7) Sūrat Al-'A`rāf

Printed format

7)

'Alif-Lām-Mīm-Şād 007-001 A. L̃. M̃. Ṣ̃. ---
Kitābun 'Unzila 'Ilayka Falā Yakun Fī Şadrika Ĥarajun Minhu Litundhira Bihi Wa Dhikrá Lilmu'uminīna 007-002 Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai.
Attabi`ū Mā 'Unzila 'Ilaykum Min Rabbikum Wa Lā Tattabi`ū Min Dūnihi 'Awliyā'a  ۗ  Qalīlāan Mā Tadhakkarūna 007-003 Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa. ~  ۗ 
Wa Kam Min Qaryatin 'Ahlaknāhā Fajā'ahā Ba'sunā Bayātāan 'Aw Hum Qā'ilūna 007-004 Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jẽ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla.
Famā Kāna Da`wāhum 'Idh Jā'ahum Ba'sunā 'Illā 'An Qālū 'Innā Kunnā Žālimīna 007-005 Sa'an nan bãbu abin da yake da'awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci,"
Falanas'alanna Al-Ladhīna 'Ursila 'Ilayhim Wa Lanas'alanna Al-Mursalīna 007-006 Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin.
Falanaquşşanna `Alayhim Bi`ilmin  ۖ  Wa Mā Kunnā Ghā'ibīna 007-007 Sa'an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba.  ۖ 
Wa Al-Waznu Yawma'idhin  ۚ  Al-Ĥaqqu Faman Thaqulat Mawāzīnuhu Fa'ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna 007-008 Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.  ۚ 
Wa Man Khaffat Mawāzīnuhu Fa'ūlā'ika Al-Ladhīna Khasirū 'Anfusahum Bimā Kānū Bi'āyātinā Yažlimūna 007-009 Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci.
Wa Laqad Makkannākum Al-'Arđi Wa Ja`alnā Lakum Fīhā Ma`āyisha  ۗ  Qalīlāan Mā Tashkurūna 007-010 Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.  ۗ 
Wa Laqad Khalaqnākum Thumma Şawwarnākum Thumma Qulnā Lilmalā'ikati Asjudū Li'dama Fasajadū 'Illā 'Iblīsa Lam Yakun Mina As-Sājidīna 007-011 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan kumaMun ce wa malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba.
Qāla Mā Mana`aka 'Allā Tasjuda 'Idh 'Amartuka  ۖ  Qāla 'Anā Khayrun Minhu Khalaqtanī Min Nārin Wa Khalaqtahu Min Ţīnin 007-012 Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka."  ۖ 
Qāla Fāhbiţ Minhā Famā Yakūnu Laka 'An Tatakabbara Fīhā Fākhruj 'Innaka Mina Aş-Şāghirīna 007-013 Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; dõmin bã, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci."
Qāla 'Anžirnī 'Ilá Yawmi Yub`athūna 007-014 Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su."
Qāla 'Innaka Mina Al-Munžarīna 007-015 Ya ce: "Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri."
Qāla Fabimā 'Aghwaytanī La'aq`udanna Lahum Şirāţaka Al-Mustaqīma 007-016 Ya ce: "To inã rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, inã zaune musu tafarkinKa madaidaici."
Thumma La'ātiyannahum Min Bayni 'Aydīhim Wa Min Khalfihim Wa `An 'Aymānihim Wa `An Shamā'ilihim  ۖ  Wa Lā Tajidu 'Aktharahum Shākirīna 007-017 "Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su, kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba."  ۖ 
Qāla Akhruj Minhā Madh'ūmāan Madĥūrāan  ۖ  Laman Tabi`aka Minhum La'amla'anna Jahannama Minkum 'Ajma`īna 007-018 Ya ce: "Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, zã Ni cika jahannama daga gare ku, gabã ɗaya."  ۖ 
Wa Yā'ādamu Askun 'Anta Wa Zawjuka Al-Jannata Fakulā Min Ĥaythu Shi'tumā Wa Lā Taqrabā Hadhihi Ash-Shajarata Fatakūnā Mina Až-Žālimīna 007-019 "Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai."
Fawaswasa Lahumā Ash-Shayţānu Liyubdiya Lahumā Mā Wūriya `Anhumā Min Saw'ātihimā Wa Qāla Mā Nahākumā Rabbukumā `An Hadhihi Ash-Shajarati 'Illā 'An Takūnā Malakayni 'Aw Takūnā Mina Al-Khālidīna 007-020 Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama."
Wa Qāsamahumā 'Innī Lakumā Lamina An-Nāşiĥīna 007-021 Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne.
Fadallāhumā Bighurūrin  ۚ  Falammā Dhāqā Ash-Shajarata Badat Lahumā Saw'ātuhumā Wa Ţafiqā Yakhşifāni `Alayhimā Min Waraqi Al-Jannati  ۖ  Wa Nādāhumā Rabbuhumā 'Alam 'Anhakumā `An Tilkumā Ash-Shajarati Wa 'Aqul Lakumā 'Inna Ash-Shayţāna Lakumā `Adūwun Mubīnun 007-022 Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?"  ۚ   ۖ 
Qālā Rabbanā Žalamnā 'Anfusanā Wa 'In Lam Taghfir Lanā Wa Tarĥamnā Lanakūnanna Mina Al-Khāsirīna 007-023 Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra."
Qāla Ahbiţū Ba`đukum Liba`đin `Adūwun  ۖ  Wa Lakum Al-'Arđi Mustaqarrun Wa Matā`un 'Ilá Ĥīnin 007-024 Ya ce: "Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi."  ۖ 
Qāla Fīhā Taĥyawna Wa Fīhā Tamūtūna Wa Minhā Tukhrajūna 007-025 Ya ce: "A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku."
Yā Banī 'Ādama Qad 'Anzalnā `Alaykum Libāsāan Yuwārī Saw''ātikum Wa Rīshāan  ۖ  Wa Libāsu At-TaqDhālika Khayrun  ۚ  Dhālika Min 'Āyā Ti Al-Lahi La`allahum Yadhdhakkarūna 007-026 Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!  ۖ   ۚ 
Yā Banī 'Ādama Lā Yaftinannakumu Ash-Shayţānu Kamā 'Akhraja 'Abawaykum Mina Al-Jannati Yanzi`u `Anhumā Libāsahumā Liyuriyahumā Saw''ātihimā  ۗ  'Innahu Yarākum Huwa Wa Qabīluhu Min Ĥaythu Lā Tarawnahum  ۗ  'Innā Ja`alnā Ash-Shayā Ţīna 'Awliyā 'A Lilladhīna Lā Yu'uminūna 007-027 Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku,shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni.  ۗ   ۗ 
Wa 'Idhā Fa`alū Fāĥishatan Qālū Wajadnā `Alayhā 'Ābā'anā Wa Allāhu 'Amaranā Bihā  ۗ  Qul 'Inna Al-Laha Lā Ya'muru Bil-Faĥshā'i  ۖ  'Ataqūlūna `Alá Al-Lahi Mā Lā Ta`lamūna 007-028 Kuma idan suka aikata alfãsha su ce: "Mun sãmi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?"  ۗ   ۖ 
Qul 'Amara Rabbī Bil-Qisţi  ۖ  Wa 'Aqīmū Wujūhakum `Inda Kulli Masjidin Wa Ad`ūhu Mukhlişīna Lahu Ad-Dīna  ۚ  Kamā Bada'akum Ta`ūdūna 007-029 Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa."  ۖ   ۚ 
Farīqāan Hadá Wa Farīqāan Ĥaqqa `Alayhimu Ađ-Đalālatu  ۗ  'Innahumu Attakhadhū Ash-Shayāţīna 'Awliyā'a Min Dūni Al-Lahi Wa Yaĥsabūna 'Annahum Muhtadūna 007-030 Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne.  ۗ 
Yā Banī 'Ādama Khudhū Zīnatakum `Inda Kulli Masjidin Wa Kulū Wa Ashrabū Wa Lā Tusrifū  ۚ  'Innahu Lā Yuĥibbu Al-Musrifīna 007-031 Yã ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bã Ya son mãsu ɓarna.  ۚ 
Qul Man Ĥarrama Zīnata Al-Lahi Allatī 'Akhraja Li`ibādihi Wa Aţ-Ţayyibāti Mina Ar-Rizqi  ۚ  Qul Hiya Lilladhīna 'Āmanū Fī Al-Ĥayāati Ad-DunKhālişatan Yawma Al-Qiyāmati  ۗ  Kadhālika Nufaşşilu Al-'Āyāti Liqawmin Ya`lamūna 007-032 Ka ce: "Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani.  ۚ   ۗ 
Qul 'Innamā Ĥarrama Rabbiya Al-Fawāĥisha Mā Žahara Minhā Wa Mā Baţana Wa Al-'Ithma Wa Al-Baghya Bighayri Al-Ĥaqqi Wa 'An Tushrikū Bil-Lahi Mā Lam Yunazzil Bihi Sulţānāan Wa 'An Taqūlū `Alá Al-Lahi Mā Lā Ta`lamūna 007-033 Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah."
