'Alif-Lām-Rā Tilka 'Āyātu Al-Kitābi Wa Qur'ānin Mubīnin    |    َ015-001 A. L̃. R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.  |    أَلِف-لَام-رَا تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ وَقُرْآن ٍ  ۚ  مُبِين ٍ  |  
    Rubamā Yawaddu Al-Ladhīna Kafarū Law Kānū Muslimīna    |    َ015-002 Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.  |    رُبَمَا يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْ كَانُوا مُسْلِمِينَ  |  
    Dharhum Ya'kulū Wa Yatamatta`ū Wa Yulhihimu Al-'Amalu  ۖ  Fasawfa Ya`lamūna    |    َ015-003 Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.  |    ذَرْهُمْ يَأْكُلُوا وَيَتَمَتَّعُوا وَيُلْهِهِمُ الأَمَلُ  ۖ  فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ  |  
     Wa Mā 'Ahlaknā Min Qaryatin 'Illā Wa Lahā Kitābun Ma`lūmun    |    َ015-004 Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.  |    وَمَا أَهْلَكْنَا مِنْ قَرْيَة ٍ إِلاَّ وَلَهَا كِتَاب ٌ مَعْلُوم ٌ  |  
    Mā Tasbiqu Min 'Ummatin 'Ajalahā Wa Mā Yasta'khirūna    |    َ015-005 Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.  |    مَا تَسْبِقُ مِنْ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسْتَأْخِرُونَ  |  
     Wa Qālū Yā 'Ayyuhā Al-Ladhī Nuzzila `Alayhi Adh-Dhikru 'Innaka Lamajnūnun    |    َ015-006 Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."  |    وَقَالُوا يَا أَيُّهَا الَّذِي نُزِّلَ عَلَيْهِ الذِّكْرُ إِنَّكَ لَمَجْنُون ٌ  |  
    Law Mā Ta'tīnā Bil-Malā'ikati 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna    |    َ015-007 "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"  |    لَوْ مَا تَأْتِينَا بِالْمَلاَئِكَةِ إِنْ كُنْتَ مِنَ الصَّادِقِينَ  |  
    Mā Nunazzilu Al-Malā'ikata 'Illā Bil-Ĥaqqi Wa Mā Kānū 'Idhāan Munžarīna    |    َ015-008 Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya, bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.  |    مَا نُنَزِّلُ الْمَلاَئِكَةَ إِلاَّ بِالْحَقِّ وَمَا كَانُوا إِذا ً مُنْظَرِينَ  |  
    'Innā Naĥnu Nazzalnā Adh-Dhikra Wa 'Innā Lahu Laĥāfižūna    |    َ015-009 Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.  |    إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإِنَّا لَه ُُ لَحَافِظُونَ  |  
     Wa Laqad 'Arsalnā Min Qablika Fī Shiya`i Al-'Awwalīna    |    َ015-010 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka.  |    وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ فِي شِيَعِ الأَوَّلِينَ  |  
     Wa Mā Ya'tīhim Min Rasūlin 'Illā Kānū Bihi Yastahzi'ūna    |    َ015-011 Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.  |    وَمَا يَأْتِيهِمْ مِنْ رَسُول ٍ إِلاَّ كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُونَ  |  
    Kadhālika Naslukuhu Fī Qulūbi Al-Mujrimīna    |    َ015-012 Kamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.  |    كَذَلِكَ نَسْلُكُه ُُ فِي قُلُوبِ الْمُجْرِمِينَ  |  
    Lā Yu'uminūna Bihi  ۖ  Wa Qad Khalat Sunnatu Al-'Awwalīna    |    َ015-013 Bã su yin ĩmãni da shi, kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.  |    لاَ يُؤْمِنُونَ بِه ِِ  ۖ  وَقَدْ خَلَتْ سُنَّةُ الأَوَّلِينَ  |  
     Wa Law Fataĥnā `Alayhim Bābāan Mina As-Samā'i Fažallū Fīhi Ya`rujūna    |    َ015-014 Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.  |    وَلَوْ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَابا ً مِنَ السَّمَاءِ فَظَلُّوا فِيه ِِ يَعْرُجُونَ  |  
    Laqālū 'Innamā Sukkirat 'Abşārunā Bal Naĥnu Qawmun Masĥūrūna    |    َ015-015 Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."  |    لَقَالُوا إِنَّمَا سُكِّرَتْ أَبْصَارُنَا بَلْ نَحْنُ قَوْم ٌ مَسْحُورُونَ  |  
