10) Sūrat Yūnis

Printed format

10)

'Alif-Lām-Rā Tilka 'Āyātu Al-Kitābi Al-Ĥakīmi 010-001 A. L̃. R. Waɗancan ãyõyin littãfi ne kyautatacce. --
'Akāna Lilnnāsi `Ajabāan 'An 'Awĥaynā 'Ilá Rajulin Minhum 'An 'Andhiri An-Nāsa Wa Bashshiri Al-Ladhīna 'Āmanū 'Anna Lahum Qadama Şidqin `Inda Rabbihim  ۗ  Qāla Al-Kāfirūna 'Inna Hādhā Lasāĥirun Mubīnun 010-002 Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, "Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu."Kãfirai suka ce: "Lalle ne wannan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne."  ۗ 
'Inna Rabbakumu Al-Lahu Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Fī Sittati 'Ayyāmin Thumma Astawá `Alá Al-`Arshi  ۖ  Yudabbiru Al-'Amra  ۖ  Mā Min Shafī`in 'Illā Min Ba`di 'Idhnihi  ۚ  Dhalikumu Al-Lahu Rabbukum Fā`budūhu  ۚ  'Afalā Tadhakkarūna 010-003 Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yanã gudãnar da al'amari. Bãbu wani macẽci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunãni?  ۖ   ۖ   ۚ  ~  ۚ 
'Ilayhi Marji`ukum Jamī`āan  ۖ  Wa`da Al-Lahi Ĥaqqāan  ۚ  'Innahu Yabda'u Al-Khalqa Thumma Yu`īduhu Liyajziya Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Bil-Qisţi Wa  ۚ  Al-Ladhīna Kafarū Lahum Sharābun Min Ĥamīmin Wa `Adhābun 'Alīmun Bimā Kānū Yakfurūna 010-004 zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.  ۖ   ۚ   ۚ 
Huwa Al-Ladhī Ja`ala Ash-Shamsa Điyā'an Wa Al-Qamara Nūrāan Wa Qaddarahu Manāzila Lita`lamū `Adada As-Sinīna Wa Al-Ĥisāba  ۚ  Mā Khalaqa Al-Lahu Dhālika 'Illā Bil-Ĥaqqi  ۚ  Yufaşşilu Al-'Āyāti Liqawmin Ya`lamūna 010-005 Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai halitta wannan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne waɗanda suke sani.  ۚ   ۚ 
'Inna Fī Akhtilāfi Al-Layli Wa An-Nahāri Wa Mā Khalaqa Al-Lahu Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi La'āyātin Liqawmin Yattaqūna 010-006 Lalle ne a cikin sãɓãwar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙaakwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin taƙawa.
'Inna Al-Ladhīna Lā Yarjūna Liqā'anā Wa Rađū Bil-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Aţma'annū Bihā Wa Al-Ladhīna Hum `An 'Āyātinā Ghāfilūna 010-007 Lalle ne waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mũ, kuma suka yarda da rãyuwar dũniya kuma suka natsu da ita, da waɗanda suke gafalallu ne daga ãyõyinMu,
'Ūlā'ika Ma'wāhumu An-Nāru Bimā Kānū Yaksibūna 010-008 Waɗannan matattãrarsu Jahannama ce sabõda abin da suka kasance sunã tsirfãtawa.
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Yahdīhim Rabbuhum Bi'īmānihim  ۖ  Tajrī Min Taĥtihimu Al-'Anhāru Fī Jannāti An-Na`īmi 010-009 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yanã shiryar da su sabõda ĩmãninsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, a cikin gidãjen Aljannar ni'ima.  ۖ 
Da`wāhum Fīhā Subĥānaka Al-Lahumma Wa Taĥīyatuhum Fīhā Salāmun  ۚ  Wa 'Ākhiru Da`wāhum 'Ani Al-Ĥamdu Lillahi Rabbi Al-`Ālamīna 010-010 Kiransu a cikinta, "TsarkinKa yã Allah!" Kuma gaisuwarsu a cikinta,"Salãmun", kuma ƙarshen kiransu, cẽwa, "Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu."  ۚ 
Wa Law Yu`ajjilu Al-Lahu Lilnnāsi Ash-Sharra Asti`jālahum Bil-Khayri Laquđiya 'Ilayhim 'Ajaluhum  ۖ  Fanadharu Al-Ladhīna Lā Yarjūna Liqā'anā Fī Ţughyānihim Ya`mahūna 010-011 Kuma dã Allah Yana gaggãwa ga mutãne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alhẽri, haƙĩƙa dã an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabõda haka Munã barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sunã ta ɗimuwa.  ۖ 
Wa 'Idhā Massa Al-'Insāna Ađ-Đurru Da`ānā Lijanbihi 'Aw Qā`idāan 'Aw Qā'imāan Falammā Kashafnā `Anhu Đurrahu Marra Ka'an Lam Yad`unā 'Ilá Đurrin Massahu  ۚ  Kadhālika Zuyyina Lilmusrifīna Mā Kānū Ya`malūna 010-012 Kuma idan cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, yanã (kwance) ga sãshensa kõ kuwa zaune, kõ kuwa a tsaye. To, a lõkacin, da Muka kuranye cũtar daga gare shi, sai ya shũɗe kamar ɗai bai kirãye Mu ba zuwa ga wata cũta wadda ta shãfe shi. Kamar wannan ne aka ƙawãta ga maɓannata, abin da suka kasance sunã aikatãwa. ~  ۚ 
Wa Laqad 'Ahlaknā Al-Qurūna Min Qablikum Lammā Žalamū  ۙ  Wa Jā'at/hum Rusuluhum Bil-Bayyināti Wa Mā Kānū Liyu'uminū  ۚ  Kadhālika Naj Al-Qawma Al-Mujrimīna 010-013 Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabãninku, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, amma ba su kasance sunã ĩmãni ba. Kamar wannan ne, Muke sãkãwa ga mutãne mãsu laifi.  ۙ   ۚ 
Thumma Ja`alnākum Khalā'ifa Fī Al-'Arđi Min Ba`dihim Linanžura Kayfa Ta`malūna 010-014 Sa'an nan kuma Muka sanya ku mãsu mayẽwa a cikin ƙasa daga bãyansu, dõmin Mu ga yãya kuke aikatãwa.