Wa Likulli 'Ummatin 'Ajalun  ۖ  Fa'idhā Jā'a 'Ajaluhum Lā Yasta'khirūna Sā`atan  ۖ  Wa Lā Yastaqdimūna 007-034 Kuma ga kõwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bã zã a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bã zã su gabãce shi ba.  ۖ   ۖ 
Yā Banī 'Ādama 'Immā Ya'tiyannakum Rusulun Minkum Yaquşşūna `Alaykum 'Āyā  ۙ  Tī Famani Attaqá Wa 'Aşlaĥa Falā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 007-035 Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki.  ۙ 
Wa Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā Wa Astakbarū `Anhā 'Ūlā'ika 'Aşĥābu  ۖ  An-Nāri Hum Fīhā Khālidūna 007-036 Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne.  ۖ 
Faman 'Ažlamu Mimmani Aftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan 'Aw Kadhdhaba Bi'āyātihi  ۚ  'Ūlā'ika Yanāluhum Naşībuhum Mina Al-Kitābi  ۖ  Ĥattá 'Idhā Jā'at/hum Rusulunā Yatawaffawnahum Qālū 'Ayna Mā Kuntum Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi  ۖ  Qālū Đallū `Annā Wa Shahidū `Alá 'Anfusihim 'Annahum Kānū Kāfirīna 007-037 To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: "Ĩnã abin da kuka kasance kunã kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kãfirai." ~  ۚ   ۖ   ۖ 
Qāla Adkhulū Fī 'Umamin Qad Khalat Min Qablikum Mina Al-Jinni Wa Al-'Insi Fī An-Nāri  ۖ  Kullamā Dakhalat 'Ummatun La`anat 'Ukhtahā  ۖ  Ĥattá 'Idhā Addārakū Fīhā Jamī`āan Qālat 'Ukhrāhum Li'wlāhum Rabbanā Hā'uulā' 'Ađallūnā Fa'ātihim `Adhābāan Đi`fāan Mina An-Nāri  ۖ  Qāla Likullin Đi`fun Wa Lakin Lā Ta`lamūna 007-038 Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba."  ۖ   ۖ   ۖ 
Wa Qālat 'Ūlāhum Li'khrāhum Famā Kāna Lakum `Alaynā Min Fađlin Fadhūqū Al-`Adhāba Bimā Kuntum Taksibūna 007-039 Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tãrãwa!"
'Inna Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā Wa Astakbarū `Anhā Lā Tufattaĥu Lahum 'Abwābu As-Samā'i Wa Lā Yadkhulūna Al-Jannata Ĥattá Yalija Al-Jamalu Fī Sammi Al-Khiyāţi  ۚ  Wa Kadhalika Naj Al-Mujrimīna 007-040 Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi.  ۚ 
Lahum Min Jahannama Mihādun Wa Min Fawqihim Ghawāshin  ۚ  Wa Kadhalika Naj Až-Žālimīna 007-041 Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lā Nukallifu Nafsāan 'Illā Wus`ahā 'Ūlā'ika 'Aşĥābu  ۖ  Al-Jannati Hum Fīhā Khālidūna 007-042 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne.  ۖ 
Wa Naza`nā Mā Fī Şudūrihim Min Ghillin Tajrī Min Taĥtihimu Al-'Anhāru  ۖ  Wa Qālū Al-Ĥamdu Lillahi Al-Ladhī Hadānā Lihadhā Wa Mā Kunnā Linahtadiya Lawlā 'An Hadānā Al-Lahu  ۖ  Laqad Jā'at Rusulu Rabbinā Bil-Ĥaqqi  ۖ  Wa Nūdū 'An Tilkumu Al-Jannatu 'Ūrithtumūhā Bimā Kuntum Ta`malūna 007-043 Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa."  ۖ   ۖ   ۖ 
Wa Nādá 'Aşĥābu Al-Jannati 'Aşĥāba An-Nāri 'An Qad Wajadnā Mā Wa`adanā Rabbunā Ĥaqqāan Fahal Wajadtum Mā Wa`ada Rabbukum Ĥaqqāan  ۖ  Qālū Na`am  ۚ  Fa'adhdhana Mu'uadhdhinun Baynahum 'An La`natu Al-Lahi `Alá Až-Žālimīna 007-044 Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."  ۖ   ۚ 
Al-Ladhīna Yaşuddūna `An Sabīli Al-Lahi Wa Yabghūnahā `Iwajāan Wa Hum Bil-'Ākhirati Kāfirūna 007-045 "Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne."
Wa Baynahumā Ĥijābun  ۚ  Wa `Alá Al-'A`rāfi Rijālun Ya`rifūna Kullāan Bisīmāhum  ۚ  Wa Nādaw 'Aşĥāba Al-Jannati 'An Salāmun `Alaykum  ۚ  Lam Yadkhulūhā Wa Hum Yaţma`ūna 007-046 Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki, kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni.  ۚ   ۚ   ۚ 
Wa 'Idhā Şurifat 'Abşāruhum Tilqā'a 'Aşĥābi An-Nāri Qālū Rabbanā Lā Taj`alnā Ma`a Al-Qawmi Až-Žālimīna 007-047 Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne azzãlumai."
Wa Nādá 'Aşĥābu Al-'A`rāfi Rijālāan Ya`rifūnahum Bisīmāhum Qālū Mā 'Aghná `Ankum Jam`ukum Wa Mā Kuntum Tastakbirūna 007-048 Kuma abõkan A'araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: "Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku?"
'Ahā'uulā' Al-Ladhīna 'Aqsamtum Lā Yanāluhumu Al-Lahu Biraĥmatin  ۚ  Adkhulū Al-Jannata Lā Khawfun `Alaykum Wa Lā 'Antum Taĥzanūna 007-049 "Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro akanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba."  ۚ 
Wa Nādá 'Aşĥābu An-Nāri 'Aşĥāba Al-Jannati 'An 'Afīđū `Alaynā Mina Al-Mā'i 'Aw Mimmā Razaqakumu Al-Lahu  ۚ  Qālū 'Inna Al-Laha Ĥarramahumā `Alá Al-Kāfirīna 007-050 Kuma 'yan wuta suka kirãyi 'yan Aljanna cẽwa: "Ku zubo a kaumu daga ruwa kõ kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan kãfirai."  ۚ 
Al-Ladhīna Attakhadhū Dīnahum Lahwan Wa La`ibāan Wa Gharrat/humu Al-Ĥayāatu Ad-Dunyā  ۚ  Fālyawma Nansāhum Kamā Nasū Liqā'a Yawmihimdhā Wa Mā Kānū Bi'āyātinā Yajĥadūna 007-051 "Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu.  ۚ 
Wa Laqad Ji'nāhum Bikitābin Faşşalnāhu `Alá `Ilmin Hudáan Wa Raĥmatan Liqawmin Yu'uminūna 007-052 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littãfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yanã shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmani.
