5) Sūrat Al-Mā'idah

Printed format

5)

Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Awfū Bil-`Uqūdi 'Uĥillat Lakum Bahīmatu Al-'An`āmi 'Illā Mā Yutlá `Alaykum Ghayra Muĥillī Aş-Şaydi Wa 'Antum Ĥurumun 'Inna Al-Laha Yaĥkumu Mā Yurīdu 005-001 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi.  ۚ   ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tuĥillū Sha`ā'ira Al-Lahi Wa Lā Ash-Shahra Al-Ĥarāma Wa Lā Al-Hadya Wa Lā Al-Qalā'ida Wa Lā 'Āmmīna Al-Bayta Al-Ĥarāma Yabtaghūna Fađlāan Min Rabbihim Wa Riđwānāan  ۚ  Wa 'Idhā Ĥalaltum Fāşţādū  ۚ  Wa Lā Yajrimannakum Shana'ānu Qawmin 'An Şaddūkum `Ani Al-Masjidi Al-Ĥarāmi 'An Ta`tadū  ۘ  Wa Ta`āwanū `Alá Al-Birri Wa At-Taqwá  ۖ  Wa Lā Ta`āwanū `Alá Al-'Ithmi Wa Al-`Udwāni  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha  ۖ  'Inna Al-Laha Shadīdu Al-`Iqābi 005-002 Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.  ۚ   ۚ   ۘ   ۖ   ۚ   ۖ 
Ĥurrimat `Alaykumu Al-Maytatu Wa Ad-Damu Wa Laĥmu Al-Khinzīri Wa Mā 'Uhilla Lighayri Al-Lahi Bihi Wa Al-Munkhaniqatu Wa Al-Mawqūdhatu Wa Al-Mutaraddiyatu Wa An-Naţīĥatu Wa Mā 'Akala As-Sabu`u 'Illā Mā Dhakkaytum Wa Mā Dhubiĥa `Alá An-Nuşubi Wa 'An Tastaqsimū Bil-'Azlāmi  ۚ  Dhālikum Fisqun  ۗ  Al-Yawma Ya'isa Al-Ladhīna Kafarū Min Dīnikum Falā Takhshawhum Wa Akhshawnī  ۚ  Al-Yawma 'Akmaltu Lakum Dīnakum Wa 'Atmamtu `Alaykum Ni`matī Wa Rađītu Lakumu Al-'Islāma Dīnāan  ۚ  Famani Ađţurra Fī Makhmaşatin Ghayra Mutajānifin L'ithmin  ۙ  Fa'inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 005-003 An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۚ   ۗ   ۚ   ۚ   ۙ 
Yas'alūnaka Mādhā 'Uĥilla Lahum  ۖ  Qul 'Uĥilla Lakumu Aţ-Ţayyibātu  ۙ  Wa Mā `Allamtum Mina Al-Jawāriĥi Mukallibīna Tu`allimūnahunna Mimmā `Allamakumu Al-Lahu  ۖ  Fakulū Mimmā 'Amsakna `Alaykum Wa Adhkurū Asma Al-Lahi `Alayhi  ۖ  Wa Attaqū Al-Laha  ۚ  'Inna Al-Laha Sarī`u Al-Ĥisābi 005-004 Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga mãsu yin mĩki, kunã mãsu sakinsu daga hannuwanku, kunã sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci daga abin da suka kama sabõda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawã ne.  ۖ   ۙ   ۖ   ۖ   ۚ 
Al-Yawma 'Uĥilla Lakumu Aţ-Ţayyibātu  ۖ  Wa Ţa`āmu Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Ĥillun Lakum Wa Ţa`āmukum Ĥillun Lahum Wa  ۖ  Al-Muĥşanātu Mina Al-Mu'umināti Wa Al-Muĥşanātu Mina Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Min Qablikum 'Idhā 'Ātaytumūhunna 'Ujūrahunna Muĥşinīna Ghayra Musāfiĥīna Wa Lā Muttakhidhī 'Akhdānin  ۗ  Wa Man Yakfur Bil-'Īmāni Faqad Ĥabiţa `Amaluhu Wa Huwa Fī Al-'Ākhirati Mina Al-Khāsirīna 005-005 A yau an halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kun je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra.  ۖ   ۖ   ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Qumtum 'Ilá Aş-Şalāati Fāghsilū Wujūhakum Wa 'Aydiyakum 'Ilá Al-Marāfiqi Wa Amsaĥū Biru'ūsikum Wa 'Arjulakum 'Ilá Al-Ka`bayni  ۚ  Wa 'In Kuntum Junubāan Fa Aţţahharū  ۚ  Wa 'In Kuntum Marđá 'Aw `Alá Safarin 'Aw Jā'a 'Aĥadun Minkum Mina Al-Ghā'iţi 'Aw Lāmastumu An-Nisā' Falam Tajidū Mā'an Fatayammamū Şa`īdāan Ţayyibāanmsaĥū Biwujūhikum Wa 'Aydīkum Minhu  ۚ  Mā Yurīdu Al-Lahu Liyaj`ala `Alaykum Min Ĥarajin Wa Lakin Yurīdu Liyuţahhirakum Waliyutimma Ni`matahu `Alaykum La`allakum Tashkurūna 005-006 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni ! idan kun tãshi zuwa ga salla, to, ku wanke fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga magincirõri, kuma ku yi shãfa ga kãnunku, kuma ku (wanke) ƙafãfunku zuwa idãnun sãwu biyu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba, to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kõ kuwa a kan tafiya, kõ kuwa ɗaya daga gare ku ya zo daga kãshi, kõ kuka yi shãfayyar junã da mãtã, sa'an nan ba ku sãmi ruwa ba to ku yi nufin wuri mai kyau, sa'an nan ku yi shãfa ga fuskõkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammãninku kunã gõdewa.  ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Adhkurū Ni`mata Al-Lahi `Alaykum Wa Mīthāqahu Al-Ladhī Wa Athaqakum Bihi 'Idh Qultum Sami`nā Wa 'Aţa`nā  ۖ  Wa Attaqū Al-Laha  ۚ  'Inna Al-Laha `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri 005-007 Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a lõkacin da kuka ce: "Mun ji kuma mun yi ɗã'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata." ~  ۖ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Kūnū Qawwāmīna Lillahi Shuhadā'a Bil-Qisţi  ۖ  Wa Lā Yajrimannakum Shana'ānu Qawmin `Alá 'Allā Ta`dilū  ۚ  A`dilū Huwa 'Aqrabu Lilttaqwá  ۖ  Wa Attaqū Al-Laha  ۚ  'Inna Al-Laha Khabīrun Bimā Ta`malūna 005-008 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.  ۖ   ۚ   ۖ   ۚ 
Wa`ada Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti  ۙ  Lahum Maghfiratun Wa 'Ajrun `Ažīmun 005-009 Allah Yã yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Sunã da wata gãfara da lãda mai girma.  ۙ 
Wa Al-Ladhīna Kafarū Wa Kadhdhabū Bi'āyātinā 'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Jaĥīmi 005-010 Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryatã, game da ãyõyinMu, waɗannan su ne abõkan wuta.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Adhkurū Ni`mata Al-Lahi `Alaykum 'Idh Hamma Qawmun 'An Yabsuţū 'Ilaykum 'Aydiyahum Fakaffa 'Aydiyahum `Ankum  ۖ  Wa Attaqū Al-Laha  ۚ  Wa `Alá Al-Lahi Falyatawakkali Al-Mu'uminūna 005-011 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.  ۖ   ۚ 
