6) Sūrat Al-'An`ām

Printed format

6)

Al-Ĥamdu Lillahi Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Ja`ala Až-Žulumāti Wa An-Nūra Thumma Al-Ladhīna Kafarū Birabbihim Ya`dilūna 006-001 Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske , sa'an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.  ۖ 
Huwa Al-Ladhī Khalaqakum Min Ţīnin Thumma Qađá 'Ajalāan  ۖ  Wa 'Ajalun Musammáan `Indahu  ۖ  Thumma 'Antum Tamtarūna 006-002 Shi ne wanda Ya halitta ku daga lãkã, sa'an nan kuma Ya yanka ajali alhãli wani ajali ambatacce yanã wurinSa. Sa'an nan kuma ku kunã yin shakka.  ۖ   ۖ 
Wa Huwa Al-Lahu Fī As-Samāwāti Wa Fī Al-'Arđi  ۖ  Ya`lamu Sirrakum Wa Jahrakum Wa Ya`lamu Mā Taksibūna 006-003 Kuma Shĩ ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin ƙasa Yanã sanin asĩrinku da bayyanenku, kuma Yanã sanin abin da kuke yi na tsirfa.  ۖ 
Wa Mā Ta'tīhim Min 'Āyatin Min 'Āyāti Rabbihim 'Illā Kānū `Anhā Mu`rīna 006-004 Kuma wata ãyã daga Ubangijinsu ba zã ta jẽ musu ba, fãce su kasance, daga gare ta, mãsu bijirẽwa.
Faqad Kadhdhabū Bil-Ĥaqqi Lammā Jā'ahum  ۖ  Fasawfa Ya'tīhim 'Anbā'u Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn 006-005 Sabõda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu.  ۖ 
'Alam Yaraw Kam 'Ahlaknā Min Qablihim Min Qarnin Makkannāhum Al-'Arđi Mā Lam Numakkin Lakum Wa 'Arsalnā As-Samā'a `Alayhim Midrārāan Wa Ja`alnā Al-'Anhāra Tajrī Min Taĥtihim Fa'ahlaknāhum Bidhunūbihim Wa 'Ansha'nā Min Ba`dihim Qarnāan 'Ākharīna 006-006 Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabãninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tanã ta zuba, kuma Muka sanya kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sa'an nan Muka halakã su sabõda zunubansu kuma Muka ƙãga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu?
Wa Law Nazzalnā `Alayka Kitābāan Fī Qirţāsin Falamasūhu Bi'aydīhim Laqāla Al-Ladhīna Kafarū 'In Hādhā 'Illā Siĥrun Mubīnun 006-007 Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce: "Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne."
Wa Qālū Lawlā 'Unzila `Alayhi Malakun  ۖ  Wa Law 'Anzalnā Malakāan Laquđiya Al-'Amru Thumma Lā Yunžarūna 006-008 Suka ce: "Don me ba a saukar da wani malã'ika ba a gare shi?" to dã Mun saukar da malã'ika haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin sa'an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba.  ۖ 
Wa Law Ja`alnāhu Malakāan Laja`alnāhu Rajulāan Wa Lalabasnā `Alayhim Mā Yalbisūna 006-009 Kuma dã Mun sanya malã'ika ya zama manzo lalle ne dã Mun mayar da shi mutum, kuma dã Mun rikita musu abin da suke rikitãwa.
Wa Laqadi Astuhzi'a Birusulin Min Qablika Faĥāqa Bial-Ladhīna Sakhirū Minhum Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn 006-010 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da manzanni daga gabaninka, sai waɗanda suka yi izgilin, abin da suka kasance sunã izgili da shi ya fãɗa musu.
Qul Sīrū Fī Al-'Arđi Thumma Anžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mukadhdhibīna 006-011 Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance."
Qul Liman Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Qul Lillahi  ۚ  Kataba `Alá Nafsihi Ar-Raĥmata  ۚ  Layajma`annakum 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati Lā Rayba Fīhi  ۚ  Al-Ladhīna Khasirū 'Anfusahum Fahum Lā Yu'uminūna 006-012 Ka ce: "Na wãne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Na Allah ne." Yã wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yanã tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ ba zã su yi ĩmani ba."  ۖ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Lahu Mā Sakana Fī Al-Layli Wa An-Nahāri  ۚ  Wa Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu 006-013 "Kuma Shĩ ne da mallakar abin da ya yi kawaici a cikin dare da yini, kuma Shi ne Mai ji, Masani."  ۚ 
Qul 'Aghayra Al-Lahi 'Attakhidhu Walīyāan Fāţiri As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Huwa Yuţ`imu Wa Lā Yuţ`amu  ۗ  Qul 'Innī 'Umirtu 'An 'Akūna 'Awwala Man 'Aslama  ۖ  Wa Lā Takūnanna Mina Al-Mushrikīna 006-014 Ka ce: "Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhãli Allah ne ) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?" Ka ce: "Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki."  ۗ   ۖ 
Qul 'Innī 'Akhāfu 'In `Aşaytu Rabbī `Adhāba Yawmin `Ažīmin 006-015 Kace: "Lalle ne nĩ inã tsõron azãbar Yini Mai girma, idan nã sãɓã wa Ubangijina."
Man Yuşraf `Anhu Yawma'idhin Faqad Raĥimahu  ۚ  Wa Dhalika Al-Fawzu Al-Mubīnu 006-016 "Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne,( Allah) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya."  ۚ 
Wa 'In Yamsaska Al-Lahu Biđurrin Falā Kāshifa Lahu 'Illā Huwa  ۖ  Wa 'In Yamsaska Bikhayrin Fahuwa `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 006-017 "Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi." ~  ۖ 
Wa Huwa Al-Qāhiru Fawqa `Ibādihi  ۚ  Wa Huwa Al-Ĥakīmu Al-Khabīru 006-018 "Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani."  ۚ 
Qul 'Ayyu Shay'in 'Akbaru Shahādatan  ۖ  Quli Al-Lahu  ۖ  Shahīdun Baynī Wa Baynakum  ۚ  Wa 'Ūĥiya 'Ilayya Hādhā Al-Qur'ānu Li'ndhirakum Bihi Wa Man Balagha  ۚ  'A'innakum Latash/hadūna 'Anna Ma`a Al-Lahi 'Ālihatan 'Ukhrá  ۚ  Qul Lā 'Ash/hadu  ۚ  Qul 'Innamā Huwa 'Ilahun Wāĥidun Wa 'Innanī Barī'un Mimmā Tushrikūna 006-019 Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa,kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar ( haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki."  ۖ   ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Al-Ladhīna 'Ātaynāhumu Al-Kitāba Ya`rifūnahu Kamā Ya`rifūna 'Abnā'ahumu  ۘ  Al-Ladhīna Khasirū 'Anfusahum Fahum Lā Yu'uminūna 006-020 Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.  ۘ 
Wa Man 'Ažlamu Mimmani Aftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan 'Aw Kadhdhaba Bi'āyātihi  ۗ  'Innahu Lā Yufliĥu Až-Žālimūna 006-021 Wãne ne mafi zãlunci daga wanda yake ƙirƙira karya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinsa? Lalle ne shĩ, azzalumai bã zã su ci nasara ba. ~  ۗ 
Wa Yawma Naĥshuruhum Jamī`āan Thumma Naqūlu Lilladhīna 'Ashrakū 'Ayna Shurakā'uukumu Al-Ladhīna Kuntum Taz`umūna 006-022 Kuma rãnar da Muka tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki: "Inã abõkan tãrayyarku waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?"
Thumma Lam Takun Fitnatuhum 'Illā 'An Qālū Wa Al-Lahi Rabbinā Mā Kunnā Mushrikīna 006-023 Sa'an nan kuma fitinarsu ba ta kasance ba, fãce dõmin sun ce: "Munã rantsuwa da Allah Ubangijinmu, ba mu kasance mãsu yin shirki ba."
Anžur Kayfa Kadhabū `Alá 'Anfusihim  ۚ  Wa Đalla `Anhum Mā Kānū Yaftarūna 006-024 Ka dũba yadda suka ƙaryata kansu! Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙira ƙaryarsa, ya ɓace daga gare su.  ۚ 
Wa Minhum Man Yastami`u 'Ilayka  ۖ  Wa Ja`alnā `Alá Qulūbihim 'Akinnatan 'An Yafqahūhu Wa Fī 'Ādhānihim Waqrāan Wa 'In  ۚ  Yaraw Kulla 'Āyatin Lā Yu'uminū Bihā Ĥattá  ۚ  'Idhā Jā'ūka Yujādilūnaka Yaqūlu Al-Ladhīna Kafarū 'In Hādhā 'Illā 'Asāţīru Al-'Awwalīna 006-025 Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa Hum Yanhawna `Anhu Wa Yan'awna `Anhu  ۖ  Wa 'In Yuhlikūna 'Illā 'Anfusahum Wa Mā Yash`urūna 006-026 Kuma sunã hanãwa daga gare shi, kuma sunã nĩsanta daga gare shi, kuma bã su halakarwa, fãce kansu, kuma bã su sansancẽwa.  ۖ 
Wa Law Tará 'Idh Wuqifū `Alá An-Nāri Faqālū Yā Laytanā Nuraddu Wa Lā Nukadhdhiba Bi'āyāti Rabbinā Wa Nakūna Mina Al-Mu'uminīna 006-027 Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu ƙaryata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai."
