12) Sūrat Yūsuf

Printed format

12)

'Alif-Lām-Rā Tilka 'Āyātu Al-Kitābi Al-Mubīni 012-001 A. L̃. R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne. --
'Innā 'Anzalnāhu Qur'ānāan `Arabīyāan La`allakum Ta`qilūna 012-002 Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta.
Naĥnu Naquşşu `Alayka 'Aĥsana Al-Qaşaşi Bimā 'Awĥaynā 'Ilayka Hādhā Al-Qur'āna Wa 'In Kunta Min Qablihi Lamina Al-Ghāfilīna 012-003 Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa,daga gafalallu.
'Idh Qāla Yūsufu Li'abīhi Yā 'Abati 'Innī Ra'aytu 'Aĥada `Ashara Kawkabāan Wa Ash-Shamsa Wa Al-Qamara Ra'aytuhum Lī Sājidīna 012-004 A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni."
Qāla Yā Bunayya Lā Taqşuş Ru'uyā Ka `Alá 'Ikhwatika Fayakīdū Laka  ۖ  Kaydāan 'Inna Ash-Shayţāna Lil'insāni `Adūwun Mubīnun 012-005 Ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.  ۖ 
Wa Kadhalika Yajtabīka Rabbuka Wa Yu`allimuka Min Ta'wīli Al-'Aĥādīthi Wa Yutimmu Ni`matahu `Alayka Wa `Alá 'Āli Ya`qūba Kamā 'Atammahā `Alá 'Abawayka Min Qablu 'Ibrāhīma Wa 'Isĥāqa  ۚ  'Inna Rabbaka `Alīmun Ĥakīmun 012-006 "Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."  ۚ 
Laqad Kāna Fī Yūsufa Wa 'Ikhwatihi 'Āyātun Lilssā'ilīna 012-007 Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa dõmin mãsu tambaya.
'Idh Qālū Layūsufu Wa 'Akhūhu 'Aĥabbu 'Ilá 'Abīnā Minnā Wa Naĥnu `Uşbatun 'Inna 'Abānā Lafī Đalālin Mubīnin 012-008 A lõkacin da suka ce: lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya. ~
Aqtulū Yūsufa 'Awi Aţraĥūhu 'Arđāan Yakhlu Lakum Wajhu 'Abīkum Wa Takūnū Min Ba`dihi Qawmāan Şāliĥīna 012-009 Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai. ~
Qāla Qā'ilun Minhum Lā Taqtulū Yūsufa Wa 'Alqūhu Fī Ghayābati Al-Jubbi Yaltaqiţhu Ba`đu As-Sayyārati 'In Kuntum Fā`ilīna 012-010 Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
Qālū Yā 'Abānā Mā Laka Lā Ta'mannā `Alá Yūsufa Wa 'Innā Lahu Lanāşiĥūna 012-011 Suka ce: "Yã bãbanmu! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?"
'Arsilhu Ma`anā Ghadāan Yarta` Wa Yal`ab Wa 'Innā Lahu Laĥāfižūna 012-012 "Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne."
Qāla 'Innī Layaĥzununī 'An Tadh/habū Bihi Wa 'Akhāfu 'An Ya'kulahu Adh-Dhi'bu Wa 'Antum `Anhu Ghāfilūna 012-013 Ya ce: "Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi."
Qālū La'in 'Akalahu Adh-Dhi'bu Wa Naĥnu `Uşbatun 'Innā 'Idhāan Lakhāsirūna 012-014 Suka ce: "Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra."
Falammā Dhahabū Bihi Wa 'Ajma`ū 'An Yaj`alūhu Fī Ghayābati Al-Jubbi  ۚ  Wa 'Awĥaynā 'Ilayhi Latunabbi'annahum Bi'amrihimdhā Wa Hum Lā Yash`urūna 012-015 To, a lõkacin da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba."  ۚ 
Wa Jā'ū 'Abāhum `Ishā'an Yabkūna 012-016 Kuma suka je wa ubansu da dare sunã kũka.
Qālū Yā 'Abānā 'Innā Dhahabnā Nastabiqu Wa Taraknā Yūsufa `Inda Matā`inā Fa'akalahu Adh-Dhi'bu  ۖ  Wa Mā 'Anta Bimu'uminin Lanā Wa Law Kunnā Şādiqīna 012-017 Suka ce: "Yã bãbanmu! Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya!"_  ۖ 
Wa Jā'ū `Alá Qamīşihi Bidamin Kadhibin  ۚ  Qāla Bal Sawwalat Lakum 'Anfusukum 'Amrāan  ۖ  Faşabrun Jamīlun Wa  ۖ  Allāhu Al-Musta`ānu `Alá Mā Taşifūna 012-018 Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: "Ã'a, zukatanku suka ƙawãta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantãwa."  ۚ   ۖ   ۖ 
Wa Jā'at Sayyāratun Fa'arsalū Wa Aridahum Fa'adlá Dalwahu  ۖ  Qāla Yā Bushrá Hādhā Ghulāmun  ۚ  Wa 'Asarrūhu Biđā`atan Wa  ۚ  Allāhu `Alīmun Bimā Ya`malūna 012-019 Kuma wani ãyari ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Yã bushãrata! Wannan yãro ne." Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa Sharawhu Bithamanin Bakhsin Darāhima Ma`dūdatin Wa Kānū Fīhi Mina Az-Zāhidīna 012-020 Kuma suka sayar da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.
