2) Sūrat Al-Baqarah

Printed format

surah &surah &2)

'Alif-Lām-Mīm 002-001 A. L̃. M̃. --
Dhālika Al-Kitābu Lā Rayba  ۛ  Fīhi  ۛ  Hudáan Lilmuttaqīna 002-002 Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.  ۛ   ۛ 
Al-Ladhīna Yu'uminūna Bil-Ghaybi Wa Yuqīmūna Aş-Şalāata Wa Mimmā Razaqnāhum Yunfiqūna 002-003 Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.
Wa Al-Ladhīna Yu'uminūna Bimā 'Unzila 'Ilayka Wa Mā 'Unzila Min Qablika Wa Bil-'Ākhirati Hum Yūqinūna 002-004 Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.
'Ūlā'ika `Alá Hudáan Min Rabbihim  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna 002-005 Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.  ۖ 
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Sawā'un `Alayhim 'A 'Andhartahum 'Am Lam Tundhirhum Lā Yu'uminūna 002-006 Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu,shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba.
Khatama Al-Lahu `Alá Qulūbihim Wa `Alá Sam`ihim  ۖ  Wa `Alá 'Abşārihim Ghishāwatun  ۖ  Wa Lahum `Adhābun `Ažīmun 002-007 Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma.  ۖ   ۖ 
Wa Mina An-Nāsi Man Yaqūlu 'Āmannā Bil-Lahi Wa Bil-Yawmi Al-'Ākhiri Wa Mā Hum Bimu'uminīna 002-008 Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwa su ba muminai ba ne.
Yukhādi`ūna Al-Laha Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Mā Yakhda`ūna 'Illā 'Anfusahum Wa Mā Yash`urūna 002-009 Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni,alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su sakankancẽwa!
Fī Qulūbihim Marađun Fazādahumu Al-Lahu Marađāan  ۖ  Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun Bimā Kānū Yakdhibūna 002-010 A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya.  ۖ 
Wa 'Idhā Qīla Lahum Lā Tufsidū Fī Al-'Arđi Qālū 'Innamā Naĥnu Muşliĥūna 002-011 Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce: "Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!"
'Alā 'Innahum Humu Al-Mufsidūna Wa Lakin Lā Yash`urūna 002-012 To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa.
Wa 'Idhā Qīla Lahum 'Āminū Kamā 'Āmana An-Nāsu Qālū 'Anu'uminu Kamā 'Āmana As-Sufahā'u  ۗ  'Alā 'Innahum Humu As-Sufahā'u Wa Lakin Lā Ya`lamūna 002-013 Kuma idan aka ce musu: "ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce: "Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani.  ۗ 
Wa 'Idhā Laqū Al-Ladhīna 'Āmanū Qālū 'Āmannā Wa 'Idhā Khalaw 'Ilá Shayāţīnihim Qālū 'Innā Ma`akum 'Innamā Naĥnu Mustahzi'ūna 002-014 Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni,sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu, sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne."
Al-Lahu Yastahzi'u Bihim Wa Yamudduhum Fī Ţughyānihim Ya`mahūna 002-015 Allah Yana yin izgili gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa.
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Ashtaraw Ađ-Đalālata Bil-Hudá Famā Rabiĥat Tijāratuhum Wa Mā Kānū Muhtadīna 002-016 Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba.
Mathaluhum Kamathali Al-Ladhī Astawqada Nārāan Falammā 'Ađā'at Mā Ĥawlahu Dhahaba Al-Lahu Binūrihim Wa Tarakahum Fī Žulumātin Lā Yubşirūna 002-017 Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani.
Şummun Bukmun `Umyun Fahum Lā Yarji`ūna 002-018 Kurãme, bẽbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa.
'Aw Kaşayyibin Mina As-Samā'i Fīhi Žulumātun Wa Ra`dun Wa Barqun Yaj`alūna 'Aşābi`ahum Fī 'Ādhānihim Mina Aş-Şawā`iqi Ĥadhara Al-Mawti Wa  ۚ  Allāhu Muĥīţun Bil-Kāfirīna 002-019 Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai!  ۚ 
Yakādu Al-Barqu Yakhţafu 'Abşārahum  ۖ  Kullamā 'Ađā'a Lahum Mashaw Fīhi Wa 'Idhā 'Ažlama `Alayhim Qāmū  ۚ  Wa Law Shā'a Al-Lahu Ladhahaba Bisam`ihim Wa 'Abşārihim  ۚ  'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 002-020 Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.  ۖ   ۚ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu A`budū Rabbakumu Al-Ladhī Khalaqakum Wa Al-Ladhīna Min Qablikum La`allakum Tattaqūna 002-021 Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku !
Al-Ladhī Ja`ala Lakumu Al-'Arđa Firāshāan Wa As-Samā'a Binā'an Wa 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an Fa'akhraja Bihi Mina Ath-Thamarāti Rizqāan Lakum  ۖ  Falā Taj`alū Lillahi 'Andādāan Wa 'Antum Ta`lamūna 002-022 Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa,kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.  ۖ 
Wa 'In Kuntum Fī Raybin Mimmā Nazzalnā `Alá `Abdinā Fa'tū Bisūratin Min Mithlihi Wa AdShuhadā'akum Min Dūni Al-Lahi 'In Kuntum Şādiqīna 002-023 Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu, to, ku zõ da sũra guda daga misalinsa (Alƙur'ãni). Kuma ku kirãwo shaidunku baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.
Fa'in Lam Taf`alū Wa Lan Taf`alū Fa Attaqū An-Nāra Allatī Waqūduhā An-Nāsu Wa Al-Ĥijāratu  ۖ  'U`iddat Lilkāfirīna 002-024 To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikataba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfurai.  ۖ 
Wa Bashshiri Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti 'Anna Lahum Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru  ۖ  Kullamā Ruziqū Minhā Min Thamaratin Rizqāan  ۙ  Qālū Hādhā Al-Ladhī Ruziqnā Min Qablu  ۖ  Wa 'Utū Bihi Mutashābihāan  ۖ  Wa Lahum Fīhā 'Azwājun Muţahharatun  ۖ  Wa Hum Fīhā Khālidūna 002-025 Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cẽwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su, sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne.  ۖ   ۙ   ۖ   ۖ   ۖ 
'Inna Al-Laha Lā Yastaĥyī 'An Yađriba Mathalāan Mā Ba`ūđatan Famā Fawqahā  ۚ  Fa'ammā Al-Ladhīna 'Āmanū Faya`lamūna 'Annahu Al-Ĥaqqu Min Rabbihim  ۖ  Wa 'Ammā Al-Ladhīna Kafarū Fayaqūlūna Mādhā 'Arāda Al-Lahu Bihadhā Mathalāan  ۘ  Yuđillu Bihi Kathīrāan Wa Yahdī Bihi Kathīrāan  ۚ  Wa Mā Yuđillu Bihi 'Illā Al-Fāsiqīna 002-026 Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: "Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli?" na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai.  ۚ   ۖ   ۘ   ۚ  ~
Al-Ladhīna Yanquđūna `Ahda Al-Lahi Min Ba`di Mīthāqihi Wa Yaqţa`ūna Mā 'Amara Al-Lahu Bihi 'An Yūşala Wa Yufsidūna Fī Al-'Arđi  ۚ  'Ūlā'ika Humu Al-Khāsirūna 002-027 Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan sũ ne mãsu hasãra. ~  ۚ 
Kayfa Takfurūna Bil-Lahi Wa Kuntum 'Amwātāan Fa'aĥyākum  ۖ  Thumma Yumītukum Thumma Yuĥyīkum Thumma 'Ilayhi Turja`ūna 002-028 Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku?  ۖ 
Huwa Al-Ladhī Khalaqa Lakum Mā Fī Al-'Arđi Jamī`āan Thumma Astawá 'Ilá As-Samā'i Fasawwāhunna Sab`a Samāwātin  ۚ  Wa Huwa Bikulli Shay'in `Alīmun 002-029 Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma Ya daidaita zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne.  ۚ 
Wa 'Idh Qāla Rabbuka Lilmalā'ikati 'Innī Jā`ilun Al-'Arđi Khalīfatan  ۖ  Qālū 'Ataj`alu Fīhā Man Yufsidu Fīhā Wa Yasfiku Ad-Dimā'a Wa Naĥnu Nusabbiĥu Biĥamdika Wa Nuqaddisu Laka  ۖ  Qāla 'Innī 'A`lamu Mā Lā Ta`lamūna 002-030 Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã'iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa," suka ce: "Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gõde maka, kuma muna tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba."  ۖ   ۖ 
Wa `Allama 'Ādama Al-'Asmā'a Kullahā Thumma `Arađahum `Alá Al-Malā'ikati Faqāla 'Anbi'ūnī Bi'asmā'i Hā'uulā' 'In Kuntum Şādiqīna 002-031 Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan malã'iku, sa'n nan Ya ce: "Ku gaya mini sũnayen waɗannan, idan kun nasance mãsu gaskiya."
Qālū Subĥānaka Lā `Ilma Lanā 'Illā Mā `Allamtanā  ۖ  'Innaka 'Anta Al-`Alīmu Al-Ĥakīmu 002-032 Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima."  ۖ 
Qāla Yā 'Ādamu 'Anbi'hum Bi'asmā'ihim  ۖ  Falammā 'Anba'ahum Bi'asmā'ihim Qāla 'Alam 'Aqul Lakum 'Innī 'A`lamu Ghayba As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa 'A`lamu Mā Tubdūna Wa Mā Kuntum Taktumūna 002-033 Ya ce: "Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu." To, a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu, (Allah) Ya ce: "Ashe, ban ce muku ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da ) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa?"  ۖ 
Wa 'Idh Qulnā Lilmalā'ikati Asjudū Li'dama Fasajadū 'Illā 'Iblīsa 'Abá Wa Astakbara Wa Kāna Mina Al-Kāfirīna 002-034 Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
Wa Qulnā Yā 'Ādamu Askun 'Anta Wa Zawjuka Al-Jannata Wa Kulā Minhā Raghadāan Ĥaythu Shi'tumā Wa Lā Taqrabā Hadhihi Ash-Shajarata Fatakūnā Mina Až-Žālimīna 002-035 Kuma muka ce: "Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku kasance daga azzãlumai."
Fa'azallahumā Ash-Shayţānu `Anhā Fa'akhrajahumā Mimmā Kānā Fīhi  ۖ  Wa Qulnā Ahbiţū Ba`đukum Liba`đin `Adūwun  ۖ  Wa Lakum Al-'Arđi Mustaqarrun Wa Matā`un 'Ilá Ĥīnin 002-036 Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: "Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci."  ۖ   ۖ 
Fatalaqqá 'Ādamu Min Rabbihi Kalimātin Fatāba `Alayhi  ۚ  'Innahu Huwa At-Tawwābu Ar-Raĥīmu 002-037 Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa, sabõda haka ya karɓi tũba a kansa. Lalle ne Shi, Shĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.  ۚ 
Qulnā Ahbiţū Minhā Jamī`āan  ۖ  Fa'immā Ya'tiyannakum Minnī Hudáan Faman Tabi`a Hudāya Falā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 002-038 Muka ce: "Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki."  ۖ 
Wa Al-Ladhīna Kafarū Wa Kadhdhabū Bi'āyātinā 'Ūlā'ika 'Aşĥābu  ۖ  An-Nāri Hum Fīhā Khālidūna 002-039 "Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ a cikinta madawwama ne."  ۖ 
Yā Banī 'Isrā'īla Adhkurū Ni`matiya Allatī 'An`amtu `Alaykum Wa 'Awfū Bi`ahdī 'Ūfi Bi`ahdikum Wa 'Īyāya Fārhabūni 002-040 Yã Banĩ Isrã'Ĩla ! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na. Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai.
Wa 'Āminū Bimā 'Anzaltu Muşaddiqāan Limā Ma`akum Wa Lā Takūnū 'Awwala Kāfirin Bihi  ۖ  Wa Lā Tashtarū Bi'āyātī Thamanāan Qalīlāan Wa 'Īyāya Fa Attaqūni 002-041 Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane.  ۖ 
Wa Lā Talbisū Al-Ĥaqqa Bil-Bāţili Wa Taktumū Al-Ĥaqqa Wa 'Antum Ta`lamūna 002-042 Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ'i tãre da mãsu yin rukũ'i.
Wa 'Aqīmū Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata Wa Arka`ū Ma`a Ar-Rāki`īna 002-043 Shin, kuna umurnin mutãne da alhẽri, kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi? Shin, bãzã ku hankalta ba?
'Ata'murūna An-Nāsa Bil-Birri Wa Tansawna 'Anfusakum Wa 'Antum Tatlūna Al-Kitāba  ۚ  'Afalā Ta`qilūna 002-044 Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa, mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah.  ۚ 
Wa Asta`īnū Biş-Şabri Wa Aş-Şalāati  ۚ  Wa 'Innahā Lakabīratun 'Illā `Alá Al-Khāshi`īna 002-045 Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu, kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne.  ۚ 
Al-Ladhīna Yažunnūna 'Annahum Mulāqū Rabbihim Wa 'Annahum 'Ilayhi Rāji`ūna 002-046 Yã banĩ Isrã'ĩla! Ku tuna ni'imaTa, wadda Na ni'imta a kanku, kuma lalle ne Ni, na fĩfĩta ku a kan tãlikai.