Hal Yanžurūna 'Illā Ta'wīlahu  ۚ  Yawma Ya'tī Ta'wīluhu Yaqūlu Al-Ladhīna Nasūhu Min Qablu Qad Jā'at Rusulu Rabbinā Bil-Ĥaqqi Fahal Lanā Min Shufa`ā'a Fayashfa`ū Lanā 'Aw Nuraddu Fana`mala Ghayra Al-Ladhī Kunnā Na`malu  ۚ  Qad Khasirū 'Anfusahum Wa Đalla `Anhum Mā Kānū Yaftarūna 007-053 Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabãni, sunã cẽwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kõ kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa?" Lalle ne sun yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu.  ۚ   ۚ 
'Inna Rabbakumu Al-Lahu Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Fī Sittati 'Ayyāmin Thumma Astawá `Alá Al-`Arshi Yughshī Al-Layla An-Nahāra Yaţlubuhu Ĥathīthāan Wa Ash-Shamsa Wa Al-Qamara Wa An-Nujūma Musakhkharātin Bi'amrihi  ۗ  'Alā Lahu Al-Khalqu Wa Al-'Amru  ۗ  Tabāraka Al-Lahu Rabbu Al-`Ālamīna 007-054 Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana! ~  ۗ   ۗ 
Ad`ū Rabbakum Tađarru`āan Wa Khufyatan  ۚ  'Innahu Lā Yuĥibbu Al-Mu`tadīna 007-055 Ku kirãyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓõye: lalle ne Shĩ, bã Yã son mãsuwuce iyãka.  ۚ 
Wa Lā Tufsidū Fī Al-'Arđi Ba`da 'Işlāĥihā Wa Ad`ūhu Khawfāan Wa Ţama`āan  ۚ  'Inna Raĥmata Al-Lahi Qarībun Mina Al-Muĥsinīna 007-056 Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa.  ۚ 
Wa Huwa Al-Ladhī Yursilu Ar-Riyāĥa Bushrāan Bayna Yaday Raĥmatihi  ۖ  Ĥattá 'Idhā 'Aqallat Saĥābāan Thiqālāan Suqnāhu Libaladin Mayyitin Fa'anzalnā Bihi Al-Mā'a Fa'akhrajnā Bihi Min Kulli Ath-Thamarāti  ۚ  Kadhālika Nukhriju Al-Mawtá La`allakum Tadhakkarūna 007-057 Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizãgizai mãsu nauyi, sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni.  ۖ   ۚ 
Wa Al-Baladu Aţ-Ţayyibu Yakhruju Nabātuhu Bi'idhni  ۖ  Rabbihi Wa Al-Ladhī Khabutha Lā Yakhruju 'Illā  ۚ  Nakidāan Kadhālika Nuşarrifu Al-'Āyāti Liqawmin Yashkurūna 007-058 Kuma gari mai kyau, tsirinsa yanã fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, (tsirinsa) bã ya fita, fãce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ãyõyi dõmin mutãne waɗanda suke gõdẽwa.  ۖ   ۚ 
Laqad 'Arsalnā Nūĥāan 'Ilá Qawmihi Faqāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu 'Innī 'Akhāfu `Alaykum `Adhāba Yawmin `Ažīmin 007-059 Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnẽnsa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta waAllah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yimuku tsõron azãbar wani Yini mai girma." ~
Qāla Al-Mala'u Min Qawmihi 'Innā Lanarāka Fī Đalālin Mubīnin 007-060 Mashawarta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya." ~
Qāla Yā Qawmi Laysa Bī Đalālatun Wa Lakinnī Rasūlun Min Rabbi Al-`Ālamīna 007-061 Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu !"
'Uballighukum Risālāti Rabbī Wa 'Anşaĥu Lakum Wa 'A`lamu Mina Al-Lahi Mā Lā Ta`lamūna 007-062 "Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina; kuma inã yi muku nasĩha, kuma inã sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba.
'Awa`ajibtum 'An Jā'akum Dhikrun Min Rabbikum `Alá Rajulin Minkum Liyundhirakum Wa Litattaqū Wa La`allakum Turĥamūna 007-063 "Shin, kunã mãmãkin cẽwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma tsammãninku anã jin ƙanku?"
Fakadhdhabūhu Fa'anjaynāhu Wa Al-Ladhīna Ma`ahu Fī Al-Fulki Wa 'Aghraq Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā  ۚ  'Innahum Kānū Qawmāan `Amīna 007-064 Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu.  ۚ 
Wa 'Ilá `Ādin 'Akhāhum Hūdāan  ۗ  Qāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu  ۚ  'Afalā Tattaqūna 007-065 Kuma zuwa ga Ãdãwa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da wani abin bautã wa, waninSa. Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?"  ۗ  ~  ۚ 
Qāla Al-Mala'u Al-Ladhīna Kafarū Min Qawmihi 'Innā Lanarāka Fī Safāhatin Wa 'Innā Lanažunnuka Mina Al-Kādhibīna 007-066 Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga maƙaryata." ~
Qāla Yā Qawmi Laysa Bī Safāhatun Wa Lakinnī Rasūlun Min Rabbi Al-`Ālamīna 007-067 Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu!"
'Uballighukum Risālāti Rabbī Wa 'Anā Lakum Nāşiĥun 'Amīnun 007-068 Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce.
'Awa`ajibtum 'An Jā'akum Dhikrun Min Rabbikum `Alá Rajulin Minkum Liyundhirakum  ۚ  Wa Adhkurū 'Idh Ja`alakum Khulafā'a Min Ba`di Qawmi Nūĥin Wa Zādakum Al-Khalqi Basţatan  ۖ  Fādhkurū 'Ālā'a Al-Lahi La`allakum Tufliĥūna 007-069 "Shin, kuma kun yi mãmãki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tunã a lõkacin da Ya sanyã ku mãsu mayẽwa daga bãyan mutãnen Nũhu, kuma Ya ƙãra muku zãti a cikin halitta. Sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah; tsammãninku kunã cin nasara."  ۚ   ۖ 
Qālū 'Aji'tanā Lina`buda Al-Laha Waĥdahu Wa Nadhara Mā Kāna Ya`budu 'Ābā'uunā  ۖ  Fa'tinā Bimā Ta`idunā 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna 007-070 Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa? To, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi idan kã kasance daga mãsu gaskiya."  ۖ 
Qāla Qad Waqa`a `Alaykum Min Rabbikum Rijsun Wa Ghađabun  ۖ  'Atujādilūnanī Fī 'Asmā'in Sammaytumūhā 'Antum Wa 'Ābā'uukum Mā Nazzala Al-Lahu Bihā Min Sulţānin  ۚ  Fāntažirū 'Innī Ma`akum Mina Al-Muntažirīna 007-071 Ya ce: "Haƙĩƙa azãba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kunã jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tãre da ku mai jira ne."  ۖ   ۚ 
Fa'anjaynāhu Wa Al-Ladhīna Ma`ahu Biraĥmatin Minnā Wa Qaţa`nā Dābira Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā  ۖ  Wa Mā Kānū Mu'uminīna 007-072 To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tãre da shi sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma ba su kasance mũminaiba.  ۖ 
Wa 'Ilá Thamūda 'Akhāhum Şāliĥāan  ۗ  Qāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu  ۖ  Qad Jā'atkum Bayyinatun Min Rabbikum  ۖ  Hadhihi Nāqatu Al-Lahi Lakum 'Āyatan  ۖ  Fadharūhā Ta'kul Fī 'Arđi Al-Lahi  ۖ  Wa Lā Tamassūhā Bisū'in Faya'khudhakum `Adhābun 'Alīmun 007-073 Kuma zuwa ga Samũdãwa ɗan'uwansu, Sãlihu, ya ce: "Yã mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba mai raɗaɗi ta kãmã ku."  ۗ   ۖ   ۖ   ۖ   ۖ 
Wa Adhkurū 'Idh Ja`alakum Khulafā'a Min Ba`di `Ādin Wa Bawwa'akum Al-'Arđi Tattakhidhūna Min Suhūlihā Quşūrāan Wa Tanĥitūna Al-Jibāla Buyūtāan  ۖ  Fādhkurū 'Ālā'a Al-Lahi Wa Lā Ta`thaw Fī Al-'Arđi Mufsidīna 007-074 "Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi."  ۖ 
Qāla Al-Mala'u Al-Ladhīna Astakbarū Min Qawmihi Lilladhīna Astuđ`ifū Liman 'Āmana Minhum 'Ata`lamūna 'Anna Şāliĥāan Mursalun Min Rabbihi  ۚ  Qālū 'Innā Bimā 'Ursila Bihi Mu'uminūna 007-075 Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar, ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: "Shin, kunã sanin cẽwaSãlihu manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, mãsu ĩmãni ne."  ۚ 
Qāla Al-Ladhīna Astakbarū 'Innā Bial-Ladhī 'Āmantum Bihi Kāfirūna 007-076 Waɗanda suka yi girman kai suka ce: "Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmãni da shi kãfirai ne."