Wa Qāla Al-Ladhī Ashtarāhu Min Mişra Li'imra'atihi 'Akrimī Mathwāhu `Asá 'An Yanfa`anā 'Aw Nattakhidhahu Waladāan  ۚ  Wa Kadhalika Makkannā Liyūsufa Fī Al-'Arđi Wa Linu`allimahu Min Ta'wīli Al-'Aĥādīthi Wa  ۚ  Allāhu Ghālibun `Alá 'Amrihi Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna 012-021 Kuma wanda ya saye shi daga Masar ya ce wa mãtarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu,a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba." ~  ۚ   ۚ 
Wa Lammā Balagha 'Ashuddahu 'Ātaynāhu Ĥukmāan Wa `Ilmāan  ۚ  Wa Kadhalika Naj Al-Muĥsinīna 012-022 Kuma a lõkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.  ۚ 
Wa Rāwadat/hu Allatī Huwa Fī Baytihā `An Nafsihi Wa Ghallaqati Al-'Abwāba Wa Qālat Hayta Laka  ۚ  Qāla Ma`ādha Al-Lahi  ۖ  'Innahu Rabbī 'Aĥsana Mathwāya  ۖ  'Innahu Lā Yufliĥu Až-Žālimūna 012-023 Kuma wadda yake a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, "Yã rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!"  ۚ   ۖ   ۖ 
Wa Laqad Hammat Bihi  ۖ  Wa Hamma Bihā Lawlā 'An Ra'á Burhāna Rabbihi  ۚ  Kadhālika Linaşrifa `Anhu As-Sū'a Wa Al-Faĥshā'a  ۚ  'Innahu Min `Ibādinā Al-Mukhlaşīna 012-024 Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa Astabaqā Al-Bāba Wa Qaddat Qamīşahu Min Duburin Wa 'Alfayā Sayyidahā Ladá Al-Bābi  ۚ  Qālat Mā Jazā'u Man 'Arāda Bi'ahlika Sū'āan 'Illā 'An Yusjana 'Aw `Adhābun 'Alīmun 012-025 Kuma suka yi tsẽre zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi."  ۚ 
Qāla Hiya Rāwadatnī `An Nafsī  ۚ  Wa Shahida Shāhidun Min 'Ahlihā 'In Kāna Qamīşuhu Qudda Min Qubulin Faşadaqat Wa Huwa Mina Al-Kādhibīna 012-026 Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: "Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata."  ۚ 
Wa 'In Kāna Qamīşuhu Qudda Min Duburin Fakadhabat Wa Huwa Mina Aş-Şādiqīna 012-027 "Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya."
Falammā Ra'á Qamīşahu Qudda Min Duburin Qāla 'Innahu Min Kaydikunna  ۖ  'Inna Kaydakunna `Ažīmun 012-028 Sa'an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce: "Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!"  ۖ 
Yūsufu 'A`riđ `An Hādhā  ۚ  Wa Astaghfirī Lidhanbiki  ۖ  'Innaki Kunti Mina Al-Khāţi'īna 012-029 "Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure."  ۚ   ۖ 
Wa Qāla Niswatun Al-Madīnati Amra'atu Al-`Azīzi Turāwidu Fatāhā `An Nafsihi  ۖ  Qad Shaghafahā Ĥubbāan  ۖ  'Innā Lanarāhā Fī Đalālin Mubīnin 012-030 Kuma waɗansu mãtã a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna."  ۖ   ۖ 
Falammā Sami`at Bimakrihinna 'Arsalat 'Ilayhinna Wa 'A`tadat Lahunna Muttaka'an Wa 'Ātat Kulla Wāĥidatin Minhunna Sikkīnāan Wa Qālati Akhruj `Alayhinna  ۖ  Falammā Ra'aynahu 'Akbarnahu Wa Qaţţa`na 'Aydiyahunna Wa Qulna Ĥāsha Lillahi Mā Hādhā Basharāan 'In Hādhā 'Illā Malakun Karīmun 012-031 Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja!"  ۖ  ~
Qālat Fadhālikunna Al-Ladhī Lumtunnanī Fīhi  ۖ  Wa Laqad Rāwadttuhu `An Nafsihi Fāsta`şama  ۖ  Wa La'in Lam Yaf`al Mā 'Āmuruhu Layusjananna Wa Layakūnāan Mina Aş-Şāghirīna 012-032 Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu."  ۖ   ۖ 
Qāla Rabbi As-Sijnu 'Aĥabbu 'Ilayya Mimmā Yad`ūnanī 'Ilayhi  ۖ  Wa 'Illā Taşrif `Annī Kaydahunna 'Aşbu 'Ilayhinna Wa 'Akun Mina Al-Jāhilīna 012-033 Ya ce: "Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai."  ۖ 
Fāstajāba Lahu Rabbuhu Faşarafa `Anhu Kaydahunna  ۚ  'Innahu Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu 012-034 Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa sabõda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shĩ ne Mai jĩ, Masani.  ۚ 
Thumma Badā Lahum Min Ba`di Mā Ra'aw Al-'Āyāti Layasjununnahu Ĥattá Ĥīnin 012-035 Sa'an nan kuma ya bayyana a gare su a bãyan sun ga alãmõmin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lõkaci.