Wa 'Idhā Tutlá `Alayhim 'Āyātunā Bayyinātin  ۙ  Qāla Al-Ladhīna Lā Yarjūna Liqā'anā A'ti Biqur'ānin Ghayri Hādhā 'Aw Baddilhu  ۚ  Qul Mā Yakūnu Lī 'An 'Ubaddilahu Min Tilqā'i Nafsī  ۖ  'In 'Attabi`u 'Illā Mā Yūĥá 'Ilayya  ۖ  'Innī 'Akhāfu 'In `Aşaytu Rabbī `Adhāba Yawmin `Ažīmin 010-015 Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi." Ka ce: "Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma."  ۙ   ۚ   ۖ   ۖ 
Qul Law Shā'a Al-Lahu Mā Talawtuhu `Alaykum Wa Lā 'Adrākum Bihi  ۖ  Faqad Labithtu Fīkum `Umurāan Min Qablihi  ۚ  'Afalā Ta`qilūna 010-016 Ka ce: "Dã Allah Ya so dã ban karanta shi ba a kanku, kuma dã ban sanar da kũ ba gameda shi, dõmin lalle ne nã zauna a cikinku a zãmani mai tsawo daga gabãnin (fãra saukar) sa. Shin fa, bã ku hankalta?"  ۖ  ~  ۚ 
Faman 'Ažlamu Mimmani Aftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan 'Aw Kadhdhaba Bi'āyātihi  ۚ  'Innahu Lā Yufliĥu Al-Mujrimūna 010-017 "Sabõda haka wãne ne mafi Zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata ãyõyinSa? Haƙĩƙa, mãsu laifibã su cin nasara!" ~  ۚ 
Wa Ya`budūna Min Dūni Al-Lahi Mā Lā Yađurruhum Wa Lā Yanfa`uhum Wa Yaqūlūna Hā'uulā' Shufa`ā'uunā `Inda Al-Lahi  ۚ  Qul 'Atunabbi'ūna Al-Laha Bimā Lā Ya`lamu Fī As-Samāwāti Wa Lā Fī Al-'Arđi  ۚ  Subĥānahu Wa Ta`ālá `Ammā Yushrikūna 010-018 Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah."Ka ce: "Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi."  ۚ   ۚ 
Wa Mā Kāna An-Nāsu 'Illā 'Ummatan Wāĥidatankhtalafū  ۚ  Wa Lawlā Kalimatun Sabaqat Min Rabbika Laquđiya Baynahum Fīmā Fīhi Yakhtalifūna 010-019 Kuma mutãne ba su kasance ba fãce al'umma guda, sa'an nan kuma suka sãɓã wa jũna, kuma ba dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, dã an yi hukunci a tsakãninsu a kan abin da yake a cikinsa suke sãɓã wa jũna.  ۚ 
Wa Yaqūlūna Lawlā 'Unzila `Alayhi 'Āyatun Min Rabbihi  ۖ  Faqul 'Innamā Al-Ghaybu Lillahi Fāntažirū 'Innī Ma`akum Mina Al-Muntažirīna 010-020 Kuma sunã cẽwa: "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a gare shi, daga Ubangijinsa?" To, ka ce: "Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira. Lalle ne nĩ, tãre da ku, inã daga mãsu jira."  ۖ 
Wa 'Idhā 'Adhaq An-Nāsa Raĥmatan Min Ba`di Đarrā'a Massat/hum 'Idhā Lahum Makrun Fī 'Āyātinā  ۚ  Quli Al-Lahu 'Asra`u Makrāan  ۚ  'Inna Rusulanā Yaktubūna Mā Tamkurūn 010-021 Kuma idan Muka ɗanɗanã wa mutãne wata rahama, a bãyan wata cũta tã shãfe su, sai gã su da mãkirci a cikin ãyõyinMu. Ka ce: "Allah ne mafi gaggãwar (sakamakon) mãkirci." Lalle ne ManzanninMu sunã rubũta abin da kuke yi na mãkirci.  ۚ   ۚ 
Huwa Al-Ladhī Yusayyirukum Al-Barri Wa Al-Baĥri  ۖ  Ĥattá 'Idhā Kuntum Al-Fulki Wa Jarayna Bihim Birīĥin Ţayyibatin Wa Fariĥū Bihā Jā'at/hā Rīĥun `Āşifun Wa Jā'ahumu Al-Mawju Min Kulli Makānin Wa Žannū 'Annahum 'Uĥīţa Bihim  ۙ  Da`aw Al-Laha Mukhlişīna Lahu Ad-Dīna La'in 'Anjaytanā Min Hadhihi Lanakūnanna Mina Ash-Shākirīna 010-022 Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya.  ۖ   ۙ 
Falammā 'Anjāhum 'Idhā Hum Yabghūna Fī Al-'Arđi Bighayri Al-Ĥaqqi  ۗ  Yā 'Ayyuhā An-Nāsu 'Innamā Baghyukum `Alá 'Anfusikum  ۖ  Matā`a Al-Ĥayāati Ad-Dunyā  ۖ  Thumma 'Ilaynā Marji`ukum Fanunabbi'ukum Bimā Kuntum Ta`malūna 010-023 To, a lõkacin da Ya kuɓutar da su, sai, gã su sunã zãlunci a cikin ƙasa, bã da wanĩ hakki ba. Yã ku mutãne! Abin sani kawai, zãluncinku a kanku yake, a bisa rãyuwar dũniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makõmarku take, sa'an nan Mu bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa,  ۗ   ۖ   ۖ 