Bal Badā Lahum Mā Kānū Yukhfūna Min Qablu  ۖ  Wa Law Ruddū La`ādū Limā Nuhū `Anhu Wa 'Innahum Lakādhibūna 006-028 Ã'aha, abin da suka kasance suna ɓõyẽwa, daga gabãni, ya bayyana a gare su. Kuma dã an mayar da su, lalle dã sun kõma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.  ۖ 
Wa Qālū 'In Hiya 'Illā Ĥayātunā Ad-Dunyā Wa Mā Naĥnu Bimabthīna 006-029 Kuma suka ce: "Ba ta zama ba, fãce rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
Wa Law Tará 'Idh Wuqifū `Alá Rabbihim  ۚ  Qāla 'Alaysa Hādhā Bil-Ĥaqqi  ۚ  Qālū Balá Wa Rabbinā  ۚ  Qāla Fadhūqū Al-`Adhāba Bimā Kuntum Takfurūna 006-030 Kuma dã kana gani, a lõkacin da aka tsayar da su ga UbangiJinsu, Ya ce: "Ashe wannan bai zama gaskiya ba?" Suka ce: "Nã'am, muna rantsuwa da Ubangijinmu!" Ya ce: "To ku ɗanɗani azaba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci."  ۚ   ۚ   ۚ 
Qad Khasira Al-Ladhīna Kadhdhabū Biliqā'i Al-Lahi  ۖ  Ĥattá 'Idhā Jā'at/humu As-Sā`atu Baghtatan Qālū Yā Ĥasratanā `Alá Mā Farraţnā Fīhā Wa Hum Yaĥmilūna 'Awzārahum `Alá Žuhūrihim  ۚ  'Alā Sā'a Mā Yazirūna 006-031 Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara, har idan Sa'a ta je musu kwatsam, sai su ce: "Yã nadãmarmu a kan abin da muka yi sakaci a cikinta!" Alhãli kuwa su suna ɗaukar kayansu masu nauyi a kan bayayyakinsu. To, abin da suke ɗauka yã mũnana.  ۖ   ۚ 
Wa Mā Al-Ĥayāatu Ad-Dunyā 'Illā La`ibun Wa Lahwun  ۖ  Wa Lalddāru Al-'Ākhiratu Khayrun Lilladhīna Yattaqūna  ۗ  'Afalā Ta`qilūna 006-032 Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba, fãce wãsa da shagala, kuma lalle ne, Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa. Shin, ba za ku yi hankali ba?  ۖ   ۗ 
Qad Na`lamu 'Innahu Layaĥzunuka Al-Ladhī Yaqūlūna  ۖ  Fa'innahum Lā Yukadhdhibūnaka Wa Lakinna Až-Žālimīna Bi'āyāti Al-Lahi Yajĥadūna 006-033 Lalle ne Muna sani cewa haƙĩƙa, abin da suke faɗa yana ɓãta maka rai. To, lalle ne su, bã su ƙaryata ka (a cikin zukatansu ) kuma amma azzãlumai da ãyõyin Allah suke musu.  ۖ 
Wa Laqad Kudhdhibat Rusulun Min Qablika Faşabarū `Alá Mā Kudhdhibū Wa 'Ūdhū Ĥattá 'Atāhum Naşrunā  ۚ  Wa Lā Mubaddila Likalimāti Al-Lahi  ۚ  Wa Laqad Jā'aka Min Naba'i Al-Mursalīna 006-034 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an ƙaryata manzanni daga gabãninka, sai suka yi haƙuri a kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cũtar da su, har taimakonMu ya je musu, kuma babu mai musanyãwa ga kalmõmin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da kai) ya zo maka daga lãbãrin (annabãwan) farko.  ۚ   ۚ 
Wa 'In Kāna Kabura `Alayka 'I`rāđuhum Fa'ini Astaţa`ta 'An Tabtaghiya Nafaqāan Al-'Arđi 'Aw Sullamāan As-Samā'i Fata'tiyahum Bi'āyatin  ۚ  Wa Law Shā'a Al-Lahu Lajama`ahum `Alá Al-Hudá  ۚ  Falā Takūnanna Mina Al-Jāhilīna 006-035 Kuma idan yã kasance cewa finjirewarsu tã yi nauyi a gare ka, to, idan kana iyãwa, ka nemi wani ɓullõ a cikin ƙasa, kõ kuwa wani tsãni a cikin sama dõmin ka zo musu da wata ãyã, ( sai ka yi). Kuma dã Allah Yã so haƙĩƙa dã Yãtãra su a kan shiriya. Sabõda haka, kada lalle ka kasance daga jãhilai.  ۚ   ۚ 
'Innamā Yastajību Al-Ladhīna Yasma`ūna Wa  ۘ  Al-Mawtá Yab`athuhumu Al-Lahu Thumma 'Ilayhi Yurja`ūna 006-036 Abin sani kawai, waɗanda suke saurare ne suke karɓãwa, kuma matattu Allah Yake tãyar da su, Sa'an nan kuma zuwa gare Shi ake mayar da su.  ۘ 
Wa Qālū Lawlā Nuzzila `Alayhi 'Āyatun Min Rabbihi  ۚ  Qul 'Inna Al-Laha Qādirun `Alá 'An Yunazzila 'Āyatan Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna 006-037 Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da ãyã ba, a kansa, daga Ubangjinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Mai ĩko ne a kan Yasaukar da ãyã, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba."  ۚ 
Wa Mā Min Dābbatin Al-'Arđi Wa Lā Ţā'irin Yaţīru Bijanāĥayhi 'Illā 'Umamun 'Amthālukum  ۚ  Mā Farraţnā Fī Al-Kitābi Min Shay'in  ۚ  Thumma 'Ilá Rabbihim Yuĥsharūna 006-038 Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa kuma bãbu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa fãce al'umma ne misãlanku. Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi, sa'an nan kuma zuwa ga Ubangjinsu ake tãra su.  ۚ   ۚ 
Wa Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā Şummun Wa Bukmun  ۗ  Až-Žulumāti Man Yasha'i Al-Lahu Yuđlilhu Wa Man Yasha' Yaj`alhu `Alá Şirāţin Mustaqīmin 006-039 Kuma waɗanda suka ƙaryata gameda ãyõyinMu, kurãme ne kuma bebãye, acikin duffai. Wanda Allah Ya so Yanã ɓatar da shi, kuma wanda Ya so zai sanya shi a kan hanya madaidaiciya.  ۗ 
Qul 'Ara'aytakum 'In 'Atākum `Adhābu Al-Lahi 'Aw 'Atatkumu As-Sā`atu 'Aghayra Al-Lahi Tad`ūna 'In Kuntum Şādiqīna 006-040 Ka ce: "Shĩn, kun gan ku, idan azãbar Allah ta zo muku, kõ Sã'ar Tashin Kiyãma ta zo muku, shin wanin Allah kuke kira, idan dai kun kasance mãsu gaskiya?"
Bal 'Īyāhu Tad`ūna Fayakshifu Mā Tad`ūna 'Ilayhi 'In Shā'a Wa Tansawna Mā Tushrikūna 006-041 "Ã'a, Shĩ dai kuke kira sai Ya kuranye abin da kuke kira zuwa gare Shi, idan Ya so, kuma kunã mantãwar abin da kuke yin shirkin tãre da shi."
Wa Laqad 'Arsalnā 'Ilá 'Umamin Min Qablika Fa'akhadhnāhum Bil-Ba'sā'i Wa Ađ-Đarrā'i La`allahum Yatađarra`ūna 006-042 Kuma lalle Mun aika zuwa ga al'ummai daga gabãninka, sai Muka kãmã su da tsanani da cũta, tsammãninsu zã su ƙanƙan da kai,
Falawlā 'Idh Jā'ahum Ba'sunā Tađarra`ū Wa Lakin Qasat Qulūbuhum Wa Zayyana Lahumu Ash-Shayţānu Mā Kānū Ya`malūn 006-043 To, don me, a lõkacin da tsananinMu ya jẽ musu ba su yi tawãlu'i ba? Kuma amma zukatansu sun ƙẽƙashe kuma shaiɗan yã ƙawãta musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Falammā Nasū Mā Dhukkirū Bihi Fataĥnā `Alayhim 'Abwāba Kulli Shay'in Ĥattá 'Idhā Fariĥū Bimā 'Ūtū 'Akhadhnāhum Baghtatan Fa'idhā Hum Mublisūna 006-044 Sa'an nan kuma alõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũɗe, a kansu, ƙõfõfin dukkan kõme, har a lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yi tsuru tsuru.
Faquţi`a Dābiru Al-Qawmi Al-Ladhīna Žalamū Wa  ۚ  Al-Ĥamdu Lillahi Rabbi Al-`Ālamīna 006-045 Sai aka katse ƙarshen mutãnen, waɗanda suka yi zãlunci. Kuma gõdiya tã tabbata ga Allah Ubangijin tãlikai.  ۚ 
Qul 'Ara'aytum 'In 'Akhadha Al-Lahu Sam`akum Wa 'Abşārakum Wa Khatama `Alá Qulūbikum Man 'Ilahun Ghayru Al-Lahi Ya'tīkum Bihi  ۗ  Anžur Kayfa Nuşarrifu Al-'Āyāti Thumma Hum Yaşdifūna 006-046 Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya riƙe jinku, da gannanku, kuma Ya sanya hãtimi a kan zukãtanku, wane abin bauttãwa ne, wanin Allah, zai jẽ muku da shi?" Ka dũba yadda Muke sarrafaãyõyi, Sa'an nan kuma sũ, sunã finjirẽwa.  ۗ 
Qul 'Ara'aytakum 'In 'Atākum `Adhābu Al-Lahi Baghtatan 'Aw Jahratan Hal Yuhlaku 'Illā Al-Qawmu Až-Žālimūna 006-047 Ka ce: "Shin, kun gan ku, idan azãbar Allah ta jẽ muku, kwatsam, kõ kuwa bayyane, shin, anã halakãwa, fãce dai mutãne azzãlumai?"
Wa Mā Nursilu Al-Mursalīna 'Illā Mubashshirīna Wa Mundhirīna  ۖ  Faman 'Āmana Wa 'Aşlaĥa Falā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 006-048 Kuma bã Mu aikãwa da manzãnni fãce mãsu bayar da bushãra, kuma mãsu gargaɗi. To, wanda ya yi ĩmãni kuma yagyãra aiki, to, babu tsõro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki.  ۖ 
Wa Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā Yamassuhumu Al-`Adhābu Bimā Kānū Yafsuqūna 006-049 Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, azãba tanã shãfar su sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.