     Wa Laqad Ja`alnā Fī As-Samā'i Burūjāan Wa Zayyannāhā Lilnnāžirīna    |    َ015-016 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.  |    وَلَقَدْ جَعَلْنَا فِي السَّمَاءِ بُرُوجا ً وَزَيَّنَّاهَا لِلنَّاظِرِينَ  |  
     Wa Ĥafižnāhā Min Kulli Shayţānin Rajīmin    |    َ015-017 Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.  |    وَحَفِظْنَاهَا مِنْ كُلِّ شَيْطَان ٍ رَجِيم ٍ  |  
    'Illā Mani Astaraqa As-Sam`a Fa'atba`ahu Shihābun Mubīnun    |    َ015-018 Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.  |    إِلاَّ مَنِ اسْتَرَقَ السَّمْعَ فَأَتْبَعَه ُُ شِهَاب ٌ مُبِين ٌ  |  
    Wa Al-'Arđa Madadnāhā Wa 'Alqaynā Fīhā Rawāsiya Wa 'Anbatnā Fīhā Min Kulli Shay'in Mawzūnin    |    َ015-019 Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.  |    وَالأَرْضَ مَدَدْنَاهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ وَأَنْبَتْنَا فِيهَا مِنْ كُلِّ شَيْء ٍ مَوْزُون ٍ  |  
     Wa Ja`alnā Lakum Fīhā Ma`āyisha Wa Man Lastum Lahu Birāziqīna    |    َ015-020 Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.  |    وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ وَمَنْ لَسْتُمْ لَه ُُ بِرَازِقِينَ  |  
     Wa 'In Min Shay'in 'Illā `Indanā Khazā'inuhu Wa Mā Nunazziluhu 'Illā Biqadarin Ma`lūmin    |    َ015-021 Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.  |    وَإِنْ مِنْ شَيْء ٍ إِلاَّ عِنْدَنَا خَزَائِنُه ُُ وَمَا نُنَزِّلُهُ~ُ إِلاَّ بِقَدَر ٍ مَعْلُوم ٍ  |  
     Wa 'Arsalnā Ar-Riyāĥa Lawāqiĥa Fa'anzalnā Mina As-Samā'i Mā'an Fa'asqaynākumūhu Wa Mā 'Antum Lahu Bikhāzinīna    |    َ015-022 Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.  |    وَأَرْسَلْنَا الرِّيَاحَ لَوَاقِحَ فَأَنْزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَأَسْقَيْنَاكُمُوه ُُ وَمَا أَنْتُمْ لَه ُُ بِخَازِنِينَ  |  
     Wa 'Innā Lanaĥnu Nuĥyī Wa Numītu Wa Naĥnu Al-Wārithūna    |    َ015-023 Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.  |    وَإِنَّا لَنَحْنُ نُحْيِي وَنُمِيتُ وَنَحْنُ الْوَارِثُونَ  |  
     Wa Laqad `Alimnā Al-Mustaqdimīna Minkum Wa Laqad `Alimnā Al-Musta'khirīna    |    َ015-024 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.  |    وَلَقَدْ عَلِمْنَا الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنْكُمْ وَلَقَدْ عَلِمْنَا الْمُسْتَأْخِرِينَ  |  
     Wa 'Inna Rabbaka Huwa Yaĥshuruhum  ۚ  'Innahu Ĥakīmun `Alīmun    |    َ015-025 Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.  |    وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحْشُرُهُمْ  ۚ  إِنَّه ُُ حَكِيمٌ عَلِيم ٌ  |  
     Wa Laqad Khalaqnā Al-'Insāna Min Şalşālin Min Ĥama'iin Masnūnin    |    َ015-026 Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.  |    وَلَقَدْ خَلَقْنَا الإِنسَانَ مِنْ صَلْصَال ٍ مِنْ حَمَإ ٍ مَسْنُون ٍ  |  
    Wa Al-Jānna Khalaqnāhu Min Qablu Min Nāri As-Samūmi    |    َ015-027 Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar iskar zafi.  |    وَالْجَانَّ خَلَقْنَاه ُُ مِنْ قَبْلُ مِنْ نَارِ السَّمُومِ  |  
     Wa 'Idh Qāla Rabbuka Lilmalā'ikati 'Innī Khāliqun Basharāan Min Şalşālin Min Ĥama'iin Masnūnin    |    َ015-028 Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."  |    وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلاَئِكَةِ إِنِّي خَالِق ٌ بَشَرا ً مِنْ صَلْصَال ٍ مِنْ حَمَإ ٍ مَسْنُون ٍ  |  
    Fa'idhā Sawwaytuhu Wa Nafakhtu Fīhi Min Rūĥī Faqa`ū Lahu Sājidīna    |    َ015-029 "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."  |    فَإِذَا سَوَّيْتُه ُُ وَنَفَخْتُ فِيه ِِ مِنْ رُوحِي فَقَعُوا لَه ُُ سَاجِدِينَ  |  
    Fasajada Al-Malā'ikatu Kulluhum 'Ajma`ūna    |    َ015-030 Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.  |    فَسَجَدَ الْمَلاَئِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ  |  