Yā Banī 'Isrā'īla Adhkurū Ni`matiya Allatī 'An`amtu `Alaykum Wa 'Annī Fađđaltukum `Alá Al-`Ālamīna 002-047 Kuma ku ji tsron wani yini, (a cikinsa) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme, kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma bã su zama ana taimakon su ba.
Wa Attaqū Yawmāan Lā Tajzī Nafsun `An Nafsin Shay'āan Wa Lā Yuqbalu Minhā Shafā`atun Wa Lā Yu'ukhadhu Minhā `Adlun Wa Lā Hum Yunşarūna 002-048 - Missing -
Wa 'Idh Najjaynākum Min 'Āli Fir`awna Yasūmūnakum Sū'a Al-`Adhābi Yudhabbiĥūna 'Abnā'akum Wa Yastaĥyūna Nisā'akum  ۚ  Wa Fī Dhālikum Balā'un Min Rabbikum `Ažīmun 002-049 Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku.  ۚ 
Wa 'Idh Faraqnā Bikumu Al-Baĥra Fa'anjaynākum Wa 'Aghraqnā 'Āla Fir`awna Wa 'Antum Tanžurūna 002-050 Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo.
Wa 'Idh Wā`adnā Mūsá 'Arba`īna Laylatan Thumma Attakhadhtumu Al-`Ijla Min Ba`dihi Wa 'Antum Žālimūna 002-051 Kuma a lõkacin da muka yi wa'adi ga Mũsa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci (da bauta masa).
Thumma `Afawnā `Ankum Min Ba`di Dhālika La`allakum Tashkurūna 002-052 Sa'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdẽwa.
Wa 'Idh 'Ātaynā Mūsá Al-Kitāba Wa Al-Furqāna La`allakum Tahtadūna 002-053 Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa, tsammãninku, kuna shiryuwa.
Wa 'Idh Qāla Mūsá Liqawmihi Yā Qawmi 'Innakum Žalamtum 'Anfusakum Biāttikhādhikumu Al-`Ijla Fatūbū 'Ilá Bāri'ikumqtulū 'Anfusakum Dhālikum Khayrun Lakum `Inda Bāri'ikum Fatāba `Alaykum  ۚ  'Innahu Huwa At-Tawwābu Ar-Raĥīmu 002-054 Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.  ۚ 
Wa 'Idh Qultum Yā Mūsá Lan Nu'umina Laka Ĥattá Nará Al-Laha Jahratan Fa'akhadhatkumu Aş-Şā`iqatu Wa 'Antum Tanžurūna 002-055 Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane," sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo.
Thumma Ba`athnākum Min Ba`di Mawtikum La`allakum Tashkurūna 002-056 Sa'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdẽwa.
Wa Žallalnā `Alaykumu Al-Ghamāma Wa 'Anzalnā `Alaykumu Al-Manna Wa As-Salwá  ۖ  Kulū Min Ţayyibāti Mā Razaqnākum  ۖ  Wa Mā Žalamūnā Wa Lakin Kānū 'Anfusahum Yažlimūna 002-057 Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta.  ۖ   ۖ 
Wa 'Idh Qulnā Adkhulū Hadhihi Al-Qaryata Fakulū Minhā Ĥaythu Shi'tum Raghadāan Wa Adkhulū Al-Bāba Sujjadāan Wa Qūlū Ĥiţţatun Naghfir Lakum Khaţāyākum  ۚ  Wa Sanazīdu Al-Muĥsinīna 002-058 Kuma a lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alƙarya. San nan ku ci daga gareta, idan kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu'i, kuma ku ce; "kãyar da zunubai" Mu gãfarta muku laifukanku, kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa."  ۚ 
Fabaddala Al-Ladhīna Žalamū Qawlāan Ghayra Al-Ladhī Qīla Lahum Fa'anzalnā `Alá Al-Ladhīna Žalamū Rijzāan Mina As-Samā'i Bimā Kānū Yafsuqūna 002-059 Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu, saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci.
Wa 'Idh Astasqá Mūsá Liqawmihi Faqulnā Ađrib Bi`aşāka Al-Ĥajara  ۖ  Fānfajarat Minhu Athnatā `Ashrata `Aynāan  ۖ  Qad `Alima Kullu 'Unāsin Mashrabahum  ۖ  Kulū Wa Ashrabū Min Rizqi Al-Lahi Wa Lā Ta`thaw Fī Al-'Arđi Mufsidīna 002-060 Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa, Muka ce; "Ka dõki dũtsen da sandarka." Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo, haƙĩƙa, kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu. "Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku, kuma kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna mãsu ɓarna."  ۖ   ۖ   ۖ 
Wa 'Idhi Qultum Yā Mūsá Lan Naşbira `Alá Ţa`āmin Wāĥidind`u Lanā Rabbaka Yukhrij Lanā Mimmā Tunbitu Al-'Arđu Min Baqlihā Wa Qiththā'ihā Wa Fūmihā Wa `Adasihā Wa Başalihā  ۖ  Qāla 'Atastabdilūna Al-Ladhī Huwa 'Adná Bial-Ladhī Huwa Khayrun  ۚ  Ahbiţū Mişrāan Fa'inna Lakum Mā Sa'altum  ۗ  Wa Đuribat `Alayhimu Adh-Dhillatu Wa Al-Maskanatu Wa Bā'ū Bighađabin Mina Al-Lahi  ۗ  Dhālika Bi'annahum Kānū Yakfurūna Bi'āyāti Al-Lahi Wa Yaqtulūna An-Nabīyīna Bighayri Al-Ĥaqqi  ۗ  Dhālika Bimā `Aşaw Wa Kānū Ya`tadūna 002-061 Kuma a lõkacin da kuka ce: "Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Aannabãwa, bãda hakki ba. Wancan, sabõda sãɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi.  ۖ   ۚ   ۗ   ۗ   ۗ 
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Al-Ladhīna Hādū Wa An-Naşārá Wa Aş-Şābi'īna Man 'Āmana Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa `Amila Şāliĥāan Falahum 'Ajruhum `Inda Rabbihim Wa Lā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 002-062 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba , da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.
Wa 'Idh 'Akhadhnā Mīthāqakum Wa Rafa`nā Fawqakumu Aţūra Khudhū Mā 'Ātaynākum Biqūwatin Wa Adhkurū Mā Fīhi La`allakum Tattaqūna 002-063 Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: "Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku.
Thumma Tawallaytum Min Ba`di Dhālika  ۖ  Falawlā Fađlu Al-Lahi `Alaykum Wa Raĥmatuhu Lakuntum Mina Al-Khāsirīna 002-064 Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra."  ۖ 
Wa Laqad `Alimtumu Al-Ladhīna A`tadaw Minkum As-Sabti Faqulnā Lahum Kūnū Qiradatan Khāsi'īna 002-065 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu."
Faja`alnāhā Nakālāan Limā Bayna Yadayhā Wa Mā Khalfahā Wa Maw`ižatan Lilmuttaqīna 002-066 Muka sanya ta (mas'alar) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa.
Wa 'Idh Qāla Mūsá Liqawmihi 'Inna Al-Laha Ya'murukum 'An Tadhbaĥū Baqaratan  ۖ  Qālū 'Atattakhidhunā Huzūan  ۖ  Qāla 'A`ūdhu Bil-Lahi 'An 'Akūna Mina Al-Jāhilīn 002-067 Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai." ~  ۖ   ۖ 
Qālū Ad`u Lanā Rabbaka Yubayyin Lanā Mā Hiya  ۚ  Qāla 'Innahu Yaqūlu 'Innahā Baqaratun Lā Fāriđun Wa Lā Bikrun `Awānun Bayna Dhālika  ۖ  Fāf`alū Mā Tu'umarūna 002-068 Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku."  ۚ   ۖ 
Qālū Ad`u Lanā Rabbaka Yubayyin Lanā Mā Lawnuhā  ۚ  Qāla 'Innahu Yaqūlu 'Innahā Baqaratun Şafrā'u Fāqi`un Lawnuhā Tasurru An-Nāžirīna 002-069 Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce: "Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta."  ۚ 
Qālū Ad`u Lanā Rabbaka Yubayyin Lanā Mā Hiya 'Inna Al-Baqara Tashābaha `Alaynā Wa 'Innā 'In Shā'a Al-Lahu Lamuhtadūna 002-070 Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne shãnu suna yi mana kamã da jũna, kuma mu, idan Allah Yã so, haƙĩƙa, shiryuwa ne."
Qāla 'Innahu Yaqūlu 'Innahā BaqaratunDhalūlun Tuthīru Al-'Arđa Wa Lā Tasqī Al-Ĥartha MusallamatunShiyata Fīhā  ۚ  Qālū Al-'Āna Ji'ta Bil-Ĥaqqi  ۚ  Fadhabaĥūhā Wa Mā Kādū Yaf`alūna 002-071 Ya ce: "Lalle ne Shi, Yana cẽwa: "Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta." Suka ce: "Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba.  ۚ   ۚ 
Wa 'Idh Qataltum Nafsāan Fa Addāra'tum Fīhā Wa  ۖ  Allāhu Mukhrijun Mā Kuntum Taktumūna 002-072 Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa, kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne.  ۖ 
Faqulnā Ađribūhu Biba`đihā  ۚ  Kadhālika Yuĥyī Al-Lahu Al-Mawtá Wa Yurīkum 'Āyātihi La`allakum Ta`qilūna 002-073 Sai Muka ce: "Ku dõke shi da wani sãshenta." Kamar wancan ne Allah Yake rãyar da matattu, kuma Ya nũna muku ayõyinSa, tsammãninku kuna hankalta.  ۚ 
Thumma Qasat Qulūbukum Min Ba`di Dhālika Fahiya Kālĥijārati 'Aw 'Ashaddu Qaswatan  ۚ  Wa 'Inna Mina Al-Ĥijārati Lamā Yatafajjaru Minhu Al-'Anhāru  ۚ  Wa 'Inna Minhā Lamā Yashshaqqaqu Fayakhruju Minhu Al-Mā'u  ۚ  Wa 'Inna Minhā Lamā Yahbiţu Min Khashyati Al-Lahi  ۗ  Wa Mā Al-Lahu Bighāfilin `Ammā Ta`malūna 002-074 San'nan kuma zukãtanku, suka ƙẽƙashe daga bãyan wancan. Sabõda haka suka zamanto kamar duwatsu. Ko mafi tsananin ƙeƙashewa. kuma lalle ne daga duwãtsu, haƙĩka, akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su, haƙĩƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma lalle ne, haƙĩƙa, daga gare su, haƙĩƙa, akwai da yake fãɗõwa dõmin tsõron Allah, kuma Allah bai zama gãfili ba daga barin abin da kuke aikatãwa.  ۚ   ۚ   ۚ   ۗ 
'Afataţma`ūna 'An Yu'uminū Lakum Wa Qad Kāna Farīqun Minhum Yasma`ūna Kalāma Al-Lahi Thumma Yuĥarrifūnahu Min Ba`di Mā `Aqalūhu Wa Hum Ya`lamūna 002-075 Shin fa kuna tsammãnin zã su yi imãni sabõda ku, alhãli kuwa, haƙĩƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar da ita daga bãyan sun gãne ta, alhãli sũ, suna sane?
Wa 'Idhā Laqū Al-Ladhīna 'Āmanū Qālū 'Āmannā Wa 'Idhā Khalā Ba`đuhum 'Ilá Ba`đin Qālū 'Atuĥaddithūnahum Bimā Fataĥa Al-Lahu `Alaykum Liyuĥājjūkum Bihi `Inda Rabbikum  ۚ  'Afalā Ta`qilūna 002-076 Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni sukan ce: "Mun yi ĩmãni," kuma idan sãshensu ya wõfinta zuwa ga sãshe, sukan ce: "Shin, kuna yi musu magana da abin da Allah Ya buɗa muku ne dõmin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?" Shin fa, bã ku hankalta?  ۚ 
'Awalā Ya`lamūna 'Anna Al-Laha Ya`lamu Mā Yusirrūna Wa Mā Yu`linūna 002-077 Shin, kuma bã su sanin cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓõyẽwa da abin da suke bayyanãwa?
Wa Minhum 'Ummīyūna Lā Ya`lamūna Al-Kitāba 'Illā 'Amānīya Wa 'In Hum 'Illā Yažunnūna 002-078 Kuma daga cikinsu akwai ummiyyai, bã su da sanin Littãfi, fãce tãtsuniyoyi, kuma sũ bã kõme suke yi ba fãce suna yin zato.