Qul Lā 'Aqūlu Lakum `InKhazā'inu Al-Lahi Wa Lā 'A`lamu Al-Ghayba Wa Lā 'Aqūlu Lakum 'Innī Malakun  ۖ  'In 'Attabi`u 'Illā Mā Yūĥá 'Ilayya  ۚ  Qul Hal Yastawī Al-'A`má Wa Al-Başīru  ۚ  'Afalā Tatafakkarūna 006-050 Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni." Ka ce: "Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni?"  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa 'Andhir Bihi Al-Ladhīna Yakhāfūna 'An Yuĥsharū 'Ilá Rabbihim  ۙ  Laysa Lahum Min Dūnihi Wa Līyun Wa Lā Shafī`un La`allahum Yattaqūna 006-051 Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masõyi baicinSa, kuma babu mai cẽto, tsammãninsu, sunã yin taƙawa.  ۙ 
Wa Lā Taţrudi Al-Ladhīna Yad`ūna Rabbahum Bil-Ghadāati Wa Al-`Ashīyi Yurīdūna Wajhahu Mā  ۖ  `Alayka Min Ĥisābihim Min Shay'in Wa Mā Min Ĥisābika `Alayhim Min Shay'in Fataţrudahum Fatakūna Mina Až-Žālimīna 006-052 Kuma kada ka kõri waɗanda suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.  ۖ 
Wa Kadhalika Fatannā Ba`đahum Biba`đin Liyaqūlū 'Ahā'uulā' Manna Al-Lahu `Alayhim Min Bayninā  ۗ  'Alaysa Al-Lahu Bi'a`lama Bish-Shākirīna 006-053 Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sãshensu da sãshe, dõmin su ce: "Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakãninmu?" Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga mãsu gõdiya?  ۗ 
Wa 'Idhā Jā'aka Al-Ladhīna Yu'uminūna Bi'āyātinā Faqul Salāmun `Alaykum  ۖ  Kataba Rabbukum `Alá Nafsihi Ar-Raĥmata  ۖ  'Annahu Man `Amila Minkum Sū'āan Bijahālatin Thumma Tāba Min Ba`dihi Wa 'Aşlaĥa Fa'annahu Ghafūrun Raĥīmun 006-054 Kuma idan waɗanda suke yin ĩmãni da ãyõyinMu suka jẽ maka, sai ka ce: "Aminci ya tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cẽwa lalle ne wanda ya aikata aibi da jãhilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tũba daga bãyansa, kuma ya gyãra, to, lalle Shi, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."  ۖ   ۖ 
Wa Kadhalika Nufaşşilu Al-'Āyāti Wa Litastabīna Sabīlu Al-Mujrimīna 006-055 Kuma kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, kuma dõmin hanyar mãsu laifi ta bayyana.
Qul 'Innī Nuhītu 'An 'A`buda Al-Ladhīna Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi  ۚ  Qul Lā 'Attabi`u 'Ahwā'akum  ۙ  Qad Đalaltu 'Idhāan Wa Mā 'Anā Mina Al-Muhtadīna 006-056 Ka ce: "Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin Allah." Ka cc: "Ba ni bin son zũciyõyinku, (dõmin in nã yi haka) lalle ne, nã ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba."  ۚ   ۙ 
Qul 'Innī `Alá Bayyinatin Min Rabbī Wa Kadhdhabtum Bihi  ۚ  Mā `Indī Mā Tasta`jilūna Bihi  ۚ  'Ini Al-Ĥukmu 'Illā Lillahi  ۖ  Yaquşşu Al-Ĥaqqa  ۖ  Wa Huwa Khayru Al-Fāşilīna 006-057 Ka ce: "Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke nẽman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin mãsu rarrabẽwa."  ۚ  ~  ۚ   ۖ   ۖ 
Qul Law 'Anna `Indī Mā Tasta`jilūna Bihi Laquđiya Al-'Amru Baynī Wa Baynakum Wa  ۗ  Allāhu 'A`lamu Biž-Žālimīna 006-058 Ka ce: "Lalle ne, dã a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugãwa da shi, haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin, a tsakãnina da tsakãninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga azzũlumai."  ۗ 
Wa `Indahu Mafātiĥu Al-Ghaybi Lā Ya`lamuhā 'Illā Huwa  ۚ  Wa Ya`lamu Mā Fī Al-Barri Wa Al-Baĥri  ۚ  Wa Mā Tasquţu Min Waraqatin 'Illā Ya`lamuhā Wa Lā Ĥabbatin Fī Žulumāti Al-'Arđi Wa Lā Raţbin Wa Lā Yā Bisin 'Illā Fī Kitābin Mubīnin 006-059 Kuma a wurinSa mabũdan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa.  ۚ   ۚ 
Wa Huwa Al-Ladhī Yatawaffākum Bil-Layli Wa Ya`lamu Mā Jaraĥtum Bin-Nahāri Thumma Yab`athukum Fīhi Liyuqđá 'Ajalun Musammáan  ۖ  Thumma 'Ilayhi Marji`ukum Thumma Yunabbi'ukum Bimā Kuntum Ta`malūna 006-060 Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.  ۖ 
Wa Huwa Al-Qāhiru Fawqa `Ibādihi  ۖ  Wa Yursilu `Alaykum Ĥafažatan Ĥattá 'Idhā Jā'a 'Aĥadakumu Al-Mawtu Tawaffat/hu Rusulunā Wa Hum Lā Yufarrūna 006-061 Kuma Shĩ ne Mai rinjãya bisa ga bãyinSa, kuma Yanã aikan mãsu tsaro a kanku, har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayanku, sai manzanninMu su karɓi ransa alhãli su ba su yin sakaci.  ۖ 
Thumma Ruddū 'Ilá Al-Lahi Mawlāhumu Al-Ĥaqqi  ۚ  'Alā Lahu Al-Ĥukmu Wa Huwa 'Asra`u Al-Ĥāsibīna 006-062 Sa'an nan kuma a mayar da su zuwa ga Allah Ubangjinsu na gaskiya. To! A gare shi hukunci yake, kuma Shi ne Mafi gaugãwar mãsu bincike.  ۚ 
Qul Man Yunajjīkum Min Žulumāti Al-Barri Wa Al-Baĥri Tad`ūnahu Tađarru`āan Wa Khufyatan La'in 'Anjānā Min Hadhihi Lanakūnanna Mina Ash-Shākirīna 006-063 Ka ce: "Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kunã kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓõye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan (masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga mãsu gõdiya?'"
Quli Al-Lahu Yunajjīkum Minhā Wa Min Kulli Karbin Thumma 'Antum Tushrikūna 006-064 Ka ce: "Allah ne Yake tsĩrar da ku daga gare ta, kuma daga dukan baƙin ciki sa'an nan kuma ku, kunã yin shirki!"
Qul Huwa Al-Qādiru `Alá 'An Yab`atha `Alaykum `Adhābāan Min Fawqikum 'Aw Min Taĥti 'Arjulikum 'Aw Yalbisakum Shiya`āan Wa Yudhīqa Ba`đakum Ba'sa Ba`đin  ۗ  Anžur Kayfa Nuşarrifu Al-'Āyāti La`allahum Yafqahūna 006-065 Ka ce: "Shĩ ne Mai ĩko a kan Ya aika da wata azãba a kanku daga bisanku, kõ kuwa daga ƙarƙashin ƙafãfunku, kõ kuwa Ya gauraya ku ƙungiyõyi, kuma Ya ɗanɗanã wa sãshenku masĩfar sãshe." "Ka dũba yadda Muke sarrafa ãyõyi, tsammãninsu sunã fahimta!"  ۗ 
Wa Kadhdhaba Bihi Qawmuka Wa Huwa Al-Ĥaqqu  ۚ  Qul Lastu `Alaykum Biwakīlin 006-066 Kuma mutãnenka sun ƙaryata (ka) game da Shi, alhãli kuwa Shi ne gaskiya. Ka ce: "Nĩban zama wakĩli a kanku ba."  ۚ 
Likulli Naba'iin Mustaqarrun  ۚ  Wa Sawfa Ta`lamūna 006-067 "Akwai matabbata ga dukan lãbãri, kuma zã ku sani."  ۚ 
Wa 'Idhā Ra'ayta Al-Ladhīna Yakhūđūna Fī 'Āyātinā Fa'a`riđ `Anhum Ĥattá Yakhūđū Fī Ĥadīthin Ghayrihi  ۚ  Wa 'Immā Yunsiyannaka Ash-Shayţānu Falā Taq`ud Ba`da Adh-Dhikrá Ma`a Al-Qawmi Až-Žālimīna 006-068 Kuma idan kã ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kũtsa a cikin wani lãbãri waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunãwa tãre da mutãne azzãlumai.  ۚ 
Wa Mā `Alá Al-Ladhīna Yattaqūna Min Ĥisābihim Min Shay'in Wa Lakin Dhikrá La`allahum Yattaqūna 006-069 Kuma babu wani abu daga hisãbinsu (mãsu kutsãwa a cikin ayõyin Allah (a kan mãsu taƙawa amma akwai tunãtarwa (a kansu), tsãmmãninsu (mãsu kutsawar) zã su yi taƙawa.
