11) Sūrat Hūd

Printed format

11)

'Alif-Lām-Rā Kitābun 'Uĥkimat 'Āyātuhu Thumma Fuşşilat Min Ladun Ĥakīmin Khabīrin 011-001 A. L̃. R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa. --  ۚ 
'Allā Ta`budū 'Illā Al-Laha  ۚ  'Innanī Lakum Minhu Nadhīrun Wa Bashīrun 011-002 Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi.  ۚ 
Wa 'Ani Astaghfirū Rabbakum Thumma Tūbū 'Ilayhi Yumatti`kum Matā`āan Ĥasanāan 'Ilá 'Ajalin Musammáan Wa Yu'uti Kulla Dhī Fađlin Fađlahu  ۖ  Wa 'In Tawallaw Fa'innī 'Akhāfu `Alaykum `Adhāba Yawmin Kabīrin 011-003 Kuma ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa'an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan ma'abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar yini mai girma a kanku.  ۖ 
'Ilá Al-Lahi Marji`ukum  ۖ  Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 011-004 Zuwa ga Allah makõmarku take, kuma Shĩ a kan kõmeMai ĩkon yi ne.  ۖ 
'Alā 'Innahum Yathnūna Şudūrahum Liyastakhfū Minhu  ۚ  'Alā Ĥīna Yastaghshūna Thiyābahum Ya`lamu Mā Yusirrūna Wa Mā Yu`linūna  ۚ  'Innahu `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri 011-005 To, lalle sũ sunã karkatar da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.  ۚ   ۚ 
Wa Mā Min Dābbatin Al-'Arđi 'Illā `Alá Al-Lahi Rizquhā Wa Ya`lamu Mustaqarrahā Wa Mustawda`ahā  ۚ  Kullun Fī Kitābin Mubīnin 011-006 Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa fãce ga Allah arzikinta yake, kuma Yanã sanin matabbatarta da ma'azarta, duka sunã cikin littãfi bayyananne.  ۚ 
Wa Huwa Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Fī Sittati 'Ayyāmin Wa Kāna `Arshuhu `Alá Al-Mā'i Liyabluwakum 'Ayyukum 'Aĥsanu `Amalāan  ۗ  Wa La'in Qulta 'Innakum Mabthūna Min Ba`di Al-Mawti Layaqūlanna Al-Ladhīna Kafarū 'In Hādhā 'Illā Siĥrun Mubīnun 011-007 Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma Al'arshinSa ya kasance akan ruwa, dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne daga cikinku mafi kyãwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: "Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a bãyan mutuwa," haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce sihiri bayyananne."  ۗ 
Wa La'in 'Akhkharnā `Anhumu Al-`Adhāba 'Ilá 'Ummatin Ma`dūdatin Layaqūlunna Mā Yaĥbisuhu  ۗ  'Alā Yawma Ya'tīhim Laysa Maşrūfāan `Anhum Wa Ĥāqa Bihim Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn 011-008 Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azãba gare su zuwa ga wani lõkaci ƙidãyayye, haƙĩƙa sunãcẽwa me yake tsare ta? To, a rãnar da zã ta je musu, ba ta zama abin karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yã wajaba a kansu. ~  ۗ 
Wa La'in 'Adhaq Al-'Insāna Minnā Raĥmatan Thumma Naza`nāhā Minhu 'Innahu Laya'ūsun Kafūrun 011-009 Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma Muka zãre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammãnine, mai yawan kãfrci.
Wa La'in 'Adhaqnāhu Na`mā'a Ba`da Đarrā'a Massat/hu Layaqūlanna Dhahaba As-Sayyi'ātu `Annī  ۚ  'Innahu Lafariĥun Fakhūrun 011-010 Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana masa ni'ima a bãyan cũta ta shãfe shi, Yana cẽwa mũnanan halaye sun tafi daga wurina. Lalle shi mai farin ciki ne, mai alfahari.  ۚ 
'Illā Al-Ladhīna Şabarū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti 'Ūlā'ika Lahum Maghfiratun Wa 'Ajrun Kabīrun 011-011 Sai waɗanda suka yi haƙuri kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai. Waɗannan sunã da gãfara da lãda mai girma.
Fala`allaka Tārikun Ba`đa Mā Yūĥá 'Ilayka Wa Đā'iqun Bihi Şadruka 'An Yaqūlū Lawlā 'Unzila `Alayhi Kanzun 'Aw Jā'a Ma`ahu Malakun  ۚ  'Innamā 'Anta Nadhīrun Wa  ۚ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Wa Kīlun 011-012 Sabõda haka tsammãninka kai mai barin sãshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dõmin sun ce: "Dõmin me ba a saukar masa da wata taska ba, kõ kuma Malã'ika ya zo tãre de shi?" Kai mai gargaɗi ne kawai. Kuma Allah ne wakili a kan kõme.  ۚ   ۚ 
'Am Yaqūlūna Aftarāhu  ۖ  Qul Fa'tū Bi`ashri Suwarin Mithlihi Muftarayātin Wa Ad`ū Mani Astaţa`tum Min Dūni Al-Lahi 'In Kuntum Şādiqīna 011-013 Kõ sunã cewa: "Yã ƙirƙira shi ne."Ka ce: "Sai ku zo da sũrõri gõma misãlinsa ƙirƙirarru, kuma ku kirãyi wanda kuke iyãwa, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya."  ۖ 
Fa'illam Yastajībū Lakum Fā`lamū 'Annamā 'Unzila Bi`ilmi Al-Lahi Wa 'An Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  Fahal 'Antum Muslimūna 011-014 To, idan ba su amsa muku ba, to, ku sani cẽwa an saukar da shi kawai ne da sanin Allah, kuma cẽwa bãbu abin bauta wa fãce Shi. To, shin, kũ mãsu sallamãwa ne?, ~  ۖ 
Man Kāna Yurīdu Al-Ĥayāata Ad-Dunyā Wa Zīnatahā Nuwaffi 'Ilayhim 'A`mālahum Fīhā Wa Hum Fīhā Lā Yubkhasūna 011-015 Wanda ya kasance yã yi nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, Munã cika musu ayyukansu zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta bã zã a rage su ba.