Fawaylun Lilladhīna Yaktubūna Al-Kitāba Bi'aydīhim Thumma Yaqūlūna Hādhā Min `Indi Al-Lahi Liyashtarū Bihi Thamanāan Qalīlāan  ۖ  Fawaylun Lahum Mimmā Katabat 'Aydīhim Wa Waylun Lahum Mimmā Yaksibūna 002-079 To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa.  ۖ 
Wa Qālū Lan Tamassanā An-Nāru 'Illā 'Ayyāmāan Ma`dūdatan  ۚ  Qul 'Āttakhadhtum `Inda Al-Lahi `Ahdāan Falan Yukhlifa Al-Lahu `Ahdahu  ۖ  'Am Taqūlūna `Alá Al-Lahi Mā Lā Ta`lamūna 002-080 Kuma suka ce: "Wuta bã zã ta shãfe mu ba, fãce, 'yan kwãnuka ƙidãyayyu."Ka ce: "Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai sãɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?"  ۚ  ~  ۖ 
Balá Man Kasaba Sayyi'atan Wa 'Aĥāţat Bihi Khī'atuhu Fa'ūlā'ika 'Aşĥābu An-Nāri  ۖ  Hum Fīhā Khālidūna 002-081 Na'am! Wanda ya yi tsiwur-wurin mũgun abu, kuma laifinsa ya kẽwaye shi, to, waɗannan su ne 'yan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.  ۖ 
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti 'Ūlā'ika 'Aşĥābu  ۖ  Al-Jannati Hum Fīhā Khālidūna 002-082 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, sũ a cikinta madawwama ne.  ۖ 
Wa 'Idh 'Akhadhnā Mīthāqa Banī 'Isrā'īla Lā Ta`budūna 'Illā Al-Laha Wa Bil-Wālidayni 'Iĥsānāan Wa Dhī Al-Qurbá Wa Al-Yatāmá Wa Al-Masākīni Wa Qūlū Lilnnāsi Ĥusnāan Wa 'Aqīmū Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata Thumma Tawallaytum 'Illā Qalīlāan Minkum Wa 'Antum Mu`rūna 002-083 Kuma a lõkacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isrã'ĩla : "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marãyu da matalauta, kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutãne, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, sa'an nan kuka jũya bãya, fãce kaɗan daga gare ku,alhãli kuwa kuna mãsu bijirẽwa.
Wa 'Idh 'Akhadhnā Mīthāqakum Lā Tasfikūna Dimā'akum Wa Lā Tukhrijūna 'Anfusakum Min Diyārikum Thumma 'Aqrartum Wa 'Antum Tash/hadūna 002-084 Lõkacin da Muka riƙi alkawarinku; bã zã ku zubar da jininku ba, kuma bã zã ku fitar da kanku daga gidãjenku ba; sa'an nan kuka tabbatar alhãli kuwa kuna bãyar da shaida (a kanku).
Thumma 'Antum Hā'uulā' Taqtulūna 'Anfusakum Wa Tukhrijūna Farīqāan Minkum Min Diyārihim Tažāharūna `Alayhim Bil-'Ithmi Wa Al-`Udwāni Wa 'In Ya'tūkum 'Usārá Tufādūhum Wa Huwa Muĥarramun `Alaykum 'Ikhrājuhum  ۚ  'A Fatu'uminūna Biba`đi Al-Kitābi Wa Takfurūna  ۚ  Biba`đin Famā Jazā'u Man Yaf`alu Dhālika Minkum 'Illā Khizyun Al-Ĥayāati  ۖ  Ad-Dunyā Wa Yawma Al-Qiyāmati Yuraddūna 'Ilá 'Ashaddi  ۗ  Al-`Adhābi Wa Mā Al-Lahu Bighāfilin `Ammā Ta`malūna 002-085 Sa'an nan kuma, gã ku, yã waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidãjensu, kuna taimakon jũna a kansu da zunubi da zãlunci kuma idan kãmammu suka je muku kuna fansarsu alhãli kuwa shĩ fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna ĩmãni da sãshen Littãfin ne, kuma ku kãfirta da sãshe? To, mẽne ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku fãce wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya? Kuma a Rãnar ¡iyãma ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azãba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatãwa.  ۚ   ۚ   ۖ   ۗ 
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Ashtaraw Al-Ĥayāata Ad-Dunyā Bil-'Ākhirati  ۖ  Falā Yukhaffafu `Anhumu Al-`Adhābu Wa Lā Hum Yunşarūna 002-086 Waɗannan su ne waɗanda suka sayi rãyuwar dũniya da Lãhira, dõmin haka bã zã a sauƙaƙa azãba ba daga kansu, kuma sũ, bã ataimakonsu.  ۖ 
Wa Laqad 'Ātaynā Mūsá Al-Kitāba Wa Qaffaynā Min Ba`dihi Bir-Rusuli  ۖ  Wa 'Ātaynā `Īsá Abna Maryama Al-Bayyināti Wa 'Ayyadnāhu Birūĥi Al-Qudusi  ۗ  'Afakullamā Jā'akum Rasūlun Bimā Lā Tahwá 'Anfusukum Astakbartum Fafarīqāan Kadhdhabtum Wa Farīqāan Taqtulūn 002-087 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Munbai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun biyar daga bãyansa da wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Ĩsã ɗan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Rũhi mai tsarki. Shinfa, kõ da yaushe wani manzo ya je muku tãre da abin da rãyukanku bã su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashẽwa?  ۖ   ۗ 
Wa Qālū Qulūbunā Ghulfun  ۚ  Bal La`anahumu Al-Lahu Bikufrihim Faqalīlāan Mā Yu'uminūna 002-088 Kuma suka ce: "Zukatanmu suna cikin rufi." A'a, Allah Yã la'ane su, dõmin kafircinsu kadan kwarai suke yin ĩmãni!  ۚ 
Wa Lammā Jā'ahum Kitābun Min `Indi Al-Lahi Muşaddiqun Limā Ma`ahum Wa Kānū Min Qablu Yastaftiĥūna `Alá Al-Ladhīna Kafarū Falammā Jā'ahum Mā `Arafū Kafarū Bihi  ۚ  Fala`natu Al-Lahi `Alá Al-Kāfirīna 002-089 Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar taimako da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la'anar Allah ta tabbata a kan kãfirai.  ۚ 
Bi'sa Mā Ashtaraw Bihi 'Anfusahum 'An Yakfurū Bimā 'Anzala Al-Lahu Baghyāan 'An Yunazzila Al-Lahu Min Fađlih `Alá Man Yashā'u Min  ۖ  `Ibādihi Fabā'ū Bighađabin `Alá  ۚ  Ghađabin Wa Lilkāfirīna `Adhābun Muhīnun 002-090 Tir, da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya saukar sabõda zãlunci; kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai azãba mai wulãƙantarwa. ~  ۖ   ۚ 
Wa 'Idhā Qīla Lahum 'Āminū Bimā 'Anzala Al-Lahu Qālū Nu'uminu Bimā 'Unzila `Alaynā Wa Yakfurūna Bimā Warā'ahu Wa Huwa Al-Ĥaqqu Muşaddiqāan Limā Ma`ahum  ۗ  Qul Falima Taqtulūna 'Anbiyā'a Al-Lahi Min Qablu 'In Kuntum Mu'uminīna 002-091 Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?"  ۗ 
Wa Laqad Jā'akum Mūsá Bil-Bayyināti Thumma Attakhadhtumu Al-`Ijla Min Ba`dihi Wa 'Antum Žālimūna 002-092 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi (daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci.
Wa 'Idh 'Akhadhnā Mīthāqakum Wa Rafa`nā Fawqakumu Aţūra Khudhū Mā 'Ātaynākum Biqūwatin Wa Asma`ū  ۖ  Qālū Sami`nā Wa `Aşaynā Wa 'Ushribū Fī Qulūbihimu Al-`Ijla Bikufrihim  ۚ  Qul Bi'samā Ya'murukum Bihi 'Īmānukum 'In Kuntum Mu'uminīna 002-093 Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, (Muka ce:) "Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji" Suka ce: "Mun ji kuma mun ƙi." Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka ce: "Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu ĩmãni!"  ۖ   ۚ  ~
Qul 'In Kānat Lakumu Ad-Dāru Al-'Ākhiratu `Inda Al-Lahi Khālişatan Min Dūni An-Nāsi Fatamannaw Al-Mawta 'In Kuntum Şādiqīna 002-094 Ka ce: "Idan Gidan Lãhira ya kasance sabõda ku, a wurin Allah keɓe bã da sauran mutãne ba, to, ku yi gũrin mutuwa, idan kun kasance mãsu gaskiya."
Wa Lan Yatamannawhu 'Abadāan Bimā Qaddamat 'Aydīhim Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Biž-Žālimīna 002-095 Kuma bã zã su yi gũrinta bahar abada sabõda abin da hannayensu, suka gabãtar. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.  ۗ 
Wa Latajidannahum 'Aĥraşa An-Nāsi `Alá Ĥayāatin Wa Mina Al-Ladhīna 'Ashrakū  ۚ  Yawaddu 'Aĥaduhum Law Yu`ammaru 'Alfa Sanatin Wa Mā Huwa Bimuzaĥziĥihi Mina Al-`Adhābi 'An Yu`ammara Wa  ۗ  Allāhu Başīrun Bimā Ya`malūna 002-096 Kuma lalle ne, zã ka sãme su mafiya kwaɗayin mutãne a kan rãyuwa, kuma sũ ne mafiya kwaɗayin rãyuwa daga waɗanda suka yi shirka. ayansu yana son dã zã a rãyar da shi shekara dubu, kuma bã ya zama mai nĩsantar da shi daga azãba dõmin an rãyar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.  ۚ   ۗ 
Qul Man Kāna `Adūwāan Lijibrīla Fa'innahu Nazzalahu `Alá Qalbika Bi'idhni Al-Lahi Muşaddiqāan Limā Bayna Yadayhi Wa Hudáan Wa Bushrá Lilmu'uminīna 002-097 Ka ce: Wanda ya kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishãra ga mũminai.
Man Kāna `Adūwāan Lillahi Wa Malā'ikatihi Wa Rusulihi Wa Jibrīla Wa Mīkāla Fa'inna Al-Laha `Adūwun Lilkāfirīna 002-098 Wanda ya kasance maƙiyi ga Allah da malã'ikunSa da manzanninSa da Jibirĩla da Mĩkã'ĩla to, lalle ne, Allah Maƙiyi ne ga kãfirai.
Wa Laqad 'Anzalnā 'Ilayka 'Āyātin Bayyinātin  ۖ  Wa Mā Yakfuru Bihā 'Illā Al-Fāsiqūna 002-099 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun saukar, zuwa gare ka, ãyõyi bayyanannu, kuma ba wanda yake kãfirta da su fãce fãsikai .  ۖ 
'Awakullamā `Āhadū `Ahdāan Nabadhahu Farīqun Minhum  ۚ  Bal 'Aktharuhum Lā Yu'uminūna 002-100 Shin, kuma a kõ da yaushe suka ƙulla wani alkawari sai wani ɓangare daga gare su ya, yi jĩfa da shi? Ã'a, mafi yawansu bã su yin ĩmãni.  ۚ 
Wa Lammā Jā'ahum Rasūlun Min `Indi Al-Lahi Muşaddiqun Limā Ma`ahum Nabadha Farīqun Mina Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Kitāba Al-Lahi Warā'a Žuhūrihim Ka'annahum Lā Ya`lamūna 002-101 Kuma a lõkacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, sai wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, suka yar da Littãfin (Alƙur'ãnin) Allah a bãyan bãyansu, kamar dai sũ ba su sani ba.