Wa Dhari Al-Ladhīna Attakhadhū Dīnahum La`ibāan Wa Lahwan Wa Gharrat/humu Al-Ĥayāatu Ad-Dunyā  ۚ  Wa Dhakkir Bihi 'An Tubsala Nafsun Bimā Kasabat Laysa Lahā Min Dūni Al-Lahi Wa Līyun Wa Lā Shafī`un Wa 'In Ta`dil Kulla `Adlin Lā Yu'ukhadh Minhā  ۗ  'Ūlā'ika Al-Ladhīna 'Ubsilū Bimā Kasabū  ۖ  Lahum Sharābun Min Ĥamīmin Wa `Adhābun 'Alīmun Bimā Kānū Yakfurūna 006-070 Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wãsa da wargi alhãli rãyuwar dũniya tã rũɗe su, kuma ka tunãtar game da shi (Alƙur'ãni): Kada a jẽfa raia cikin halaka sabõda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai cẽto; kuma, kõ ya daidaita dukan fansa, ba zã a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammãni sabõda abin da suka tsirfanta; sunã da wani abin shã daga ruwan zãfi, da wata azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.  ۚ  ~  ۗ   ۖ 
Qul 'Anad`ū Min Dūni Al-Lahi Mā Lā Yanfa`unā Wa Lā Yađurrunā Wa Nuraddu `Alá 'A`qābinā Ba`da 'Idh Hadānā Al-Lahu Kālladhī Astahwat/hu Ash-Shayāţīnu Fī Al-'Arđi Ĥayrāna Lahu 'Aşĥābun Yad`ūnahu 'Ilá Al-Hudá A'tinā  ۗ  Qul 'Inna Hudá Al-Lahi Huwa Al-Hudá  ۖ  Wa 'Umirnā Linuslima Lirabbi Al-`Ālamīna 006-071 Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'" Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai." ~ ~  ۗ   ۖ 
Wa 'An 'Aqīmū Aş-Şalāata Wa Attaqūhu  ۚ  Wa Huwa Al-Ladhī 'Ilayhi Tuĥsharūna 006-072 "Kuma (an ce mana): Ku tsai da salla kuma ku bĩ shi (Allah) da taƙawa kuma Shi ne wanda Yake zuwa gare Shi ake tãra ku."  ۚ 
Wa Huwa Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Bil-Ĥaqqi  ۖ  Wa Yawma Yaqūlu Kun Fayakūnu  ۚ  Qawluhu Al-Ĥaqqu  ۚ  Wa Lahu Al-Mulku Yawma Yunfakhu Fī Aş-Şūri  ۚ  `Ālimu Al-Ghaybi Wa Ash-Shahādati  ۚ  Wa Huwa Al-Ĥakīmu Al-Khabīr 006-073 Kuma Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da mulkinSa, kuma a Rãnar da Yake cẽwa: "Ka kasance," sai abu ya yi ta kasancẽwa. MaganarSa ce gaskiya, kuma gare Shi mulki yake a Rãnar da ake bũsa a cikin ƙaho. Masanin fake da bayyane ne, Kuma Shi ne Mai hikima Masani.  ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa 'Idh Qāla 'Ibrāhīmu Li'abīhi 'Āzara 'Atattakhidhu 'Aşnāmāan 'Ālihatan  ۖ  'Innī 'Arāka Wa Qawmaka Fī Đalālin Mubīnin 006-074 Kuma a lõkacin da Ibrãhĩma ya ce wa ubansa Ãzara: "Shin, kanã riƙon gumãka abũbuwan bautãwa? Lalle nĩ, inã ganin ka kai damutã- nenka, a cikin ɓata bayyananniya."  ۖ 
Wa Kadhalika Nurī 'Ibrāhīma Malakūta As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Liyakūna Mina Al-Mūqinīna 006-075 Kuma kamar wancan ne, Muke nũna wa Ibrãhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dõmin ya kasance daga mãsu yaƙĩni.
Falammā Janna `Alayhi Al-Laylu Ra'á Kawkabāan  ۖ  Qāla Hādhā Rabbī  ۖ  Falammā 'Afala Qāla Lā 'Uĥibbu Al-'Āfilīna 006-076 To, a lõkacin da dare ya rufe a kansa, ya ga wani taurãro, ya ce: "Wannan ne, ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya faɗi, ya ce: "Ba ni son mãsu fãɗuwa."  ۖ   ۖ 
Falammā Ra'á Al-Qamara Bāzighāan Qāla Hādhā Rabbī  ۖ  Falammā 'Afala Qāla La'in Lam Yahdinī Rabbī La'akūnanna Mina Al-Qawmi Ađ-Đāllīna 006-077 Sa'an nan a lõkacin da ya ga watã yanã mai bayyana, ya ce: "Wannan ne Ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya fãɗi, ya ce: "Lalle ne idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa, inã kasancẽwa daga mutãne ɓatattu."  ۖ 
Falammā Ra'á Ash-Shamsa Bāzighatan Qāla Hādhā Rabbī Hādhā 'Akbaru  ۖ  Falammā 'Afalat Qāla Yā Qawmi 'Innī Barī'un Mimmā Tushrikūna 006-078 Sa'an nan a lõkacin da ya ga rãnã tanã bayyana, ya ce: "Wannan shĩ ne Ubangijina, wannan ne mafi girma?" Sa'an nan a lõkacin da ta fãɗi, ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki."  ۖ 
'Innī Wajjahtu Wajhiya Lilladhī Faţara As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Ĥanīfāan Wa Mā  ۖ  'Anā Mina Al-Mushrikīna 006-079 "Lalle ne nĩ, na fuskantar da fuskata ga wanda, Ya ƙãga halittar sammai da ƙasa, inã mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bã ni cikin mãsu shirki."  ۖ 
Wa Ĥājjahu Qawmuhu  ۚ  Qāla 'Atuĥājjūnī Fī Al-Lahi Wa Qad Hadāni  ۚ  Wa Lā 'Akhāfu Mā Tushrikūna Bihi 'Illā 'An Yashā'a Rabbī Shay'āan  ۗ  Wasi`a Rabbī Kulla Shay'in `Ilmāan  ۗ  'Afalā Tatadhakkarūna 006-080 Kuma mutãnensa suka yi musu da shi. Ya ce: "Shin kunã musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhãli kuwa Yã shiryai da ni? Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, fãce idan Ubangijina Yã so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõme da ilmi. Shin, ba zã ku yi tunãni ba?"  ۚ   ۚ  ~  ۗ   ۗ 
Wa Kayfa 'Akhāfu Mā 'Ashraktum Wa Lā Takhāfūna 'Annakum 'Ashraktum Bil-Lahi Mā Lam Yunazzil Bihi `Alaykum Sulţānāan  ۚ  Fa'ayyu Al-Farīqayni 'Aĥaqqu Bil-'Amni  ۖ  'In Kuntum Ta`lamūna 006-081 "Kuma yãyã nake jin tsõron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsõron cẽwa lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane ɓangare daga sãshen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kunã sani?"  ۚ   ۖ 
Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Lam Yalbisū 'Īmānahum Bižulmin 'Ūlā'ika Lahumu Al-'Amnu Wa Hum Muhtadūna 006-082 "Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma ba su gauraya ĩmãninsu da zãlunci ba, waɗannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu."
Wa Tilka Ĥujjatunā 'Ātaynāhā 'Ibrāhīma `Alá Qawmihi  ۚ  Narfa`u Darajātin Man Nashā'u  ۗ  'Inna Rabbaka Ĥakīmun `Alīmun 006-083 Kuma waccan ita ce hujjarMu, Mun bayãr da ita ga Ibrãhĩma a kan mutãnensa. Munã ɗaukaka wanda Muka so da darajõji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani.  ۚ   ۗ 
Wa Wahabnā Lahu 'Isĥāqa Wa Ya`qūba  ۚ  Kullāan Hadaynā  ۚ  Wa Nūĥāan Hadaynā Min Qablu  ۖ  Wa Min Dhurrīyatihi Dāwūda Wa Sulaymāna Wa 'Ayyūba Wa Yūsufa Wa Mūsá Wa Hārūna  ۚ  Wa Kadhalika Naj Al-Muĥsinīna 006-084 Kuma Muka bã shi Is'hãƙa da Yãƙubu, dukansu Mun shiryar, kuma Nũhu Mun shiryar da shi a gabãni, kuma daga zuriyarsa akwai Dãwũda da Sulaimãnu da Ayyũba, da Yũsufu da Mũsã da Hãrũna, kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. ~  ۚ   ۚ   ۖ   ۚ 
Wa Zakarīyā Wa Yaĥyá Wa `Īsá Wa 'Ilyāsa  ۖ  Kullun Mina Aş-Şāliĥīna 006-085 Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Ilyasu dukansu daga sãlihai suke.  ۖ 
Wa 'Ismā`īla Wa Al-Yasa`a Wa Yūnus Wa Lūţāan  ۚ  Wa Kullāan Fađđalnā `Alá Al-`Ālamīna 006-086 Da Ismã'la da Ilyasa, a da Yũnusa da Luɗu, kuma dukansu Mun fĩfĩtã su a kan tãlikai.  ۚ 
Wa Min 'Ābā'ihim Wa Dhurrīyātihim Wa 'Ikhwānihim  ۖ  Wa Ajtabaynāhum Wa Hadaynāhum 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin 006-087 Kuma daga ubanninsu, da zũriyarsu, da 'yan'uwansu, kuma Muka zãɓe su, kuma Muka shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.  ۖ 