Wa Dakhala Ma`ahu As-Sijna Fatayāni  ۖ  Qāla 'Aĥaduhumā 'Innī 'Arānī 'A`şiru Khamrāan  ۖ  Wa Qāla Al-'Ākharu 'Innī 'Arānī 'Aĥmilu Fawqa Ra'sī Khubzāan Ta'kulu Aţ-Ţayru Minhu  ۖ  Nabbi'nā Bita'wīlihi  ۖ  'Innā Narāka Mina Al-Muĥsinīna 012-036 Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi. ayansu ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa."  ۖ   ۖ   ۖ  ~  ۖ 
Qāla Lā Ya'tīkumā Ţa`āmun Turzaqānihi 'Illā Nabba'tukumā Bita'wīlihi Qabla 'An Ya'tiyakumā  ۚ  Dhālikumā Mimmā `Allamanī Rabbī  ۚ  'Innī Taraktu Millata Qawmin Lā Yu'uminūna Bil-Lahi Wa Hum Bil-'Ākhirati Hum Kāfirūna 012-037 Ya ce: "Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa , kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne." ~  ۚ   ۚ 
Wa Attaba`tu Millata 'Ābā'ī 'Ibrāhīma Wa 'Isĥāqa Wa Ya`qūba  ۚ  Mā Kāna Lanā 'An Nushrika Bil-Lahi Min Shay'in  ۚ  Dhālika Min Fađli Al-Lahi `Alaynā Wa `Alá An-Nāsi Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Yashkurūna 012-038 "Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa."  ۚ   ۚ 
Yā Şāĥibayi As-Sijni 'A'arbābun Mutafarriqūna Khayrun 'Ami Al-Lahu Al-Wāĥidu Al-Qahhāru 012-039 "Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa?"
Mā Ta`budūna Min Dūnihi 'Illā 'Asmā'an Sammaytumūhā 'Antum Wa 'Ābā'uukum Mā 'Anzala Al-Lahu Bihā Min Sulţānin  ۚ  'Ini Al-Ĥukmu 'Illā Lillahi  ۚ  'Amara 'Allā Ta`budū 'Illā 'Īyāhu  ۚ  Dhālika Ad-Dīnu Al-Qayyimu Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna 012-040 "Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku.Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba." ~  ۚ   ۚ   ۚ 
Yā Şāĥibayi As-Sijni 'Ammā 'Aĥadukumā Fayasqī Rabbahu Khamrāan  ۖ  Wa 'Ammā Al-'Ākharu Fayuşlabu Fata'kulu Aţ-Ţayru Min Ra'sihi  ۚ  Quđiya Al-'Amru Al-Ladhī Fīhi Tastaftiyāni 012-041 "Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shãyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa."  ۖ   ۚ 
Wa Qāla Lilladhī Žanna 'Annahu Nājin Minhumā Adhkurnī `Inda Rabbika Fa'ansāhu Ash-Shayţānu Dhikra Rabbihi Falabitha Fī As-Sijni Biđ`a Sinīna 012-042 Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, "Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka." Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunãwar Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru.
Wa Qāla Al-Maliku 'Innī 'Ará Sab`a Baqarātin Simānin Ya'kuluhunna Sab`un `Ijāfun Wa Sab`a Sunbulātin Khrin Wa 'Ukhara Yā  ۖ  Bisātin Yā 'Ayyuhā Al-Mala'u 'Aftūnī Fī Ru'uyā Ya 'In Kuntum Lilrru'uyā Ta`burūna 012-043 Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, nã yi mafarki; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa."  ۖ 
Qālū 'Ađghāthu 'Aĥlāmin  ۖ  Wa Mā Naĥnu Bita'wīli Al-'Aĥlāmi Bi`ālimīna 012-044 Suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yãye-yãyen mafarki ba."  ۖ 
Wa Qāla Al-Ladhī Najā Minhumā Wa Aiddakara Ba`da 'Ummatin 'Anā 'Unabbi'ukum Bita'wīlihi Fa'arsilūni 012-045 Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce: a bãyan yã yi tunãni a lõkaci mai tsawo, "Nĩ, inã bã ku lãbãri game da fassararsa. Sai ku aike ni."