Wa Attaba`ū Mā Tatlū Ash-Shayāţīnu `Alá Mulki Sulaymāna  ۖ  Wa Mā Kafara Sulaymānu Wa Lakinna Ash-Shayāţīna Kafarū Yu`allimūna An-Nāsa As-Siĥra Wa Mā 'Unzila `Alá Al-Malakayni Bibābila Hārūta Wa Mārūta  ۚ  Wa Mā Yu`allimāni Min 'Aĥadin Ĥattá Yaqūlā 'Innamā Naĥnu Fitnatun Falā Takfur  ۖ  Fayata`allamūna Minhumā Mā Yufarriqūna Bihi Bayna Al-Mar'i Wa Zawjihi  ۚ  Wa Mā Hum Biđārrīna Bihi Min 'Aĥadin 'Illā Bi'idhni Al-Lahi  ۚ  Wa Yata`allamūna Mā Yađurruhum Wa Lā Yanfa`uhum  ۚ  Wa Laqad `Alimū Lamani Ashtarāhu Mā Lahu Fī Al-'Ākhirati Min Khalāqin  ۚ  Wa Labi'sa Mā Sharaw Bihi 'Anfusahum  ۚ  Law Kānū Ya`lamūna 002-102 Kuma suka bi abin da shaiɗãnu ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani.  ۖ   ۚ   ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ  ~  ۚ 
Wa Law 'Annahum 'Āmanū Wa Attaqaw Lamathūbatun Min `Indi Al-Lahi Khayrun  ۖ  Law Kānū Ya`lamūna 002-103 Kuma dã lalle ne sũ, sun yi ĩmani, kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa, da sakamako daga wurin Allah shi ne mafi alhẽri, dã sun kasance suna sani.  ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Taqūlū Rā`inā Wa Qūlū Anžurnā Wa Asma`ū  ۗ  Wa Lilkāfirīna `Adhābun 'Alīmun 002-104 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ce: 'Rã'inã' kuma ku ce: 'Jinkirtã manã', kuma ku saurara. Kuma kãfirai suna da azãba mai raɗaɗi.  ۗ 
Mā Yawaddu Al-Ladhīna Kafarū Min 'Ahli Al-Kitābi Wa Lā Al-Mushrikīna 'An Yunazzala `Alaykum Min Khayrin Min Rabbikum Wa  ۗ  Allāhu Yakhtaşşu Biraĥmatihi Man Yashā'u Wa  ۚ  Allāhu Dhū Al-Fađli Al-`Ažīmi 002-105 Waɗanda suka kãfirta daga Ma'abuta Littãfi, bã su son a saukar da wani alhẽri a kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai mã bã su so. Kuma Allah Yana keɓance da wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abũcin falala mai girma ne.  ۗ   ۚ 
Mā Nansakh Min 'Āyatin 'Aw Nunsihā Na'ti Bikhayrin Minhā 'Aw Mithlihā  ۗ  'Alam Ta`lam 'Anna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 002-106 Abin da Muka shãfe daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne?  ۗ 
'Alam Ta`lam 'Anna Al-Laha Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۗ  Wa Mā Lakum Min Dūni Al-Lahi Min Wa Līyin Wa Lā Naşīrin 002-107 Shin ba ka sani ba, cẽwa lalle ne Allah, Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa kuma bã ku da, baicin Allah, wani majiɓinci, kuma bã ku da wani mataimaki?  ۗ 
'Am Turīdūna 'An Tas'alū Rasūlakum Kamā Su'ila Mūsá Min Qablu  ۗ  Wa Man Yatabaddali Al-Kufra Bil-'Īmāni Faqad Đalla Sawā'a As-Sabīli 002-108 Kõ kuna nufin ku tambayi Manzonku, kamar yadda aka tambayi Mũsã a gabãnin haka? Kuma wanda ya musanya kãfirci da ĩmãni, to, lalle ne yã ɓace tsakar hanya.  ۗ 
Wadda Kathīrun Min 'Ahli Al-Kitābi Law Yaruddūnakum Min Ba`di 'Īmānikum Kuffārāan Ĥasadāan Min `Indi 'Anfusihim Min Ba`di Mā Tabayyana Lahumu Al-Ĥaqqu  ۖ  Fā`fū Wa Aşfaĥū Ĥattá Ya'tiya Al-Lahu Bi'amrihi  ۗ  'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 002-109 Mãsu yawa daga Ma'abuta Littãfi sunã gũrin dã sun mayar da ku, daga bãyan ĩmãninku, kãfirai,sabõda hãsada daga wurin rãyukansu, daga bayãn gaskiya tã bayyana a gare su. To, ku yãfe, kuma ku kau da kai, sai Allah Yã zo da umurninSa. Lalle ne Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne.  ۖ  ~  ۗ 
Wa 'Aqīmū Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata  ۚ  Wa Mā Tuqaddimū Li'nfusikum Min Khayrin Tajidūhu `Inda Al-Lahi  ۗ  'Inna Al-Laha Bimā Ta`malūna Başīrun 002-110 Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka. Kuma abin da kuka gabãtar dõmin kanku daga alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah. Lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.  ۚ   ۗ 
Wa Qālū Lan Yadkhula Al-Jannata 'Illā Man Kāna Hūdāan 'Aw Naşārá  ۗ  Tilka 'Amānīyuhum  ۗ  Qul Hātū Burhānakum 'In Kuntum Şādiqīn 002-111 Kuma suka ce: "Bãbu mai shiga Aljanna fãce waɗanda suka zama Yahũdu ko Nasãra." Waɗancan tãtsũniyõyinsu ne. Ka ce: "Ku kãwo dalilinku idan kun kasance mãsu gaskiya."  ۗ   ۗ 
Balá Man 'Aslama Wajhahu Lillahi Wa Huwa Muĥsinun Falahu 'Ajruhu `Inda Rabbihi Wa Lā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 002-112 Na'am! Wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yana mai kyautatãwa, to, yana da ijãrarsa, a wurin Ubangijinsa, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba. ~
Wa Qālati Al-Yahūdu Laysati An-Naşārá `Alá Shay'in Wa Qālati An-Naşārá Laysati Al-Yahūdu `Alá Shay'in Wa Hum Yatlūna Al-Kitāba  ۗ  Kadhālika Qāla Al-Ladhīna Lā Ya`lamūna Mithla Qawlihim  ۚ  Fa-Allāhu Yaĥkumu Baynahum Yawma Al-Qiyāmati Fīmā Kānū Fīhi Yakhtalifūna 002-113 Kuma Yahũdãwa suka ce: "Nasãra ba su zamana a kan kõme ba," kuma Nasãra suka ce: "Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba," alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.  ۗ   ۚ 
Wa Man 'Ažlamu Mimman Mana`a Masājida Al-Lahi 'An Yudhkara Fīhā Asmuhu Wa Sa`á Fī Kharābihā  ۚ  'Ūlā'ika Mā Kāna Lahum 'An Yadkhulūhā 'Ilā Khā'ifīna  ۚ  Lahum Ad-DunKhizyun Wa Lahum Al-'Ākhirati `Adhābun `Ažīmun 002-114 Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya hana masallãtan Allah, dõmin kada a ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan bã ya kasancẽwa a gare su su shigẽ su fãce suna mãsu tsõro. Suna da, a cikin duniya wani wulãkanci, kuma suna da, a cikin Lãhira, azãba mai girma.  ۚ   ۚ 
Wa Lillahi Al-Mashriqu Wa Al-Maghribu  ۚ  Fa'aynamā Tuwallū Fathamma Wajhu Al-Lahi 'Inna  ۚ  Al-Laha Wāsi`un `Alīmun 002-115 Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma sabõda haka, inda duk aka jũyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadãci ne, Mai ilmi.  ۚ   ۚ 
Wa Qālū Attakhadha Al-Lahu Waladāan  ۗ  Subĥānahu  ۖ  Bal Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Kullun Lahu Qānitūna 002-116 Kuma suka ce: "Allah Yã riƙi ɗã." Tsarki yã tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, mãsu ƙanƙan da kai ne.  ۗ   ۖ   ۖ 
Badī`u As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Wa 'Idhā Qađá 'Amrāan Fa'innamā Yaqūlu Lahu Kun Fayakūnu 002-117 Mai kyautata halittar sammai da ƙasa, kuma idan Ya hukunta wani al'amari, sai kawai Ya ce masa: "Kasance." Sai ya yi ta kasancewa.  ۖ 
Wa Qāla Al-Ladhīna Lā Ya`lamūna Lawlā Yukallimunā Al-Lahu 'Aw Ta'tīnā 'Āyatun  ۗ  Kadhālika Qāla Al-Ladhīna Min Qablihim Mithla Qawlihim  ۘ  Tashābahat Qulūbuhum  ۗ  Qad Bayyannā Al-'Āyāti Liqawmin Yūqinūna 002-118 Kuma waɗanda bã su da sani suka ce: "Don me Allah bã Ya yi mana magana, ko wata ãyã ta zo mana?" Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka faɗa, kamar maganarsu. zukãtansu sun yi kamã da jũna. Lalle ne, Mun bayyana ãyõyi ga mutãne masu sakankancewa.  ۗ   ۘ   ۗ 
'Innā 'Arsalnāka Bil-Ĥaqqi Bashīrāan Wa Nadhīrāan  ۖ  Wa Lā Tus'alu `An 'Aşĥābi Al-Jaĥīmi 002-119 Lalle ne Mun aike ka da gaskiya, kana mai bãyar da bishãra, kuma mai gargaɗi, kuma bã zã a tambaye ka ba, game da abõkan Wuta.  ۖ 
Wa Lan Tarđá `Anka Al-Yahūdu Wa Lā An-Naşārá Ĥattá Tattabi`a Millatahum  ۗ  Qul 'Inna Hudá Al-Lahi Huwa Al-Hudá  ۗ  Wa La'ini Attaba`ta 'Ahwā'ahum Ba`da Al-Ladhī Jā'aka Mina Al-`Ilmi  ۙ  Mā Laka Mina Al-Lahi Min Wa Līyin Wa Lā Naşīrin 002-120 Kuma Yahũdu bã zã su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasãra bã zã su yarda ba, sai kã bi irin aƙidarsu. Ka ce: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya." Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bã ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma bãbu wani mataimaki.  ۗ   ۗ   ۙ 
Al-Ladhīna 'Ātaynāhumu Al-Kitāba Yatlūnahu Ĥaqqa Tilāwatihi 'Ūlā'ika Yu'uminūna Bihi  ۗ  Wa Man Yakfur Bihi Fa'ūlā'ika Humu Al-Khāsirūna 002-121 Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karãtunsa a kan haƙƙin karãtunsa, waɗannan suna ĩmani da shi (Alƙur'ãni). Kuma wanda ya kãfirta da shi, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra. ~  ۗ 
Yā Banī 'Isrā'īla Adhkurū Ni`matiya Allatī 'An`amtu `Alaykum Wa 'Annī Fađđaltukum `Alá Al-`Ālamīna 002-122 Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Nĩ, Nã fĩfĩtã ku a kan tãlikai.
Wa Attaqū Yawmāan Lā Tajzī Nafsun `An Nafsin Shay'āan Wa Lā Yuqbalu Minhā `Adlun Wa Lā Tanfa`uhā Shafā`atun Wa Lā Hum Yunşarūna 002-123 Ku ji tsõron wani yini, (a cikinsa) wani rai bã ya tunkuɗe wa wani rai kõme kuma bã a karɓar fansa daga gare shi, kuma wani cẽto bã ya amfanin sa, kuma ba su zama ana taimakon su ba.
Wa 'Idh Abtalá 'Ibrāhīma Rabbuhu Bikalimātin Fa'atammahunna  ۖ  Qāla 'Innī Jā`iluka Lilnnāsi 'Imāmāan  ۖ  Qāla Wa Min Dhurrīyatī  ۖ  Qāla Lā Yanālu `Ahdī Až-Žālimīna 002-124 Kuma a lõkacin da Ubangijin Ibrãhim Ya jarrabẽ shi da wasu kalmõmi, sai ya cika su. Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Mai sanya ka shugaba dõmin mutãne ne." Ya ce: "Kuma daga zũriyata." Ya ce: "AlkawarĩNa bã zai sãmu azzãlumai ba."  ۖ   ۖ   ۖ 
Wa 'Idh Ja`alnā Al-Bayta Mathābatan Lilnnāsi Wa 'Amnāan Wa Attakhidhū Min Maqāmi 'Ibrāhīma Muşalláan  ۖ  Wa `Ahidnā 'Ilá 'Ibrāhīma Wa 'Ismā`īla 'An Ţahhirā Baytiya Lilţţā'ifīna Wa Al-`Ākifīna Wa Ar-Rukka`i As-Sujūdi 002-125 Kuma a lõkacin da Muka sanya ãkin ya zama makõma ga mutãne, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙãmi Ibrãhĩm, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrãhĩm, da Ismã'ila da cẽwa: "Ku tsarkake ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu lizimta da mãsu rukũ'i, mãsu sujada."  ۖ 
Wa 'Idh Qāla 'Ibrāhīmu Rabbi Aj`al Hādhā Baladāan 'Āmināan Wa Arzuq 'Ahlahu Mina Ath-Thamarāti Man 'Āmana Minhum Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri  ۖ  Qāla Wa Man Kafara Fa'umatti`uhu Qalīlāan Thumma 'Ađţarruhu 'Ilá `Adhābi An-Nāri  ۖ  Wa Bi'sa Al-Maşīru 002-126 Kuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira." Allah Ya ce: "Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana."  ۖ  ~  ۖ 
Wa 'Idh Yarfa`u 'Ibrāhīmu Al-Qawā`ida Mina Al-Bayti Wa 'Ismā`īlu Rabbanā Taqabbal Minnā  ۖ  'Innaka 'Anta As-Samī`u Al-`Alīmu 002-127 Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm yake ɗaukaka harsãshin gini ga ãkin, da Ismã'ĩla (suna cẽwa:) "Yã Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani.  ۖ 
Rabbanā Wa Aj`alnā Muslimayni Laka Wa Min Dhurrīyatinā 'Ummatan Muslimatan Laka Wa 'Arinā Manāsikanā Wa Tub `Alaynā  ۖ  'Innaka 'Anta At-Tawwābu Ar-Raĥīmu 002-128 "Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al'amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al'umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama.  ۖ 
Rabbanā Wa Ab`ath Fīhim Rasūlāan Minhum Yatlū `Alayhim 'Āyātika Wa Yu`allimuhumu Al-Kitāba Wa Al-Ĥikmata Wa Yuzakkīhim  ۚ  'Innaka 'Anta Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu 002-129 "Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo daga gare su, yana karanta musu ãyõyinKa, kuma yana karantar da su Littãfin da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi Mai hikima."  ۚ 
Wa Man Yarghabu `An Millati 'Ibrāhīma 'Illā Man Safiha Nafsahu  ۚ  Wa Laqadi Aşţafaynāhu Fī Ad-Dunyā  ۖ  Wa 'Innahu Fī Al-'Ākhirati Lamina Aş-Şāliĥīna 002-130 Kuma wãne ne yake gudu daga aƙĩdar Ibrãhĩm, fãce wanda ya jãhilta ga ransa? Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe shi, a cikin dũniya, kuma lalle ne shi, a cikin Lãhira, haƙĩƙa, yana daga sãlihai.  ۚ   ۖ 
'Idh Qāla Lahu Rabbuhu 'Aslim  ۖ  Qāla 'Aslamtu Lirabbi Al-`Ālamīna 002-131 A lõkacin da Ubangijinsa Ya ce masa: "Ka miƙa wuya," ya ce: "Nã miƙa wuya ga Ubangijin tãlikai." ~  ۖ 
Wa Waşşá Bihā 'Ibrāhīmu Banīhi Wa Ya`qūbu Yā Banīya 'Inna Al-Laha Aşţafá Lakumu Ad-Dīna Falā Tamūtunna 'Illā Wa 'Antum Muslimūna 002-132 Kuma lbrãhĩm ya yi wasiyya da ita ga ɗiyansa, kuma Ya'aƙũbu (ya yi wasiyya,suka ce:) "Yã ɗiyãna! Lalle ne, Allah Ya zãɓã muku addini don haka kada ku mutu, lalle, fãce kuna Musulmi."
