4) Sūrat An-Nisā'

Printed format

4)

Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Attaqū Rabbakumu Al-Ladhī Khalaqakum Min Nafsin Wāĥidatin Wa Khalaqa Minhā Zawjahā Wa Baththa Minhumā Rijālāan Kathīrāan Wa Nisā'an Wa Attaqū Al-Laha Al-Ladhī Tatasā'alūna Bihi Wa Al-'Arĥāma 'Inna Al-Laha Kāna `Alaykum Raqībāan 004-001 Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta . Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.  ۚ   ۚ 
Wa 'Ā Al-Yatāmá 'Amwālahum  ۖ  Wa Lā Tatabaddalū Al-Khabītha Biţ-Ţayyibi  ۖ  Wa Lā Ta'kulū 'Amwālahum 'Ilá 'Amwālikum  ۚ  'Innahu Kāna Ĥūbāan Kabīrāan 004-002 Kuma ku bai wa marãyu dũkiyõyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau. Kuma kada ku ci dũkiyõyinsu zuwa ga dũkiyõyinku. Lalle shi, yã kasance zunubi ne mai girma.  ۖ   ۖ   ۚ 
Wa 'In Khiftum 'Allā Tuqsiţū Fī Al-Yatāmá Fānkiĥū Mā Ţāba Lakum Mina An-Nisā' Mathná Wa Thulātha Wa Rubā`a  ۖ  Fa'in Khiftum 'Allā Ta`dilū Fawāĥidatan 'Aw Mā Malakat 'Aymānukum  ۚ  Dhālika 'Adná 'Allā Ta`ūlū 004-003 Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, (akwai yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.  ۖ   ۚ 
Wa 'Ā An-Nisā' Şaduqātihinna Niĥlatan  ۚ  Fa'in Ţibna Lakum `An Shay'in Minhu Nafsāan Fakulūhu Hanī'āan Marī'āan 004-004 Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin haɗiya.  ۚ 
Wa Lā Tu'utū As-Sufahā'a 'Amwālakumu Allatī Ja`ala Al-Lahu Lakum Qiyāmāan Wa Arzuqūhum Fīhā Wa Aksūhum Wa Qūlū Lahum Qawlāan Ma`rūfāan 004-005 Kada ku bai wa wãwãye dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu tsayuwa (ga gyãranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.
Wa Abtalū Al-Yatāmá Ĥattá 'Idhā Balaghū An-Nikāĥa Fa'in 'Ānastum Minhum Rushdāandfa`ū 'Ilayhim 'Amwālahum  ۖ  Wa Lā Ta'kulūhā 'Isrāfāan Wa Bidārāan 'An Yakbarū  ۚ  Wa Man Kāna Ghanīyāan Falyasta`fif  ۖ  Wa Man Kāna Faqīrāan Falya'kul Bil-Ma`rūfi  ۚ  Fa'idhā Dafa`tum 'Ilayhim 'Amwālahum Fa'ash/hidū `Alayhim  ۚ  Wa Kafá Bil-Lahi Ĥasībāan 004-006 Kuma ku jarraba marãyu, har a lõkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyõyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma da gaggawa kãfin su girma. Kuma wanda yake wadãtacce, to, ya kãma kãnsa, kuma wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu dũkiyõyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike.  ۖ   ۚ   ۖ   ۚ   ۚ 
Lilrrijāli Naşībun Mimmā Taraka Al-Wālidāni Wa Al-'Aqrabūna Wa Lilnnisā'i Naşībun Mimmā Taraka Al-Wālidāni Wa Al-'Aqrabūna Mimmā Qalla Minhu 'Aw Kathura  ۚ  Naşībāan Mafrūđāan 004-007 Maza suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.  ۚ 
Wa 'Idhā Ĥađara Al-Qismata 'Ū Al-Qurbá Wa Al-Yatāmá Wa Al-Masākīnu Fārzuqūhum Minhu Wa Qūlū Lahum Qawlāan Ma`rūfāan 004-008 Kuma idan ma'abũta zumunta da marãyu da matalauta suka halarci rabon, to, ku azurta su daga gare shi, kuma ku faɗa musu magana sananniya ta alhẽri.
Wa Līakhsha Al-Ladhīna Law Tarakū Min Khalfihim Dhurrīyatan Đi`āfāan Khāfū `Alayhim Falyattaqū Al-Laha Wa Līaqūlū Qawlāan Sadīdāan 004-009 Kuma waɗanda suke dã sun bar zuriyya mãsu rauni a bãyansu, zã su ji tsõro a kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana madaidaiciya.
'Inna Al-Ladhīna Ya'kulūna 'Amwāla Al-Yatāmá Žulmāan 'Innamā Ya'kulūna Fī Buţūnihim Nārāan  ۖ  Wa Sayaşlawna Sa`īrāan 004-010 Lalle ne, waɗanda suke cĩn dũkiyar marãyu da zãlunci, to, wuta kawai suke ci a cikin cikkunansu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani.  ۖ 
Yūşīkumu Al-Lahu Fī 'Awlādikum  ۖ  Lildhdhakari Mithlu Ĥažži Al-'Unthayayni  ۚ  Fa'in Kunna Nisā'an Fawqa Athnatayni Falahunna Thuluthā Mā Taraka  ۖ  Wa 'In Kānat Wāĥidatan Falahā An-Nişfu  ۚ  Wa Li'abawayhi Likulli Wāĥidin Minhumā As-Sudusu Mimmā Taraka 'In Kāna Lahu Waladun  ۚ  Fa'in Lam Yakun Lahu Waladun Wa Warithahu 'Abawāhu Fali'ammihi Ath-Thuluthu  ۚ  Fa'in Kāna Lahu 'Ikhwatun Fali'ammihi As-Sudusu  ۚ  Min Ba`di Waşīyatin Yūşī Bihā 'Aw Daynin  ۗ  'Ābā'uukum Wa 'Abnā'uukum Lā Tadrūna 'Ayyuhum 'Aqrabu Lakum Naf`āan  ۚ  Farīđatan Mina Al-Lahi  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna `Alīmāan Ĥakīmāan 004-011 Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu. Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi (ɗaya daga cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima.  ۖ   ۚ   ۖ   ۚ   ۚ  ~  ۚ  ~  ۚ   ۗ   ۚ   ۗ 
Wa Lakum Nişfu Mā Taraka 'Azwājukum 'In Lam Yakun Lahunna Waladun  ۚ  Fa'in Kāna Lahunna Waladun Falakumu Ar-Rubu`u Mimmā Tarakna  ۚ  Min Ba`di Waşīyatin Yūşīna Bihā 'Aw Daynin  ۚ  Wa Lahunna Ar-Rubu`u Mimmā Taraktum 'In Lam Yakun Lakum Waladun  ۚ  Fa'in Kāna Lakum Waladun Falahunna Ath-Thumunu Mimmā Taraktum  ۚ  Min Ba`di Waşīyatin Tūşūna Bihā 'Aw Daynin  ۗ  Wa 'In Kāna Rajulun Yūrathu Kalālatan 'Aw Amra'atun Wa Lahu 'Akhun 'Aw 'Ukhtun Falikulli Wāĥidin Minhumā As-Sudusu  ۚ  Fa'in Kānū 'Akthara Min Dhālika Fahum Shurakā'u Fī Ath-Thuluthi  ۚ  Min Ba`di Waşīyatin Yūşá Bihā 'Aw Daynin Ghayra Muđārrin  ۚ  Waşīyatan Mina Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥalīmun 004-012 Kuma kunã da rabin abin da mãtanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kunã da rubu'i (ɗaya daga cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bãyan wasiyya wadda suka yi kõ kuma bãshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sunã da sumuni (ɗaya daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bãyan wasiyya wadda kuka yi kõ kuwa bãshi. Idan wani namiji ya kasance ana gãdon sa bisa kalãla, ko kuwa wata mace alhãli kuwa yana da ɗan'uwa kõ 'yar'uwa to, kõwane ɗaya daga cikinsu yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa daga wannan, to, sũ abõkan tãrayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bãyan wasiyya wadda aka yi kõ kuma bãshi. Bã da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۗ  ~  ۚ   ۚ   ۚ   ۗ 
Tilka Ĥudūdu Al-Lahi  ۚ  Wa Man Yuţi`i Al-Laha Wa Rasūlahu Yudkhilhu Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā  ۚ  Wa Dhalika Al-Fawzu Al-`Ažīmu 004-013 Waɗancan iyãkõkin Allah ne. Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba.  ۚ   ۚ 
Wa Man Ya`şi Al-Laha Wa Rasūlahu Wa Yata`adda Ĥudūdahu Yudkhilhu Nārāan Khālidāan Fīhā Wa Lahu `Adhābun Muhīnun 004-014 Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa.
Wa Al-Lātī Ya'tīna Al-Fāĥishata Min Nisā'ikum Fāstash/hidū `Alayhinna 'Arba`atan  ۖ  Minkum Fa'in Shahidū Fa'amsikūhunna Fī Al-Buyūti Ĥattá Yatawaffāhunna Al-Mawtu 'Aw Yaj`ala Al-Lahu Lahunna Sabīlāan 004-015 Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nẽmi Shaidar mutãne huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su.  ۖ 
Wa Al-Ladhāni Ya'tiyānihā Minkum  ۖ  Fa'ādhūhumā Fa'in Tābā Wa 'Aşlaĥā Fa'a`riđū  ۗ  `Anhumā 'Inna Al-Laha Kāna Tawwābāan Raĥīmāan 004-016 Kuma waɗanda (mazã biyu) suka je mata daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan idan sun tũba kuma suka kyautata hãlãyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu. Lalle ne Allah Yã kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai  ۖ   ۗ 
'Innamā At-Tawbatu `Alá Al-Lahi Lilladhīna Ya`malūna As-Sū'a Bijahālatin Thumma Yatūbūna Min Qarībin Fa'ūlā'ika Yatūbu Al-Lahu `Alayhim  ۗ  Wa Kāna Al-Lahu `Alīmāan Ĥakīmāan 004-017 Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatãwar mugun aiki da jãhilci sa'an nan su tũba nan kusa to, waɗannan Allah Yanã karɓar tũ barsu kuma Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.  ۗ 
Wa Laysati At-Tawbatu Lilladhīna Ya`malūna As-Sayyi'āti Ĥattá 'Idhā Ĥađara 'Aĥadahumu Al-Mawtu Qāla 'Innī Tubtu Al-'Āna Wa Lā Al-Ladhīna Yamūtūna Wa Hum Kuffārun  ۚ  'Ūlā'ika 'A`tadnā Lahum `Adhābāan 'Alīmāan 004-018 Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tũba yanzu," kuma bã tũba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Yaĥillu Lakum 'An Tarithū An-Nisā' Karhāan  ۖ  Wa Lā Ta`đulūhunna Litadh/habū Biba`đi Mā 'Ātaytumūhunna 'Illā 'An Ya'tīna Bifāĥishatin Mubayyinatin  ۚ  Wa `Āshirūhunna Bil-Ma`rūfi  ۚ  Fa'in Karihtumūhunna Fa`asá 'An Takrahū Shay'āan Wa Yaj`ala Al-Lahu Fīhi Khayrāan Kathīrāan 004-019 Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da wata alfãsha bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa.  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa 'In 'Aradtumu Astibdāla Zawjin Makāna Zawjin Wa 'Ātaytum 'Iĥdāhunna Qinţārāan Falā Ta'khudhū Minhu Shay'āan  ۚ  'Ata'khudhūnahu Buhtānāan Wa 'Ithmāan Mubīnāan 004-020 Kuma idan kun yi nufin musanya mãta a matsayin wata mãta, alhãli kuwa kun bai wa ɗayarsu ƙinɗari to kada ku karɓi kõme daga gare, shi, shin, zã ku karɓe shi da ƙarya da zunubi bãyyananne?  ۚ 
Wa Kayfa Ta'khudhūnahu Wa Qad 'Afđá Ba`đukum 'Ilá Ba`đin Wa 'Akhadhna Minkumthāqāan Ghalīžāan 004-021 Kuma yãyã zã ku karɓe shi alhãli kuwa, haƙĩƙa, sãshenkuyã sãdu zuwa ga sãshe, kuma sun riƙi alkawari mai kauri daga gare ku?