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Laysa Lahum Al-'Ākhirati 'Illā An-Nāru  ۖ  Wa Ĥabiţa Mā Şana`ū Fīhā Wa Bāţilun Mā Kānū Ya`malūna 011-016 Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka sanã'anta a cikinta (dũniya) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa ɓãtacce ne.  ۖ 
'Afaman Kāna `Alá Bayyinatin Min Rabbihi Wa Yatlūhu Shāhidun Minhu Wa Min Qablihi Kitābu Mūsá 'Imāmāan Wa Raĥmatan  ۚ  'Ūlā'ika Yu'uminūna Bihi  ۚ  Wa Man Yakfur Bihi Mina Al-'Aĥzābi Fālnnāru Maw`iduhu  ۚ  Falā Takun Fī Miryatin Minhu  ۚ  'Innahu Al-Ĥaqqu Min Rabbika Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Yu'uminūna 011-017 Shin, wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma wata shaida tanã biyar sa daga gare Shi, kuma a gabãninsa akwai littãfin Mũsãabin kõyi da rahama? Waɗannan sunã yin ĩmãni da shi, kuma wanda ya kãfirta da shi daga ƙungiyõyi, to, wutã ce makõmarsa. Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga gare shi. Lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka, amma kuma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Man 'Ažlamu Mimmani Aftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan  ۚ  'Ūlā'ika Yu`rađūna `Alá Rabbihim Wa Yaqūlu Al-'Ash/hādu Hā'uulā' Al-Ladhīna Kadhabū `Alá Rabbihim  ۚ  'Alā La`natu Al-Lahi `Alá Až-Žālimīna 011-018 Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah? Waɗannan anã gitta su ga Ubangijinsu, kuma mãsu shaida su ce: "Waɗannan ne suka yi ƙarya ga Ubangijinsu. To, la'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."  ۚ   ۚ 
Al-Ladhīna Yaşuddūna `An Sabīli Al-Lahi Wa Yabghūnahā `Iwajāan Wa Hum Bil-'Ākhirati Hum Kāfirūna 011-019 Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah kuma sunã nẽman ta karkace, kuma sũ ga Lãhira sunã kãfirta.
'Ūlā'ika Lam Yakūnū Mu`jizīna Fī Al-'Arđi Wa Mā Kāna Lahum Min Dūni Al-Lahi Min 'Awliyā'a  ۘ  Yuđā`afu Lahumu Al-`Adhābu  ۚ  Mā Kānū Yastaţī`ūna As-Sam`a Wa Mā Kānū Yubşirūna 011-020 Waɗannan ne ba su kasance mabuwãya ba a cikin ƙasa, kuma waɗansu masõya ba su kasance ba a gare su, baicin Allah. Anã ninka musu azãba, ba su kasance sunã iya ji ba, kuma ba su kasance sunã gani ba.  ۘ   ۚ 
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Khasirū 'Anfusahum Wa Đalla `Anhum Mā Kānū Yaftarūna 011-021 Waɗannan ne wɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirawa ya ɓace musu.
Lā Jarama 'Annahum Al-'Ākhirati Humu Al-'Akhsarūna 011-022 Bãbu makawã cẽwa, haƙĩƙa, sũ a lãhira, sũ ne mafi hasãra.
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Wa 'Akhbatū 'Ilá Rabbihim 'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Jannati  ۖ  Hum Fīhā Khālidūna 011-023 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi tawãlu'i zuwa ga Ubangijinsu, waɗannan ne abõkan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.  ۖ 
Mathalu Al-Farīqayni Kāl'a`má Wa Al-'Aşammi Wa Al-Başīri Wa As-Samī`i  ۚ  Hal Yastawiyāni Mathalāan  ۚ  'Afalā Tadhakkarūna 011-024 Misãlin ɓangaren biyu kamar makãho ne da kurmã, da mai gani da mai ji. Shin, sunã daidaita ga misãli? Ashe, bã ku yin tunãni?  ۚ   ۚ 
Wa Laqad 'Arsalnā Nūĥāan 'Ilá Qawmihi 'Innī Lakum Nadhīrun Mubīnun 011-025 Kuma haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutanensa, (ya ce): "Lalle ne ni, a gare ku mai gargaɗi bayyananne ne." ~
'An Lā Ta`budū 'Illā Al-Laha  ۖ  'Innī 'Akhāfu `Alaykum `Adhāba Yawmin 'Alīmin 011-026 "Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ, inã jin tsõron azãbar yini mai raɗaɗi a kanku."  ۖ 
Faqāla Al-Mala'u Al-Ladhīna Kafarū Min Qawmihi Mā Narāka 'Illā Basharāan Mithlanā Wa Mā Narāka Attaba`aka 'Illā Al-Ladhīna Hum 'Arādhilunā Bādiya Ar-Ra'yi Wa Mā Nará Lakum `Alaynā Min Fađlin Bal Nažunnukumdhibīna 011-027 Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta, daga mutãnensa, suka ce: "Bã mu ganin ka fãce mutum kake kamarmu, kuma ba mu ganin wani ya bĩ ka fãce waɗanda suke sũ ƙasƙantattunmu ne marasa tunani. Kuma bã mu ganin wata falalã agare ka a kanmu. Ã'a, Munã zaton ku maƙaryata ne."
Qāla Yā Qawmi 'Ara'aytum 'In Kuntu `Alá Bayyinatin Min Rabbī Wa 'Ātānī Raĥmatan Min `Indihi Fa`ummiyat `Alaykum 'Anulzimukumūhā Wa 'Antum Lahā Kārihūna 011-028 Ya ce: "Ya mutãnena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Yã bã ni wata Rahama daga wurinSa, Sa'an nan aka rufe ta (ita Rahamar) daga gare ku, shin, zã mu tĩlasta mukuita, alhãli kuwa kũ mãsu ƙi gare ta ne?