    'Illā 'Iblīsa 'Abá 'An Yakūna Ma`a As-Sājidīna    |    َ015-031 Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.  |    إِلاَّ إِبْلِيسَ أَبَى أَنْ يَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَ  |  
    Qāla Yā 'Iblīsu Mā Laka 'Allā Takūna Ma`a As-Sājidīna    |    َ015-032 Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"  |    قَالَ يَا إِبْلِيسُ مَا لَكَ أَلاَّ تَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَ  |  
    Qāla Lam 'Akun Li'sjuda Libasharin Khalaqtahu Min Şalşālin Min Ĥama'iin Masnūnin    |    َ015-033 Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."  |    قَالَ لَمْ أَكُنْ لِأسْجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقْتَه ُُ مِنْ صَلْصَال ٍ مِنْ حَمَإ ٍ مَسْنُون ٍ  |  
    Qāla Fākhruj Minhā Fa'innaka Rajīmun    |    َ015-034 Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."  |    قَالَ فَاخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيم ٌ  |  
     Wa 'Inna `Alayka Al-La`nata 'Ilá Yawmi Ad-Dīni    |    َ015-035 "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."  |    وَإِنَّ عَلَيْكَ اللَّعْنَةَ إِلَى يَوْمِ الدِّينِ  |  
    Qāla Rabbi Fa'anžirnī 'Ilá Yawmi Yub`athūna    |    َ015-036 Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."  |    قَالَ رَبِّ فَأَنْظِرْنِي إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ  |  
    Qāla Fa'innaka Mina Al-Munžarīna    |    َ015-037 Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."  |    قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ الْمُنْظَرِينَ  |  
    'Ilá Yawmi Al-Waqti Al-Ma`lūmi    |    َ015-038 "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne."  |    إِلَى يَوْمِ الْوَقْتِ الْمَعْلُومِ  |  
    Qāla Rabbi Bimā 'Aghwaytanī La'uzayyinanna Lahum Fī Al-'Arđi Wa La'ughwiyannahum 'Ajma`īna    |    َ015-039 Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."  |    قَالَ رَبِّ بِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِي الأَرْضِ وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ  |  
    'Illā `Ibādaka Minhumu Al-Mukhlaşīna    |    َ015-040 "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."  |    إِلاَّ عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ  |  
    Qāla Hādhā Şirāţun `Alayya Mustaqīmun    |    َ015-041 Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."  |    قَالَ هَذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيم ٌ  |  
    'Inna `Ibādī Laysa Laka `Alayhim Sulţānun 'Illā Mani Attaba`aka Mina Al-Ghāwīna    |    َ015-042 "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."  |    إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَان ٌ إِلاَّ مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْغَاوِينَ  |  
     Wa 'Inna Jahannama Lamaw`iduhum 'Ajma`īna    |    َ015-043 Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabã ɗaya.  |    وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوْعِدُهُمْ أَجْمَعِينَ  |  
    Lahā Sab`atu 'Abwābin Likulli Bābin Minhum Juz'un Maqsūmun    |    َ015-044 Tanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.  |    لَهَا سَبْعَةُ أَبْوَاب ٍ لِكُلِّ بَاب ٍ مِنْهُمْ جُزْء ٌ مَقْسُوم ٌ  |  
    'Inna Al-Muttaqīna Fī Jannātin Wa `Uyūnin    |    َ015-045 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.  |    إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّات ٍ وَعُيُون ٍ  |  
    Adkhulūhā Bisalāmin 'Āminīna    |    َ015-046 "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."  |    ادْخُلُوهَا بِسَلاَم ٍ آمِنِينَ  |  
     Wa Naza`nā Mā Fī Şudūrihim Min Ghillin 'Ikhwānāan `Alá Sururin Mutaqābilīna    |    َ015-047 Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.  |    وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِمْ مِنْ غِلّ ٍ إِخْوَاناً عَلَى سُرُر ٍ مُتَقَابِلِينَ  |  
