8) Sūrat Al-'Anfāl

Printed format

8)

Yas'alūnaka `Ani Al-'Anfāl Quli Al-'Anfāli Lillahi Wa Ar-Rasūli Fa Attaqū Al-Laha Wa 'Aşliĥū Dhāta Baynikum Wa 'Aţī`ū Al-Laha Wa Rasūlahu 'In Kuntum Mu'uminīna 008-001 Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."  ۖ   ۖ  ~  ۖ 
'Innamā Al-Mu'uminūna Al-Ladhīna 'Idhā Dhukira Al-Lahu Wajilat Qulūbuhum Wa 'Idhā Tuliyat `Alayhim 'Āyātuhu Zādat/hum 'Īmānāan Wa `Alá Rabbihim Yatawakkalūna 008-002 Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.
Al-Ladhīna Yuqīmūna Aş-Şalāata Wa Mimmā Razaqnāhum Yunfiqūna 008-003 Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.
'Ūlā'ika Humu Al-Mu'uminūna Ĥaqqāan  ۚ  Lahum Darajātun `Inda Rabbihim Wa Maghfiratun Wa Rizqun Karīmun 008-004 Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci.  ۚ 
Kamā 'Akhrajaka Rabbuka Min Baytika Bil-Ĥaqqi Wa 'Inna Farīqāan Mina Al-Mu'uminīna Lakārihūna 008-005 Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma.
Yujādilūnaka Fī Al-Ĥaqqi Ba`damā Tabayyana Ka'annamā Yusāqūna 'Ilá Al-Mawti Wa Hum Yanžurūna 008-006 Sunã jãyayya da kai a cikin (sha'anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo.
Wa 'Idh Ya`idukumu Al-Lahu 'Iĥdá Aţā'ifatayni 'Annahā Lakum Wa Tawaddūna 'Anna Ghayra Dhāti Ash-Shawkati Takūnu Lakum Wa Yurīdu Al-Lahu 'An Yuĥiqqa Al-Ĥaqqa Bikalimātihi Wa Yaqţa`a Dābira Al-Kāfirīna 008-007 Kuma a lõkacin da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai;
Liyuĥiqqa Al-Ĥaqqa Wa Yubţila Al-Bāţila Wa Law Kariha Al-Mujrimūna 008-008 Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi.
'Idh Tastaghīthūna Rabbakum Fāstajāba Lakum 'Annī Mumiddukum Bi'alfin Mina Al-Malā'ikati Murdifīna 008-009 A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku tairnako, sai Ya karɓa muku cẽwa: "Lalle ne Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã'iku, jẽre."
Wa Mā Ja`alahu Al-Lahu 'Illā Bushrá Wa Litaţma'inna Bihi Qulūbukum  ۚ  Wa Mā An-Naşru 'Illā Min `Indi Al-Lahi  ۚ  'Inna Al-Laha `Azīzun Ĥakīmun 008-010 Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.  ۚ   ۚ 
'Idh Yughashshīkumu An-Nu`āsa 'Amanatan Minhu Wa Yunazzilu `Alaykum Mina As-Samā'i Mā'an Liyuţahhirakum Bihi Wa Yudh/hiba `Ankum Rijza Ash-Shayţāni Wa Liyarbiţa `Alá Qulūbikum Wa Yuthabbita Bihi Al-'Aqdāma 008-011 A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.
'Idh Yūĥī Rabbuka 'Ilá Al-Malā'ikati 'Annī Ma`akum Fathabbitū Al-Ladhīna 'Āmanū  ۚ  Sa'ulqī Fī Qulūbi Al-Ladhīna Kafarū Ar-Ru`ba Fāđribū Fawqa Al-'A`nāqi Wa Ađribū Minhum Kulla Banānin 008-012 A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu .  ۚ 
Dhālika Bi'annahum Shāqqū Al-Laha Wa Rasūlahu  ۚ  Wa Man Yushāqiqi Al-Laha Wa Rasūlahu Fa'inna Al-Laha Shadīdu Al-`Iqābi 008-013 Wancan ne, dõmin lalle ne sũ, sunã sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.  ۚ 
Dhālikum Fadhūqūhu Wa 'Anna Lilkāfirīna `Adhāba An-Nāri 008-014 Wancan ne: "Ku ɗanɗane shi, kuma lalle ne akwai azãbar wuta ga kãfirai."