Wa Yāqawmi Lā 'As'alukum `Alayhi Mālāan 'In  ۖ  'Ajriya 'Illā `Alá Al-Lahi Wa Mā  ۚ  'Anā Biţāridi Al-Ladhīna 'Āmanū 'Innahum  ۚ  Mulāqū Rabbihim Wa Lakinnī 'Arākum Qawmāan Tajhalūna 011-029 "Kuma yã mutãnena! Bã zan tambaye ku wata dũkiya ba akansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce daga Allah, kuma ban zama mai kõrar waɗanda suka yĩ ĩmãni ba. Haƙĩƙa sũ, mãsu haɗuwa da Ubangijinsu ne, kuma amma ni, inã ganin ku mutãne ne jãhilai."  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa Yāqawmi Man Yanşurunī Mina Al-Lahi 'In Ţaradtuhum 'Afalā  ۚ  Tadhakkarūna 011-030 "Kuma ya mutãnena! Wãne ne yake taimakõna daga Allah idan na kõre su? Ashe, bã ku tunãni?"  ۚ 
Wa Lā 'Aqūlu Lakum `InKhazā'inu Al-Lahi Wa Lā 'A`lamu Al-Ghayba Wa Lā 'Aqūlu 'Innī Malakun Wa Lā 'Aqūlu Lilladhīna Tazdarī 'A`yunukum Lan Yu'utiyahumu Al-Lahu Khayrāan  ۖ  Al-Lahu 'A`lamu Bimā Fī 'Anfusihim  ۖ  'Innī 'Idhāan Lamina Až-Žālimīna 011-031 "Kuma bã ni ce muku a wurĩna taskõkin Allah suke kuma bã inã sanin gaibi ba ne. Kuma ba inã cẽwa ni Malã'ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idãnunku suke wulãkantãwa, Allah bã zai bã su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nã yi haka) dã ina daga cikin azzalumai."  ۖ   ۖ 
Qālū Yā Nūĥu Qad Jādaltanā Fa'aktharta Jidālanā Fa'tinā Bimā Ta`idunā 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna 011-032 Suka ce: "Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa'an nan kã yawaita yi mana jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Qāla 'Innamā Ya'tīkum Bihi Al-Lahu 'In Shā'a Wa Mā 'Antum Bimu`jizīna 011-033 Ya ce: "Allah kawai ne Yake zo muku da shi idan Ya so. Kuma ba ku zama mabuwãya ba."
Wa Lā Yanfa`ukum Nuşĥī 'In 'Aradtu 'An 'Anşaĥa Lakum 'In Kāna Al-Lahu Yurīdu 'An Yughwiyakum  ۚ  Huwa Rabbukum Wa 'Ilayhi Turja`ūna 011-034 "Kuma nasĩhãta bã zã ta amfãne ku ba, idan nã yi nufin in yi muku nasĩha, idan Allah Yakasance Yanã nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."  ۚ 
'Am Yaqūlūna Aftarāhu  ۖ  Qul 'Ini Aftaraytuhu Fa`alayya 'Ijrāmī Wa 'Anā Barī'un Mimmā Tujrimūna 011-035 Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: "Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to, laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi."  ۖ 
Wa 'Ūĥiya 'Ilá Nūĥin 'Annahu Lan Yu'umina Min Qawmika 'Illā Man Qad 'Āmana Falā Tabta'is Bimā Kānū Yaf`alūna 011-036 Kuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne bãbu mai yin ĩmãni daga mutãnenka fãce wanda ya riga ya yi ĩmãnin, sabõdahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Wa Aşna`i Al-Fulka Bi'a`yuninā Wa Waĥyinā Wa Lā Tukhāţibnī Fī Al-Ladhīna Žalamū  ۚ  'Innahum Mughraqūna 011-037 Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini magana a cikin sha'anin waɗanda suka kãfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa ne.  ۚ 
Wa Yaşna`u Al-Fulka Wa Kullamā Marra `Alayhi Mala'un Min Qawmihi Sakhirū Minhu  ۚ  Qāla 'In Taskharū Minnā Fa'innā Naskharu Minkum Kamā Taskharūna 011-038 Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili.  ۚ 
Fasawfa Ta`lamūna Man Ya'tīhi `Adhābun Yukhzīhi Wa Yaĥillu `Alayhi `Adhābun Muqīmun 011-039 "Sa'an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira)."
Ĥattá 'Idhā Jā'a 'Amrunā Wa Fāra At-Tannūru Qulnā Aĥmil Fīhā Min Kullin Zawjayni Athnayni Wa 'Ahlaka 'Illā Man Sabaqa `Alayhi Al-Qawlu Wa Man 'Āmana  ۚ  Wa Mā 'Āmana Ma`ahu 'Illā Qalīlun 011-040 Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa, da wanda ya yi ĩmãni." Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan."  ۚ  ~
Wa Qāla Arkabū Fīhā Bismi Al-Lahi Majrāhā Wa Mursāhā  ۚ  'Inna Rabbī Laghafūrun Raĥīmun 011-041 Kuma ya ce: "Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudãnarta da matabbatarta. Lalle ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."  ۚ 
Wa Hiya Tajrī Bihim Fī Mawjin Kāljibāli Wa Nādá Nūĥun Abnahu Wa Kāna Fī Ma`zilin Yā Bunayya Arkab Ma`anā Wa Lā Takun Ma`a Al-Kāfirīna 011-042 Kuma ita tanã gudãna da su a cikin tãguwar ruwa kamai duwãtsu, sai Nũhu ya kirãyi ɗansa alhãli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. "Yã ƙaramin ɗãnã! zo ka hau tãre da mu, kuma kada ka kasance tãre da kãfirai!"
Qāla Sa'āwī 'Ilá Jabalin Ya`şimunī Mina Al-Mā'i  ۚ  Qāla Lā `Āşima Al-Yawma Min 'Amri Al-Lahi 'Illā Man Raĥima  ۚ  Wa Ĥāla Baynahumā Al-Mawju Fakāna Mina Al-Mughraqīna 011-043 Ya ce: "Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan." (Nũhu) ya ce: "Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama." Sai taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar.  ۚ   ۚ 
Wa Qīla Yā 'Arđu Abla`ī Mā'aki Wa Yā Samā'u 'Aqli`ī Wa Ghīđa Al-Mā'u Wa Quđiya Al-'Amru Wa Astawat `Alá Al-Jūdīyi  ۖ  Wa Qīla Bu`dāan Lilqawmi Až-Žālimīna 011-044 Kuma aka ce: "Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme."Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi, kuma aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai."  ۖ 
Wa Nādá Nūĥun Rabbahu Faqāla Rabbi 'Inna Abnī Min 'Ahlī Wa 'Inna Wa`daka Al-Ĥaqqu Wa 'Anta 'Aĥkamu Al-Ĥākimīna 011-045 Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu yin hukunci."