    Lā Yamassuhum Fīhā Naşabun Wa Mā Hum Minhā Bimukhrajīna    |    َ015-048 Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba.  |    لاَ يَمَسُّهُمْ فِيهَا نَصَب ٌ وَمَا هُمْ مِنْهَا بِمُخْرَجِينَ  |  
    Nabbi' `Ibādī 'Annī 'Anā Al-Ghafūru Ar-Raĥīmu    |    َ015-049 Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.  |    نَبِّئْ عِبَادِي أَنِّي أَنَا الْغَفُورُ الرَّحِيمُ  |  
     Wa 'Anna `Adhābī Huwa Al-`Adhābu Al-'Alīmu    |    َ015-050 Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi.  |    وَأَنَّ عَذَابِي هُوَ الْعَذَابُ الأَلِيمُ  |  
     Wa Nabbi'hum `An Đayfi 'Ibrāhīma    |    َ015-051 Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.  |    وَنَبِّئْهُمْ عَنْ ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَ  |  
    'Idh Dakhalū `Alayhi Faqālū Salāmāan Qāla 'Innā Minkum Wajilūna    |    َ015-052 A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."  |    إِذْ دَخَلُوا عَلَيْهِ فَقَالُوا سَلاَما ً قَالَ إِنَّا مِنْكُمْ وَجِلُونَ  |  
    Qālū Lā Tawjal 'Innā Nubashshiruka Bighulāmin `Alīmin    |    َ015-053 Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."  |    قَالُوا لاَ تَوْجَلْ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلاَمٍ عَلِيم ٍ  |  
    Qāla 'Abashshartumūnī `Alá 'An Massaniya Al-Kibaru Fabima Tubashshirūna    |    َ015-054 Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"  |    قَالَ أَبَشَّرْتُمُونِي عَلَى أَنْ مَسَّنِيَ الْكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَ  |  
    Qālū Bashsharnāka Bil-Ĥaqqi Falā Takun Mina Al-Qāniţīna    |    َ015-055 Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."  |    قَالُوا بَشَّرْنَاكَ بِالْحَقِّ فَلاَ تَكُنْ مِنَ الْقَانِطِينَ  |  
    Qāla Wa Man Yaqnaţu Min Raĥmati Rabbihi 'Illā Ađ-Đāllūna    |    َ015-056 Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?"  |    قَالَ وَمَنْ يَقْنَطُ مِنْ رَحْمَةِ رَبِّهِ~ِ إِلاَّ الضَّالُّونَ  |  
    Qāla Famā Khaţbukum 'Ayyuhā Al-Mursalūna    |    َ015-057 Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!"  |    قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا الْمُرْسَلُونَ  |  
    Qālū 'Innā 'Ursilnā 'Ilá Qawmin Mujrimīna    |    َ015-058 Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."  |    قَالُوا إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَى قَوْم ٍ مُجْرِمِينَ  |  
    'Illā 'Āla Lūţin 'Innā Lamunajjūhum 'Ajma`īna    |    َ015-059 "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ,haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."  |    إِلاَّ آلَ لُوط ٍ إِنَّا لَمُنَجُّوهُمْ أَجْمَعِينَ  |  
    'Illā Amra'atahu Qaddarnā  ۙ  'Innahā Lamina Al-Ghābirīna    |    َ015-060 "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."  |    إِلاَّ امْرَأَتَه ُُ قَدَّرْنَا  ۙ  إِنَّهَا لَمِنَ الْغَابِرِينَ  |  
    Falammā Jā'a 'Āla Lūţin Al-Mursalūna    |    َ015-061 To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,  |    فَلَمَّا جَاءَ آلَ لُوط ٍ الْمُرْسَلُونَ  |  
    Qāla 'Innakum Qawmun Munkarūna    |    َ015-062 Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."  |    قَالَ إِنَّكُمْ قَوْم ٌ مُنْكَرُونَ  |  
    Qālū Bal Ji'nāka Bimā Kānū Fīhi Yamtarūna    |    َ015-063 Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."  |    قَالُوا بَلْ جِئْنَاكَ بِمَا كَانُوا فِيه ِِ يَمْتَرُونَ  |  
     Wa 'Ataynāka Bil-Ĥaqqi Wa 'Innā Laşādiqūna    |    َ015-064 "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."  |    وَأَتَيْنَاكَ بِالْحَقِّ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ  |  