Yūsufu 'Ayyuhā Aş-Şiddīqu 'Aftinā Fī Sab`i Baqarātin Simānin Ya'kuluhunna Sab`un `Ijāfun Wa Sab`i Sunbulātin Khrin Wa 'Ukhara Yā Bisātin La`allī 'Arji`u 'Ilá An-Nāsi La`allahum Ya`lamūna 012-046 "Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani."
Qāla Tazra`ūna Sab`a Sinīna Da'abāan Famā Ĥaşadtum Fadharūhu Fī Sunbulihi 'Illā Qalīlāan Mimmā Ta'kulūna 012-047 Ya ce: "Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa, sai kaɗan daga abin da kuke ci." ~
Thumma Ya'tī Min Ba`di Dhālika Sab`un Shidādun Ya'kulna Mā Qaddamtum Lahunna 'Illā Qalīlāan Mimmā Tuĥşinūna 012-048 "Sa'an nan kuma waɗansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kaɗan daga abin da kuke ãdanãwa."
Thumma Ya'tī Min Ba`di Dhālika `Āmun Fīhi Yughāthu An-Nāsu Wa Fīhi Ya`şirūna 012-049 "Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha."
Wa Qāla Al-Maliku A'tūnī Bihi  ۖ  Falammā Jā'ahu Ar-Rasūlu Qāla Arji` 'Ilá Rabbika Fās'alhu Mā Bālu An-Niswati Al-Lātī Qaţţa`na 'Aydiyahunna  ۚ  'Inna Rabbī Bikaydihinna `Alīmun 012-050 Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lõkacin da manzo ya je masa (Yũsufu), ya ce: "Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidinsu."  ۖ   ۚ 
Qāla Mā Khaţbukunna 'Idh Rāwadttunna Yūsufa `An Nafsihi  ۚ  Qulna Ĥāsha Lillahi Mā `Alimnā `Alayhi Min Sū'in  ۚ  Qālati Amra'atu Al-`Azīzi Al-'Āna Ĥaşĥaşa Al-Ĥaqqu 'Anā Rāwadttuhu `An Nafsihi Wa 'Innahu Lamina Aş-Şādiqīna 012-051 Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mãtar Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya.  ۚ   ۚ 
Dhālika Liya`lama 'Annī Lam 'Akhunhu Bil-Ghaybi Wa 'Anna Al-Laha Lā Yahdī Kayda Al-Khā'inīna 012-052 "Wancan ne, dõmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a ɓõye, kuma lalle Allah bã Ya shiryar da kaidin mayaudara."
Wa Mā 'Ubarri'u Nafsī  ۚ  'Inna An-Nafsa La'ammāratun Bis-Sū'i 'Illā Mā Raĥima Rabbī  ۚ  'Inna Rabbī Ghafūrun Raĥīmun 012-053 "Kuma bã ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."  ۚ   ۚ 
Wa Qāla Al-Maliku A'tūnī Bihi 'Astakhlişhu Linafsī  ۖ  Falammā Kallamahu Qāla 'Innaka Al-Yawma Ladaynā Makīnun 'Amīnun 012-054 Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina." To, a lõkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce." ~  ۖ 
Qāla Aj`alnī `Alá Khazā'ini Al-'Arđi  ۖ  'Innī Ĥafīžun `Alīmun 012-055 Ya ce: "Ka sanya ni a kan taskõkin ƙasa. Lalle ne nĩ, mai tsarẽwa ne, kuma masani."  ۖ 
Wa Kadhalika Makkannā Liyūsufa Fī Al-'Arđi Yatabawwa'u Minhā Ĥaythu Yashā'u  ۚ  Nuşību Biraĥmatinā Man Nashā'u  ۖ  Wa Lā Nuđī`u 'Ajra Al-Muĥsinīna 012-056 Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa.  ۚ   ۖ 
Wa La'ajru Al-'Ākhirati Khayrun Lilladhīna 'Āmanū Wa Kānū Yattaqūna 012-057 Kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗandasuka yi ĩmãni, kuma suka kasance mãsu taƙawa.
Wa Jā'a 'Ikhwatu Yūsufa Fadakhalū `Alayhi Fa`arafahum Wa Hum Lahu Munkirūna 012-058 Kuma 'yan'uwan Yũsufu suka jẽ, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya gãne su, alhãli kuwa su, sunã mãsu musunsa.