Qāla Yā Nūĥu 'Innahu Laysa Min 'Ahlika  ۖ  'Innahu `Amalun Ghayru Şāliĥin  ۖ  Falā Tas'alni Mā Laysa Laka Bihi `Ilmun  ۖ  'Innī 'A`ižuka 'An Takūna Mina Al-Jāhilīna 011-046 Ya ce: "Yã Nũhu! Lalle ne shi bã ya a ciki iyãlanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda ba na ƙwarai ba, sabõda haka kada ka tambaye Ni abin da bã ka da ilmi a kansa. Haƙĩƙa, Nĩ Inã yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jãhilai."  ۖ   ۖ   ۖ 
Qāla Rabbi 'Innī 'A`ūdhu Bika 'An 'As'alaka Mā Laysa Lī Bihi `Ilmun  ۖ  Wa 'Illā Taghfir Lī Wa Tarĥamnī 'Akun Mina Al-Khāsirīna 011-047 Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra."  ۖ 
Qīla Yā Nūĥu Ahbiţ Bisalāmin Minnā Wa Barakātin `Alayka Wa `Alá 'Umamin Mimman Ma`aka  ۚ  Wa 'Umamun Sanumatti`uhum Thumma Yamassuhum Minnā `Adhābun 'Alīmun 011-048 Aka ce: "Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da waɗansu al'ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa'an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta shafe su daga gare Mu."  ۚ 
Tilka Min 'Anbā'i Al-Ghaybi Nūĥīhā 'Ilayka  ۖ  Mā Kunta Ta`lamuhā 'Anta Wa Lā Qawmuka Min Qabli Hādhā  ۖ  Fāşbir  ۖ  'Inna Al-`Āqibata Lilmuttaqīna 011-049 Waccan ƙissa tanã daga lãbãran gaibi, Munã yin wahayinsu zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance kanã sanin su ba, haka kuma mutãnenka ba su sani ba daga gabãnin wannan. Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ãƙiba tanã ga mãsu taƙawa,  ۖ   ۖ   ۖ 
Wa 'Ilá `Ādin 'Akhāhum Hūdāan  ۚ  Qāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu  ۖ  'In 'Antum 'Illā Muftarūna 011-050 Kuma zuwa ga Ãdãwa, (Mun aika) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: "Yã kũ mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Ba ku kasance ba fãce kunã mãsu ƙirƙirãwa.  ۚ  ~  ۖ 
Yā Qawmi Lā 'As'alukum `Alayhi 'Ajrāan  ۖ  'In 'Ajriya 'Illā `Alá Al-Ladhī Faţaranī  ۚ  'Afalā Ta`qilūna 011-051 "Yã ku mutãnena! Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce ga wanda Ya ƙãga halittata. Shin fa, bã ku hankalta?"  ۖ   ۚ 
Wa Yā Qawmi Astaghfirū Rabbakum Thumma Tūbū 'Ilayhi Yursili As-Samā'a `Alaykum Midrārāan Wa Yazidkum Qūwatan 'Ilá Qūwatikum Wa Lā Tatawallaw Mujrimīna 011-052 "Kuma, ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi,zai saki sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi."
Qālū Yā Hūdu Mā Ji'tanā Bibayyinatin Wa Mā Naĥnu Bitārikī 'Ālihatinā `An Qawlika Wa Mā Naĥnu Laka Bimu'uminīna 011-053 Suka ce: "Yã Hũdu! Ba ka zo mana da wata hujja bayyananna ba, kuma ba mu zama mãsu barin abũbuwan bautawarmu ba dõmin maganarka, kuma ba mu zama mãsu yin ĩmãni da kai ba."
'In Naqūlu 'Illā A`tarāka Ba`đu 'Ālihatinā Bisū'in  ۗ  Qāla 'Innī 'Ush/hidu Al-Laha Wa Ash/hadū 'Annī Barī'un Mimmā Tushrikūna 011-054 "Bã mu cẽwa, sai dai kurum sashen abũbuwan bautawarmu ya sãme ka da cũtar hauka." Yace: "Lalle ne nĩ, inã shaida waAllah, kuma ku yi shaidar cẽwa" lalle ne nĩ mai barranta ne dagb abin da kuke yin shirki da shi."  ۗ 
Min Dūnihi  ۖ  Fakīdūnī Jamī`āan Thumma Lā Tunžirūni 011-055 "Baicin Allah: Sai ku yi mini kaidi gabã ɗaya, sa'an nan kuma kada ku yi mini jinkiri."  ۖ 
'Innī Tawakkaltu `Alá Al-Lahi Rabbī Wa Rabbikum  ۚ  Mā Min Dābbatin 'Illā Huwa 'Ākhidhun Bināşiyatihā  ۚ  'Inna Rabbī `Alá Şirāţin Mustaqīmin 011-056 "Haƙĩƙa, ni na dõgara ga Allah, Ubangijĩna kuma Ubangijinku. Bãbu wata dabba fãce Shi ne Mai riko ga kwarkwaɗarta. Haƙĩƙa, Ubangijĩna Yanã (kan) tafarki madaidaici."  ۚ   ۚ 
Fa'in Tawallaw Faqad 'Ablaghtukum Mā 'Ursiltu Bihi 'Ilaykum  ۚ  Wa Yastakhlifu Rabbī Qawmāan Ghayrakum Wa Lā Tađurrūnahu Shay'āan  ۚ  'Inna Rabbī `Alá Kulli Shay'in Ĥafīžun 011-057 "To! Idan kun jũya, haƙĩƙa, nã iyar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku. Kuma Ubangijĩna Yanã musanya waɗansu mutãne, waɗansunku su maye muku. Kuma bã ku cũtar Sa da kõme. Lalle Ubangijina a kan dukkan kõme, Matsari ne." ~  ۚ   ۚ 
Wa Lammā Jā'a 'Amrunā Najjaynā Hūdāan Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Ma`ahu Biraĥmatin Minnā Wa Najjaynāhum Min `Adhābin Ghalīžin 011-058 Kuma a lõkacin da umurninmu ya je, Muka kuɓutar da Hũdu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõdawata rahama daga gare Mu. Kuma Muka kuɓutr da su daga azãba mai kauri.
