9) Sūrat At-Tawbah

Printed format

9)

Barā'atun Mina Al-Lahi Wa Rasūlihi 'Ilá Al-Ladhīna `Āhadttum Mina Al-Mushrikīna 009-001 Barranta daga Allah da ManzonSa zuwa ga waɗanda kuka yi wa alkawari daga mãsu shirki ~
Fasīĥū Fī Al-'Arđi 'Arba`ata 'Ash/hurin Wa A`lamū 'Annakum Ghayru Mu`jizī Al-Lahi  ۙ  Wa 'Anna Al-Laha Mukh Al-Kāfirīna 009-002 Sabõda haka ku yi tafiya a cikin ƙasa watã huɗu, kuma ku sani lalle kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne, kuma lalle Allah ne Mai kunyatar da kãfirai.  ۙ 
Wa 'Adhānun Mina Al-Lahi Wa Rasūlihi 'Ilá An-Nāsi Yawma Al-Ĥajji Al-'Akbari 'Anna Al-Laha Barī'un Mina Al-Mushrikīna  ۙ  Wa Rasūluhu  ۚ  Fa'in Tubtum Fahuwa Khayrun Lakum  ۖ  Wa 'In Tawallaytum Fā`lamū 'Annakum Ghayru Mu`jizī Al-Lahi  ۗ  Wa Bashshiri Al-Ladhīna Kafarū Bi`adhābin 'Alīmin 009-003 Kuma da yẽkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cẽwa lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan kun tũba to shi ne mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka kãfirta, da azãba mai raɗaɗi. ~  ۙ   ۚ   ۖ   ۗ 
'Illā Al-Ladhīna `Āhadttum Mina Al-Mushrikīna Thumma Lam Yanquşūkum Shay'āan Wa Lam Yužāhirū `Alaykum 'Aĥadāan Fa'atimmū 'Ilayhim `Ahdahum 'Ilá Muddatihim  ۚ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Muttaqīna 009-004 Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare su, har ga iyakar yarjẽjẽyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.  ۚ 
Fa'idhā Ansalakha Al-'Ash/huru Al-Ĥurumu Fāqtulū Al-Mushrikīna Ĥaythu Wajadtumūhum Wa Khudhūhum Wa Aĥşurūhumq`udū Lahum Kulla Marşadin  ۚ  Fa'in Tābū Wa 'Aqāmū Aş-Şalāata Wa 'Ātaw Az-Zakāata Fakhallū Sabīlahum  ۚ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 009-005 Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka sãmẽ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata. To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara,Mai jin ƙai.  ۚ   ۚ 
Wa 'In 'Aĥadun Mina Al-Mushrikīna Astajāraka Fa'ajirhu Ĥattá Yasma`a Kalāma Al-Lahi Thumma 'Abligh/hu Ma'manahu  ۚ  Dhālika Bi'annahum Qawmun Lā Ya`lamūna 009-006 Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa domin lalle ne su, mutãne ne waɗanda ba su sani ba.  ۚ 
Kayfa Yakūnu Lilmushrikīna `Ahdun `Inda Al-Lahi Wa `Inda Rasūlihi 'Illā Al-Ladhīna `Āhadtum `Inda Al-Masjidi Al-Ĥarāmi  ۖ  Famā Astaqāmū Lakum Fāstaqīmū Lahum  ۚ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Muttaqīna 009-007 Yãya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancẽwa ga mushirikai, fãce ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun tsaya sõsai gare ku, sai ku tsayu sõsai gare su. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa. ~  ۖ   ۚ 
Kayfa Wa 'In Yažharū `Alaykum Lā Yarqubū Fīkum 'Illāan Wa Lā Dhimmatan  ۚ  Yurđūnakum Bi'afwāhihim Wa Ta'bá Qulūbuhum Wa 'Aktharuhum Fāsiqūna 009-008 Yãya, alhãli idan sun ci nasara a kanku, bã zã su tsare wata zumun ta ba a cikinku, kuma haka wata amãna, sunã yardar da ku da bãkunansu kuma zukãtansu sunã ƙi? Kuma mafi yawansu fãsiƙai ne.  ۚ 
Ashtaraw Bi'āyāti Al-Lahi Thamanāan Qalīlāan Faşaddū `An Sabīlihi  ۚ  'Innahum Sā'a Mā Kānū Ya`malūna 009-009 Sun saya da ãyõyin Allah, 'yan kuɗi kaɗan, sa'an nan suka kange daga hanyar Allah. Lalle ne sũ, abin da suka kasance sunã aikatãwa yã mũnana. ~  ۚ 
Lā Yarqubūna Fī Mu'uminin 'Illāan Wa Lā Dhimmatan  ۚ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Mu`tadūna 009-010 Bã su tsaron wata zumunta a cikin mũminai, kuma haka bãsu tsaron wata amãna. Kuma waɗannan ne mãsu ta'adi.  ۚ 
Fa'in Tābū Wa 'Aqāmū Aş-Şalāata Wa 'Ātaw Az-Zakāata Fa'ikhwānukum Ad-Dīni  ۗ  Wa Nufaşşilu Al-'Āyāti Liqawmin Ya`lamūna 009-011 Sa'an nan idan sun tũba kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.  ۗ 
Wa 'In Nakathū 'Aymānahum Min Ba`di `Ahdihim Wa Ţa`anū Fī Dīnikum Faqātilū 'A'immata Al-Kufri  ۙ  'Innahum Lā 'Aymāna Lahum La`allahum Yantahūna 009-012 Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãninsu sunã hanuwa.  ۙ 
'Alā Tuqātilūna Qawmāan Nakathū 'Aymānahum Wa Hammū Bi'ikhrāji Ar-Rasūli Wa Hum Bada'ūkum 'Awwala Marratin  ۚ  'Atakhshawnahum  ۚ  Fa-Allāhu 'Aĥaqqu 'An Takhshawhu 'In Kuntum Mu'uminīna 009-013 Shin, bã ku yaƙin mutãne, waɗanda suka warware rantsuwõyinsu, kuma suka yi niyya ga fitar da Manzo, kuma sũ ne suka fãra muku, tun a farkon lõkaci? Shin kunã tsõron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsõronSa, idan kun kasance mũminai!  ۚ   ۚ 
Qātilūhum Yu`adhdhibhumu Al-Lahu Bi'aydīkum Wa Yukhzihim Wa Yanşurkum `Alayhim Wa Yashfi Şudūra Qawmin Mu'uminīna 009-014 Ku yãƙe su, Allah Ya yi musu azabã da hannãyenku, kuma Ya kunyatar da su, kuma Ya taimake ku, kuma Ya warkar da ƙirãzan mutãne mũminai.