Wa Laqad 'Akhadha Al-Lahu Mīthāqa Banī 'Isrā'īla Wa Ba`athnā Minhumu Athnay `Ashara Naqībāan  ۖ  Wa Qāla Al-Lahu 'Innī Ma`akum  ۖ  La'in 'Aqamtumu Aş-Şalāata Wa 'Ātaytumu Az-Zakāata Wa 'Āmantum Birusulī Wa `Azzartumūhum Wa 'Aqrađtumu Al-Laha Qarđāan Ĥasanāan La'ukaffiranna `Ankum Sayyi'ātikum Wa La'udkhilannakum Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru  ۚ  Faman Kafara Ba`da Dhālika Minkum Faqad Đalla Sawā'a As-Sabīli 005-012 Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya."  ۖ   ۖ   ۚ 
Fabimā Naqđihimthāqahum La`annāhum Wa Ja`alnā Qulūbahum Qāsiyatan  ۖ  Yuĥarrifūna Al-Kalima `An Mawāđi`ihi  ۙ  Wa Nasū Ĥažžāan Mimmā Dhukkirū Bihi  ۚ  Wa Lā Tazālu Taţţali`u `Alá Khā'inatin Minhum 'Illā Qalīlāan Minhum  ۖ  Fā`fu `Anhum Wa Aşfaĥ  ۚ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Muĥsinīna 005-013 To, sabõda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukãtansu ƙeƙasassu, sunã karkatar da magana daga wurãrenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, kuma bã zã ka gushe ba kana tsinkãyar yaudara daga gare su fãce kaɗan daga gare su. To, ka yãfe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu kyautatãwa.  ۖ   ۙ   ۚ   ۖ   ۚ 
Wa Mina Al-Ladhīna Qālū 'Innā Naşārá 'Akhadhnā Mīthāqahum Fanasū Ĥažžāan Mimmā Dhukkirū Bihi Fa'aghraynā Baynahumu Al-`Adāwata Wa Al-Baghđā'a 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati  ۚ  Wa Sawfa Yunabbi'uhumu Al-Lahu Bimā Kānū Yaşna`ūna 005-014 Kuma daga waɗanda suka ce: "Lalle ne mu Nasãra ne" Mun riƙi alkawarinsu, sai suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka shushuta adãwa da ƙeta a tsakãninsu har ya zuwa ga Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah zai bã su lãbari da abin da suka kasance sunã sanã'antawa.  ۚ 
Yā 'Ahla Al-Kitābi Qad Jā'akum Rasūlunā Yubayyinu Lakum Kathīrāan Mimmā Kuntum Tukhfūna Mina Al-Kitābi Wa Ya`fū `An Kathīrin  ۚ  Qad Jā'akum Mina Al-Lahi Nūrun Wa Kitābun Mubīnun 005-015 Yã Mutãnen littãfi! Lalle ne, ManzonMu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga abu mai yawa. Haƙĩƙa,wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga Allah.  ۚ 
Yahdī Bihi Al-Lahu Mani Attaba`a Riđwānahu Subula As-Salāmi Wa Yukhrijuhum Mina Až-Žulumāti 'Ilá An-Nūri Bi'idhnihi Wa Yahdīhim 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin 005-016 Dashĩ, Allah Yanã shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, kuma Yanã fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yanã shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.
Laqad Kafara Al-Ladhīna Qālū 'Inna Al-Laha Huwa Al-Masīĥu Abnu Maryama  ۚ  Qul Faman Yamliku Mina Al-Lahi Shay'āan 'In 'Arāda 'An Yuhlika Al-Masīĥa Abna Maryama Wa 'Ummahu Wa Man Al-'Arđi Jamī`āan  ۗ  Wa Lillahi Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā  ۚ  Ykhluqu Mā Yashā'u Wa  ۚ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 005-017 Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama," sun kãfirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yã nufi Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabã ɗaya?" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, Yanã halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne.  ۚ   ۗ   ۚ   ۚ 
Wa Qālati Al-Yahūdu Wa An-Naşārá Naĥnu 'Abnā'u Al-Lahi Wa 'Aĥibbā'uuhu  ۚ  Qul Falima Yu`adhdhibukum Bidhunūbikum  ۖ  Bal 'Antum Basharun Mimman Khalaqa  ۚ  Yaghfiru Liman Yashā'u Wa Yu`adhdhibu Man Yashā'u  ۚ  Wa Lillahi Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā  ۖ  Wa 'Ilayhi Al-Maşīru 005-018 Kuma Yahudu da Nasãra sun ce: "Mu ne ɗiyan Allah, kuma masõyansa." Ka ce: "To, don me Yake yi muku azãba da zunubanku? Ã'a ku mutãne ne daga waɗanda Ya halitta, Yanã gãfartãwa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so. Kuma Allah ne da mulkin sammai da ƙasa da abin da ke tsakãninsu kuma zuwa gare shi makomã take."  ۚ   ۖ   ۚ   ۚ   ۖ 
Yā 'Ahla Al-Kitābi Qad Jā'akum Rasūlunā Yubayyinu Lakum `Alá Fatratin Mina Ar-Rusuli 'An Taqūlū Mā Jā'anā Min Bashīrin Wa Lā Nadhīrin  ۖ  Faqad Jā'akum Bashīrun Wa Nadhīrun Wa  ۗ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 005-019 Yã Mutãnen Littãfi! Lalle ManzonMu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushãra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba." To, haƙĩƙa, mai bãyar da bushãra da mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi.  ۖ   ۗ 
Wa 'Idh Qāla Mūsá Liqawmihi Yā Qawmi Adhkurū Ni`mata Al-Lahi `Alaykum 'Idh Ja`ala Fīkum 'Anbiyā'a Wa Ja`alakum Mulūkāan Wa 'Ātākum Mā Lam Yu'uti 'Aĥadāan Mina Al-`Ālamīna 005-020 Kuma a lõkacin da Musa ya ce wa mutãnensa: "Yã ku mutãnena! Ku tuna ni'imar Allah a kanku; dõmin Yã sanya annabãwa a cikinku, kuma Yã sanya ku sarãkuna, kuma Yã bã ku abin da bai bai wa kõwa ba daga tãlikai."
Yā Qawmi Adkhulū Al-'Arđa Al-Muqaddasata Allatī Kataba Al-Lahu Lakum Wa Lā Tartaddū `Alá 'Adrikum Fatanqalibū Khāsirīna 005-021 "Yã mutãnena! Ku shiga ƙasar nan, abar tsarkakewa, wadda Allah Ya rubuta sabõda ku, kuma kada ku kõma da bãya, har ku juya kunã mãsu hasara."
Qālū Yā Mūsá 'Inna Fīhā Qawmāan Jabbārīna Wa 'Innā Lan Nadkhulahā Ĥattá Yakhrujū Minhā Fa'in Yakhrujū Minhā Fa'innā Dākhilūna 005-022 Suka ce: "Ya Musã! Lalle ne, a cikinta akwai wasu mutãne mãsu ƙarfi kuma lalle ne bã zã mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare ta, to, lalle ne mu, masu shiga ne."
