ  Wa 'Inna Laka Maw`idāan Lan Tukhlafahu  ۖ  Wa Anžur 'Ilá 'Ilahika Al-Ladhī Žalta `Alayhi `Ākifāan  ۖ  Lanuĥarriqannahu Thumma Lanansifannahu Fī Al-Yammi Nasfāan َ020-097 (Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi, sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa." قَالَ فَاذْهَبْ فَإِنَّ لَكَ فِي الْحَيَاةِ أَنْ تَقُولَ لاَ مِسَاسَ  ۖ  وَإِنَّ لَكَ مَوْعِدا ً لَنْ تُخْلَفَه ُُ  ۖ  وَانظُرْ إِلَى إِلَهِكَ الَّذِي ظَلْتَ عَلَيْهِ عَاكِفا ً  ۖ  لَنُحَرِّقَنَّه ُُ ثُمَّ لَنَنسِفَنَّه ُُ فِي الْيَمِّ نَسْفا ً
'Innamā 'Ilahukumu Al-Lahu Al-Ladhī Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۚ  Wasi`a Kulla Shay'in `Ilmāan َ020-098 Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci dukkan kõme da ilmi. إِنَّمَا إِلَهُكُمُ اللَّهُ الَّذِي لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ  ۚ  وَسِعَ كُلَّ شَيْءٍ عِلْما ً
Kadhālika Naquşşu `Alayka Min 'Anbā'i Mā Qad Sabaqa  ۚ  Wa Qad 'Ātaynāka Min Ladunnā Dhikrāan َ020-099 Kamar wancan ne Muke lãbartãwa a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gunMu. كَذَلِكَ نَقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنْبَاءِ مَا قَدْ سَبَقَ  ۚ  وَقَدْ آتَيْنَاكَ مِنْ لَدُنَّا ذِكْرا ً
Man 'A`rađa `Anhu Fa'innahu Yaĥmilu Yawma Al-Qiyāmati Wizrāan َ020-100 Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma. مَنْ أَعْرَضَ عَنْهُ فَإِنَّه ُُ يَحْمِلُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وِزْرا ً
Khālidīna Fīhi  ۖ  Wa Sā'a Lahum Yawma Al-Qiyāmati Ĥiman َ020-101 Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma. خَالِدِينَ فِيه ِِ  ۖ  وَسَاءَ لَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ حِمْلا ً
Yawma Yunfakhu Fī Aş-Şūri  ۚ  Wa Naĥshuru Al-Mujrimīna Yawma'idhin Zurqāan َ020-102 A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu. يَوْمَ يُنْفَخُ فِي الصُّورِ  ۚ  وَنَحْشُرُ الْمُجْرِمِينَ يَوْمَئِذ ٍ زُرْقا ً
Yatakhāfatūna Baynahum 'In Labithtum 'Illā `Ashan َ020-103 Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma." يَتَخَافَتُونَ بَيْنَهُمْ إِنْ لَبِثْتُمْ إِلاَّ عَشْرا ً
Naĥnu 'A`lamu Bimā Yaqūlūna 'Idh Yaqūlu 'Amthaluhum Ţarīqatan 'In Labithtum 'Illā Yawmāan َ020-104 Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda." نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ إِذْ يَقُولُ أَمْثَلُهُمْ طَرِيقَة ً إِنْ لَبِثْتُمْ إِلاَّ يَوْما ً
Wa Yas'alūnaka `Ani Al-Jibāli Faqul Yansifuhā Rabbī Nasfāan َ020-105 Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa, وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْجِبَالِ فَقُلْ يَنسِفُهَا رَبِّي نَسْفا ً
Fayadharuhā Qā`āan Şafşafāan َ020-106 Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi. فَيَذَرُهَا قَاعا ً صَفْصَفا ً
Lā Tará Fīhā `Iwajāan Wa Lā 'Aman َ020-107 "Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu." لاَ تَرَى فِيهَا عِوَجا ً وَلاَ أَمْتا ً
