16) Sūrat An-Naĥl

Printed format

16) سُورَة النَّحل

'Atá 'Amru Al-Lahi Falā Tasta`jilūhu Subĥānahu Wa Ta`ālá `Ammā Yushrikūna َ016-001 Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka. أَتَى أَمْرُ اللَّهِ فَلاَ تَسْتَعْجِلُوه ُُ سُبْحَانَه ُُ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ
Yunazzilu Al-Malā'ikata Bir-Rūĥi Min 'Amrihi `Alá Man Yashā'u Min `Ibādihi 'An 'Andhirū 'Annahu Lā 'Ilāha 'Illā 'Anā Fa Attaqūni َ016-002 Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa. يُنَزِّلُ الْمَلاَئِكَةَ بِالرُّوحِ مِنْ أَمْرِه ِِ عَلَى مَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ~ِ أَنْ أَنذِرُوا أَنَّهُ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ أَنَا فَاتَّقُونِ
Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Bil-Ĥaqqi  ۚ  Ta`ālá `Ammā Yushrikūna َ016-003 Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka. خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِالْحَقِّ  ۚ  تَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ
Khalaqa Al-'Insāna Min Nuţfatin Fa'idhā Huwa Khīmun Mubīnun َ016-004 Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya. خَلَقَ الإِنسَانَ مِنْ نُطْفَة ٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيم ٌ مُبِين ٌ
Wa Al-'An`āma  ۗ  Khalaqahā Lakum Fīhā Dif'un Wa Manāfi`u Wa Minhā Ta'kulūna َ016-005 Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci. وَالأَنعَامَ خَلَقَهَا  ۗ  لَكُمْ فِيهَا دِفْء ٌ وَمَنَافِعُ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
Wa Lakum Fīhā Jamālun Ĥīna Turīĥūna Wa Ĥīna Tasraĥūna َ016-006 Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã. وَلَكُمْ فِيهَا جَمَالٌ حِينَ تُرِيحُونَ وَحِينَ تَسْرَحُونَ
Wa Taĥmilu 'Athqālakum 'Ilá Baladin Lam Takūnū Bālighīhi 'Illā Bishiqqi Al-'Anfusi  ۚ  'Inna Rabbakum Lara'ūfun Raĥīmun َ016-007 Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai. وَتَحْمِلُ أَثْقَالَكُمْ إِلَى بَلَد ٍ لَمْ تَكُونُوا بَالِغِيهِ~ِ إِلاَّ بِشِقِّ الأَنفُسِ  ۚ  إِنَّ رَبَّكُمْ لَرَءُوف ٌ رَحِيم ٌ
Wa Al-Khayla Wa Al-Bighāla Wa Al-Ĥamīra Litarkabūhā  ۚ  Wa Zīnatan Wa Yakhluqu Mā Lā Ta`lamūna َ016-008 Kuma da dawãki da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba. وَالْخَيْلَ وَالْبِغَالَ وَالْحَمِيرَ لِتَرْكَبُوهَا وَزِينَة ً  ۚ  وَيَخْلُقُ مَا لاَ تَعْلَمُونَ
Wa `Alá Al-Lahi Qaşdu As-Sabīli Wa Minhā Jā'irun  ۚ  Wa Law Shā'a Lahadākum 'Ajma`īna َ016-009 Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya. وَعَلَى اللَّهِ قَصْدُ السَّبِيلِ وَمِنْهَا جَائِر ٌ  ۚ  وَلَوْ شَاءَ لَهَدَاكُمْ أَجْمَعِينَ
Huwa Al-Ladhī 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an  ۖ  Lakum Minhu Sharābun Wa Minhu Shajarun Fīhi Tusīmūna َ016-010 Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo. هُوَ الَّذِي أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً  ۖ  لَكُمْ مِنْهُ شَرَاب ٌ وَمِنْهُ شَجَر ٌ فِيه ِِ تُسِيمُونَ
Yunbitu Lakum Bihi Az-Zar`a Wa Az-Zaytūna Wa An-Nakhīla Wa Al-'A`nāba Wa Min Kulli Ath-Thamarāti  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Liqawmin Yatafakkarūna َ016-011 Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. يُنْبِتُ لَكُمْ بِهِ الزَّرْعَ وَالزَّيْتُونَ وَالنَّخِيلَ وَالأَعْنَابَ وَمِنْ كُلِّ الثَّمَرَاتِ  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِقَوْم ٍ يَتَفَكَّرُونَ
Wa Sakhkhara Lakumu Al-Layla Wa An-Nahāra Wa Ash-Shamsa Wa Al-Qamara Wa  ۖ  An-Nujūmu Musakhkharātun Bi'amrihi  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Ya`qilūna َ016-012 Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta. وَسَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ  ۖ  وَالنُّجُومُ مُسَخَّرَات ٌ بِأَمْرِهِ~ِ  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِقَوْم ٍ يَعْقِلُونَ
Wa Mā Dhara'a Lakum Al-'Arđi Mukhtalifāan 'Alwānuhu  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Liqawmin Yadhdhakkarūna َ016-013 Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa. وَمَا ذَرَأَ لَكُمْ فِي الأَرْضِ مُخْتَلِفاً أَلْوَانُهُ~ُ  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِقَوْم ٍ يَذَّكَّرُونَ
Wa Huwa Al-Ladhī Sakhkhara Al-Baĥra Lita'kulū Minhu Laĥmāan Ţarīyāan Wa Tastakhrijū Minhu Ĥilyatan Talbasūnahā Wa Tará Al-Fulka Mawākhira Fīhi Wa Litabtaghū Min Fađlihi Wa La`allakum Tashkurūna َ016-014 Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa. وَهُوَ الَّذِي سَخَّرَ الْبَحْرَ لِتَأْكُلُوا مِنْهُ لَحْما ً طَرِيّا ً وَتَسْتَخْرِجُوا مِنْهُ حِلْيَة ً تَلْبَسُونَهَا وَتَرَى الْفُلْكَ مَوَاخِرَ فِيه ِِ وَلِتَبْتَغُوا مِنْ فَضْلِه ِِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Wa 'Alqá Fī Al-'Arđi Rawāsiya 'An Tamīda Bikum Wa 'Anhārāan Wa Subulāan Lla`allakum Tahtadūna َ016-015 Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãninku kunã shiryuwa. وَأَلْقَى فِي الأَرْضِ رَوَاسِيَ أَنْ تَمِيدَ بِكُمْ وَأَنْهَارا ً وَسُبُلا ً لَّعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
Wa `Alāmātin  ۚ  Wa Bin-Najmi Hum Yahtadūna َ016-016 Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci). وَعَلاَمَات ٍ  ۚ  وَبِالنَّجْمِ هُمْ يَهْتَدُونَ
'Afaman Yakhluqu Kaman Lā Yakhluqu  ۗ  'Afalā Tadhakkarūna َ016-017 Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa? أَفَمَنْ يَخْلُقُ كَمَنْ لاَ يَخْلُقُ  ۗ  أَفَلاَ تَذَكَّرُونَ
Wa 'In Ta`uddū Ni`mata Al-Lahi Lā Tuĥşūhā  ۗ  'Inna Al-Laha Laghafūrun Raĥīmun َ016-018 Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. وَإِنْ تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللَّهِ لاَ تُحْصُوهَا  ۗ  إِنَّ اللَّهَ لَغَفُور ٌ رَحِيم ٌ
Wa Allāhu Ya`lamu Mā Tusirrūna Wa Mā Tu`linūna َ016-019 Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke asirtãwa da abin da kuke bayyanãwa. وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعْلِنُونَ
Wa Al-Ladhīna Yad`ūna Min Dūni Al-Lahi Lā Yakhluqūna Shay'āan Wa Hum Yukhlaqūna َ016-020 Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kõme ba, kuma sũ ne ake halittawa. وَالَّذِينَ يَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ لاَ يَخْلُقُونَ شَيْئا ً وَهُمْ يُخْلَقُونَ