    Fa'asri Bi'ahlika Biqiţ`in Mina Al-Layli Wa Attabi` 'Adbārahum Wa Lā Yaltafit Minkum 'Aĥadun Wa Amđū Ĥaythu Tu'umarūna    |    َ015-065 "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."  |    فَأَسْرِ بِأَهْلِكَ بِقِطْع ٍ مِنَ اللَّيْلِ وَاتَّبِعْ أَدْبَارَهُمْ وَلاَ يَلْتَفِتْ مِنْكُمْ أَحَد ٌ وَامْضُوا حَيْثُ تُؤْمَرُونَ  |  
     Wa Qađaynā 'Ilayhi Dhālika Al-'Amra 'Anna Dābira Hā'uulā' Maqţū`un Muşbiĥīna    |    َ015-066 Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.  |    وَقَضَيْنَا إِلَيْهِ ذَلِكَ الأَمْرَ أَنَّ دَابِرَ هَاؤُلاَء مَقْطُوع ٌ مُصْبِحِينَ  |  
     Wa Jā'a 'Ahlu Al-Madīnati Yastabshirūna    |    َ015-067 Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.  |    وَجَاءَ أَهْلُ الْمَدِينَةِ يَسْتَبْشِرُونَ  |  
    Qāla 'Inna Hā'uulā' Đayfī Falā Tafđaĥūni    |    َ015-068 Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."  |    قَالَ إِنَّ هَاؤُلاَء ضَيْفِي فَلاَ تَفْضَحُونِ  |  
     Wa Attaqū Al-Laha Wa Lā Tukhzūni    |    َ015-069 "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."  |    وَاتَّقُوا اللَّهَ وَلاَ تُخْزُونِ  |  
    Qālū 'Awalam Nanhaka `Ani Al-`Ālamīna    |    َ015-070 Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"  |    قَالُوا أَوَلَمْ نَنْهَكَ عَنِ الْعَالَمِينَ  |  
    Qāla Hā'uulā' Banātī 'In Kuntum Fā`ilīna    |    َ015-071 Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."  |    قَالَ هَاؤُلاَء بَنَاتِي إِنْ كُنْتُمْ فَاعِلِينَ  |  
    La`amruka 'Innahum Lafī Sakratihim Ya`mahūna    |    َ015-072 Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.  |    لَعَمْرُكَ إِنَّهُمْ لَفِي سَكْرَتِهِمْ يَعْمَهُونَ  |  
    Fa'akhadhat/humu Aş-Şayĥatu Mushriqīna    |    َ015-073 Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.  |    فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُشْرِقِينَ  |  
    Faja`alnā `Āliyahā Sāfilahā Wa 'Amţarnā `Alayhim Ĥijāratan Min Sijjīlin    |    َ015-074 Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.  |    فَجَعَلْنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ حِجَارَة ً مِنْ سِجِّيل ٍ  |  
    'Inna Fī Dhālika La'āyātin Lilmutawassimīna    |    َ015-075 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.  |    إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِلْمُتَوَسِّمِينَ  |  
     Wa 'Innahā Labisabīlin Muqīmin    |    َ015-076 Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.  |    وَإِنَّهَا لَبِسَبِيل ٍ مُقِيم ٍ  |  
    'Inna Fī Dhālika La'āyatan Lilmu'uminīna    |    َ015-077 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.  |    إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِلْمُؤْمِنِينَ  |  
     Wa 'In Kāna 'Aşĥābu Al-'Aykati Lažālimīna    |    َ015-078 Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!  |    وَإِنْ كَانَ أَصْحَابُ الأَيْكَةِ لَظَالِمِينَ  |  
    Fāntaqamnā Minhum Wa 'Innahumā Labi'imāmin Mubīnin    |    َ015-079 Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.  |    فَانْتَقَمْنَا مِنْهُمْ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَام ٍ مُبِين ٍ  |  
     Wa Laqad Kadhdhaba 'Aşĥābu Al-Ĥijri Al-Mursalīna    |    َ015-080 Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni.  |    وَلَقَدْ كَذَّبَ أَصْحَابُ الْحِجْرِ الْمُرْسَلِينَ  |  
     Wa 'Ātaynāhum 'Āyātinā Fakānū `Anhā Mu`riđīna    |    َ015-081 Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.  |    وَآتَيْنَاهُمْ آيَاتِنَا فَكَانُوا عَنْهَا مُعْرِضِينَ  |  
     Wa Kānū Yanĥitūna Mina Al-Jibāli Buyūtāan 'Āminīna    |    َ015-082 Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.  |    وَكَانُوا يَنْحِتُونَ مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتا ً آمِنِينَ  |  
    Fa'akhadhat/humu Aş-Şayĥatu Muşbiĥīna    |    َ015-083 Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.  |    فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُصْبِحِينَ  |  