Qāla Rajulāni Mina Al-Ladhīna Yakhāfūna 'An`ama Al-Lahu `Alayhimā Adkhulū `Alayhimu Al-Bāba Fa'idhā Dakhaltumūhu Fa'innakum Ghālibūna  ۚ  Wa `Alá Al-Lahi Fatawakkalū 'In Kuntum Mu'uminīna 005-023 Wasu maza biyu daga waɗanda suke tsõron Allah, Allah Yã yi ni'ima a kansu, suka ce: "Ku shiga gare su, daga ƙõfar, dõmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku, mãsu rinjãya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai."  ۚ 
Qālū Yā Mūsá 'Innā Lan Nadkhulahā 'Abadāan Mā Dāmū Fīhā  ۖ  Fādh/hab 'Anta Wa Rabbuka Faqātilā 'Innā Hāhunā Qā`idūna 005-024 Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bã za mu shige ta ba har abada matuƙar sun dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dõmin ku yi yãƙi. Lalle ne mu, munã a nan zaune."  ۖ 
Qāla Rabbi 'Innī Lā 'Amliku 'Illā Nafsī Wa 'Akhī  ۖ  Fāfruq Baynanā Wa Bayna Al-Qawmi Al-Fāsiqīna 005-025 Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, bã ni mallakar kõwa fãce kaina da ɗan'uwãna, sai Ka rarrabe a tsakãninmu da tsakãnin mutãne fãsiƙai."  ۖ 
Qāla Fa'innahā Muĥarramatun `Alayhim  ۛ  'Arba`īna Sanatan  ۛ  Yatīhūna Fī Al-'Arđi  ۚ  Falā Ta'sa `Alá Al-Qawmi Al-Fāsiqīna 005-026 (Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtãwa ce a gare su, shekara arba'in, sunã yin ɗimuwa a cikin ƙasa. Sabõda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne fãsiƙai."  ۛ   ۛ   ۚ 
Wa Atlu `Alayhim Naba'a Abnay 'Ādama Bil-Ĥaqqi 'Idh Qarrabā Qurbānāan Fatuqubbila Min 'Aĥadihimā Wa Lam Yutaqabbal Mina Al-'Ākhari Qāla La'aqtulannaka  ۖ  Qāla 'Innamā Yataqabbalu Al-Lahu Mina Al-Muttaqīna 005-027 Kuma karantã musu lãbãrin ɗiya biyu na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne."  ۖ 
La'in Basaţta 'Ilayya Yadaka Litaqtulanī Mā 'Anā Bibāsiţin Yadiya 'Ilayka Li'qtulaka  ۖ  'Innī 'Akhāfu Al-Laha Rabba Al-`Ālamīna 005-028 "Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai.  ۖ 
'Innī 'Urīdu 'An Tabū'a Bi'ithmī Wa 'Ithmika Fatakūna Min 'Aşĥābi An-Nāri  ۚ  Wa Dhalika Jazā'u Až-Žālimīna 005-029 "Lalle ne nĩ inã nufin ka kõma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abõkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzãlumai."  ۚ 
Faţawwa`at Lahu Nafsuhu Qatla 'Akhīhi Faqatalahu Fa'aşbaĥa Mina Al-Khāsirīna 005-030 Sai ransa ya ƙawãtar masa kashewar ɗan'uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa'an nan ya wayi gari daga mãsu hasãra.
Faba`atha Al-Lahu Ghurābāan Yabĥathu Fī Al-'Arđi Liyuriyahu Kayfa Yuwārī Saw'ata 'Akhīhi  ۚ  Qāla Yā Waylatā 'A`ajaztu 'An 'Akūna Mithla Hādhā Al-Ghurābi Fa'uwāriya Saw'ata 'Akhī  ۖ  Fa'aşbaĥa Mina An-Nādimīna 005-031 Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan'uwana?" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã.  ۚ   ۖ 
Min 'Ajli Dhālika Katabnā `Alá Banī 'Isrā'īla 'Annahu Man Qatala Nafsāan Bighayri Nafsin 'Aw Fasādin Al-'Arđi Faka'annamā Qatala An-Nāsa Jamī`āan Wa Man 'Aĥyāhā Faka'annamā 'Aĥyā An-Nāsa Jamī`āan  ۚ  Wa Laqad Jā'at/hum Rusulunā Bil-Bayyināti Thumma 'Inna Kathīrāan Minhum Ba`da Dhālika Fī Al-'Arđi Lamusrifūna 005-032 Daga sababin wannan, Muka rubuta a kan Banĩ lsrã'ĩla cewa, lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, ManzanninMu sun je musu da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, mãsu yawa daga gare su, a bãyan wannan, haƙĩƙa, mãsuɓarna ne a cikin ƙasa.  ۚ 
'Innamā Jazā'u Al-Ladhīna Yuĥāribūna Al-Laha Wa Rasūlahu Wa Yas`awna Fī Al-'Arđi Fasādāan 'An Yuqattalū 'Aw Yuşallabū 'Aw Tuqaţţa`a 'Aydīhim Wa 'Arjuluhum Min Khilāfin 'Aw Yunfaw Mina Al-'Arđi  ۚ  Dhālika Lahum Khizyun Ad-Dunyā  ۖ  Wa Lahum Al-'Ākhirati `Adhābun `Ažīmun 005-033 Abin sani kawai sakamakon waɗanda suke Yãƙin Allah da Manzonsa, kuma sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kõ kuwa a kakkãtse hannuwansu da ƙafãfunsu daga sãɓãni, ko kuwa a kõre su daga ƙasa. Sannan gare su wulakanci ne a cikin rãyuwar duniya, kuma a Lãhira sunã da wata azãba mai girma.  ۚ   ۖ 
'Illā Al-Ladhīna Tābū Min Qabli 'An Taqdirū `Alayhim  ۖ  Fā`lamū 'Anna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 005-034 Fãce fa waɗanda suka tuba tun a gabãnin ku sãmi ĩko akansu, to, ku sani cewa lalle ne, Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Attaqū Al-Laha Wa Abtaghū 'Ilayhi Al-Wasīlata Wa Jāhidū Fī Sabīlihi La`allakum Tufliĥūna 005-035 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara.
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Law 'Anna Lahum Mā Fī Al-'Arđi Jamī`āan Wa Mithlahu Ma`ahu Liyaftadū Bihi Min `Adhābi Yawmi Al-Qiyāmati Mā Tuqubbila Minhum  ۖ  Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun 005-036 Lalle ne waɗanda suka kãfirta, lalle dã sunã da abin da ke a cikin ƙasa gabã ɗaya da misãlinsa tãre da shi, dõmin su yi fansa da shi daga azãbar Rãnar ¡iyãma, bã a karɓarsa daga gare su, kuma sunã da azãba mai raɗadi.  ۖ 
Yurīdūna 'An Yakhrujū Mina An-Nāri Wa Mā Hum Bikhārijīna Minhā  ۖ  Wa Lahum `Adhābun Muqīmun 005-037 Sunã nufin su fita ne daga wuta, kuma ba su zama mãsu fita daga gare ta ba, kuma sunã da azãba zaunanniya.  ۖ 
Wa As-Sāriqu Wa As-Sāriqatu Fāqţa`ū 'Aydiyahumā Jazā'an Bimā Kasabā Nakālāan Mina  ۗ  Al-Lahi Wa Allāhu `Azīzun Ĥakīmun 005-038 Kuma ɓarãwo da ɓarauniya sai ku yanke hannuwansu, bisa sakamako ga abin da suka tsirfanta, a kan azãba daga Allah. Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.  ۗ 
Faman Tāba Min Ba`di Žulmihi Wa 'Aşlaĥa Fa'inna Al-Laha Yatūbu `Alayhi  ۗ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 005-039 To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra (halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۗ 
'Alam Ta`lam 'Anna Al-Laha Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Yu`adhdhibu Man Yashā'u Wa Yaghfiru Liman Yashā'u Wa  ۗ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 005-040 Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yanã azãbtar da wanda Yake so, kuma Yanã yin gãfara ga wanda yake so, kuma Allah a dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne?  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Ar-Rasūlu Lā Yaĥzunka Al-Ladhīna Yusāri`ūna Fī Al-Kufri Mina Al-Ladhīna Qālū 'Āmannā Bi'afwāhihim Wa Lam Tu'umin Qulūbuhum  ۛ  Wa Mina Al-Ladhīna Hādū  ۛ  Sammā`ūna Lilkadhibi Sammā`ūna Liqawmin 'Ākharīna Lam Ya'tūka  ۖ  Yuĥarrifūna Al-Kalima Min Ba`di Mawāđi`ihi  ۖ  Yaqūlūna 'In 'Ūtītumdhā Fakhudhūhu Wa 'In Lam Tu'utawhu Fāĥdharū  ۚ  Wa Man Yuridi Al-Lahu Fitnatahu Falan Tamlika Lahu Mina Al-Lahi Shay'āan  ۚ  'Ūlā'ika Al-Ladhīna Lam Yuridi Al-Lahu 'An Yuţahhira Qulūbahum  ۚ  Lahum Ad-DunKhizyun  ۖ  Wa Lahum Al-'Ākhirati `Adhābun `Ažīmun 005-041 Yã kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kãfirci su ɓãta maka rai, daga waɗanda suka ce: "Mun yi ĩmãni" da bãkunansu, alhãli zukatansu ba su yi ĩmãnin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) mãsu yawan saurare ga wasu mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sunã karkatar da zance daga bãyan wurarensa, sunã cewa: "Idan an bã ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bã ku shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bã zã ka mallaka masa kõme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukãtansu ba. Sunã da kunya a cikin duniya, kuma sunã da wata azãba mai girma a cikin 1ãhira.  ۛ   ۛ   ۖ   ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۖ 
