19) Sūrat Maryam

Printed format

19)

Kāf-Hā-Yā-`Ayn-Şād 019-001 K̃. H. Y. I . Ṣ̃. ----
Dhikru Raĥmati Rabbika `Abdahu Zakarīyā 019-002 Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.
'Idh Nādá Rabbahu Nidā'an Khafīyāan 019-003 A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye.
Qāla Rabbi 'Innī Wahana Al-`Ažmu Minnī Wa Ashta`ala Ar-Ra'su Shaybāan Wa Lam 'Akun Bidu`ā'ika Rabbi Shaqīyāan 019-004 Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!"
Wa 'Innī Khiftu Al-Mawāliya Min Warā'ī Wa Kānati Amra'atī `Āqirāan Fahab Lī Min Ladunka Walīyāan 019-005 "Kuma lalle nĩ, na ji tsõron dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa."
Yarithunī Wa Yarithu Min 'Āli Ya`qūba  ۖ  Wa Aj`alhu Rabbi Rađīyāan 019-006 "Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!"  ۖ 
Yā Zakarīyā 'Innā Nubashshiruka Bighulāmin Asmuhu Yaĥyá Lam Naj`al Lahu Min Qablu Samīyāan 019-007 (Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni."
Qāla Rabbi 'Anná Yakūnu Lī Ghulāmun Wa Kānat Amra'atī `Āqirāan Wa Qad Balaghtu Mina Al-Kibari `Itīyāan 019-008 Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?"
Qāla Kadhālika Qāla Rabbuka Huwa `Alayya Hayyinun Wa Qad Khalaqtuka Min Qablu Wa Lam Taku Shay'āan 019-009 Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba."
Qāla Rabbi Aj`al Lī 'Āyatan  ۚ  Qāla 'Āyatuka 'Allā Tukallima An-Nāsa Thalātha Layālin Sawīyāan 019-010 Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai."  ۚ 
Fakharaja `Alá Qawmihi Mina Al-Miĥrābi Fa'awĥá 'Ilayhim 'An Sabbiĥū Bukratan Wa `Ashīyāan 019-011 Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma."
Yā Yaĥyá Khudhi Al-Kitāba Biqūwatin  ۖ  Wa 'Ātaynāhu Al-Ĥukma Şabīyāan 019-012 Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro.  ۖ 
Wa Ĥanānāan Min Ladunnā Wa Zakāatan  ۖ  Wa Kāna Taqīyāan 019-013 Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa.  ۖ 
Wa Barrāan Biwālidayhi Wa Lam Yakun Jabbārāan `Aşīyāan 019-014 Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba.
Wa Salāmun `Alayhi Yawma Wulida Wa Yawma Yamūtu Wa Yawma Yub`athu Ĥayyāan 019-015 Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai.
Wa Adhkur Fī Al-Kitābi Maryama 'Idh Antabadhat Min 'Ahlihā Makānāan Sharqīyāan 019-016 Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
Fāttakhadhat Min Dūnihim Ĥijābāan Fa'arsalnā 'Ilayhā Rūĥanā Fatamaththala Lahā Basharāan Sawīyāan 019-017 Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.
Qālat 'Innī 'A`ūdhu Bir-Raĥmani Minka 'In Kunta Taqīyāan 019-018 Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!"
Qāla 'Innamā 'Anā Rasūlu Rabbiki Li'haba Laki Ghulāmāan Zakīyāan 019-019 Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki."
Qālat 'Anná Yakūnu Lī Ghulāmun Wa Lam Yamsasnī Basharun Wa Lam 'Aku Baghīyāan 019-020 Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?"
Qāla Kadhāliki Qāla Rabbuki Huwa `Alayya Hayyinun  ۖ  Wa Linaj`alahu 'Āyatan Lilnnāsi Wa Raĥmatan Minnā  ۚ  Wa Kāna 'Amrāan Maqđīyāan 019-021 Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce."  ۖ   ۚ 
Faĥamalat/hu Fāntabadhat Bihi Makānāan Qaşīyāan 019-022 Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.
Fa'ajā'ahā Al-Makhāđu 'Ilá Jidh`i An-Nakhlati Qālat Yā Laytanī Mittu Qabla Hādhā Wa Kuntu Nasyāan Mansīyāan 019-023 Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"
Fanādāhā Min Taĥtihā 'Allā Taĥzanī Qad Ja`ala Rabbuki Taĥtaki Sarīyāan 019-024 Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.
Wa Huzzī 'Ilayki Bijidh`i An-Nakhlati Tusāqiţ `Alayki Ruţabāan Janīyāan 019-025 "Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu."