Wa Tilka `Ādun  ۖ  Jaĥadū Bi'āyāti Rabbihim Wa `Aşaw Rusulahu Wa Attaba`ū 'Amra Kulli Jabbārin `Anīdin 011-059 Haka Ãdãwa suka kasance, sun yi musun ãyõyin Ubangijinsu, kuma sun sãɓa wa ManzanninSa, kuma sun bi umurnin dukan mai girman kai, makangari.  ۖ 
Wa 'Utbi`ū Fī Hadhihi Ad-Dunyā La`natan Wa Yawma Al-Qiyāmati  ۗ  'Alā 'Inna `Ādāan Kafarū Rabbahum  ۗ  'Alā Bu`dāan Li`ādin Qawmi Hūdin 011-060 Kuma an biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. To! Lalle ne Ãdãwa sun kãfirta da Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Ãdãwa, mutãnen Hũdu!  ۗ   ۗ 
Wa 'Ilá Thamūda 'Akhāhum Şāliĥāan  ۚ  Qāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu  ۖ  Huwa 'Ansha'akum Mina Al-'Arđi Wa Asta`marakum Fīhā Fāstaghfirūhu Thumma Tūbū 'Ilayhi  ۚ  'Inna Rabbī Qarībun Mujībun 011-061 Kuma zuwa ga Samũdãwa (an aika) ɗan'uwansu Sãlihu. Ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Shĩ ne Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma Ya sanya ku mãsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karɓãwa."  ۚ   ۖ   ۚ 
Qālū Yā Şāliĥu Qad Kunta Fīnā Marjūwāan Qabla Hādhā  ۖ  'Atanhānā 'An Na`buda Mā Ya`budu 'Ābā'uunā Wa 'Innanā Lafī Shakkin Mimmā Tad`ūnā 'Ilayhi Murībin 011-062 Suka ce: "Ya Sãlihu! Haƙĩƙa, kã kasance a cikinmu, wanda ake fatan wani alhẽri da shi a gabãnin wannan. Shin kana hana mu bauta wa abin da ubanninmu suke bauta wa? Kuma haƙĩƙa mũ, munã cikin shakka daga abin da kake kiran mu gare shi, mai sanya kõkanto."  ۖ 
Qāla Yā Qawmi 'Ara'aytum 'In Kuntu `Alá Bayyinatin Min Rabbī Wa 'Ātānī Minhu Raĥmatan Faman Yanşurunī Mina Al-Lahi 'In `Aşaytuhu  ۖ  Famā Tazīdūnanī Ghayra Takhsīrin 011-063 Ya ce: "Ya mutãnẽna! Kun gani? Idan na kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Ya bã ni rahama daga gare Shi, to, wane ne zai taimake ni daga Allah idan nã sãɓa Masa? Sa'an nan bã zã ku ƙãre ni da kõme ba fãce hasãra."  ۖ 
Wa Yā Qawmi Hadhihi Nāqatu Al-Lahi Lakum 'Āyatan Fadharūhā Ta'kul Fī 'Arđi Al-Lahi Wa Lā Tamassūhā Bisū'in Faya'khudhakum `Adhābun Qarībun 011-064 "Kuma ya mutãnena! wannan rãƙumar Allah ce, tanã ãyã a gare ku. Sai ku bar ta ta ci a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta kar azãba makusanciya ta kãma ku."
Fa`aqarūhā Faqāla Tamatta`ū Fī Dārikum Thalāthata 'Ayyāmin  ۖ  Dhālika Wa`dun Ghayru Makdhūbin 011-065 Sai suka sõke ta. Sai ya ce: "Kuji dãɗi a cikin gidãjenku kwãna uku. Wannan wa'adi ne bã abin ƙaryatãwa ba."  ۖ 
Falammā Jā'a 'Amrunā Najjaynā Şāliĥāan Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Ma`ahu Biraĥmatin Minnā Wa Min Khizyi Yawmi'idhin  ۗ  'Inna Rabbaka Huwa Al-Qawīyu Al-`Azīzu 011-066 To, a lõkacin da umurninMu ya je, muka kuɓutar da Sãlihu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma daga wulãkancin rãnar nan. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMai ƙarfi, Mabuwãyi.  ۗ 
Wa 'Akhadha Al-Ladhīna Žalamū Aş-Şayĥatu Fa'aşbaĥū Fī Diyārihimthimīna 011-067 Sai tsãwa ta kãma waɗanda suka yi zãlunci, sai suka wãyi gari sunã guggurfãne a cikin gidãjensu.
Ka'an Lam Yaghnaw Fīhā  ۗ  'Alā 'Inna Thamūda Kafarū Rabbahum  ۗ  'Alā Bu`dāan Lithamūda 011-068 Kamar dai ba su zauna a cikinta ba. To! Lalle ne samũdãwa sun kãfirce wa Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Samũdãwa.  ۗ   ۗ 
Wa Laqad Jā'at Rusulunā 'Ibrāhīma Bil-Bushrá Qālū Salāmāan  ۖ  Qāla Salāmun  ۖ  Famā Labitha 'An Jā'a Bi`ijlin Ĥanīdhin 011-069 Kuma haƙĩƙa, manzanninMu sun je wa Ibrãhim da bushãra suka ce: "Aminci." Ya ce: "Aminci (ya tabbata a gare ku)." Sa'an nan bai yi jinkiri ba ya je da maraƙi ƙawãtacce.  ۖ   ۖ 
Falammā Ra'á 'Aydiyahum Lā Taşilu 'Ilayhi Nakirahum Wa 'Awjasa Minhum Khīfatan  ۚ  Qālū Lā Takhaf 'Innā 'Ursilnā 'Ilá Qawmi Lūţin 011-070 Sa'an nan a lõkacin da ya ga hannayensu bã su sãduwa zuwa gare shi (maraƙin), sai ya yi ƙyãmarsu, kuma ya ji tsõronsu. Suka ce, "Kada kaji tsõro lalle ne mũ, an aiko mu ne zuwa ga mutãnen Lũɗu"  ۚ 
Wa Amra'atuhu Qā'imatun Fađaĥikat Fabashsharnāhā Bi'isĥāqa Wa Min Warā'i 'Isĥāqa Ya`qūba 011-071 Kuma mãtarsa tanã tsaye . Ta yi dãriya. Sai Muka yi mata bushãra (da haihuwar) Is'hãƙa, kuma a bayan Is'hãƙa, Yãƙũbu.
Qālat Yā Waylatā 'A'alidu Wa 'Anā `Ajūzun Wa Hadhā Ba`lī Shaykhāan  ۖ  'Inna Hādhā Lashay'un `Ajībun 011-072 Sai ta ce: "Yã kaitõna! Shin, zan haihu ne alhãli kuwa inã tsõhuwa, kuma ga mijĩna tsõho ne? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmãki."  ۖ 
Qālū 'Ata`jabīna Min 'Amri Al-Lahi  ۖ  Raĥmatu Al-Lahi Wa Barakātuhu `Alaykum 'Ahla Al-Bayti  ۚ  'Innahu Ĥamīdun Majīdun 011-073 Suka ce: "Shin kinã mãmaki ne daga al'amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarSa su tabbata a kanku, ya mutãnen babban gida! Lalle ne Shĩ abin gõdewa ne, Mai girma."  ۖ   ۚ 
Falammā Dhahaba `An 'Ibrāhīma Ar-Raw`u Wa Jā'at/hu Al-Bushrá Yujādilunā Fī Qawmi Lūţin 011-074 To, a lõkacin da firgita ta tafi daga Ibrãhĩm, kuma bushãra tã je masa, Yanã mai jayayya a gare Mu, sabõda mutãnen Lũɗu!