Fa`aqarū An-Nāqata Wa `Ataw `An 'Amri Rabbihim Wa Qālū Yā Şāliĥu A'tinā Bimā Ta`idunā 'In Kunta Mina Al-Mursalīna 007-077 Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: "Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kã kasance daga manzanni !"
Fa'akhadhat/humu Ar-Rajfatu Fa'aşbaĥū Fī Dārihimthimīna 007-078 Sai tsãwa ta kãmã su, sabõda haka suka wãyi gari a cikin gidansu guggurfãne!
Fatawallá `Anhum Wa Qāla Yā Qawmi Laqad 'Ablaghtukum Risālata Rabbī Wa Naşaĥtu Lakum Wa Lakin Lā Tuĥibbūna An-Nāşiĥīna 007-079 Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu nasĩha!"
Wa Lūţāan 'Idh Qāla Liqawmihi 'Ata'tūna Al-Fāĥishata Mā Sabaqakum Bihā Min 'Aĥadin Mina Al-`Ālamīna 007-080 Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: "Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu?" ~
'Innakum Lata'tūna Ar-Rijāla Shahwatan Min Dūni An-Nisā'  ۚ  Bal 'Antum Qawmun Musrifūna 007-081 "Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata."  ۚ 
Wa Mā Kāna Jawāba Qawmihi 'Illā 'An Qālū 'Akhrijūhum Min Qaryatikum  ۖ  'Innahum 'Unāsun Yataţahharūn 007-082 Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da'awar tsarki!" ~  ۖ 
Fa'anjaynāhu Wa 'Ahlahu 'Illā Amra'atahu Kānat Mina Al-Ghābirīna 007-083 Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa. ~
Wa 'Amţarnā `Alayhim Maţarāan  ۖ  Fānžur Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mujrimīna 007-084 Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance!  ۖ 
Wa 'Ilá Madyana 'Akhāhum Shu`aybāan  ۗ  Qāla Yā Qawmi A`budū Al-Laha Mā Lakum Min 'Ilahin Ghayruhu  ۖ  Qad Jā'atkum Bayyinatun Min Rabbikum  ۖ  Fa'awfū Al-Kayla Wa Al-Mīzāna Wa Lā Tabkhasū An-Nāsa 'Ashyā 'Ahum Wa Lā Tufsidū Fī Al-'Arđi Ba`da  ۚ  'Işlāĥihā Dhālikum Khayrun Lakum 'In Kuntum Mu'uminīna 007-085 Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku tã zõ muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Wannan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance mũminai."  ۗ   ۖ   ۖ   ۚ 
Wa Lā Taq`udū Bikulli Şirāţin Tū`idūna Wa Taşuddūna `An Sabīli Al-Lahi Man 'Āmana Bihi Wa Tabghūnahā `Iwajāan  ۚ  Wa Adhkurū 'Idh Kuntum Qalīlāan Fakaththarakum  ۖ  Wa Anžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mufsidīna 007-086 "Kuma kada ku zauna ga kõwane tafarki kunã ƙyacẽwa, kuma kunã kangẽwa, daga hanyar Allah, ga wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma kunã nẽman ta ta zama karkatacciya, kuma ku tuna, a lõkacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu fasãdi ta kasance:"  ۚ   ۖ 
Wa 'In Kāna Ţā'ifatun Minkum 'Āmanū Bial-Ladhī 'Ursiltu Bihi Wa Ţā'ifatun Lam Yu'uminū Fāşbirū Ĥattá Yaĥkuma Al-Lahu Baynanā  ۚ  Wa Huwa Khayru Al-Ĥākimīna 007-087 "Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi ĩmãni da abin da aka aiko ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi ĩmãni ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya yi hukunci a tsakãninmu; kuma Shi ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci."  ۚ 
Qāla Al-Mala'u Al-Ladhīna Astakbarū Min Qawmihi Lanukhrijannaka Yā Shu`aybu Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Ma`aka Min Qaryatinā 'Aw Lata`ūdunna Fī Millatinā  ۚ  Qāla 'Awalaw Kunnā Kārihīna 007-088 Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?"  ۚ 
Qadi Aftaraynā `Alá Al-Lahi Kadhibāan 'In `Udnā Fī Millatikum Ba`da 'Idh Najjānā Al-Lahu Minhā  ۚ  Wa Mā Yakūnu Lanā 'An Na`ūda Fīhā 'Illā 'An Yashā'a Al-Lahu Rabbunā  ۚ  Wasi`a Rabbunā Kulla Shay'in `Ilmāan  ۚ  `Alá Al-Lahi Tawakkalnā  ۚ  Rabbanā Aftaĥ Baynanā Wa Bayna Qawminā Bil-Ĥaqqi Wa 'Anta Khayru Al-Fātiĥīna 007-089 "Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci."  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Qāla Al-Mala'u Al-Ladhīna Kafarū Min Qawmihi La'ini Attaba`tum Shu`aybāan 'Innakum 'Idhāan Lakhāsirūna 007-090 Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne."
Fa'akhadhat/humu Ar-Rajfatu Fa'aşbaĥū Fī Dārihimthimīna 007-091 Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidansu, sunã guggurfãne.
Al-Ladhīna Kadhdhabū Shu`aybāan Ka'an Lam Yaghnaw Fīhā  ۚ  Al-Ladhīna Kadhdhabū Shu`aybāan Kānū Humu Al-Khāsirīna 007-092 Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra!  ۚ 
Fatawallá `Anhum Wa Qāla Yā Qawmi Laqad 'Ablaghtukum Risālāti Rabbī Wa Naşaĥtu Lakum  ۖ  Fakayfa 'Āsá `Alá Qawmin Kāfirīna 007-093 Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai?"  ۖ 
Wa Mā 'Arsalnā Fī Qaryatin Min Nabīyin 'Illā 'Akhadhnā 'Ahlahā Bil-Ba'sā'i Wa Ađ-Đarrā'i La`allahum Yađđarra`ūna 007-094 Kuma ba Mu aika wani Annabi a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai.
Thumma Baddalnā Makāna As-Sayyi'ati Al-Ĥasanata Ĥattá `Afaw Wa Qālū Qad Massa 'Ābā'anā Ađ-Đarrā'u Wa As-Sarrā'u Fa'akhadhnāhum Baghtatan Wa Hum Lā Yash`urūna 007-095 Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu." ( sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa."
Wa Law 'Anna 'Ahla Al-Qurá 'Āmanū Wa Attaqaw Lafataĥnā `Alayhim Barakātin Mina As-Samā'i Wa Al-'Arđi Wa Lakin Kadhdhabū Fa'akhadhnāhum Bimā Kānū Yaksibūna 007-096 Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa.
'Afa'amina 'Ahlu Al-Qurá 'An Ya'tiyahum Ba'sunā Bayātāan Wa Hum Nā'imūna 007-097 Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jẽ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci?
'Awa 'Amina 'Ahlu Al-Qurá 'An Ya'tiyahum Ba'sunā Đuĥáan Wa Hum Yal`abūna 007-098 Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa?