Wa Lammā Jahhazahum Bijahāzihim Qāla A'tūnī Bi'akhin Lakum Min 'Abīkum  ۚ  'Alā Tarawna 'Annī 'Ū Al-Kayla Wa 'Anā Khayru Al-Munzilīna 012-059 Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani ɗan'uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma'auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?"  ۚ 
Fa'in Lam Ta'tūnī Bihi Falā Kayla Lakum `Indī Wa Lā Taqrabūni 012-060 "Sa'an nan idan ba ku zo mini da shĩ ba, to, bãbu awoa gare ku a wurĩna, kuma kada ku,kasance ni."
Qālū Sanurāwidu `Anhu 'Abāhu Wa 'Innā Lafā`ilūna 012-061 Suka ce: "Zã mu nẽme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu aikatãwa ne."
Wa Qāla Lifityānihi Aj`alū Biđā`atahumRiĥālihim La`allahum Ya`rifūnahā 'Idhā Anqalabū 'Ilá 'Ahlihim La`allahum Yarji`ūna 012-062 Kuma ya ce wa yaransa, "Ku sanya hajjarsu a cikin kãyansu, tsammãninsu sunã gãne ta idan sun jũya zuwa ga mutãnensu, tsammã ninsu, zã su kõmo."
Falammā Raja`ū 'Ilá 'Abīhim Qālū Yā 'Abānā Muni`a Minnā Al-Kaylu Fa'arsil Ma`anā 'Akhānā Naktal Wa 'Innā Lahu Laĥāfižūna 012-063 To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: "Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan'uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu lũra da Shi ne."
Qāla Hal 'Āmanukum `Alayhi 'Illā Kamā 'Amintukum `Alá 'Akhīhi Min Qablu  ۖ  Fa-Allāhu Khayrun Ĥāfižāan  ۖ  Wa Huwa 'Arĥamu Ar-Rāĥimīna 012-064 Ya ce: "Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama."  ۖ   ۖ 
Wa Lammā Fataĥū Matā`ahum Wa Jadū Biđā`atahum Ruddat 'Ilayhim  ۖ  Qālū Yā 'Abānā Mā Nabghī  ۖ  Hadhihi Biđā`atunā Ruddat 'Ilaynā  ۖ  Wa Namīru 'Ahlanā Wa Naĥfažu 'Akhānā Wa Nazdādu Kayla Ba`īrin  ۖ  Dhālika Kaylun Yasīrun 012-065 Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: "Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙãra awon kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki."  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ 
Qāla Lan 'Ursilahu Ma`akum Ĥattá Tu'utūni Mawthiqāan Mina Al-Lahi Lata'tunanī Bihi 'Illā 'An Yuĥāţa Bikum  ۖ  Falammā 'Ātawhu Mawthiqahum Qāla Al-Lahu `Alá Mā Naqūlu Wa Kīlun 012-066 Ya ce: "Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku." To, a, lõkacinda suka yi mãsa alkawari, ya ce: "Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa." ~  ۖ 
Wa Qāla Yā Banīya Lā Tadkhulū Min Bābin Wāĥidin Wa Adkhulū Min 'Abwābin Mutafarriqatin  ۖ  Wa Mā 'Ughnī `Ankum Mina Al-Lahi Min Shay'in  ۖ  'Ini Al-Ĥukmu 'Illā Lillahi  ۖ  `Alayhi Tawakkaltu  ۖ  Wa `Alayhi Falyatawakkali Al-Mutawakkilūna 012-067 Kuma ya ce: "Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara."  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ 
Wa Lammā Dakhalū Min Ĥaythu 'Amarahum 'Abūhum Mmā Kāna Yughnī `Anhum Mmina Al-Lahi Min Shay'in 'Illā Ĥājatan Fī Nafsi Ya`qūba Qađāhā  ۚ  Wa 'Innahu Ladhū `Ilmin Limā `Allamnāhu Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna 012-068 Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu,ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba.  ۚ 
Wa Lammā Dakhalū `Alá Yūsufa 'Āwá 'Ilayhi 'Akhāhu  ۖ  Qāla 'Innī 'Anā 'Akhūka Falā Tabta'is Bimā Kānū Ya`malūna 012-069 Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: "Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa."  ۖ 
Falammā Jahhazahum Bijahāzihim Ja`ala As-Siqāyata Fī Raĥli 'Akhīhi Thumma 'Adhdhana Mu'uadhdhinun 'Ayyatuhā Al-`Īru 'Innakum Lasāriqūna 012-070 Sa'an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kãyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa," Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne."
Qālū Wa 'Aqbalū `Alayhimdhā Tafqidūna 012-071 Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su: "Mẽne ne kuke nẽma?"