'Innamā Mathalu Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Kamā'in 'Anzalnāhu Mina As-Samā'i Fākhtalaţa Bihi Nabātu Al-'Arđi Mimmā Ya'kulu An-Nāsu Wa Al-'An`ām Ĥattá 'Idhā 'Akhadhati Al-'Arđu Zukhrufahā Wa Azzayyanat Wa Žanna 'Ahluhā 'Annahum Qādirūna `Alayhā 'Atāhā 'Amrunā Laylāan 'Aw Nahārāan Faja`alnāhā Ĥaşīdāan Ka'an Lam Taghna Bil-'Amsi  ۚ  Kadhālika Nufaşşilu Al-'Āyāti Liqawmin Yatafakkarūna 010-024 Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare kõ kuma da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗanda suke tunãni.  ۚ 
Wa Allāhu Yad`ū 'Ilá Dāri As-Salāmi Wa Yahdī Man Yashā'u 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin 010-025 Kuma Allah Yanã kira zuwa ga gidan aminci, kuma, Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga tafarki madaidaici.
Lilladhīna 'Aĥsanū Al-Ĥusná Wa Ziyādatun  ۖ  Wa Lā Yarhaqu Wujūhahum Qatarun Wa Lā Dhillatun  ۚ  'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Jannati  ۖ  Hum Fīhā Khālidūna 010-026 Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari, wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.  ۖ   ۚ   ۖ 
Wa Al-Ladhīna Kasabū As-Sayyi'āti Jazā'u Sayyi'atin Bimithlihā Wa Tarhaquhum  ۖ  Dhillatun Mā Lahum Mina Al-Lahi Min  ۖ  `Āşimin Ka'annamā 'Ughshiyat Wujūhuhum Qiţa`āan Mina Al-Layli  ۚ  Mužlimāan 'Ūlā'ika 'Aşĥābu  ۖ  An-Nāri Hum Fīhā Khālidūna 010-027 Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yanã rufe su. Bã su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntãyen ƙirãruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abõkan wuta, sunã madawwama a cikinta.  ۖ   ۖ   ۚ   ۖ 
Wa Yawma Naĥshuruhum Jamī`āan Thumma Naqūlu Lilladhīna 'Ashrakū Makānakum 'Antum Wa Shurakā'uukum  ۚ  Fazayyalnā Baynahum  ۖ  Wa Qāla Shurakā'uuhum Mā Kuntum 'Īyānā Ta`budūna 010-028 Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, "Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku." Sa'an nan Mu rarrabe a tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: "Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa ba."  ۚ   ۖ 
Fakafá Bil-Lahi Shahīdāan Baynanā Wa Baynakum 'In Kunnā `An `Ibādatikum Laghāfilīna 010-029 "To, kuma Allah Yã isa zama shaida a tsakãninmu da tsakãninku. Haƙĩƙa mun kasance ba mu san kõme ba na bautãwarku a gare mu!"
Hunālika Tablū Kullu Nafsin Mā 'Aslafat  ۚ  Wa Ruddū 'Ilá Al-Lahi Mawlāhumu Al-Ĥaqqi  ۖ  Wa Đalla `Anhum Mā Kānū Yaftarūna 010-030 A can ne kõwane rai yake jarraba abin da ya bãyar bãshi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace musu.  ۚ   ۖ 
Qul Man Yarzuqukum Mina As-Samā'i Wa Al-'Arđi 'Amman Yamliku As-Sam`a Wa Al-'Abşāra Wa Man Yukhriju Al-Ĥayya Mina Al-Mayyiti Wa Yukhriju Al-Mayyita Mina Al-Ĥayyi Wa Man Yudabbiru Al-'Amra  ۚ  Fasayaqūlūna Al-Lahu  ۚ  Faqul 'Afalā Tattaqūna 010-031 Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?"  ۚ   ۚ 
Fadhalikumu Al-Lahu Rabbukumu Al-Ĥaqqu  ۖ  Famādhā Ba`da Al-Ĥaqqi 'Illā Ađ-Đalālu  ۖ  Fa'annā Tuşrafūna 010-032 To, Wancan ne Allah, Ubangijinku Tobbatacce. To, mẽne ne a bãyan gaskiya fãce ɓãta? To, yãya ake karkatar da ku?  ۖ   ۖ 
Kadhālika Ĥaqqat Kalimatu Rabbika `Alá Al-Ladhīna Fasaqū 'Annahum Lā Yu'uminūna 010-033 Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi fãsiƙanci, cẽwa haƙĩƙa sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.