Wa Lā Tankiĥū Mā Nakaĥa 'Ābā'uukum Mina An-Nisā' 'Illā Mā Qad Salafa  ۚ  'Innahu Kāna Fāĥishatan Wa Maqtāan Wa Sā'a Sabīlāan 004-022 Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfãsha da abin ƙyãma. Kuma ya mũnana ya zama hanya.  ۚ 
Ĥurrimat `Alaykum 'Ummahātukum Wa Banātukum Wa 'Akhawātukum Wa `Ammātukum Wa Khālātukum Wa Banātu Al-'Akhi Wa Banātu Al-'Ukhti Wa 'Ummahātukumu Al-Lātī 'Arđa`nakum Wa 'Akhawātukum Mina Ar-Rađā`ati Wa 'Ummahātu Nisā'ikum Wa Rabā'ibukumu Al-Lātī Fī Ĥujūrikum Min Nisā'ikumu Al-Lātī Dakhaltum Bihinna Fa'in Lam Takūnū Dakhaltum Bihinna Falā Junāĥa `Alaykum Wa Ĥalā'ilu 'Abnā'ikumu Al-Ladhīna Min 'Aşlābikum Wa 'An Tajma`ū Bayna Al-'Ukhtayni 'Illā Mā Qad Salafa  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna Ghafūrāan Raĥīmāan 004-023 An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mãtã, da goggonninku, da innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma, da 'yan'uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan 'yã'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai.  ۗ 
Wa Al-Muĥşanātu Mina An-Nisā' 'Illā Mā Malakat  ۖ  'Aymānukum Kitāba Al-Lahi  ۚ  `Alaykum Wa 'Uĥilla Lakum Mā Warā'a Dhālikum 'An Tabtaghū Bi'amwālikum Muĥşinīna Ghayra  ۚ  Musāfiĥīna Famā Astamta`tum Bihi Minhunna Fa'ātūhunna 'Ujūrahunna  ۚ  Farīđatan Wa Lā Junāĥa `Alaykum Fīmā Tarāđaytum Bihi Min Ba`di  ۚ  Al-Farīđati 'Inna Al-Laha Kāna `Alīmāan Ĥakīmāan 004-024 Da tsararrun auren wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya da shi a bãyan farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.  ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Man Lam Yastaţi` Minkum Ţawlāan 'An Yankiĥa Al-Muĥşanāti Al-Mu'umināti Famin Mā Malakat 'Aymānukum Min Fatayātikumu Al-Mu'umināti Wa  ۚ  Allāhu 'A`lamu Bi'īmānikum  ۚ  Ba`đukum Min Ba`đin  ۚ  Fānkiĥūhunna Bi'idhni 'Ahlihinna Wa 'Ātūhunna 'Ujūrahunna Bil-Ma`rūfi Muĥşanātin Ghayra Musāfiĥātin Wa Lā Muttakhidhāti 'Akhdānin  ۚ  Fa'idhā 'Uĥşinna Fa'in 'Atayna Bifāĥishatin Fa`alayhinna Nişfu Mā `Alá Al-Muĥşanāti Mina Al-`Adhābi  ۚ  Dhālika Liman Khashiya Al-`Anata Minkum  ۚ  Wa 'An Taşbirū Khayrun Lakum Wa  ۗ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 004-025 Kuma wanda bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya aura)daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۗ 
Yurīdu Al-Lahu Liyubayyina Lakum Wa Yahdiyakum Sunana Al-Ladhīna Min Qablikum Wa Yatūba `Alaykum Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 004-026 Allah Yanã nufin Ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyõyin waɗanda suke a gabãninku kuma Ya karɓi tũbarku. Kuma Allah Masani ne Mai hikima.  ۗ 
Wa Allāhu Yurīdu 'An Yatūba `Alaykum Wa Yurīdu Al-Ladhīna Yattabi`ūna Ash-Shahawāti 'An Tamīlū Maylāan `Ažīmāan 004-027 Kuma Allah Yanã nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha'awõyi suna nufin ku karkata, karkata mai girma.
Yurīdu Al-Lahu 'An Yukhaffifa `Ankum  ۚ  Wa Khuliqa Al-'Insānu Đa`īfāan 004-028 Allah Yana nufin Ya yi muku sauƙi, kuma an halitta mutum yana mai rauni.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Ta'kulū 'Amwālakum Baynakum Bil-Bāţili 'Illā 'An Takūna Tijāratan `An Tarāđin Minkum  ۚ  Wa Lā Taqtulū 'Anfusakum  ۚ  'Inna Al-Laha Kāna Bikum Raĥīmāan 004-029 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara, fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne.  ۚ   ۚ 
Wa Man Yaf`al Dhālika `Udwānāan Wa Žulmāan Fasawfa Nuşlīhi Nārāan  ۚ  Wa Kāna Dhālika `Alá Al-Lahi Yasīrāan 004-030 Wanda ya aikata wancan bisa ta'adi da zãlunci, to, zã Mu ƙõne shi da Wuta. Kuma wannan yã kasance ga Allah (abu ne) mai sauƙi.  ۚ 
'In Tajtanibū Kabā'ira Mā Tunhawna `Anhu Nukaffir `Ankum Sayyi'ātikum Wa Nudkhilkum Mudkhalāan Karīmāan 004-031 Idan kuka nĩsanci manyan abubuwan da ake hana ku aikatãwa, to, zã Mu kankare mũnanan ayyukanku daga gare ku, kuma Mu shigar da ku mashiga ta karimci.
Wa Lā Tatamannaw Mā Fađđala Al-Lahu Bihi Ba`đakum `Alá Ba`đin  ۚ  Lilrrijāli Naşībun Mimmā Aktasabū  ۖ  Wa Lilnnisā'i Naşībun Mimmā Aktasabna  ۚ  Wa As'alū Al-Laha Min Fađlihi  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna Bikulli Shay'in `Alīmāan 004-032 Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sãshenku da shi a kan sãshe; maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mãtã suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku rõƙi Allah daga falalarSa. Lalle ne Allah Yã kasance ga dukkan kõme, Masani.  ۚ   ۖ   ۚ  ~  ۗ 
Wa Likullin Ja`alnā Mawāliya Mimmā Taraka Al-Wālidāni Wa Al-'Aqrabūna Wa  ۚ  Al-Ladhīna `Aqadat 'Aymānukum Fa'ātūhum Naşībahum  ۚ  'Inna Al-Laha Kāna `Alá Kulli Shay'in Shahīdāan 004-033 Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla ku bã su rabonsu. Lalle ne, Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci.  ۚ   ۚ 
Ar-Rijālu Qawwāmūna `Alá An-Nisā' Bimā Fađđala Al-Lahu Ba`đahum `Alá Ba`đin Wa Bimā 'Anfaqū Min 'Amwālihim  ۚ  Fālşşāliĥātu Qānitātun Ĥāfižātun Lilghaybi Bimā Ĥafiža Al-Lahu Wa  ۚ  Al-Lātī Takhāfūna Nushūzahunna Fa`ižūhunna Wa Ahjurūhunna Fī Al-Mađāji`i Wa Ađribūhunna  ۖ  Fa'in 'Aţa`nakum Falā Tabghū `Alayhinna Sabīlāan  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna `Alīyāan Kabīrāan 004-034 Maza mãsu tsayuwa ne a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.  ۚ   ۚ   ۖ   ۗ 
Wa 'In Khiftum Shiqāqa Baynihimā Fāb`athū Ĥakamāan Min 'Ahlihi Wa Ĥakamāan Min 'Ahlihā 'In Yurīdā 'Işlāĥāan Yuwaffiqi Al-Lahu Baynahumā  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna `Alīmāan Khabīrāan 004-035 Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.  ۗ 
Wa A`budū Al-Laha Wa Lā Tushrikū Bihi Shay'āan  ۖ  Wa Bil-Wālidayni 'Iĥsānāan Wa Bidhī Al-Qurbá Wa Al-Yatāmá Wa Al-Masākīni Wa Al-Jāri Dhī Al-Qurbá Wa Al-Jāri Al-Junubi Wa Aş-Şāĥibi Bil-Janbi Wa Abni As-Sabīli Wa Mā Malakat 'Aymānukum  ۗ  'Inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Man Kāna Mukhtālāan Fakhūrāan 004-036 Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta, da maƙwabci ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin da hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance mai tãƙama, mai yawan alfahari.  ۖ   ۗ 
Al-Ladhīna Yabkhalūna Wa Ya'murūna An-Nāsa Bil-Bukhli Wa Yaktumūna Mā 'Ātāhumu Al-Lahu Min Fađlihi  ۗ  Wa 'A`tadnā Lilkāfirīna `Adhābāan Muhīnāan 004-037 Waɗanda suke yin rõwa, kuma sunã umurnin mutãne da yin rõwa, kuma suna ɓõyewar abin da Allah Ya bã su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, sabõda kãfirai, azãba mai walãkantarwa.  ۗ 
Wa Al-Ladhīna Yunfiqūna 'Amwālahum Ri'ā'a An-Nāsi Wa Lā Yu'uminūna Bil-Lahi Wa Lā Bil-Yawmi  ۗ  Al-'Ākhiri Wa Man Yakuni Ash-Shayţānu Lahu Qarīnāan Fasā'a Qarīnāan 004-038 Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu dõmin nũna wa mutãne, kuma bã su yin ĩmãni da Allah, kuma bã su yin ĩmãnida Rãnar Lãhira kuma wanda Shaiɗan ya kasance abõkin haɗi a gare shi, to, yã mũnana ga abõkinhaɗi.  ۗ 
Wa Mādhā `Alayhim Law 'Āmanū Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa 'Anfaqū Mimmā Razaqahumu Al-Lahu  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Bihim `Alīmāan 004-039 Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmãni da Allah, kumada Rãnar Lãhira, kuma sun ciyar da abin da Allah Yã azurtã su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani?  ۚ 
'Inna Al-Laha Lā Yažlimu Mithqāla Dharratin  ۖ  Wa 'In Taku Ĥasanatan Yuđā`ifhā Wa Yu'uti Min Ladunhu 'Ajrāan `Ažīmāan 004-040 Lalle ne, Allah bã Ya zãluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alhẽri ce, zai riɓanya ta, kuma Ya kãwo daga gunsa ijãra mai girma.  ۖ 
Fakayfa 'Idhā Ji'nā Min Kulli 'Ummatin Bishahīdin Wa Ji'nā Bika `Alá Hā'uulā' Shahīdāan 004-041 To, yãyã, idan Mun zo da shaidu daga dukkan al'umma, kuma Muka zo da kai a kan waɗannan, kana mai shaida!