'Inna 'Ibrāhīma Laĥalīmun 'Awwāhun Munībun 011-075 Lalle Ibrãhĩm, haƙĩƙa mai haƙuri ne, mai yawan addu'a, mai tawakkali.
Yā 'Ibrāhīmu 'A`riđ `An Hādhā  ۖ  'Innahu Qad Jā'a 'Amru Rabbika  ۖ  Wa 'Innahum 'Ātīhim `Adhābun Ghayru Mardūdin 011-076 Ya Ibrãhĩm! Ka bijira daga wannan. Lalle shi, haƙĩƙa, umurnin Ubangijinka ne ya zo, kuma lalle ne sũ, abin da yake mai je musu azãba ce wadda bã a iya hanãwa.  ۖ   ۖ 
Wa Lammā Jā'at Rusulunā Lūţāan Sī'a Bihim Wa Đāqa Bihim Dhar`āan Wa Qāla Hādhā Yawmun `Aşībun 011-077 Kuma a lõkacin da manzanninMu suka je wa Lũɗu aka ɓãta masa rai game da su, ya, ƙuntata rai sabõda su. Ya ce: "Wannan yini ne mai tsananin masĩfa."
Wa Jā'ahu Qawmuhu Yuhra`ūna 'Ilayhi Wa Min Qablu Kānū Ya`malūna As-Sayyi'āti  ۚ  Qāla Yā Qawmi Hā'uulā' Banātī Hunna 'Aţharu Lakum Fa  ۖ  Attaqū Al-Laha Wa Lā Tukhzūnī Fī Đayfī  ۖ  'Alaysa Minkum Rajulun Rashīdun 011-078 Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: "Yã mutãnẽna! waɗannan, 'yã'yã na sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku?"  ۚ   ۖ   ۖ 
Qālū Laqad `Alimta Mā Lanā Fī Banātika Min Ĥaqqin Wa 'Innaka Lata`lamu Mā Nurīdu 011-079 Suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kã sani, bã mu da wani hakki a cikin 'ya'yanka, kuma lalle kai haƙĩƙa, kanã sane da abin da muke nufi."
Qāla Law 'Anna Lī Bikum Qūwatan 'Aw 'Āwī 'Ilá Ruknin Shadīdin 011-080 Ya ce: "Dã dai inã da wani ƙarfi game da ku, kõ kuwa inã da gõyon bãya daga wani rukuni mai ƙarfi?"
Qālū Yā Lūţu 'Innā Rusulu Rabbika Lan Yaşilū 'Ilayka  ۖ  Fa'asri Bi'ahlika Biqiţ`in Mina Al-Layli Wa Lā Yaltafit Minkum 'Aĥadun 'Illā Amra'ataka  ۖ  'Innahu Muşībuhā Mā 'Aşābahum  ۚ  'Inna Maw`idahumu Aş-Şubĥu  ۚ  'Alaysa Aş-Şubĥu Biqarībin 011-081 (Manzannin) Suka ce: "Yã Lũɗu! Lalle mũ, manzannin Ubangijinka ne. Bã zã su iya sãduwa zuwa gare ka ba. Sai ka yi tafiyarka a wani yankin dare da iyãlinka, kuma kada wani daga gare ku ya waiwaya fãce mãtarka. Lalle ne abin da ya same su mai sãmunta ne. Lalle wa'adinsu lõkacin sãfiya ne. Shin lõkacin sãfiya bã kusa ba ne?"  ۖ   ۖ   ۚ   ۚ 
Falammā Jā'a 'Amrunā Ja`alnā `Āliyahā Sāfilahā Wa 'Amţarnā `Alayhā Ĥijāratan Min Sijjīlin Manđūdin 011-082 Sa'an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre.
Musawwamatan `Inda Rabbika  ۖ  Wa Mā Hiya Mina Až-Žālimīna Biba`īdin 011-083 Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita (ƙasar Lũɗu)ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai (kuraishãwa).  ۖ 
Wa 'Ilá Madyana 'Akhāhum Shu`aybāan  ۚ  Qāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu  ۖ  Wa Lā Tanquşū Al-Mikyā La Wa  ۚ  Al-Mīzāna 'Innī 'Arākum Bikhayrin Wa 'Innī 'Akhāfu `Alaykum `Adhāba Yawmin Muĥīţin 011-084 Kuma zuwa ga Madyana (Mun aika) ɗan'uwansu Shu'aibu. Ya ce: "Ya Mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce shi kuma kada ku rage mũdu da sikẽli. Lalle nĩ, inã ganin ku da wadãta. Kuma lalle inã ji muku tsõron azãbar yini mai kẽwayẽwa."  ۚ   ۖ   ۚ 
Wa Yā Qawmi 'Awfū Al-Mikyāla Wa Al-Mīzāna Bil-Qisţi  ۖ  Wa Lā Tabkhasū An-Nāsa 'Ashyā'ahum Wa Lā Ta`thaw Fī Al-'Arđi Mufsidīna 011-085 "Ya mutãnẽna! Ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, kuma kada ku naƙasta wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi ɓarnã a cikin ƙasa kunã mãsu fasãdi."  ۖ 
Baqīyatu Al-Lahi Khayrun Lakum 'In Kuntum Mu'uminīna  ۚ  Wa Mā 'Anā `Alaykum Biĥafīžin 011-086 "Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni bã mai tsaro ne a kanku ba."  ۚ 
Qālū Yā Shu`aybu 'Aşalātuka Ta'muruka 'An Natruka Mā Ya`budu 'Ābā'uunā 'Aw 'An Naf`ala Fī 'Amwālinā Mā Nashā'u  ۖ  'Innaka La'anta Al-Ĥalīmu Ar-Rashīdu 011-087 Suka ce: "Yã Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautãwa, kõ kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dũkiyõyinmu? Lalle, haƙĩƙa kai ne mai haƙuri shiryayye!"  ۖ 
Qāla Yā Qawmi 'Ara'aytum 'In Kuntu `Alá Bayyinatin Min Rabbī Wa Razaqanī Minhu Rizqāan Ĥasanāan  ۚ  Wa Mā 'Urīdu 'An 'Ukhālifakum 'Ilá Mā 'Anhākum `Anhu  ۚ  'In 'Urīdu 'Illā Al-'Işlāĥa Mā Astaţa`tu  ۚ  Wa Mā Tawfīqī 'Illā Bil-Lahi  ۚ  `Alayhi Tawakkaltu Wa 'Ilayhi 'Unību 011-088 Ya ce: "Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfaƙãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala."  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Yā Qawmi Lā Yajrimannakum Shiqāqī 'An Yuşībakum Mithlu Mā 'Aşāba Qawma Nūĥin 'Aw Qawma Hūdin 'Aw Qawma Şāliĥin  ۚ  Wa Mā Qawmu Lūţin Minkum Biba`īdin 011-089 "Kuma ya mutãnena! Kada sãɓa mini ya ɗauke ku ga misãlin abin da ya sãmi mutãnen Nũhu kõ kuwa mutãnen Hũdu kõ kuwa mutãnen Sãlihu ya sãme ku. Mutãnen Lũɗu ba su zama a wuri mai nĩsa ba daga gare ku."  ۚ 
