Bismi Al-Lahi Ar-Raĥmāni Ar-Raĥīmi  | َ001-001 Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. | بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ |
Al-Ĥamdu Lillahi Rabbi Al-`Ālamīna  | َ001-002 Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu; | الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ |
Ar-Raĥmāni Ar-Raĥīmi  | َ001-003 Mai rahama, Mai jin ƙai; | الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ |
Māliki Yawmi Ad-Dīni  | َ001-004 Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako. | مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ |
'Īyāka Na`budu Wa 'Īyāka Nasta`īnu  | َ001-005 Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa. | إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ |
Ahdinā Aş-Şirāţa Al-Mustaqīma  | َ001-006 Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. | اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ |
Şirāţa Al-Ladhīna 'An`amta `Alayhim Ghayri Al-Maghđūbi `Alayhim Wa Lā Ađ-Đāllīna  | َ001-007 Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba. | صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلاَ الضَّالِّينَ |