Fakulī Wa Ashrabī Wa Qarrī `Aynāan  ۖ  Fa'immā Taraynna Mina Al-Bashari 'Aĥadāan Faqūlī 'Innī Nadhartu Lilrraĥmani Şawmāan Falan 'Ukallima Al-Yawma 'Insīyāan 019-026 "Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."  ۖ 
Fa'atat Bihi Qawmahā Taĥmiluhu  ۖ  Qālū Yā Maryamu Laqad Ji'ti Shay'āan Farīyāan 019-027 Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!  ۖ 
Yā 'Ukhta Hārūna Mā Kāna 'Abūki Amra'a Saw'in Wa Mā Kānat 'Ummuki Baghīyāan 019-028 "Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba."
Fa'ashārat 'Ilayhi  ۖ  Qālū Kayfa Nukallimu Man Kāna Fī Al-Mahdi Şabīyāan 019-029 Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?"  ۖ 
Qāla 'Innī `Abdu Al-Lahi 'Ātāniya Al-Kitāba Wa Ja`alanī Nabīyāan 019-030 Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."
Wa Ja`alanī Mubārakāan 'Ayna Mā Kuntu Wa 'Awşānī Biş-Şalāati Wa Az-Zakāati Mā Dumtu Ĥayyāan 019-031 "Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai."
Wa Barrāan Biwālidatī Wa Lam Yaj`alnī Jabbārāan Shaqīyāan 019-032 "Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."
Wa As-Salāmu `Alayya Yawma Wulidtu Wa Yawma 'Amūtu Wa Yawma 'Ub`athu Ĥayyāan 019-033 "Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai."
Dhālika `Īsá Abnu Maryama  ۚ  Qawla Al-Ĥaqqi Al-Ladhī Fīhi Yamtarūna 019-034 Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.  ۚ 
Mā Kāna Lillahi 'An Yattakhidha Min Waladin  ۖ  Subĥānahu  ۚ  'Idhā Qađá 'Amrāan Fa'innamā Yaqūlu Lahu Kun Fayakūnu 019-035 Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.  ۖ  ~  ۚ 
Wa 'Inna Al-Laha Rabbī Wa Rabbukum Fā`budūhu  ۚ  Hādhā Şirāţun Mustaqīmun 019-036 "Kuma lalle Allah ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."  ۚ 
khtalafa Al-'Aĥzābu Min Baynihim  ۖ  Fawaylun Lilladhīna Kafarū Min Mash/hadi Yawmin `Ažīmin 019-037 Sai ƙungiyõyin suka sãɓã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.  ۖ 
'Asmi` Bihim Wa 'Abşir Yawma Ya'tūnanā  ۖ  Lakini Až-Žālimūna Al-Yawma Fī Đalālin Mubīnin 019-038 Mẽne ne ya yi jinsu, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.  ۖ 
Wa 'Andhirhum Yawma Al-Ĥasrati 'Idh Quđiya Al-'Amru Wa HumGhaflatin Wa Hum Lā Yu'uminūna 019-039 Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni.
'Innā Naĥnu Narithu Al-'Arđa Wa Man `Alayhā Wa 'Ilaynā Yurja`ūna 019-040 Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.
Wa Adhkur Fī Al-Kitābi 'Ibrāhīma  ۚ  'Innahu Kāna Şiddīqāan Nabīyāan 019-041 Kuma ambaci Ibrãhĩm a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.  ۚ 
'Idh Qāla Li'abīhi Yā 'Abati Lima Ta`budu Mā Lā Yasma`u Wa Lā Yubşiru Wa Lā Yughnī `Anka Shay'āan 019-042 A lõkacin da ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka?"
Yā 'Abati 'Innī Qad Jā'anī Mina Al-`Ilmi Mā Lam Ya'tika Fa Attabi`nī 'Ahdika Şirāţāan Sawīyāan 019-043 "Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici."
Yā 'Abati Lā Ta`budi Ash-Shayţāna  ۖ  'Inna Ash-Shayţāna Kāna Lilrraĥmani `Aşīyāan 019-044 "Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama."  ۖ 
Yā 'Abati 'Innī 'Akhāfu 'An Yamassaka `Adhābun Mina Ar-Raĥmāni Fatakūna Lilshshayţāni Walīyāan 019-045 "Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan."
Qāla 'Arāghibun 'Anta `An 'Ālihatī Yā 'Ibrāhīmu  ۖ  La'in Lam Tantahi La'arjumannaka  ۖ  Wa Ahjurnī Malīyāan 019-046 Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci."  ۖ   ۖ 
Qāla Salāmun `Alayka  ۖ  Sa'astaghfiru Laka Rabbī  ۖ  'Innahu Kāna Bī Ĥafīyāan 019-047 Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka. Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni."  ۖ   ۖ 
Wa 'A`tazilukum Wa Mā Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi Wa 'Ad`ū Rabbī `Asá 'Allā 'Akūna Bidu`ā'i Rabbī Shaqīyāan 019-048 "Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina."