Dhālika Hudá Al-Lahi Yahdī Bihi Man Yashā'u Min `Ibādihi  ۚ  Wa Law 'Ashrakū Laĥabiţa `Anhum Mā Kānū Ya`malūna 006-088 Wancan ne shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Yake so daga bayinSa. Kuma dã sun yi shirki dã haƙĩƙa abin da suka kasance sunã ,aikatãwa yã lãlãce.  ۚ 
'Ūlā'ika Al-Ladhīna 'Ātaynāhumu Al-Kitāba Wa Al-Ĥukma Wa An-Nubūwata  ۚ  Fa'in Yakfur Bihā Hā'uulā' Faqad Wa Kkalnā Bihā Qawmāan Laysū Bihā Bikāfirīna 006-089 Waɗancan ne waɗanda Muka bai wa Littãfi da hukunci da Annabci. To idan waɗannan (mutãne ) sun kãfirta da ita, to, haƙĩƙa, Mun wakkala wasu mutãne gare ta, ba su zama game da ita kãfirai ba.  ۚ 
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Hadá Al-Lahu  ۖ  Fabihudāhumu Aqtadihi  ۗ  Qul Lā 'As'alukum `Alayhi 'Ajrāan  ۖ  'In Huwa 'Illā Dhikrá Lil`ālamīna 006-090 Waɗancan ne Allah Ya shiryar, sabõda haka ka yi kõyi da shiryarsu. Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijãra. Shĩ (Alƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ga tãlikai."  ۖ   ۗ   ۖ 
Wa Mā Qadarū Al-Laha Ĥaqqa Qadrihi 'Idh Qālū Mā 'Anzala Al-Lahu `Alá Basharin Min Shay'in  ۗ  Qul Man 'Anzala Al-Kitāba Al-Ladhī Jā'a Bihi Mūsá Nūrāan Wa Hudáan Lilnnāsi  ۖ  Taj`alūnahu Qarāţīsa Tubdūnahā Wa Tukhfūna Kathīrāan  ۖ  Wa `Ullimtum Mā Lam Ta`lamū 'Antum Wa Lā 'Ābā'uukum  ۖ  Quli Al-Lahu  ۖ  Thumma DharhumKhawđihim Yal`abūna 006-091 Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lõkacin da suka ce: "Allah bai saukar da kõme ba ga wani mutum." Ka ce: "Wãne ne ya saukar da Littãfi wanda Mũsã ya zo da shi, yanã haske da shiriya ga mutãne, kunã sanya shi takardu, kũna bayyana su, kuma kunã ɓõye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah," sa'an nan ka bar su a cikin sharhõliyarsu sunã wãsã. ~  ۗ   ۖ   ۖ   ۖ   ۖ 
Wa Hadhā Kitābun 'Anzalnāhu Mubārakun Muşaddiqu Al-Ladhī Bayna Yadayhi Wa Litundhira 'Umma Al-Qurá Wa Man Ĥawlahā Wa  ۚ  Al-Ladhīna Yu'uminūna Bil-'Ākhirati Yu'uminūna Bihi  ۖ  Wa Hum `Alá Şalātihim Yuĥāfižūna 006-092 Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda yake a gabansa ne, kuma dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda yake gefenta. Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da Lãhira sunã ĩmãni da shi (Alƙur'ãni), kuma sũ, a kan sallarsu, sunã tsarẽwa.  ۚ   ۖ 
Wa Man 'Ažlamu Mimmani Aftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan 'Aw Qāla 'Ūĥiya 'Ilayya Wa Lam Yūĥa 'Ilayhi Shay'un Wa Man Qāla Sa'unzilu Mithla Mā 'Anzala Al-Lahu  ۗ  Wa Law Tará 'Idhi Až-Žālimūna Fī Ghamarāti Al-Mawti Wa Al-Malā'ikatu Bāsiţū 'Aydīhim 'Akhrijū 'Anfusakumu  ۖ  Al-Yawma Tujzawna `Adhāba Al-Hūni Bimā Kuntum Taqūlūna `Alá Al-Lahi Ghayra Al-Ĥaqqi Wa Kuntum `An 'Āyātihi Tastakbirūna 006-093 Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai."  ۗ   ۖ 
Wa Laqad Ji'tumūnā Furādá Kamā Khalaqnākum 'Awwala Marratin Wa TaraktumKhawwalnākum Warā'a Žuhūrikum  ۖ  Wa Mā Nará Ma`akum Shufa`ā'akumu Al-Ladhīna Za`amtum 'Annahum Fīkum Shurakā'u  ۚ  Laqad Taqaţţa`a Baynakum Wa Đalla `Ankum Mā Kuntum Taz`umūna 006-094 Kuma lalle ne haƙĩƙa, kun zo Mana ɗai ɗai, kamar yadda Muka halittã ku a farkon lõkaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma ba Mu gani a tãre da kũ ba, macẽtanku waɗanda kuka riya cẽwa lalle ne sũ, a cikinku mãsu tãrayya ne. Lalle ne, hãƙĩƙa,kõme yã yanyanke a tsakãninku, kuma abin da kuka kasance kunã riyãwa ya ɓace daga gare ku.  ۖ   ۚ 
'Inna Al-Laha Fāliqu Al-Ĥabbi Wa An-Nawá  ۖ  Yukhriju Al-Ĥayya Mina Al-Mayyiti Wa Mukhriju Al-Mayyiti Mina Al-Ĥayyi  ۚ  Dhalikumu Al-Lahu  ۖ  Fa'anná Tu'ufakūna 006-095 Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai, wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?  ۖ   ۚ   ۖ 
Fāliqu Al-'Işbāĥi Wa Ja`ala Al-Layla Sakanāan Wa Ash-Shamsa Wa Al-Qamara Ĥusbānāan  ۚ  Dhālika Taqdīru Al-`Azīzi Al-`Alīmi 006-096 Mai tsãgẽwar sãfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da rãna da watã a bisa lissãfi. vwannan ne ƙaddarãwar Mabuwãyi Masani.  ۚ 
Wa Huwa Al-Ladhī Ja`ala Lakumu An-Nujūma Litahtadū Bihā Fī Žulumāti Al-Barri Wa Al-Baĥri  ۗ  Qad Faşşalnā Al-'Āyāti Liqawmin Ya`lamūna 006-097 Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.  ۗ 
Wa Huwa Al-Ladhī 'Ansha'akum Min Nafsin Wāĥidatin Famustaqarrun Wa Mustawda`un  ۗ  Qad Faşşalnā Al-'Āyāti Liqawmin Yafqahūn 006-098 Kuma Shi ne Ya ƙãga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke fahimta.  ۗ 
Wa Huwa Al-Ladhī 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an Fa'akhrajnā Bihi Nabāta Kulli Shay'in Fa'akhrajnā Minhu Khađirāan Nukhriju Minhu Ĥabbāan Mutarākibāan Wa Mina An-Nakhli Min Ţal`ihā Qinwānun Dāniyatun Wa Jannātin Min 'A`nābin Wa Az-Zaytūna Wa Ar-Rummāna Mushtabihāan Wa Ghayra Mutashābihin  ۗ  Anžurū 'Ilá Thamarihi 'Idhā 'Athmara Wa Yan`ihi  ۚ  'Inna Fī Dhālikum La'āyātin Liqawmin Yu'uminūna 006-099 Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren), kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni.  ۗ  ~ ~  ۚ 
Wa Ja`alū Lillahi Shurakā'a Al-Jinna Wa Khalaqahum  ۖ  Wa Kharaqū Lahu Banīna Wa Banātin Bighayri `Ilmin  ۚ  Subĥānahu Wa Ta`ālá `Ammā Yaşifūna 006-100 Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa.  ۖ   ۚ 
Badī`u As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  'Anná Yakūnu Lahu Waladun Wa Lam Takun Lahu Şāĥibatun  ۖ  Wa Khalaqa Kulla Shay'in  ۖ  Wa Huwa Bikulli Shay'in `Alīmun 006-101 Mafarin halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?  ۖ   ۖ   ۖ 
Dhalikumu Al-Lahu Rabbukum  ۖ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  Khāliqu Kulli Shay'in Fā`budūhu  ۚ  Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Wa Kīlun 006-102 Wancan ne Allah Ubangijinku. Bãbu wani abin bautãwa fãce Shĩ, Mahaliccin dukan kõme. Sabõda haka ku bauta Masa kuma Shi ne wakĩli a kan dukan, kõme.  ۖ  ~  ۖ   ۚ 
Lā Tudrikuhu Al-'Abşāru Wa Huwa Yudriku Al-'Abşāra  ۖ  Wa Huwa Al-Laţīfu Al-Khabīr 006-103 Gannai bã su iya riskuwarSa, kuma Shĩ Yanã riskuwar gannai, kuma Shĩ ne Mai tausasãwa,Masani.  ۖ 
Qad Jā'akum Başā'iru Min Rabbikum  ۖ  Faman 'Abşara Falinafsihi  ۖ  Wa Man `Amiya Fa`alayhā  ۚ  Wa Mā 'Anā `Alaykum Biĥafīžin 006-104 Lalle ne abũbuwan lũra sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to, dõmin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yanã a kansa, kuma nĩ, a kanku, bã mai tsaro ba ne.  ۖ   ۖ   ۚ 
Wa Kadhalika Nuşarrifu Al-'Āyāti Wa Liyaqūlū Darasta Wa Linubayyinahu Liqawmin Ya`lamūna 006-105 Kamar wannan ne Muke sarrafa ãyõyi, kuma dõmin su ce: "Kã karanta!" Kuma dõmin Mu bayyana shi ga mutãne waɗanda sunã sani.