Sammā`ūna Lilkadhibi 'Akkālūna Lilssuĥti  ۚ  Fa'in Jā'ūka Fāĥkum Baynahum 'Aw 'A`riđ `Anhum  ۖ  Wa 'In Tu`riđ `Anhum Falan Yađurrūka Shay'āan  ۖ  Wa 'In Ĥakamta Fāĥkum Baynahum Bil-Qisţi  ۚ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Muqsiţīna 005-042 Mãsu yawan saurãre ga ƙarya ne, mãsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka, sai ka yi hukunci a tsakãninsu kõ ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira daga gare su, to, bã zã su cuce ka da kõme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai ka hukunta a tsakãninsu da ãdalci. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu ãdalci.  ۚ   ۖ   ۖ   ۚ 
Wa Kayfa Yuĥakkimūnaka Wa `Indahumu At-Tawrāatu Fīhā Ĥukmu Al-Lahi Thumma Yatawallawna Min Ba`di Dhālika  ۚ  Wa Mā 'Ūlā'ika Bil-Mu'uminīna 005-043 Kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci, alhãli a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan? waɗannan bã muminai ba ne!  ۚ 
'Innā 'Anzalnā At-Tawrāata Fīhā Hudáan Wa Nūrun  ۚ  Yaĥkumu Bihā An-Nabīyūna Al-Ladhīna 'Aslamū Lilladhīna Hādū Wa Ar-Rabbānīyūna Wa Al-'Aĥbāru Bimā Astuĥfižū Min Kitābi Al-Lahi Wa Kānū `Alayhi Shuhadā'a  ۚ  Falā Takhshaw An-Nāsa Wa Akhshawnī Wa Lā Tashtarū Bi'āyātī Thamanāan Qalīlāan  ۚ  Wa Man Lam Yaĥkum Bimā 'Anzala Al-Lahu Fa'ūlā'ika Humu Al-Kāfirūna 005-044 Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji tsõron mutãne kuma ku ji tsõroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyoyiNa. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai.  ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Katabnā `Alayhim Fīhā 'Anna An-Nafsa Bin-Nafsi Wa Al-`Ayna Bil-`Ayni Wa Al-'Anfa Bil-'Anfi Wa Al-'Udhuna Bil-'Udhuni Wa As-Sinna Bis-Sinni Wa Al-Jurūĥa Qişāşun  ۚ  Faman Taşaddaqa Bihi Fahuwa Kaffāratun Lahu  ۚ  Wa Man Lam Yaĥkum Bimā 'Anzala Al-Lahu Fa'ūlā'ika Humu Až-Žālimūna 005-045 Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (anã kashe) rai sabõda rai, kuma (anã ɗebe) idõ sabõda idõ, kuma (ana katse) hanci sabõda hanci, kuma kunne sabõda kunne kuma haƙori sabõda haƙõri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai.  ۚ   ۚ 
Wa Qaffaynā `Alá 'Āthārihim Bi`īsá Abni Maryama Muşaddiqāan Limā Bayna Yadayhi Mina At-Tawrāati  ۖ  Wa 'Ātaynāhu Al-'Injīla Fīhi Hudáan Wa Nūrun Wa Muşaddiqāan Limā Bayna Yadayhi Mina At-Tawrāati Wa Hudáan Wa Maw`ižatan Lilmuttaqīna 005-046 Kuma Muka biyar a kan gurãbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yãnã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bã shi Injĩla a cikinsa akwai shiriya da haske, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga mãsu taƙawa.  ۖ 
Wa Līaĥkum 'Ahlu Al-'Injīli Bimā 'Anzala Al-Lahu Fīhi  ۚ  Wa Man Lam Yaĥkum Bimā 'Anzala Al-Lahu Fa'ūlā'ika Humu Al-Fāsiqūna 005-047 Kuma sai mutãnen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fãsiƙai.  ۚ 
Wa 'Anzalnā 'Ilayka Al-Kitāba Bil-Ĥaqqi Muşaddiqāan Limā Bayna Yadayhi Mina Al-Kitābi Wa Muhaymināan `Alayhi  ۖ  Fāĥkum Baynahum Bimā 'Anzala Al-Lahu  ۖ  Wa Lā Tattabi` 'Ahwā'ahum `Ammā Jā'aka Mina Al-Ĥaqqi  ۚ  Likullin Ja`alnā Minkum Shir`atan Wa Minhājāan  ۚ  Wa Law Shā'a Al-Lahu Laja`alakum 'Ummatan Wāĥidatan Wa Lakin Liyabluwakum Fī Mā 'Ātākum  ۖ  Fāstabiqū Al-Khayrāti  ۚ  'Ilá Al-Lahi Marji`ukum Jamī`āan Fayunabbi'ukum Bimā Kuntum Fīhi Takhtalifūna 005-048 Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyiniu daga abin da ya zo maka daga gaskiya . Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya ku al'umma guda, kuma amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã sãɓãwa a cikinsa.  ۖ   ۖ   ۚ   ۚ   ۖ   ۚ 
Wa 'Ani Aĥkum Baynahum Bimā 'Anzala Al-Lahu Wa Lā Tattabi` 'Ahwā'ahum Wa Aĥdharhum 'An Yaftinūka `An Ba`đi Mā 'Anzala Al-Lahu 'Ilayka  ۖ  Fa'in Tawallaw Fā`lam 'Annamā Yurīdu Al-Lahu 'An Yuşībahum Biba`đi Dhunūbihim  ۗ  Wa 'Inna Kathīrāan Mina An-Nāsi Lafāsiqūna 005-049 Kuma ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga sãshen abin da Allah Ya saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya bãya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana nufin Ya sãme su da masĩfa ne sabõda sãshen zunubansu. Kuma lalle ne, mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, fãsiƙai ne.  ۖ   ۗ 
'Afaĥukma Al-Jāhilīyati Yabghūna  ۚ  Wa Man 'Aĥsanu Mina Al-Lahi Ĥukmāan Liqawmin Yūqinūna 005-050 Shin, hukuncin Jãhiliyya suke nema? Kuma wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah sabõda mutãne waɗanda suke yin yaƙĩni (tabbataccen ĩmãni)?  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tattakhidhū Al-Yahūda Wa An-Naşārá 'Awliyā'a  ۘ  Ba`đuhum 'Awliyā'u Ba`đin  ۚ  Wa Man Yatawallahum Minkum Fa'innahu Minhum  ۗ  'Inna Al-Laha Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna 005-051 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra majiɓinta. Sãshensu majiɓinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.  ۘ   ۚ   ۗ 
Fatará Al-Ladhīna Fī Qulūbihim Marađun Yusāri`ūna Fīhim Yaqūlūna Nakhshá 'An Tuşībanā Dā'iratun  ۚ  Fa`asá Al-Lahu 'An Ya'tiya Bil-Fatĥi 'Aw 'Amrin Min `Indihi Fayuşbiĥū `Alá Mā 'Asarrū Fī 'Anfusihim Nādimīna 005-052 Sai ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, sunã tseren gaugawa a cikinsu, sunã cewa: "Munã tsõron kada wata masĩfa ta sãme mu." To, akwai tsammãnin Allah Ya zo da buɗi, kõ kuwa wani umurni daga wurinSa, har su wãyi gari a kan abin da suka ɓõye a cikin zukatansu, sunã mãsu nadãmã.  ۚ 