Qul Hal Min Shurakā'ikum Man Yabda'u Al-Khalqa Thumma Yu`īduhu  ۚ  Quli Al-Lahu Yabda'u Al-Khalqa Thumma Yu`īduhu  ۖ  Fa'anná Tu'ufakūna 010-034 Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake fãra halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita?" Ka ce: "Allah ne Yake fãra halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yãyã akejũyar da ku?"  ۚ   ۖ 
Qul Hal Min Shurakā'ikum Man Yahdī 'Ilá Al-Ĥaqqi  ۚ  Quli Al-Lahu Yahdī Lilĥaqqi  ۗ  'Afaman Yahdī 'Ilá Al-Ĥaqqi 'Aĥaqqu 'An Yuttaba`a 'Amman Lā Yahiddī 'Illā 'An Yuhdá  ۖ  Famā Lakum Kayfa Taĥkumūna 010-035 Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?" Ka ce: "Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bã ya shiryarwa fãce dai a shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yãya kuke yin hukunci?"  ۚ   ۗ   ۖ 
Wa Mā Yattabi`u 'Aktharuhum 'Illā Žannāan  ۚ  'Inna Až-Žanna Lā Yughnī Mina Al-Ĥaqqi Shay'āan  ۚ  'Inna Al-Laha `Alīmun Bimā Yaf`alūna 010-036 Kuma mafi yawansu bã su biyar kõme fãce zato. Lalle ne zato bã ya wadãtar da kõme daga gaskiya. Lalle Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.  ۚ   ۚ 
Wa Mā Kāna Hādhā Al-Qur'ānu 'An Yuftará Min Dūni Al-Lahi Wa Lakin Taşdīqa Al-Ladhī Bayna Yadayhi Wa Tafşīla Al-Kitābi Lā Rayba Fīhi Min Rabbi Al-`Ālamīna 010-037 Kuma wannan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãninsa da bayãnin hukuncin littãffan Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake.
'Am Yaqūlūna Aftarāhu  ۖ  Qul Fa'tū Bisūratin Mithlihi Wa Ad`ū Mani Astaţa`tum Min Dūni Al-Lahi 'In Kuntum Şādiqīna 010-038 Kõ sunã cẽwa, "Yã ƙirƙira shi?" Ka ce: "Ku zo da sũra guda misãlinsa, kuma ku kirãyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya."  ۖ 
Bal Kadhdhabū Bimā Lam Yuĥīţū Bi`ilmihi Wa Lammā Ya'tihim Ta'wīluhu  ۚ  Kadhālika Kadhdhaba Al-Ladhīna Min Qablihim  ۖ  Fānžur Kayfa Kāna `Āqibatu Až-Žālimīna 010-039 Ã'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassararsa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba, yãya ãƙibar azzãlumai ta kasance?  ۚ   ۖ 
Wa Minhum Man Yu'uminu Bihi Wa Minhum Man Lā Yu'uminu Bihi  ۚ  Wa Rabbuka 'A`lamu Bil-Mufsidīna 010-040 Kuma daga cikinsu akwai wanda yake yin ĩmãni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bã ya yin ĩmãni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata.  ۚ 
Wa 'In Kadhdhabūka Faqul Lī `Amalī Wa Lakum `Amalukum  ۖ  'Antum Barī'ūna Mimmā 'A`malu Wa 'Anā Barī'un Mimmā Ta`malūna 010-041 Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: "Inã da aikĩna kuma kunã da aikinku, kũ kuɓutattu ne daga abin da nake aikatãwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatãwa."  ۖ 
Wa Minhum Man Yastami`ūna 'Ilayka  ۚ  'Afa'anta Tusmi`u Aş-Şumma Wa Law Kānū Lā Ya`qilūna 010-042 Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke saurare zuwa gare ka. Shin fa, kai kana jiyar da kurma, kuma kõ dã sun kasance bã su hankalta?  ۚ 
Wa Minhum Man Yanžuru 'Ilayka  ۚ  'Afa'anta Tahdī Al-`Umya Wa Law Kānū Lā Yubşirūna 010-043 Kuma daga cikinsu akwai wanda yake tsõkaci zuwa gare ka. Shin fa, kai kana shiryar da makãfi, kuma kõ dã sun kasance bã su gani?  ۚ 
'Inna Al-Laha Lā Yažlimu An-Nāsa Shay'āan Wa Lakinna An-Nāsa 'Anfusahum Yažlimūna 010-044 Lalle ne Allah ba Ya zãluntar mutãne da kõme, amma mutãnen ne ke zãluntar kansu.
Wa Yawma Yaĥshuruhum Ka'an Lam Yalbathū 'Illā Sā`atan Mina An-Nahāri Yata`ārafūna Baynahum  ۚ  Qad Khasira Al-Ladhīna Kadhdhabū Biliqā'i Al-Lahi Wa Mā Kānū Muhtadīna 010-045 Kuma rãnar da Yake tãra su, kamar ba su zauna ba fãce sa'a guda daga yini. Sunã gãne jũna a tsakãninsu. Haƙĩƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasãra. Kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.  ۚ 
Wa 'Immā Nuriyannaka Ba`đa Al-Ladhī Na`iduhum 'Aw Natawaffayannaka Fa'ilaynā Marji`uhum Thumma Al-Lahu Shahīdun `Alá Mā Yaf`alūna 010-046 Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu alkawari, kõ kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makõmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatãwa.
Wa Likulli 'Ummatin Rasūlun  ۖ  Fa'idhā Jā'a Rasūluhum Quđiya Baynahum Bil-Qisţi Wa Hum Lā Yužlamūna 010-047 Kuma ga kõwace al'umma akwai Manzo. Sa'an nan idan Manzonsu ya je, sai a yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma sũ, bã a zãluntar su.  ۖ 
Wa Yaqūlūna Matá Hādhā Al-Wa`du 'In Kuntum Şādiqīna 010-048 Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai auku, idan kun kasance mãsu gaskiya?"