'Amwātun Ghayru 'Aĥyā'in  ۖ  Wa Mā Yash`urūna 'Ayyāna Yub`athūna َ016-021 Matattũ ne, bã su da rai, kuma ba su san a wane lõkaci ake tãyar da su ba. أَمْوَاتٌ غَيْرُ أَحْيَاء ٍ  ۖ  وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
'Ilahukum 'Ilahun Wāĥidun  ۚ  Fa-Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati Qulūbuhum Munkiratun Wa Hum Mustakbirūna َ016-022 Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne. إِلَهُكُمْ إِلَه ٌ ٌ وَاحِد ٌ  ۚ  فَالَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ قُلُوبُهُمْ مُنكِرَة ٌ وَهُمْ مُسْتَكْبِرُونَ
Lā Jarama 'Anna Al-Laha Ya`lamu Mā Yusirrūna Wa Mā Yu`linūna  ۚ  'Innahu Lā Yuĥibbu Al-Mustakbirīna َ016-023 Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai. لاَ جَرَمَ أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ  ۚ  إِنَّهُ لاَ يُحِبُّ الْمُسْتَكْبِرِينَ
Wa 'Idhā Qīla Lahumdhā 'Anzala Rabbukum  ۙ  Qālū 'Asāţīru Al-'Awwalīna َ016-024 Idan aka ce musu: "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tãtsũniyõyin mutãnen farko." وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ مَاذَا أَنزَلَ رَبُّكُمْ  ۙ  قَالُوا أَسَاطِيرُ الأَوَّلِينَ
Liyaĥmilū 'Awzārahum Kāmilatan Yawma Al-Qiyāmati  ۙ  Wa Min 'Awzāri Al-Ladhīna Yuđillūnahum Bighayri `Ilmin  ۗ  'Alā Sā'a Mā Yazirūna َ016-025 Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana. لِيَحْمِلُوا أَوْزَارَهُمْ كَامِلَة ً يَوْمَ الْقِيَامَةِ  ۙ  وَمِنْ أَوْزَارِ الَّذِينَ يُضِلُّونَهُمْ بِغَيْرِ عِلْمٍ  ۗ  أَلاَ سَاءَ مَا يَزِرُونَ
Qad Makara Al-Ladhīna Min Qablihim Fa'atá Al-Lahu Bunyānahum Mina Al-Qawā`idi Fakharra `Alayhimu As-Saqfu Min Fawqihim Wa 'Atāhumu Al-`Adhābu Min Ĥaythu Lā Yash`urūna َ016-026 Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa, sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba. قَدْ مَكَرَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ فَأَتَى اللَّهُ بُنْيَانَهُمْ مِنَ الْقَوَاعِدِ فَخَرَّ عَلَيْهِمُ السَّقْفُ مِنْ فَوْقِهِمْ وَأَتَاهُمُ الْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لاَ يَشْعُرُونَ
Thumma Yawma Al-Qiyāmati Yukhzīhim Wa Yaqūlu 'Ayna Shurakā'iya Al-Ladhīna Kuntum Tushāqqūna Fīhim  ۚ  Qāla Al-Ladhīna 'Ū Al-`Ilma 'Inna Al-Khizya Al-Yawma Wa As-Sū'a `Alá Al-Kāfirīna َ016-027 Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai." ثُمَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يُخْزِيهِمْ وَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَائِيَ الَّذِينَ كُنْتُمْ تُشَاقُّونَ فِيهِمْ  ۚ  قَالَ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ إِنَّ الْخِزْيَ الْيَوْمَ وَالسُّوءَ عَلَى الْكَافِرِينَ
Al-Ladhīna Tatawaffāhumu Al-Malā'ikatu Žālimī 'Anfusihim  ۖ  Fa'alqaw As-Salama Mā Kunnā Na`malu Min Sū'in  ۚ  Balá 'Inna Al-Laha `Alīmun Bimā Kuntum Ta`malūna َ016-028 Waɗanda malãiku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu zãluntar kansu. Sai suka jẽfa nẽman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa. الَّذِينَ تَتَوَفَّاهُمُ الْمَلاَئِكَةُ ظَالِمِي أَنفُسِهِمْ  ۖ  فَأَلْقَوْا السَّلَمَ مَا كُنَّا نَعْمَلُ مِنْ سُوء ٍ  ۚ  بَلَى إِنَّ اللَّهَ عَلِيم ٌ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ
dkhulū 'Abwāba Jahannama Khālidīna Fīhā  ۖ  Falabi'sa Math Al-Mutakabbirīna َ016-029 Sai ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kunã madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin mãsu girman kai. فَادْخُلُوا أَبْوَابَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا  ۖ  فَلَبِئْسَ مَثْوَى الْمُتَكَبِّرِينَ
Wa Qīla Lilladhīna Attaqaw Mādhā 'Anzala Rabbukum  ۚ  Qālū Khayrāan  ۗ  Lilladhīna 'Aĥsanū Fī Hadhihi Ad-Dunyā Ĥasanatun  ۚ  Wa Ladāru Al-'Ākhirati Khayrun  ۚ  Wa Lani`ma Dāru Al-Muttaqīna َ016-030 Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa. وَقِيلَ لِلَّذِينَ اتَّقَوْا مَاذَا أَنْزَلَ رَبُّكُمْ  ۚ  قَالُوا خَيْرا ً  ۗ  لِلَّذِينَ أَحْسَنُوا فِي هَذِهِ الدُّنْيَا حَسَنَة ٌ  ۚ  وَلَدَارُ الآخِرَةِ خَيْر ٌ  ۚ  وَلَنِعْمَ دَارُ الْمُتَّقِينَ
Jannātu `Adnin Yadkhulūnahā Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru  ۖ  Lahum Fīhā Mā Yashā'ūna  ۚ  Kadhālika Yaj Al-Lahu Al-Muttaqīna َ016-031 Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke sãkã wa mãsu taƙawa. جَنَّاتُ عَدْن ٍ يَدْخُلُونَهَا تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ  ۖ  لَهُمْ فِيهَا مَا يَشَاءُونَ  ۚ  كَذَلِكَ يَجْزِي اللَّهُ الْمُتَّقِينَ
Al-Ladhīna Tatawaffāhumu Al-Malā'ikatu Ţayyibīna  ۙ  Yaqūlūna Salāmun `Alaykumu Adkhulū Al-Jannata Bimā Kuntum Ta`malūna َ016-032 Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa." الَّذِينَ تَتَوَفَّاهُمُ الْمَلاَئِكَةُ طَيِّبِينَ  ۙ  يَقُولُونَ سَلاَمٌ عَلَيْكُمُ ادْخُلُوا الْجَنَّةَ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hal Yanžurūna 'Illā 'An Ta'tiyahumu Al-Malā'ikatu 'Aw Ya'tiya 'Amru Rabbika  ۚ  Kadhālika Fa`ala Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  Wa Mā Žalamahumu Al-Lahu Wa Lakin Kānū 'Anfusahum Yažlimūna َ016-033 Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta. هَلْ يَنظُرُونَ إِلاَّ أَنْ تَأْتِيَهُمُ الْمَلاَئِكَةُ أَوْ يَأْتِيَ أَمْرُ رَبِّكَ  ۚ  كَذَلِكَ فَعَلَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ  ۚ  وَمَا ظَلَمَهُمُ اللَّهُ وَلَكِنْ كَانُوا أَنْفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Fa'aşābahum Sayyi'ātu Mā `Amilū Wa Ĥāqa Bihim Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn َ016-034 Sai mũnãnan abũbuwan da suka aikata ya sãme su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu. فَأَصَابَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا عَمِلُوا وَحَاقَ بِهِمْ مَا كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُون
Wa Qāla Al-Ladhīna 'Ashrakū Law Shā'a Al-Lahu Mā `Abadnā Min Dūnihi Min Shay'in Naĥnu Wa Lā 'Ābā'uunā Wa Lā Ĥarramnā Min Dūnihi Min Shay'in  ۚ  Kadhālika Fa`ala Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  Fahal `Alá Ar-Rusuli 'Illā Al-Balāghu Al-Mubīnu َ016-035 Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã? وَقَالَ الَّذِينَ أَشْرَكُوا لَوْ شَاءَ اللَّهُ مَا عَبَدْنَا مِنْ دُونِه ِِ مِنْ شَيْء ٍ نَحْنُ وَلاَ آبَاؤُنَا وَلاَ حَرَّمْنَا مِنْ دُونِه ِِ مِنْ شَيْء ٍ  ۚ  كَذَلِكَ فَعَلَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ  ۚ  فَهَلْ عَلَى الرُّسُلِ إِلاَّ الْبَلاَغُ الْمُبِينُ