Yawma'idhin Yawaddu Al-Ladhīna Kafarū Wa `Aşaw Ar-Rasūla Law Tusawwá Bihimu Al-'Arđu Wa Lā Yaktumūna Al-Laha Ĥadīthāan 004-042 A rãnar nan, waɗanda suka kãfirta kuma suka sãɓã wa Manzo, sunã gũrin dã an baje ƙasa dasu, kuma bã su ɓõye wa Allah wani labãri.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Taqrabū Aş-Şalāata Wa 'Antum Sukārá Ĥattá Ta`lamū Mā Taqūlūna Wa Lā Junubāan 'Illā `Ābirī Sabīlin Ĥattá Taghtasilū  ۚ  Wa 'In Kuntum Marđá 'Aw `Alá Safarin 'Aw Jā'a 'Aĥadun Minkum Mina Al-Ghā'iţi 'Aw Lāmastumu An-Nisā' Falam Tajidū Mā'an Fatayammamū Şa`īdāan Ţayyibāanmsaĥū Biwujūhikum Wa 'Aydīkum  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna `Afūwāan Ghafūrāan 004-043 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku . Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.  ۚ   ۗ 
'Alam Tara 'Ilá Al-Ladhīna 'Ūtū Naşībāan Mina Al-Kitābi Yashtarūna Ađ-Đalālata Wa Yurīdūna 'An Tađillū As-Sabīla 004-044 Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo daga Littafi, suna sayen ɓata, kuma suna nẽman ku ɓace daga hanya?
Wa Allāhu 'A`lamu  ۚ  Bi'a`dā'ikum Wa Kafá Bil-Lahi Walīyāan Wa Kafá Bil-Lahi Naşīrāan 004-045 Kuma Allah ne Mafi sani ga maƙiyanku, kuma Allah Yã isa Ya zama Majibinci, kuma Yã isa Ya zama Mataimaki.  ۚ 
Mina Al-Ladhīna Hādū Yuĥarrifūna Al-Kalima `An Mawāđi`ihi Wa Yaqūlūna Sami`nā Wa `Aşaynā Wa Asma` Ghayra Musma`in Wa Rā`inā Layyāan Bi'alsinatihim Wa Ţa`nāan Ad-Dīni  ۚ  Wa Law 'Annahum Qālū Sami`nā Wa 'Aţa`nā Wa Asma` Wa Anžurnā Lakāna Khayrāan Lahum Wa 'Aqwama Wa Lakin La`anahumu Al-Lahu Bikufrihim Falā Yu'uminūna 'Illā Qalīlāan 004-046 Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sunã karkatar da magana daga wurãrenta suna cẽwa: "Munjiya kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa, kuma rã'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," dõmin karkatarwa da harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: "Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana," haƙĩƙa, dã ya kasance mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba 'Āminū Bimā Nazzalnā Muşaddiqāan Limā Ma`akum Min Qabli 'An Naţmisa Wujūhāan Fanaruddahā `Alá 'Adrihā 'Aw Nal`anahum Kamā La`annā 'Aşĥāba As-Sabti  ۚ  Wa Kāna 'Amru Al-Lahi Maf`ūlāan 004-047 Yã kũ waɗanda aka bai wa Littãfi! Ku yi ĩmãni da abinda Muka saukar, yana mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, tun gabanin Mu shãfe wasu fuskõki, sa'an nan Mu mayar da su a kan bãyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatãwa.  ۚ 
'Inna Al-Laha Lā Yaghfiru 'An Yushraka Bihi Wa Yaghfiru Mā Dūna Dhālika Liman Yashā'u  ۚ  Wa Man Yushrik Bil-Lahi Faqadi Aftará 'Ithmāan `Ažīmāan 004-048 Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma.  ۚ 
'Alam Tara 'Ilá Al-Ladhīna Yuzakkūna 'Anfusahum  ۚ  Bali Al-Lahu Yuzakkī Man Yashā'u Wa Lā Yužlamūna Fatīlāan 004-049 Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ã'a, Allah ne Yake tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba.  ۚ 
Anžur Kayfa Yaftarūna `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba  ۖ  Wa Kafá Bihi 'Ithmāan Mubīnāan 004-050 Ka dũba yadda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah! Kuma shi ya isa ga zama zunubi bayyananne.  ۖ  ~
'Alam Tara 'Ilá Al-Ladhīna 'Ūtū Naşībāan Mina Al-Kitābi Yu'uminūna Bil-Jibti Wa Aţ-Ţāghūti Wa Yaqūlūna Lilladhīna Kafarū Hā'uulā' 'Ahdá Mina Al-Ladhīna 'Āmanū Sabīlāan 004-051 Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabõ da ga Littafi suna ĩmãni da gunki da Shaiɗan kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kãfirta: "Waɗannan ne mafiya shiriya daga waɗanda suka yi ĩmãni ga hanya"?
'Ūlā'ika Al-Ladhīna La`anahumu Al-Lahu  ۖ  Wa Man Yal`ani Al-Lahu Falan Tajida Lahu Naşīrāan 004-052 Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bã zã ka sãmi mataimaki a gare shi ba.  ۖ 
'Am Lahum Naşībun Mina Al-Mulki Fa'idhāan Lā Yu'utūna An-Nāsa Naqīrāan 004-053 Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa'an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin gurtsun dabino ba.
'Am Yaĥsudūna An-Nāsa `Alá Mā 'Ātāhumu Al-Lahu Min Fađlihi  ۖ  Faqad 'Ātaynā 'Āla 'Ibrāhīma Al-Kitāba Wa Al-Ĥikmata Wa 'Ātaynāhum Mulkāan `Ažīmāan 004-054 Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.  ۖ 
Faminhum Man 'Āmana Bihi Wa Minhum Man Şadda `Anhu  ۚ  Wa Kafá Bijahannama Sa`īrāan 004-055 To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Bi'āyātinā Sawfa Nuşlīhim Nārāan Kullamā Nađijat Julūduhum Baddalnāhum Julūdāan Ghayrahā Liyadhūqū Al-`Adhāba  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna `Azīzāan Ĥakīmāan 004-056 Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.  ۗ 
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Sanudkhiluhum Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā  ۖ  'Abadāan Lahum Fīhā 'Azwājun  ۖ  Muţahharatun Wa Nudkhiluhum Žillā Žalīlāan 004-057 Kuma waɗanda suka yiĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.  ۖ   ۖ 
'Inna Al-Laha Ya'murukum 'An Tu'uaddū Al-'Amānāti 'Ilá 'Ahlihā Wa 'Idhā Ĥakamtum Bayna An-Nāsi 'An Taĥkumū Bil-`Adli  ۚ  'Inna Al-Laha Ni`immā Ya`ižukum Bihi  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna Samī`āan Başīrāan 004-058 Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ. Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani.  ۚ  ~  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Aţī`ū Al-Laha Wa 'Aţī`ū Ar-Rasūla Wa 'Ū Al-'Amri Minkum  ۖ  Fa'in Tanāza`tumShay'in Faruddūhu 'Ilá Al-Lahi Wa Ar-Rasūli 'In Kuntum Tu'uminūna Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri  ۚ  Dhālika Khayrun Wa 'Aĥsanu Ta'wīlāan 004-059 Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.  ۖ  ~  ۚ 
'Alam Tara 'Ilá Al-Ladhīna Yaz`umūna 'Annahum 'Āmanū Bimā 'Unzila 'Ilayka Wa Mā 'Unzila Min Qablika Yurīdūna 'An Yataĥākamū 'Ilá Aţ-Ţāghūti Wa Qad 'Umirū 'An Yakfurū Bihi Wa Yurīdu Ash-Shayţānu 'An Yuđillahum Đalālāan Ba`īdāan 004-060 Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra zuwa ga ãgũtu alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.
Wa 'Idhā Qīla Lahum Ta`ālaw 'Ilá Mā 'Anzala Al-Lahu Wa 'Ilá Ar-Rasūli Ra'ayta Al-Munāfiqīna Yaşuddūna `Anka Şudūdāan 004-061 Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo" zã ka ga munãfukai sunã kange mutãne daga gare ka, kangẽwa.
Fakayfa 'Idhā 'Aşābat/hum Muşībatun Bimā Qaddamat 'Aydīhim Thumma Jā'ūka Yaĥlifūna Bil-Lahi 'In 'Aradnā 'Illā 'Iĥsānāan Wa Tawfīqāan 004-062 To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, "Ba mu yi nufin kõme ba sai kyautatawa da daidaitãwa."?
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Ya`lamu Al-Lahu Mā Fī Qulūbihim Fa'a`riđ `Anhum Wa `Ižhum Wa Qul Lahum Fī 'Anfusihim Qawlāan Balīghāan 004-063 Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha.
Wa Mā 'Arsalnā Min Rasūlin 'Illā Liyuţā`a Bi'idhni Al-Lahi  ۚ  Wa Law 'Annahum 'Idh Žalamū 'Anfusahum Jā'ūka Fāstaghfarū Al-Laha Wa Astaghfara Lahumu Ar-Rasūlu Lawajadū Al-Laha Tawwābāan Raĥīmāan 004-064 Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, sun zo maka sa'an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.  ۚ 
Falā Wa Rabbika Lā Yu'uminūna Ĥattá Yuĥakkimūka Fīmā Shajara Baynahum Thumma Lā Yajidū Fī 'Anfusihim Ĥarajāan Mimmā Qađayta Wa Yusallimū Taslīmāan 004-065 To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa.
Wa Law 'Annā Katabnā `Alayhim 'Ani Aqtulū 'Anfusakum 'Aw Akhrujū Min Diyārikum Mā Fa`alūhu 'Illā Qalīlun Minhum  ۖ  Wa Law 'Annahum Fa`alū Mā Yū`ažūna Bihi Lakāna Khayrāan Lahum Wa 'Ashadda Tathbītāan 004-066 Kuma dã dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, "Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita daga gidãjenku," dã ba su aikata shi ba, fãce kaɗan daga gare su. Kuma dã dai lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa. ~  ۖ 
Wa 'Idhāan La'ātaynāhum Min Ladunnā 'Ajrāan `Ažīmāan 004-067 Kuma a sa'an nan, haƙĩƙa, dã Mun bã su, lãda mai girma, daga gunMu.
Wa Lahadaynāhum Şirāţāan Mustaqīmāan 004-068 Kuma lalle ne, dã Mun shiryar da su hanya madaidaiciya.
Wa Man Yuţi`i Al-Laha Wa Ar-Rasūla Fa'ūlā'ika Ma`a Al-Ladhīna 'An`ama Al-Lahu `Alayhim Mina An-Nabīyīna Wa Aş-Şiddīqīna Wa Ash-Shuhadā'i Wa Aş-Şāliĥīna  ۚ  Wa Ĥasuna 'Ūlā'ika Rafīqāan 004-069 Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da masu shahãda da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya.  ۚ 
Dhālika Al-Fađlu Mina Al-Lahi  ۚ  Wa Kafá Bil-Lahi `Alīmāan 004-070 Waccan falalar daga Allah take, kuma Allah Yã isa zama Masani.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Khudhū Ĥidhrakumnfirū Thubātin 'Aw Anfirū Jamī`āan 004-071 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku riƙi shirinku sa'an nan ku fitar da hari jama'a, jama'a ko ku fitar da yaƙi gaba ɗaya.