Qul Lā 'Amliku Linafsī Đarrāan Wa Lā Naf`āan 'Illā Mā Shā'a Al-Lahu  ۗ  Likulli 'Ummatin 'Ajalun  ۚ  'Idhā Jā'a 'Ajaluhum Falā Yasta'khirūna Sā`atan  ۖ  Wa Lā Yastaqdimūna 010-049 Ka ce: "Ba na mallaka wa kaina wata cũta, haka kuma wani amfãni, sai abin da Allah Ya so. Ga kõwace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, bã zã su yi jinkiri daga gare shi ba, kõ dã sã'ã guda, kuma bã zã su gabãta ba."  ۗ   ۚ   ۖ 
Qul 'Ara'aytum 'In 'Atākum `Adhābuhu Bayātāan 'Aw Nahārāandhā Yasta`jilu Minhu Al-Mujrimūna 010-050 Ka ce: "Shin, kun gani, idan azãbarSa ta zo muku da dare ko da rãna? Mẽne ne daga gare shimãsu laifi suke nẽman gaggãwarsa?"
'Athumma 'Idhā Mā Waqa`a 'Āmantum Bihi  ۚ  'Āl'āna Wa Qad Kuntum Bihi Tasta`jilūna 010-051 Shin sa'an nan kuma idan har ya auku, kun yi ĩmãni da shi? Ashe? Yanzu kuwa, alhãli kun kasance game da shi kunã nẽman gaggãwar aukuwarsa? ~  ۚ 
Thumma Qīla Lilladhīna Žalamū Dhūqū `Adhāba Al-Khuldi Hal Tujzawna 'Illā Bimā Kuntum Taksibūna 010-052 Sa'an nan kuma aka ce ga waɗanda suka yi zãlunci, "Ku ɗanɗani azãbar dawwama! Shin, anã sãka muku fãce da abin da kuka kasance kuna aikatãwa?"
Wa Yastanbi'ūnaka 'Aĥaqqun Huwa  ۖ  Qul 'Ī Wa Rabbī 'Innahu Laĥaqqun  ۖ  Wa Mā 'Antum Bimu`jizīna 010-053 Kuma sunã tambayar ka: Shin gaskiya ne? Ka ce: "Ĩ, ina rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle gaskiya ne, kuma ba ku zama mãsu buwãya ba."  ۖ   ۖ 
Wa Law 'Anna Likulli Nafsin Žalamat Mā Fī Al-'Arđi Lāftadat Bihi  ۗ  Wa 'Asarrū An-Nadāmata Lammā Ra'aw Al-`Adhāba  ۖ  Wa Quđiya Baynahum Bil-Qisţi  ۚ  Wa Hum Lā Yužlamūna 010-054 Kuma dã kõwane rai wanda ya yi zãlunci yã mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, dã yã yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma bã zã a zãlunce su ba.  ۗ   ۖ   ۚ 
'Alā 'Inna Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۗ  'Alā 'Inna Wa`da Al-Lahi Ĥaqqun Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna 010-055 To! Haƙĩƙa Allah Ya mallaki abin da yake a cikin sammai da ƙasa. To! Haƙĩƙa wa'adin Allah gaskiya ne. Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.  ۗ 
Huwa Yuĥyī Wa Yumītu Wa 'Ilayhi Turja`ūna 010-056 Shi ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku.
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Qad Jā'atkum Maw`ižatun Min Rabbikum Wa Shifā'un Limā Fī Aş-Şudūri Wa Hudáan Wa Raĥmatun Lilmu'uminīna 010-057 Ya ku mutãne! Lalle wa'azi yã jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirãza, da shiriya da rahama ga muminai.
Qul Bifađli Al-Lahi Wa Biraĥmatihi Fabidhālika Falyafraĥū Huwa Khayrun Mimmā Yajma`ūna 010-058 Ka ce: "Da falalar Allah da rahamarSa. Sai su yi farin ciki da wannan." Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.
Qul 'Ara'aytum Mā 'Anzala Al-Lahu Lakum Min Rizqin Faja`altum Minhu Ĥarāmāan Wa Ĥalālāan Qul 'Ālllahu 'Adhina Lakum  ۖ  'Am `Alá Al-Lahi Taftarūna 010-059 Ka ce: "Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabõda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?" Ka ce: "Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirãwar ƙarya?"  ۖ 
Wa Mā Žannu Al-Ladhīna Yaftarūna `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba Yawma Al-Qiyāmati  ۗ  'Inna Al-Laha Ladhū Fađlin `Alá An-Nāsi Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Yashkurūna 010-060 Kuma mẽne ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Rãnar ¡iyãma? Lalle haƙĩƙa,Allah Ma, abũcin falala ne a kan mutãne, amma kuma mafi yawansu bã su gõdẽwa.  ۗ 
Wa Mā Takūnu Fī Sha'nin Wa Mā Tatlū Minhu Min Qur'ānin Wa Lā Ta`malūna Min `Amalin 'Illā Kunnā `Alaykum Shuhūdāan 'Idh Tufīđūna Fīhi  ۚ  Wa Mā Ya`zubu `An Rabbika Min Mithqāli Dharratin Al-'Arđi Wa Lā Fī As-Samā'i Wa Lā 'Aşghara Min Dhālika Wa Lā 'Akbara 'Illā Fī Kitābin Mubīnin 010-061 Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne.  ۚ 
'Alā 'Inna 'Awliyā'a Al-Lahi Lā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 010-062 To, Lalle ne masõyan Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba.
Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Kānū Yattaqūna 010-063 Waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa.
Lahumu Al-Bushrá Fī Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Fī Al-'Ākhirati  ۚ  Lā Tabdīla Likalimāti Al-Lahi  ۚ  Dhālika Huwa Al-Fawzu Al-`Ažīmu 010-064 Sunã da bushãra a cikin rãyuwar dũniya da ta Lãhira.Bãbu musanyãwa ga kalmõmin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma,  ۚ   ۚ 
Wa Lā Yaĥzunka Qawluhum  ۘ  'Inna Al-`Izzata Lillahi Jamī`āan  ۚ  Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu 010-065 Kada maganarsu ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani.  ۘ   ۚ 
'Alā 'Inna Lillahi Man As-Samāwāti Wa Man Al-'Arđi  ۗ  Wa Mā Yattabi`u Al-Ladhīna Yad`ūna Min Dūni Al-Lahi Shurakā'a  ۚ  'In Yattabi`ūna 'Illā Až-Žanna Wa 'In Hum 'Illā Yakhruşūna 010-066 To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa (ga Allah a MulkinSa). Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi kawai.  ۗ   ۚ 
Huwa Al-Ladhī Ja`ala Lakumu Al-Layla Litaskunū Fīhi Wa An-Nahāra Mubşirāan  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yasma`ūna 010-067 Shĩ ne wanda Ya sanya muku dare, dõmin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda sukẽ ji.  ۚ 
Qālū Attakhadha Al-Lahu Waladāan  ۗ  Subĥānahu  ۖ  Huwa Al-Ghanīyu  ۖ  Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۚ  'In `Indakum Min Sulţānin Bihadhā  ۚ  'Ataqūlūna `Alá Al-Lahi Mā Lā Ta`lamūna 010-068 Suka ce: "Allah Ya riƙi ɗa." Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah?  ۗ   ۖ   ۖ   ۚ   ۚ 
Qul 'Inna Al-Ladhīna Yaftarūna `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba Lā Yufliĥūna 010-069 Ka ce: "Haƙĩƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, bã zã su ci nasara ba."
Matā`un Ad-DunThumma 'Ilaynā Marji`uhum Thumma Nudhīquhumu Al-`Adhāba Ash-Shadīda Bimā Kānū Yakfurūna 010-070 Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
Wa Atlu `Alayhim Naba'a Nūĥin 'Idh Qāla Liqawmihi Yā Qawmi 'In Kāna Kabura `Alaykum Maqāmī Wa Tadhrī Bi'āyā Ti Al-Lahi Fa`alá Al-Lahi Tawakkaltu Fa'ajmi`ū 'Amrakum Wa Shurakā'akum Thumma Lā Yakun 'Amrukum `Alaykum Ghummatan Thumma Aqđū 'Ilayya Wa Lā Tunžirūni 010-071 Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ya mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri."
Fa'in Tawallaytum Famā Sa'altukum Min 'Ajrin  ۖ  'In 'Ajrī 'Illā `Alá Al-Lahi  ۖ  Wa 'Umirtu 'An 'Akūna Mina Al-Muslimīna 010-072 "Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."  ۖ   ۖ 
Fakadhdhabūhu Fanajjaynāhu Wa Man Ma`ahu Fī Al-Fulki Wa Ja`alnāhum Khalā'ifa Wa 'Aghraq Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā  ۖ  Fānžur Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mundharīna 010-073 Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.  ۖ 
Thumma Ba`athnā Min Ba`dihi Rusulāan 'Ilá Qawmihim Fajā'ūhum Bil-Bayyināti Famā Kānū Liyu'uminū Bimā Kadhdhabū Bihi Min Qablu  ۚ  Kadhālika Naţba`u `Alá Qulūbi Al-Mu`tadīna 010-074 Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bãyansa zuwa ga mutãnensu, suka jẽmusu da hujjõji bayyanannu, to, ba su kasance zã su yi ĩmãni ba sabõda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukãtan mãsu ta'addi.  ۚ 
Thumma Ba`athnā Min Ba`dihim Mūsá Wa Hārūna 'Ilá Fir`awna Wa Mala'ihi Bi'āyātinā Fāstakbarū Wa Kānū Qawmāan Mujrimīna 010-075 Sa'an nan kuma a bãyansu Muka aika Mũsa da Hãrũna zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, tãre da ãyõyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutãne mãsu laifi.
Falammā Jā'ahumu Al-Ĥaqqu Min `Indinā Qālū 'Inna Hādhā Lasiĥrun Mubīnun 010-076 Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga gare Mu, suka ce: "Wannan haƙĩƙa sihiri ne bayyananne."
Qāla Mūsá 'Ataqūlūna Lilĥaqqi Lammā Jā'akum  ۖ  'Asiĥrun Hādhā Wa Lā Yufliĥu As-Sāĥirūna 010-077 Mũsã ya ce: " Shin, kunã cẽwa ga gaskiya a lõkacin data zo muku? Shin, sihiri ne wannan? Lalle masihirci, bã ya cin nasara."  ۖ 
Qālū 'Aji'tanā Litalfitanā `Ammā Wajadnā `Alayhi 'Ābā'anā Wa Takūna Lakumā Al-Kibriyā'u Fī Al-'Arđi Wa Mā Naĥnu Lakumā Bimu'uminīna 010-078 Suka ce: "Shin, ka zo mana ne dõmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bã zã mu zama mãsu ĩmãni ba sabõda ku."