Wa Yudh/hib Ghayža Qulūbihim  ۗ  Wa Yatūbu Al-Lahu `Alá Man Yashā'u Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 009-015 Kuma Ya tafĩ da fushin zukãtansu, kuma Ya karɓi tũba a kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.  ۗ   ۗ 
'Am Ĥasibtum 'An Tutrakū Wa Lammā Ya`lami Al-Lahu Al-Ladhīna Jāhadū Minkum Wa Lam Yattakhidhū Min Dūni Al-Lahi Wa Lā Rasūlihi Wa Lā Al-Mu'uminīna Walījatan Wa  ۚ  Allāhu Khabīrun Bimā Ta`malūna 009-016 Kõ kunã zaton a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihãdi ba daga gare ku, kuma sũ ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da mũminai? Kuma Allah ne Mai jarrabãwa ga abin da kuke aikatãwa.  ۚ 
Mā Kāna Lilmushrikīna 'An Ya`murū Masājida Al-Lahi Shāhidīna `Alá 'Anfusihim Bil-Kufri  ۚ  'Ūlā'ika Ĥabiţat 'A`māluhum Wa Fī An-Nāri Hum Khālidūna 009-017 Bã ya kasancewa ga mãsu shirki su rãya masallatan Allah, alhãli kuwa sunã mãsu bãyar da shaida a kan rãyukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓãci, kuma a cikin wutã sũ madawwama  ۚ 
'Innamā Ya`muru Masājida Al-Lahi Man 'Āmana Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa 'Aqāma Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata Wa Lam Yakhsha 'Illā Al-Laha  ۖ  Fa`asá 'Ūlā'ika 'An Yakūnū Mina Al-Muhtadīna 009-018 Abin sani kawai, mai rãya masallãtan Allah, shĩ ne wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya tsayar da salla kuma ya bãyar da zakka, kuma bai ji tsõron kõwa ba fãce Allah. To, akwai tsammãnin waɗannan su kasance daga shiryayyu.  ۖ 
'Aja`altum Siqāyata Al-Ĥājji Wa `Imārata Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Kaman 'Āmana Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa Jāhada Fī Sabīli Al-Lahi  ۚ  Lā Yastawūna `Inda Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna 009-019 Shin, kun sanya shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.  ۚ   ۗ 
Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Hājarū Wa Jāhadū Fī Sabīli Al-Lahi Bi'amwālihim Wa 'Anfusihim 'A`žamu Darajatan `Inda Al-Lahi  ۚ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Fā'izūna 009-020 Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi, a cikin hanyar Allah, da dũkiyõyinsu, da rãyukansu, sũ ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah, kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.  ۚ 
Yubashshiruhum Rabbuhum Biraĥmatin Minhu Wa Riđwānin Wa Jannātin Lahum Fīhā Na`īmun Muqīmun 009-021 Ubangijinsu Yanã yi musu bishãra da wata rahama daga gare shi, da yarda, da gidãjen Aljanna. sunã da, a cikinsu, ni'ima zaunanniya.
Khālidīna Fīhā 'Abadāan  ۚ  'Inna Al-Laha `Indahu 'Ajrun `Ažīmun 009-022 Sunã madawwamã a cikinsu, har abada. Lalle ne Allah a wurinSa akwai lãda mai girma.  ۚ  ~
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tattakhidhū 'Ābā'akum Wa 'Ikhwānakum 'Awliyā'a 'Ini Astaĥabbū Al-Kufra `Alá Al-'Īmāni  ۚ  Wa Man Yatawallahum Minkum Fa'ūlā'ika Humu Až-Žālimūna 009-023 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masõya, idan sun nũna son kãfirci a kan ĩmãni. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, waɗannan sũ ne azzãlumai.  ۚ 
Qul 'In Kāna 'Ābā'uukum Wa 'Abnā'uukum Wa 'Ikhwānukum Wa 'Azwājukum Wa `Ashīratukum Wa 'Amwālun Aqtaraftumūhā Wa Tijāratun Takhshawna Kasādahā Wa Masākinu Tarđawnahā 'Aĥabba 'Ilaykum Mina Al-Lahi Wa Rasūlihi Wa Jihādin Fī Sabīlihi Fatarabbaşū Ĥattá Ya'tiya Al-Lahu Bi'amrihi Wa  ۗ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Al-Fāsiqīna 009-024 Ka ce: "Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da mãtanku da danginku da dũkiyõyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsõron tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya sõyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihãdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah Ya zo da umurninSa! Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai."  ۗ 
Laqad Naşarakumu Al-Lahu Fī Mawāţina Kathīratin  ۙ  Wa Yawma Ĥunaynin  ۙ  'Idh 'A`jabatkum Kathratukum Falam Tughni `Ankum Shay'āan Wa Đāqat `Alaykumu Al-'Arđu Bimā Raĥubat Thumma Wallaytum Mudbirīna 009-025 Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar Hunainu, a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã mãsu bãyar da bãya.  ۙ   ۙ 
Thumma 'Anzala Al-Lahu Sakīnatahu `Alá Rasūlihi Wa `Alá Al-Mu'uminīna Wa 'Anzala Junūdāan Lam Tarawhā Wa `Adhdhaba Al-Ladhīna Kafarū  ۚ  Wa Dhalika Jazā'u Al-Kāfirīna 009-026 Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa kuma a kan mũminai, kuma Ya saukar da rundunõni waɗanda ba ku gan su ba, kuma Ya azabtar da waɗanda suka kãfirta: Wancan ne sakamakon kãfirai.  ۚ 
Thumma Yatūbu Al-Lahu Min Ba`di Dhālika `Alá Man Yashā'u Wa  ۗ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 009-027 Sa'an nan kuma Allah Ya karɓi tũba daga bãyan wancana kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai rahama.  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Innamā Al-Mushrikūna Najasun Falā Yaqrabū Al-Masjida Al-Ĥarāma Ba`da `Āmihimdhā  ۚ  Wa 'In Khiftum `Aylatan Fasawfa Yughnīkumu Al-Lahu Min Fađlihi 'In Shā'a  ۚ  'Inna Al-Laha `Alīmun Ĥakīmun 009-028 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bãyan shẽkararsu wannan. Kuma idan kun ji tsõron talauci to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalarSa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima.  ۚ  ~  ۚ 
Qātilū Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-Lahi Wa Lā Bil-Yawmi Al-'Ākhiri Wa Lā Yuĥarrimūna Mā Ĥarrama Al-Lahu Wa Rasūluhu Wa Lā Yadīnūna Dīna Al-Ĥaqqi Mina Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Ĥattá Yu`ţū Al-Jizyata `An Yadin Wa Hum Şāghirūna 009-029 Ku yãƙi waɗanda bã su yin ĩmãni da Allah kuma bã su ĩmãni da Rãnar Lãhira kumabã su haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta, kuma bã su yin addini, addinin gaskiya, daga waɗanda aka bai wa Littãfi, har sai sun bãyar da jizya daga, hannu, kuma sunã ƙasƙantattu.
Wa Qālati Al-Yahūdu `Uzayrun Abnu Al-Lahi Wa Qālati An-Naşārá Al-Masīĥu Abnu Al-Lahi  ۖ  Dhālika Qawluhum Bi'afwāhihim  ۖ  Yuđāhi'ūna Qawla Al-Ladhīna Kafarū Min Qablu  ۚ  Qātalahumu Al-Lahu  ۚ  'Anná Yu'ufakūna 009-030 Kuma Yahũdãwa suka ce: "Uzairu ɗan Allah ne."Kuma Nasãra suka ce: "Masĩhu ɗan Allah ne." Wancan zancensu ne da bãkunansu. Sunã kamã da maganar waɗanda suka kãfirta daga gabãni. Allah Yã la'ance su! Yãya aka karkatar da su?  ۖ   ۖ   ۚ   ۚ 
Attakhadhū 'Aĥbārahum Wa Ruhbānahum 'Arbābāan Min Dūni Al-Lahi Wa Al-Masīĥa Abna Maryama Wa Mā 'Umirū 'Illā Liya`budū 'Ilahāan Wāĥidāan  ۖ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۚ  Subĥānahu `Ammā Yushrikūna 009-031 Sun riƙi mãlamansu (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi Masĩhu ɗan Maryama ( haka). Kuma ba a umurce su ba fãce da su bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga barin abin da suke yin shirki da shi.  ۖ  ~  ۚ 
Yurīdūna 'An Yuţfi'ū Nūra Al-Lahi Bi'afwāhihim Wa Ya'bá Al-Lahu 'Illā 'An Yutimma Nūrahu Wa Law Kariha Al-Kāfirūna 009-032 Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunãnsu. Kuma Allah Yanã ki, fãce dai Ya cika haskenSa, kuma kõ da kãfirai sun ƙi.