Wa Yaqūlu Al-Ladhīna 'Āmanū 'Ahā'uulā' Al-Ladhīna 'Aqsamū Bil-Lahi Jahda 'Aymānihim  ۙ  'Innahum Lama`akum  ۚ  Ĥabiţat 'A`māluhum Fa'aşbaĥū Khāsirīna 005-053 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cewa: "Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi rantsuwa da Allah iyãkar rantsuwõyinsu, cewa su, lalle sunã tãre da ku?" Ayyukansu sun ɓãci, sabõda haka suka wãyi gari sunã mãsu hasãra.  ۙ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Man Yartadda Minkum `An Dīnihi Fasawfa Ya'tī Al-Lahu Biqawmin Yuĥibbuhum Wa Yuĥibbūnahu 'Adhillatin `Alá Al-Mu'uminīna 'A`izzatin `Alá Al-Kāfirīna Yujāhidūna Fī Sabīli Al-Lahi Wa Lā Yakhāfūna Lawmata Lā'imin  ۚ  Dhālika Fađlu Al-Lahi Yu'utīhi Man Yashā'u Wa  ۚ  Allāhu Wāsi`un `Alīmun 005-054 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to, Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu'i a kan muminai mãsu izza a kan kãfurai. Sunã yin, jihãdi a cikin hanyar Allah, kuma bã su tsõron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi. ~  ۚ   ۚ 
'Innamā Wa Līyukumu Al-Lahu Wa Rasūluhu Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Al-Ladhīna Yuqīmūna Aş-Şalāata Wa Yu'utūna Az-Zakāata Wa Hum Rāki`ūna 005-055 Abin sani kawai, majiɓincinku Allah ne da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmãni,waɗanda suke sunã tsayar da salla kuma sunã bãyar da zakka kuma sunã ruku'i,
Wa Man Yatawalla Al-Laha Wa Rasūlahu Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Fa'inna Ĥizba Al-Lah 005-056 Kuma wanda ya jiɓinci Allah da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmãni, to, ƙungiyar Allah sune mãsu rinjãya.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tattakhidhū Al-Ladhīna Attakhadhū Dīnakum Huzūan Wa La`ibāan Mina Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Min Qablikum Wa Al-Kuffāra 'Awliyā'a  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha 'In Kuntum Mu'uminīna 005-057 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi waɗanda suka riƙi addininku bisa izgili da wãsa, daga waɗanda aka bai wa Littãfi daga gabãninku da kãfirai, masõya, Kuma ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai.  ۚ 
Wa 'Idhā Nādaytum 'Ilá Aş-Şalāati Attakhadhūhā Huzūan Wa La`ibāan  ۚ  Dhālika Bi'annahum Qawmun Lā Ya`qilūna 005-058 Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su riƙe ta bisa izgili da wãsa. Wannan dõmin lalle ne su, mutãne ne (waɗanda) bã su hankalta.  ۚ 
Qul Yā 'Ahla Al-Kitābi Hal Tanqimūna Minnā 'Illā 'An 'Āmannā Bil-Lahi Wa Mā 'Unzila 'Ilaynā Wa Mā 'Unzila Min Qablu Wa 'Anna 'Aktharakum Fāsiqūna 005-059 Ka ce: "Ya Mutãnen Littãfi! Shin, kunã ganin wani laifi daga gare mu? Fãce dai dõmin mun yi ĩmãni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar daga gabãni, kuma dõmin mafi yawanku fãsiƙai ne."
Qul Hal 'Unabbi'ukum Bisharrin Min Dhālika Mathūbatan `Inda Al-Lahi  ۚ  Man La`anahu Al-Lahu Wa Ghađiba `Alayhi Wa Ja`ala Minhumu Al-Qiradata Wa Al-Khanāzīra Wa `Abada Aţ-Ţāghūta  ۚ  'Ūlā'ika Sharrun Makānāan Wa 'Ađallu `An Sawā'i As-Sabīli 005-060 Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ãguta. Waɗannan ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya."  ۚ   ۚ 
Wa 'Idhā Jā'ūkum Qālū 'Āmannā Wa Qad Dakhalū Bil-Kufri Wa Hum Qad Kharajū Bihi Wa  ۚ  Allāhu 'A`lamu Bimā Kānū Yaktumūna 005-061 Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmãni." Alhãli kuwa haƙĩƙa, sun shigo da kãfirci,kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da suka kasance sunã ɓõyewa.  ۚ 
Wa Tará Kathīrāan Minhum Yusāri`ūna Fī Al-'Ithmi Wa Al-`Udwāni Wa 'Aklihimu As-Suĥta  ۚ  Labi'sa Mā Kānū Ya`malūna 005-062 Kuma kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã tseren gaugawa a cikin zunubi da zãlunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatãwa.  ۚ 
Lawlā Yanhāhumu Ar-Rabbānīyūna Wa Al-'Aĥbāru `An Qawlihimu Al-'Ithma Wa 'Aklihimu As-Suĥta  ۚ  Labi'sa Mā Kānū Yaşna`ūna 005-063 Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hanã su daga faɗarsu ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.  ۚ 
Wa Qālati Al-Yahūdu Yadu Al-Lahi Maghlūlatun  ۚ  Ghullat 'Aydīhim Wa Lu`inū Bimā Qālū  ۘ  Bal Yadāhu Mabsūţatāni Yunfiqu Kayfa Yashā'u  ۚ  Wa Layazīdanna Kathīrāan Minhum Mā 'Unzila 'Ilayka Min Rabbika Ţughyānāan Wa Kufrāan  ۚ  Wa 'Alqaynā Baynahumu Al-`Adāwata Wa Al-Baghđā'a 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati  ۚ  Kullamā 'Awqadū Nārāan Lilĥarbi 'Aţfa'ahā Al-Lahu  ۚ  Wa Yas`awna Fī Al-'Arđi Fasādāan Wa  ۚ  Allāhu Lā Yuĥibbu Al-Mufsidīna 005-064 Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi.  ۚ   ۘ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Law 'Anna 'Ahla Al-Kitābi 'Āmanū Wa Attaqaw Lakaffarnā `Anhum Sayyi'ātihim Wa La'adkhalnāhum Jannāti An-Na`īmi 005-065 Kuma dã dai lalle Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dã Mun kankare miyãgun ayyukansu daga gare su, kuma dã Mun shigar da su gidãjen Aljannar Ni'ima.
Wa Law 'Annahum 'Aqāmū At-Tawrāata Wa Al-'Injīla Wa Mā 'Unzila 'Ilayhim Min Rabbihim La'akalū Min Fawqihim Wa Min Taĥti 'Arjulihim  ۚ  Minhum 'Ummatun Muqtaşidatun  ۖ  Wa Kathīrun Minhum Sā'a Mā Ya`malūna 005-066 Kuma dã dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dã sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin ƙafãfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaitãwa kuma mãsu yawa daga gare su, abin da suke aikatawa yã munana.  ۚ   ۖ 
Yā 'Ayyuhā Ar-Rasūlu Balligh Mā 'Unzila 'Ilayka Min Rabbika  ۖ  Wa 'In Lam Taf`al Famā Ballaghta Risālatahu Wa  ۚ  Allāhu Ya`şimuka Mina An-Nāsi  ۗ  'Inna Al-Laha Lā Yahdī Al-Qawma Al-Kāfirīna 005-067 Yã kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yanã tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.  ۖ   ۚ   ۗ 
Qul Yā 'Ahla Al-Kitābi Lastum `Alá Shay'in Ĥattá Tuqīmū At-Tawrāata Wa Al-'Injīla Wa Mā 'Unzila 'Ilaykum Min Rabbikum  ۗ  Wa Layazīdanna Kathīrāan Minhum Mā 'Unzila 'Ilayka Min Rabbika Ţughyānāan Wa Kufrāan  ۖ  Falā Ta'sa `Alá Al-Qawmi Al-Kāfirīna 005-068 Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ba ku zama a kan kõme ba, sai kun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku."Kuma lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yanã ƙara wa mãsu yawa daga gare su girman kai da kãfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai.  ۗ   ۖ 
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Al-Ladhīna Hādū Wa Aş-Şābi'ūna Wa An-Naşārá Man 'Āmana Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa `Amila Şāliĥāan Falā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 005-069 Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da Nasãra, wanda ya yi ĩmãni da Allahda Rãnar Lãhira, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su zamo sunã baƙin ciki ba.