Yawma'idhin Yattabi`ūna Ad-Dā`ī Lā `Iwaja Lahu  ۖ  Wa Khasha`ati Al-'Aşwātu Lilrraĥmani Falā Tasma`u 'Illā Haman َ020-108 A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya. يَوْمَئِذ ٍ يَتَّبِعُونَ الدَّاعِي لاَ عِوَجَ لَه ُُ  ۖ  وَخَشَعَتِ الأَصْوَاتُ لِلرَّحْمَنِ فَلاَ تَسْمَعُ إِلاَّ هَمْسا ً
Yawma'idhin Lā Tanfa`u Ash-Shafā`atu 'Illā Man 'Adhina Lahu Ar-Raĥmānu Wa Rađiya Lahu Qawlāan َ020-109 A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da magan يَوْمَئِذ ٍ لاَ تَنفَعُ الشَّفَاعَةُ إِلاَّ مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَنُ وَرَضِيَ لَه ُُ قَوْلا ً
Ya`lamu Mā Bayna 'Aydīhim Wa Mā Khalfahum Wa Lā Yuĥīţūna Bihi `Ilmāan َ020-110 Yanã sanin abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani. يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِه ِِ عِلْما ً
Wa `Anati Al-Wujūhu Lilĥayyi Al-Qayyūmi  ۖ  Wa Qad Khāba Man Ĥamala Žulmāan َ020-111 Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye,Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe. وَعَنَتِ الْوُجُوه ُُ لِلْحَيِّ الْقَيُّومِ  ۖ  وَقَدْ خَابَ مَنْ حَمَلَ ظُلْما ً
Wa Man Ya`mal Mina Aş-Şāliĥāti Wa Huwa Mu'uminun Falā Yakhāfu Žulmāan Wa Lā Hađmāan َ020-112 Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa. وَمَنْ يَعْمَلْ مِنَ الصَّالِحَاتِ وَهُوَ مُؤْمِن ٌ فَلاَ يَخَافُ ظُلْما ً وَلاَ هَضْما ً
Wa Kadhalika 'Anzalnāhu Qur'ānāan `Arabīyāan Wa Şarrafnā Fīhi Mina Al-Wa`īdi La`allahum Yattaqūna 'Aw Yuĥdithu Lahum Dhikrāan َ020-113 Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa. وَكَذَلِكَ أَنزَلْنَاه ُُ قُرْآناً عَرَبِيّا ً وَصَرَّفْنَا فِيه ِِ مِنَ الْوَعِيدِ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ أَوْ يُحْدِثُ لَهُمْ ذِكْرا ً
Fata`ālá Al-Lahu Al-Maliku Al-Ĥaqqu  ۗ  Wa Lā Ta`jal Bil-Qur'āni Min Qabli 'An Yuqđá 'Ilayka Waĥyuhu  ۖ  Wa Qul Rabbi Zidnī `Ilmāan َ020-114 Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi." فَتَعَالَى اللَّهُ الْمَلِكُ الْحَقُّ  ۗ  وَلاَ تَعْجَلْ بِالْقُرْآنِ مِنْ قَبْلِ أَنْ يُقْضَى إِلَيْكَ وَحْيُه ُُ  ۖ  وَقُلْ رَبِّ زِدْنِي عِلْما ً
Wa Laqad `Ahidnā 'Ilá 'Ādama Min Qablu Fanasiya Wa Lam Najid Lahu `Azmāan َ020-115 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shiba. وَلَقَدْ عَهِدْنَا إِلَى آدَمَ مِنْ قَبْلُ فَنَسِيَ وَلَمْ نَجِدْ لَه ُُ عَزْما ً
Wa 'Idh Qulnā Lilmalā'ikati Asjudū Li'dama Fasajadū 'Illā 'Iblīsa 'Abá َ020-116 Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya. وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلاَئِكَةِ اسْجُدُوا لِأدَمَ فَسَجَدُوا إِلاَّ إِبْلِيسَ أَبَى
Faqulnā Yā 'Ādamu 'Inna Hādhā `Adūwun Laka Wa Lizawjika Falā Yukhrijannakumā Mina Al-Jannati Fatash َ020-117 Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala." فَقُلْنَا يَاآدَمُ إِنَّ هَذَا عَدُوّ ٌ لَكَ وَلِزَوْجِكَ فَلاَ يُخْرِجَنَّكُمَا مِنَ الْجَنَّةِ فَتَشْقَى