Wa Laqad Ba`athnā Fī Kulli 'Ummatin Rasūlāan 'Ani Au`budū Al-Laha Wa Ajtanibū Aţ-Ţāghūta  ۖ  Faminhum Man Hadá Al-Lahu Wa Minhum Man Ĥaqqat `Alayhi Ađ-Đalālatu  ۚ  Fasīrū Fī Al-'Arđi Fānžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mukadhdhibīna َ016-036 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance. وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّة ٍ رَسُولاً أَنِ اُعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ  ۖ  فَمِنْهُمْ مَنْ هَدَى اللَّهُ وَمِنْهُمْ مَنْ حَقَّتْ عَلَيْهِ الضَّلاَلَةُ  ۚ  فَسِيرُوا فِي الأَرْضِ فَانْظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ
'In Taĥriş `Alá Hudāhum Fa'inna Al-Laha Lā Yahdī Man Yuđillu  ۖ  Wa Mā Lahum Min Nāşirīna َ016-037 Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bã Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bã su da waɗansu mataimaka. إِنْ تَحْرِصْ عَلَى هُدَاهُمْ فَإِنَّ اللَّهَ لاَ يَهْدِي مَنْ يُضِلُّ  ۖ  وَمَا لَهُمْ مِنْ نَاصِرِينَ
Wa 'Aqsamū Bil-Lahi Jahda 'Aymānihim  ۙ  Lā Yab`athu Al-Lahu Man Yamūtu  ۚ  Balá Wa`dāan `Alayhi Ĥaqqāan Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna َ016-038 Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. وَأَقْسَمُوا بِاللَّهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ  ۙ  لاَ يَبْعَثُ اللَّهُ مَنْ يَمُوتُ  ۚ  بَلَى وَعْداً عَلَيْهِ حَقّا ً وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ
Liyubayyina Lahumu Al-Ladhī Yakhtalifūna Fīhi Wa Liya`lama Al-Ladhīna Kafarū 'Annahum Kānū Kādhibīna َ016-039 Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗanda suka kãfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã. لِيُبَيِّنَ لَهُمُ الَّذِي يَخْتَلِفُونَ فِيه ِِ وَلِيَعْلَمَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّهُمْ كَانُوا كَاذِبِينَ
'Innamā Qawlunā Lishay'in 'Idhā 'Aradnāhu 'An Naqūla Lahu Kun Fayakūnu َ016-040 Abin sani kawai, MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, "Ka kasance; sai yanã kasancẽwa. إِنَّمَا قَوْلُنَا لِشَيْء ٍ إِذَا أَرَدْنَاهُ~ُ أَنْ نَقُولَ لَه ُُ كُنْ فَيَكُونُ
Wa Al-Ladhīna Hājarū Fī Al-Lahi Min Ba`di Mā Žulimū Lanubawwi'annahum Ad-Dunyā  ۖ  Ĥasanatan Wa La'ajru Al-'Ākhirati  ۚ  'Akbaru Law Kānū Ya`lamūna َ016-041 Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani. وَالَّذِينَ هَاجَرُوا فِي اللَّهِ مِنْ بَعْدِ مَا ظُلِمُوا لَنُبَوِّئَنَّهُمْ فِي الدُّنْيَا حَسَنَة ً  ۖ  وَلَأَجْرُ الآخِرَةِ أَكْبَرُ  ۚ  لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
Al-Ladhīna Şabarū Wa `Alá Rabbihim Yatawakkalūna َ016-042 Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara. الَّذِينَ صَبَرُوا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Wa Mā 'Arsalnā Min Qablika 'Illā Rijālāan Nūĥī 'Ilayhim  ۚ  Fās'alū 'Ahla Adh-Dhikri 'In Kuntum Lā Ta`lamūna َ016-043 Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, fãce waɗansu mazãje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutãnen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba. وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ إِلاَّ رِجَالا ً نُوحِي إِلَيْهِمْ  ۚ  فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لاَ تَعْلَمُونَ
Bil-Bayyināti Wa Az-Zuburi  ۗ  Wa 'Anzalnā 'Ilayka Adh-Dhikra Litubayyina Lilnnāsi Mā Nuzzila 'Ilayhim Wa La`allahum Yatafakkarūna َ016-044 Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni. بِالْبَيِّنَاتِ وَالزُّبُرِ  ۗ  وَأَنزَلْنَا إِلَيْكَ الذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ
'Afa'amina Al-Ladhīna Makarū As-Sayyi'āti 'An Yakhsifa Al-Lahu Bihimu Al-'Arđa 'Aw Ya'tiyahumu Al-`Adhābu Min Ĥaythu Lā Yash`urūna َ016-045 Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba? أَفَأَمِنَ الَّذِينَ مَكَرُوا السَّيِّئَاتِ أَنْ يَخْسِفَ اللَّهُ بِهِمُ الأَرْضَ أَوْ يَأْتِيَهُمُ الْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لاَ يَشْعُرُونَ
'Aw Ya'khudhahum Fī Taqallubihim Famā Hum Bimu`jizīna َ016-046 Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Sabõda haka ba su zama masu buwãya ba. أَوْ يَأْخُذَهُمْ فِي تَقَلُّبِهِمْ فَمَا هُمْ بِمُعْجِزِينَ
'Aw Ya'khudhahum `Alá Takhawwufin Fa'inna Rabbakum Lara'ūfun Raĥīmun َ016-047 Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙĩƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai. أَوْ يَأْخُذَهُمْ عَلَى تَخَوُّف ٍ فَإِنَّ رَبَّكُمْ لَرَءُوف ٌ رَحِيم ٌ
'Awalam Yaraw 'Ilá Mā Khalaqa Al-Lahu Min Shay'in Yatafayya'u Žilāluhu `Ani Al-Yamīni Wa Ash-Shamā'ili Sujjadāan Lillahi Wa Humkhirūna َ016-048 Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu ƙasƙantar da kai? أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى مَا خَلَقَ اللَّهُ مِنْ شَيْء ٍ يَتَفَيَّأُ ظِلاَلُه ُُ عَنِ الْيَمِينِ وَالشَّمَائِلِ سُجَّدا ً لِلَّهِ وَهُمْ دَاخِرُونَ
Wa Lillahi Yasjudu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Min Dābbatin Wa Al-Malā'ikatu Wa Hum Lā Yastakbirūna َ016-049 Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma bã su kangara. وَلِلَّهِ يَسْجُدُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مِنْ دَابَّة ٍ وَالْمَلاَئِكَةُ وَهُمْ لاَ يَسْتَكْبِرُونَ
Yakhāfūna Rabbahum Min Fawqihim Wa Yaf`alūna Mā Yu'umarūna َ016-050 Suna tsõron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su. يَخَافُونَ رَبَّهُمْ مِنْ فَوْقِهِمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ
Wa Qāla Al-Lahu Lā Tattakhidhū 'Ilahayni Athnayni  ۖ  'Innamā Huwa 'Ilahun Wāĥidun  ۖ  Fa'īyāya Fārhabūni َ016-051 Kuma Allah Ya ce: "Kada ku riƙi abũbuwan bautãwa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautãwa guda ne, sa'an nan sai kuji tsõroNa, Ni kawai." وَقَالَ اللَّهُ لاَ تَتَّخِذُوا إِلَهَيْنِ اثْنَيْنِ  ۖ  إِنَّمَا هُوَ إِلَه ٌ ٌ وَاحِد ٌ  ۖ  فَإِيَّايَ فَارْهَبُونِ
Wa Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Lahu Ad-Dīnu Wa Aşibāan  ۚ  'Afaghayra Al-Lahi Tattaqūna َ016-052 Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bĩ da taƙãwa? وَلَه ُُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَلَهُ الدِّينُ وَاصِباً  ۚ  أَفَغَيْرَ اللَّهِ تَتَّقُونَ