Wa Astaghfirū Rabbakum Thumma Tūbū 'Ilayhi  ۚ  'Inna Rabbī Raĥīmun Wadūdun 011-090 "Kuma ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare shi. Lalle Ubangijĩna Mai Jin ƙai ne, Mai nũna sõyayya."  ۚ 
Qālū Yā Shu`aybu Mā Nafqahu Kathīrāan Mimmā Taqūlu Wa 'Innā Lanarāka Fīnā Đa`īfāan  ۖ  Wa Lawlā Rahţuka Larajamnāka  ۖ  Wa Mā 'Anta `Alaynā Bi`azīzin 011-091 Suka ce: "Yã Shu'aibu! Bã mu fahimta da yawa daga abin da kake faɗi, kuma munã ganin ka mai rauni a cikinmu. Kuma bã dõmin jama'arka ba dã mun jẽfe ka, sabõda ba ka zama mai daraja a gunmu ba."  ۖ   ۖ 
Qāla Yā Qawmi 'Arahţī 'A`azzu `Alaykum Mina Al-Lahi Wa Attakhadhtumūhu Warā'akum Žihrīyāan  ۖ  'Inna Rabbī Bimā Ta`malūna Muĥīţun 011-092 Ya ce: "Ya mutãnena! Ashe, jama'ãta ce mafi daraja a gare ku daga Allah, kuma kun riƙẽ Shi a bãyanku abin jẽfarwa? Lallene Ubangijĩna Mai kẽwayẽwa nega abin da kuke aikatãwa."  ۖ 
Wa Yā Qawmi A`malū `Alá Makānatikum 'Innī `Āmilun  ۖ  Sawfa Ta`lamūna Man Ya'tīhi `Adhābun Yukhzīhi Wa Man Huwa Kādhibun  ۖ  Wa Artaqibū 'Innī Ma`akum Raqībun 011-093 "Kuma ya mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku. Lalle nĩmai aiki ne. Da sannu zã ku san wãne ne azãba zã ta zo masa, ta wulakanta shi, kuma wãne ne maƙaryaci. Kuma ku yi jiran dãko, lalle ni mai dãko ne tãre da ku."  ۖ   ۖ 
Wa Lammā Jā'a 'Amrunā Najjaynā Shu`aybāan Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Ma`ahu Biraĥmatin Minnā Wa 'Akhadhati Al-Ladhīna Žalamū Aş-Şayĥatu Fa'aşbaĥū Fī Diyārihimthimīna 011-094 Kuma a lõkacin da umurninMu yã je, Muka kuɓutar da Shu'aibu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsãwa ta kama waɗanda suka yi zãlunci. Sai suka wãyi gari guggurfãne a cikin gidãjensu.
Ka'an Lam Yaghnaw Fīhā  ۗ  'Alā Bu`dāan Limadyana Kamā Ba`idat Thamūdu 011-095 Kamar ba su zaunã ba a cikinsu. To, halaka ta tabbata ga Madyana kamar yadda Samũdãwa suka halaka.  ۗ 
Wa Laqad 'Arsalnā Mūsá Bi'āyātinā Wa Sulţānin Mubīnin 011-096 Kuma haƙĩƙa Mun aiki Mũsã da ãyõyinMu, da dalĩli bayyananne.
'Ilá Fir`awna Wa Mala'ihi Fa Attaba`ū 'Amra Fir`awna  ۖ  Wa Mā 'Amru Fir`awna Birashīdin 011-097 Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa. Sai suka bi umurnin Fir'auna, amma al'amarin Fir'auna bai zama shiryayye ba.  ۖ 
Yaqdumu Qawmahu Yawma Al-Qiyāmati Fa'awradahumu An-Nāra  ۖ  Wa Bi'sa Al-Wirdu Al-Mawrūdu 011-098 Yanã shũgabantar mutãnensa a Rãnar Kiyãma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir da irin tuzgãwarsu.  ۖ 
Wa 'Utbi`ū Fī Hadhihi La`natan Wa Yawma Al-Qiyāmati  ۚ  Bi'sa Ar-Rifdu Al-Marfūdu 011-099 Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar da ake yi musu.  ۚ 
Dhālika Min 'Anbā'i Al-Qurá Naquşşuhu `Alayka  ۖ  Minhā Qā'imun Wa Ĥaşīdun 011-100 Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe.  ۖ 
Wa Mā Žalamnāhum Wa Lakin Žalamū 'Anfusahum  ۖ  Famā 'Aghnat `Anhum 'Ālihatuhumu Allatī Yad`ūna Min Dūni Al-Lahi Min Shay'in Lammā Jā'a 'Amru Rabbika  ۖ  Wa Mā Zādūhum Ghayra Tatbībin 011-101 Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu waɗanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijinka ya je, kuma (gumãkan) ba su ƙãra musu wani abu ba fãce hasãra.  ۖ   ۖ 
Wa Kadhalika 'Akhdhu Rabbika 'Idhā 'Akhadha Al-Qurá Wa Hiya Žālimatun  ۚ  'Inna 'Akhdhahu 'Alīmun Shadīdun 011-102 Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijinka, idan Ya kãma alƙaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũnSa mai raɗaɗi ne, mai tsanani.  ۚ  ~
'Inna Fī Dhālika La'āyatan Liman Khāfa `Adhāba Al-'Ākhirati  ۚ  Dhālika Yawmun Majmū`un Lahu An-Nāsu Wa Dhalika Yawmun Mash/hūdun 011-103 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta.  ۚ 
Wa Mā Nu'uakhkhiruhu 'Illā Li'jalin Ma`dūdin 011-104 Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali ƙidãyayye. ~
Yawma Ya'ti Lā Takallamu Nafsun 'Illā Bi'idhnihi  ۚ  Faminhum Shaqīyun Wa Sa`īdun 011-105 Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shaƙiyyi da mai arziki.  ۚ 
Fa'ammā Al-Ladhīna Shaqū Fafī An-Nāri Lahum Fīhā Zafīrun Wa Shahīqun 011-106 To, amma waɗanda suka yi shaƙãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu ƙãra da shẽka acikinta.