'Inna Laka 'Allā Tajū`a Fīhā Wa Lā Ta`rá َ020-118 Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba. إِنَّ لَكَ أَلاَّ تَجُوعَ فِيهَا وَلاَ تَعْرَى
Wa 'Annaka Lā Tažma'u Fīhā Wa Lā Tađĥá َ020-119 "Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba." وَأَنَّكَ لاَ تَظْمَأُ فِيهَا وَلاَ تَضْحَى
Fawaswasa 'Ilayhi Ash-Shayţānu Qāla Yā 'Ādamu Hal 'Adulluka `Alá Shajarati Al-Khuldi Wa Mulkin Lā Yab َ020-120 Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: "Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa?" فَوَسْوَسَ إِلَيْهِ الشَّيْطَانُ قَالَ يَاآدَمُ هَلْ أَدُلُّكَ عَلَى شَجَرَةِ الْخُلْدِ وَمُلْك ٍ لاَ يَبْلَى
Fa'akalā Minhā Fabadat Lahumā Saw'ātuhumā Wa Ţafiqā Yakhşifāni `Alayhimā Min Waraqi Al-Jannati  ۚ  Wa `Aşá 'Ādamu Rabbahu Faghawá َ020-121 Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace. فَأَكَلاَ مِنْهَا فَبَدَتْ لَهُمَا سَوْآتُهُمَا وَطَفِقَا يَخْصِفَانِ عَلَيْهِمَا مِنْ وَرَقِ الْجَنَّةِ  ۚ  وَعَصَى آدَمُ رَبَّه ُُ فَغَوَى
Thumma Ajtabāhu Rabbuhu Fatāba `Alayhi Wa Hadá َ020-122 Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi). ثُمَّ اجْتَبَاه ُُ رَبُّه ُُ فَتَابَ عَلَيْهِ وَهَدَى
Qāla Ahbiţā Minhā Jamī`āan  ۖ  Ba`đukum Liba`đin `Adūwun  ۖ  Fa'immā Ya'tiyannakum Minnī Hudáan Famani Attaba`a Hudāya Falā Yađillu Wa Lā Yash َ020-123 Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala." قَالَ اهْبِطَا مِنْهَا جَمِيعا ً  ۖ  بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوّ ٌ  ۖ  فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ مِنِّي هُدى ً فَمَنِ اتَّبَعَ هُدَايَ فَلاَ يَضِلُّ وَلاَ يَشْقَى
Wa Man 'A`rađa `An Dhikrī Fa'inna Lahu Ma`īshatan Đankāan Wa Naĥshuruhu Yawma Al-Qiyāmati 'A`má َ020-124 "Kuma wanda ya bijire daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho." وَمَنْ أَعْرَضَ عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ لَه ُُ مَعِيشَة ً ضَنكا ً وَنَحْشُرُه ُُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى
Qāla Rabbi Lima Ĥashartanī 'A`má Wa Qad Kuntu Başīrāan َ020-125 Ya ce: "Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani?" قَالَ رَبِّ لِمَ حَشَرْتَنِي أَعْمَى وَقَدْ كُنتُ بَصِيرا ً
Qāla Kadhālika 'Atatka 'Āyātunā Fanasītahā  ۖ  Wa Kadhalika Al-Yawma Tun َ020-126 Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyinMu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka." قَالَ كَذَلِكَ أَتَتْكَ آيَاتُنَا فَنَسِيتَهَا  ۖ  وَكَذَلِكَ الْيَوْمَ تُنسَى
Wa Kadhalika Najzī Man 'Asrafa Wa Lam Yu'umin Bi'āyāti Rabbihi  ۚ  Wa La`adhābu Al-'Ākhirati 'Ashaddu Wa 'Ab َ020-127 Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita, kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa وَكَذَلِكَ نَجْزِي مَنْ أَسْرَفَ وَلَمْ يُؤْمِنْ بِآيَاتِ رَبِّه ِِ  ۚ  وَلَعَذَابُ الآخِرَةِ أَشَدُّ وَأَبْقَى