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Laqītumu Al-Ladhīna Kafarū Zaĥfāan Falā Tuwallūhumu Al-'Adbāra 008-015 Yã kũ wacɗanda suka yiĩmãni! Idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta ga yãƙi, to, kada ku jũya musu bãyayyakinku.
Wa Man Yuwallihim Yawma'idhin Duburahu 'Illā Mutaĥarrifāan Liqitālin 'Aw Mutaĥayyizāan 'Ilá Fi'atin Faqad Bā'a Bighađabin Mina Al-Lahi Wa Ma'wāhu Jahannamu  ۖ  Wa Bi'sa Al-Maşīru 008-016 Kuma duka wanda ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita! ~  ۖ 
Falam Taqtulūhum Wa Lakinna Al-Laha Qatalahum  ۚ  Wa Mā Ramayta 'Idh Ramayta Wa Lakinna Al-Laha Ramá  ۚ  Wa Liyubliya Al-Mu'uminīna Minhu Balā'an Ĥasanāan  ۚ  'Inna Al-Laha Samī`un `Alīmun 008-017 To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa; kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.  ۚ   ۚ   ۚ 
Dhālikum Wa 'Anna Al-Laha Mūhinu Kaydi Al-Kāfirīna 008-018 Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne.
'In Tastaftiĥū Faqad Jā'akumu Al-Fatĥu  ۖ  Wa 'In Tantahū Fahuwa Khayrun Lakum  ۖ  Wa 'In Ta`ūdū Na`ud Wa Lan Tughniya `Ankum Fi'atukum Shay'āan Wa Law Kathurat Wa 'Anna Al-Laha Ma`a Al-Mu'uminīna 008-019 Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah Yanã tãre da mũminai!  ۖ   ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Aţī`ū Al-Laha Wa Rasūlahu Wa Lā Tawallaw `Anhu Wa 'Antum Tasma`ūna 008-020 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya daga barinSa, alhãli kunã ji.
Wa Lā Takūnū Kālladhīna Qālū Sami`nā Wa Hum Lā Yasma`ūna 008-021 Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: "Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji."
'Inna Sharra Ad-Dawābbi `Inda Al-Lahi Aş-Şummu Al-Bukmu Al-Ladhīna Lā Ya`qilūna 008-022 Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã, su yin hankali.
Wa Law `Alima Al-Lahu Fīhim Khayrāan La'asma`ahum  ۖ  Wa Law 'Asma`ahum Latawallaw Wa Hum Mu`rūna 008-023 Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa,dã sun jũya , alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa.  ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Astajībū Lillahi Wa Lilrrasūli 'Idhā Da`ākum Limā Yuĥyīkum  ۖ  Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Yaĥūlu Bayna Al-Mar'i Wa Qalbihi Wa 'Annahu 'Ilayhi Tuĥsharūna 008-024 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku.  ۖ  ~
Wa Attaqū Fitnatan Lā Tuşībanna Al-Ladhīna Žalamū Minkum Khāşşatan  ۖ  Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Shadīdu Al-`Iqābi 008-025 Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.  ۖ 
Wa Adhkurū 'Idh 'Antum Qalīlun Mustađ`afūna Fī Al-'Arđi Takhāfūna 'An Yatakhaţţafakumu An-Nāsu Fa'āwākum Wa 'Ayyadakum Binaşrihi Wa Razaqakum Mina Aţ-Ţayyibāti La`allakum Tashkurūna 008-026 Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Takhūnū Al-Laha Wa Ar-Rasūla Wa Takhūnū 'Amānātikum Wa 'Antum Ta`lamūna 008-027 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane.