Huwa Al-Ladhī 'Arsala Rasūlahu Bil-Hudá Wa Dīni Al-Ĥaqqi Liyužhirahu `Alá Ad-Dīni Kullihi Wa Law Kariha Al-Mushrikūna 009-033 Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyanl shi a kan addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Inna Kathīrāan Mina Al-'Aĥbāri Wa Ar-Ruhbāni Laya'kulūna 'Amwāla An-Nāsi Bil-Bāţili Wa Yaşuddūna `An Sabīli Al-Lahi Wa  ۗ  Al-Ladhīna Yaknizūna Adh-Dhahaba Wa Al-Fiđđata Wa Lā Yunfiqūnahā Fī Sabīli Al-Lahi Fabashshirhum Bi`adhābin 'Alīmin 009-034 Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.  ۗ 
Yawma Yuĥmá `Alayhā Fī Nāri Jahannama Fatukwá Bihā Jibāhuhum Wa Junūbuhum Wa Žuhūruhum  ۖ  Hādhā Mā Kanaztum Li'nfusikum Fadhūqū Mā Kuntum Taknizūna 009-035 A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska."  ۖ 
'Inna `Iddata Ash-Shuhūri `Inda Al-Lahi Athnā `Ashara Shahrāan Fī Kitābi Al-Lahi Yawma Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Minhā 'Arba`atun Ĥurumun  ۚ  Dhālika Ad-Dīnu Al-Qayyimu  ۚ  Falā Tažlimū Fīhinna 'Anfusakum  ۚ  Wa Qātilū Al-Mushrikīna Kāffatan Kamā Yuqātilūnakum Kāffatan  ۚ  Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Ma`a Al-Muttaqīna 009-036 Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
'Innamā An-Nasī'u Ziyādatun Al-Kufri  ۖ  Yuđallu Bihi Al-Ladhīna Kafarū Yuĥillūnahu `Āmāan Wa Yuĥarrimūnahu `Āmāan Liyuwāţi'ū `Iddata Mā Ĥarrama Al-Lahu Fayuĥillū Mā Ĥarrama Al-Lahu  ۚ  Zuyyina Lahum Sū'u 'A`mālihim Wa  ۗ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Al-Kāfirīna 009-037 Abin sani kawai, "Jinkirtãwa" ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.  ۖ   ۚ   ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Mā Lakum 'Idhā Qīla Lakum Anfirū Fī Sabīli Al-Lahi Aththāqaltum 'Ilá Al-'Arđi  ۚ  'Arađītum Bil-Ĥayāati Ad-Dunyā Mina Al-'Ākhirati  ۚ  Famā Matā`u Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Fī Al-'Ākhirati 'Illā Qalīlun 009-038 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan.  ۚ   ۚ 
'Illā Tanfirū Yu`adhdhibkum `Adhābāan 'Alīmāan Wa Yastabdil Qawmāan Ghayrakum Wa Lā Tađurrūhu Shay'āan Wa  ۗ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 009-039 Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya musanya wasu mutãne, wasunku (a maimakonku). Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.  ۗ 
'Illā Tanşurūhu Faqad Naşarahu Al-Lahu 'Idh 'Akhrajahu Al-Ladhīna Kafarū Thāniya Athnayni 'Idh Humā Fī Al-Ghāri 'Idh Yaqūlu Lişāĥibihi Lā Taĥzan 'Inna Al-Laha Ma`anā  ۖ  Fa'anzala Al-Lahu Sakīnatahu `Alayhi Wa 'Ayyadahu Bijunūdin Lam Tarawhā Wa Ja`ala Kalimata Al-Ladhīna Kafarū As-Suflá  ۗ  Wa Kalimatu Al-Lahi Hiya Al-`Ulyā Wa  ۗ  Allāhu `Azīzun Ĥakīmun 009-040 Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: "Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yanã tãre da mu." Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.  ۖ   ۗ   ۗ 
Anfirū Khifāfāan Wa Thiqālāan Wa Jāhidū Bi'amwālikum Wa 'Anfusikum Fī Sabīli Al-Lahi  ۚ  Dhālikum Khayrun Lakum 'In Kuntum Ta`lamūna 009-041 Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.  ۚ 
Law Kāna `Arađāan Qarībāan Wa Safarāan Qāşidāan Lāttaba`ūka Wa Lakin Ba`udat `Alayhimu Ash-Shuqqatu  ۚ  Wa Sayaĥlifūna Bil-Lahi Law Astaţa`nā Lakharajnā Ma`akum Yuhlikūna 'Anfusahum Wa Allāhu Ya`lamu 'Innahum Lakādhibūna 009-042 Dã yã kasance wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa.Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah, "Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.'  ۚ 
`Afā Al-Lahu `Anka Lima 'Adhinta Lahum Ĥattá Yatabayyana Laka Al-Ladhīna Şadaqū Wa Ta`lama Al-Kādhibīna 009-043 Allah Ya yãfe maka laifi. Dõmin me ka yi musu izinin zama? Sai waɗanda suka yi gaskiya ssun bayyana a gare ka, kuma ka san maƙaryata.
Lā Yasta'dhinuka Al-Ladhīna Yu'uminūna Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri 'An Yujāhidū Bi'amwālihim Wa 'Anfusihim Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Bil-Muttaqīna 009-044 Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin, jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa.  ۗ 
'Innamā Yasta'dhinuka Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa Artābat Qulūbuhum Fahum Fī Raybihim Yataraddadūna 009-045 Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin kai kãwo.
Wa Law 'Arādū Al-Khurūja La'a`addū Lahu `Uddatan Wa Lakin Kariha Al-Lahu Anbi`āthahum Fathabbaţahum Wa Qīla Aq`udū Ma`a Al-Qā`idīna 009-046 Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu zama.