Attabi` Mā 'Ūĥiya 'Ilayka Min Rabbika  ۖ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  Wa 'A`riđ `Ani Al-Mushrikīna 006-106 Ka bi abin da aka yi wahayi zuwa gare ka daga Ubangijinka; babu wani abin bautãwa fãce Shi, kuma ka bijire daga mãsu shirki.  ۖ  ~  ۖ 
Wa Law Shā'a Al-Lahu Mā 'Ashrakū  ۗ  Wa Mā Ja`alnāka `Alayhim Ĥafīžāan  ۖ  Wa Mā 'Anta `Alayhim Biwakīlin 006-107 Kuma dã Allah Yã so, dã ba su yi shirki ba, kuma ba Mu, sanya ka mai tsaro a kansu ba, kuma ba kai ne wakĩli a kansu ba.  ۗ   ۖ 
Wa Lā Tasubbū Al-Ladhīna Yad`ūna Min Dūni Al-Lahi Fayasubbū Al-Laha `Adwan Bighayri `Ilmin  ۗ  Kadhālika Zayyannā Likulli 'Ummatin `Amalahum Thumma 'Ilá Rabbihim Marji`uhum Fayunabbi'uhum Bimā Kānū Ya`malūna 006-108 Kuma kada ku zãgi waɗanda suke kira, baicin Allah, har su zãgi Allah bisa zãlunci, ba, da ilmi ba. Kamar wannan ne Muka ƙawãta ga kõwace al'umma aikinsu, sa'an nan zuwa ga Ubangijinsu makõmarsu take, sa'an nan Ya ba su lãbari da abin da suka kasance sunã aikatãwa.  ۗ 
Wa 'Aqsamū Bil-Lahi Jahda 'Aymānihim La'in Jā'at/hum 'Āyatun Layu'uminunna Bihā  ۚ  Qul 'Innamā Al-'Āyātu `Inda Al-Lahi  ۖ  Wa Mā Yush`irukum 'Annahā 'Idhā Jā'at Lā Yu'uminūna 006-109 Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwõyinsu (cẽwa) lalle ne idan wata ãyã ta jẽmusu, haƙĩƙa, sunã yin ĩmãni da ita. Ka ce: "Abin sani kawai, ãyõyi a wurin Allah suke. Kuma mẽne nezai sanya ku ku sansance cẽwa,lalle ne su, idan ãyõyin sun je, ba zã su yi ĩmãni ba?"  ۚ   ۖ 
Wa Nuqallibu 'Af'idatahum Wa 'Abşārahum Kamā Lam Yu'uminū Bihi 'Awwala Marratin Wa Nadharuhum Fī Ţughyānihim Ya`mahūna 006-110 Kuma Munã jujjũya zukãtansu da ganansu, kamar yadda ba su yi ĩmãni da shi ba a farkon lõkaci kuma Munã barin su a cikin kũtsãwarsu, sunã ɗĩmuwa. ~
Wa Law 'Annanā Nazzalnā 'Ilayhimu Al-Malā'ikata Wa Kallamahumu Al-Mawtá Wa Ĥasharnā `Alayhim Kulla Shay'in Qubulāan Mā Kānū Liyu'uminū 'Illā 'An Yashā'a Al-Lahu Wa Lakinna 'Aktharahum Yajhalūna 006-111 Kuma dã a ce, lalle Mũ Mun saukar da Malã'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tãra dukkan kõme a kansu, gungu-gungu, ba su kasance sunã iya yin ĩmãni ba, sai fa idan Allah Yã so, Kuma amma mafi yawansu sunã jãhiltar haka.
Wa Kadhalika Ja`alnā Likulli Nabīyin `Adūwāan Shayāţīna Al-'Insi Wa Al-Jinni Yūĥī Ba`đuhum 'Ilá Ba`đin Zukhrufa Al-Qawli Ghurūrāan  ۚ  Wa Law Shā'a Rabbuka Mā Fa`alūhu  ۖ  Fadharhum Wa Mā Yaftarūna 006-112 Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa.  ۚ   ۖ 
Wa Litaşghá 'Ilayhi 'Af'idatu Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati Wa Liyarđawhu Wa Liyaqtarifū Mā Hum Muqtarifūna 006-113 Kuma dõmin zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata.
'Afaghayra Al-Lahi 'Abtaghī Ĥakamāan Wa Huwa Al-Ladhī 'Anzala 'Ilaykumu Al-Kitāba Mufaşşalāan Wa  ۚ  Al-Ladhīna 'Ātaynāhumu Al-Kitāba Ya`lamūna 'Annahu Munazzalun Min Rabbika Bil-Ĥaqqi  ۖ  Falā Takūnanna Mina Al-Mumtarīna 006-114 Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi (Alƙur'ãni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakka.  ۚ   ۖ 
Wa Tammat Kalimatu Rabbika Şidqāan Wa `Adlāan  ۚ  Lā Mubaddila Likalimātihi  ۚ  Wa Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu 006-115 Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.  ۚ   ۚ 
Wa 'In Tuţi` 'Akthara Man Al-'Arđi Yuđillūka `An Sabīli Al-Lahi  ۚ  'In Yattabi`ūna 'Illā Až-Žanna Wa 'In Hum 'Illā Yakhruşūna 006-116 Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah. Ba su bin kõme sai fãce ƙaddari-faɗi suke yi.  ۚ 
'Inna Rabbaka Huwa 'A`lamu Man Yađillu `An Sabīlihi  ۖ  Wa Huwa 'A`lamu Bil-Muhtadīna 006-117 Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda yake ɓacẽwa daga hanyarsa kuma Shi ne mafi sani ga masu shiryuwa.  ۖ 
Fakulū Mimmā Dhukira Asmu Al-Lahi `Alayhi 'In Kuntum Bi'āyātihi Mu'uminīna 006-118 Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa.
Wa Mā Lakum 'Allā Ta'kulū Mimmā Dhukira Asmu Al-Lahi `Alayhi Wa Qad Faşşala Lakum Mā Ĥarrama `Alaykum 'Illā Mā Ađţurirtum 'Ilayhi  ۗ  Wa 'Inna Kathīrāan Layuđillūna Bi'ahwā'ihim Bighayri `Ilmin  ۗ  'Inna Rabbaka Huwa 'A`lamu Bil-Mu`tadīna 006-119 Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã zã ku ci ba daga abin da aka ambaci sũnan Allah a kansa,alhãli kuwa, haƙĩƙa, Ya rarrabe, muku daki-daki, abin da Ya haramta a kanku, fãce fa abin da aka bukãtar da ku bisa lalũra zuwa gare shi? Kuma lalle ne mãsu yawa sunã ɓatarwa, da son zũciyõyinsu, ba da wani ilmi ba. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga mãsu ta'addi.  ۗ   ۗ 
Wa Dharū Žāhira Al-'Ithmi Wa Bāţinahu  ۚ  'Inna Al-Ladhīna Yaksibūna Al-'Ithma Sayujzawna Bimā Kānū Yaqtarifūna 006-120 Kuma ku bar bayyanannen zunubi da ɓõyayyensa. Lalle ne waɗanda suke tsiwurwurin zunubi za a sãka musu da abin da suka kasance sunã kamfata. ~  ۚ 
Wa Lā Ta'kulū Mimmā Lam Yudhkari Asmu Al-Lahi `Alayhi Wa 'Innahu Lafisqun  ۗ  Wa 'Inna Ash-Shayāţīna Layūĥūna 'Ilá 'Awliyā'ihim Liyujādilūkum  ۖ  Wa 'In 'Aţa`tumūhum 'Innakum Lamushrikūna 006-121 Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa . Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne.  ۗ   ۖ 
'Awaman Kāna Maytāan Fa'aĥyaynāhu Wa Ja`alnā Lahu Nūrāan Yamshī Bihi Fī An-Nāsi Kaman Mathaluhu Fī Až-Žulumāti Laysa Bikhārijin Minhā  ۚ  Kadhālika Zuyyina Lilkāfirīna Mā Kānū Ya`malūna 006-122 Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya wani haske dõminsa, yanã tafiya da shi, yanã zama kamar wanda misãlinsa yanã cikin duffai, shĩ kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka ƙawãta wa kãfirai abin da suka kasance sunã aikatãwa.  ۚ 
Wa Kadhalika Ja`alnā Fī Kulli Qaryatin 'Akābira Mujrimīhā Liyamkurū Fīhā  ۖ  Wa Mā Yamkurūna 'Illā Bi'anfusihim Wa Mā Yash`urūna 006-123 Kuma kamar wancan ne Mun sanya a cikin kõwace alƙarya, shugabanni sũ ne mãsu laifinta dõmin su yi mãkirci a cikinta, alhãli kuwa ba su yin makirci fãce ga rayukansu, kuma ba su sansancẽwa.  ۖ 
Wa 'Idhā Jā'at/hum 'Āyatun Qālū Lan Nu'umina Ĥattá Nu'utá Mithla Mā 'Ūtiya Rusulu Al-Lahi  ۘ  Al-Lahu 'A`lamu Ĥaythu Yaj`alu Risālatahu  ۗ  Sayuşību Al-Ladhīna 'Ajramū Şaghārun `Inda Al-Lahi Wa `Adhābun Shadīdun Bimā Kānū Yamkurūna 006-124 Kuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: "Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa. Wani wulaƙanci a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi waɗanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci.  ۘ   ۗ 
Faman Yuridi Al-Lahu 'An Yahdiyahu Yashraĥ Şadrahu Lil'islāmi  ۖ  Wa Man Yurid 'An Yuđillahu Yaj`al Şadrahu Đayyiqāan Ĥarajāan Ka'annamā Yaşşa``adu Fī As-Samā'i  ۚ  Kadhālika Yaj`alu Al-Lahu Ar-Rijsa `Alá Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna 006-125 Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni.  ۖ   ۚ 
Wa Hadhā Şirāţu Rabbika Mustaqīmāan  ۗ  Qad Faşşalnā Al-'Āyāti Liqawmin Yadhdhakkarūna 006-126 Wannan ita ce hanya ta Ubangijinka madaidaiciya. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki ga mutãne mãsu karɓar tunãtarwa.  ۗ 
Lahum Dāru As-Salāmi `Inda Rabbihim  ۖ  Wa Huwa Walīyuhum Bimā Kānū Ya`malūna 006-127 Sunã da gidan aminci a wurin Ubangjinsu, kuma Shĩ ne Majiɓincinsu, sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.  ۖ 
Wa Yawma Yaĥshuruhum Jamī`āan Yā Ma`shara Al-Jinni Qadi Astakthartum Mina Al-'Insi  ۖ  Wa Qāla 'Awliyā'uuhum Mina Al-'Insi Rabbanā Astamta`a Ba`đunā Biba`đin Wa Balaghnā 'Ajalanā Al-Ladhī 'Ajjalta Lanā  ۚ  Qāla An-Nāru Mathwākum Khālidīna Fīhā 'Illā Mā Shā'a Al-Lahu  ۗ  'Inna Rabbaka Ĥakīmun `Alīmun 006-128 Kuma rãnar da yake tãra su gaba ɗaya (Yanã cẽwa): "Yã jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne." Kuma majiɓantansu daga mutãne suka ce: "Yã Ubangjinmu! Sãshenmu ya ji dãɗi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!" (Allah) Ya ce: "Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani."  ۖ   ۚ   ۗ 
Wa Kadhalika Nuwallī Ba`đa Až-Žālimīna Ba`đāan Bimā Kānū Yaksibūna 006-129 Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa.