Wa Mā Bikum Min Ni`matin Famina Al-Lahi  ۖ  Thumma 'Idhā Massakumu Ađ-Đurru Fa'ilayhi Taj'arūna َ016-053 Kuma abin da yake a gare ku na ni'ima, to, daga Allah ne. Sa'an nan kuma idan cũta ta shãfeku, to, zuwa gare Shi kuke hargõwa. وَمَا بِكُمْ مِنْ نِعْمَة ٍ فَمِنَ اللَّهِ  ۖ  ثُمَّ إِذَا مَسَّكُمُ الضُّرُّ فَإِلَيْهِ تَجْأَرُونَ
Thumma 'Idhā Kashafa Ađ-Đurra `Ankum 'Idhā Farīqun Minkum Birabbihim Yushrikūna َ016-054 sa'an nan idan Ya kuranye cũtar daga gare ku, sai gã wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijinsu sunã shirki. ثُمَّ إِذَا كَشَفَ الضُّرَّ عَنْكُمْ إِذَا فَرِيق ٌ مِنْكُمْ بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ
Liyakfurū Bimā 'Ātaynāhum  ۚ  Fatamatta`ū  ۖ  Fasawfa Ta`lamūna َ016-055 Dõmin su kãfirta da abin da Muka bã su. To, ku ji dãɗi, sa'an nan da sannu zã ku sani. لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ  ۚ  فَتَمَتَّعُوا  ۖ  فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ
Wa Yaj`alūna Limā Lā Ya`lamūna Naşībāan Mimmā Razaqnāhum  ۗ  Ta-Allāhi Latus'alunna `Ammā Kuntum Taftarūna َ016-056 Kuma sunã sanya rabõ ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa. وَيَجْعَلُونَ لِمَا لاَ يَعْلَمُونَ نَصِيبا ً مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ  ۗ  تَاللَّهِ لَتُسْأَلُنَّ عَمَّا كُنْتُمْ تَفْتَرُونَ
Wa Yaj`alūna Lillahi Al-Banāti Subĥānahu  ۙ  Wa Lahum Mā Yashtahūna َ016-057 Kuma sunã danganta 'ya'ya mãta ga Allah. Tsarkinsa yã tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha'awa. وَيَجْعَلُونَ لِلَّهِ الْبَنَاتِ سُبْحَانَه ُُ  ۙ  وَلَهُمْ مَا يَشْتَهُونَ
Wa 'Idhā Bushshira 'Aĥaduhum Bil-'Unthá Žalla Wajhuhu Muswaddāan Wa Huwa Kažīmun َ016-058 Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki. وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُمْ بِالأُنثَى ظَلَّ وَجْهُه ُُ مُسْوَدّا ً وَهُوَ كَظِيم ٌ
Yatawārá Mina Al-Qawmi Min Sū'i Mā Bushshira Bihi  ۚ  'Ayumsikuhu `Alá Hūnin 'Am Yadussuhu Fī At-Turābi  ۗ  'Alā Sā'a Mā Yaĥkumūna َ016-059 Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana. يَتَوَارَى مِنَ الْقَوْمِ مِنْ سُوءِ مَا بُشِّرَ بِهِ~ِ  ۚ  أَيُمْسِكُه ُُ عَلَى هُونٍ أَمْ يَدُسُّه ُُ فِي التُّرَابِ  ۗ  أَلاَ سَاءَ مَا يَحْكُمُونَ
Lilladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati Mathalu As-Saw'i  ۖ  Wa Lillahi Al-Mathalu Al-'A`lá  ۚ  Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ016-060 Ga waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwãyi, Mai hikima. لِلَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ مَثَلُ السَّوْءِ  ۖ  وَلِلَّهِ الْمَثَلُ الأَعْلَى  ۚ  وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Wa Law Yu'uākhidhu Al-Lahu An-Nāsa Bižulmihim Mā Taraka `Alayhā Min Dābbatin Wa Lakin Yu'uakhkhiruhum 'Ilá 'Ajalin Musammáan  ۖ  Fa'idhā Jā'a 'Ajaluhum Lā Yasta'khirūna Sā`atan  ۖ  Wa Lā Yastaqdimūna َ016-061 Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu, dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta ba. وَلَوْ يُؤَاخِذُ اللَّهُ النَّاسَ بِظُلْمِهِمْ مَا تَرَكَ عَلَيْهَا مِنْ دَابَّة ٍ وَلَكِنْ يُؤَخِّرُهُمْ إِلَى أَجَل ٍ مُسَمّى ً  ۖ  فَإِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ لاَ يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَة ً  ۖ  وَلاَ يَسْتَقْدِمُونَ
Wa Yaj`alūna Lillahi Mā Yakrahūna Wa Taşifu 'Alsinatuhumu Al-Kadhiba 'Anna Lahumu Al-Ĥusná  ۖ  Lā Jarama 'Anna Lahumu An-Nāra Wa 'Annahum Mufraţūna َ016-062 Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta) . وَيَجْعَلُونَ لِلَّهِ مَا يَكْرَهُونَ وَتَصِفُ أَلْسِنَتُهُمُ الْكَذِبَ أَنَّ لَهُمُ الْحُسْنَى  ۖ  لاَ جَرَمَ أَنَّ لَهُمُ النَّارَ وَأَنَّهُمْ مُفْرَطُونَ
Ta-Allāhi Laqad 'Arsalnā 'Ilá 'Umamin Min Qablika Fazayyana Lahumu Ash-Shayţānu 'A`mālahum Fahuwa Walīyuhumu Al-Yawma Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun َ016-063 Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. تَاللَّهِ لَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَى أُمَم ٍ مِنْ قَبْلِكَ فَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَهُوَ وَلِيُّهُمُ الْيَوْمَ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Wa Mā 'Anzalnā `Alayka Al-Kitāba 'Illā Litubayyina Lahumu Al-Ladhī Akhtalafū Fīhi  ۙ  Wa Hudáan Wa Raĥmatan Liqawmin Yu'uminūna َ016-064 Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. وَمَا أَنزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ إِلاَّ لِتُبَيِّنَ لَهُمُ الَّذِي اخْتَلَفُوا فِيه ِِ  ۙ  وَهُدى ً وَرَحْمَة ً لِقَوْم ٍ يُؤْمِنُونَ
Wa Allāhu 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an Fa'aĥyā Bihi Al-'Arđa Ba`da  ۚ  Mawtihā 'Inna Fī Dhālika La'āyatan Liqawmin Yasma`ūna َ016-065 Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre. وَاللَّهُ أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَأَحْيَا بِهِ الأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِقَوْم ٍ يَسْمَعُونَ
Wa 'Inna Lakum Al-'An`ām La`ibratan  ۖ  Nusqīkum Mimmā Fī Buţūnihi Min Bayni Farthin Wa Damin Labanāan Khālişāan Sā'ighāan Lilshshāribīna َ016-066 Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima;Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã. وَإِنَّ لَكُمْ فِي الأَنعَام لَعِبْرَة ً  ۖ  نُسْقِيكُمْ مِمَّا فِي بُطُونِه ِِ مِنْ بَيْنِ فَرْث ٍ وَدَم ٍ لَبَناً خَالِصا ً سَائِغا ً لِلشَّارِبِينَ
Wa Min Thamarāti An-Nakhīli Wa Al-'A`nābi Tattakhidhūna Minhu Sakarāan Wa Rizqāan Ĥasanāan  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Liqawmin Ya`qilūna َ016-067 Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta. وَمِنْ ثَمَرَاتِ النَّخِيلِ وَالأَعْنَابِ تَتَّخِذُونَ مِنْهُ سَكَرا ً وَرِزْقاً حَسَنا ً  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِقَوْم ٍ يَعْقِلُونَ
Wa 'Awĥá Rabbuka 'Ilá An-Naĥli 'Ani Attakhidhī Mina Al-Jibāli Buyūtāan Wa Mina Ash-Shajari Wa Mimmā Ya`rishūna َ016-068 Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa." وَأَوْحَى رَبُّكَ إِلَى النَّحْلِ أَنِ اتَّخِذِي مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتا ً وَمِنَ الشَّجَرِ وَمِمَّا يَعْرِشُونَ