'Am Kuntum Shuhadā'a 'Idh Ĥađara Ya`qūba Al-Mawtu 'Idh Qāla Libanīhi Mā Ta`budūna Min Ba`dī Qālū Na`budu 'Ilahaka Wa 'Ilaha 'Ābā'ika 'Ibrāhīma Wa 'Ismā`īla Wa 'Isĥāqa 'Ilahāan Wāĥidāan Wa Naĥnu Lahu Muslimūna 002-133 Ko kun kasance halarce a lõkacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙũbu, a lõkacin da ya ce wa ɗiyansa: "Mẽne ne zã ku bauta wa daga bãyãna?" Suka ce: "Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrãhĩm da lsmã'ĩla da Is'hãƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi mãsu miƙa wuya ne."
Tilka 'Ummatun Qad Khalat  ۖ  Lahā Mā Kasabat Wa Lakum Mā Kasabtum  ۖ  Wa Lā Tus'alūna `Ammā Kānū Ya`malūna 002-134 Waccan, wata al'umma ce, ta riga ta shige, tana da abin da ta sanã'anta kuma kuna da abin da kuka sanã'anta, Kuma bã zã a tambaye ku ba daga abin da suka kasance suna aikatãwa.  ۖ   ۖ 
Wa Qālū Kūnū Hūdāan 'Aw Naşārá Tahtadū  ۗ  Qul Bal Millata 'Ibrāhīma Ĥanīfāan  ۖ  Wa Mā Kāna Mina Al-Mushrikīna 002-135 Kuma suka ce: "Ku kasance Yahũdãwa ko Nasãra, kwã shiryu."Ka ce: "A'a aƙidar Ibrãhĩm dai, maikarkata, zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."  ۗ   ۖ 
Qūlū 'Āmannā Bil-Lahi Wa Mā 'Unzila 'Ilaynā Wa Mā 'Unzila 'Ilá 'Ibrāhīma Wa 'Ismā`īla Wa 'Isĥāqa Wa Ya`qūba Wa Al-'Asbāţi Wa Mā 'Ūtiya Mūsá Wa `Īsá Wa Mā 'Ūtiya An-Nabīyūna Min Rabbihim Lā Nufarriqu Bayna 'Aĥadin Minhum Wa Naĥnu Lahu Muslimūna 002-136 Ku ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne."
Fa'in 'Āmanū Bimithli Mā 'Āmantum Bihi Faqadi Ahtadaw  ۖ  Wa 'In Tawallaw Fa'innamā HumShiqāqin  ۖ  Fasayakfīkahumu Al-Lahu  ۚ  Wa Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu 002-137 To, idan sun yi ĩmãni da misãlin abin da kuka yi ĩmãni da shi, to, lalle ne sun shiryu, kuma idan sun jũya bãya, to, suna a cikin sãɓãni kawai sabõda haka Allah zai isar maka a gare su, kuma Shi ne Mai ji, Masani.  ۖ   ۖ   ۚ 
Şibghata Al-Lahi  ۖ  Wa Man 'Aĥsanu Mina Al-Lahi Şibghatan  ۖ  Wa Naĥnu Lahu `Ābidūna 002-138 Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, mãsu bautãwa ne.  ۖ   ۖ 
Qul 'Atuĥājjūnanā Fī Al-Lahi Wa Huwa Rabbunā Wa Rabbukum Wa Lanā 'A`mālunā Wa Lakum 'A`mālukum Wa Naĥnu Lahu Mukhlişūna 002-139 Ka ce: Shin kuna jãyayyar hujia ne da mu a cikin al'amarin Allah, alhãli kuwa Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku, kuma muna da ayyukanmu, kuma kuna da ayyukanku, kuma mũ, a gare Shi, mãsu tsarkakẽwane?
'Am Taqūlūna 'Inna 'Ibrāhīma Wa 'Ismā`īla Wa 'Isĥāqa Wa Ya`qūba Wa Al-'Asbāţa Kānū Hūdāan 'Aw Naşārá  ۗ  Qul 'A'antum 'A`lamu 'Ami Al-Lahu  ۗ  Wa Man 'Ažlamu Mimman Katama Shahādatan `Indahu Mina Al-Lahi  ۗ  Wa Mā Al-Lahu Bighāfilin `Ammā Ta`malūna 002-140 Ko kuna cẽwa: Lalle ne, Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Ya'aƙũbu da Jĩkõki, sun kasance Yahũdãwa kõ kuwa Nasãra? Ka ce: Shin kũ ne kuke mafi sani kõAllah? Kuma wãne ne ya zama mafi zãlunci daga wanda ya bõye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa!  ۗ   ۗ   ۗ 
Tilka 'Ummatun Qad Khalat  ۖ  Lahā Mā Kasabat Wa Lakum Mā Kasabtum  ۖ  Wa Lā Tus'alūna `Ammā Kānū Ya`malūna 002-141 Waccan, wata al'umma ce, tã riga ta shige, suna da abin da suka sana'anta kuma kuna da abin da kuka sana'anta kuma bã a tambayar ku daga abin da suka kasance suna aikatãwa.  ۖ   ۖ 
Sayaqūlu As-Sufahā'u Mina An-Nāsi Mā Wa Llāhum `An Qiblatihimu Allatī Kānū `Alayhā  ۚ  Qul Lillahi Al-Mashriqu Wa Al-Maghribu  ۚ  Yahdī Man Yashā'u 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin 002-142 Wãwãye daga mutãne zã su ce: Mẽne ne ya jũyar da su daga alƙiblarsu wadda suka kasance a kanta? Ka ce: "Allah ai ne Yake da gabas da yamma, Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya."  ۚ   ۚ 
Wa Kadhalika Ja`alnākum 'Ummatan Wasaţāan Litakūnū Shuhadā'a `Alá An-Nāsi Wa Yakūna Ar-Rasūlu `Alaykum Shahīdāan  ۗ  Wa Mā Ja`alnā Al-Qiblata Allatī Kunta `Alayhā 'Illā Lina`lama Man Yattabi`u Ar-Rasūla Mimman Yanqalibu `Alá `Aqibayhi  ۚ  Wa 'In Kānat Lakabīratan 'Illā `Alá Al-Ladhīna Hadá Al-Lahu  ۗ  Wa Mā Kāna Al-Lahu Liyuđī`a 'Īmānakum  ۚ  'Inna Al-Laha Bin-Nāsi Lara'ūfun Raĥīmun 002-143 Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla wadda ka kasance a kanta ba, fãce dõmin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake jũyãwa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, tã kasance haƙĩƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tõzartar da ĩmãninku. Lalle ne, Allah, ga mutãne, haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.  ۗ   ۚ   ۗ   ۚ 
Qad Nará Taqalluba Wajhika Fī As-Samā'i Falanuwalliyannaka  ۖ  Qiblatan Tarđāhā Fawalli Wajhaka  ۚ  Shaţra Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Wa Ĥaythu Mā  ۚ  Kuntum Fawallū Wujūhakum Shaţrahu Wa 'Inna Al-Ladhīna  ۗ  'Ū Al-Kitāba Laya`lamūna 'Annahu Al-Ĥaqqu Min Rabbihim Wa Mā Al-Lahu  ۗ  Bighāfilin `Ammā Ya`malūna 002-144 Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littãfi, haƙĩƙa su, sunã sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatãwa.  ۖ   ۚ   ۚ   ۗ   ۗ 
Wa La'in 'Atayta Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Bikulli 'Āyatin Mā Tabi`ū Qiblataka  ۚ  Wa Mā 'Anta Bitābi`in Qiblatahum  ۚ  Wa Mā Ba`đuhum Bitābi`in Qiblata Ba`đin  ۚ  Wa La'ini Attaba`ta 'Ahwā'ahum Min Ba`di Mā Jā'aka Mina Al-`Ilmi  ۙ  'Innaka 'Idhāan Lamina Až-Žālimīna 002-145 Kuma hakĩka, idan ka je wawaɗanda aka bai wa Littafi da dukan ãyã, bã zã su bi Alƙiblarka ba, kuma kai ba ka zama mai bin Alƙiblarsu ba, kuma sãshensu bã mai bin Alƙiblar sãshe ba ne. Kuma haƙĩƙa, idan ka bi son zũciyõyinsu daga bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, lalle ne kai, sa'an nan, haƙiƙa, azzãlumi kake.  ۚ   ۚ   ۚ   ۙ 
Al-Ladhīna 'Ātaynāhumu Al-Kitāba Ya`rifūnahu Kamā Ya`rifūna 'Abnā'ahum  ۖ  Wa 'Inna Farīqāan Minhum Layaktumūna Al-Ĥaqqa Wa Hum Ya`lamūna 002-146 Waɗanda Muka bã su Littãfi, suna saninsa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Kuma lalle ne wani ɓangare daga gare su, haƙiƙa, suna ɓõyewar gaskiya alhãli kuwa sũ, suna sane.  ۖ 
Al-Ĥaqqu Min Rabbika  ۖ  Falā Takūnanna Mina Al-Mumtarīna 002-147 Gaskiya daga Ubangijinka take sabõda haka, lalle kada ka kasance daga mãsu shakka.  ۖ 
Wa Likullin Wijhatun Huwa Muwallīhā  ۖ  Fāstabiqū Al-Khayrāti  ۚ  'Ayna Mā Takūnū Ya'ti Bikumu Al-Lahu Jamī`āan  ۚ  'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 002-148 Kuma kõwane ɓangare yana da alƙibla wadda yake shi mai fuskantar ta ne. Sai ku yi tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri, inda kuka kasance duka Allah zai zo da ku gabã ɗaya. Lalle ne Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne.  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa Min Ĥaythu Kharajta Fawalli Wajhaka Shaţra Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Wa 'Innahu  ۖ  Lalĥaqqu Min Rabbika Wa Mā  ۗ  Al-Lahu Bighāfilin `Ammā Ta`malūna 002-149 Kuma daga inda ka fita, to, sai ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma lalle tabbas, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa ba.  ۖ   ۗ 
Wa Min Ĥaythu Kharajta Fawalli Wajhaka Shaţra Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Wa Ĥaythu  ۚ  Mā Kuntum Fawallū Wujūhakum Shaţrahu Li'allā Yakūna Lilnnāsi `Alaykum Ĥujjatun 'Illā Al-Ladhīna Žalamū Minhum Falā Takhshawhum Wa Akhshawnī Wa Li'atimma Ni`matī `Alaykum Wa La`allakum Tahtadūna 002-150 Kuma daga inda ka fita, to, ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku jũyar da fuskõkinku a wajensa, dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kanku, fãce waɗanda suka yi zãlunci daga gare su. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõrõNa kuma dõmin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammãninku zã ku shiryu.  ۚ 
Kamā 'Arsalnā Fīkum Rasūlāan Minkum Yatlū `Alaykum 'Āyātinā Wa Yuzakkīkum Wa Yu`allimukumu Al-Kitāba Wa Al-Ĥikmata Wa Yu`allimukum Mā Lam Takūnū Ta`lamūna 002-151 Kamar yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ãyõyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littãfi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba.
dhkurūnī 'Adhkurkum Wa Ashkurū Lī Wa Lā Takfurūni 002-152 Sabõda haka, ku tuna Ni, In tunã ku, kuma ku yi gõdiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Asta`īnū Biş-Şabri Wa Aş-Şalāati  ۚ  'Inna Al-Laha Ma`a Aş-Şābirīna 002-153 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nẽmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri.  ۚ 
Wa Lā Taqūlū Liman Yuqtalu Fī Sabīli Al-Lahi 'Amwātun  ۚ  Bal 'Aĥyā'un Wa Lakin Lā Tash`urūna 002-154 Kada ku ce ga waɗanda ake kashẽwa a cikin hanyar Allah: "Matattu ne." Ã'a, rãyayyu ne, kuma amma bã ku sansancẽwa.  ۚ 
Wa Lanabluwannakum Bishay'in Mina Al-Khawfi Wa Al-Jū`i Wa Naqşin Mina Al-'Amwli Wa Al-'Anfusi Wa Ath-Thamarāti  ۗ  Wa Bashshiri Aş-Şābirīna 002-155 Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri.  ۗ 
Al-Ladhīna 'Idhā 'Aşābat/hum Muşībatun Qālū 'Innā Lillahi Wa 'Innā 'Ilayhi Rāji`ūna 002-156 Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa."