    Famā 'Aghná `Anhum Mā Kānū Yaksibūna    |    َ015-084 Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.  |    فَمَا أَغْنَى عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَكْسِبُونَ  |  
     Wa Mā Khalaqnā As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā 'Illā Bil-Ĥaqqi  ۗ  Wa 'Inna As-Sā`ata La'ātiyatun  ۖ  Fāşfaĥi Aş-Şafĥa Al-Jamīla    |    َ015-085 Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.  |    وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلاَّ بِالْحَقِّ  ۗ  وَإِنَّ السَّاعَةَ لَآتِيَة ٌ  ۖ  فَاصْفَحِ الصَّفْحَ الْجَمِيلَ  |  
    'Inna Rabbaka Huwa Al-Khallāqu Al-`Alīmu    |    َ015-086 Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.  |    إِنَّ رَبَّكَ هُوَ الْخَلاَّقُ الْعَلِيمُ  |  
     Wa Laqad 'Ātaynāka Sab`āan Mina Al-Mathānī Wa Al-Qur'āna Al-`Ažīma    |    َ015-087 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur'ãni mai girma.  |    وَلَقَدْ آتَيْنَاكَ سَبْعا ً مِنَ الْمَثَانِي وَالْقُرْآنَ الْعَظِيمَ  |  
    Lā Tamuddanna `Aynayka 'Ilá Mā Matta`nā Bihi 'Azwājāan Minhum Wa Lā Taĥzan `Alayhim Wa Akhfiđ Janāĥaka Lilmu'uminīna    |    َ015-088 Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.  |    لاَ تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَى مَا مَتَّعْنَا بِهِ~ِ أَزْوَاجا ً مِنْهُمْ وَلاَ تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَاخْفِضْ جَنَاحَكَ لِلْمُؤْمِنِينَ  |  
     Wa Qul 'Innī 'Anā An-Nadhīru Al-Mubīnu    |    َ015-089 Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne."  |    وَقُلْ إِنِّي أَنَا النَّذِيرُ الْمُبِينُ  |  
    Kamā 'Anzalnā `Alá Al-Muqtasimīna    |    َ015-090 Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,  |    كَمَا أَنْزَلْنَا عَلَى الْمُقْتَسِمِينَ  |  
    Al-Ladhīna Ja`alū Al-Qur'āna `Iđīna    |    َ015-091 Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.  |    الَّذِينَ جَعَلُوا الْقُرْآنَ عِضِينَ  |  
    Fawarabbika Lanas'alannahum 'Ajma`īna    |    َ015-092 To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.  |    فَوَرَبِّكَ لَنَسْأَلَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ  |  
    `Ammā Kānū Ya`malūna    |    َ015-093 Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.  |    عَمَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ  |  
    Fāşda` Bimā Tu'umaru Wa 'A`riđ `Ani Al-Mushrikīna    |    َ015-094 Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.  |    فَاصْدَعْ بِمَا تُؤْمَرُ وَأَعْرِضْ عَنِ الْمُشْرِكِينَ  |  
    'Innā Kafaynāka Al-Mustahzi'īna    |    َ015-095 Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili.  |    إِنَّا كَفَيْنَاكَ الْمُسْتَهْزِئِينَ  |  
    Al-Ladhīna Yaj`alūna Ma`a Al-Lahi 'Ilahāan 'Ākhara  ۚ  Fasawfa Ya`lamūna    |    َ015-096 Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.  |    الَّذِينَ يَجْعَلُونَ مَعَ اللَّهِ إِلَها ً آخَرَ  ۚ  فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ  |  
     Wa Laqad Na`lamu 'Annaka Yađīqu Şadruka Bimā Yaqūlūna    |    َ015-097 Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).  |    وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدْرُكَ بِمَا يَقُولُونَ  |  
    Fasabbiĥ Biĥamdi Rabbika Wa Kun Mina As-Sājidīna    |    َ015-098 Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.  |    فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَكُنْ مِنَ السَّاجِدِينَ  |  
     Wa A`bud Rabbaka Ĥattá Ya'tiyaka Al-Yaqīnu    |    َ015-099 Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.  |    وَاعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّى يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ  |