Thumma Kulī Min Kulli Ath-Thamarāti Fāslukī Subula Rabbiki Dhululāan  ۚ  Yakhruju Min Buţūnihā Sharābun Mukhtalifun 'Alwānuhu Fīhi Shifā'un Lilnnāsi  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Liqawmin Yatafakkarūna َ016-069 "Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. ثُمَّ كُلِي مِنْ كُلِّ الثَّمَرَاتِ فَاسْلُكِي سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلا ً  ۚ  يَخْرُجُ مِنْ بُطُونِهَا شَرَاب ٌ مُخْتَلِفٌ أَلْوَانُه ُُ فِيه ِِ شِفَاء ٌ لِلنَّاسِ  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِقَوْم ٍ يَتَفَكَّرُونَ
Wa Allāhu Khalaqakum Thumma  ۚ  Yatawaffākum Wa Minkum Man Yuraddu 'Ilá 'Ardhali Al-`Umuri Likay Lā Ya`lama Ba`da `Ilmin  ۚ  Shay'āan 'Inna Al-Laha `Alīmun Qadīrun َ016-070 Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi. وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ ثُمَّ يَتَوَفَّاكُمْ  ۚ  وَمِنْكُمْ مَنْ يُرَدُّ إِلَى أَرْذَلِ الْعُمُرِ لِكَيْ لاَ يَعْلَمَ بَعْدَ عِلْم ٍ شَيْئا ً  ۚ  إِنَّ اللَّهَ عَلِيم ٌ قَدِير ٌ
Wa Allāhu Fađđala Ba`đakum `Alá Ba`đin  ۚ  Ar-Rizqi Famā Al-Ladhīna Fuđđilū Birāddī Rizqihim `Alá Mā Malakat 'Aymānuhum Fahum Fīhi  ۚ  Sawā'un 'Afabini`mati Al-Lahi Yajĥadūna َ016-071 Kuma Allah Ya fifita sãshenku a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu? وَاللَّهُ فَضَّلَ بَعْضَكُمْ عَلَى بَعْض ٍ فِي الرِّزْقِ  ۚ  فَمَا الَّذِينَ فُضِّلُوا بِرَادِّي رِزْقِهِمْ عَلَى مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَهُمْ فِيه ِِ سَوَاءٌ  ۚ  أَفَبِنِعْمَةِ اللَّهِ يَجْحَدُونَ
Wa Allāhu Ja`ala Lakum Min 'Anfusikum 'Azwājāan Wa Ja`ala Lakum Min 'Azwājikum Banīna Wa Ĥafadatan Wa Razaqakum Mina  ۚ  Aţ-Ţayyibāti 'Afabiālbāţili Yu'uminūna Wa Bini`mati Al-Lahi Hum Yakfurūna َ016-072 Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta? وَاللَّهُ جَعَلَ لَكُمْ مِنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجا ً وَجَعَلَ لَكُمْ مِنْ أَزْوَاجِكُمْ بَنِينَ وَحَفَدَة ً وَرَزَقَكُمْ مِنَ الطَّيِّبَاتِ  ۚ  أَفَبِالْبَاطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَةِ اللَّهِ هُمْ يَكْفُرُونَ
Wa Ya`budūna Min Dūni Al-Lahi Mā Lā Yamliku Lahum Rizqāan Mina As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Shay'āan Wa Lā Yastaţī`ūna َ016-073 Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme) . وَيَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لاَ يَمْلِكُ لَهُمْ رِزْقا ً مِنَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ شَيْئا ً وَلاَ يَسْتَطِيعُونَ
Falā Tađribū Lillahi Al-'Amthāla  ۚ  'Inna Al-Laha Ya`lamu Wa 'Antum Lā Ta`lamūna َ016-074 Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba. فَلاَ تَضْرِبُوا لِلَّهِ الأَمْثَالَ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ وَأَنْتُمْ لاَ تَعْلَمُونَ
Đaraba Al-Lahu Mathalāan `Abdāan Mamlūkāan Lā Yaqdiru `Alá Shay'in Wa Man Razaqnāhu Minnā Rizqāan Ĥasanāan Fahuwa Yunfiqu Minhu Sirrāan Wa Jahrāan  ۖ  Hal Yastawūna  ۚ  Al-Ĥamdu Lillahi  ۚ  Bal 'Aktharuhum Lā Ya`lamūna َ016-075 Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba. ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلاً عَبْدا ً مَمْلُوكا ً لاَ يَقْدِرُ عَلَى شَيْء ٍ وَمَنْ رَزَقْنَاه ُُ مِنَّا رِزْقاً حَسَنا ً فَهُوَ يُنفِقُ مِنْهُ سِرّا ً وَجَهْراً  ۖ  هَلْ يَسْتَوُونَ  ۚ  الْحَمْدُ لِلَّهِ  ۚ  بَلْ أَكْثَرُهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ
Wa Đaraba Al-Lahu Mathalāan Rajulayni 'Aĥaduhumā 'Abkamu Lā Yaqdiru `Alá Shay'in Wa Huwa Kallun `Alá Mawlāhu 'Aynamā Yuwajjhhhu Lā Ya'ti Bikhayrin  ۖ  Hal Yastawī Huwa Wa Man Ya'muru Bil-`Adli  ۙ  Wa Huwa `Alá Şirāţin Mustaqīmin َ016-076 Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici? وَضَرَبَ اللَّهُ مَثَلا ً رَجُلَيْنِ أَحَدُهُمَا أَبْكَمُ لاَ يَقْدِرُ عَلَى شَيْء ٍ وَهُوَ كَلٌّ عَلَى مَوْلاَهُ~ُ أَيْنَمَا يُوَجّههُّ لاَ يَأْتِ بِخَيْرٍ  ۖ  هَلْ يَسْتَوِي هُوَ وَمَنْ يَأْمُرُ بِالْعَدْلِ  ۙ  وَهُوَ عَلَى صِرَاط ٍ مُسْتَقِيم ٍ
Wa Lillahi Ghaybu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Wa Mā 'Amru As-Sā`ati 'Illā Kalamĥi Al-Başari 'Aw Huwa 'Aqrabu  ۚ  'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ016-077 Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne. وَلِلَّهِ غَيْبُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۚ  وَمَا أَمْرُ السَّاعَةِ إِلاَّ كَلَمْحِ الْبَصَرِ أَوْ هُوَ أَقْرَبُ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Wa Allāhu 'Akhrajakum Min Buţūni 'Ummahātikum Lā Ta`lamūna Shay'āan Wa Ja`ala Lakumu As-Sam`a Wa Al-'Abşāra Wa  ۙ  Al-'Af'idata La`allakum Tashkurūna َ016-078 Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde. وَاللَّهُ أَخْرَجَكُمْ مِنْ بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ لاَ تَعْلَمُونَ شَيْئا ً وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالأَبْصَارَ وَالأَفْئِدَةَ  ۙ  لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
'Alam Yaraw 'Ilá Aţ-Ţayri Musakhkharātin Fī Jawwi As-Samā'i Mā Yumsikuhunna 'Illā Al-Lahu  ۗ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yu'uminūna َ016-079 Shin ba su ga tsuntsãye ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. أَلَمْ يَرَوْا إِلَى الطَّيْرِ مُسَخَّرَات ٍ فِي جَوِّ السَّمَاءِ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلاَّ اللَّهُ  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِقَوْم ٍ يُؤْمِنُونَ
Wa Allāhu Ja`ala Lakum Min Buyūtikum Sakanāan Wa Ja`ala Lakum Min Julūdi Al-'An`āmi Buyūtāan Tastakhiffūnahā Yawma Ža`nikum Wa Yawma  ۙ  'Iqāmatikum Wa Min 'Aşwāfihā Wa 'Awbārihā Wa 'Ashrihā 'Athāthāan Wa Matā`āan 'Ilá Ĥīnin َ016-080 Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci. وَاللَّهُ جَعَلَ لَكُمْ مِنْ بُيُوتِكُمْ سَكَنا ً وَجَعَلَ لَكُمْ مِنْ جُلُودِ الأَنعَامِ بُيُوتا ً تَسْتَخِفُّونَهَا يَوْمَ ظَعْنِكُمْ وَيَوْمَ إِقَامَتِكُمْ  ۙ  وَمِنْ أَصْوَافِهَا وَأَوْبَارِهَا وَأَشْعَارِهَا أَثَاثا ً وَمَتَاعا ً إِلَى حِين ٍ
Wa Allāhu Ja`ala Lakum Mimmā Khalaqa Žilālāan Wa Ja`ala Lakum Mina Al-Jibāli 'Aknānāan Wa Ja`ala Lakum Sarābīla Taqīkumu Al-Ĥarra Wa Sarābīla Taqīkum  ۚ  Ba'sakum Kadhālika Yutimmu Ni`matahu `Alaykum La`allakum Tuslimūna َ016-081 Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa. وَاللَّهُ جَعَلَ لَكُمْ مِمَّا خَلَقَ ظِلاَلا ً وَجَعَلَ لَكُمْ مِنَ الْجِبَالِ أَكْنَانا ً وَجَعَلَ لَكُمْ سَرَابِيلَ تَقِيكُمُ الْحَرَّ وَسَرَابِيلَ تَقِيكُمْ بَأْسَكُمْ  ۚ  كَذَلِكَ يُتِمُّ نِعْمَتَه ُُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تُسْلِمُونَ