Qālū Nafqidu Şuwā`a Al-Maliki Wa Liman Jā'a Bihi Ĥimlu Ba`īrin Wa 'Anā Bihi Za`īmun 012-072 Suka ce: "Munã nẽman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi."
Qālū Ta-Allāhi Laqad `Alimtum Mā Ji'nā Linufsida Fī Al-'Arđi Wa Mā Kunnā Sāriqīna 012-073 Suka ce: "Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba."
Qālū Famā Jazā'uuhu 'In Kuntumdhibīna 012-074 Suka ce: "To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?" ~
Qālū Jazā'uuhu Man Wujida Fī Raĥlihi Fahuwa Jazā'uuhu  ۚ  Kadhālika Naj Až-Žālimīna 012-075 Suka ce: "Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa, kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai."  ۚ 
Fabada'a Bi'aw`iyatihim Qabla Wi`ā'i 'Akhīhi Thumma Astakhrajahā Min Wi`ā'i 'Akhīhi  ۚ  Kadhālika Kidnā Liyūsufa  ۖ  Mā Kāna Liya'khudha 'Akhāhu Fī Dīni Al-Maliki 'Illā 'An Yashā'a Al-Lahu  ۚ  Narfa`u Darajātin Man Nashā'u  ۗ  Wa Fawqa Kulli Dhī `Ilmin `Alīmun 012-076 To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani.  ۚ   ۖ   ۚ   ۗ 
Qālū 'In Yasriq Faqad Saraqa 'Akhun Lahu Min Qablu  ۚ  Fa'asarrahā Yūsufu Fī Nafsihi Wa Lam Yubdihā Lahum  ۚ  Qāla 'Antum Sharrun Makānāan Wa  ۖ  Allāhu 'A`lamu Bimā Taşifūna 012-077 Suka ce: "Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa."  ۚ   ۚ   ۖ 
Qālū Yā 'Ayyuhā Al-`Azīzu 'Inna Lahu 'Abāan Shaykhāan Kabīrāan Fakhudh 'Aĥadanā Makānahu  ۖ  'Innā Narāka Mina Al-Muĥsinīna 012-078 Suka ce: "Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa.Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa." ~ ~  ۖ 
Qāla Ma`ādha Al-Lahi 'An Na'khudha 'Illā Man Wajadnā Matā`anā `Indahu 'Innā 'Idhāan Lažālimūna 012-079 Ya ce: "Allah Ya tsare mu daga mu kãma wani fãce wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lõkacin nan,haƙĩƙa, azzãlumai ne." ~
Falammā Astay'asū Minhu Khalaşū Najīyāan  ۖ  Qāla Kabīruhum 'Alam Ta`lamū 'Anna 'Abākum Qad 'Akhadha `Alaykum Mawthiqāan Mina Al-Lahi Wa Min Qablu Mā Farraţtum Fī Yūsufa  ۖ  Falan 'Abraĥa Al-'Arđa Ĥattá Ya'dhana Lī 'Abī 'Aw Yaĥkuma Al-Lahu Lī  ۖ  Wa Huwa Khayru Al-Ĥākimīna 012-080 Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa. Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta."  ۖ   ۖ   ۖ 
Arji`ū 'Ilá 'Abīkum Faqūlū Yā 'Abānā 'Inna Abnaka Saraqa Wa Mā Shahidnā 'Illā Bimā `Alimnā Wa Mā Kunnā Lilghaybi Ĥāfižīna 012-081 "Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba."
Wa As'ali Al-Qaryata Allatī Kunnā Fīhā Wa Al-`Īra Allatī 'Aqbalnā Fīhā  ۖ  Wa 'Innā Laşādiqūna 012-082 "Kuma ka tambayi alƙarya wadda muka kasance a cikinta da ãyari wanda muka gabãto acikinsa, kuma lalle ne haƙĩƙa, mũ mãsu gaskiya ne."  ۖ 
Qāla Bal Sawwalat Lakum 'Anfusukum 'Amrāan  ۖ  Faşabrun Jamīlun  ۖ  `Asá Al-Lahu 'An Ya'tiyanī Bihim Jamī`āan  ۚ  'Innahu Huwa Al-`Alīmu Al-Ĥakīmu 012-083 Ya ce: "Ã'a, zukatanku sun ƙawãta wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyãwo, akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã ɗaya ( Yũsufu da 'yan'uwansa). Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima."  ۖ   ۖ   ۚ 
Wa Tawallá `Anhum Wa Qāla Yā 'Asafá `Alá Yūsufa Wa Abyađđat `Aynāhu Mina Al-Ĥuzni Fahuwa Kažīmun 012-084 Kuma ya jũya daga gare su, kuma ya ce: "Yã baƙin cikina a kan Yũsufu!" Kuma idãnunsa suka yi fari sabõda huznu sa'an nan yanã ta haɗẽwar haushi.