Law Kharajū Fīkum Mā Zādūkum 'Illā Khabālāan Wa La'awđa`ū Khilālakum Yabghūnakumu Al-Fitnata Wa Fīkum Sammā`ūna Lahum Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Biž-Žālimīna 009-047 Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,  ۗ 
Laqadi Abtaghaw Al-Fitnata Min Qablu Wa Qallabū Laka Al-'Umūra Ĥattá Jā'a Al-Ĥaqqu Wa Žahara 'Amru Al-Lahi Wa Humrihūna 009-048 Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka al'amari, har gaskiya ta zo, kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu ƙyãma,
Wa Minhum Man Yaqūlu A'dhan Lī Wa Lā Taftinnī  ۚ  'Alā Fī Al-Fitnati Saqaţū  ۗ  Wa 'Inna Jahannama Lamuĥīţatun Bil-Kāfirīna 009-049 Kuma daga cikinsu akwai mai cẽwa, "Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni." To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.  ۚ   ۗ 
'In Tuşibka Ĥasanatun Tasu'uhum  ۖ  Wa 'In Tuşibka Muşībatun Yaqūlū Qad 'Akhadhnā 'Amranā Min Qablu Wa Yatawallaw Wa Hum Farūna 009-050 Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka sai su ce: "Haƙĩƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabãni."Kuma sujũya, alhãli kuwa sunã mãsu farin ciki.  ۖ 
Qul Lan Yuşībanā 'Illā Mā Kataba Al-Lahu Lanā Huwa Mawlānā  ۚ  Wa `Alá Al-Lahi Falyatawakkali Al-Mu'uminūna 009-051 Ka ce: "Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara."  ۚ 
Qul Hal Tarabbaşūna Binā 'Illā 'Iĥdá Al-Ĥusnayayni  ۖ  Wa Naĥnu Natarabbaşu Bikum 'An Yuşībakumu Al-Lahu Bi`adhābin Min `Indihi 'Aw Bi'aydīnā  ۖ  Fatarabbaşū 'Innā Ma`akum Mutarabbişūna 009-052 Ka ce: "Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu mãsu kyau, alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne."  ۖ  ~  ۖ 
Qul 'Anfiqū Ţaw`āan 'Aw Karhāan Lan Yutaqabbala Minkum  ۖ  'Innakum Kuntum Qawmāan Fāsiqīna 009-053 Ka ce: "Ku ciyar a kan yarda kõ kuwa a kan tĩlas. Bã zã a karɓa daga gare ku ba. Lalle ne kũ, kun kasance mutãne fãsiƙai."  ۖ 
Wa Mā Mana`ahum 'An Tuqbala Minhum Nafaqātuhum 'Illā 'Annahum Kafarū Bil-Lahi Wa Birasūlihi Wa Lā Ya'tūna Aş-Şalāata 'Illā Wa Hum Kusālá Wa Lā Yunfiqūna 'Illā Wa Humrihūna 009-054 Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma.
Falā Tu`jibka 'Amwāluhum Wa Lā 'Awlāduhum  ۚ  'Innamā Yurīdu Al-Lahu Liyu`adhdhibahum Bihā Fī Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Tazhaqa 'Anfusuhum Wa Hum Kāfirūna 009-055 Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.  ۚ 
Wa Yaĥlifūna Bil-Lahi 'Innahum Laminkum Wa Mā Hum Minkum Wa Lakinnahum Qawmun Yafraqūna 009-056 Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro.
Law Yajidūna Malja'an 'Aw Maghārātin 'Aw Muddakhalāan Lawallaw 'Ilayhi Wa Hum Yajmaĥūna 009-057 Dã sunã sãmun mafaka kõ kuwa waɗansu ɓulõli, kõ kuwa wani mashigi, da sun, jũya zuwa gare shi, kuma suna gaggawar shiga.
Wa Minhum Man Yalmizuka Fī Aş-Şadaqāti Fa'in 'U`ţū Minhā Rađū Wa 'In Lam Yu`ţaw Minhā 'Idhā Hum Yaskhūna 009-058 Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dũkiyõyin sadaka, sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta sai su zamo sunã mãsu fushi.
Wa Law 'Annahum Rađū Mā 'Ātāhumu Al-Lahu Wa Rasūluhu Wa Qālū Ĥasbunā Al-Lahu Sayu'utīnā Al-Lahu Min Fađlihi Wa Rasūluhu 'Innā 'Ilá Al-Lahi Rāghibūna 009-059 Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka ce: "Ma'ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa (zai bã mu). Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne." ~
'Innamā Aş-Şadaqātu Lilfuqarā'i Wa Al-Masākīni Wa Al-`Āmilīna `Alayhā Wa Al-Mu'uallafati Qulūbuhum Wa Fī Ar-Riqābi Wa Al-Ghārimīna Wa Fī Sabīli Al-Lahi Wa Aibni As-Sabīli  ۖ  Farīđatan Mina Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 009-060 Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.  ۖ   ۗ 
Wa Minhumu Al-Ladhīna Yu'udhūna An-Nabīya Wa Yaqūlūna Huwa 'Udhunun  ۚ  Qul 'Udhunu Khayrin Lakum Yu'uminu Bil-Lahi Wa Yu'uminu Lilmu'uminīna Wa Raĥmatun Lilladhīna 'Āmanū Minkum Wa  ۚ  Al-Ladhīna Yu'udhūna Rasūla Al-Lahi Lahum `Adhābun 'Alīmun 009-061 Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa "Shi kunne ne." Ka ce: "Kunnen alhẽri gare ku,Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku."Kuma waɗanda suke cũtar Manzon Allah sunã da azãba mai raɗaɗi.  ۚ   ۚ 
Yaĥlifūna Bil-Lahi Lakum Liyurđūkum Wa Allāhu Wa Rasūluhu 'Aĥaqqu 'An Yurđūhu 'In Kānū Mu'uminīna 009-062 Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai. ~ ~
'Alam Ya`lamū 'Annahu Man Yuĥādidi Al-Laha Wa Rasūlahu Fa'anna Lahu Nāra Jahannama Khālidāan Fīhā  ۚ  Dhālika Al-Khizyu Al-`Ažīmu 009-063 Shin, ba su sani ba cẽwa "Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa babba!"  ۚ 
Yaĥdharu Al-Munāfiqūna 'An Tunazzala `Alayhim Sūratun Tunabbi'uhum Bimā Fī Qulūbihim  ۚ  Quli Astahzi'ū 'Inna Al-Laha Mukhrijun Mā Taĥdharūna 009-064 Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu,wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro."  ۚ 
Wa La'in Sa'altahum Layaqūlunna 'Innamā Kunnā Nakhūđu Wa Nal`abu  ۚ  Qul 'Abiālllahi Wa 'Āyātihi Wa Rasūlihi Kuntum Tastahzi'ūna 009-065 Kuma lalle ne, idan ka tambaye , su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"  ۚ 
Lā Ta`tadhirū Qad Kafartum Ba`da 'Īmānikum  ۚ  'In Na`fu `An Ţā'ifatin Minkum Nu`adhdhib Ţā'ifatan Bi'annahum Kānū Mujrimīna 009-066 "Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun kasance mãsu laifi."  ۚ 
Al-Munāfiqūna Wa Al-Munāfiqātu Ba`đuhum Min Ba`đin  ۚ  Ya'murūna Bil-Munkari Wa Yanhawna `Ani Al-Ma`rūfi Wa Yaqbiđūna 'Aydiyahum  ۚ  Nasū Al-Laha Fanasiyahum  ۗ  'Inna Al-Munāfiqīna Humu Al-Fāsiqūna 009-067 Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi kuma sunã hani daga alhẽri.Kuma sunã damƙẽwar hannayensu.Sun mance Allah, sai Ya mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai.  ۚ   ۚ   ۗ 