'Ūlā'ika `Alayhim Şalawātun Min Rabbihim Wa Raĥmatun  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Muhtadūna 002-157 Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu.  ۖ 
'Inna Aş-Şafā Wa Al-Marwata Min Sha`ā'iri Al-Lahi  ۖ  Faman Ĥajja Al-Bayta 'Aw A`tamara Falā Junāĥa `Alayhi 'An Yaţţawwafa Bihimā  ۚ  Wa Man Taţawwa`a Khayrāan Fa'inna Al-Laha Shākirun `Alīmun 002-158 Lalle ne Safã da Marwa suna daga wurãren ibãdar Allah, to, wanda ya yi hajin ãki kõ kuwa ya yi Umra, to, bãbu laifi a kansa ga ya yi ɗawãfi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙãra yin wani aikin alhẽri to, lalle ne Allah Mai gõdiya ne, Masani.  ۖ   ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Yaktumūna Mā 'Anzalnā Mina Al-Bayyināti Wa Al-Hudá Min Ba`di Mā Bayyannāhu Lilnnāsi Fī Al-Kitābi  ۙ  'Ūlā'ika Yal`anuhumu Al-Lahu Wa Yal`anuhumu Al-Lā`inūna 002-159 Lalle ne waɗanda suke ɓõyẽwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur'ãni), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma mãsu la'ana suna la'anar su.  ۙ 
'Illā Al-Ladhīna Tābū Wa 'Aşlaĥū Wa Bayyanū Fa'ūlā'ika 'Atūbu `Alayhim  ۚ  Wa 'Anā At-Tawwābu Ar-Raĥīmu 002-160 Sai waɗanda suka tũba,kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Wa Mātū Wa Hum Kuffārun 'Ūlā'ika `Alayhim La`natu Al-Lahi Wa Al-Malā'ikati Wa An-Nāsi 'Ajma`īna 002-161 Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai, waɗannan akwai, a kansu, la'anar Allah da Malã'iku da mutãne gabã ɗaya.
Khālidīna Fīhā  ۖ  Lā Yukhaffafu `Anhumu Al-`Adhābu Wa Lā Hum Yunžarūna 002-162 Suna madawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãba daga barinsu, kuma ba su zama ana jinkirta musu ba.  ۖ 
Wa 'Ilahukum 'Ilahun Wāĥidun  ۖ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Ar-Raĥmānu Ar-Raĥīmu 002-163 Kuma Ubangijinku Ubangiji Guda ne. Bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai.  ۖ  ~
'Inna Fī Khalqi As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Akhtilāfi Al-Layli Wa An-Nahāri Wa Al-Fulki Allatī Tajrī Fī Al-Baĥri Bimā Yanfa`u An-Nāsa Wa Mā 'Anzala Al-Lahu Mina As-Samā'i Min Mā'in Fa'aĥyā Bihi Al-'Arđa Ba`da Mawtihā Wa Baththa Fīhā Min Kulli Dābbatin Wa Taşrīfi Ar-Riyāĥi Wa As-Saĥābi Al-Musakhkhari Bayna As-Samā'i Wa Al-'Arđi La'āyātin Liqawmin Ya`qilūna 002-164 Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da sãɓãwar dare da yini, da jirãge wadaɗnda suke gudana a cikin tẽku (ɗauke) da abin da yake amfãnin mutãne, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta, kuma Ya wãtsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da jũyãwar iskõki da girgije hõrarre a tsakãnin sama da ƙasa; haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
Wa Mina An-Nāsi Man Yattakhidhu Min Dūni Al-Lahi 'Andādāan Yuĥibbūnahum Kaĥubbi Al-Lahi Wa  ۖ  Al-Ladhīna 'Āmanū 'Ashaddu Ĥubbāan Lillahi  ۗ  Wa Law Yará Al-Ladhīna Žalamū 'Idh Yarawna Al-`Adhāba 'Anna Al-Qūwata Lillahi Jamī`āan Wa 'Anna Al-Laha Shadīdu Al-`Adhābi 002-165 Kuma akwai daga mutãne wanda yake riƙon kinãye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi ĩmãni ne mafiya tsananin so ga Allah. Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci, suna ganin lõkacin da zã su ga azãba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cẽwa lalle neAllah Mai tsananin azãba ne.  ۖ   ۗ 
'Idh Tabarra'a Al-Ladhīna Attubi`ū Mina Al-Ladhīna Attaba`ū Wa Ra'aw Al-`Adhāba Wa Taqaţţa`at Bihimu Al-'Asbābu 002-166 A lõkacin da waɗanda aka bi suka barranta daga waɗanda suka bi, kuma suka ga azãba, kuma sabubba suka yanke da su.
Wa Qāla Al-Ladhīna Attaba`ū Law 'Anna Lanā Karratan Fanatabarra'a Minhum Kamā Tabarra'ū Minnā  ۗ  Kadhālika Yurīhimu Al-Lahu 'A`mālahum Ĥasarātin `Alayhim  ۖ  Wa Mā Hum Bikhārijīna Mina An-Nāri 002-167 Kuma waɗanda suka bi, suka ce: "Dã lalle ne muna da wata kõmãwa (dũniya) sai mu barranta dagagare su kamar yadda suka barranta daga gare mu (dã ba su riƙi kinãyen ba)." Kamar wancan ne Allah ke nũna musu ayyukansu, suna da nadãmõmi a kansu, kuma ba su zama mãsu fita daga wutar ba.  ۗ   ۖ 
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Kulū Mimmā Fī Al-'Arđi Ĥalālāan Ţayyibāan Wa Lā Tattabi`ū Khuţuwāti Ash-Shayţāni  ۚ  'Innahu Lakum `Adūwun Mubīn 002-168 Yã ku mutãne! Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai dãɗi. Kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne.  ۚ 
'Innamā Ya'murukum Bis-Sū'i Wa Al-Faĥshā'i Wa 'An Taqūlū `Alá Al-Lahi Mā Lā Ta`lamūna 002-169 Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfãsha, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba ga Allah.
Wa 'Idhā Qīla Lahum Attabi`ū Mā 'Anzala Al-Lahu Qālū Bal Nattabi`u Mā 'Alfaynā `Alayhi 'Ābā'anā  ۗ  'Awalaw Kāna 'Ābā'uuhum Lā Ya`qilūna Shay'āan Wa Lā Yahtadūna 002-170 Kuma idan aka ce musu: "Ku bi abin da Allah Ya saukar," sai su ce: Ã'a, muna bin abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kõ dã ubanninsu bã su hankaltar kõme, kuma bã su shiryuwa?  ۗ 
Wa Mathalu Al-Ladhīna Kafarū Kamathali Al-Ladhī Yan`iqu Bimā Lā Yasma`u 'Illā Du`ā'an Wa Nidā'an  ۚ  Şummun Bukmun `Umyun Fahum Lā Ya`qilūna 002-171 Kuma misãlin (mai kiran) waɗanda suka kãfirta kamar misãlin wanda ke yin me! me! ga abin da ba ya ji ne, fãce kira da ƙãra, kurãme, bẽbãye, makafi, sabõda haka bã su hankalta.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Kulū Min Ţayyibāti Mā Razaqnākum Wa Ashkurū Lillahi 'In Kuntum 'Īyāhu Ta`budūna 002-172 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ci ku sha daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku. Kuma ku gõde wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa.
'Innamā Ĥarrama `Alaykumu Al-Maytata Wa Ad-Dama Wa Laĥma Al-Khinzīri Wa Mā 'Uhilla Bihi Lighayri Al-Lahi  ۖ  Famani Ađţurra Ghayra Bāghin Wa Lā `Ādin Falā 'Ithma `Alayhi  ۚ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 002-173 Kawai abin da Ya haramta a kanku, mũshe da Jini da nãman alade da abin da aka kurũrũta game da shi ga wanin Allah. To, wanda aka matsã, wanin ɗan tãwãye, kuma banda mai zãlunci, to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۖ   ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Yaktumūna Mā 'Anzala Al-Lahu Mina Al-Kitābi Wa Yashtarūna Bihi Thamanāan Qalīlāan  ۙ  'Ūlā'ika Mā Ya'kulūna Fī Buţūnihim 'Illā An-Nāra Wa Lā Yukallimuhumu Al-Lahu Yawma Al-Qiyāmati Wa Lā Yuzakkīhim Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun 002-174 Lalle ne waɗannan da suke ɓõye abin da Allah Ya saukar daga Littãfi, kuma suna sayen kuɗi kaɗan da shi; waɗannan bã su cin kome a cikin cikkunansu fãce wuta, kuma Allah bã zai yi musu magana ba a Rãnar ¡iyãma, kuma bã zai tsarkake su ba, kuma suna da azãba mai raɗaɗi.  ۙ 
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Ashtaraw Ađ-Đalālata Bil-Hudá Wa Al-`Adhāba Bil-Maghfirati  ۚ  Famā 'Aşbarahum `Alá An-Nāri 002-175 Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, kuma azãba da gãfara. To, me ya yi haƙurinsu a kan Wuta!  ۚ 
Dhālika Bi'anna Al-Laha Nazzala Al-Kitāba Bil-Ĥaqqi  ۗ  Wa 'Inna Al-Ladhīna Akhtalafū Fī Al-Kitābi Lafī Shiqāqin Ba`īdin 002-176 Wancan dõmin lalle ne Allah Ya saukar da Littafi da gaskiya, kuma lalle ne waɗanda suka sãɓã a cikin Littãfin, haƙĩƙa, suna a cikin sãɓãni mai nĩsa.  ۗ 
Laysa Al-Birra 'An Tuwallū Wujūhakum Qibala Al-Mashriqi Wa Al-Maghribi Wa Lakinna Al-Birra Man 'Āmana Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa Al-Malā'ikati Wa Al-Kitābi Wa An-Nabīyīna Wa 'Ā Al-Māla `Alá Ĥubbihi Dhawī Al-Qurbá Wa Al-Yatāmá Wa Al-Masākīna Wa Abna As-Sabīli Wa As-Sā'ilīna Wa Fī Ar-Riqābi Wa 'Aqāma Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata Wa Al-Mūfūna Bi`ahdihim 'Idhā `Āhadū Wa  ۖ  Aş-Şābirīna Fī Al-Ba'sā'i Wa Ađ-Đarrā'i Wa Ĥīna Al-Ba'si  ۗ  'Ūlā'ika Al-Ladhīna Şadaqū  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Muttaqūna 002-177 Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa.  ۖ   ۗ   ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Kutiba `Alaykumu Al-Qişāşu Fī Al-Qatlá  ۖ  Al-Ĥurru Bil-Ĥurri Wa Al-`Abdu Bil-`Abdi Wa Al-'Unthá Bil-'Unthá  ۚ  Faman `Ufiya Lahu Min 'Akhīhi Shay'un Fa Attibā`un Bil-Ma`rūfi Wa 'Adā'un 'Ilayhi Bi'iĥsānin  ۗ  Dhālika Takhfīfun Min Rabbikum Wa Raĥmatun  ۗ  Famani A`tadá Ba`da Dhālika Falahu `Adhābun 'Alīmun 002-178 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin ƙisãsi a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare, shi da kyautatãwa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, to, yana da azãba mai raɗaɗi.  ۖ   ۚ   ۗ   ۗ 
Wa Lakum Al-Qişāşi Ĥayāatun Yā 'Ū Al-'Albābi La`allakum Tattaqūna 002-179 Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa.