Yā Ma`shara Al-Jinni Wa Al-'Insi 'Alam Ya'tikum Rusulun Minkum Yaquşşūna `Alaykum 'Āyā Tī Wa Yundhirūnakum Liqā'a Yawmikum  ۚ  Hādhā Qālū Shahidnā `Alá  ۖ  'Anfusinā Wa Gharrat/humu Al-Ĥayā Atu Ad-Dunyā Wa Shahidū `Alá 'Anfusihim 'Annahum Kānū Kāfirīna 006-130 Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kãwunanmu." Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai.  ۚ   ۖ 
Dhālika 'An Lam Yakun Rabbuka Muhlika Al-Qurá Bižulmin Wa 'Ahluhā Ghāfilūna 006-131 Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.
Wa Likullin Darajātun Mimmā `Amilū  ۚ  Wa Mā Rabbuka Bighāfilin `Ammā Ya`malūna 006-132 Kuma ga kõwanne, akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.  ۚ 
Wa Rabbuka Al-Ghanīyu Dhū Ar-Raĥmati  ۚ  'In Yasha' Yudh/hibkum Wa Yastakhlif Min Ba`dikum Mā Yashā'u Kamā 'Ansha'akum Min Dhurrīyati Qawmin 'Ākharīna 006-133 Kuma Ubangijinika Wadãtacce ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.  ۚ 
'Inna Mā Tū`adūna La'ātin  ۖ  Wa Mā 'Antum Bimu`jizīna 006-134 Lalle ne abin da ake yi muku wa'adi lalle mai zuwa ne kuma ba ku zama mãsu buwãya ba,  ۖ 
Qul Yā Qawmi A`malū `Alá Makānatikum 'Innī `Āmilun  ۖ  Fasawfa Ta`lamūna Man Takūnu Lahu `Āqibatu Ad-Dāri  ۗ  'Innahu Lā Yufliĥu Až-Žālimūna 006-135 Ka ce: "Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa'an nan da sannu zã ku san wanda ãƙibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzãlumai bã zã su ci nasarã ba."  ۖ   ۗ 
Wa Ja`alū Lillahi Mimmā Dhara'a Mina Al-Ĥarthi Wa Al-'An`ām Naşībāan Faqālū Hādhā Lillahi Biza`mihim Wa Hadhā Lishurakā'inā  ۖ  Famā Kāna Lishurakā'ihim Falā Yaşilu 'Ilá Al-Lahi  ۖ  Wa Mā Kāna Lillahi Fahuwa Yaşilu 'Ilá Shurakā'ihim  ۗ  Sā'a Mā Yaĥkumūna 006-136 Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: "Wannan na Allah ne," da riyãwarsu "Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne." Sa'an nan  ۖ   ۖ   ۗ 
Wa Kadhalika Zayyana Likathīrin Mina Al-Mushrikīna Qatla 'Awlādihim Shurakā'uuhum Liyurdūhum Wa Liyalbisū `Alayhim Dīnahum  ۖ  Wa Law Shā'a Al-Lahu Mā Fa`alūhu  ۖ  Fadharhum Wa Mā Yaftarūna 006-137 Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.  ۖ   ۖ 
Wa Qālū Hadhihi 'An`āmun Wa Ĥarthun Ĥijrun Lā Yaţ`amuhā 'Illā Man Nashā'u Biza`mihim Wa 'An`āmun Ĥurrimat Žuhūruhā Wa 'An`āmun Lā Yadhkurūna Asma Al-Lahi `Alayhā Aftirā'an `Alayhi  ۚ  Sayajzīhim Bimā Kānū Yaftarūna 006-138 Kuma sukace: "Waɗannan dabbõbi da shũka hanannu ne; bãbu mai ɗanɗanar su fãce wanda muke so," ga riyãwarsu. Da wasu dabbõbi an hana bãyayyakinsu, da wasu dabbõbi bã su ambatar sũnan Allah a kansu, bisa ƙirƙiren ƙarya gare Shi. Zai sãka musu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa. ~  ۚ 
Wa Qālū Mā Fī Buţūni Hadhihi Al-'An`āmi Khālişatun Lidhukūrinā Wa Muĥarramun `Alá 'Azwājinā  ۖ  Wa 'In Yakun Maytatan Fahum Fīhi Shurakā'u  ۚ  Sayajzīhim Waşfahum  ۚ  'Innahu Ĥakīmun `Alīmun 006-139 Kuma suka ce: "Abin da yake a cikin cikkunan waɗannan dabbõbi kẽɓantacce ne ga mazanmu, kuma hananne ne a kan mãtan aurenmu. Kuma idan ya kasance mũshe, to, a cikinsa sũ abõkan tãrayya ne, zai sãka musu sifantãwarsu. Lalle ne Shĩ, Mai hikima ne, Masani."  ۖ   ۚ   ۚ 
Qad Khasira Al-Ladhīna Qatalū 'Awlādahum Safahāan Bighayri `Ilmin Wa Ĥarramū Mā Razaqahumu Al-Lahu Aftirā'an `Alá Al-Lahi  ۚ  Qad Đallū Wa Mā Kānū Muhtadīna 006-140 Lalle ne waɗanda suka kashe ɗiyansu sabõda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasãra! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne sun ɓace, kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.  ۚ 
Wa Huwa Al-Ladhī 'Ansha'a Jannātin Ma`rūshātin Wa Ghayra Ma`rūshātin Wa An-Nakhla Wa Az-Zar`a Mukhtalifāan 'Ukuluhu Wa Az-Zaytūna Wa Ar-Rummāna Mutashābihāan Wa Ghayra Mutashābihin  ۚ  Kulū Min Thamarihi 'Idhā 'Athmara Wa 'Ātū Ĥaqqahu Yawma Ĥaşādihi  ۖ  Wa Lā Tusrifū  ۚ  'Innahu Lā Yuĥibbu Al-Musrifīna 006-141 Kuma Shĩ ne Wanda Ya ƙãga halittar gõnaki mãsu rumfuna da wasun mãsu rumfuna da dabĩnai da shũka, mai sãɓãwa ga 'yã'yansa na ci, da zaituni da rummãni mai kama da jũna da wanin mai kama da jũna. Ku ci daga 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'yã'yan, kuma ku bãyar da hakkinSa a rãnar girbinsa, kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ, ba Ya son mafarauta.  ۚ  ~  ۖ   ۚ 
Wa Mina Al-'An`āmi Ĥamūlatan Wa Farshāan  ۚ  Kulū Mimmā Razaqakumu Al-Lahu Wa Lā Tattabi`ū Khuţuwāti Ash-Shayţāni  ۚ  'Innahu Lakum `Adūwun Mubīnun 006-142 Kuma daga dabbõbi (Ya ƙãga halittar) mai ɗaukar kãya da ƙanãna; Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, kuma kada ku bi zambiyõyin shaiɗan: LalLe ne shi, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne.  ۚ   ۚ 
Thamāniyata 'Azwājin  ۖ  Mina Ađ-Đa'ni Athnayni Wa Mina Al-Ma`zi Athnayni  ۗ  Qul 'Āldhdhakarayni Ĥarrama 'Ami Al-'Unthayayni 'Ammā Ashtamalat `Alayhi 'Arĥāmu Al-'Unthayayni  ۖ  Nabbi'ūnī Bi`ilmin 'In Kuntum Şādiqīna 006-143 Nau'õ'i takwas daga tumãkai biyu, kuma daga awãkai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko mãtan biyu, ko abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Ku bã ni lãbãri da ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya.  ۖ   ۗ   ۖ 
Wa Mina Al-'Ibili Athnayni Wa Mina Al-Baqari Athnayni  ۗ  Qul 'Āldhdhakarayni Ĥarrama 'Ami Al-'Unthayayni 'Ammā Ashtamalat `Alayhi 'Arĥāmu Al-'Unthayayni  ۖ  'Am Kuntum Shuhadā'a 'Idh Waşşākumu Al-Lahu Bihadhā  ۚ  Faman 'Ažlamu Mimmani Aftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan Liyuđilla An-Nāsa Bighayri `Ilmin  ۗ  'Inna Al-Laha Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna 006-144 Kuma daga rãƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, dõmin ya ɓatar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.  ۗ   ۖ   ۚ   ۗ 
Qul Lā 'Ajidu Fī Mā 'Ūĥiya 'Ilayya Muĥarramāan `Alá Ţā`imin Yaţ`amuhu 'Illā 'An Yakūna Maytatan 'Aw Damāan Masfūĥāan 'Aw Laĥma Khinzīrin Fa'innahu Rijsun 'Aw Fisqāan 'Uhilla Lighayri Al-Lahi Bihi  ۚ  Famani Ađţurra Ghayra Bāghin Wa Lā `Ādin Fa'inna Rabbaka Ghafūrun Raĥīmun 006-145 Ka ce: "Bã ni sãmu, a cikin abin da aka yõ wahayi zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. ~  ۚ 
Wa `Alá Al-Ladhīna Hādū Ĥarramnā Kulla Dhī Žufurin  ۖ  Wa Mina Al-Baqari Wa Al-Ghanami Ĥarramnā `Alayhim Shuĥūmahumā 'Illā Mā Ĥamalat Žuhūruhumā 'Awi Al-Ĥawāyā 'Aw Mā Akhtalaţa Bi`ažmin  ۚ  Dhālika Jazaynāhum Bibaghyihim  ۖ  Wa 'Innā Laşādiqūna 006-146 Kuma a kan waɗanda suka tũba (Yahũdu) Mun haramta dukan mai akaifa, kuma daga shãnu da bisãshe Mun haramta musu kitsattsansu fãce abin da bãyukansu suka ɗauka, kõ kuwa kãyan ciki, kõ kuwa abin da ya garwaya da ƙashĩ wannan ne Muka sãka musu sabõda zãluncinsu, kuma Mu, haƙĩƙa, Mãsu gaskiya ne.  ۖ   ۚ   ۖ 
Fa'in Kadhdhabūka Faqul Rabbukum Dhū Raĥmatin Wāsi`atin Wa Lā Yuraddu Ba'suhu `Ani Al-Qawmi Al-Mujrimīna 006-147 To, idan sun ƙaryatã ka, sai ka ce: "Ubangijinku Ma'abũcin rahama ne Mai yalwa; kuma bã a mayar da azãbarSa daga mutãne mãsu laifi."