Laqad 'Akhadhnā Mīthāqa Banī 'Isrā'īla Wa 'Arsalnā 'Ilayhim Rusulāan  ۖ  Kullamā Jā'ahum Rasūlun Bimā Lā Tahwá 'Anfusuhum Farīqāan Kadhdhabū Wa Farīqāan Yaqtulūna 005-070 Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isrã'ĩla, kumaMun aiki manzanni zuwa gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da rãyukansu bã su so, wani ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sunã kashewa,  ۖ 
Wa Ĥasibū 'Allā Takūna Fitnatun Fa`amū Wa Şammū Thumma Tāba Al-Lahu `Alayhim Thumma `Amū Wa Şammū Kathīrun Minhum Wa  ۚ  Allāhu Başīrun Bimā Ya`malūna 005-071 Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bã zã ta kasance ba sai Suka makanta, kuma suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta kuma suka kurunta mãsu yawa daga gare su, alhãli Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.  ۚ 
Laqad Kafara Al-Ladhīna Qālū 'Inna Al-Laha Huwa Al-Masīĥu Abnu Maryama  ۖ  Wa Qāla Al-Masīĥu Yā Banī 'Isrā'īla A`budū Al-Laha Rabbī Wa Rabbakum  ۖ  'Innahu Man Yushrik Bil-Lahi Faqad Ĥarrama Al-Lahu `Alayhi Al-Jannata Wa Ma'wāhu An-Nāru  ۖ  Wa Mā Lilžžālimīna Min 'Anşārin 005-072 Lalle ne haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama," sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.  ۖ   ۖ   ۖ 
Laqad Kafara Al-Ladhīna Qālū 'Inna Al-Laha Thālithu Thalāthatin  ۘ  Wa Mā Min 'Ilahin 'Illā 'Ilahun Wāĥidun  ۚ  Wa 'In Lam Yantahū `Ammā Yaqūlūna Layamassanna Al-Ladhīna Kafarū Minhum `Adhābun 'Alīmun 005-073 Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kãfirta, kuma babu wani abin bautãwa fãce Ubangji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga gare su.  ۘ  ~  ۚ 
'Afalā Yatūbūna 'Ilá Al-Lahi Wa Yastaghfirūnahu Wa  ۚ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 005-074 shin fã, bã su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi gãfara, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?  ۚ 
Al-Masīĥu Abnu Maryama 'Illā Rasūlun Qad Khalat Min Qablihi Ar-Rusulu Wa 'Ummuhu Şiddīqatun  ۖ  Kānā Ya'kulāni Aţ-Ţa`āma  ۗ  Anžur Kayfa Nubayyinu Lahumu Al-'Āyāti Thumma Anžur 'Anná Yu'ufakūna 005-075 Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.  ۖ   ۗ 
Qul 'Ata`budūna Min Dūni Al-Lahi Mā Lā Yamliku Lakum Đarrāan Wa Lā Naf`āan Wa  ۚ  Allāhu Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu 005-076 Ka ce: "Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?"  ۚ 
Qul Yā 'Ahla Al-Kitābi Lā Taghlū Fī Dīnikum Ghayra Al-Ĥaqqi Wa Lā Tattabi`ū 'Ahwā'a Qawmin Qad Đallū Min Qablu Wa 'Ađallū Kathīrāan Wa Đallū `An Sawā'i As-Sabīli 005-077 Ka ce: "Yã ku Mutanen Littãfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bã gaskiya ba, kuma kada ku bĩbiyi son zuciyõyin waɗansu mutãne waɗanda suka riga suka ɓace a gabãni, kuma suka ɓatar da wasu mãsu yawa, kuma suka ɓace daga tsakar hanya."
Lu`ina Al-Ladhīna Kafarū Min Banī 'Isrā'īla `Alá Lisāni Dāwūda Wa `Īsá Abni Maryama  ۚ  Dhālika Bimā `Aşaw Wa Kānū Ya`tadūna 005-078 An la'ani waɗanda suka kãfirta daga Banĩ Isrã'ĩla a kan harshen Dãwuda da Ĩsa ɗan Maryama. wannan kuwa sabõda sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'addi .  ۚ 
Kānū Lā Yatanāhawna `An Munkarin Fa`alūhu  ۚ  Labi'sa Mā Kānū Yaf`alūna 005-079 Sun kasance bã su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka kasancesunã aikatãwa yã munana.  ۚ 
Tará Kathīrāan Minhum Yatawallawna Al-Ladhīna Kafarū  ۚ  Labi'sa Mā Qaddamat Lahum 'Anfusuhum 'An Sakhiţa Al-Lahu `Alayhim Wa Fī Al-`Adhābi Hum Khālidūna 005-080 Kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã jiɓintar waɗanda suka kãfirta. Haƙĩƙa tir da abin da rãyukansu suka gabãtar sabõda su, watau Allah Yã yi fushi da su, kuma a cikin azãba su mãsu dawwama ne  ۚ 
Wa Law Kānū Yu'uminūna Bil-Lahi Wa An-Nabīyi Wa Mā 'Unzila 'Ilayhi Mā Attakhadhūhum 'Awliyā'a Wa Lakinna Kathīrāan Minhum Fāsiqūna 005-081 Kuma dã sun kasance sunã ĩmãni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa gare shi, dã ba su riƙe su masõya ba. Kuma amma mãsu yawa daga gare su, fãsiƙai ne.
Latajidanna 'Ashadda An-Nāsi `Adāwatan Lilladhīna 'Āmanū Al-Yahūda Wa Al-Ladhīna 'Ashrakū  ۖ  Wa Latajidanna 'Aqrabahum Mawaddatan Lilladhīna 'Āmanū Al-Ladhīna Qālū 'Innā Naşārá  ۚ  Dhālika Bi'anna Minhum Qissīsīna Wa Ruhbānāan Wa 'Annahum Lā Yastakbirūna 005-082 Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni,Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu ne Nasãra." Wancan kuwa sabõda akwai ¡issawa da ruhubãnãwa daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai.  ۖ   ۚ 
Wa 'Idhā Sami`ū Mā 'Unzila 'Ilá Ar-Rasūli Tará 'A`yunahum Tafīđu Mina Ad-Dam`i Mimmā `Arafū Mina Al-Ĥaqqi  ۖ  Yaqūlūna Rabbanā 'Āmannā Fāktubnā Ma`a Ash-Shāhidīna 005-083 Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kanã ganin idanunsu sunã zubar da hawãye, sabõda abin da suka sani daga gaskiya, sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni,sai ka rubuta mu tãre da mãsu shaida.  ۖ 
Wa Mā Lanā Lā Nu'uminu Bil-Lahi Wa Mā Jā'anā Mina Al-Ĥaqqi Wa Naţma`u 'An Yudkhilanā Rabbunā Ma`a Al-Qawmi Aş-Şāliĥīna 005-084 "Kuma mene ne yake gare mu, bã zã mu yi ĩmãni daAllah ba, da kuma abin da ya zo mana daga gaskiya, kuma munã gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tãre da mutãne sãlihai?"