Wa`ada Al-Lahu Al-Munāfiqīna Wa Al-Munāfiqāti Wa Al-Kuffāra Nāra Jahannama Khālidīna Fīhā  ۚ  Hiya Ĥasbuhum  ۚ  Wa La`anahumu Al-Lahu  ۖ  Wa Lahum `Adhābun Muqīmun 009-068 Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance su, kuma sunã da azãba zaunanniya.  ۚ   ۚ   ۖ 
Kālladhīna Min Qablikum Kānū 'Ashadda Minkum Qūwatan Wa 'Akthara 'Amwālāan Wa 'Awlādāan Fāstamta`ū Bikhalāqihim Fāstamta`tum Bikhalāqikum Kamā Astamta`a Al-Ladhīna Min Qablikum Bikhalāqihim Wa Khuđtum Kālladhī Khāđū  ۚ  'Ūlā'ika Ĥabiţat 'A`māluhum Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Khāsirūna 009-069 Kamar waɗanda suke a gabãninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku, kuma mafi yawan dũkiyõyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabãninku suka ji dãɗi, da rabonsu, kuma kuka kũtsa kamar kũtsãwarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓãci a dũniya da Lãhira, kuma waɗannan sũ ne mãsu hasãra.  ۚ   ۖ 
'Alam Ya'tihim Naba'u Al-Ladhīna Min Qablihim Qawmi Nūĥin Wa `Ādin Wa Thamūda Wa Qawmi 'Ibrāhīma Wa 'Aşĥābi Madyana Wa Al-Mu'utafikāti  ۚ  'Atat/hum Rusuluhum Bil-Bayyināti  ۖ  Famā Kāna Al-Lahu Liyažlimahum Wa Lakin Kānū 'Anfusahum Yažlimūna 009-070 Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice? Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta.  ۚ   ۖ 
Wa Al-Mu'uminūna Wa Al-Mu'uminātu Ba`đuhum 'Awliyā'u  ۚ  Ba`đin Ya'murūna Bil-Ma`rūfi Wa Yanhawna `Ani Al-Munkari Wa Yuqīmūna Aş-Şalāata Wa Yu'utūna Az-Zakāata Wa Yuţī`ūna Al-Laha  ۚ  Wa Rasūlahu 'Ūlā'ika Sayarĥamuhumu  ۗ  Al-Lahu 'Inna Al-Laha `Azīzun Ĥakīmun 009-071 Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da alhẽri kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.  ۚ  ~  ۚ   ۗ 
Wa`ada Al-Lahu Al-Mu'uminīna Wa Al-Mu'umināti Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā Wa Masākina Ţayyibatan Fī Jannāti `Adnin  ۚ  Wa Riđwānun Mina Al-Lahi 'Akbaru  ۚ  Dhālika Huwa Al-Fawzu Al-`Ažīmu 009-072 Kuma Allah Yã yi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mãtã da gidãjen Aljanna ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu, da wurãren zama mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.  ۚ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu Jāhidi Al-Kuffāra Wa Al-Munāfiqīna Wa Aghluž `Alayhim  ۚ  Wa Ma'wāhum Jahannamu  ۖ  Wa Bi'sa Al-Maşīru 009-073 Ya kai Annabi! Ka yãƙi kãfirai da munãfukai kuma ka tsaurara a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce. Tir da ta zama makõmar!  ۚ   ۖ 
Yaĥlifūna Bil-Lahi Mā Qālū Wa Laqad Qālū Kalimata Al-Kufri Wa Kafarū Ba`da 'Islāmihim Wa Hammū Bimā Lam Yanālū  ۚ  Wa Mā Naqamū 'Illā 'An 'Aghnāhumu Al-Lahu Wa Rasūluhu Min Fađlihi  ۚ  Fa'in Yatūbū Yaku Khayrāan Lahum  ۖ  Wa 'In Yatawallaw Yu`adhdhibhumu Al-Lahu `Adhābāan 'Alīmāan Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati  ۚ  Wa Mā Lahum Al-'Arđi Min Wa Līyin Wa Lā Naşīrin 009-074 Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare su,kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa.  ۚ   ۚ   ۖ   ۚ 
Wa Minhum Man `Āhada Al-Laha La'in 'Ātānā Min Fađlihi Lanaşşaddaqanna Wa Lanakūnanna Mina Aş-Şāliĥīna 009-075 Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, "Lalle ne idan ya kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã kasancẽwa, daga sãlihai."
Falammā 'Ātāhum Min Fađlihi Bakhilū Bihi Wa Tawallaw Wa Hum Mu`rūna 009-076 To, a lõkacin da Ya bã su daga falalarSa, sai suka yi rõwa da shi, kuma suka jũya bãya sunã mãsu bijirẽwa,
Fa'a`qabahum Nifāqāan Fī Qulūbihim 'Ilá Yawmi Yalqawnahu Bimā 'Akhlafū Al-Laha Mā Wa`adūhu Wa Bimā Kānū Yakdhibūna 009-077 Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatansu har zuwa ga Rãnar da suke haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda abin da suka kasance sunã yi na ƙarya.
'Alam Ya`lamū 'Anna Al-Laha Ya`lamu Sirrahum Wa Najwāhum Wa 'Anna Al-Laha `Allāmu Al-Ghuyūbi 009-078 Shin, ba su sani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã sanin asĩrinsuda gãnawarsu, kuma lalle Allah ne Masanin abũbuwan fake?
Al-Ladhīna Yalmizūna Al-Muţţawwi`īna Mina Al-Mu'uminīna Fī Aş-Şadaqāti Wa Al-Ladhīna Lā Yajidūna 'Illā Juhdahum Fayaskharūna Minhum  ۙ  Sakhira Al-Lahu Minhum Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun 009-079 Waɗanda suke aibanta mãsu yin alhẽri daga mummunaia cikin dũkiyõyin sadaka, da waɗanda ba su sãmu fãce iyãkar ƙõƙarinsu, sai sanã yi musu izgili. Allah Yanã yin izgili gare su. Kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.  ۙ 
Astaghfir Lahum 'Aw Lā Tastaghfir Lahum 'In Tastaghfir Lahum Sab`īna Marratan Falan Yaghfira Al-Lahu Lahum  ۚ  Dhālika Bi'annahum Kafarū Bil-Lahi Wa Rasūlihi Wa  ۗ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Al-Fāsiqīna 009-080 Kõ kã nẽma musu gãfara ko ba ka nẽma musu ba, idan ka nẽma musu gãfara sau saba'in, to, Allah bã zai gãfarta musu ba. Sabõda sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.  ۚ   ۗ 
Fariĥa Al-Mukhallafūna Bimaq`adihim Khilāfa Rasūli Al-Lahi Wa Karihū 'An Yujāhidū Bi'amwālihim Wa 'Anfusihim Fī Sabīli Al-Lahi Wa Qālū Lā Tanfirū Fī Al-Ĥarri  ۗ  Qul Nāru Jahannama 'Ashaddu Ĥarrāan  ۚ  Law Kānū Yafqahūna 009-081 Waɗanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bãyan Manzon Allah, kuma suka ƙi su yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce: "Kada ku fita zuwa yãƙi a cikin zãfi."Ka ce: "Wutar Jahannama ce mafi tsanlnin zãfi." Dã sun kasance sunã fahimta!  ۗ   ۚ 
Falyađĥakū Qalīlāan Wa Līabkū Kathīrāan Jazā'an Bimā Kānū Yaksibūna 009-082 Sabõda haka su yi dãriya kaɗan, kuma su yi kũkada yawa a kan sãkamako ga abin da suka kasance sunã tsirfatãwa.