Sayaqūlu Al-Ladhīna 'Ashrakū Law Shā'a Al-Lahu Mā 'Ashraknā Wa Lā 'Ābā'uunā Wa Lā Ĥarramnā Min Shay'in  ۚ  Kadhālika Kadhdhaba Al-Ladhīna Min Qablihim Ĥattá Dhāqū Ba'sanā  ۗ  Qul Hal `Indakum Min `Ilmin Fatukhrijūhu Lanā  ۖ  'In Tattabi`ūna 'Illā Až-Žanna Wa 'In 'Antum 'Illā Takhruşūna 006-148 Waɗanda suka yi shirki zã su ce: "Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi."  ۚ   ۗ   ۖ 
Qul Falillāhi Al-Ĥujjatu Al-Bālighatu  ۖ  Falaw Shā'a Lahadākum 'Ajma`īna 006-149 Ka ce: "To Allah ne da hujja isasshiya, sabõda haka: Dã Yã so, dã Yã shiryar da ku gabã ɗaya."  ۖ 
Qul Halumma Shuhadā'akumu Al-Ladhīna Yash/hadūna 'Anna Al-Laha Ĥarrama Hādhā  ۖ  Fa'in Shahidū Falā Tash/had Ma`ahum  ۚ  Wa Lā Tattabi` 'Ahwā'a Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyātinā Wa Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati Wa Hum Birabbihim Ya`dilūna 006-150 Ka ce: "Ku kãwo shaidunku, waɗanda suke bãyar da shaidar cẽwa Allah ne Ya haramta wannan." To idan sun kãwo shaida kada ka yi shaida tãre da su. Kuma kada ka bi son zũciyõyin waɗanda suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, da waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira, alhãli kuwa sũ daga Ubangijinsu suna karkacẽwa.  ۖ   ۚ 
Qul Ta`ālaw 'Atlu Mā Ĥarrama Rabbukum `Alaykum  ۖ  'Allā Tushrikū Bihi Shay'āan  ۖ  Wa Bil-Wālidayni 'Iĥsānāan  ۖ  Wa Lā Taqtulū 'Awlādakum Min 'Imlāqin  ۖ  Naĥnu Narzuqukum Wa 'Īyāhum  ۖ  Wa Lā Taqrabū Al-Fawāĥisha Mā Žahara Minhā Wa Mā Baţana  ۖ  Wa Lā Taqtulū An-Nafsa Allatī Ĥarrama Al-Lahu 'Illā Bil-Ĥaqqi  ۚ  Dhālikum Waşşākum Bihi La`allakum Ta`qilūna 006-151 Ka ce: "Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta." wãjibi ne a kanku kada ku yi shirkin kõme da Shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatãwa, kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su, kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammãninku, kunã hankalta.  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۚ 
Wa Lā Taqrabū Māla Al-Yatīmi 'Illā Bi-Atī Hiya 'Aĥsanu Ĥattá Yablugha 'Ashuddahu  ۖ  Wa 'Awfū Al-Kayla Wa Al-Mīzāna Bil-Qisţi  ۖ  Lā Nukallifu Nafsāan 'Illā Wus`ahā  ۖ  Wa 'Idhā Qultum Fā`dilū Wa Law Kāna Dhā Qurbá  ۖ  Wa Bi`ahdi Al-Lahi 'Awfū  ۚ  Dhālikum Waşşākum Bihi La`allakum Tadhakkarūna 006-152 Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa.  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۚ 
Wa 'Anna Hādhā Şirāţī Mustaqīmāan Fa Attabi`ūhu  ۖ  Wa Lā Tattabi`ū As-Subula Fatafarraqa Bikum `An Sabīlihi  ۚ  Dhālikum Waşşākum Bihi La`allakum Tattaqūna 006-153 Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa.  ۖ   ۚ 
Thumma 'Ātaynā Mūsá Al-Kitāba Tamāmāan `Alá Al-Ladhī 'Aĥsana Wa Tafşīlāan Likulli Shay'in Wa Hudáan Wa Raĥmatan La`allahum Biliqā'i Rabbihim Yu'uminūna 006-154 Sa'an nan kuma Mun bai wa Mũsã Littãfi, yanã cikakke bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah) da rarrabẽwa, daki-daki, ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu, sunã yin ĩmãni da haɗuwa da Ubangijinsu.
Wa Hadhā Kitābun 'Anzalnāhu Mubārakun Fa Attabi`ūhu Wa Attaqū La`allakum Turĥamūna 006-155 Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.
'An Taqūlū 'Innamā 'Unzila Al-Kitābu `Alá Ţā'ifatayni Min Qablinā Wa 'In Kunnā `An Dirāsatihim Laghāfilīna 006-156 (Dõmin) kada ku ce: "Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan ƙungiya biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance, daga karatunsu, haƙĩƙa, gãfilai."
'Aw Taqūlū Law 'Annā 'Unzila `Alaynā Al-Kitābu Lakunnā 'Ahdá Minhum  ۚ  Faqad Jā'akum Bayyinatun Min Rabbikum Wa Hudáan Wa Raĥmatun  ۚ  Faman 'Ažlamu Mimman Kadhdhaba Bi'āyāti Al-Lahi Wa Şadafa `Anhā  ۗ  Sanaj Al-Ladhīna Yaşdifūna `An 'Āyātinā Sū'a Al-`Adhābi Bimā Kānū Yaşdifūna 006-157 Kõ kuwa ku ce: "Dã dai lalle mũ an saukar da Littãfi a kanmu, haƙĩƙa, dã mun kasance mafiya,shiryuwa daga gare su." To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, tã zo muku, da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Zã Mu sãka wa waɗanda suke finjirẽwa daga barin ãyõyinMu da mugunyar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na hinjirẽwa.  ۚ   ۚ   ۗ 
Hal Yanžurūna 'Illā 'An Ta'tiyahumu Al-Malā'ikatu 'Aw Ya'tiya Rabbuka 'Aw Ya'tiya Ba`đu 'Āyāti Rabbika  ۗ  Yawma Ya'tī Ba`đu 'Āyāti Rabbika Lā Yanfa`u Nafsāan 'Īmānuhā Lam Takun 'Āmanat Min Qablu 'Aw Kasabat Fī 'Īmānihā Khayrāan  ۗ  Qul Antažirū 'Innā Muntažirūna 006-158 Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku su je musu kõ kuwa Ubangijinka Ya je, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka ya je. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka yake zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba a gabãni, kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri, bã ya amfãninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne."  ۗ   ۗ 
'Inna Al-Ladhīna Farraqū Dīnahum Wa Kānū Shiya`āan Lasta MinhumShay'in  ۚ  'Innamā 'Amruhum 'Ilá Al-Lahi Thumma Yunabbi'uhum Bimā Kānū Yaf`alūna 006-159 Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.  ۚ 
Man Jā'a Bil-Ĥasanati Falahu `Ashru 'Amthālihā  ۖ  Wa Man Jā'a Bis-Sayyi'ati Falā Yujzá 'Illā Mithlahā Wa Hum Lā Yužlamūna 006-160 Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su.  ۖ 
Qul 'Innanī Hadānī Rabbī 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin Dīnāan Qiyamāan Millata 'Ibrāhīma Ĥanīfāan  ۚ  Wa Mā Kāna Mina Al-Mushrikīna 006-161 Ka ce: "Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni, ƙĩmantãwa ( ga abũbuwa), mai aƙĩdar Ibrãhĩm, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."  ۚ 
Qul 'Inna Şalātī Wa Nusukī Wa Maĥyāya Wa Mamātī Lillahi Rabbi Al-`Ālamīna 006-162 Ka ce: "Lalle ne sallãta, da baikõna, da rãyuwãta, da mutuwãta, na Allah ne Ubangijin tãlikai."
Sharīka Lahu  ۖ  Wa Bidhalika 'Umirtu Wa 'Anā 'Awwalu Al-Muslimīna 006-163 "Bãbu abõkin tãrayya a gare Shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon mãsu sallamãwa."  ۖ 
Qul 'Aghayra Al-Lahi 'Abghī Rabbāan Wa Huwa Rabbu Kulli Shay'in  ۚ  Wa Lā Taksibu Kullu Nafsin 'Illā `Alayhā  ۚ  Wa Lā Taziru Wāziratun Wizra 'Ukhrá  ۚ  Thumma 'Ilá Rabbikum Marji`ukum Fayunabbi'ukum Bimā Kuntum Fīhi Takhtalifūna 006-164 Ka ce: "Shin wanin Allah nake nẽma ya zama Ubangiji, alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce dõmin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?"  ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Huwa Al-Ladhī Ja`alakum Khalā'ifa Al-'Arđi Wa Rafa`a Ba`đakum Fawqa Ba`đin Darajātin Liyabluwakum Fī Mā 'Ātākum  ۗ  'Inna Rabbaka Sarī`u Al-`Iqābi Wa 'Innahu Laghafūrun Raĥīmun 006-165 "Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya ku mãsu maye wa jũnaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sãshenku bisa ga sãshe da darajõji; dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku." Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggãwar uƙkũba ne, kuma lalle ne Shi, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۗ 
Next Sūrah