Wa A`lamū 'Annamā 'Amwālukum Wa 'Awlādukum Fitnatun Wa 'Anna Al-Laha `Indahu 'Ajrun `Ažīmun 008-028 Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijãra mai girma. ~
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'In Tattaqū Al-Laha Yaj`al Lakum Furqānāan Wa Yukaffir `Ankum Sayyi'ātikum Wa Yaghfir Lakum Wa  ۗ  Allāhu Dhū Al-Fađli Al-`Ažīmi 008-029 Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma.  ۗ 
Wa 'Idh Yamkuru Bika Al-Ladhīna Kafarū Liyuthbitūka 'Aw Yaqtulūka 'Aw Yukhrijūka  ۚ  Wa Yamkurūna Wa Yamkuru Al-Lahu Wa  ۖ  Allāhu Khayru Al-Mākirīna 008-030 Kuma a lõkacin da waɗanda suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.  ۚ   ۖ 
Wa 'Idhā Tutlá `Alayhim 'Āyātunā Qālū Qad Sami`nā Law Nashā'u Laqulnā Mithla Hādhā  ۙ  'In Hādhā 'Illā 'Asāţīru Al-'Awwalīna 008-031 Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: "Lalle ne mun ji dã muna so, haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen farko."  ۙ 
Wa 'Idh Qālū Al-Lahumma 'In Kāna Hādhā Huwa Al-Ĥaqqa Min `Indika Fa'amţir `Alaynā Ĥijāratan Mina As-Samā'i 'Aw A'tinā Bi`adhābin 'Alīmin 008-032 A lõkacin da suka ce: "Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata azãba, mai raɗaɗi."
Wa Mā Kāna Al-Lahu Liyu`adhdhibahum Wa 'Anta Fīhim  ۚ  Wa Mā Kāna Al-Lahu Mu`adhdhibahum Wa Hum Yastaghfirūna 008-033 Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu, kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri.  ۚ 
Wa Mā Lahum 'Allā Yu`adhdhibahumu Al-Lahu Wa Hum Yaşuddūna `Ani Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Wa Mā Kānū 'Awliyā'ahu  ۚ  'In 'Awliyā'uuhu 'Illā Al-Muttaqūna Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna 008-034 Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba. ~  ۚ  ~
Wa Mā Kāna Şalātuhum `Inda Al-Bayti 'Illā Mukā'an Wa Taşdiyatan  ۚ  Fadhūqū Al-`Adhāba Bimā Kuntum Takfurūna 008-035 Kuma sallarsu a wurin ãkin ba ta kasance ba fãce shẽwa da yãyã; sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Yunfiqūna 'Amwālahum Liyaşuddū `An Sabīli Al-Lahi  ۚ  Fasayunfiqūnahā Thumma Takūnu `Alayhim Ĥasratan Thumma Yughlabūna Wa  ۗ  Al-Ladhīna Kafarū 'Ilá Jahannama Yuĥsharūna 008-036 Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama ake tãra su;  ۚ   ۗ 
Liyamīza Al-Lahu Al-Khabītha Mina Aţ-Ţayyibi Wa Yaj`ala Al-Khabītha Ba`đahu `Alá Ba`đin Fayarkumahu Jamī`āan Fayaj`alahu Fī Jahannama  ۚ  'Ūlā'ika Humu Al-Khāsirūna 008-037 Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra.  ۚ 
Qul Lilladhīna Kafarū 'In Yantahū Yughfar Lahum Mā Qad Salafa Wa 'In Ya`ūdū Faqad Mađat Sunnatu Al-'Awwalīna 008-038 Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe.
Wa Qātilūhum Ĥattá Lā Takūna Fitnatun Wa Yakūna Ad-Dīnu Kulluhu Lillahi  ۚ  Fa'ini Antahaw Fa'inna Al-Laha Bimā Ya`malūna Başīrun 008-039 Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.  ۚ 
Wa 'In Tawallaw Fā`lamū 'Anna Al-Laha Mawlākum  ۚ  Ni`ma Al-Mawlá Wa Ni`ma An-Naşīru 008-040 Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ.  ۚ 
Wa A`lamū 'Annamā Ghanimtum Min Shay'in Fa'anna Lillahi Khumusahu Wa Lilrrasūli Wa Lidhī Al-Qurbá Wa Al-Yatāmá Wa Al-Masākīni Wa Abni As-Sabīli 'In Kuntum 'Āmantum Bil-Lahi Wa Mā 'Anzalnā `Alá `Abdinā Yawma Al-Furqāni Yawma At-Taqá Al-Jam`āni Wa  ۗ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 008-041 Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.  ۗ 
'Idh 'Antum Bil-`Udwati Ad-Dunyā Wa Hum Bil-`Udwati Al-Quşwá Wa Ar-Rakbu 'Asfala Minkum  ۚ  Wa Law Tawā`adttumkhtalaftum Al-Mī`ādi  ۙ  Wa Lakin Liyaqđiya Al-Lahu 'Amrāan Kāna Maf`ūlāan Liyahlika Man Halaka `An Bayyinatin Wa Yaĥyá Man Ĥayya `An Bayyinatin  ۗ  Wa 'Inna Al-Laha Lasamī`un `Alīmun 008-042 A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa'adi, dã kun sãɓa ga wa'adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa. Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani.  ۚ   ۙ   ۗ 
'Idh Yurīkahumu Al-Lahu Fī Manāmika Qalīlāan  ۖ  Wa Law 'Arākahum Kathīrāan Lafashiltum Wa Latanāza`tum Al-'Amri Wa Lakinna Al-Laha Sallama  ۗ  'Innahu `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri 008-043 A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake a cikin ƙirãza.  ۖ   ۗ 
Wa 'Idh Yurīkumūhum 'Idhi At-Taqaytum Fī 'A`yunikum Qalīlāan Wa Yuqallilukum Fī 'A`yunihim Liyaqđiya Al-Lahu 'Amrāan Kāna Maf`ūlāan  ۗ  Wa 'Ilá Al-Lahi Turja`u Al-'Umūru 008-044 Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani al'amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'umurra.  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Laqītum Fi'atanthbutū Wa Adhkurū Al-Laha Kathīrāan La`allakum Tufliĥūna 008-045 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.