Wa Qāla Fir`awnu A'tūnī Bikulli Sāĥirin `Alīmin 010-079 Kuma Fir'auna ya ce: "Ku zo mini da dukan masihirci, masani."
Falammā Jā'a As-Saĥaratu Qāla Lahum Mūsá 'Alqū Mā 'Antum Mulqūna 010-080 To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa."
Falammā 'Alqaw Qāla Mūsá Mā Ji'tum Bihi As-Siĥru  ۖ  'Inna Al-Laha Sayubţiluhu  ۖ  'Inna Al-Laha Lā Yuşliĥu `Amala Al-Mufsidīna 010-081 To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata.  ۖ  ~  ۖ 
Wa Yuĥiqqu Al-Lahu Al-Ĥaqqa Bikalimātihi Wa Law Kariha Al-Mujrimūna 010-082 "Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi."
Famā 'Āmana Limūsá 'Illā Dhurrīyatun Min Qawmihi `Alá Khawfin Min Fir`awna Wa Mala'ihim 'An Yaftinahum  ۚ  Wa 'Inna Fir`awna La`ālin Al-'Arđi Wa 'Innahu Lamina Al-Musrifīna 010-083 Sa'an nan bãbu wanda ya yi ĩmãni da Mũsa fãce zuriya daga mutãnensa, a kan tsõron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjãyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga mãsu ɓarna.  ۚ 
Wa Qāla Mūsá Yā Qawmi 'In Kuntum 'Āmantum Bil-Lahi Fa`alayhi Tawakkalū 'In Kuntum Muslimīna 010-084 Kuma Mũsã ya ce: "Yã kũ mutãnena! Idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah, to, a gare Shi sai ku dõgara, idan kun kasance Musulmi."
Faqālū `Alá Al-Lahi Tawakkalnā Rabbanā Lā Taj`alnā Fitnatan Lilqawmi Až-Žālimīna 010-085 Sai suka ce: "Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu fitina ga mutãne azzãlumai.
Wa Najjinā Biraĥmatika Mina Al-Qawmi Al-Kāfirīna 010-086 "Kuma Ka kuɓutar da mu dõmin RahamarKa, daga mutãne kãfirai."
Wa 'Awĥaynā 'Ilá Mūsá Wa 'Akhīhi 'An Tabawwa'ā Liqawmikumā Bimişra Buyūtāan Wa Aj`alū Buyūtakum Qiblatan Wa 'Aqīmū Aş-Şalāata  ۗ  Wa Bashshiri Al-Mu'uminīna 010-087 Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla , kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni. ~  ۗ 
Wa Qāla Mūsá Rabbanā 'Innaka 'Ātayta Fir`awna Wa Mala'ahu Zīnatan Wa 'Amwālāan Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Rabbanā Liyuđillū `An Sabīlika  ۖ  Rabbanā Aţmis `Alá 'Amwālihim Wa Ashdud `Alá Qulūbihim Falā Yu'uminū Ĥattá Yaraw Al-`Adhāba Al-'Alīma 010-088 Sai MũSã ya ce: "Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar (damutãne) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi."  ۖ 
Qāla Qad 'Ujībat Da`watukumā Fāstaqīmā Wa Lā Tattabi`āni Sabīla Al-Ladhīna Lā Ya`lamūna 010-089 (Allah) Yã ce: "Lalle ne an karɓi addu'arku. Sai ku daidaitu kuma kada ku bi hanyar waɗanda ba su sani ba."
Wa Jāwaznā Bibanī 'Isrā'īla Al-Baĥra Fa'atba`ahum Fir`awnu Wa Junūduhu Baghyāan Wa`adwan  ۖ  Ĥattá 'Idhā 'Adrakahu Al-Gharaqu Qāla 'Āmantu 'Annahu Lā 'Ilāha 'Illā Al-Ladhī 'Āmanat Bihi Banū 'Isrā'īla Wa 'Anā Mina Al-Muslimīna 010-090 Kuma Muka ƙẽtãrar da Banĩ Isrã'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zãlunci da ƙẽtare haddi, har a lõkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: "Nã yi ĩmãni cẽwa, haƙĩƙa, bãbu abin bautawa fãce wannan da Banũ Isrã'il suka yi ĩmãni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi."  ۖ  ~
'Āl'āna Wa Qad `Aşayta Qablu Wa Kunta Mina Al-Mufsidīna 010-091 Ashe! A yanzu! Alhãli kuwa, haƙĩƙa ka sãɓa a gabãni, kuma ka kasance daga mãsu ɓarna?
Fālyawma Nunajjīka Bibadanika Litakūna Liman Khalfaka 'Āyatan  ۚ  Wa 'Inna Kathīrāan Mina An-Nāsi `An 'Āyātinā Laghāfilūna 010-092 To, a yau Munã kuɓutar da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu.  ۚ 
Wa Laqad Bawwa'nā Banī 'Isrā'īla Mubawwa'a Şidqin Wa Razaqnāhum Mina Aţ-Ţayyibāti Famā Akhtalafū Ĥattá Jā'ahumu Al-`Ilmu  ۚ  'Inna Rabbaka Yaqđī Baynahum Yawma Al-Qiyāmati Fīmā Kānū Fīhi Yakhtalifūna 010-093 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar da Banĩ Isrã'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa mãsu dãɗi. Sa'an nan ba su sãɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Kiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna.  ۚ 
Fa'in Kunta Fī Shakkin Mimmā 'Anzalnā 'Ilayka Fās'ali Al-Ladhīna Yaqra'ūna Al-Kitāba Min Qablika  ۚ  Laqad Jā'aka Al-Ĥaqqu Min Rabbika Falā Takūnanna Mina Al-Mumtarīna 010-094 To, idan ka kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littãfi daga gabaninka. Lalle ne, haƙĩƙa, gaskiya tã jẽ maka daga Ubangijinka dõmin haka kada ka kasance daga mãsu kõkanto.  ۚ 
Wa Lā Takūnanna Mina Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyāti Al-Lahi Fatakūna Mina Al-Khāsirīna 010-095 Kuma kada ka kasance daga waɗanda suke ƙaryatãwa game da ãyõyin Allah, har ka kasance daga mãsu hasãra.