Fa'athābahumu Al-Lahu Bimā Qālū Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā  ۚ  Wa Dhalika Jazā'u Al-Muĥsinīna 005-085 Sabõda haka, Allah Yã sãkã musu, dõmin abin da suka faɗa da gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu, kuma wannan ne sakamakon mãsu kyautatãwa.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna Kafarū Wa Kadhdhabū Bi'āyātinā 'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Jaĥīmi 005-086 Kuma waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗancan ne abõkan Wuta.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tuĥarrimū Ţayyibāti Mā 'Aĥalla Al-Lahu Lakum Wa Lā Ta`tadū  ۚ  'Inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Al-Mu`tadīna 005-087 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi.  ۚ 
Wa Kulū Mimmā Razaqakumu Al-Lahu Ĥalālāan Ţayyibāan  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha Al-Ladhī 'Antum Bihi Mu'uminūna 005-088 Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, mãsu ĩmãni ne da shi.  ۚ 
Lā Yu'uākhidhukumu Al-Lahu Bil-Laghwi Fī 'Aymānikum Wa Lakin Yu'uākhidhukum Bimā `Aqqadtumu Al-'Īmāna  ۖ  Fakaffāratuhu 'Iţ`āmu `Asharati Masākīna Min 'Awsaţi Mā Tuţ`imūna 'Ahlīkum 'Aw Kiswatuhum 'Aw Taĥrīru Raqabatin  ۖ  Faman Lam Yajid Faşiyāmu Thalāthati 'Ayyāmin  ۚ  Dhālika Kaffāratu 'Aymānikum 'Idhā Ĥalaftum  ۚ  Wa Aĥfažū 'Aymānakum  ۚ  Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu Lakum 'Āyātihi La`allakum Tashkurūna 005-089 Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa.  ۖ  ~  ۖ   ۚ   ۚ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Innamā Al-Khamru Wa Al-Maysiru Wa Al-'Anşābu Wa Al-'Azlāmu Rijsun Min `Amali Ash-Shayţāni Fājtanibūhu La`allakum Tufliĥūna 005-090 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara.
'Innamā Yurīdu Ash-Shayţānu 'An Yūqi`a Baynakumu Al-`Adāwata Wa Al-Baghđā'a Fī Al-Khamri Wa Al-Maysiri Wa Yaşuddakum `An Dhikri Al-Lahi Wa `Ani Aş-Şalāati  ۖ  Fahal 'Antum Muntahūna 005-091 Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne?  ۖ 
Wa 'Aţī`ū Al-Laha Wa 'Aţī`ū Ar-Rasūla Wa Aĥdharū  ۚ  Fa'in Tawallaytum Fā`lamū 'Annamā `Alá Rasūlinā Al-Balāghu Al-Mubīnu 005-092 Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya.  ۚ 
Laysa `Alá Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Junāĥun Fīmā Ţa`imū 'Idhā Mā Attaqaw Wa 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Thumma Attaqaw Wa 'Āmanū Thumma Attaqaw Wa 'Aĥsanū Wa  ۗ  Allāhu Yuĥibbu Al-Muĥsinīna 005-093 Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni,sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Layabluwannakumu Al-Lahu Bishay'in Mina Aş-Şaydi Tanāluhu 'Aydīkum Wa Rimāĥukum Liya`lama Al-Lahu Man Yakhāfuhu Bil-Ghaybi  ۚ  Famani A`tadá Ba`da Dhālika Falahu `Adhābun 'Alīmun 005-094 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi. ~  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Taqtulū Aş-Şayda Wa 'Antum Ĥurumun  ۚ  Wa Man Qatalahu Minkum Muta`ammidāan Fajazā'un Mithlu Mā Qatala Mina An-Na`ami Yaĥkumu Bihi Dhawā `Adlin Minkum Hadyāan Bāligha Al-Ka`bati 'Aw Kaffāratun Ţa`āmu Masākīna 'Aw `Adlu Dhālika Şiyāmāan Liyadhūqa Wabāla 'Amrihi  ۗ  `Afā Al-Lahu `Ammā Salafa  ۚ  Wa Man `Āda Fayantaqimu Al-Lahu Minhu Wa  ۗ  Allāhu `Azīzun Dhū Antiqāmin 005-095 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa.  ۚ   ۗ   ۚ   ۗ 
'Uĥilla Lakum Şaydu Al-Baĥri Wa Ţa`āmuhu Matā`āan Lakum Wa Lilssayyārati  ۖ  Wa Ĥurrima `Alaykum Şaydu Al-Barri Mā Dumtum Ĥurumāan  ۗ  Wa Attaqū Al-Laha Al-Ladhī 'Ilayhi Tuĥsharūna 005-096 An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãɗi a gare ku, kuma dõmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama mãsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tãra ku.  ۖ   ۗ 
Ja`ala Al-Lahu Al-Ka`bata Al-Bayta Al-Ĥarāma Qiyāmāan Lilnnāsi Wa Ash-Shahra Al-Ĥarāma Wa Al-Hadya Wa Al-Qalā'ida  ۚ  Dhālika Lita`lamū 'Anna Al-Laha Ya`lamu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Wa 'Anna Al-Laha Bikulli Shay'in `Alīmun 005-097 Allah Ya sanya Ka'aba aki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yã sanya watã Mai alfarma da hadaya da rãtayõyin Allah Yã san abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kõme, Masani ne.  ۚ 
A`lamū 'Anna Al-Laha Shadīdu Al-`Iqābi Wa 'Anna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 005-098 Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Mā `Alá Ar-Rasūli 'Illā Al-Balāghu Wa  ۗ  Allāhu Ya`lamu Mā Tubdūna Wa Mā Taktumūna 005-099 Bãbu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa, kuma Allah Yanã sanin abin da kuke bayyanãwa da abin da kuke ɓõyewa.  ۗ 
Qul Lā Yastawī Al-Khabīthu Wa Aţ-Ţayyibu Wa Law 'A`jabaka Kathratu Al-Khabīthi Fa  ۚ  Attaqū Al-Laha Yā 'Ū Al-'Albābi La`allakum Tufliĥūna 005-100 Ka ce: "Mummuna da mai kyau bã su daidaita, kuma kõ dã yawan mummuan yã bã ka sha'awa. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abuta hankula ko la'alla zã ku ci nasara."  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tas'alū `An 'Ashyā'a 'In Tubda Lakum Tasu'ukum Wa 'In Tas'alū `Anhā Ĥīna Yunazzalu Al-Qur'ānu Tubda Lakum `Afā Al-Lahu `Anhā Wa  ۗ  Allāhu Ghafūrun Ĥalīmun 005-101 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin da ake saukar da Alƙur'ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.  ۗ 
Qad Sa'alahā Qawmun Min Qablikum Thumma 'Aşbaĥū Bihā Kāfirīna 005-102 Lalle ne wasu mutãne sun tambaye su daga gabãninku, sa'an nan kuma suka wãyi gari da su sanã kãfirai.
Mā Ja`ala Al-Lahu Min Baĥīratin Wa Lā Sā'ibatin Wa Lā Waşīlatin Wa Lā Ĥāmin  ۙ  Wa Lakinna Al-Ladhīna Kafarū Yaftarūna `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba  ۖ  Wa 'Aktharuhum Lā Ya`qilūna 005-103 Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka sã'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hãmi, amma waɗanda suka kãfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi yawansu bã su hankalta.  ۙ   ۖ 
Wa 'Idhā Qīla Lahum Ta`ālaw 'Ilá Mā 'Anzala Al-Lahu Wa 'Ilá Ar-Rasūli Qālū Ĥasbunā Mā Wajadnā `Alayhi 'Ābā'anā  ۚ  'Awalaw Kāna 'Ābā'uuhum Lā Ya`lamūna Shay'āan Wa Lā Yahtadūna 005-104 Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo," sai su ce: "Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kõ dã ubanninsu sun kasance bã su sanin kõme kuma bã su shiryuwa?  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū `Alaykum 'Anfusakum  ۖ  Lā Yađurrukum Man Đalla 'Idhā Ahtadaytum  ۚ  'Ilá Al-Lahi Marji`ukum Jamī`āan Fayunabbi'ukum Bimā Kuntum Ta`malūna 005-105 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci rãyukanku, wanda ya ɓace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.  ۖ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Shahādatu Baynikum 'Idhā Ĥađara 'Aĥadakumu Al-Mawtu Ĥīna Al-Waşīyati Athnāni Dhawā `Adlin Minkum 'Aw 'Ākharāni Min Ghayrikum 'In 'Antum Đarabtum Al-'Arđi Fa'aşābatkum Muşībatu Al-Mawti  ۚ  Taĥbisūnahumā Min Ba`di Aş-Şalāati Fayuqsimāni Bil-Lahi 'Ini Artabtum Lā Nashtarī Bihi Thamanāan Wa Law Kāna Dhā Qurbá  ۙ  Wa Lā Naktumu Shahādata Al-Lahi 'Innā 'Idhāan Lamina Al-'Āthimīna 005-106 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi."  ۚ   ۙ 
Fa'in `Uthira `Alá 'Annahumā Astaĥaqqā 'Ithmāan Fa'ākharāni Yaqūmāni Maqāmahumā Mina Al-Ladhīna Astaĥaqqa `Alayhimu Al-'Awlayāni Fayuqsimāni Bil-Lahi Lashahādatunā 'Aĥaqqu Min Shahādatihimā Wa Mā A`tadaynā 'Innā 'Idhāan Lamina Až-Žālimīna 005-107 To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu matsayibsu daga waɗanda suka karɓa daga gare su, mutãne biyu mafiya cancanta, sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: "Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga shaidarsu, kuma ba mu yi zãlunci ba. Lalle mu, a lõkacin haƙĩƙa, munã daga azzãlumai."