Fa'in Tawallaw Fa'innamā `Alayka Al-Balāghu Al-Mubīnu َ016-082 To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã. فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْكَ الْبَلاَغُ الْمُبِينُ
Ya`rifūna Ni`mata Al-Lahi Thumma Yunkirūnahā Wa 'Aktharuhumu Al-Kāfirūna َ016-083 Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne. يَعْرِفُونَ نِعْمَةَ اللَّهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا وَأَكْثَرُهُمُ الْكَافِرُونَ
Wa Yawma Nab`athu Min Kulli 'Ummatin Shahīdāan Thumma Lā Yu'udhanu Lilladhīna Kafarū Wa Lā Hum Yusta`tabūna َ016-084 Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba. وَيَوْمَ نَبْعَثُ مِنْ كُلِّ أُمَّة ٍ شَهِيدا ً ثُمَّ لاَ يُؤْذَنُ لِلَّذِينَ كَفَرُوا وَلاَ هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ
Wa 'Idhā Ra'á Al-Ladhīna Žalamū Al-`Adhāba Falā Yukhaffafu `Anhum Wa Lā Hum Yunžarūna َ016-085 Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa'an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba. وَإِذَا رَأَى الَّذِينَ ظَلَمُوا الْعَذَابَ فَلاَ يُخَفَّفُ عَنْهُمْ وَلاَ هُمْ يُنظَرُونَ
Wa 'Idhā Ra'á Al-Ladhīna 'Ashrakū Shurakā'ahum Qālū Rabbanā Hā'uulā' Shurakā'uunā Al-Ladhīna Kunnā Nad`ū Min Dūnika  ۖ  Fa'alqaw 'Ilayhimu Al-Qawla 'Innakum Lakādhibūna َ016-086 Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne." وَإِذَا رَأَى الَّذِينَ أَشْرَكُوا شُرَكَاءَهُمْ قَالُوا رَبَّنَا هَاؤُلاَء شُرَكَاؤُنَا الَّذِينَ كُنَّا نَدْعُو مِنْ دُونِكَ  ۖ  فَأَلْقَوْا إِلَيْهِمُ الْقَوْلَ إِنَّكُمْ لَكَاذِبُونَ
Wa 'Alqaw 'Ilá Al-Lahi Yawma'idhin As-Salama  ۖ  Wa Đalla `Anhum Mā Kānū Yaftarūna َ016-087 Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su. وَأَلْقَوْا إِلَى اللَّهِ يَوْمَئِذ ٍ السَّلَمَ  ۖ  وَضَلَّ عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Al-Ladhīna Kafarū Wa Şaddū `An Sabīli Al-Lahi Zidnāhum `Adhābāan Fawqa Al-`Adhābi Bimā Kānū Yufsidūna َ016-088 Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙãra musu wata azãba bisa ga azãbar, sabõda abin da suka kasance sunã yi na fasãdi. الَّذِينَ كَفَرُوا وَصَدُّوا عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ زِدْنَاهُمْ عَذَابا ً فَوْقَ العَذَابِ بِمَا كَانُوا يُفْسِدُونَ
Wa Yawma Nab`athu Fī Kulli 'Ummatin Shahīdāan `Alayhim Min 'Anfusihim  ۖ  Wa Ji'nā Bika Shahīdāan `Alá Hā'uulā'  ۚ  Wa Nazzalnā `Alayka Al-Kitāba Tibyānāan Likulli Shay'in Wa Hudáan Wa Raĥmatan Wa Bushrá Lilmuslimīna َ016-089 Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi). وَيَوْمَ نَبْعَثُ فِي كُلِّ أُمَّة ٍ شَهِيداً عَلَيْهِمْ مِنْ أَنفُسِهِمْ  ۖ  وَجِئْنَا بِكَ شَهِيداً عَلَى هَاؤُلاَء  ۚ  وَنَزَّلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ تِبْيَانا ً لِكُلِّ شَيْء ٍ وَهُدى ً وَرَحْمَة ً وَبُشْرَى لِلْمُسْلِمِينَ
'Inna Al-Laha Ya'muru Bil-`Adli Wa Al-'Iĥsāni Wa 'Ītā'i Dhī Al-Qurbá Wa Yanhá `Ani Al-Faĥshā'i Wa Al-Munkari Wa Al-Baghyi  ۚ  Ya`ižukum La`allakum Tadhakkarūna َ016-090 Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa. إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُ بِالْعَدْلِ وَالإِحْسَانِ وَإِيتَاءِ ذِي الْقُرْبَى وَيَنْهَى عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ وَالْبَغْيِ  ۚ  يَعِظُكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Wa 'Awfū Bi`ahdi Al-Lahi 'Idhā `Āhadtum Wa Lā Tanquđū Al-'Aymāna Ba`da Tawkīdihā Wa Qad Ja`altumu Al-Laha `Alaykum Kafīlāan  ۚ  'Inna Al-Laha Ya`lamu Mā Taf`alūna َ016-091 Kuma ku cika da alkãwarin Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa. وَأَوْفُوا بِعَهْدِ اللَّهِ إِذَا عَاهَدْتُمْ وَلاَ تَنقُضُوا الأَيْمَانَ بَعْدَ تَوْكِيدِهَا وَقَدْ جَعَلْتُمُ اللَّهَ عَلَيْكُمْ كَفِيلا ً  ۚ  إِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَ
Wa Lā Takūnū Kāllatī Naqađat Ghazlahā Min Ba`di Qūwatin 'Anthāan Tattakhidhūna 'Aymānakum Dakhalāan Baynakum 'An Takūna 'Ummatun Hiya 'Arbá Min 'Ummatin  ۚ  'Innamā Yablūkumu Al-Lahu Bihi  ۚ  Wa Layubayyinanna Lakum Yawma Al-Qiyāmati Mā Kuntum Fīhi Takhtalifūna َ016-092 Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin kasancẽwar wata al'umma tãfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yanã jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar ¡iyãma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wajũna. وَلاَ تَكُونُوا كَالَّتِي نَقَضَتْ غَزْلَهَا مِنْ بَعْدِ قُوَّةٍ أَنكَاثا ً تَتَّخِذُونَ أَيْمَانَكُمْ دَخَلا ً بَيْنَكُمْ أَنْ تَكُونَ أُمَّةٌ هِيَ أَرْبَى مِنْ أُمَّة ٍ  ۚ  إِنَّمَا يَبْلُوكُمُ اللَّهُ بِه ِِ  ۚ  وَلَيُبَيِّنَنَّ لَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مَا كُنْتُمْ فِيه ِِ تَخْتَلِفُونَ
Wa Law Shā'a Al-Lahu Laja`alakum 'Ummatan Wāĥidatan Wa Lakin Yuđillu Man Yashā'u Wa Yahdī Man Yashā'u  ۚ  Wa Latus'alunna `Ammā Kuntum Ta`malūna َ016-093 Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al'umma gudã, kuma Yanã ɓatar da wanda Ya so. kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da kuka kasance kunã aikatãwa. وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّة ً وَاحِدَة ً وَلَكِنْ يُضِلُّ مَنْ يَشَاءُ وَيَهْدِي مَنْ يَشَاءُ  ۚ  وَلَتُسْأَلُنَّ عَمَّا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Wa Lā Tattakhidhū 'Aymānakum Dakhalāan Baynakum Fatazilla Qadamun Ba`da Thubūtihā Wa Tadhūqū As-Sū'a Bimā Şadadtum `An Sabīli Al-Lahi  ۖ  Wa Lakum `Adhābun `Ažīmun َ016-094 Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma. وَلاَ تَتَّخِذُوا أَيْمَانَكُمْ دَخَلا ً بَيْنَكُمْ فَتَزِلَّ قَدَم ٌ بَعْدَ ثُبُوتِهَا وَتَذُوقُوا السُّوءَ بِمَا صَدَدْتُمْ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ  ۖ  وَلَكُمْ عَذَابٌ عَظِيم ٌ