Wa 'Inna Minkum Laman Layubaţţi'anna Fa'in 'Aşābatkum Muşībatun Qāla Qad 'An`ama Al-Lahu `Alayya 'Idh Lam 'Akun Ma`ahum Shahīdāan 004-072 Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fãsarwa . To idan wata masĩfa ta sãme ku, sai ya ce: "Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dõmin ban kasance mahalarci tãre da su ba."
Wa La'in 'Aşābakum Fađlun Mina Al-Lahi Layaqūlanna Ka'an Lam Takun Baynakum Wa Baynahu Mawaddatun Yā Laytanī Kuntu Ma`ahum Fa'afūza Fawzāan `Ažīmāan 004-073 Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta sãme ku haƙĩƙa, tabbas, yanã cẽwa, kamar wata sõyayya ba ta kasance a tsakãninku da shi ba: "Yã kaitona! Dã na zama tãre da su dai, dõmin in rabonta da rabõ mai girma!"
Falyuqātil Fī Sabīli Al-Lahi Al-Ladhīna Yashrūna Al-Ĥayāata Ad-Dunyā Bil-'Ākhirati  ۚ  Wa Man Yuqātil Fī Sabīli Al-Lahi Fayuqtal 'Aw Yaghlib Fasawfa Nu'utīhi 'Ajrāan `Ažīmāan 004-074 Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lãhira su yi yãƙi, a cikin hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yãki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa ya rinjãya, sa'an nan zã Mu ba shi ijãra mai girma.  ۚ  ~
Wa Mā Lakum Lā Tuqātilūna Fī Sabīli Al-Lahi Wa Al-Mustađ`afīna Mina Ar-Rijāli Wa An-Nisā' Wa Al-Wildāni Al-Ladhīna Yaqūlūna Rabbanā 'Akhrijnā Min Hadhihi Al-Qaryati Až-Žālimi 'Ahluhā Wa Aj`al Lanā Min Ladunka Walīyāan Wa Aj`al Lanā Min Ladunka Naşīrāan 004-075 Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa."?
Al-Ladhīna 'Āmanū Yuqātilūna Fī Sabīli Al-Lahi Wa  ۖ  Al-Ladhīna Kafarū Yuqātilūna Fī Sabīli Aţ-Ţāghūti Faqātilū 'Awliyā'a Ash-Shayţāni  ۖ  'Inna Kayda Ash-Shayţāni Kāna Đa`īfāan 004-076 Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta sunã yãƙi a cikin hanyar ãgũtu (Shaiɗan). To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni.  ۖ   ۖ 
'Alam Tara 'Ilá Al-Ladhīna Qīla Lahum Kuffū 'Aydiyakum Wa 'Aqīmū Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata Falammā Kutiba `Alayhimu Al-Qitālu 'Idhā Farīqun Minhum Yakhshawna An-Nāsa Kakhashyati Al-Lahi 'Aw 'Ashadda Khashyatan  ۚ  Wa Qālū Rabbanā Lima Katabta `Alaynā Al-Qitāla Lawlā 'Akhkhartanā 'Ilá 'Ajalin Qarībin  ۗ  Qul Matā`u Ad-Dunyā Qalīlun Wa Al-'Ākhiratu Khayrun Limani Attaqá Wa Lā Tužlamūna Fatīlāan 004-077 Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!  ۚ   ۗ 
'Aynamā Takūnū Yudrikkumu Al-Mawtu Wa Law Kuntum Fī Burūjin Mushayyadatin  ۗ  Wa 'In Tuşibhum Ĥasanatun Yaqūlū Hadhihi Min `Indi Al-Lahi  ۖ  Wa 'In Tuşibhum Sayyi'atun Yaqūlū Hadhihi Min `Indika  ۚ  Qul Kullun Min `Indi Al-Lahi  ۖ  Famāli Hā'uulā' Al-Qawmi Lā Yakādūna Yafqahūna Ĥadīthāan 004-078 "Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin gãnuwõyi ingãtattu!"Kuma idan wani alhẽri ya sãme su sai su ce: "Wannan daga wurin Allah ne," kuma idan wata cũta ta sãme su, sai su ce: "Wannan daga gare ka ne."Ka ce: "Dukkansu daga Allah ne." To, me ya sãmi waɗannan mutãne, bã su kusantar fahimtar magana?  ۗ   ۖ   ۚ   ۖ 
Mā 'Aşābaka Min Ĥasanatin Famina Al-Lahi  ۖ  Wa Mā 'Aşābaka Min Sayyi'atin Famin Nafsika  ۚ  Wa 'Arsalnāka Lilnnāsi Rasūlāan  ۚ  Wa Kafá Bil-Lahi Shahīdāan 004-079 Abin da ya sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutãne, (kana) Manzo, kuma Allah Yã isa ga zama shaida.  ۖ   ۚ   ۚ 
Man Yuţi`i Ar-Rasūla Faqad 'Aţā`a Al-Laha  ۖ  Wa Man Tawallá Famā 'Arsalnāka `Alayhim Ĥafīžāan 004-080 Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah. Kuma wanda ya jũya bãya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu.  ۖ 
Wa Yaqūlūna Ţā`atun Fa'idhā Barazū Min `Indika Bayyata Ţā'ifatun Minhum Ghayra Al-Ladhī Taqūlu Wa  ۖ  Allāhu Yaktubu Mā Yubayyitūna  ۖ  Fa'a`riđ `Anhum Wa Tawakkal `Alá Al-Lahi  ۚ  Wa Kafá Bil-Lahi Wa Kīlāan 004-081 Kuma sunã cẽwa, "Dã'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwãna da niyyar wanin abin da take faɗa, alhãli kuwa Allah na rubũta abin da suke kwãna da niyyarsa. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dõgara ga Allah, kuma Allah Yã isa ya zama wakĩli.  ۖ   ۖ   ۚ 
'Afalā Yatadabbarūna Al-Qur'āna  ۚ  Wa Law Kāna Min `Indi Ghayri Al-Lahi Lawajadū Fīhi Akhtilāfāan Kathīrāan 004-082 Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũnamai yawa?  ۚ 
Wa 'Idhā Jā'ahum 'Amrun Mina Al-'Amni 'Awi Al-Khawfi 'Adhā`ū Bihi  ۖ  Wa Law Raddūhu 'Ilá Ar-Rasūli Wa 'Ilá 'Ū Al-'Amri Minhum La`alimahu Al-Ladhīna Yastanbiţūnahu Minhum  ۗ  Wa Lawlā Fađlu Al-Lahi `Alaykum Wa Raĥmatuhu Lāttaba`tumu Ash-Shayţāna 'Illā Qalīlāan 004-083 Kuma idan wani al'amari daga aminci ko tsõro ya je musu, sai su wãtsa shi. Dã sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, zã su san shi. Kuma bã dõmin falalar Allah bã a kanku da rahamarSa, haƙĩƙa, dã kun bi Shaiɗan fãce kaɗan.  ۖ  ~  ۗ 
Faqātil Fī Sabīli Al-Lahi Lā Tukallafu 'Illā Nafsaka  ۚ  Wa Ĥarriđi Al-Mu'uminīna  ۖ  `Asá Al-Lahu 'An Yakuffa Ba'sa Al-Ladhīna Kafarū Wa  ۚ  Allāhu 'Ashaddu Ba'sāan Wa 'Ashaddu Tankīlāan 004-084 Sabõda haka, ka yi yãƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a kanka, kuma ka kwaɗaitar da mũminai. Akwai tsammãnin Allah Ya kange gãfin waɗanda suka kãfirta, kuma Allah ne Mafi tsananin gãfi, kuma Mafi tsananin azabtãwa.  ۚ   ۖ   ۚ 
Man Yashfa` Shafā`atan Ĥasanatan Yakun Lahu Naşībun Minhā  ۖ  Wa Man Yashfa` Shafā`atan Sayyi'atan Yakun Lahu Kiflun Minhā  ۗ  Wa Kāna Al-Lahu `Alá Kulli Shay'in Muqītāan 004-085 Wanda ya yi cẽto, cẽto mai kyau, zai sãmi rabo daga gare shi, kuma wanda ya yi cẽto,cẽto mummũna, zai sãmi ma'aunidaga gare shi, Kuma Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mai ƙayyade lõkaci.  ۖ   ۗ 
Wa 'Idhā Ĥuyyītum Bitaĥīyatin Faĥayyū Bi'aĥsana Minhā 'Aw Ruddūhā  ۗ  'Inna Al-Laha Kāna `Alá Kulli Shay'in Ĥasībāan 004-086 Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, kõ kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yã kasance a kan dukkan kõme Mai lissãfi.  ۗ 
Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۚ  Layajma`annakum 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati Lā Rayba Fīhi  ۗ  Wa Man 'Aşdaqu Mina Al-Lahi Ĥadīthāan 004-087 Allah bãbu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙĩƙa Yana tãra ku har zuwa ga Yinin ¡iyãma bãbu shakka a cikinsa. Kuma wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga 1ãbãri. ~  ۚ   ۗ 
Famā Lakum Al-Munāfiqīna Fi'atayni Wa Allāhu 'Arkasahum Bimā Kasabū  ۚ  'Aturīdūna 'An Tahdū Man 'Ađalla Al-Lahu  ۖ  Wa Man Yuđlili Al-Lahu Falan Tajida Lahu Sabīlāan 004-088 To, mẽne ne ya sãme ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi wata hanya ba zuwa gare shi.  ۚ   ۖ 
Wa Ddū Law Takfurūna Kamā Kafarū Fatakūnūna Sawā'an  ۖ  Falā Tattakhidhū Minhum 'Awliyā'a Ĥattá Yuhājirū Fī Sabīli Al-Lahi  ۚ  Fa'in Tawallaw Fakhudhūhumqtulūhum Ĥaythu Wajadtumūhum  ۖ  Wa Lā Tattakhidhū Minhum Walīyāan Wa Lā Naşīrāan 004-089 Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar Allah. Sa'an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki.  ۖ   ۚ   ۖ 
'Illā Al-Ladhīna Yaşilūna 'Ilá Qawmin Baynakum Wa Baynahumthāqun 'Aw Jā'ūkum Ĥaşirat Şudūruhum 'An Yuqātilūkum 'Aw Yuqātilū Qawmahum  ۚ  Wa Law Shā'a Al-Lahu Lasallaţahum `Alaykum Falaqātalūkum  ۚ  Fa'ini A`tazalūkum Falam Yuqātilūkum Wa 'Alqaw 'Ilaykumu As-Salama Famā Ja`ala Al-Lahu Lakum `Alayhim Sabīlāan 004-090 Fãce dai waɗanda suke sãduwa zuwa ga wasu mutãne waɗanda a tsakãninku da su akwai alkawari, kõ kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirãzansu sun yi ƙunci ga su yãke ku, kõ su yãƙi mutãnensu. Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yãke ku. To, idan sun nĩsance ku sa'an nan ba su yãƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu.  ۚ   ۚ 
Satajidūna 'Ākharīna Yurīdūna 'An Ya'manūkum Wa Ya'manū Qawmahum Kulla Mā Ruddū 'Ilá Al-Fitnati 'Urkisū Fīhā  ۚ  Fa'in Lam Ya`tazilūkum Wa Yulqū 'Ilaykumu As-Salama Wa Yakuffū 'Aydiyahum Fakhudhūhumqtulūhum Ĥaythu Thaqiftumūhum  ۚ  Wa 'Ūla'ikum Ja`alnā Lakum `Alayhim Sulţānāan Mubīnāan 004-091 Za ku sãmi wasu sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu.  ۚ   ۚ 