Dhālika 'Adná 'An Ya'tū Bish-Shahādati `Alá Wajhihā 'Aw Yakhāfū 'An Turadda 'Aymānun Ba`da 'Aymānihim Wa Attaqū  ۗ  Al-Laha Wa Asma`ū Wa Allāhu  ۗ  Lā Yahdī Al-Qawma Al-Fāsiqīna 005-108 Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kõ kuwa su yi tsõron a tũre rantsuwõyi a bãyan rantsuwõyinsu. Kuma ku bi Allah da taƙawa kuma ku saurara, kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.  ۗ   ۗ 
Yawma Yajma`u Al-Lahu Ar-Rusula Fayaqūlu Mādhā 'Ujibtum  ۖ  Qālū Lā `Ilma Lanā  ۖ  'Innaka 'Anta `Allāmu Al-Ghuyūbi 005-109 A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karɓa muku?" (zã) su ce: "Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake."  ۖ   ۖ 
'Idh Qāla Al-Lahu Yā `Īsá Abna Maryama Adhkur Ni`matī `Alayka Wa `Alá Wa A-Datika 'Idh 'Ayyadttuka Birūĥi Al-Qudusi Tukallimu An-Nāsa Fī Al-Mahdi Wa Kahlāan  ۖ  Wa 'Idh `Allamtuka Al-Kitāba Wa Al-Ĥikmata Wa At-Tawrāata Wa Al-'Injīla  ۖ  Wa 'Idh Takhluqu Mina Aţīni Kahay'ati Aţ-Ţayri Bi'idhnī Fatanfukhu Fīhā Fatakūnu Ţayrāan Bi'idhnī  ۖ  Wa Tubri'u Al-'Akmaha Wa Al-'Abraşa Bi'idhnī  ۖ  Wa 'Idh Tukhriju Al-Mawtá Bi'idhnī  ۖ  Wa 'Idh Kafaftu Banī 'Isrā'īla `Anka 'Idh Ji'tahum Bil-Bayyināti Faqāla Al-Ladhīna Kafarū Minhum 'In Hādhā 'Illā Siĥrun Mubīnun 005-110 A lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama!Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ¡udusi,kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne.'  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۖ 
Wa 'Idh 'Awĥaytu 'Ilá Al-Ĥawārīyīna 'An 'Āminū Bī Wa Birasūlī Qālū 'Āmannā Wa Ash/had Bi'annanā Muslimūna 005-111 "Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da ManzoNa. Suka ce: "Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne."
'Idh Qāla Al-Ĥawārīyūna Yā `Īsá Abna Maryama Hal Yastaţī`u Rabbuka 'An Yunazzila `Alaynā Mā'idatan Mina As-Samā'i  ۖ  Qāla Attaqū Al-Laha 'In Kuntum Mu'uminīna 005-112 A lõkacin da Hawarãyãwa suka ce: "Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yanã iyãwa Ya saukar da kaɓaki a kanmu daga samã?" (Ĩsã) Ya ce: "Ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai."  ۖ 
Qālū Nurīdu 'An Na'kula Minhā Wa Taţma'inna Qulūbunā Wa Na`lama 'An Qad Şadaqtanā Wa Nakūna `Alayhā Mina Ash-Shāhidīna 005-113 Suka ce: "Munã nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukãtanmu su natsu kuma mu san cewa lalle ne, kã yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga mãsu shaida a kansa."
Qāla `Īsá Abnu Maryama Al-Lahumma Rabbanā 'Anzil `Alaynā Mā'idatan Mina As-Samā'i Takūnu Lanā `Īdāan Li'wwalinā Wa 'Ākhirinā Wa 'Āyatan Minka  ۖ  Wa Arzuqnā Wa 'Anta Khayru Ar-Rāziqīna 005-114 Ĩsã ɗan Maryam ya ce: "Yã Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kaɓaki a kanmu daga sama dõmin ya zama ĩdi ga na farkonmu da na ƙarshenmu, kuma ya zama ãyã daga gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin mãsu azurtawa."  ۖ 
Qāla Al-Lahu 'Innī Munazziluhā `Alaykum  ۖ  Faman Yakfur Ba`du Minkum Fa'innī 'U`adhdhibuhu `Adhābāan Lā 'U`adhdhibuhu 'Aĥadāan Mina Al-`Ālamīna 005-115 Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya kãfirta daga gare ku, to, lalle ne Nĩ, Inã azabta shi, da wata azãba wadda bã Ni azabta ta ga kõwa daga tãlikai."  ۖ  ~
Wa 'Idh Qāla Al-Lahu Yā `Īsá Abna Maryama 'A'anta Qulta Lilnnāsi Attakhidhūnī Wa 'Ummiya 'Ilahayni Min Dūni Al-Lahi  ۖ  Qāla Subĥānaka Mā Yakūnu Lī 'An 'Aqūla Mā Laysa Lī Biĥaqqin  ۚ  'In Kuntu Qultuhu Faqad `Alimtahu  ۚ  Ta`lamu Mā Fī Nafsī Wa Lā 'A`lamu Mā Fī Nafsika  ۚ  'Innaka 'Anta `Allāmu Al-Ghuyūbi 005-116 Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsã) Ya ce: "Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne."  ۖ   ۚ   ۚ   ۚ 
Mā Qultu Lahum 'Illā Mā 'Amartanī Bihi 'Ani A`budū Al-Laha Rabbī Wa Rabbakum  ۚ  Wa Kuntu `Alayhim Shahīdāan Mā Dumtu Fīhim  ۖ  Falammā Tawaffaytanī Kunta 'Anta Ar-Raqība `Alayhim  ۚ  Wa 'Anta `Alá Kulli Shay'in Shahīdun 005-117 "Ban faɗa musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kõme, Halartacce ne. ~  ۚ   ۖ   ۚ 
'In Tu`adhdhibhum Fa'innahum `Ibāduka  ۖ  Wa 'In Taghfir Lahum Fa'innaka 'Anta Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu 005-118 "Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima."  ۖ 
Qāla Al-Lahu Hādhā Yawmu Yanfa`u Aş-Şādiqīna Şidquhum  ۚ  Lahum Jannātun Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā 'Abadāan  ۚ  Rađiya Al-Lahu `Anhum Wa Rađū `Anhu  ۚ  Dhālika Al-Fawzu Al-`Ažīmu 005-119 Allah Ya ce: "Wannan ce rãnar da mãsu gaskiya, gaskiyarsu take amfãninsu. Sunã da gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. wannan ne babban rabo mai girma."  ۚ   ۚ   ۚ 
Lillahi Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Fīhinna  ۚ  Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 005-120 Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a cikinsu kuma shi, a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne.  ۚ 
Next Sūrah