Fa'in Raja`aka Al-Lahu 'Ilá Ţā'ifatin Minhum Fāsta'dhanūka Lilkhurūji Faqul Lan Takhrujū Ma`iya 'Abadāan Wa Lan Tuqātilū Ma`iya `Adūwāan  ۖ  'Innakum Rađītum Bil-Qu`ūdi 'Awwala Marratinq`udū Ma`a Al-Khālifīna 009-083 To, idan Allah Ya mayar da kai zuwa ga wata ƙungiyã daga gare su sa'an nan suka nẽme ka izni dõmin su fita, to, ka ce: "Bã zã ku fita tãre da nĩ ba har abada,kuma bã zã ku yi yãƙi tãre da nĩ ba a kan wani maƙiyi. Lalle ne kũ, kun yarda da zama a farkon lõkaci, sai ku zauna tãre da mãtã mãsu zaman gida."  ۖ 
Wa Lā Tuşalli `Alá 'Aĥadin Minhum Māta 'Abadāan Wa Lā Taqum `Alá Qabrihi  ۖ  'Innahum Kafarū Bil-Lahi Wa Rasūlihi Wa Mātū Wa Hum Fāsiqūna 009-084 Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai. ~  ۖ 
Wa Lā Tu`jibka 'Amwāluhum Wa 'Awlāduhum  ۚ  'Innamā Yurīdu Al-Lahu 'An Yu`adhdhibahum Bihā Fī Ad-Dunyā Wa Tazhaqa 'Anfusuhum Wa Hum Kāfirūna 009-085 Kuma kada dũkiyõyinsu da ɗiyansu su bã ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba da su a cikin dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.  ۚ 
Wa 'Idhā 'Unzilat Sūratun 'An 'Āminū Bil-Lahi Wa Jāhidū Ma`a Rasūlihi Asta'dhanaka 'Ū Aţ-Ţawli Minhum Wa Qālū Dharnā Nakun Ma`a Al-Qā`idīna 009-086 Kuma idan aka saukar da wata sũra cẽwa; Ku yi ĩmãni da Allah kuma ku yi jihãdi tãre da ManzionSa. Sai mawadãta daga gare su su nẽmi izninka, kuma su ce: Ka bar mu mu kasance tãre da mazauna.
Rađū Bi'an Yakūnū Ma`a Al-Khawālifi Wa Ţubi`a `Alá Qulūbihim Fahum Lā Yafqahūna 009-087 Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama (a cikin gidãje). Kuma aka rufe a kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta.
Lakini Ar-Rasūlu Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Ma`ahu Jāhadū Bi'amwālihim Wa 'Anfusihim  ۚ  Wa 'Ūlā'ika Lahumu Al-Khayrātu  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna 009-088 Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sun yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu. Kuma waɗannan sunã da ayyukan alhẽri, kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.  ۚ   ۖ 
'A`adda Al-Lahu Lahum Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā  ۚ  Dhālika Al-Fawzu Al-`Ažīmu 009-089 Allah yã yi musu tattalin gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu. Wancan ne babban rabo mai girma.  ۚ 
Wa Jā'a Al-Mu`adhdhirūna Mina Al-'A`rābi Liyu'udhana Lahum Wa Qa`ada Al-Ladhīna Kadhabū Al-Laha Wa Rasūlahu  ۚ  Sayuşību Al-Ladhīna Kafarū Minhum `Adhābun 'Alīmun 009-090 Kuma mãsu uzuri daga ƙauyãwa zuka zo dõmin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azãba mai raɗaɗi zã ta sãmi waɗanda suka kãfirta daga gare su.  ۚ 
Laysa `Alá Ađ-Đu`afā'i Wa Lā `Alá Al-Marđá Wa Lā `Alá Al-Ladhīna Lā Yajidūna Mā Yunfiqūna Ĥarajun 'Idhā Naşaĥū Lillahi Wa Rasūlihi  ۚ  Mā `Alá Al-Muĥsinīna Min Sabīlin Wa  ۚ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 009-091 Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi.  ۚ   ۚ 
Wa Lā `Alá Al-Ladhīna 'Idhā Mā 'Atawka Litaĥmilahum Qulta Lā 'Ajidu Mā 'Aĥmilukum `Alayhi Tawallaw Wa 'A`yunuhum Tafīđu Mina Ad-Dam`i Ĥazanāan 'Allā Yajidū Mā Yunfiqūna 009-092 Kuma bãbu (laifi) a kan waɗanda idan sun je maka dõmin ka ɗauke su ka ce: "Bã ni da abin da nake ɗaukar ku a kansa," suka jũya alhãli kuwa idãnunsu sunã zubar da hawãye dõmin baƙin ciki cẽwa ba su sãmi abin da suke ciyarwa ba.
'Innamā As-Sabīlu `Alá Al-Ladhīna Yasta'dhinūnaka Wa Hum 'Aghniyā'u  ۚ  Rađū Bi'an Yakūnū Ma`a Al-Khawālifi Wa Ţaba`a Al-Lahu `Alá Qulūbihim Fahum Lā Ya`lamūna 009-093 Abin sani kawai, laifi Yanã a kan waɗanda suke nẽman izininka alhãli kuwa sũ mawadãta ne.Sun yarda su kasance tãre da mãtã mamaya (gidãje), kuma Allah Yã danne a kan zukãtansu, dõmin haka sũ, bã su gãnẽwa.  ۚ 
Ya`tadhirūna 'Ilaykum 'Idhā Raja`tum 'Ilayhim  ۚ  Qul Lā Ta`tadhirū Lan Nu'umina Lakum Qad Nabba'anā Al-Lahu Min 'Akhrikum  ۚ  Wa Sayará Al-Lahu `Amalakum Wa Rasūluhu Thumma Turaddūna 'Ilá `Ālimi Al-Ghaybi Wa Ash-Shahādati Fayunabbi'ukum Bimā Kuntum Ta`malūna 009-094 Sunã kãwo uzurinsu zuwa gare ku idan kun kõma zuwa gare su Ka ce: "Kada ku kãwo wani uzuri, bã zã mu amince muku ba. Haƙĩƙa, Allah Yã bã mu lãbãri daga lãbãrunku, Allah zai ga aikinku kuma ManzonSa (zai gani). Sa'an nan kuma a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibi da bayyane, sai Ya bã ku lãbarin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."  ۚ   ۚ 
Sayaĥlifūna Bil-Lahi Lakum 'Idhā Anqalabtum 'Ilayhim Litu`riđū `Anhum  ۖ  Fa'a`riđū `Anhum  ۖ  'Innahum Rijsun  ۖ  Wa Ma'wāhum Jahannamu Jazā'an Bimā Kānū Yaksibūna 009-095 Zã su yi rantsuwa da Allah a gare ku idan kun jũya zuwa gare su, dõmin ku kau da kai daga gare su. To, ku kau da kai daga gare su don kõ sũ ƙarantã ne, kuma Jahannama ce matattararsu bisa ga sãkamakon abin da suka kasance sunã tsirfatãwa.  ۖ   ۖ   ۖ 
Yaĥlifūna Lakum Litarđaw `Anhum  ۖ  Fa'in Tarđaw `Anhum Fa'inna Al-Laha Lā Yarđá `Ani Al-Qawmi Al-Fāsiqīna 009-096 Sunã rantsuwã gare ku dõmin ku yarda da su. To, idan kun yarda da su, to, lalle ne Allah bã shi yarda da mutãne fãsiƙai.  ۖ 
Al-'A`rābu 'Ashaddu Kufrāan Wa Nifāqāan Wa 'Ajdaru 'Allā Ya`lamū Ĥudūda Mā 'Anzala Al-Lahu `Alá Rasūlihi Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 009-097 ¡auyãwã ne mafi tsananin kãfirci da munãfinci, kuma sũne mafi kamanta ga, rashin sanin haddõjin abin da Allah Ya saukar a kan ManzonSa. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.  ۗ 
Wa Mina Al-'A`rābi Man Yattakhidhu Mā Yunfiqu Maghramāan Wa Yatarabbaşu Bikumu Ad-Dawā'ira  ۚ  `Alayhim Dā'iratu As-Saw'i Wa  ۗ  Allāhu Samī`un `Alīmun 009-098 Kuma daga ƙauyãwã akwai waɗanda suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tãra ce, kuma sunã saurãron aukuwar masĩfa a gare ku, aukuwar mummunar masĩfa ta tabbata a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.  ۚ   ۗ 