Wa Mā Kāna Limu'uminin 'An Yaqtula Mu'umināan 'Illā Khaţa'an  ۚ  Wa Man Qatala Mu'umināan Khaţa'an Fataĥrīru Raqabatin Mu'uminatin Wa Diyatun Musallamatun 'Ilá 'Ahlihi 'Illā 'An Yaşşaddaqū  ۚ  Fa'in Kāna Min Qawmin `Adūwin Lakum Wa Huwa Mu'uminun Fataĥrīru Raqabatin Mu'uminatin  ۖ  Wa 'In Kāna Min Qawmin Baynakum Wa Baynahumthāqun Fadiyatun Musallamatun 'Ilá 'Ahlihi Wa Taĥrīru Raqabatin Mu'uminatin  ۖ  Faman Lam Yajid Faşiyāmu Shahrayni Mutatābi`ayni Tawbatan Mina Al-Lahi  ۗ  Wa Kāna Al-Lahu `Alīmāan Ĥakīmāan 004-092 Kuma bã ya kasancẽwa ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutãnensa, ãce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutãne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutãne ne (waɗanda) a tsakãninku da tsakãninsu akwai alkawari, sai ya bãyar da diyya ga mutãnensa, tare da 'yanta wuya mũmina. To, wanda bai sãmi (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jẽre, dõmin tũba daga Allah. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.  ۚ  ~  ۚ   ۖ   ۖ   ۗ 
Wa Man Yaqtul Mu'umināan Muta`ammidāan Fajazā'uuhu Jahannamu Khālidāan Fīhā Wa Ghađiba Al-Lahu `Alayhi Wa La`anahu Wa 'A`adda Lahu `Adhābāan `Ažīmāan 004-093 Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Yã yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azãba mai girma.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Đarabtum Fī Sabīli Al-Lahi Fatabayyanū Wa Lā Taqūlū Liman 'Alqá 'Ilaykumu As-Salāma Lasta Mu'umināan Tabtaghūna `Arađa Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Fa`inda Al-Lahi Maghānimu Kathīratun  ۚ  Kadhālika Kuntum Min Qablu Famanna Al-Lahu `Alaykum Fatabayyanū  ۚ  'Inna Al-Laha Kāna Bimā Ta`malūna Khabīrāan 004-094 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), dõmin jihãdi, to, ku nẽmi bãyani. Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: "Bã Musulmi kake ba." Kunã nẽman hãjar rãyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai ganimõmi mãsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabãnin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Sabõda haka ku zan nẽman bayãni.Lalle ne Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.  ۚ   ۚ 
Lā Yastawī Al-Qā`idūna Mina Al-Mu'uminīna Ghayru 'Ū Ađ-Đarari Wa Al-Mujāhidūna Fī Sabīli Al-Lahi Bi'amwālihim Wa 'Anfusihim  ۚ  Fađđala Al-Lahu Al-Mujāhidīna Bi'amwālihim Wa 'Anfusihim `Alá Al-Qā`idīna Darajatan  ۚ  Wa Kullāan Wa`ada Al-Lahu Al-Ĥusná  ۚ  Wa Fađđala Al-Lahu Al-Mujāhidīna `Alá Al-Qā`idīna 'Ajrāan `Ažīmāan 004-095 Mãsu zama daga barin yãƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da mãsu jihãdi a cikin hanyar Allah da dũkiyõyinsu da rãyukansu, bã su zama daidai. Allah Yã fĩfĩta mãsu jihãdi da dũkiyoyinsu da rãyukansu a kan mãsu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Yã yi musu alkawari da abu mai kyau . Kuma Allah yã fĩfĩta mãsu jihãdi a kan mãsu zama da lãda mai girma.  ۚ   ۚ   ۚ 
Darajātin Minhu Wa Maghfiratan Wa Raĥmatan  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Ghafūrāan Raĥīmāan 004-096 Darajõji daga gare Shi da gãfara da rahama. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Tawaffāhumu Al-Malā'ikatu Žālimī 'Anfusihim Qālū Fīma Kuntum  ۖ  Qālū Kunnā Mustađ`afīna Fī Al-'Arđi  ۚ  Qālū 'Alam Takun 'Arđu Al-Lahi Wāsi`atan Fatuhājirū Fīhā  ۚ  Fa'ūlā'ika Ma'wāhum Jahannamu  ۖ  Wa Sā'at Maşīrāan 004-097 Lalle ne, waɗanda malã'ĩku suka karɓi rãyukansu, (alhãli) sunã mãsu zãluntar kansu,sun ce (musu): "A cikin me kuka kasance?" (Su kuma) suka ce: "Mun kasance waɗanda aka raunana a cikin ƙasa." Suka ce: "Ashe ƙasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba, dõmin ku yi hijira a cikinta?" To, waɗannan makõmarsu Jahannama ce. Kuma tã mũnana ta zama makõma.  ۖ   ۚ   ۚ   ۖ 
'Illā Al-Mustađ`afīna Mina Ar-Rijāli Wa An-Nisā' Wa Al-Wildāni Lā Yastaţī`ūna Ĥīlatan Wa Lā Yahtadūna Sabīlāan 004-098 Fãce waɗanda aka raunana daga maza da mãtã da yãra waɗanda bã su iya yin wata dabãra, kuma bã su shiryuwa ga hanya.
Fa'ūlā'ika `Asá Al-Lahu 'An Ya`fuwa `Anhum  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Afūwāan Ghafūrāan 004-099 To, waɗannan akwai tsammãnin Allah Ya yãfe laifi daga gare su, kuma Allah Yã kasance Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.  ۚ 
Wa Man Yuhājir Fī Sabīli Al-Lahi Yajid Al-'Arđi Murāghamāan Kathīrāan Wa Sa`atan  ۚ  Wa Man Yakhruj Min Baytihi Muhājirāan 'Ilá Al-Lahi Wa Rasūlihi Thumma Yudrik/hu Al-Mawtu Faqad Waqa`a 'Ajruhu `Alá Al-Lahi  ۗ  Wa Kāna Al-Lahu Ghafūrāan Raĥīmāan 004-100 Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar Allah, zai sãmu, a cikin ƙasa, wurãren jũyãwa mãsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lãdarsa tã auku ga Allah, Kuma Allah Yã kasance, a gare ku, Mai gãfara, Mai jin ƙai.  ۚ   ۗ 
Wa 'Idhā Đarabtum Al-'Arđi Falaysa `Alaykum Junāĥun 'An Taqşurū Mina Aş-Şalāati 'In Khiftum 'An Yaftinakumu Al-Ladhīna Kafarū  ۚ  'Inna Al-Kāfirīna Kānū Lakum `Adūwāan Mubīnāan 004-101 Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, bãbu laifi a kanku ku rage daga salla idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku. Lalle ne kãfirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne.  ۚ 
Wa 'Idhā Kunta Fīhim Fa'aqamta Lahumu Aş-Şalāata Faltaqum Ţā'ifatun Minhum Ma`aka Wa Līa'khudhū 'Asliĥatahum Fa'idhā Sajadū Falyakūnū Min Warā'ikum Wa Lta'ti Ţā'ifatun 'Ukhrá Lam Yuşallū Falyuşallū Ma`aka Wa Līa'khudhū Ĥidhrahum Wa 'Asliĥatahum  ۗ  Wadda Al-Ladhīna Kafarū Law Taghfulūna `An 'Asliĥatikum Wa 'Amti`atikum Fayamīlūna `Alaykum Maylatan Wāĥidatan  ۚ  Wa Lā Junāĥa `Alaykum 'In Kāna Bikum 'Adháan Min Maţarin 'Aw Kuntum Marđá 'An Tađa`ū 'Asliĥatakum  ۖ  Wa Khudhū Ĥidhrakum  ۗ  'Inna Al-Laha 'A`adda Lilkāfirīna `Adhābāan Muhīnāan 004-102 Kuma idan kã kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tãre da kai, kuma sai su riƙe makãmansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bãyanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tãre da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makãmansu. Waɗanda suka kãfirta sun yi gũrin dã dai kuna shagala daga makamanku da kãyanku dõmin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma bãbu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, kõ kuwa kun kasance mãsu jinya ga ku ajiye makãmanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Yã yi tattali, ga kãfirai, azãba mai walakantarwa.  ۗ   ۚ   ۖ   ۗ 
Fa'idhā Qađaytumu Aş-Şalāata Fādhkurū Al-Laha Qiyāmāan Wa Qu`ūdāan Wa `Alá Junūbikum  ۚ  Fa'idhā Aţma'nantum Fa'aqīmū Aş-Şalāata  ۚ  'Inna Aş-Şalāata Kānat `Alá Al-Mu'uminīna Kitābāan Mawqūtāan 004-103 Sa'an nan idan kun ƙãre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan sãsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tã kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta.  ۚ   ۚ 
Wa Lā Tahinū Fī Abtighā'i Al-Qawmi  ۖ  'In Takūnū Ta'lamūna Fa'innahum Ya'lamūna Kamā Ta'lamūna  ۖ  Wa Tarjūna Mina Al-Lahi Mā Lā Yarjūna  ۗ  Wa Kāna Al-Lahu `Alīmāan Ĥakīmāan 004-104 Kuma kada ku sassauta a cikin nẽman mutãnen idankun kasance kuna jin zõgi, to, lalle sũ ma, suna jin zõgi kamar yadda kuke jin zõgi. Kuma kuna tsammãni, daga Allah, abin da bã su tsammãni. Kuma Allah Yã kasance Masani Mai hikima.  ۖ   ۖ   ۗ 
'Innā 'Anzalnā 'Ilayka Al-Kitāba Bil-Ĥaqqi Litaĥkuma Bayna An-Nāsi Bimā 'Arāka Al-Lahu  ۚ  Wa Lā Takun Lilkhā'inīna Khaşīmāan 004-105 Lalle ne, Mũ, Mun saukar , zuwa gare ka, Littãfi da gaskiya, dõmin ka yi hukunci a tsakãnin mutãne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma dõmin mãsu yaudara.  ۚ 
Wa Astaghfiri Al-Laha  ۖ  'Inna Al-Laha Kāna Ghafūrāan Raĥīmāan 004-106 Kuma ka nẽmi Allah gãfara. Lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.  ۖ 
Wa Lā Tujādil `Ani Al-Ladhīna Yakhtānūna 'Anfusahum  ۚ  'Inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Man Kāna Khawwānāan 'Athīmāan 004-107 Kuma kada ka yi jãyayya dõmin tunkuɗe wa waɗanda suka yaudari kansu. Lalle ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai yawan hã'inci mai yawan zunubi.  ۚ 
Yastakhfūna Mina An-Nāsi Wa Lā Yastakhfūna Mina Al-Lahi Wa Huwa Ma`ahum 'Idh Yubayyitūna Mā Lā Yarđá Mina Al-Qawli  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Bimā Ya`malūna Muĥīţāan 004-108 Suna nẽman ɓõyewa daga mutãne kuma bã su nẽmanɓõyewa daga Allah, alhãli kuwa Shi Yana tãre da su a lõkacin da suke kwãna da niyyar yin abin da bã Ya yarda da shi daga maganar. Kuma Allah Yã kasance ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.  ۚ 
Hā'antum Hā'uulā' Jādaltum `Anhum Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Faman Yujādilu Al-Laha `Anhum Yawma Al-Qiyāmati 'Am Man Yakūnu `Alayhim Wa Kīlāan 004-109 Gã ku, yã waɗannan ! Kun yi jidãli, dõmin tunkuɗe musu (kunya)a cikin rãyuwar dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rãnar ¡iyãma? Ko kuwa wãne ne zai kasance wakĩli a kansu?