Wa Lā Tashtarū Bi`ahdi Al-Lahi Thamanāan Qalīlāan  ۚ  'Innamā `Inda Al-Lahi Huwa Khayrun Lakum 'In Kuntum Ta`lamūna َ016-095 Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani. وَلاَ تَشْتَرُوا بِعَهْدِ اللَّهِ ثَمَنا ً قَلِيلا ً  ۚ  إِنَّمَا عِنْدَ اللَّهِ هُوَ خَيْر ٌ لَكُمْ إِنْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Mā `Indakum Yanfadu  ۖ  Wa Mā `Inda Al-Lahi Bāqin  ۗ  Wa Lanajziyanna Al-Ladhīna Şabarū 'Ajrahum Bi'aĥsani Mā Kānū Ya`malūna َ016-096 Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa. مَا عِنْدَكُمْ يَنفَدُ  ۖ  وَمَا عِنْدَ اللَّهِ بَاق ٍ  ۗ  وَلَنَجْزِيَنَّ الَّذِينَ صَبَرُوا أَجْرَهُمْ بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Man `Amila Şāliĥāan Min Dhakarin 'Aw 'Unthá Wa Huwa Mu'uminun Falanuĥyiyannahu Ĥayāatan Ţayyibatan  ۖ  Wa Lanajziyannahum 'Ajrahum Bi'aĥsani Mā Kānū Ya`malūna َ016-097 Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa. مَنْ عَمِلَ صَالِحا ً مِنْ ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى وَهُوَ مُؤْمِن ٌ فَلَنُحْيِيَنَّه ُُ حَيَاة ً طَيِّبَة ً  ۖ  وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُمْ بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Fa'idhā Qara'ta Al-Qur'āna Fāsta`idh Bil-Lahi Mina Ash-Shayţāni Ar-Rajīmi َ016-098 Sa'an nan idan ka karantã Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe. فَإِذَا قَرَأْتَ الْقُرْآنَ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ
'Innahu Laysa Lahu Sulţānun `Alá Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Alá Rabbihim Yatawakkalūna َ016-099 Lalle ne shi, bã shi da wani ƙarfi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu. إِنَّه ُُ لَيْسَ لَه ُُ سُلْطَانٌ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
'Innamā Sulţānuhu `Alá Al-Ladhīna Yatawallawnahu Wa Al-Ladhīna Hum Bihi Mushrikūna َ016-100 Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne. إِنَّمَا سُلْطَانُه ُُ عَلَى الَّذِينَ يَتَوَلَّوْنَه ُُ وَالَّذِينَ هُمْ بِه ِِ مُشْرِكُونَ
Wa 'Idhā Baddalnā 'Āyatan Makāna 'Āyatin Wa  ۙ  Allāhu 'A`lamu Bimā Yunazzilu Qālū 'Innamā 'Anta Muftarin  ۚ  Bal 'Aktharuhum Lā Ya`lamūna َ016-101 Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." Ã'a, mafi yawansu bã swa sani. وَإِذَا بَدَّلْنَا آيَة ً مَكَانَ آيَة ٍ  ۙ  وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُنَزِّلُ قَالُوا إِنَّمَا أَنْتَ مُفْتَر ٍ  ۚ  بَلْ أَكْثَرُهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ
Qul Nazzalahu Rūĥu Al-Qudusi Min Rabbika Bil-Ĥaqqi Liyuthabbita Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Hudáan Wa Bushrá Lilmuslimīna َ016-102 Ka ce: "Rũhul ¡udusi ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma(dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi." قُلْ نَزَّلَه ُُ رُوحُ الْقُدُسِ مِنْ رَبِّكَ بِالْحَقِّ لِيُثَبِّتَ الَّذِينَ آمَنُوا وَهُدى ً وَبُشْرَى لِلْمُسْلِمِينَ
Wa Laqad Na`lamu 'Annahum Yaqūlūna 'Innamā Yu`allimuhu Basharun  ۗ  Lisānu Al-Ladhī Yulĥidūna 'Ilayhi 'A`jamīyun Wa Hadhā Lisānun `Arabīyun Mubīnun َ016-103 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin (cẽwa) lalle ne sũ, sunã cẽwa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ãni) harshe ne Balãrabe bayyananne. وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّهُمْ يَقُولُونَ إِنَّمَا يُعَلِّمُه ُُ بَشَر ٌ  ۗ  لِسَانُ الَّذِي يُلْحِدُونَ إِلَيْهِ أَعْجَمِيّ ٌ وَهَذَا لِسَانٌ عَرَبِيّ ٌ مُبِين ٌ
'Inna Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bi'āyāti Al-Lahi Lā Yahdīhimu Al-Lahu Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun َ016-104 Lalle ne waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, Allahbã zai shiryar da su ba, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. إِنَّ الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ لاَ يَهْدِيهِمُ اللَّهُ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
'Innamā Yaftarī Al-Kadhiba Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bi'āyāti Al-Lahi  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Kādhibūna َ016-105 Abin sani kawai waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata. إِنَّمَا يَفْتَرِي الْكَذِبَ الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ  ۖ  وَأُوْلَائِكَ هُمُ الْكَاذِبُونَ
Man Kafara Bil-Lahi Min Ba`di 'Īmānihi 'Illā Man 'Ukriha Wa Qalbuhu Muţma'innun Bil-'Īmāni Wa Lakin Man Sharaĥa Bil-Kufri Şadrāan Fa`alayhim Ghađabun Mina Al-Lahi Wa Lahum `Adhābun `Ažīmun َ016-106 Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma. مَنْ كَفَرَ بِاللَّهِ مِنْ بَعْدِ إِيمَانِهِ~ِ إِلاَّ مَنْ أُكْرِه ََ وَقَلْبُه ُُ مُطْمَئِنّ ٌ بِالإِيمَانِ وَلَكِنْ مَنْ شَرَحَ بِالْكُفْرِ صَدْرا ً فَعَلَيْهِمْ غَضَب ٌ مِنَ اللَّهِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيم ٌ
Dhālika Bi'annahumu Astaĥabbū Al-Ĥayāata Ad-Dunyā `Alá Al-'Ākhirati Wa 'Anna Al-Laha Lā Yahdī Al-Qawma Al-Kāfirīna َ016-107 Waɗancan ne kãfirai dõmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lãhira, kuma lalle ne Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai. ذَلِكَ بِأَنَّهُمُ اسْتَحَبُّوا الْحَيَاةَ الدُّنْيَا عَلَى الآخِرَةِ وَأَنَّ اللَّهَ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Ţaba`a Al-Lahu `Alá Qulūbihim Wa Sam`ihim Wa 'Abşārihim  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Ghāfilūna َ016-108 Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukãtansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗancan sũ ne gafalallu. أُوْلَائِكَ الَّذِينَ طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قُلُوبِهِمْ وَسَمْعِهِمْ وَأَبْصَارِهِمْ  ۖ  وَأُوْلَائِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ
Lā Jarama 'Annahum Al-'Ākhirati Humu Al-Khāsirūna َ016-109 Bãbu shakka lalle ne a Lãhira sũ ne mãsu hasãra. لاَ جَرَمَ أَنَّهُمْ فِي الآخِرَةِ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Thumma 'Inna Rabbaka Lilladhīna Hājarū Min Ba`di Mā Futinū Thumma Jāhadū Wa Şabarū 'Inna Rabbaka Min Ba`dihā Laghafūrun Raĥīmun َ016-110 Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ هَاجَرُوا مِنْ بَعْدِ مَا فُتِنُوا ثُمَّ جَاهَدُوا وَصَبَرُوا إِنَّ رَبَّكَ مِنْ بَعْدِهَا لَغَفُور ٌ رَحِيم ٌ
Yawma Ta'tī Kullu Nafsin Tujādilu `An Nafsihā Wa Tuwaffá Kullu Nafsin Mā `Amilat Wa Hum Lā Yužlamūna َ016-111 A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba. يَوْمَ تَأْتِي كُلُّ نَفْس ٍ تُجَادِلُ عَنْ نَفْسِهَا وَتُوَفَّى كُلُّ نَفْس ٍ مَا عَمِلَتْ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ
Wa Đaraba Al-Lahu Mathalāan Qaryatan Kānat 'Āminatan Muţma'innatan Ya'tīhā Rizquhā Raghadāan Min Kulli Makānin Fakafarat Bi'an`umi Al-Lahi Fa'adhāqahā Al-Lahu Libāsa Al-Jū`i Wa Al-Khawfi Bimā Kānū Yaşna`ūna َ016-112 Kuma Allah Ya buga misãli, wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa. وَضَرَبَ اللَّهُ مَثَلا ً قَرْيَة ً كَانَتْ آمِنَة ً مُطْمَئِنَّة ً يَأْتِيهَا رِزْقُهَا رَغَدا ً مِنْ كُلِّ مَكَان ٍ فَكَفَرَتْ بِأَنْعُمِ اللَّهِ فَأَذَاقَهَا اللَّهُ لِبَاسَ الْجُوعِ وَالْخَوْفِ بِمَا كَانُوا يَصْنَعُونَ
Wa Laqad Jā'ahum Rasūlun Minhum Fakadhdhabūhu Fa'akhadhahumu Al-`Adhābu Wa Hum Žālimūna َ016-113 Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci. وَلَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُول ٌ مِنْهُمْ فَكَذَّبُوه ُُ فَأَخَذَهُمُ الْعَذَابُ وَهُمْ ظَالِمُونَ
Fakulū Mimmā Razaqakumu Al-Lahu Ĥalālāan Ţayyibāan Wa Ashkurū Ni`mata Al-Lahi 'In Kuntum 'Īyāhu Ta`budūna َ016-114 Sa'an nan ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa. فَكُلُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللَّهُ حَلالا ً طَيِّبا ً وَاشْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ إِنْ كُنْتُمْ إِيَّاه ُُ تَعْبُدُونَ
'Innamā Ĥarrama `Alaykumu Al-Maytata Wa Ad-Dama Wa Laĥma Al-Khinzīri Wa Mā 'Uhilla Lighayri Al-Lahi Bihi  ۖ  Famani Ađţurra Ghayra Bāghin Wa Lā `Ādin Fa'inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun َ016-115 Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةَ وَالدَّمَ وَلَحْمَ الْخِنْزِيرِ وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللَّهِ بِه ِِ  ۖ  فَمَنِ اضْطُرَّ غَيْرَ بَاغ ٍ وَلاَ عَاد ٍ فَإِنَّ اللَّهَ غَفُور ٌ رَحِيم ٌ
Wa Lā Taqūlū Limā Taşifu 'Alsinatukumu Al-Kadhiba Hādhā Ĥalālun Wa Hadhā Ĥarāmun Litaftarū `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba  ۚ  'Inna Al-Ladhīna Yaftarūna `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba Lā Yufliĥūna َ016-116 Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba. وَلاَ تَقُولُوا لِمَا تَصِفُ أَلْسِنَتُكُمُ الْكَذِبَ هَذَا حَلاَل ٌ وَهَذَا حَرَام ٌ لِتَفْتَرُوا عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ  ۚ  إِنَّ الَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ لاَ يُفْلِحُونَ
Matā`un Qalīlun Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun َ016-117 Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi. مَتَاع ٌ قَلِيل ٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Wa `Alá Al-Ladhīna Hādū Ĥarramnā Mā Qaşaşnā `Alayka Min Qablu  ۖ  Wa Mā Žalamnāhum Wa Lakin Kānū 'Anfusahum Yažlimūna َ016-118 Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni, kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta. وَعَلَى الَّذِينَ هَادُوا حَرَّمْنَا مَا قَصَصْنَا عَلَيْكَ مِنْ قَبْلُ  ۖ  وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَكِنْ كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Thumma 'Inna Rabbaka Lilladhīna `Amilū As-Sū'a Bijahālatin Thumma Tābū Min Ba`di Dhālika Wa 'Aşlaĥū 'Inna Rabbaka Min Ba`dihā Laghafūrun Raĥīmun َ016-119 Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُوا السُّوءَ بِجَهَالَة ٍ ثُمَّ تَابُوا مِنْ بَعْدِ ذَلِكَ وَأَصْلَحُوا إِنَّ رَبَّكَ مِنْ بَعْدِهَا لَغَفُور ٌ رَحِيم ٌ
'Inna 'Ibrāhīma Kāna 'Ummatan Qānitāan Lillahi Ĥanīfāan Wa Lam Yaku Mina Al-Mushrikīna َ016-120 Lalle ne Ibrãhĩm ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba. إِنَّ إِبْرَاهِيمَ كَانَ أُمَّة ً قَانِتا ً لِلَّهِ حَنِيفا ً وَلَمْ يَكُ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
Shākirāan Li'n`umihi  ۚ  Ajtabāhu Wa Hadāhu 'Ilá Şirāţin Mustaqīm َ016-121 Mai gõdiya ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici. شَاكِرا ً لِأنْعُمِهِ  ۚ  اجْتَبَاه ُُ وَهَدَاهُ~ُ إِلَى صِرَاط ٍ مُسْتَقِيم
Wa 'Ātaynāhu Fī Ad-Dunyā Ĥasanatan  ۖ  Wa 'Innahu Fī Al-'Ākhirati Lamina Aş-Şāliĥīna َ016-122 Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai. وَآتَيْنَاه ُُ فِي الدُّنْيَا حَسَنَة ً  ۖ  وَإِنَّه ُُ فِي الآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِينَ
Thumma 'Awĥaynā 'Ilayka 'Ani Attabi` Millata 'Ibrāhīma Ĥanīfāan  ۖ  Wa Mā Kāna Mina Al-Mushrikīna َ016-123 Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), "Ka bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.' ثُمَّ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ أَنِ اتَّبِعْ مِلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفا ً  ۖ  وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
'Innamā Ju`ila As-Sabtu `Alá Al-Ladhīna Akhtalafū Fīhi  ۚ  Wa 'Inna Rabbaka Layaĥkumu Baynahum Yawma Al-Qiyāmati Fīmā Kānū Fīhi Yakhtalifūna َ016-124 Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa,Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã. إِنَّمَا جُعِلَ السَّبْتُ عَلَى الَّذِينَ اخْتَلَفُوا فِيه ِِ  ۚ  وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَحْكُمُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيه ِِ يَخْتَلِفُونَ
Ad`u 'Ilá Sabīli Rabbika Bil-Ĥikmati Wa Al-Maw`ižati Al-Ĥasanati  ۖ  Wa Jādilhum Bi-Atī Hiya 'Aĥsanu  ۚ  'Inna Rabbaka Huwa 'A`lamu Biman Đalla `An Sabīlihi  ۖ  Wa Huwa 'A`lamu Bil-Muhtadīna َ016-125 Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa. ادْعُ إِلَى سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ  ۖ  وَجَادِلْهُمْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ  ۚ  إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنْ ضَلَّ عَنْ سَبِيلِه ِِ  ۖ  وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ
Wa 'In `Āqabtum Fa`āqibū Bimithli Mā `Ūqibtum Bihi  ۖ  Wa La'in Şabartum Lahuwa Khayrun Lilşşābirīna َ016-126 Kuma idan kuka sãka wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri. وَإِنْ عَاقَبْتُمْ فَعَاقِبُوا بِمِثْلِ مَا عُوقِبْتُمْ بِه ِِ  ۖ  وَلَئِنْ صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْر ٌ لِلصَّابِرِينَ
Wa Aşbir Wa Mā Şabruka 'Illā Bil-Lahi  ۚ  Wa Lā Taĥzan `Alayhim Wa Lā Taku Fī Đayqin Mimmā Yamkurūna َ016-127 Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci. وَاصْبِرْ وَمَا صَبْرُكَ إِلاَّ بِاللَّهِ  ۚ  وَلاَ تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلاَ تَكُ فِي ضَيْق ٍ مِمَّا يَمْكُرُونَ
'Inna Al-Laha Ma`a Al-Ladhīna Attaqaw Wa Al-Ladhīna Hum Muĥsinūna َ016-128 Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne. إِنَّ اللَّهَ مَعَ الَّذِينَ اتَّقَوْا وَالَّذِينَ هُمْ مُحْسِنُونَ
Next Sūrah