'Afa'aminū Makra Al-Lahi  ۚ  Falā Ya'manu Makra Al-Lahi 'Illā Al-Qawmu Al-Khāsirūna 007-099 Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra!  ۚ 
'Awalam Yahdi Lilladhīna Yarithūna Al-'Arđa Min Ba`di 'Ahlihā 'An Law Nashā'u 'Aşabnāhum Bidhunūbihim  ۚ  Wa Naţba`u `Alá Qulūbihim Fahum Lā Yasma`ūna 007-100 Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cẽwa da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su zama bã su ji?  ۚ 
Tilka Al-Qurá Naquşşu `Alayka Min 'Anbā'ihā  ۚ  Wa Laqad Jā'at/hum Rusuluhum Bil-Bayyināti Famā Kānū Liyu'uminū Bimā Kadhdhabū Min Qablu  ۚ  Kadhālika Yaţba`u Al-Lahu `Alá Qulūbi Al-Kāfirīna 007-101 Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jẽ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin ĩmãnida abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a kan zukãtan kãfirai.  ۚ   ۚ 
Wa Mā Wajadnā Li'ktharihim Min `Ahdin  ۖ  Wa 'In Wajadnā 'Aktharahum Lafāsiqīna 007-102 Kuma ba Mu sãmi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sãmi mafi yawansu, haƙĩƙa, fãsiƙai.  ۖ 
Thumma Ba`athnā Min Ba`dihim Mūsá Bi'āyātinā 'Ilá Fir`awna Wa Mala'ihi Fažalamū Bihā  ۖ  Fānžur Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mufsidīna 007-103 Sa'an nan kuma Mun aika Musa, daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata take.  ۖ 
Wa Qāla Mūsá Yā Fir`awnu 'Innī Rasūlun Min Rabbi Al-`Ālamīna 007-104 Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu."
Ĥaqīqun `Alá 'An Lā 'Aqūla `Alá Al-Lahi 'Illā Al-Ĥaqqa  ۚ  Qad Ji'tukum Bibayyinatin Min Rabbikum Fa'arsil Ma`ī Banī 'Isrā'īla 007-105 "Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni."  ۚ 
Qāla 'In Kunta Ji'ta Bi'āyatin Fa'ti Bihā 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna 007-106 Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Fa'alqá `Aşāhu Fa'idhā Hiya Thu`bānun Mubīnun 007-107 Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne!
Wa Naza`a Yadahu Fa'idhā Hiya Bayđā'u Lilnnāžirīna 007-108 Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi!
Qāla Al-Mala'u Min Qawmi Fir`awna 'Inna Hādhā Lasāĥirun `Alīmun 007-109 Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi."
Yurīdu 'An Yukhrijakum Min 'Arđikum  ۖ  Famādhā Ta'murūna 007-110 " Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?"  ۖ 
Qālū 'Arjihi Wa 'Akhāhu Wa 'Arsil Fī Al-Madā'ini Ĥāshirīna 007-111 Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa.
Ya'tūka Bikulli Sāĥirin `Alīmin 007-112 "Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi."
Wa Jā'a As-Saĥaratu Fir`awna Qālū 'Inna Lanā La'ajrāan 'In Kunnā Naĥnu Al-Ghālibīna 007-113 Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?"
Qāla Na`am Wa 'Innakum Lamina Al-Muqarrabīna 007-114 Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta."
Qālū Yā Mūsá 'Immā 'An Tulqiya Wa 'Immā 'An Nakūna Naĥnu Al-Mulqīna 007-115 Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa?"
Qāla 'Alqū  ۖ  Falammā 'Alqaw Saĥarū 'A`yuna An-Nāsi Wa Astarhabūhum Wa Jā'ū Bisiĥrin `Ažīmin 007-116 Ya ce: "Ku jẽfa." To a 1õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma."  ۖ 
Wa 'Awĥaynā 'Ilá Mūsá 'An 'Alqi `Aşāka  ۖ  Fa'idhā Hiya Talqafu Mā Ya'fikūna 007-117 Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!  ۖ 
Fawaqa`a Al-Ĥaqqu Wa Baţala Mā Kānū Ya`malūna 007-118 Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.
Faghulibū Hunālika Wa Anqalabū Şāghirīna 007-119 Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu.
Wa 'Ulqiya As-Saĥaratu Sājidīna 007-120 Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada.
Qālū 'Āmannā Birabbi Al-`Ālamīna 007-121 Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu."
Rabbi Mūsá Wa Hārūna 007-122 "Ubangijin Mũsã da Harũna."
Qāla Fir`awnu 'Āmantum Bihi Qabla 'An 'Ādhana Lakum  ۖ  'Inna Hādhā Lamakrun Makartumūhu Fī Al-Madīnati Litukhrijū Minhā 'Ahlahā  ۖ  Fasawfa Ta`lamūna 007-123 Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani."  ۖ   ۖ 
La'uqaţţi`anna 'Aydiyakum Wa 'Arjulakum Min Khilāfin Thumma La'uşallibannakum 'Ajma`īna 007-124 "Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya."
Qālū 'Innā 'Ilá Rabbinā Munqalibūna 007-125 Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne."
Wa Mā Tanqimu Minnā 'Illā 'An 'Āmannā Bi'āyāti Rabbinā Lammā Jā'atnā  ۚ  Rabbanā 'Afrigh `Alaynā Şabrāan Wa Tawaffanā Muslimīna 007-126 "Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai! "  ۚ 
Wa Qāla Al-Mala'u Min Qawmi Fir`awna 'Atadharu Mūsá Wa Qawmahu Liyufsidū Fī Al-'Arđi Wa Yadharaka Wa 'Ālihataka  ۚ  Qāla Sanuqattilu 'Abnā'ahum Wa Nastaĥyī Nisā'ahum Wa 'Innā Fawqahum Qāhirūna 007-127 Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne."  ۚ 
Qāla Mūsá Liqawmihi Asta`īnū Bil-Lahi Wa Aşbirū  ۖ  'Inna Al-'Arđa Lillahi Yūrithuhā Man Yashā'u Min `Ibādihi Wa  ۖ  Al-`Āqibatu Lilmuttaqīna 007-128 Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce."  ۖ   ۖ 
Qālū 'Ūdhīnā Min Qabli 'An Ta'tiyanā Wa Min Ba`di Mā Ji'tanā  ۚ  Qāla `Asá Rabbukum 'An Yuhlika `Adūwakum Wa Yastakhlifakum Al-'Arđi Fayanžura Kayfa Ta`malūna 007-129 Suka ce: "An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana." Ya ce: "Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa."  ۚ 
Wa Laqad 'Akhadhnā 'Āla Fir`awna Bis-Sinīna Wa Naqşin Mina Ath-Thamarāti La`allahum Yadhdhakkarūna 007-130 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kãma mutãnen Fir'auna da tsananin shẽkaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan itãce; Tsammãninsu sunã tunãwa.
Fa'idhā Jā'at/humu Al-Ĥasanatu Qālū Lanā Hadhihi  ۖ  Wa 'In Tuşibhum Sayyi'atun Yaţţayyarū Bimūsá Wa Man Ma`ahu  ۗ  'Alā 'Innamā Ţā'iruhum `Inda Al-Lahi Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna 007-131 Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: "Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani!"  ۖ  ~  ۗ 
Wa Qālū Mahmā Ta'tinā Bihi Min 'Āyatin Litasĥaranā Bihā Famā Naĥnu Laka Bimu'uminīna 007-132 Kuma suka ce: "Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba."
Fa'arsalnā `Alayhimu Aţ-Ţūfāna Wa Al-Jarāda Wa Al-Qummala Wa Ađ-Đafādi`a Wa Ad-Dama 'Āyātin Mufaşşalātin Fāstakbarū Wa Kānū Qawmāan Mujrimīna 007-133 Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.
Wa Lammā Waqa`a `Alayhimu Ar-Rijzu Qālū Yā Mūsá Ad`u Lanā Rabbaka Bimā `Ahida `Indaka  ۖ  La'in Kashafta `Annā Ar-Rijza Lanu'uminanna Laka Wa Lanursilanna Ma`aka Banī 'Isrā'īla 007-134 Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai."  ۖ 
Falammā Kashafnā `Anhumu Ar-Rijza 'Ilá 'Ajalin Hum Bālighūhu 'Idhā Hum Yankuthūna 007-135 To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa! ~
ntaqamnā Minhum Fa'aghraqnāhum Al-Yammi Bi'annahum Kadhdhabū Bi'āyātinā Wa Kānū `Anhā Ghāfilīna 007-136 Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai.