Qālū Ta-Allāhi Tafta'u Tadhkuru Yūsufa Ĥattá Takūna Ĥarađāan 'Aw Takūna Mina Al-Hālikīna 012-085 Suka ce: "Tallahi! Bã zã ka gushe ba, kanã ambaton Yũsufu, har ka kasance Mai rauni ƙwarai, kõ kuwa ka kasance daga mãsu halaka."
Qāla 'Innamā 'Ashkū Baththī Wa Ĥuznī 'Ilá Al-Lahi Wa 'A`lamu Mina Al-Lahi Mā Lā Ta`lamūna 012-086 Ya ce: "Abin sani kawai, inã kai ƙarar baƙin cikĩna da sunõna zuwa ga Allah, kuma na san abin da ba ku sani ba daga Allah."
Yā Banīya Adh/habū Fataĥassasū Min Yūsufa Wa 'Akhīhi Wa Lā Tay'asū Min Rawĥi Al-Lahi  ۖ  'Innahu Lā Yay'asu Min Rawĥi Al-Lahi 'Illā Al-Qawmu Al-Kāfirūna 012-087 "Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar Allah fãce mutãne kãfirai."  ۖ 
Falammā Dakhalū `Alayhi Qālū Yā 'Ayyuhā Al-`Azīzu Massanā Wa 'Ahlanā Ađ-Đurru Wa Ji'nā Bibiđā`atin Muzjāatin Fa'awfi Lanā Al-Kayla Wa Taşaddaq `Alaynā  ۖ  'Inna Al-Laha Yaj Al-Mutaşaddiqīna 012-088 Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: "Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. "  ۖ 
Qāla Hal `Alimtum Mā Fa`altum Biyūsufa Wa 'Akhīhi 'Idh 'Antum Jāhilūna 012-089 Ya ce: "Shin, kan san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan'uwansa a lõkacin da kuke jãhilai?" ~
Qālū 'A'innaka La'anta Yūsufu  ۖ  Qāla 'Anā Yūsufu Wa Hadhā 'Akhī  ۖ  Qad Manna Al-Lahu `Alaynā  ۖ  'Innahu Man Yattaqi Wa Yaşbir Fa'inna Al-Laha Lā Yuđī`u 'Ajra Al-Muĥsinīna 012-090 Saka ce: "Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa."  ۖ   ۖ   ۖ 
Qālū Ta-Allāhi Laqad 'Ātharaka Al-Lahu `Alaynā Wa 'In Kunnā Lakhāţi'īna 012-091 Suka ce: "Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yã zãɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, mãsu kuskure."
Qāla Lā Tathrība `Alaykumu Al-Yawma  ۖ  Yaghfiru Al-Lahu Lakum  ۖ  Wa Huwa 'Arĥamu Ar-Rāĥimīna 012-092 Ya ce: "Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama."  ۖ   ۖ 
Adh/habū Biqamīşī Hādhā Fa'alqūhu `Alá Wajhi 'Abī Ya'ti Başīrāan Wa 'Tūnī Bi'ahlikum 'Ajma`īna 012-093 "Ku tafi da rĩgãta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki ɗaya."
Wa Lammā Faşalati Al-`Īru Qāla 'Abūhum 'Innī La'ajidu Rīĥa Yūsufa  ۖ  Lawlā 'An Tufannidūni 012-094 Kuma, a lõkacin da ãyari ya bar (Masar) ubansa ya ce: "Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba."  ۖ 
Qālū Ta-Allāhi 'Innaka Lafī Đalālika Al-Qadīmi 012-095 Suka ce: "Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kanã a cikin ɓatarka daɗaɗɗa."
Falammā 'An Jā'a Al-Bashīru 'Alqāhu `Alá Wajhihi Fārtadda Başīrāan Qāla  ۖ  'Alam 'Aqul Lakum 'Innī 'A`lamu Mina Al-Lahi Mā Lā Ta`lamūna 012-096 Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?"  ۖ 
Qālū Yā 'Abānā Astaghfir Lanā Dhunūbanā 'Innā Kunnā Khāţi'īna 012-097 Suka ce: "Yã ubanmu! ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure."
Qāla Sawfa 'Astaghfiru Lakum Rabbī  ۖ  'Innahu Huwa Al-Ghafūru Ar-Raĥīmu 012-098 Ya ce: "Da sannu zã ni nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."  ۖ 
Falammā Dakhalū `Alá Yūsufa 'Āwá 'Ilayhi 'Abawayhi Wa Qāla Adkhulū Mişra 'In Shā'a Al-Lahu 'Āminīna 012-099 Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: "Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu."