Falammā A`tazalahum Wa Mā Ya`budūna Min Dūni Al-Lahi Wahabnā Lahu 'Isĥāqa Wa Ya`qūba  ۖ  Wa Kullā Ja`alnā Nabīyāan 019-049 To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi. ~  ۖ 
Wa Wahabnā Lahum Min Raĥmatinā Wa Ja`alnā Lahum Lisāna Şidqin `Alīyāan 019-050 Kuma Muka yi musu kyauta daga RahamarMu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya maɗaukaki.
Wa Adhkur Fī Al-Kitābi Mūsá  ۚ  'Innahu Kāna Mukhlaşāan Wa Kāna Rasūlāan Nabīyāan 019-051 Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi.  ۚ 
Wa Nādaynāhu Min Jānibi Aţūri Al-'Aymani Wa Qarrabnāhu Najīyāan 019-052 Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa.
Wa Wahabnā Lahu Min Raĥmatinā 'Akhāhu Hārūna Nabīyāan 019-053 Kuma Muka yi masa kyauta daga RahamarMu da ɗan'uwansa Hãrũna, ya zama Annabi.
Wa Adhkur Fī Al-Kitābi 'Ismā`īla  ۚ  'Innahu Kāna Şādiqa Al-Wa`di Wa Kāna Rasūlāan Nabīyāan 019-054 Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi.  ۚ 
Wa Kāna Ya'muru 'Ahlahu Biş-Şalāati Wa Az-Zakāati Wa Kāna `Inda Rabbihi Marđīyāan 019-055 Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.
Wa Adhkur Fī Al-Kitābi 'Idrīsa  ۚ  'Innahu Kāna Şiddīqāan Nabīyāan 019-056 Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.  ۚ 
Wa Rafa`nāhu Makānāan `Alīyāan 019-057 Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki.
'Ūlā'ika Al-Ladhīna 'An`ama Al-Lahu `Alayhim Mina An-Nabīyīna Min Dhurrīyati 'Ādama Wa Mimman Ĥamalnā Ma`a Nūĥin Wa Min Dhurrīyati 'Ibrāhīma Wa 'Isrā'īla Wa Mimman Hadaynā Wa Ajtabaynā  ۚ  'Idhā Tutlá `Alayhim 'Āyātu Ar-Raĥmāni Kharrū Sujjadāan Wa Bukīyāan 019-058 Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka.  ۚ 
Fakhalafa Min Ba`dihim Khalfun 'Ađā`ū Aş-Şalāata Wa Attaba`ū Ash-Shahawāti  ۖ  Fasawfa Yalqawna Ghayyāan 019-059 Sai waɗansu 'yan bãya suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri.  ۖ 
'Illā Man Tāba Wa 'Āmana Wa `Amila Şāliĥāan Fa'ūlā'ika Yadkhulūna Al-Jannata Wa Lā Yužlamūna Shay'āan 019-060 Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme.
Jannāti `Adnin Allatī Wa`ada Ar-Raĥmānu `Ibādahu Bil-Ghaybi  ۚ  'Innahu Kāna Wa`duhu Ma'tīyāan 019-061 Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa.  ۚ 
Lā Yasma`ūna Fīhā Laghwan 'Illā Salāmāan  ۖ  Wa Lahum Rizquhum Fīhā Bukratan Wa `Ashīyāan 019-062 Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice.  ۖ 
Tilka Al-Jannatu Allatī Nūrithu Min `Ibādinā Man Kāna Taqīyāan 019-063 Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa.
Wa Mā Natanazzalu 'Illā Bi'amri Rabbika  ۖ  Lahu Mā Bayna 'Aydīnā Wa Mā Khalfanā Wa Mā Bayna Dhālika  ۚ  Wa Mā Kāna Rabbuka Nasīyāan 019-064 (Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.  ۖ   ۚ 
Rabbu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā Fā`bud/hu Wa Aşţabir Li`ibādatihi  ۚ  Hal Ta`lamu Lahu Samīyāan 019-065 Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara a gare shi?  ۚ 
Wa Yaqūlu Al-'Insānu 'A'idhā Mā Mittu Lasawfa 'Ukhraju Ĥayyāan 019-066 Kuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai?"
'Awalā Yadhkuru Al-'Insānu 'Annā Khalaqnāhu Min Qablu Wa Lam Yaku Shay'āan 019-067 Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba?
Fawarabbika Lanaĥshurannahum Wa Ash-Shayāţīna Thumma Lanuĥđirannahum Ĥawla Jahannama Jithīyāan 019-068 To, Munã rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne.
Thumma Lananzi`anna Min Kulli Shī`atin 'Ayyuhum 'Ashaddu `Alá Ar-Raĥmāni `Itīyāan 019-069 Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya.