Wa 'Awrath Al-Qawma Al-Ladhīna Kānū Yustađ`afūna Mashāriqa Al-'Arđi Wa Maghāribahā Allatī Bāraknā Fīhā  ۖ  Wa Tammat Kalimatu Rabbika Al-Ĥusná `Alá Banī 'Isrā'īla Bimā Şabarū  ۖ  Wa Dammarnā Mā Kāna Yaşna`u Fir`awnu Wa Qawmuhu Wa Mā Kānū Ya`rishūna 007-137 Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa.  ۖ   ۖ 
Wa Jāwaznā Bibanī 'Isrā'īla Al-Baĥra Fa'ataw `Alá Qawmin Ya`kufūna `Alá 'Aşnāmin Lahum  ۚ  Qālū Yā Mūsá Aj`al Lanā 'Ilahāan Kamā Lahum 'Ālihatun  ۚ  Qāla 'Innakum Qawmun Tajhalūna 007-138 Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: "Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa " Ya ce: "Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta."  ۚ   ۚ 
'Inna Hā'uulā' Mutabbarun Mā Hum Fīhi Wa Bāţilun Mā Kānū Ya`malūna 007-139 "Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa ƙarya ne."
Qāla 'Aghayra Al-Lahi 'Abghīkum 'Ilahāan Wa Huwa Fađđalakum `Alá Al-`Ālamīna 007-140 Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?"
Wa 'Idh 'Anjaynākum Min 'Āli Fir`awna Yasūmūnakum Sū'a Al-`Adhābi  ۖ  Yuqattilūna 'Abnā'akum Wa Yastaĥyūna Nisā'akum  ۚ  Wa Fī Dhālikum Balā'un Min Rabbikum `Ažīmun 007-141 Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku, Mai girma.  ۖ   ۚ 
Wa Wā`adnā Mūsá Thalāthīna Laylatan Wa 'Atmamnāhā Bi`ashrin Fatamma Mīqātu Rabbihi 'Arba`īna Laylatan  ۚ  Wa Qāla Mūsá Li'khīhi Hārūna Akhlufnī Fī Qawmī Wa 'Aşliĥ Wa Lā Tattabi` Sabīla Al-Mufsidīna 007-142 Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi." Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: "Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni." Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai." ~  ۚ 
Wa Lammā Jā'a Mūsá Limīqātinā Wa Kallamahu Rabbuhu Qāla Rabbi 'Arinī 'Anžur 'Ilayka  ۚ  Qāla Lan Tarānī Wa Lakini Anžur 'Ilá Al-Jabali Fa'ini Astaqarra Makānahu Fasawfa Tarānī  ۚ  Falammā Tajallá Rabbuhu Liljabali Ja`alahu Dakkāan Wa Kharra Mūsá Şa`iqāan  ۚ  Falammā 'Afāqa Qāla Subĥānaka Tubtu 'Ilayka Wa 'Anā 'Awwalu Al-Mu'uminīna 007-143 - Missing -  ۚ   ۚ   ۚ 
Qāla Yā Mūsá 'Innī Aşţafaytuka `Alá An-Nāsi Birisālātī Wa Bikalāmī Fakhudh Mā 'Ātaytuka Wa Kun Mina Ash-Shākirīna 007-144 Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya."
Wa Katabnā Lahu Fī Al-'Alwāĥi Min Kulli Shay'in Maw`ižatan Wa Tafşīlāan Likulli Shay'in Fakhudh/hā Biqūwatin Wa 'Mur Qawmaka Ya'khudhū Bi'aĥsanihā  ۚ  Sa'urīkum Dāra Al-Fāsiqīna 007-145 Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai."  ۚ 
Sa'aşrifu `An 'Āyātiya Al-Ladhīna Yatakabbarūna Fī Al-'Arđi Bighayri Al-Ĥaqqi Wa 'In Yaraw Kulla 'Āyatin Lā Yu'uminū Bihā Wa 'In Yaraw Sabīla Ar-Rushdi Lā Yattakhidhūhu Sabīlāan Wa 'In Yaraw Sabīla Al-Ghayyi Yattakhidhūhu Sabīlāan  ۚ  Dhālika Bi'annahum Kadhdhabū Bi'āyātinā Wa Kānū `Anhā Ghāfilīna 007-146 Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā Wa Liqā'i Al-'Ākhirati Ĥabiţat  ۚ  'A`māluhum Hal Yujzawna 'Illā Mā Kānū Ya`malūna 007-147 Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa?  ۚ 
Wa Attakhadha Qawmu Mūsá Min Ba`dihi Min Ĥulīyihim `Ijlāan Jasadāan Lahu Khuwārun  ۚ  'Alam Yaraw 'Annahu Lā Yukallimuhum Wa Lā Yahdīhim Sabīlāan  ۘ  Attakhadhūhu Wa Kānū Žālimīna 007-148 Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci.  ۚ   ۘ 
Wa Lammā Suqiţa Fī 'Aydīhim Wa Ra'aw 'Annahum Qad Đallū Qālū La'in Lam Yarĥamnā Rabbunā Wa Yaghfir Lanā Lanakūnanna Mina Al-Khāsirīna 007-149 Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra."
Wa Lammā Raja`a Mūsá 'Ilá Qawmihi Ghađbāna 'Asifāan Qāla Bi'samā Khalaftumūnī Min Ba`dī  ۖ  'A`ajiltum 'Amra Rabbikum  ۖ  Wa 'Alqá Al-'Alwāĥa Wa 'Akhadha Bira'si 'Akhīhi Yajurruhu 'Ilayhi  ۚ  Qāla Abna 'Umma 'Inna Al-Qawma Astađ`afūnī Wa Kādū Yaqtulūnanī Falā Tushmit Biya Al-'A`dā'a Wa Lā Taj`alnī Ma`a Al-Qawmi Až-Žālimīna 007-150 Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bãyanã! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yã ɗan'uwata! Lalle ne mutãnen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka dãrantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne azzãlumai."  ۖ   ۖ  ~  ۚ 
Qāla Rabbi Aghfir Lī Wa Li'akhī Wa 'Adkhilnā Fī Raĥmatika  ۖ  Wa 'Anta 'Arĥamu Ar-Rāĥimīna 007-151 Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama!"  ۖ 
'Inna Al-Ladhīna Attakhadhū Al-`Ijla Sayanāluhum Ghađabun Min Rabbihim Wa Dhillatun Al-Ĥayāati Ad-Dunyā  ۚ  Wa Kadhalika Naj Al-Muftarīna 007-152 Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya, zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu ƙirƙira ƙarya.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna `Amilū As-Sayyi'āti Thumma Tābū Min Ba`dihā Wa 'Āmanū 'Inna Rabbaka Min Ba`dihā Laghafūrun Raĥīmun 007-153 Kuma waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga bãyansu kuma sukayi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, haƙĩƙa, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.
Wa Lammā Sakata `An Mūsá Al-Ghađabu 'Akhadha Al-'Alwāĥa  ۖ  Wa Fī Nuskhatihā Hudáan Wa Raĥmatun Lilladhīna Hum Lirabbihim Yarhabūna 007-154 Kuma a lõkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsã, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, mãsu jin tsõro ne.  ۖ 
Wa Akhtāra Mūsá Qawmahu Sab`īna Rajulāan Limīqātinā  ۖ  Falammā 'Akhadhat/humu Ar-Rajfatu Qāla Rabbi Law Shi'ta 'Ahlaktahum Min Qablu Wa 'Īyāya  ۖ  'Atuhlikunā Bimā Fa`ala As-Sufahā'u Minnā  ۖ  'In Hiya 'Illā Fitnatuka Tuđillu Bihā Man Tashā'u Wa Tahdī Man Tashā'u  ۖ  'Anta Walīyunā Fāghfir Lanā Wa Arĥamnā  ۖ  Wa 'Anta Khayru Al-Ghāfirīna 007-155 Kuma Mũsã ya zãɓi mutãnensa, namiji saba'in dõmin miƙãtinMu. To, a lõkacin da tsãwa ta kãma su, ya ce: "Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarKa Kanã ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kanã shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãfara."  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۖ 
Wa Aktub Lanā Fī Hadhihi Ad-Dunyā Ĥasanatan Wa Fī Al-'Ākhirati 'Innā Hudnā 'Ilayka  ۚ  Qāla `Adhābī 'Uşību Bihi Man 'Ashā'u  ۖ  Wa Raĥmatī Wasi`at Kulla Shay'in  ۚ  Fasa'aktubuhā Lilladhīna Yattaqūna Wa Yu'utūna Az-Zakāata Wa Al-Ladhīna Hum Bi'āyātinā Yu'uminūna 007-156 "Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ,mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyinMu mũminai ne."  ۚ   ۖ   ۚ 
Al-Ladhīna Yattabi`ūna Ar-Rasūla An-Nabīya Al-'Ummīya Al-Ladhī Yajidūnahu Maktūbāan `Indahum At-Tawrāati Wa Al-'Injīli Ya'muruhum Bil-Ma`rūfi Wa Yanhāhum `Ani Al-Munkari Wa Yuĥillu Lahumu Aţ-Ţayyibāti Wa Yuĥarrimu `Alayhimu Al-Khabā'itha Wa Yađa`u `Anhum 'Işrahum Wa Al-'Aghlāla Allatī Kānat `Alayhim  ۚ  Fa-Al-Ladhīna 'Āmanū Bihi Wa `Azzarūhu Wa Naşarūhu Wa Attaba`ū An-Nūra Al-Ladhī 'Unzila Ma`ahu  ۙ  'Ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna 007-157 "Waɗanda suke sunã bin Manzo, Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.  ۚ  ~  ۙ 
Qul Yā 'Ayyuhā An-Nāsu 'Innī Rasūlu Al-Lahi 'Ilaykum Jamī`āan Al-Ladhī Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Yuĥyī Wa Yumītu  ۖ  Fa'āminū Bil-Lahi Wa Rasūlihi An-Nabīyi Al-'Ummīyi Al-Ladhī Yu'uminu Bil-Lahi Wa Kalimātihi Wa Attabi`ūhu La`allakum Tahtadūna 007-158 Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa."  ۖ  ~  ۖ 
Wa Min Qawmi Mūsá 'Ummatun Yahdūna Bil-Ĥaqqi Wa Bihi Ya`dilūna 007-159 Kuma daga mutãnen Mũsã akwai al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci.