Wa Mina Al-'A`rābi Man Yu'uminu Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa Yattakhidhu Mā Yunfiqu Qurubātin `Inda Al-Lahi Wa Şalawāti Ar-Rasūli  ۚ  'Alā 'Innahā Qurbatun Lahum  ۚ  Sayudkhiluhumu Al-Lahu Fī Raĥmatihi  ۗ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 009-099 Kuma daga ƙauyãwã akawi waɗanda suke yin ĩmanida Allah da Rãnar Lãhira, kuma sunã riƙon abin da suke ciyarwa (tamkar) waɗansu ibãdõdin nẽman kusanta ne a wurin Allah da addu'õ'in ManzonSa. To, lalle ne ita (ciyarwar nan) ibãdar nẽman kusanta ce a gare su. Allah zai shigar da su a cikin RahamarSa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.  ۚ   ۚ  ~  ۗ 
Wa As-Sābiqūna Al-'Awwalūna Mina Al-Muhājirīna Wa Al-'Anşāri Wa Al-Ladhīna Attaba`ūhum Bi'iĥsānin Rađiya Al-Lahu `Anhum Wa Rađū `Anhu Wa 'A`adda Lahum Jannātin Tajrī Taĥtahā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā  ۚ  'Abadāan Dhālika Al-Fawzu Al-`Ažīmu 009-100 Kuma mãsu tsẽrẽwa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; ¡õramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.  ۚ 
Wa Mimman Ĥawlakum Mina Al-'A`rābi Munāfiqūna  ۖ  Wa Min 'Ahli Al-Madīnati  ۖ  Maradū `Alá An-Nifāqi Lā Ta`lamuhum  ۖ  Naĥnu Na`lamuhum  ۚ  Sanu`adhdhibuhum Marratayni Thumma Yuraddūna 'Ilá `Adhābin `Ažīmin 009-101 Kuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai, haka kuma daga mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su. zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma.  ۖ   ۖ   ۖ   ۚ 
Wa 'Ākharūna A`tarafū Bidhunūbihim Khalaţū `Amalāan Şāliĥāan Wa 'Ākhara Sayyi'āan `Asá Al-Lahu 'An Yatūba `Alayhim  ۚ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 009-102 Kuma da waɗansu, sun yi furuci da laifinsu, sun haɗa aiki na ƙwarai da wani mummuna. Akwai tsammãnin Allah Ya karɓi tũba a kansu. Lallai Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.  ۚ 
Khudh Min 'Amwālihim Şadaqatan Tuţahhiruhum Wa Tuzakkīhim Bihā Wa Şalli `Alayhim  ۖ  'Inna Şalātaka Sakanun Lahum Wa  ۗ  Allāhu Samī`un `Alīmun 009-103 Ka karɓi sadaka daga dũkiyõyinsu kana tsarkake su, kuma kana tabbatar da kirkinsu da ita. Kuma ka yi musu addu'a. Lallai addu'õ'inKa natsuwã ne a gare su. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.  ۖ   ۗ 
'Alam Ya`lamū 'Anna Al-Laha Huwa Yaqbalu At-Tawbata `An `Ibādihi Wa Ya'khudhu Aş-Şadaqāti Wa 'Anna Al-Laha Huwa At-Tawwābu Ar-Raĥīmu 009-104 Shin, ba su sani ba cẽwa lallai Allah, ne Yake karɓar tũbã daga bãyinSa, kuma Yanã karɓar sadakõkinsu, kuma lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai?
Wa Quli A`malū Fasayará Al-Lahu `Amalakum Wa Rasūluhu Wa Al-Mu'uminūna  ۖ  Wa Saturaddūna 'Ilá `Ālimi Al-Ghaybi Wa Ash-Shahādati Fayunabbi'ukum Bimā Kuntum Ta`malūna 009-105 Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da ManzonSa da Muminai kuma zã a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa."  ۖ 
Wa 'Ākharūna Murjawna Li'amri Al-Lahi 'Immā Yu`adhdhibuhum Wa 'Immā Yatūbu `Alayhim Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 009-106 Kuma da waɗansu waɗanda aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu.Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.  ۗ 
Wa Al-Ladhīna Attakhadhū Masjidāan Đirārāan Wa Kufrāan Wa Tafrīqāan Bayna Al-Mu'uminīna Wa 'Irşādāan Liman Ĥāraba Al-Laha Wa Rasūlahu Min  ۚ  Qablu Wa Layaĥlifunna 'In 'Aradnā 'Illā  ۖ  Al-Ĥusná Wa Allāhu Yash/hadu 'Innahum Lakādhibūna 009-107 Kuma waɗanda suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa,su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.  ۚ   ۖ 
Lā Taqum Fīhi 'Abadāan  ۚ  Lamasjidun 'Ussisa `Alá At-Taqwá Min 'Awwali Yawmin 'Aĥaqqu 'An Taqūma Fīhi  ۚ  Fīhi Rijālun Yuĥibbūna 'An Yataţahharū Wa  ۚ  Allāhu Yuĥibbu Al-Muţţahhirīna 009-108 Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka. Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman tsarkakuwa. ~  ۚ   ۚ   ۚ 
'Afaman 'Assasa Bunyānahu `Alá Taqwá Mina Al-Lahi Wa Riđwānin Khayrun 'Am Man 'Assasa Bunyānahu `Alá Shafā Jurufin Hārin Fānhāra Bihi Fī Nāri Jahannama Wa  ۗ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna 009-109 Shin, wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne mafi alhẽri kõ kuwa wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan gãɓar rãmi mai tusgãwa? Sai ya rũsa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.  ۗ 
Lā Yazālu Bunyānuhumu Al-Ladhī Banaw Rībatan Fī Qulūbihim 'Illā 'An Taqaţţa`a Qulūbuhum Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 009-110 Gininsu, wanda suka gina, bã zai gushe ba Yanã abin shakka a cikin zukãtansu fãce idan zukãtansu sun yanyanke. Kuma Allah ne Masani, Mai Hikima.  ۗ 
'Inna Al-Laha Ashtará Mina Al-Mu'uminīna 'Anfusahum Wa 'Amwālahum Bi'anna Lahumu Al-Jannata  ۚ  Yuqātilūna Fī Sabīli Al-Lahi Fayaqtulūna Wa Yuqtalūna  ۖ  Wa`dāan `Alayhi Ĥaqqāan At-Tawrāati Wa Al-'Injīli Wa Al-Qur'āni  ۚ  Wa Man 'Awfá Bi`ahdihi Mina Al-Lahi  ۚ  Fāstabshirū Bibay`ikumu Al-Ladhī Bāya`tum Bihi  ۚ  Wa Dhalika Huwa Al-Fawzu Al-`Ažīmu 009-111 Lalle ne, Allah Ya saya daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ su. (Allah Yã yi)wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma.  ۚ   ۖ   ۚ   ۚ   ۚ 
At-Tā'ibūna Al-`Ābidūna Al-Ĥāmidūna As-Sā'iĥūna Ar-Rāki`ūna As-Sājidūna Al-'Āmirūna Bil-Ma`rūfi Wa An-Nāhūna `Ani Al-Munkari Wa Al-Ĥāfižūna Liĥudūdi Al-Lahi  ۗ  Wa Bashshiri Al-Mu'uminīna 009-112 Mãsu tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai.  ۗ 
Mā Kāna Lilnnabīyi Wa Al-Ladhīna 'Āmanū 'An Yastaghfirū Lilmushrikīna Wa Law Kānū 'Ūlī Qurbá Min Ba`di Mā Tabayyana Lahum 'Annahum 'Aşĥābu Al-Jaĥīmi 009-113 Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne.