Khālidīna Fīhā Mā Dāmati As-Samāwātu Wa Al-'Arđu 'Illā Mā Shā'a Rabbuka  ۚ  'Inna Rabbaka Fa``ālun Limā Yurīdu 011-107 Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi.  ۚ 
Wa 'Ammā Al-Ladhīna Su`idū Fafī Al-Jannati Khālidīna Fīhā Mā Dāmati As-Samāwātu Wa Al-'Arđu 'Illā Mā Shā'a Rabbuka  ۖ  `Aţā'an Ghayra Majdhūdhin 011-108 Amma waɗanda suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama ,a cikinta, matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa.  ۖ 
Falā Taku Fī Miryatin Mimmā Ya`budu Hā'uulā'  ۚ  Mā Ya`budūna 'Illā Kamā Ya`budu 'Ābā'uuhum Min Qablu  ۚ  Wa 'Innā Lamuwaffūhum Naşībahum Ghayra Manqūşin 011-109 Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba.  ۚ   ۚ 
Wa Laqad 'Ātaynā Mūsá Al-Kitāba Fākhtulifa Fīhi  ۚ  Wa Lawlā Kalimatun Sabaqat Min Rabbika Laquđiya Baynahum  ۚ  Wa 'Innahum Lafī Shakkin Minhu Murībin 011-110 Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto.  ۚ   ۚ 
Wa 'Inna Kullā Lammā Layuwaffiyannahum Rabbuka 'A`mālahum  ۚ  'Innahu Bimā Ya`malūna Khabīrun 011-111 Kuma lalle, haƙĩƙa, Ubangijinka Mai cika wa kõwa (sakamakon) ayyukansa ne. Lalle Shĩ, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke aikatãwa.  ۚ 
Fāstaqim Kamā 'Umirta Wa Man Tāba Ma`aka Wa Lā Taţghaw  ۚ  'Innahu Bimā Ta`malūna Başīrun 011-112 Sai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.  ۚ 
Wa Lā Tarkanū 'Ilá Al-Ladhīna Žalamū Fatamassakumu An-Nāru Wa Mā Lakum Min Dūni Al-Lahi Min 'Awliyā'a Thumma Lā Tunşarūna 011-113 Kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba.
Wa 'Aqimi Aş-Şalāata Ţarafayi An-Nahāri Wa Zulafāan Mina Al-Layli  ۚ  'Inna Al-Ĥasanāti Yudh/hibna As-Sayyi'āti  ۚ  Dhālika Dhikrá Lildhdhākirīna 011-114 Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. wancan ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.  ۚ   ۚ 
Wa Aşbir Fa'inna Al-Laha Lā Yuđī`u 'Ajra Al-Muĥsinīna 011-115 Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa.
Falawlā Kāna Mina Al-Qurūni Min Qablikum 'Ūlū Baqīyatin Yanhawna `Ani Al-Fasādi Fī Al-'Arđi 'Illā Qalīlāan Mimman 'Anjaynā Minhum  ۗ  Wa Attaba`a Al-Ladhīna Žalamū Mā 'Utrifū Fīhi Wa Kānū Mujrimīna 011-116 To, don me mãsu hankali ba su kasance daga mutãnen ƙarnõnin da suke a gabãninku ba, sunã hani daga ɓarna a cikin ƙasa? fãce kaɗan daga wanda Muka kuɓutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma waɗanda suka yi zãlunci suka bin abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance mãsu laifi.  ۗ 
Wa Mā Kāna Rabbuka Liyuhlika Al-Qurá Bižulmin Wa 'Ahluhā Muşliĥūna 011-117 Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alƙaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa.
Wa Law Shā'a Rabbuka Laja`ala An-Nāsa 'Ummatan Wāĥidatan  ۖ  Wa Lā Yazālūna Mukhtalifīna 011-118 Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã Yã sanya mutãne al'umma guda. Kuma bã zã su gushe ba sunã mãsu sãɓã wa jũna.  ۖ 
'Illā Man Raĥima Rabbuka  ۚ  Wa Lidhalika Khalaqahum  ۗ  Wa Tammat Kalimatu Rabbika La'amla'anna Jahannama Mina Al-Jinnati Wa An-Nāsi 'Ajma`īna 011-119 Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan ne Ya halicce su. Kuma kalmar "Ubangijinka" Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba ɗaya" ta cika.  ۚ   ۗ 
Wa Kullāan Naquşşu `Alayka Min 'Anbā'i Ar-Rusuli Mā Nuthabbitu Bihi Fu'uādaka  ۚ  Wa Jā'aka Fī Hadhihi Al-Ĥaqqu Wa Maw`ižatun Wa Dhikrá Lilmu'uminīna 011-120 Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni.  ۚ 
Wa Qul Lilladhīna Lā Yu'uminūna A`malū `Alá Makānatikum 'Innā `Āmilūna 011-121 kuma kace wa waɗanda bã su yin ĩmãni, "Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne.
Wa Antažirū 'Innā Muntažirūna 011-122 "Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko ne."
Wa Lillahi Ghaybu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa 'Ilayhi Yurja`u Al-'Amru Kulluhu Fā`bud/hu Wa Tawakkal `Alayhi  ۚ  Wa Mā Rabbuka Bighāfilin `Ammā Ta`malūna 011-123 Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake. Kuma zuwa gare Shi ake mayar da dukan al'amari. Sabõda haka ku bauta Masa kuma ku dõgara a kanSa. Kuma Ubangijinka bai zama Mai gafala daga abin da kuke aikatãwa ba.  ۚ 
Next Sūrah