Wa 'Aţī`ū Al-Laha Wa Rasūlahu Wa Lā Tanāza`ū Fatafshalū Wa Tadh/haba Rīĥukum  ۖ  Wa Aşbirū  ۚ  'Inna Al-Laha Ma`a Aş-Şābirīna 008-046 Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana kuma iskarku ta tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.  ۖ   ۚ 
Wa Lā Takūnū Kālladhīna Kharajū Min Diyārihim Baţarāan Wa Ri'ā'a An-Nāsi Wa Yaşuddūna `An Sabīli Al-Lahi Wa  ۚ  Allāhu Bimā Ya`malūna Muĥīţun 008-047 Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu , sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.  ۚ 
Wa 'Idh Zayyana Lahumu Ash-Shayţānu 'A`mālahum Wa Qāla Lā Ghāliba Lakumu Al-Yawma Mina An-Nāsi Wa 'Innī Jārun Lakum  ۖ  Falammā Tarā'ati Al-Fi'atāni Nakaşa `Alá `Aqibayhi Wa Qāla 'Innī Barī'un Minkum 'Innī 'Ará Mā Lā Tarawna 'Inniyi 'Akhāfu Al-Laha Wa  ۚ  Allāhu Shadīdu Al-`Iqābi 008-048 Kuma a lõkacin da Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne."  ۖ   ۚ 
'Idh Yaqūlu Al-Munāfiqūna Wa Al-Ladhīna Fī Qulūbihim Marađun Gharra Hā'uulā' Dīnuhum  ۗ  Wa Man Yatawakkal `Alá Al-Lahi Fa'inna Al-Laha `Azīzun Ĥakīmun 008-049 A lõkacin da munãfukai da waɗanda suke akwai cũtã a cikin zukãtansu, suke cẽwa: "Addĩnin waɗannan yã rũɗe su" Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.  ۗ 
Wa Law Tará 'Idh Yatawaffá Al-Ladhīna Kafarū  ۙ  Al-Malā'ikatu Yađribūna Wujūhahum Wa 'Adbārahum Wa Dhūqū `Adhāba Al-Ĥarīqi 008-050 Kuma dã kã gani, a lõkacin da Malã'iku suke karɓar rãyukan waɗanda suka kãfirta, sunã dukar fuskõkinsu da ɗuwãwunsu, kuma suna cẽwa: "Ku ɗanɗani azãbar Gõbara."  ۙ 
Dhālika Bimā Qaddamat 'Aydīkum Wa 'Anna Al-Laha Laysa Bižallāmin Lil`abīdi 008-051 "Wancan sabõda abin da hannãyenku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne, Allah bai zama Mai zãlunci ba ga, bãyinSa."