Wa Man Ya`mal Sū'āan 'Aw Yažlim Nafsahu Thumma Yastaghfiri Al-Laha Yajidi Al-Laha Ghafūrāan Raĥīmāan 004-110 Kuma wanda ya aikata cũta kõ kuwa ya zãlunci kansa, sa'an nan kuma ya nẽmi Allah gãfara, zai sãmi Allah Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Wa Man Yaksib 'Ithmāan Fa'innamā Yaksibuhu `Alá Nafsihi  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Alīmāan Ĥakīmāan 004-111 Kuma wanda ya yi tsirfanci zunubi, to yanã tsirfarsa ne a kan kansa kawai. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.  ۚ 
Wa Man Yaksib Khī'atan 'Aw 'Ithmāan Thumma Yarmi Bihi Barī'āan Faqadi Aĥtamala Buhtānāan Wa 'Ithmāan Mubīnāan 004-112 Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi sa'an nan kuma ya jẽfi wani barrantacce da shi, to, lalle ne yã tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne.
Wa Lawlā Fađlu Al-Lahi `Alayka Wa Raĥmatuhu Lahammat Ţā'ifatun Minhum 'An Yuđillūka Wa Mā Yuđillūna 'Illā 'Anfusahum  ۖ  Wa Mā Yađurrūnaka Min Shay'in  ۚ  Wa 'Anzala Al-Lahu `Alayka Al-Kitāba Wa Al-Ĥikmata Wa `Allamaka Mā Lam Takun Ta`lamu  ۚ  Wa Kāna Fađlu Al-Lahi `Alayka `Ažīmāan 004-113 Kuma bã dõmin falalar Allah ba, a kanka, da rahamarSa, haƙĩƙa, dã wata ƙungiya daga gare su ta himmatu ga su ɓatar da kai. Kuma bã su ɓatarwa fãce kansu, kuma bã su cũtar ka daga kõme, Kuma Allah Yã saukar da Littãfi da hikima gare ka, kuma Ya sanar da kai abin da ba ka kasance kã sani ba. Kuma falalar Allah tã kasance mai girma a gare ka.  ۖ   ۚ   ۚ 
Khayra Fī Kathīrin Min Najwāhum 'Illā Man 'Amara Bişadaqatin 'Aw Ma`rūfin 'Aw 'Işlāĥin Bayna An-Nāsi  ۚ  Wa Man Yaf`al Dhālika Abtighā'a Marđāati Al-Lahi Fasawfa Nu'utīhi 'Ajrāan `Ažīmāan 004-114 Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.  ۚ  ~
Wa Man Yushāqiqi Ar-Rasūla Min Ba`di Mā Tabayyana Lahu Al-Hudá Wa Yattabi` Ghayra Sabīli Al-Mu'uminīna Nuwallihi Mā Tawallá Wa Nuşlihi Jahannama  ۖ  Wa Sā'at Maşīrāan 004-115 Kuma wanda ya sãɓã wa Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar mũminai, zã Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙõne shi da Jahannama. Kuma tã mũnana ta zama makõma.  ۖ 
'Inna Al-Laha Lā Yaghfiru 'An Yushraka Bihi Wa Yaghfiru Mā Dūna Dhālika Liman Yashā'u  ۚ  Wa Man Yushrik Bil-Lahi Faqad Đalla Đalālāan Ba`īdāan 004-116 Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nĩsa.  ۚ 
'In Yad`ūna Min Dūnihi 'Illā 'Ināthāan Wa 'In Yad`ūna 'Illā Shayţānāan Marīdāan 004-117 Bã su kiran kõwa, baicin Shi, fãce mãtã kuma bã su kiran kõwa fãce Shaiɗan, mai tsaurin kai. ~
La`anahu Al-Lahu  ۘ  Wa Qāla La'attakhidhanna Min `Ibādika Naşībāan Mafrūđāan 004-118 Allah Yã la'ane shi. Kuma ya ce: "Lalle ne, zã ni riƙi rabõ yankakke , daga bãyinKa.  ۘ 
Wa La'uđillannahum Wa La'umanniyannahum Wa La'āmurannahum Falayubattikunna 'Ādhāna Al-'An`ām Wa La'āmurannahum Falayughayyirunna Khalqa Al-Lahi  ۚ  Wa Man Yattakhidhi Ash-Shayţāna Walīyāan Min Dūni Al-Lahi Faqad Khasira Khusrānāan Mubīnāan 004-119 "Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dõmin su kãtse kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su dõmin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya.  ۚ 
Ya`iduhum Wa Yumannīhim  ۖ  Wa Mā Ya`iduhumu Ash-Shayţānu 'Illā Ghurūrāan 004-120 Yanã yi musu alkawari, kuma yanã sanya musu gũri, alhãli Shaiɗan bã ya yi musu wani wa'adĩn kõme face ruɗi.  ۖ 
'Ūlā'ika Ma'wāhum Jahannamu Wa Lā Yajidūna `Anhā Maĥīşāan 004-121 Waɗannan matattararsu Jahannama ce, kuma bã sãmun makarkata daga gare ta.
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Sanudkhiluhum Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā  ۖ  'Abadāan Wa`da Al-Lahi  ۚ  Ĥaqqāan Wa Man 'Aşdaqu Mina Al-Lahi Qīlāan 004-122 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, zã mu shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?  ۖ   ۚ 
Laysa Bi'amānīyikum Wa Lā 'Amānīyi 'Ahli Al-Kitābi  ۗ  Man Ya`mal Sū'āan Yujza Bihi Wa Lā Yajid Lahu Min Dūni Al-Lahi Walīyāan Wa Lā Naşīrāan 004-123 (Al'amari) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma ba gũrace- gũracen Mutãnen Littãfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki zã a sãka masa da shi kuma bã zai sãmi wani masõyi ba, baicin Allah, kuma bã zai sãmi mataimaki ba.  ۗ 
Wa Man Ya`mal Mina Aş-Şāliĥāti Min Dhakarin 'Aw 'Unthá Wa Huwa Mu'uminun Fa'ūlā'ika Yadkhulūna Al-Jannata Wa Lā Yužlamūna Naqīrāan 004-124 Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhãli kuwa Yanã mũmini, to, waɗannan sunã shiga Aljanna kuma bã zã a zãlunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba.
Wa Man 'Aĥsanu Dīnāan Mimman 'Aslama Wajhahu Lillahi Wa Huwa Muĥsinun Wa Attaba`a Millata 'Ibrāhīma Ĥanīfāan Wa Attakhadha  ۗ  Al-Lahu 'Ibrāhīma Khalīlāan 004-125 Kuma wãne ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yanã mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrãhĩm, Yanã mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Yã riƙi Ibrãhĩm badãɗayi .  ۗ 
Wa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Bikulli Shay'in Muĥīţāan 004-126 Kuma Allah ke da (mallakar) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã kasance, a dukkan, kõme, Mai kẽwayewa.  ۚ 
Wa Yastaftūnaka Fī An-Nisā'  ۖ  Quli Al-Lahu Yuftīkum Fīhinna Wa Mā Yutlá `Alaykum Al-Kitābi Fī Yatāmá An-Nisā' Al-Lātī Lā Tu'utūnahunna Mā Kutiba Lahunna Wa Targhabūna 'An Tankiĥūhunna Wa Al-Mustađ`afīna Mina Al-Wildāni Wa 'An Taqūmū Lilyatāmá Bil-Qisţi  ۚ  Wa Mā Taf`alū Min Khayrin Fa'inna Al-Laha Kāna Bihi `Alīmāan 004-127 Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: "Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu (na gãdo) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi."  ۖ   ۚ 
Wa 'Ini Amra'atun Khāfat Min Ba`lihā Nushūzāan 'Aw 'I`rāđāan Falā Junāĥa `Alayhimā 'An Yuşliĥā Baynahumā Şulĥāan Wa  ۚ  Aş-Şulĥu Khayrun  ۗ  Wa 'Uĥđirati Al-'Anfusu Ash-Shuĥĥa  ۚ  Wa 'In Tuĥsinū Wa Tattaqū Fa'inna Al-Laha Kāna Bimā Ta`malūna Khabīrāan 004-128 Kuma idan wata mace ta ji tsõron ƙiyo daga mijinta kõ kuwa bijirẽwa to, bãbu laifi a kansu su yi sulhu a tsakãninsu, sulhu (mai kyau) Kuma yin sulhu ne mafi alhẽri. Kuma an halartar wa rayũka yin rõwa. Kuma idan kun kyautata, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne, Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.  ۚ   ۗ   ۚ 
Wa Lan Tastaţī`ū 'An Ta`dilū Bayna An-Nisā' Wa Law Ĥaraştum  ۖ  Falā Tamīlū Kulla Al-Mayli Fatadharūhā Kālmu`allaqati  ۚ  Wa 'In Tuşliĥū Wa Tattaqū Fa'inna Al-Laha Kāna Ghafūrāan Raĥīmāan 004-129 Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.  ۖ   ۚ 
Wa 'In Yatafarraqā Yughni Al-Lahu Kullā Min Sa`atihi  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Wāsi`āan Ĥakīmāan 004-130 Kuma idan sun rabu, Allah zai wadãtar da kõwanne daga yalwarSa. Kuma Allah Yã kasance Mayalwaci, Mai hikima.  ۚ 
Wa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۗ  Wa Laqad Waşşaynā Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Min Qablikum Wa 'Īyākum 'Ani Attaqū Al-Laha  ۚ  Wa 'In Takfurū Fa'inna Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Ghanīyāan Ĥamīdāan 004-131 Kuma Allah ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku, da kũ, cẽwa ku bi Allah da taƙawa, kuma idan kun kãfirta, to, lalle ne, Allah Yanã da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa. Kuma Allah Yã kasance wadãtacce, Gõdadde.  ۗ   ۚ   ۚ 
Wa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۚ  Wa Kafá Bil-Lahi Wa Kīlāan 004-132 Kuma Allah ne da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa, kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli.  ۚ 
'In Yasha' Yudh/hibkum 'Ayyuhā An-Nāsu Wa Ya'ti Bi'ākharīna  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Alá Dhālika Qadīrāan 004-133 Idan Yã so, zã Ya tafi da ku, yã kũ mutãne! kuma Ya zo da wasu. Allah Yã kasance a kan haka, Mai ĩkon yi ne.  ۚ 
Man Kāna Yurīdu Thawāba Ad-Dunyā Fa`inda Al-Lahi Thawābu Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Samī`āan Başīrāan 004-134 Wanda ya kasance Yanã nufin sakamakon dũniya, to, a wurin Allah sakamakon dũniya da Lãhira yake. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Mai gani.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Kūnū Qawwāmīna Bil-Qisţi Shuhadā'a Lillahi Wa Law `Alá 'Anfusikum 'Awi Al-Wālidayni Wa Al-'Aqrabīna  ۚ  'In Yakun Ghanīyāan 'Aw Faqīrāan Fa-Allāhu 'Awlá Bihimā  ۖ  Falā Tattabi`ū Al-Hawá 'An Ta`dilū  ۚ  Wa 'In Talwū 'Aw Tu`riđū Fa'inna Al-Laha Kāna Bimā Ta`malūna Khabīrāan 004-135 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.  ۚ   ۖ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Āminū Bil-Lahi Wa Rasūlihi Wa Al-Kitābi Al-Ladhī Nazzala `Alá Rasūlihi Wa Al-Kitābi Al-Ladhī 'Anzala Min Qablu  ۚ  Wa Man Yakfur Bil-Lahi Wa Malā'ikatihi Wa Kutubihi Wa Rusulihi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Faqad Đalla Đalālāan Ba`īdāan 004-136 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Thumma Kafarū Thumma 'Āmanū Thumma Kafarū Thumma Azdādū Kufrāan Lam Yakuni Al-Lahu Liyaghfira Lahum Wa Lā Liyahdiyahum Sabīlāan 004-137 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sa'an nan kuma suka yi ĩmani, sa'an nan kuma suka kãfirta sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci, Allah bai kasance Yanã gãfarta musu ba, kuma bã zai shiryar da su ga hanya ba.