Kutiba `Alaykum 'Idhā Ĥađara 'Aĥadakumu Al-Mawtu 'In Taraka Khayrāan Al-Waşīyatu Lilwālidayni Wa Al-'Aqrabīna Bil-Ma`rūfi  ۖ  Ĥaqqāan `Alá Al-Muttaqīna 002-180 Kuma an wajabta, a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa.  ۖ 
Faman Baddalahu Ba`damā Sami`ahu Fa'innamā 'Ithmuhu `Alá Al-Ladhīna Yubaddilūnahu  ۚ  'Inna Al-Laha Samī`un `Alīmun 002-181 To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani. ~  ۚ 
Faman Khāfa Min Mūşin Janafāan 'Aw 'Ithmāan Fa'aşlaĥa Baynahum Falā 'Ithma `Alayhi  ۚ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 002-182 To, wanda ya ji tsõron karkata ko kuwa wani zunubi daga mai wasiyyar, sai ya yi sulhi a tsakãninsu to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah, Mai gãfara ne,Mai jin ƙai.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Kutiba `Alaykumu Aş-Şiyāmu Kamā Kutiba `Alá Al-Ladhīna Min Qablikum La`allakum Tattaqūna 002-183 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa,
'Ayyāmāan Ma`dūdātin  ۚ  Faman Kāna Minkum Marīđāan 'Aw `Alá Safarin Fa`iddatun Min 'Ayyāmin 'Ukhara  ۚ  Wa `Alá Al-Ladhīna Yuţīqūnahu Fidyatun Ţa`āmu Miskīnin  ۖ  Faman Taţawwa`a Khayrāan Fahuwa Khayrun Lahu  ۚ  Wa 'An Taşūmū Khayrun Lakum  ۖ  'In Kuntum Ta`lamūna 002-184 Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani.  ۚ   ۚ   ۖ   ۚ   ۖ 
Shahru Ramađāna Al-Ladhī 'Unzila Fīhi Al-Qur'ānu Hudáan Lilnnāsi Wa Bayyinātin Mina Al-Hudá Wa Al-Furqāni  ۚ  Faman Shahida Minkumu Ash-Shahra Falyaşumhu  ۖ  Wa Man Kāna Marīđāan 'Aw `Alá Safarin Fa`iddatun Min 'Ayyāmin 'Ukhara  ۗ  Yurīdu Al-Lahu Bikumu Al-Yusra Wa Lā Yurīdu Bikumu Al-`Usra Wa Litukmilū Al-`Iddata Wa Litukabbirū Al-Laha `Alá Mā Hadākum Wa La`allakum Tashkurūna 002-185 Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde.  ۚ   ۖ   ۗ 
Wa 'Idhā Sa'alaka `Ibādī `Annī Fa'innī Qarībun  ۖ  'Ujību Da`wata Ad-Dā`i 'Idhā Da`āni  ۖ  Falyastajībū Lī Wa Līu'uminū Bī La`allahum Yarshudūna 002-186 Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.  ۖ   ۖ 
'Uĥilla Lakum Laylata Aş-Şiyāmi Ar-Rafathu 'Ilá Nisā'ikum  ۚ  Hunna Libāsun Lakum Wa 'Antum Libāsun Lahunna  ۗ  `Alima Al-Lahu 'Annakum Kuntum Takhtānūna 'Anfusakum Fatāba `Alaykum Wa `Afā `Ankum  ۖ  Fāl'āna Bāshirūhunna Wa Abtaghū Mā Kataba Al-Lahu Lakum  ۚ  Wa Kulū Wa Ashrabū Ĥattá Yatabayyana Lakumu Al-Khayţu Al-'Abyađu Mina Al-Khayţi Al-'Aswadi Mina Al-Fajri  ۖ  Thumma 'Atimmū Aş-Şiyāma 'Ilá Al-Layli  ۚ  Wa Lā Tubāshirūhunna Wa 'Antum `Ākifūna Fī Al-Masājidi  ۗ  Tilka Ĥudūdu Al-Lahi Falā Taqrabūhā  ۗ  Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu 'Āyātihi Lilnnāsi La`allahum Yattaqūna 002-187 An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi taƙawa.  ۚ   ۗ   ۖ   ۚ   ۖ   ۚ   ۗ   ۗ 
Wa Lā Ta'kulū 'Amwālakum Baynakum Bil-Bāţili Wa Tudlū Bihā 'Ilá Al-Ĥukkāmi Lita'kulū Farīqāan Min 'Amwāli An-Nāsi Bil-'Ithmi Wa 'Antum Ta`lamūna 002-188 Kada ku ci dukiyõyinku a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane.
Yas'alūnaka `Ani Al-'Ahillati  ۖ  Qul Hiya Mawāqītu Lilnnāsi Wa Al-Ĥajji  ۗ  Wa Laysa Al-Birru Bi'an Ta'tū Al-Buyūta Min Žuhūrihā Wa Lakinna Al-Birra Mani Attaqá  ۗ  Wa 'Tū Al-Buyūta Min 'Abwābihā  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha La`allakum Tufliĥūna 002-189 Kuma suna tambayar ka daga jirajiran wata. Ka ce: "Su lõkatai ne dõmin mutãne da haji, kuma bã addini ba ne ku je wa gidãje daga bãyansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku je wa gidãje daga ƙõfõfinsu, kuma ku bi Allah da taƙawa: tsammãninku, ku ci nasara.  ۖ   ۗ   ۗ   ۚ 
Wa Qātilū Fī Sabīli Al-Lahi Al-Ladhīna Yuqātilūnakum Wa Lā Ta`tadū  ۚ  'Inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Al-Mu`tadīna 002-190 Kuma ku yãƙi waɗanda suke yãƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsõkana, lalle ne Allah bã Ya son mãsu tsõkana.  ۚ 
qtulūhum Ĥaythu Thaqiftumūhum Wa 'Akhrijūhum Min Ĥaythu 'Akhrajūkum Wa  ۚ  Al-Fitnatu 'Ashaddu Mina Al-Qatli  ۚ  Wa Lā Tuqātilūhum `Inda Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Ĥattá Yuqātilūkum Fīhi  ۖ  Fa'in Qātalūkumqtulūhum  ۗ  Kadhālika Jazā'u Al-Kāfirīna 002-191 Kuma ku yãƙe su inda kuka sãme su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa. Kuma kada ku yãƙe su a wurin Masallãci Tsararre (Hurumin Makka) fãce fa idan sun yãƙe ku a cikinsa. To, idan sun yãƙe ku, sai ku yãƙe su. Kamar wancan ne sakamakon kãfirai yake.  ۚ   ۚ   ۖ   ۗ 
Fa'ini Antahaw Fa'inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 002-192 Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Wa Qātilūhum Ĥattá Lā Takūna Fitnatun Wa Yakūna Ad-Dīnu Lillahi  ۖ  Fa'ini Antahaw Falā `Udwāna 'Illā `Alá Až-Žālimīna 002-193 Kuma ku yãƙe su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai.  ۖ 
Ash-Shahru Al-Ĥarāmu Bish-Shahri Al-Ĥarāmi Wa Al-Ĥurumātu Qişāşun  ۚ  Famani A`tadá `Alaykum Fā`tadū `Alayhi Bimithli Mā A`tadá `Alaykum  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Ma`a Al-Muttaqīna 002-194 Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmõmi mãsu dũkar jũna ne. Sabõda haka wanda ya yi tsõkana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misãlin abin da ya yi tsõkana a kanku. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Yana tãre da mãsu taƙawa.  ۚ   ۚ 
Wa 'Anfiqū Fī Sabīli Al-Lahi Wa Lā Tulqū Bi'aydīkum 'Ilá At-Tahlukati  ۛ  Wa 'Aĥsinū  ۛ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Muĥsinīna 002-195 Kuma ku ciyar a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.  ۛ   ۛ 
Wa 'Atimmū Al-Ĥajja Wa Al-`Umrata Lillahi  ۚ  Fa'in 'Uĥşirtum Famā Astaysara Mina Al-Hadyi  ۖ  Wa Lā Taĥliqū Ru'ūsakum Ĥattá Yablugha Al-Hadyu Maĥillahu  ۚ  Faman Kāna Minkum Marīđāan 'Aw Bihi 'Adháan Min Ra'sihi Fafidyatun Min Şiyāmin 'Aw Şadaqatin 'Aw Nusukin  ۚ  Fa'idhā 'Amintum Faman Tamatta`a Bil-`Umrati 'Ilá Al-Ĥajji Famā Astaysara Mina Al-Hadyi  ۚ  Faman Lam Yajid Faşiyāmu Thalāthati 'Ayyāmin Al-Ĥajji Wa Sab`atin 'Idhā Raja`tum  ۗ  Tilka `Asharatun Kāmilatun  ۗ  Dhālika Liman Lam Yakun 'Ahluhu Ĥāđirī Al-Masjidi Al-Ĥarāmi  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Shadīdu Al-`Iqābi 002-196 Kuma ku cika hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne.  ۚ   ۖ   ۚ  ~  ۚ   ۚ   ۗ   ۗ   ۚ 
Al-Ĥajju 'Ash/hurun Ma`lūmātun  ۚ  Faman Farađa Fīhinna Al-Ĥajja Falā Rafatha Wa Lā Fusūqa Wa Lā Jidāla Fī Al-Ĥajji  ۗ  Wa Mā Taf`alū Min Khayrin Ya`lamhu Al-Lahu  ۗ  Wa Tazawwadū Fa'inna Khayra Az-Zādi At-Taqwá  ۚ  Wa Attaqūnī Yā 'Ū Al-'Albābi 002-197 Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsiƙanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula.  ۚ   ۗ   ۗ   ۚ 
Laysa `Alaykum Junāĥun 'An Tabtaghū Fađlāan Min Rabbikum  ۚ  Fa'idhā 'Afađtum Min `Arafātindhkurū Al-Laha `Inda Al-Mash`ari Al-Ĥarāmi  ۖ  Wa Adhkurūhu Kamā Hadākum Wa 'In Kuntum Min Qablihi Lamina Ađ-Đāllīna 002-198 Bãbu laifi a kanku ga ku nẽmi falala daga Ubangijinku. Sa'an nan idan kun malãlo daga Arafãt, sai ku yi ta ambatar Allah a wurin Mash'aril Harãmi kuma ku tuna Shi kamar shiriyar da Ya yi muku kuma lalle ne kun kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga ɓatattu.  ۚ   ۖ 
Thumma 'Afīđū Min Ĥaythu 'Afāđa An-Nāsu Wa Astaghfirū Al-Laha  ۚ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 002-199 Sa'an nan kuma ku malãlo daga inda mutãne suke malalowa. Kuma ku nemi gafara ga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۚ 
Fa'idhā Qađaytum Manāsikakumdhkurū Al-Laha Kadhikrikum 'Ābā'akum 'Aw 'Ashadda Dhikrāan  ۗ  Famina An-Nāsi Man Yaqūlu Rabbanā 'Ātinā Fī Ad-Dunyā Wa Mā Lahu Fī Al-'Ākhirati Min Khalāqin 002-200 To, idan kun ƙãre ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, kõ kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutãne akwai wanda yake cẽwa: "Ya Ubangjinmu! Ka bã mu a cikin dũniya! Kuma bã ya da wanirabo a cikin Lãhira.  ۗ 
Wa Minhum Man Yaqūlu Rabbanā 'Ātinā Fī Ad-Dunyā Ĥasanatan Wa Fī Al-'Ākhirati Ĥasanatan Wa Qinā `Adhāba An-Nāri 002-201 Kuma daga gare su akwai wanda yake cẽwa: "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!"
'Ūlā'ika Lahum Naşībun Mimmā Kasabū Wa  ۚ  Allāhu Sarī`u Al-Ĥisābi 002-202 Waɗannan suna da rabo daga abin da suka sanã'anta; kuma Allah Mai gaggãwar sakamako da yawa ne.  ۚ 
Wa Adhkurū Al-Laha Fī 'Ayyāmin Ma`dūdātin  ۚ  Faman Ta`ajjala Fī Yawmayni Falā 'Ithma `Alayhi Wa Man Ta'akhkhara Falā 'Ithma `Alayhi  ۚ  Limani Attaqá  ۗ  Wa Attaqū Al-Laha Wa A`lamū 'Annakum 'Ilayhi Tuĥsharūna 002-203 Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu. To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku.  ۚ   ۚ   ۗ 
Wa Mina An-Nāsi Man Yu`jibuka Qawluhu Fī Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Yush/hidu Al-Laha `Alá Mā Fī Qalbihi Wa Huwa 'Aladdu Al-Khāmi 002-204 Kuma akwai daga mutãne wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne.
Wa 'Idhā Tawallá Sa`á Fī Al-'Arđi Liyufsida Fīhā Wa Yuhlika Al-Ĥartha Wa An-Nasla Wa  ۗ  Allāhu Lā Yuĥibbu Al-Fasāda 002-205 Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa dõmin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shũka da 'ya'yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son ɓarna.  ۗ 
Wa 'Idhā Qīla Lahu Attaqi Al-Laha 'Akhadhat/hu Al-`Izzatu Bil-'Ithmi  ۚ  Faĥasbuhu Jahannamu  ۚ  Wa Labi'sa Al-Mihādu 002-206 Kuma idan an ce masa: "Ka ji tsõron Allah," sai girman kai da yin zunubi ya ɗauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma haƙĩƙa, shimfiɗa tã munana.  ۚ   ۚ 
Wa Mina An-Nāsi Man Yashrī Nafsahu Abtighā'a Marđāati Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu Ra'ūfun Bil-`Ibādi 002-207 Kuma akwai daga mutãne wanda yake sayar da ransa, dõmin nẽman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bãyi ne.  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Adkhulū Fī As-Silmi Kāffatan Wa Lā Tattabi`ū Khuţuwāti Ash-Shayţāni  ۚ  'Innahu Lakum `Adūwun Mubīnun 002-208 Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã ɗaya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan; lalle ne shĩ a gare ku maƙiyine, bayyananne.  ۚ 
Fa'in Zalaltum Min Ba`di Mā Jā'atkumu Al-Bayyinātu Fā`lamū 'Anna Al-Laha `Azīzun Ĥakīmun 002-209 To, idan kun karkace daga bayan hujjõji bayyanannu sun zo muku to ku sani cẽwa lalle ne Allah, Mabuwãyi ne, Mai hikima.