Kada'bi 'Āli Fir`awna Wa  ۙ  Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  Kafarū Bi'āyāti Al-Lahi Fa'akhadhahumu Al-Lahu Bidhunūbihim  ۗ  'Inna Al-Laha Qawīyun Shadīdu Al-`Iqābi 008-052 "Kamar al'ãdar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke gabãninsu, sun kãfirta da ãyõyin Allah, sai Allah Ya kãma su da zunubansu. Lalle Allah ne Mai ƙarfi, Mai tsananin uƙũba.  ۙ   ۚ   ۗ 
Dhālika Bi'anna Al-Laha Lam Yaku Mughayyirāan Ni`matan 'An`amahā `Alá Qawmin Ĥattá Yughayyirū Mā Bi'anfusihim  ۙ  Wa 'Anna Al-Laha Samī`un `Alīmun 008-053 "Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya ni'imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu, kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ,Masani."  ۙ 
Kada'bi 'Āli Fir`awna Wa  ۙ  Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  Kadhdhabū Bi'āyāti Rabbihim Fa'ahlaknāhum Bidhunūbihim Wa 'Aghraqnā 'Āla Fir`awna  ۚ  Wa Kullun Kānū Žālimīna 008-054 Kamar al'adar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu zãlunci.  ۙ   ۚ   ۚ 
'Inna Sharra Ad-Dawābbi `Inda Al-Lahi Al-Ladhīna Kafarū Fahum Lā Yu'uminūna 008-055 Lalle mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne waɗanda suka kãfirta, sa'an nan bã zã su yi ĩmãni ba.
Al-Ladhīna `Āhadta Minhum Thumma Yanquđūna `Ahdahum Fī Kulli Marratin Wa Hum Lā Yattaqūna 008-056 Waɗanda ka yi ƙullin alkawari da su, daga gare su, sa'an nan kuma sunã warwarewar alkawarinsu a kõwane lõkaci kuma sũ, bã su yin taƙawa.
Fa'immā Tathqafannahum Al-Ĥarbi Fasharrid Bihim Man Khalfahum La`allahum Yadhdhakkarūna 008-057 To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre waɗanda suke a bãyansu, game da su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa.
Wa 'Immā Takhāfanna Min Qawmin Khiyānatannbidh 'Ilayhim `Alá Sawā'in  ۚ  'Inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Al-Khā'inīna 008-058 Kuma in ka ji tsõron wata yaudara daga wasu mutãne, to, ka jẽfar da alkawarin, zuwa gare su, a kan daidaita: Lalle ne Allah, bã Ya son mayaudara.  ۚ 
Wa Lā Yaĥsabanna Al-Ladhīna Kafarū Sabaqū  ۚ  'Innahum Lā Yu`jizūna 008-059 Kuma waɗanda suka kãfirta kada su yi zaton sun tsẽre: Lalle ne sũ, bã zã su gãgara ba.  ۚ 
Wa 'A`iddū LahumAstaţa`tum Min Qūwatin Wa Min Ribāţi Al-Khayli Turhibūna Bihi `Adūwa Al-Lahi Wa `Adūwakum Wa 'Ākharīna Min Dūnihim Lā Ta`lamūnahumu Al-Lahu Ya`lamuhum  ۚ  Wa Mā Tunfiqū Min Shay'in Fī Sabīli Al-Lahi Yuwaffa 'Ilaykum Wa 'Antum Lā Tužlamūna 008-060 Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi, kuma da ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba a zãluntar ku.  ۚ 
Wa 'In Janaĥū Lilssalmi Fājnaĥ Lahā Wa Tawakkal `Alá Al-Lahi  ۚ  'Innahu Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu 008-061 Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani.  ۚ 
Wa 'In Yurīdū 'An Yakhda`ūka Fa'inna Ĥasbaka Al-Lahu  ۚ  Huwa Al-Ladhī 'Ayyadaka Binaşrihi Wa Bil-Mu'uminīna 008-062 Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to, lalle ma'ishinka Allah ne, Shĩ ne wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai.  ۚ 
Wa 'Allafa Bayna Qulūbihim  ۚ  Law 'Anfaqta Mā Fī Al-'Arđi Jamī`āan Mā 'Allafta Bayna Qulūbihim Wa Lakinna Al-Laha 'Allafa Baynahum  ۚ  'Innahu `Azīzun Ĥakīmun 008-063 Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.  ۚ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu Ĥasbuka Al-Lahu Wa Mani Attaba`aka Mina Al-Mu'uminīna 008-064 Ya kai Annabi! Ma'ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka daga mũminai.