Wa Mā Kāna Astighfāru 'Ibrāhīma Li'abīhi 'Illā `An Maw`idatin Wa`adahā 'Īyāhu Falammā Tabayyana Lahu 'Annahu `Adūwun Lillahi Tabarra'a Minhu  ۚ  'Inna 'Ibrāhīma La'awwāhun Ĥalīmun 009-114 Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi (Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri. ~ ~  ۚ 
Wa Mā Kāna Al-Lahu Liyuđilla Qawmāan Ba`da 'Idh Hadāhum Ĥattá Yubayyina Lahum Mā Yattaqūna  ۚ  'Inna Al-Laha Bikulli Shay'in `Alīmun 009-115 Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutãne a bãyan Yã shiryar da su ba, sai Ya bayyanã musu abin da zã su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kõme, Masani ne.  ۚ 
'Inna Al-Laha Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Yuĥyī Wa Yumītu  ۚ  Wa Mā Lakum Min Dūni Al-Lahi Min Wa Līyin Wa Lā Naşīrin 009-116 Lalle ne Allah Yanã da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah.  ۖ   ۚ 
Laqad Tāba Al-Lahu `Alá An-Nabīyi Wa Al-Muhājirīna Wa Al-'Anşāri Al-Ladhīna Attaba`ūhu Fī Sā`ati Al-`Usrati Min Ba`di Mā Kāda Yazīghu Qulūbu Farīqin Minhum Thumma Tāba `Alayhim  ۚ  'Innahu Bihim Ra'ūfun Raĥīmun 009-117 Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan ( Allah) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su.  ۚ 
Wa `Alá Ath-Thalāthati Al-Ladhīna Khullifū Ĥattá 'Idhā Đāqat `Alayhimu Al-'Arđu Bimā Raĥubat Wa Đāqat `Alayhim 'Anfusuhum Wa Žannū 'An Lā Malja'a Mina Al-Lahi 'Illā 'Ilayhi Thumma Tāba `Alayhim Liyatūbū  ۚ  'Inna Al-Laha Huwa At-Tawwābu Ar-Raĥīmu 009-118 Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Attaqū Al-Laha Wa Kūnū Ma`a Aş-Şādiqīna 009-119 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku kasance tãre da mãsu gaskiya.
Mā Kāna Li'hli Al-Madīnati Wa Man Ĥawlahum Mina Al-'A`rābi 'An Yatakhallafū `An Rasūli Al-Lahi Wa Lā Yarghabū Bi'anfusihim `An Nafsihi  ۚ  Dhālika Bi'annahum Lā Yuşībuhum Žama'un Wa Lā Naşabun Wa Lā Makhmaşatun Fī Sabīli Al-Lahi Wa Lā Yaţa'ūna Mawţi'āan Yaghīžu Al-Kuffāra Wa Lā Yanālūna Min `Adūwin Naylāan 'Illā Kutiba Lahum Bihi `Amalun Şāliĥun  ۚ  'Inna Al-Laha Lā Yuđī`u 'Ajra Al-Muĥsinīna 009-120 Bã ya kasancẽwa ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.  ۚ   ۚ 
Wa Lā Yunfiqūna Nafaqatan Şaghīratan Wa Lā Kabīratan Wa Lā Yaqţa`ūna Wa Adīāan 'Illā Kutiba Lahum Liyajziyahumu Al-Lahu 'Aĥsana Mā Kānū Ya`malūna 009-121 Kuma bã su ciyar da wata ciyarwa, ƙarama kõ babba, kuma bã su kẽta wani rafi sai an rubutã musu, dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyãwon abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Wa Mā Kāna Al-Mu'uminūna Liyanfirū Kāffatan  ۚ  Falawlā Nafara Min Kulli Firqatin Minhum Ţā'ifatun Liyatafaqqahū Fī Ad-Dīni Wa Liyundhirū Qawmahum 'Idhā Raja`ū 'Ilayhim La`allahum Yaĥdharūna 009-122 Kuma bã ya kasancẽwã ga muminai su fita zuwa yãƙi gabã ɗaya. Sabõda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita (zuwa nẽman ilimi ba) dõmin su nẽmi ilimi ga fahimtar addĩni kuma dõmin su yi gargaɗi ga mutãnensu idan sun kõma zuwa gare su, tsammãninsu, sunã yin sauna?  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Qātilū Al-Ladhīna Yalūnakum Mina Al-Kuffāri Wa Līajidū Fīkum Ghilžatan  ۚ  Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Ma`a Al-Muttaqīna 009-123 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yãƙi waɗanda suke kusantar ku daga kãfirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.  ۚ 
Wa 'Idhā Mā 'Unzilat Sūratun Faminhum Man Yaqūlu 'Ayyukum Zādat/hu Hadhihi 'Īmānāan  ۚ  Fa'ammā Al-Ladhīna 'Āmanū Fazādat/hum 'Īmānāan Wa Hum Yastabshirūna 009-124 Kuma idan aka saukar da wata sũra, to, daga gare su akwai waɗanda suke cẽwa: "Wãne a cikinku wannan sũra ta ƙãra masa ĩmãni?" To amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sũ, sunã yin bushãra (da ita). ~  ۚ 
Wa 'Ammā Al-Ladhīna Fī Qulūbihim Marađun Fazādat/hum Rijsāan 'Ilá Rijsihim Wa Mātū Wa Hum Kāfirūna 009-125 Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai.
'Awalā Yarawna 'Annahum Yuftanūna Fī Kulli `Āmin Marratan 'Aw Marratayni Thumma Lā Yatūbūna Wa Lā Hum Yadhdhakkarūna 009-126 Shin, bã su ganin cẽwa anã fitinar su a cikin kõwace shẽkara: Sau ɗaya kõ kuwa sau biyu, sa'an nan kuma bã su tũba, kuma ba su zama sunã tunãni ba?
Wa 'Idhā Mā 'Unzilat Sūratun Nažara Ba`đuhum 'Ilá Ba`đin Hal Yarākum Min 'Aĥadin Thumma Anşarafū  ۚ  Şarafa Al-Lahu Qulūbahum Bi'annahum Qawmun Lā Yafqahūna 009-127 "Kuma idan haƙĩƙa, aka saukar da wata sũra, sai sãshensu ya yi dũbi zuwa ga wani sãshe, (su ce): "Shin, wani mutum yanã ganin ku?" Sa'an nan kuma sai su jũya. Allah Ya jũyar da zukãtansu,dõmin, haƙĩƙa sũ mutãne ne, bã su fahimta.  ۚ 
Laqad Jā'akum Rasūlun Min 'Anfusikum `Azīzun `Alayhi Mā `Anittum Ĥarīşun `Alaykum Bil-Mu'uminīna Ra'ūfun Raĥīmun 009-128 Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
Fa'in Tawallaw Faqul Ĥasbī Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  `Alayhi Tawakkaltu  ۖ  Wa Huwa Rabbu Al-`Arshi Al-`Ažīmi 009-129 To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma'ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma. ~  ۖ   ۖ 
Next Sūrah