Wa Qaţţa`nāhumu Athnatay `Ashrata 'Asbāţāan 'Umamāan  ۚ  Wa 'Awĥaynā 'Ilá Mūsá 'Idh Astasqāhu Qawmuhu 'Ani Ađrib Bi`aşāka Al-Ĥajara  ۖ  Fānbajasat Minhu Athnatā `Ashrata `Aynāan  ۖ  Qad `Alima Kullu 'Unāsin Mashrabahum  ۚ  Wa Žallalnā `Alayhimu Al-Ghamāma Wa 'Anzalnā `Alayhimu Al-Manna Wa As-Salwá  ۖ  Kulū Min Ţayyibāti Mā Razaqnākum  ۚ  Wa Mā Žalamūnā Wa Lakin Kānū 'Anfusahum Yažlimūna 007-160 Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dõki dũtsen da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta.  ۚ  ~  ۖ   ۖ   ۚ   ۖ   ۚ 
Wa 'Idh Qīla Lahumu Askunū Hadhihi Al-Qaryata Wa Kulū Minhā Ĥaythu Shi'tum Wa Qūlū Ĥiţţatun Wa Adkhulū Al-Bāba Sujjadāan Naghfir Lakum Khī'ātikum  ۚ  Sanazīdu Al-Muĥsinīna 007-161 Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya, kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa."  ۚ 
Fabaddala Al-Ladhīna Žalamū Minhum Qawlāan Ghayra Al-Ladhī Qīla Lahum Fa'arsalnā `Alayhim Rijzāan Mina As-Samā'i Bimā Kānū Yažlimūna 007-162 Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci.
Wa As'alhum `Ani Al-Qaryati Allatī Kānat Ĥāđirata Al-Baĥri 'Idh Ya`dūna Fī As-Sabti 'Idh Ta'tīhim Ĥītānuhum Yawma Sabtihim Shurra`āan Wa Yawma Lā Yasbitūna  ۙ  Lā Ta'tīhim  ۚ  Kadhālika Nablūhum Bimā Kānū Yafsuqūna 007-163 Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.  ۙ   ۚ 
Wa 'Idh Qālat 'Ummatun Minhum Lima Ta`ižūna Qawmāan  ۙ  Al-Lahu Muhlikuhum 'Aw Mu`adhdhibuhum `Adhābāan Shadīdāan  ۖ  Qālū Ma`dhiratan 'Ilá Rabbikum Wa La`allahum Yattaqūna 007-164 Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?" Suka ce: "Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa."  ۙ   ۖ 
Falammā Nasū Mā Dhukkirū Bihi 'Anjaynā Al-Ladhīna Yanhawna `Ani As-Sū'i Wa 'Akhadh Al-Ladhīna Žalamū Bi`adhābin Ba'īsin Bimā Kānū Yafsuqūna 007-165 To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci. ~
Falammā `Ataw `An Mā Nuhū `Anhu Qulnā Lahum Kūnū Qiradatan Khāsi'īna 007-166 Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu."
Wa 'Idh Ta'adhdhana Rabbuka Layab`athanna `Alayhim 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati Man Yasūmuhum Sū'a Al-`Adhābi  ۗ  'Inna Rabbaka Lasarī`u Al-`Iqābi  ۖ  Wa 'Innahu Laghafūrun Raĥīmun 007-167 Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rãnar¡iyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۗ   ۖ 
Wa Qaţţa`nāhum Al-'Arđi 'Umamāan  ۖ  Minhumu Aş-Şāliĥūna Wa Minhum Dūna Dhālika  ۖ  Wa Balawnāhum Bil-Ĥasanāti Wa As-Sayyi'āti La`allahum Yarji`ūna 007-168 Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa.  ۖ   ۖ 
Fakhalafa Min Ba`dihim Khalfun Warithū Al-Kitāba Ya'khudhūna `Arađa Hādhā Al-'Adná Wa Yaqūlūna Sayughfaru Lanā Wa 'In Ya'tihim `Arađun Mithluhu Ya'khudhūhu 'Alam  ۚ  Yu'ukhadh `Alayhimthāqu Al-Kitābi 'An Lā Yaqūlū `Alá Al-Lahi 'Illā Al-Ĥaqqa Wa Darasū Mā Fīhi Wa Ad-Dāru  ۗ  Al-'Ākhiratu Khayrun Lilladhīna Yattaqūna 'Afalā  ۗ  Ta`qilūna 007-169 Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba? ~  ۚ   ۗ   ۗ 
Wa Al-Ladhīna Yumassikūna Bil-Kitābi Wa 'Aqāmū Aş-Şalāata 'Innā Lā Nuđī`u 'Ajra Al-Muşliĥīna 007-170 Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa.
Wa 'Idh Nataq Al-Jabala Fawqahum Ka'annahu Žullatun Wa Žannū 'Annahu Wāqi`un Bihim Khudhū Mā 'Ātaynākum Biqūwatin Wa Adhkurū Mā Fīhi La`allakum Tattaqūna 007-171 Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa."
Wa 'Idh 'Akhadha Rabbuka Min Banī 'Ādama Min Žuhūrihim Dhurrīyatahum Wa 'Ash/hadahum `Alá 'Anfusihim 'Alastu Birabbikum  ۖ  Qālū Balá  ۛ  Shahidnā  ۛ  'An Taqūlū Yawma Al-Qiyāmati 'Innā Kunnā `An Hādhā Ghāfilīna 007-172 Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne."  ۖ   ۛ   ۛ 
'Aw Taqūlū 'Innamā 'Ashraka 'Ābā'uunā Min Qablu Wa Kunnā Dhurrīyatan Min Ba`dihim  ۖ  'Afatuhlikunā Bimā Fa`ala Al-Mubţilūna 007-173 Kõ kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa,Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata?"  ۖ 
Wa Kadhalika Nufaşşilu Al-'Āyāti Wa La`allahum Yarji`ūna 007-174 Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa.
Wa Atlu `Alayhim Naba'a Al-Ladhī 'Ātaynāhu 'Āyātinā Fānsalakha Minhā Fa'atba`ahu Ash-Shayţānu Fakāna Mina Al-Ghāwīna 007-175 Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.