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu Ĥarriđi Al-Mu'uminīna `Alá Al-Qitāli  ۚ  'In Yakun Minkum `Ishrūna Şābirūna Yaghlibū Miā'atayni  ۚ  Wa 'In Yakun Minkum Miā'atun Yaghlibū 'Alfāan Mina Al-Ladhīna Kafarū Bi'annahum Qawmun Lā Yafqahūna 008-065 Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne bã su fahimta.  ۚ   ۚ 
Al-'Āna Khaffafa Al-Lahu `Ankum Wa `Alima 'Anna Fīkum Đa`fāan  ۚ  Fa'in Yakun Minkum Miā'atun Şābiratun Yaghlibū Miā'atayni  ۚ  Wa 'In Yakun Minkum 'Alfun Yaghlibū 'Alfayni Bi'idhni Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu Ma`a Aş-Şābirīna 008-066 A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.  ۚ   ۚ   ۗ 
Mā Kāna Linabīyin 'An Yakūna Lahu 'Asrá Ĥattá Yuthkhina Fī Al-'Arđi  ۚ  Turīdūna `Arađa Ad-Dunyā Wa Allāhu Yurīdu Al-'Ākhirata Wa  ۗ  Allāhu `Azīzun Ĥakīmun 008-067 Bã ya kasancewa ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima. ~  ۚ   ۗ 
Lawlā Kitābun Mina Al-Lahi Sabaqa Lamassakum Fīmā 'Akhadhtum `Adhābun `Ažīmun 008-068 Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta , dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma.
Fakulū Mimmā Ghanimtum Ĥalālāan Ţayyibāan  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha  ۚ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 008-069 Sabõda haka, ku ci daga abin da kuka sãmu ganĩma, Yanã halal mai kyau. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.  ۚ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu Qul Liman Fī 'Aydīkum Mina Al-'Asrá 'In Ya`lami Al-Lahu Fī Qulūbikum Khayrāan Yu'utikum Khayrāan Mimmā 'Ukhidha Minkum Wa Yaghfir Lakum Wa  ۗ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 008-070 Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."  ۗ 
Wa 'In Yurīdū Khiyānataka Faqad Khānū Al-Laha Min Qablu Fa'amkana Minhum Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 008-071 Kuma idan sun yi nufin yaudararka, to, haƙĩƙa, sun yaudari Allahdaga gabãni sai Ya bãyar da dãmã daga gare su: Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.  ۗ 
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Hājarū Wa Jāhadū Bi'amwālihim Wa 'Anfusihim Fī Sabīli Al-Lahi Wa Al-Ladhīna 'Āwaw Wa Naşarū 'Ūlā'ika Ba`đuhum 'Awliyā'u Ba`đin Wa  ۚ  Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Lam Yuhājarū Mā Lakum Min Walāyatihim Min Shay'in Ĥattá Yuhājirū  ۚ  Wa 'Ini Astanşarūkum Ad-Dīni Fa`alaykumu An-Naşru 'Illā `Alá Qawmin Baynakum Wa Baynahumthāqun Wa  ۗ  Allāhu Bimā Ta`malūna Başīrun 008-072 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.  ۚ   ۚ   ۗ 
Wa Al-Ladhīna Kafarū Ba`đuhum 'Awliyā'u  ۚ  Ba`đin 'Illā Taf`alūhu Takun Fitnatun Al-'Arđi Wa Fasādun Kabīrun 008-073 Kuma waɗanda suka kãfirta sãshensu ne waliyyan sãshe, idan ba ku aikata shi ba, wata fitina zã ta kasance a cikin ƙasa, da fasãdi babba.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Hājarū Wa Jāhadū Fī Sabīli Al-Lahi Wa Al-Ladhīna 'Āwaw Wa Naşarū 'Ūlā'ika Humu Al-Mu'uminūna  ۚ  Ĥaqqāan Lahum Maghfiratun Wa Rizqun Karīmun 008-074 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Min Ba`du Wa Hājarū Wa Jāhadū Ma`akum Fa'ūlā'ika  ۚ  Minkum Wa 'Ū Al-'Arĥāmi Ba`đuhum 'Awlá Biba`đin Fī Kitābi  ۗ  Al-Lahi 'Inna Al-Laha Bikulli Shay'in `Alīmun 008-075 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abũta zumunta, sãshensu ne waliyyan sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani.  ۚ   ۗ 
Next Sūrah