Thumma Lanaĥnu 'A`lamu Bial-Ladhīna Hum 'Awlá Bihā Şilīyāan 019-070 Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗanda suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita.
Wa 'In Minkum 'Illā Wa Ariduhā  ۚ  Kāna `Alá Rabbika Ĥatmāan Maqđīyāan 019-071 Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata. Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce.  ۚ 
Thumma Nunajjī Al-Ladhīna Attaqaw Wa Nadharu Až-Žālimīna Fīhā Jithīyāan 019-072 Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne.
Wa 'Idhā Tutlá `Alayhim 'Āyātunā Bayyinātin Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lilladhīna 'Āmanū 'Ayyu Al-Farīqayni Khayrun Maqāmāan Wa 'Aĥsanu Nadīyāan 019-073 Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?"
Wa Kam 'Ahlaknā Qablahum Min Qarnin Hum 'Aĥsanu 'Athāthāan Wa Ri'yāan 019-074 Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã.
Qul Man Kāna Fī Ađ-Đalālati Falyamdud Lahu Ar-Raĥmānu Maddāan  ۚ  Ĥattá 'Idhā Ra'aw Mā Yū`adūna 'Immā Al-`Adhāba Wa 'Immā As-Sā`ata Fasaya`lamūna Man Huwa Sharrun Makānāan Wa 'Ađ`afu Junan 019-075 Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna!"  ۚ 
Wa Yazīdu Al-Lahu Al-Ladhīna Ahtadaw Hudáan Wa  ۗ  Al-Bāqiyātu Aş-Şāliĥātu Khayrun `Inda Rabbika Thawābāan Wa Khayrun Maraddāan 019-076 Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma.  ۗ 
'Afara'ayta Al-Ladhī Kafara Bi'āyātinā Wa Qāla La'ūtayanna Mālāan Wa Waladāan 019-077 Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?"
'Āţţala`a Al-Ghayba 'Am Attakhadha `Inda Ar-Raĥmāni `Ahdāan 019-078 Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?
Kallā  ۚ  Sanaktubu Mā Yaqūlu Wa Namuddu Lahu Mina Al-`Adhābi Maddāan 019-079 Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa.  ۚ 
Wa Narithuhu Mā Yaqūlu Wa Ya'tīnā Fardāan 019-080 Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai.
Wa Attakhadhū Min Dūni Al-Lahi 'Ālihatan Liyakūnū Lahum `Izzāan 019-081 Kuma suka riƙi gumãka, baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.
Kallā  ۚ  Sayakfurūna Bi`ibādatihim Wa Yakūnūna `Alayhim Điddāan 019-082 Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.  ۚ 
'Alam Tara 'Annā 'Arsalnā Ash-Shayāţīna `Alá Al-Kāfirīna Ta'uuzzuhum 'Azzāan 019-083 Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?
Falā Ta`jal `Alayhim  ۖ  'Innamā Na`uddu Lahum `Addāan 019-084 Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar ajali ne kawai, ƙidãyãwa.  ۖ 
Yawma Naĥshuru Al-Muttaqīna 'Ilá Ar-Raĥmāni Wafdāan 019-085 A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma.
Wa Nasūqu Al-Mujrimīna 'Ilá Jahannama Wiran 019-086 Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa.
Lā Yamlikūna Ash-Shafā`ata 'Illā Mani Attakhadha `Inda Ar-Raĥmāni `Ahdāan 019-087 Ba su mal1akar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama.
Wa Qālū Attakhadha Ar-Raĥmānu Waladāan 019-088 Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã!"
Laqad Ji'tum Shay'āan 'Iddāan 019-089 Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni.
Takādu As-Samāwātu Yatafaţţarna Minhu Wa Tanshaqqu Al-'Arđu Wa Takhirru Al-Jibālu Haddāan 019-090 Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu.
'An Da`aw Lilrraĥmani Waladāan 019-091 Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama.
Wa Mā Yanbaghī Lilrraĥmani 'An Yattakhidha Waladāan 019-092 Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã.
'In Kullu Man As-Samāwāti Wa Al-'Arđi 'Illā 'Ā Ar-Raĥmāni `Aban 019-093 Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã.
Laqad 'Aĥşāhum Wa `Addahum `Addāan 019-094 Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya.
Wa Kulluhum 'Ātīhi Yawma Al-Qiyāmati Fardāan 019-095 Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai.
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Sayaj`alu Lahumu Ar-Raĥmānu Wuddāan 019-096 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so.
Fa'innamā Yassarnāhu Bilisānika Litubashshira Bihi Al-Muttaqīna Wa Tundhira Bihi Qawmāan Luddāan 019-097 Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma.
Wa Kam 'Ahlaknā Qablahum Min Qarnin Hal Tuĥissu Minhum Min 'Aĥadin 'Aw Tasma`u Lahum Rikzāan 019-098 Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu?
Next Sūrah