Wa Law Shi'nā Larafa`nāhu Bihā Wa Lakinnahu 'Akhlada 'Ilá Al-'Arđi Wa Attaba`a Hawāhu  ۚ  Famathaluhu Kamathali Al-Kalbi 'In Taĥmil `Alayhi Yalhath 'Aw Tatruk/hu Yalhath  ۚ  Dhālika Mathalu Al-Qawmi Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā  ۚ  Fāqşuşi Al-Qaşaşa La`allahum Yatafakkarūna 007-176 Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni. ~  ۚ   ۚ   ۚ 
Sā'a Mathalāan Al-Qawmu Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā Wa 'Anfusahum Kānū Yažlimūna 007-177 Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta.
Man Yahdi Al-Lahu Fahuwa Al-Muhtadī  ۖ  Wa Man Yuđlil Fa'ūlā'ika Humu Al-Khāsirūna 007-178 Wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.  ۖ 
Wa Laqad Dhara'nā Lijahannama Kathīrāan Mina Al-Jinni Wa Al-'Insi  ۖ  Lahum Qulūbun Lā Yafqahūna Bihā Wa Lahum 'A`yunun Lā Yubşirūna Bihā Wa Lahum 'Ādhānun Lā Yasma`ūna Bihā  ۚ  'Ūlā'ika Kāl'an`āmi Bal Hum 'Ađallu  ۚ  'Ūlā'ika Humu Al-Ghāfilūna 007-179 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu.  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa Lillahi Al-'Asmā'u Al-Ĥusná Fād`ūhu Bihā  ۖ  Wa Dharū Al-Ladhīna Yulĥidūna Fī 'Asmā'ihi  ۚ  Sayujzawna Mā Kānū Ya`malūna 007-180 Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau. Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa:zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.  ۖ   ۚ 
Wa Mimman Khalaqnā 'Ummatun Yahdūna Bil-Ĥaqqi Wa Bihi Ya`dilūna 007-181 Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma,da ita suke yin ãdalci.
Wa Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā Sanastadrijuhum Min Ĥaythu Lā Ya`lamūna 007-182 Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
Wa 'Umlī Lahum  ۚ  'Inna Kaydī Matīnun 007-183 Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne.  ۚ 
'Awalam Yatafakkarū  ۗ  Mā Bişāĥibihim Min Jinnatin  ۚ  'In Huwa 'Illā Nadhīrun Mubīnun 007-184 Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu? shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa.  ۗ   ۚ 
'Awalam Yanžurū Fī Malakūti As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Khalaqa Al-Lahu Min Shay'in Wa 'An `Asá 'An Yakūna Qadi Aqtaraba 'Ajaluhum  ۖ  Fabi'ayyi Ĥadīthin Ba`dahu Yu'uminūna 007-185 Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To,da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni?  ۖ 
Man Yuđlili Al-Lahu Falā Hādiya Lahu  ۚ  Wa Yadharuhum Fī Ţughyānihim Ya`mahūna 007-186 Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa.  ۚ 
Yas'alūnaka `Ani As-Sā`ati 'Ayyāna Mursāhā  ۖ  Qul 'Innamā `Ilmuhā `Inda Rabbī  ۖ  Lā Yujallīhā Liwaqtihā 'Illā Huwa  ۚ  Thaqulat Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Lā Ta'tīkum 'Illā Baghtatan  ۗ  Yas'alūnaka Ka'annaka Ĥafīyun `Anhā  ۖ  Qul 'Innamā `Ilmuhā `Inda Al-Lahi Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna 007-187 Sunã tambayar ka daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani."  ۖ   ۖ   ۚ   ۚ   ۗ   ۖ 
Qul Lā 'Amliku Linafsī Naf`āan Wa Lā Đarrāan 'Illā Mā Shā'a Al-Lahu  ۚ  Wa Law Kuntu 'A`lamu Al-Ghayba Lāstakthartu Mina Al-Khayri Wa Mā Massaniya As-Sū'u  ۚ  'In 'Anā 'Illā Nadhīrun Wa Bashīrun Liqawmin Yu'uminūna 007-188 Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni."  ۚ   ۚ 
Huwa Al-Ladhī Khalaqakum Min Nafsin Wāĥidatin Wa Ja`ala Minhā Zawjahā Liyaskuna 'Ilayhā  ۖ  Falammā Taghashshāhā Ĥamalat Ĥamlāan Khafīfāan Famarrat Bihi  ۖ  Falammā 'Athqalat Da`awā Al-Laha Rabbahumā La'in 'Ātaytanā Şāliĥāan Lanakūnanna Mina Ash-Shākirīna 007-189 Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya."  ۖ   ۖ 
Falammā 'Ātāhumā Şāliĥāan Ja`alā Lahu Shurakā'a Fīmā 'Ātāhumā  ۚ  Fata`ālá Al-Lahu `Ammā Yushrikūna 007-190 To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki.  ۚ 
'Ayushrikūna Mā Lā Yakhluqu Shay'āan Wa Hum Yukhlaqūna 007-191 Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa?
Wa Lā Yastaţī`ūna Lahum Naşrāan Wa Lā 'Anfusahum Yanşurūna 007-192 Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka!
Wa 'In Tad`ūhum 'Ilá Al-Hudá Lā Yattabi`ūkum  ۚ  Sawā'un `Alaykum 'Ada`awtumūhum 'Am 'Antum Şāmitūna 007-193 Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne!  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi `Ibādun 'Amthālukum  ۖ  Fād`ūhum Falyastajībū Lakum 'In Kuntum Şādiqīna 007-194 Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya!  ۖ 
'Alahum 'Arjulun Yamshūna Bihā  ۖ  'Am Lahum 'Aydin Yabţishūna Bihā  ۖ  'Am Lahum 'A`yunun Yubşirūna Bihā  ۖ  'Am Lahum 'Ādhānun Yasma`ūna Bihā  ۗ  Quli AdShurakā'akum Thumma Kīdūni Falā Tunžirūni 007-195 Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: "Ku kirãwo abũbuwan shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini."  ۖ   ۖ   ۖ   ۗ 
'Inna Walīyiya Al-Lahu Al-Ladhī Nazzala Al-Kitāba  ۖ  Wa Huwa Yatawallá Aş-Şāliĥīna 007-196 "Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai,"  ۖ 
Wa Al-Ladhīna Tad`ūna Min Dūnihi Lā Yastaţī`ūna Naşrakum Wa Lā 'Anfusahum Yanşurūna 007-197 "Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka."
Wa 'In Tad`ūhum 'Ilá Al-Hudá Lā Yasma`ū  ۖ  Wa Tarāhum Yanžurūna 'Ilayka Wa Hum Lā Yubşirūna 007-198 Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani.  ۖ 
Khudhi Al-`Afwa Wa 'Mur Bil-`Urfi Wa 'A`riđ `Ani Al-Jāhilīna 007-199 Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai.
Wa 'Immā Yanzaghannaka Mina Ash-Shayţāni Nazghun Fāsta`idh Bil-Lahi  ۚ  'Innahu Samī`un `Alīmun 007-200 Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Attaqaw 'Idhā Massahum Ţā'ifun Mina Ash-Shayţāni Tadhakkarū Fa'idhā Hum Mubşirūna 007-201 Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra.
Wa 'Ikhwānuhum Yamuddūnahum Al-Ghayyi Thumma Lā Yuqşirūna 007-202 Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa.
Wa 'Idhā Lam Ta'tihim Bi'āyatin Qālū Lawlā Ajtabaytahā  ۚ  Qul 'Innamā 'Attabi`u Mā Yūĥá 'Ilayya Min Rabbī  ۚ  Hādhā Başā'iru Min Rabbikum Wa Hudáan Wa Raĥmatun Liqawmin Yu'uminūna 007-203 Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka ƙãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni."  ۚ   ۚ 
Wa 'Idhā Quri'a Al-Qur'ānu Fāstami`ū Lahu Wa 'Anşitū La`allakum Turĥamūna 007-204 Kuma idan an karanta Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.
Wa Adhkur Rabbaka Fī Nafsika Tađarru`āan Wa Khīfatan Wa Dūna Al-Jahri Mina Al-Qawli Bil-Ghudūwi Wa Al-'Āşāli Wa Lā Takun Mina Al-Ghāfilīna 007-205 Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.
'Inna Al-Ladhīna `Inda Rabbika Lā Yastakbirūna `An `Ibādatihi Wa Yusabbiĥūnahu Wa Lahu Yasjudūna 007-206 Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada.
Next Sūrah