'Inna Al-Ladhīna Ĥaqqat `Alayhim Kalimatu Rabbika Lā Yu'uminūna 010-096 Lalle ne waɗanda kalmar Ubangijinka ta wajaba a kansu, bã zã su yi ĩmãni ba.
Wa Law Jā'at/hum Kullu 'Āyatin Ĥattá Yaraw Al-`Adhāba Al-'Alīma 010-097 Kuma kõ dã kõwace ãyã ta jẽ musu, sai sun ga azãba mai raɗaɗi.
Falawlā Kānat Qaryatun 'Āmanat Fanafa`ahā 'Īmānuhā 'Illā Qawma Yūnis Lammā 'Āmanū Kashafnā `Anhum `Adhāba Al-Khizyi Fī Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Matta`nāhum 'Ilá Ĥīnin 010-098 To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.
Wa Law Shā'a Rabbuka La'āmana Man Al-'Arđi Kulluhum Jamī`āan  ۚ  'Afa'anta Tukrihu An-Nāsa Ĥattá Yakūnū Mu'uminīna 010-099 Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi ĩmãni dukansu gabã ɗaya. Shin, kai kanã tĩlasta mutãnene har su kasance mãsu ĩmãni?  ۚ 
Wa Mā Kāna Linafsin 'An Tu'umina 'Illā Bi'idhni Al-Lahi  ۚ  Wa Yaj`alu Ar-Rijsa `Alá Al-Ladhīna Lā Ya`qilūna 010-100 Kuma ba ya kasancẽwa ga wani rai ya yi ĩmãni fãce da iznin Allah, kuma (Allah) Yanã sanya ƙazanta a kan waɗanda bã su yin hankali.  ۚ 
Qul Anžurū Mādhā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Wa Mā Tugh Al-'Āyātu Wa An-Nudhuru `An Qawmin Lā Yu'uminūna 010-101 Ka ce: "Ku dũbi abin da yake cikin sammai da ƙasa."Kuma ãyõyi da gargaɗi bã su wadãtarwa ga mutãne waɗanda bã su yin ĩmãni.  ۚ 
Fahal Yantažirūna 'Illā Mithla 'Ayyāmi Al-Ladhīna Khalaw Min Qablihim  ۚ  Qul Fāntažirū 'Innī Ma`akum Mina Al-Muntažirīna 010-102 To, Shin sunã jiran wani abu fãce kamar misãlin kwãnukan waɗanda suka shũɗe daga gabãninsu? Ka ce: "Ku yi jira! Lalle nĩ tãre da ku, inã daga mãsu jira."  ۚ 
Thumma Nunajjī Rusulanā Wa Al-Ladhīna 'Āmanū  ۚ  Kadhālika Ĥaqqāan `Alaynā Nunji Al-Mu'uminīna 010-103 Sa'an nan kuma Munã kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da mãsu ĩmãni.  ۚ 
Qul Yā 'Ayyuhā An-Nāsu 'In KuntumShakkin Min Dīnī Falā 'A`budu Al-Ladhīna Ta`budūna Min Dūni Al-Lahi Wa Lakin 'A`budu Al-Laha Al-Ladhī Yatawaffākum  ۖ  Wa 'Umirtu 'An 'Akūna Mina Al-Mu'uminīna 010-104 Ka ce: "Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa,waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni."  ۖ 
Wa 'An 'Aqim Wajhaka Lilddīni Ĥanīfāan Wa Lā Takūnanna Mina Al-Mushrikīna 010-105 "Kuma (an ce mini ): Ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka.
Wa Lā Tad`u Min Dūni Al-Lahi Mā Lā Yanfa`uka Wa Lā Yađurruka  ۖ  Fa'in Fa`alta Fa'innaka 'Idhāan Mina Až-Žālimīna 010-106 "Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci."  ۖ 
Wa 'In Yamsaska Al-Lahu Biđurrin Falā Kāshifa Lahu 'Illā Huwa  ۖ  Wa 'In Yuridka Bikhayrin Falā Rādda Lifađlihi  ۚ  Yuşību Bihi Man Yashā'u Min `Ibādihi  ۚ  Wa Huwa Al-Ghafūru Ar-Raĥīmu 010-107 Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyẽ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhẽri, to, bãbumai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. ~  ۖ   ۚ   ۚ 
Qul Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Qad Jā'akumu Al-Ĥaqqu Min Rabbikum  ۖ  Famani Ahtadá Fa'innamā Yahtadī Linafsihi  ۖ  Wa Man Đalla Fa'innamā Yađillu `Alayhā  ۖ  Wa Mā 'Anā `Alaykum Biwakīlin 010-108 Ka ce: "Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba."  ۖ   ۖ   ۖ 
Wa Attabi` Mā Yūĥá 'Ilayka Wa Aşbir Ĥattá Yaĥkuma Al-Lahu  ۚ  Wa Huwa Khayru Al-Ĥākimīna 010-109 Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci.  ۚ 
Next Sūrah