Bashshiri Al-Munāfiqīna Bi'anna Lahum `Adhābāan 'Alīmāan 004-138 Ka yi wa munãfukai bushãra da cẽwa lalle ne sunã da azãba mai raɗaɗi.
Al-Ladhīna Yattakhidhūna Al-Kāfirīna 'Awliyā'a Min Dūni Al-Mu'uminīna  ۚ  'Ayabtaghūna `Indahumu Al-`Izzata Fa'inna Al-`Izzata Lillahi Jamī`āan 004-139 Waɗanda suke riƙon kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin sunã nẽman izza ne a wurinsu? To, lalle ne izza ga Allah take gabã ɗaya.  ۚ 
Wa Qad Nazzala `Alaykum Al-Kitābi 'An 'Idhā Sami`tum 'Āyāti Al-Lahi Yukfaru Bihā Wa Yustahza'u Bihā Falā Taq`udū Ma`ahum Ĥattá Yakhūđū Fī Ĥadīthin Ghayrihi  ۚ  'Innakum 'Idhāan Mithluhum  ۗ  'Inna Al-Laha Jāmi`u Al-Munāfiqīna Wa Al-Kāfirīna Fī Jahannama Jamī`āan 004-140 Kuma lalle ne Yã sassaukar muku a cikin Littãfi cẽwa idan kun ji ãyõyin Allah, anã kãfirta da su, kuma anã izgili da su, to, kada ku zauna tãre da sũ, sai sun shiga cikin wani lãbãri. Lalle ne kũ, a lõkacin nan misãlinsu kuke. Lalle ne, Allah Mai tãra munãfukai da kãfirai ne a cikin Jahannama gabã ɗaya. ~  ۚ   ۗ 
Al-Ladhīna Yatarabbaşūna Bikum Fa'in Kāna Lakum Fatĥun Mina Al-Lahi Qālū 'Alam Nakun Ma`akum Wa 'In Kāna Lilkāfirīna Naşībun Qālū 'Alam Nastaĥwidh `Alaykum Wa Namna`kum Mina Al-Mu'uminīna  ۚ  Fa-Allāhu Yaĥkumu Baynakum Yawma Al-Qiyāmati  ۗ  Wa Lan Yaj`ala Al-Lahu Lilkāfirīna `Alá Al-Mu'uminīna Sabīlāan 004-141 Waɗanda suke jiran dãko game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: "Ashe, ba mu kasance tãre da kũ ba?" Kuma idan wani rabo ya sãmu ga kãfirai sai su ce: "Ashe ba mu rinjãye ku ba, kuma muka tsare ku daga mũminai?" To,Allah ne Yake yin hukunci tsakãninku a Rãnar ¡iyãma, kuma Allah bã zai sanya hanya ba ga kãfirai a kan mũminai.  ۚ   ۗ 
'Inna Al-Munāfiqīna Yukhādi`ūna Al-Laha Wa Huwa Khādi`uhum Wa 'Idhā Qāmū 'Ilá Aş-Şalāati Qāmū Kusālá Yurā'ūna An-Nāsa Wa Lā Yadhkurūna Al-Laha 'Illā Qalīlāan 004-142 Lalle ne munãfukai sunã yaudarẽwa da Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga salla, sai su tãshi sunã mãsu kasãla. Suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan.
Mudhabdhabīna Bayna Dhālika Lā 'Ilá Hā'uulā' Wa Lā 'Ilá Hā'uulā'  ۚ  Wa Man Yuđlili Al-Lahu Falan Tajida Lahu Sabīlāan 004-143 Mãsu kai-kawo ne a tsakãnin wancan; bã zuwa ga waɗannan ba, kuma bã zuwa ga waɗannan ba. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã za ka sãmar masa wata hanya ba.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tattakhidhū Al-Kāfirīna 'Awliyā'a Min Dūni Al-Mu'uminīna  ۚ  'Aturīdūna 'An Taj`alū Lillahi `Alaykum Sulţānāan Mubīnāan 004-144 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin, kanã nufin ku sanyã wa Allah dalĩli bayyananne a kanku?  ۚ 
'Inna Al-Munāfiqīna Fī Ad-Darki Al-'Asfali Mina An-Nāri Wa Lan Tajida Lahum Naşīrāan 004-145 Lalle ne, manãfukai sunã a magangara mafi ƙasƙanci daga wuta. Kuma bã zã ka sãma musu mataimaki ba.
'Illā Al-Ladhīna Tābū Wa 'Aşlaĥū Wa A`taşamū Bil-Lahi Wa 'Akhlaşū Dīnahum Lillahi Fa'ūlā'ika Ma`a Al-Mu'uminīna  ۖ  Wa Sawfa Yu'uti Al-Lahu Al-Mu'uminīna 'Ajrāan `Ažīmāan 004-146 Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka nẽmi fakuwa ga Allah, kuma suka tsarkake addininsu dõmin Allah, to, waɗannan sunã tãre da mũminai, kuma Allah zai bai wa mũminai lãda mai girma.  ۖ 
Mā Yaf`alu Al-Lahu Bi`adhābikum 'In Shakartum Wa 'Āmantum  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Shākirāan `Alīmāan 004-147 Mẽne ne Allah zai amfãna da yi maku azãba idan kun gõde, kuma kun yi ĩmãni? Allah Yã ksance Mai gõdiya Masani.  ۚ 
Lā Yuĥibbu Al-Lahu Al-Jahra Bis-Sū'i Mina Al-Qawli 'Illā Man Žulima  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Samī`āan `Alīmāan 004-148 Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani.  ۚ 
'In TubKhayrāan 'Aw Tukhfūhu 'Aw Ta`fū `An Sū'in Fa'inna Al-Laha Kāna `Afūwāan Qadīrāan 004-149 Idan kun bayyana alhẽri, kõ kuwa kuka ɓõye shi, kõ kuwa kuka yãfe laifi daga cũta, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfewa, Mai ikon yi. ~
'Inna Al-Ladhīna Yakfurūna Bil-Lahi Wa Rusulihi Wa Yurīdūna 'An Yufarriqū Bayna Al-Lahi Wa Rusulihi Wa Yaqūlūna Nu'uminu Biba`đin Wa Nakfuru Biba`đin Wa Yurīdūna 'An Yattakhidhū Bayna Dhālika Sabīlāan 004-150 Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: "Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe." Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan.
'Ūlā'ika Humu Al-Kāfirūna Ĥaqqāan  ۚ  Wa 'A`tadnā Lilkāfirīna `Adhābāan Muhīnāan 004-151 Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa.  ۚ 
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Bil-Lahi Wa Rusulihi Wa Lam Yufarriqū Bayna 'Aĥadin Minhum 'Ūlā'ika Sawfa Yu'utīhim  ۗ  'Ujūrahum Wa Kāna Al-Lahu Ghafūrāan Raĥīmāan 004-152 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma ba su rarrabe a tsakãnin kõwa ba daga gare su, waɗannan zã Mu bã su ijãrõrinsu, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.  ۗ 
Yas'aluka 'Ahlu Al-Kitābi 'An Tunazzila `Alayhim Kitābāan Mina As-Samā'i  ۚ  Faqad Sa'alū Mūsá 'Akbara Min Dhālika Faqālū 'Arinā Al-Laha Jahratan Fa'akhadhat/humu Aş-Şā`iqatu Bižulmihim  ۚ  Thumma Attakhadhū Al-`Ijla Min Ba`di Mā Jā'at/humu Al-Bayyinātu Fa`afawnā `An Dhālika  ۚ  Wa 'Ātaynā Mūsá Sulţānāan Mubīnāan 004-153 Mutãnen Littãfi sunã tambayar ka ka saukar da wani littãfi daga sama, a kansu, to, lalle ne sun tambayi Mũsã mũfã girma daga wannan, suka ce: "Ka nũna mana Allah bayyane." Sai tsãwa ta kãmã su sabõda zãluncinsu, sa'an nan kuma suka riƙi maraƙi (abin bautãwa) bãyan hujjoji bayyanannu sun je musu. Sa'an nan Muka yãfe laifi daga wancan. Kuma Mun bai wa Mũsã dalĩli bayyananne.  ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Rafa`nā Fawqahumu Aţūra Bimīthāqihim Wa Qulnā Lahum Adkhulū Al-Bāba Sujjadāan Wa Qulnā Lahumu Lā Ta`dū Fī As-Sabti Wa 'Akhadhnā Minhumthāqāan Ghalīžāan 004-154 Kuma Muka ɗaukaka dũtse sãma da su, sabõda alkawarinsu, kuma Muka ce musu: "Ku shiga ƙõfar kunã mãsu tawãli'u," Kuma Muka ce musu: "Kada ku ƙẽtare haddi a cikin Asabat," kuma Muka riƙi alkawari mai kauri daga gare su."
Fabimā Naqđihimthāqahum Wa Kufrihim Bi'āyāti Al-Lahi Wa Qatlihimu Al-'Anbiyā'a Bighayri Ĥaqqin Wa Qawlihim Qulūbunā Ghulfun  ۚ  Bal Ţaba`a Al-Lahu `Alayhā Bikufrihim Falā Yu'uminūna 'Illā Qalīlāan 004-155 To, sabõda warwarẽwarsu ga alkawarinsu, da kãfirtarsu da ãyõyin Allah, da kisansu ga Annabãwa, bã da hakki ba, da maganarsu: "Zukãtanmu sunã cikin rufi." Ã'a, Allah ne Ya yunƙe a kansu sabõda kãfircinsu, sabõda haka bã zã su yi ĩmãni ba fãce kaɗan.  ۚ 
Wa Bikufrihim Wa Qawlihim `Alá Maryama Buhtānāan `Ažīmāan 004-156 Kuma sabõda kãfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma.