'Afalam Yahdi Lahum Kam 'Ahlaknā Qablahum Mina Al-Qurūni Yamshūna Fī Masākinihim  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Li'wlī An-Nuhá َ020-128 Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula. أَفَلَمْ يَهْدِ لَهُمْ كَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُمْ مِنَ الْقُرُونِ يَمْشُونَ فِي مَسَاكِنِهِمْ  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِأوْلِي النُّهَى
Wa Lawlā Kalimatun Sabaqat Min Rabbika Lakāna Lizāmāan Wa 'Ajalun Musammáan َ020-129 Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta. وَلَوْلاَ كَلِمَة ٌ سَبَقَتْ مِنْ رَبِّكَ لَكَانَ لِزَاما ً وَأَجَل ٌ مُسَمّى ً
Fāşbir `Alá Mā Yaqūlūna Wa Sabbiĥ Biĥamdi Rabbika Qabla Ţulū`i Ash-Shamsi Wa Qabla Ghurūbihā  ۖ  Wa Min 'Ānā'i Al-Layli Fasabbiĥ Wa 'Aţrāfa An-Nahāri La`allaka Tarđá َ020-130 Sai ka yi haƙuri a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda. فَاصْبِرْ عَلَى مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ غُرُوبِهَا  ۖ  وَمِنْ آنَاءِ اللَّيْلِ فَسَبِّحْ وَأَطْرَافَ النَّهَارِ لَعَلَّكَ تَرْضَى
Wa Lā Tamuddanna `Aynayka 'Ilá Mā Matta`nā Bihi 'Azwājāan Minhum Zahrata Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Linaftinahum Fīhi  ۚ  Wa Rizqu Rabbika Khayrun Wa 'Ab َ020-131 Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikinsa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa. وَلاَ تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَى مَا مَتَّعْنَا بِهِ~ِ أَزْوَاجا ً مِنْهُمْ زَهْرَةَ الْحَيَاةِ الدُّنيَا لِنَفْتِنَهُمْ فِيه ِِ  ۚ  وَرِزْقُ رَبِّكَ خَيْر ٌ وَأَبْقَى
Wa 'Mur 'Ahlaka Biş-Şalāati Wa Aşţabir `Alayhā  ۖ  Lā Nas'aluka Rizqāan  ۖ  Naĥnu Narzuquka Wa  ۗ  Al-`Āqibatu Lilttaq َ020-132 Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa. وَأْمُرْ أَهْلَكَ بِالصَّلاَةِ وَاصْطَبِرْ عَلَيْهَا  ۖ  لاَ نَسْأَلُكَ رِزْقا ً  ۖ  نَحْنُ نَرْزُقُكَ  ۗ  وَالْعَاقِبَةُ لِلتَّقْوَى
Wa Qālū Lawlā Ya'tīnā Bi'āyatin Min Rabbihi  ۚ  'Awalam Ta'tihim Bayyinatu Mā Fī Aş-Şuĥufi Al-'Ū َ020-133 Kuma suka ce: "Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba? وَقَالُوا لَوْلاَ يَأْتِينَا بِآيَة ٍ مِنْ رَبِّهِ~ِ  ۚ  أَوَلَمْ تَأْتِهِمْ بَيِّنَةُ مَا فِي الصُّحُفِ الأُولَى
Wa Law 'Annā 'Ahlaknāhum Bi`adhābin Min Qablihi Laqālū Rabbanā Lawlā 'Arsalta 'Ilaynā Rasūlāan Fanattabi`a 'Āyātika Min Qabli 'An Nadhilla Wa Nakh َ020-134 Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: "Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu!" وَلَوْ أَنَّا أَهْلَكْنَاهُمْ بِعَذَاب ٍ مِنْ قَبْلِه ِِ لَقَالُوا رَبَّنَا لَوْلاَ أَرْسَلْتَ إِلَيْنَا رَسُولا ً فَنَتَّبِعَ آيَاتِكَ مِنْ قَبْلِ أَنْ نَذِلَّ وَنَخْزَى
Qul Kullun Mutarabbişun Fatarabbaşū  ۖ  Fasata`lamūna Man 'Aşĥābu Aş-Şirāţi As-Sawīyi Wa Mani Ahtadá َ020-135 Ka ce: "Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa." قُلْ كُلّ ٌ مُتَرَبِّص ٌ فَتَرَبَّصُوا  ۖ  فَسَتَعْلَمُونَ مَنْ أَصْحَابُ الصِّرَاطِ السَّوِيِّ وَمَنِ اهْتَدَى
Next Sūrah