Wa Rafa`a 'Abawayhi `Alá Al-`Arshi Wa Kharrū Lahu Sujjadāan  ۖ  Wa Qāla Yā 'Abati Hādhā Ta'wīlu Ru'uyā Y Min Qablu Qad Ja`alahā Rabbī  ۖ  Ĥaqqāan Wa Qad 'Aĥsana Bī 'Idh 'Akhrajanī Mina As-Sijni Wa Jā'a Bikum Mina Al-Badwi Min Ba`di 'An Nazagha Ash-Shayţānu Baynī Wa Bayna  ۚ  'Ikhwatī 'Inna Rabbī Laţīfun Limā  ۚ  Yashā'u 'Innahu Huwa Al-`Alīmu Al-Ĥakīmu 012-100 Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada. Kuma ya ce: "Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ,Shĩ ne Masani, Mai hikima."  ۖ   ۖ   ۚ   ۚ 
Rabbi Qad 'Ātaytanī Mina Al-Mulki Wa `Allamtanī Min Ta'wīli Al-'Aĥādīthi  ۚ  Fāţira As-Samāwāti Wa Al-'Arđi 'Anta Wa Līyi Fī Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati  ۖ  Tawaffanī Muslimāan Wa 'Alĥiqnī Biş-Şāliĥīna 012-101 "Yã Ubangijina lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."  ۚ   ۖ 
Dhālika Min 'Anbā'i Al-Ghaybi Nūĥīhi 'Ilayka  ۖ  Wa Mā Kunta Ladayhim 'Idh 'Ajma`ū 'Amrahum Wa Hum Yamkurūna 012-102 Wannan daga lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci. ~  ۖ 
Wa Mā 'Aktharu An-Nāsi Wa Law Ĥaraşta Bimu'uminīna 012-103 Kuma mafi yawan mutãne ba su zama mãsu ĩmãni ba,kõ da kã yi kwaɗayin haka.
Wa Mā Tas'aluhum `Alayhi Min 'Ajrin  ۚ  'In Huwa 'Illā Dhikrun Lil`ālamīna 012-104 Kuma bã ka tambayar su wata lãdã a kansa. Shĩ bai zama ba fãce ambato dõmin halittu.  ۚ 
Wa Ka'ayyin Min 'Āyatin As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Yamurrūna `Alayhā Wa Hum `Anhā Mu`rūna 012-105 Kuma da yawa, wata ãyã a cikin sammai da ƙasa sunã shũɗẽwa a kanta kuma sũ, sunã bijirẽwa daga gare ta.
Wa Mā Yu'uminu 'Aktharuhum Bil-Lahi 'Illā Wa Hum Mushrikūna 012-106 Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmãni da Allah fãce kuma sunã mãsu shirki.
'Afa'aminū 'An Ta'tiyahum Ghāshiyatun Min `Adhābi Al-Lahi 'Aw Ta'tiyahumu As-Sā`atu Baghtatan Wa Hum Lā Yash`urūna 012-107 Shin fa, sun amince cẽwa wata masĩfa daga azãbar Allah ta zo musu ko kuwa Tãshin ¡iyãma ta zo musu kwatsam, alhãli sũ ba su sani ba?
Qul Hadhihi Sabīlī 'Ad`ū 'Ilá Al-Lahi  ۚ  `Alá Başīratin 'Anā Wa Mani Attaba`anī  ۖ  Wa Subĥāna Al-Lahi Wa Mā 'Anā Mina Al-Mushrikīna 012-108 Ka ce: "Wannan ce hanyãta ; inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."  ۚ   ۖ 
Wa Mā 'Arsalnā Min Qablika 'Illā Rijālāan Nūĥī 'Ilayhim Min 'Ahli Al-Qurá  ۗ  'Afalam Yasīrū Fī Al-'Arđi Fayanžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Ladhīna Min Qablihim  ۗ  Wa Ladāru Al-'Ākhirati Khayrun Lilladhīna Attaqaw  ۗ  'Afalā Ta`qilūna 012-109 Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta?  ۗ   ۗ   ۗ 
Ĥattá 'Idhā Astay'asa Ar-Rusulu Wa Žannū 'Annahum Qad Kudhibū Jā'ahum Naşrunā Fanujjiya Man Nashā'u  ۖ  Wa Lā Yuraddu Ba'sunā `Ani Al-Qawmi Al-Mujrimīna 012-110 Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke so, kuma bã a mayar da azãbarMu daga mutãne mãsu laifi.  ۖ 
Laqad Kāna Fī Qaşaşihim `Ibratun Li'wlī Al-'Albābi  ۗ  Mā Kāna Ĥadīthāan Yuftará Wa Lakin Taşdīqa Al-Ladhī Bayna Yadayhi Wa Tafşīla Kulli Shay'in Wa Hudáan Wa Raĥmatan Liqawmin Yu'uminūna 012-111 Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.  ۗ 
Next Sūrah