Wa Qawlihim 'Innā Qatalnā Al-Masīĥa `Īsá Abna Maryama Rasūla Al-Lahi Wa Mā Qatalūhu Wa Mā Şalabūhu Wa Lakin Shubbiha Lahum  ۚ  Wa 'Inna Al-Ladhīna Akhtalafū Fīhi Lafī Shakkin Minhu  ۚ  Mā Lahum Bihi Min `Ilmin 'Illā Attibā`a Až-Žanni  ۚ  Wa Mā Qatalūhu Yaqīnāan 004-157 Da faɗarsu : "Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah," alhãli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka sãɓã wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare, shi, bã da wani ilmi fãce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni.  ۚ   ۚ   ۚ 
Bal Rafa`ahu Al-Lahu 'Ilayhi  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Azīzāan Ĥakīmāan 004-158 Ã'a, Allah Ya ɗauke shi zuwa garẽ Shi, kuma Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.  ۚ 
Wa 'In Min 'Ahli Al-Kitābi 'Illā Layu'uminanna Bihi Qabla Mawtihi  ۖ  Wa Yawma Al-Qiyāmati Yakūnu `Alayhim Shahīdāan 004-159 Kuma bãbu kõwa daga Mutãnen Littafi , fãce lalle yanã ĩmãni da shi a gabãnin mutuwarsa, kuma a Rãnar ¡iyãma yana kasancẽwa mai shaida, a kansu.  ۖ 
Fabižulmin Mina Al-Ladhīna Hādū Ĥarramnā `Alayhim Ţayyibātin 'Uĥillat Lahum Wa Bişaddihim `An Sabīli Al-Lahi Kathīrāan 004-160 To, sabõda zãlunci daga waɗanda suka tũba (Yahũdu) Muka haramta musu abũbuwa masu dãɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma sabõda taushẽwarsu daga hanyar Allah da yawa.
Wa 'Akhdhihimu Ar-Ribā Wa Qad Nuhū `Anhu Wa 'Aklihim 'Amwāla An-Nāsi Bil-Bāţili  ۚ  Wa 'A`tadnā Lilkāfirīna Minhum `Adhābāan 'Alīmāan 004-161 Da karɓarsu ga riba, alhãli kuwa an hana su daga gare ta, da cin su ga dũkiyar mutãne daƙarya. Kuma Muka yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai raɗaɗi.  ۚ 
Lakini Ar-Rāsikhūna Fī Al-`Ilmi Minhum Wa Al-Mu'uminūna Yu'uminūna Bimā 'Unzila 'Ilayka Wa Mā 'Unzila Min Qablika Wa  ۚ  Al-Muqīmīna Aş-Şalāata Wa  ۚ  Al-Mu'utūna Az-Zakāata Wa Al-Mu'uminūna Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri 'Ūlā'ika Sanu'utīhim 'Ajrāan `Ažīmāan 004-162 Amma tabbatattu a cikin ilmi daga gare su, da mũminai, suna ĩmani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, madalla da masu tsai da salla, da mãsu bãyar da zakka, da mãsu ĩmãni daAllah da Rãnar Lãhira. Waɗannan zã Mu bã su lãda mai girma.  ۚ   ۚ 
'Innā 'Awĥaynā 'Ilayka Kamā 'Awĥaynā 'Ilá Nūĥin Wa An-Nabīyīna Min Ba`dihi  ۚ  Wa 'Awĥaynā 'Ilá 'Ibrāhīma Wa 'Ismā`īla Wa 'Isĥāqa Wa Ya`qūba Wa Al-'Asbāţi Wa `Īsá Wa 'Ayyūba Wa Yūnus Wa Hārūna Wa Sulaymāna  ۚ  Wa 'Ātaynā Dāwūda Zabūrāan 004-163 Lalle ne Mu, Mun yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa. Kuma Mun yi wahayi zuwa ga Ibrãhĩma da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Yaƙũbu da jĩkõki da ĩsa da Ayũba da Yũnusa da Hãruna da Sulaimãn. Kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.  ۚ   ۚ 
Wa Rusulāan Qad Qaşaşnāhum `Alayka Min Qablu Wa Rusulāan Lam Naqşuşhum `Alayka  ۚ  Wa Kallama Al-Lahu Mūsá Taklīmāan 004-164 Da wasu Manzanni, haƙĩ ƙa, Mun bã da lãbarinsu a gare ka daga gabãni, da wasu manzanni waɗanda ba Mu bã da lãbãrinsu ba a gare ka, kuma Allah Yã yi magana da Mũsã, magana sõsai.  ۚ 
Rusulāan Mubashshirīna Wa Mundhirīna Li'llā Yakūna Lilnnāsi `Alá Al-Lahi Ĥujjatun Ba`da Ar-Rusuli  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Azīzāan Ĥakīmāan 004-165 Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin. Kuma Allah yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.  ۚ 
Lakini Al-Lahu Yash/hadu Bimā 'Anzala 'Ilayka  ۖ  'Anzalahu Bi`ilmihi Wa  ۖ  Al-Malā'ikatu Yash/hadūna  ۚ  Wa Kafá Bil-Lahi Shahīdāan 004-166 Amma Allah Yanã shaida da abin da Ya saukar zuwa gare ka. Yã saukar da shi da saninSa. Kuma malã'iku sunã shaida. Kuma Allah Yã isa Ya zama shaida.  ۖ   ۖ   ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Wa Şaddū `An Sabīli Al-Lahi Qad Đallū Đalālāan Ba`īdāan 004-167 Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka kange (wasu mutãne) daga hanyar Allah, haƙĩƙa, sun ɓace, ɓata mai nĩsa.
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Wa Žalamū Lam Yakuni Al-Lahu Liyaghfira Lahum Wa Lā Liyahdiyahum Ţarīqāan 004-168 Lalle ne waɗanda suka kãfirta, kuma suka yi zãlunci, Allah bai kasance Yana yi musu gãfara ba, kuma bã Ya shiryar da su ga hanya.
'Illā Ţarīqa Jahannama Khālidīna Fīhā 'Abadāan  ۚ  Wa Kāna Dhālika `Alá Al-Lahi Yasīrāan 004-169 Fãce hanyar Jahannama, sunã mãsu dawwama a cikinta har abada, kuma wannan yã kasance, ga Allah, mai sauƙi.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Qad Jā'akumu Ar-Rasūlu Bil-Ĥaqqi Min Rabbikum Fa'āminū Khayrāan Lakum  ۚ  Wa 'In Takfurū Fa'inna Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Alīmāan Ĥakīmāan 004-170 Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.  ۚ   ۚ 
Yā 'Ahla Al-Kitābi Lā Taghlū Fī Dīnikum Wa Lā Taqūlū `Alá Al-Lahi 'Illā Al-Ĥaqqa  ۚ  'Innamā Al-Masīĥu `Īsá Abnu Maryama Rasūlu Al-Lahi Wa Kalimatuhu 'Alqāhā 'Ilá Maryama Wa Rūĥun Minhu  ۖ  Fa'āminū Bil-Lahi Wa Rusulihi  ۖ  Wa Lā Taqūlū Thalāthatun  ۚ  Antahū Khayrāan Lakum  ۚ  'Innamā Al-Lahu 'Ilahun Wāĥidun  ۖ  Subĥānahu 'An Yakūna Lahu Waladun  ۘ  Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۗ  Wa Kafá Bil-Lahi Wa Kīlāan 004-171 Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, "Uku". Ku hanu (daga faɗin haka) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli.  ۚ  ~  ۖ   ۖ   ۚ   ۚ   ۖ  ~  ۘ   ۗ 
Lan Yastankifa Al-Masīĥu 'An Yakūna `Abdāan Lillahi Wa Lā Al-Malā'ikatu Al-Muqarrabūna  ۚ  Wa Man Yastankif `An `Ibādatihi Wa Yastakbir Fasayaĥshuruhum 'Ilayhi Jamī`āan 004-172 Masĩhu bã ya ƙyãmar ya kasance bãwa ga Allah, kuma haka malã'ikun nan makusanta. Kuma wanda ya yi ƙyãmar bautarSa kuma yi yi girman kai, to, zai tãra su zuwa gare shi gabã ɗaya.  ۚ 
Fa'ammā Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Fayuwaffīhim 'Ujūrahum Wa Yazīduhum Min Fađlihi  ۖ  Wa 'Ammā Al-Ladhīna Astankafū Wa Astakbarū Fayu`adhdhibuhum `Adhābāan 'Alīmāan Wa Lā Yajidūna Lahum Min Dūni Al-Lahi Walīyāan Wa Lā Naşīrāan 004-173 To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to zã Ya cika musu ijãrõrinsu, kuma Yanã ƙãra musu daga falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyãma, kuma suka yi girman kai, to, zã Ya yi musu azãba, azãba mai raɗɗi kuma bã su samun wani masõyi dõmin kansu, baicin Allah, kuma bã su samun mataimaki.  ۖ 
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Qad Jā'akum Burhānun Min Rabbikum Wa 'Anzalnā 'Ilaykum Nūrāan Mubīnāan 004-174 Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa wani dalĩli daga Ubangijinku yã je muku kuma Mun saukar da wani haske, bayyananne zuwa gare ku.
Fa'ammā Al-Ladhīna 'Āmanū Bil-Lahi Wa A`taşamū Bihi Fasayudkhiluhum Fī Raĥmatin Minhu Wa Fađlin Wa Yahdīhim 'Ilayhi Şirāţāan Mustaqīmāan 004-175 To, amma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah kuma suka faku a gare Shi, to, zai shigar da su cikin wata rahama daga gare Shi da wata falala, kuma Ya shiryar da su zuwa gare Shi ga tafarki madaidaici.
Yastaftūnaka Quli Al-Lahu Yuftīkum Al-Kalālati  ۚ  'Ini Amru'uun Halaka Laysa Lahu Waladun Wa Lahu 'Ukhtun Falahā Nişfu Mā Taraka  ۚ  Wa Huwa Yarithuhā 'In Lam Yakun Lahā Waladun  ۚ  Fa'in Kānatā Athnatayni Falahumā Ath-Thuluthāni Mimmā Taraka  ۚ  Wa 'In Kānū 'Ikhwatan Rijālāan Wa Nisā'an Falildhdhakari Mithlu Ĥažži Al-'Unthayayni  ۗ  Yubayyinu Al-Lahu Lakum 'An Tađillū Wa  ۗ  Allāhu Bikulli Shay'in `Alīmun 004-176 Sunã yi maka fatawa. Ka ce: "Allah Yanã bayyana muku fatawa a cikin 'Kalãla."' Idan mutum ya halaka, ba shi da, rẽshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gãdon ta, idan wani rẽshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ('yan'uwa mãtã) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mãtã to namiji yana da misãlin rabon mãtã biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, dõmin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kõme.  ۚ  ~  ۚ   ۚ   ۚ   ۗ   ۗ 
Next Sūrah