Hal Yanžurūna 'Illā 'An Ya'tiyahumu Al-Lahu Fī Žulalin Mina Al-Ghamāmi Wa Al-Malā'ikatu Wa Quđiya Al-'Amru  ۚ  Wa 'Ilá Al-Lahi Turja`u Al-'Umūru 002-210 Shin suna jira, fãce dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwõyi na girgije, da malã'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su.  ۚ 
Sal Banī 'Isrā'īla Kam 'Ātaynāhum Min 'Āyatin Bayyinatin  ۗ  Wa Man Yubaddil Ni`mata Al-Lahi Min Ba`di Mā Jā'at/hu Fa'inna Al-Laha Shadīdu Al-`Iqābi 002-211 Ka tambayi Banĩ Isrã'ila, da yawa Muka bã su daga ãyõyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bãyan tã je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.  ۗ 
Zuyyina Lilladhīna Kafarū Al-Ĥayāatu Ad-Dunyā Wa Yaskharūna Mina Al-Ladhīna 'Āmanū Wa  ۘ  Al-Ladhīna Attaqaw Fawqahum Yawma Al-Qiyāmati Wa  ۗ  Allāhu Yarzuqu Man Yashā'u Bighayri Ĥisābin 002-212 An ƙawata rãyuwar dũniya ga waɗanda suka kãfirta, kuma suna izgili daga waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su, a Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, bã da lissãfi ba.  ۘ   ۗ 
Kāna An-Nāsu 'Ummatan Wāĥidatan Faba`atha Al-Lahu An-Nabīyīna Mubashshirīna Wa Mundhirīna Wa 'Anzala Ma`ahumu Al-Kitāba Bil-Ĥaqqi Liyaĥkuma Bayna An-Nāsi Fīmā Akhtalafū Fīhi  ۚ  Wa Mā Akhtalafa Fīhi 'Illā Al-Ladhīna 'Ūtūhu Min Ba`di Mā Jā'at/humu Al-Bayyinātu Baghyāan Baynahum  ۖ  Fahadá Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Limā Akhtalafū Fīhi Mina Al-Ĥaqqi Bi'idhnihi Wa  ۗ  Allāhu Yahdī Man Yashā'u 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin 002-213 Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa. kuma bãbu wanda ya sãɓã, a cikinsa, fãce waɗanda aka bai wa shi daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu dõmin zãlunci a tsakãninsu. Sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi ĩmani ga abin da suka sãɓã a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya.  ۚ  ~  ۖ   ۗ 
'Am Ĥasibtum 'An Tadkhulū Al-Jannata Wa Lammā Ya'tikum Mathalu Al-Ladhīna Khalaw Min Qablikum  ۖ  Massat/humu Al-Ba'sā'u Wa Ađ-Đarrā'u Wa Zulzilū Ĥattá Yaqūla Ar-Rasūlu Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Ma`ahu Matá Naşru Al-Lahi  ۗ  'Alā 'Inna Naşra Al-Lahi Qarībun 002-214 Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin waɗanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!  ۖ   ۗ 
Yas'alūnaka Mādhā Yunfiqūna  ۖ  Qul Mā 'Anfaqtum Min Khayrin Falilwālidayni Wa Al-'Aqrabīna Wa Al-Yatāmá Wa Al-Masākīni Wa Abni As-Sabīli  ۗ  Wa Mā Taf`alū Min Khayrin Fa'inna Al-Laha Bihi `Alīmun 002-215 Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne.  ۖ   ۗ 
Kutiba `Alaykumu Al-Qitālu Wa Huwa Kurhun Lakum  ۖ  Wa `Asá 'An Takrahū Shay'āan Wa Huwa Khayrun Lakum  ۖ  Wa `Asá 'An Tuĥibbū Shay'āan Wa Huwa Sharrun Lakum Wa  ۗ  Allāhu Ya`lamu Wa 'Antum Lā Ta`lamūna 002-216 An wajabta yãƙi a kanku, alhãli kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba.  ۖ   ۖ   ۗ 
Yas'alūnaka `Ani Ash-Shahri Al-Ĥarāmi Qitālin Fīhi  ۖ  Qul Qitālun Fīhi Kabīrun  ۖ  Wa Şaddun `An Sabīli Al-Lahi Wa Kufrun Bihi Wa Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Wa 'Ikhrāju 'Ahlihi Minhu 'Akbaru `Inda Al-Lahi Wa  ۚ  Al-Fitnatu 'Akbaru Mina Al-Qatli  ۗ  Wa Lā Yazālūna Yuqātilūnakum Ĥattá Yaruddūkum `An Dīnikum 'Ini Astaţā`ū  ۚ  Wa Man Yartadid Minkum `An Dīnihi Fayamut Wa Huwa Kāfirun Fa'ūlā'ika Ĥabiţat 'A`māluhum Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati  ۖ  Wa 'Ūlā'ika 'Aşĥābu An-Nāri  ۖ  Hum Fīhā Khālidūna 002-217 Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: "Yin yãƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma waɗannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.  ۖ   ۖ   ۚ   ۗ   ۚ   ۖ   ۖ 
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Al-Ladhīna Hājarū Wa Jāhadū Fī Sabīli Al-Lahi 'Ūlā'ika Yarjūna Raĥmata Al-Lahi Wa  ۚ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 002-218 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fãtar (sãmun) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۚ 
Yas'alūnaka `Ani Al-Khamri Wa Al-Maysiri  ۖ  Qul Fīhimā 'Ithmun Kabīrun Wa Manāfi`u Lilnnāsi Wa 'Ithmuhumā 'Akbaru Min Naf`ihimā  ۗ  Wa Yas'alūnaka Mādhā Yunfiqūna Quli Al-`Afwa  ۗ  Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu Lakumu Al-'Āyāti La`allakum Tatafakkarūna 002-219 Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: "A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: "Abin da ya rage." Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni.  ۖ   ۗ   ۗ 
Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati  ۗ  Wa Yas'alūnaka `Ani Al-Yatāmá  ۖ  Qul 'Işlāĥun Lahum Khayrun  ۖ  Wa 'In Tukhāliţūhum Fa'ikhwānukum Wa  ۚ  Allāhu Ya`lamu Al-Mufsida Mina Al-Muşliĥi  ۚ  Wa Law Shā'a Al-Lahu La'a`natakum  ۚ  'Inna Al-Laha `Azīzun Ĥakīmun 002-220 A cikin dũniya da Lãhira. Kuma suna tambayar ka game da marãyu. Ka ce: "Kyautatãwa gare su ne mafi alhẽri, kuma idan kun haɗa da su (wajen abinci), to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai ɓãtãwa daga mai kyautatãwa. Kuma dã Allah Yã so, dã Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.  ۗ   ۖ   ۖ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa Lā Tankiĥū Al-Mushrikāti Ĥattá Yu'uminna  ۚ  Wa La'amatun Mu'uminatun Khayrun Min Mushrikatin Wa Law 'A`jabatkum  ۗ  Wa Lā Tunkiĥū Al-Mushrikīna Ĥattá Yu'uminū  ۚ  Wa La`abdun Mu'uminun Khayrun Min Mushrikin Wa Law 'A`jabakum  ۗ  'Ūlā'ika Yad`ūna 'Ilá An-Nāri Wa  ۖ  Allāhu Yad`ū 'Ilá Al-Jannati Wa Al-Maghfirati Bi'idhnihi  ۖ  Wa Yubayyinu 'Āyātihi Lilnnāsi La`allahum Yatadhakkarūna 002-221 Kuma kada ku auri mãtã mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhẽri daga ɗiya kãfira,kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa.  ۚ   ۗ   ۚ   ۗ   ۖ   ۖ 
Wa Yas'alūnaka `Ani Al-Maĥīđi  ۖ  Qul Huwa 'Adháan Fā`tazilū An-Nisā' Fī Al-Maĥīđi  ۖ  Wa Lā Taqrabūhunna Ĥattá Yaţhurna  ۖ  Fa'idhā Taţahharna Fa'tūhunna Min Ĥaythu 'Amarakumu Al-Lahu  ۚ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu At-Tawwābīna Wa Yuĥibbu Al-Mutaţahhirīna 002-222 Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.  ۖ   ۖ   ۖ   ۚ 
Nisā'uukum Ĥarthun Lakum Fa'tū Ĥarthakum 'Anná Shi'tum  ۖ  Wa Qaddimū Li'nfusikum  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha Wa A`lamū 'Annakum Mulāqūhu  ۗ  Wa Bashshiri Al-Mu'uminīna 002-223 Mãtanku gõnaki ne a gare ku, sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar (da alheri) sabõda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai.  ۖ   ۚ   ۗ 
Wa Lā Taj`alū Al-Laha `Urđatan Li'ymānikum 'An Tabarrū Wa Tattaqū Wa Tuşliĥū Bayna An-Nāsi Wa  ۗ  Allāhu Samī`un `Alīmun 002-224 Kuma kada ku sanya Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.  ۗ 
Lā Yu'uākhidhukumu Al-Lahu Bil-Laghwi Fī 'Aymānikum Wa Lakin Yu'uākhidhukum Bimā Kasabat Qulūbukum Wa  ۗ  Allāhu Ghafūrun Ĥalīmun 002-225 Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.  ۗ 
Lilladhīna Yu'ulūna Min Nisā'ihim Tarabbuşu 'Arba`ati 'Ash/hurin  ۖ  Fa'in Fā'ū Fa'inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 002-226 Ga waɗanda suke yin rantsuwa daga matansu akwai jinkirin watã huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۖ 
Wa 'In `Azamū Aţ-Ţalāqa Fa'inna Al-Laha Samī`un `Alīmun 002-227 Kuma idan sun yi niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.
Wa Al-Muţallaqātu Yatarabbaşna Bi'anfusihinna Thalāthata  ۚ  Qurū'in Wa Lā Yaĥillu Lahunna 'An Yaktumna Mā Khalaqa Al-Lahu Fī 'Arĥāmihinna 'In Kunna Yu'uminna Bil-Lahi Wa Al-Yawmi  ۚ  Al-'Ākhiri Wa Bu`ūlatuhunna 'Aĥaqqu Biraddihinna Fī Dhālika 'In 'Arādū  ۚ  'Işlāĥāan Wa Lahunna Mithlu Al-Ladhī `Alayhinna  ۚ  Bil-Ma`rūfi Wa Lilrrijāli `Alayhinna  ۗ  Darajatun Wa Allāhu `Azīzun Ĥakīmun 002-228 Kuma mãtã waɗanda aka saki aurensu, suna jinkiri da kansu tsarki uku. Kuma bã ya halatta a gare su, su ɓõye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifunsu, idan sun kasance suna yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyãrawa. Kuma sũ mãtan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu (su mãtan). Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۗ 
Aţ-Ţalāqu Marratāni  ۖ  Fa'imsākun Bima`rūfin 'Aw Tasrīĥun Bi'iĥsānin  ۗ  Wa Lā Yaĥillu Lakum 'An Ta'khudhū Mimmā 'Ātaytumūhunna Shay'āan 'Illā 'An Yakhāfā 'Allā Yuqīmā Ĥudūda Al-Lahi  ۖ  Fa'in Khiftum 'Allā Yuqīmā Ĥudūda Al-Lahi Falā Junāĥa `Alayhimā Fīmā Aftadat Bihi  ۗ  Tilka Ĥudūdu Al-Lahi Falā Ta`tadūhā  ۚ  Wa Man Yata`adda Ĥudūda Al-Lahi Fa'ūlā'ika Humu Až-Žālimūna 002-229 Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai.  ۖ   ۗ   ۖ   ۗ   ۚ 
Fa'in Ţallaqahā Falā Taĥillu Lahu Min Ba`du Ĥattá Tankiĥa Zawjāan Ghayrahu  ۗ  Fa'in Ţallaqahā Falā Junāĥa `Alayhimā 'An Yatarāja`ā 'In Žannā 'An Yuqīmā Ĥudūda Al-Lahi  ۗ  Wa Tilka Ĥudūdu Al-Lahi Yubayyinuhā Liqawmin Ya`lamūna 002-230 Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna,idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.  ۗ   ۗ 
Wa 'Idhā Ţallaqtumu An-Nisā' Fabalaghna 'Ajalahunna Fa'amsikūhunna Bima`rūfin 'Aw Sarriĥūhunna Bima`rūfin  ۚ  Wa Lā Tumsikūhunna Đirārāan Lita`tadū  ۚ  Wa Man Yaf`al Dhālika Faqad Žalama Nafsahu  ۚ  Wa Lā Tattakhidhū 'Āyāti Al-Lahi Huzūan  ۚ  Wa Adhkurū Ni`mata Al-Lahi `Alaykum Wa Mā 'Anzala `Alaykum Mina Al-Kitābi Wa Al-Ĥikmati Ya`ižukum Bihi  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Bikulli Shay'in `Alīmun 002-231 Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Wa 'Idhā Ţallaqtumu An-Nisā' Fabalaghna 'Ajalahunna Falā Ta`đulūhunna 'An Yankiĥna 'Azwājahunna 'Idhā Tarāđaw Baynahum Bil-Ma`rūfi  ۗ  Dhālika Yū`ažu Bihi Man Kāna Minkum Yu'uminu Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri  ۗ  Dhālikum 'Azká Lakum Wa 'Aţharu Wa  ۗ  Allāhu Ya`lamu Wa 'Antum Lā Ta`lamūna 002-232 Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku,kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba.  ۗ   ۗ   ۗ 
Wa Al-Wālidātu Yurđi`na 'Awlādahunna Ĥawlayni  ۖ  Kāmilayni Liman 'Arāda 'An Yutimma  ۚ  Ar-Rađā`ata Wa `Alá Al-Mawlūdi Lahu Rizquhunna Wa Kiswatuhunna  ۚ  Bil-Ma`rūfi Lā Tukallafu Nafsun 'Illā  ۚ  Wus`ahā Lā Tuđārra Wa A-Datun Biwaladihā Wa Lā Mawlūdun Lahu  ۚ  Biwaladihi Wa `Alá Al-Wārithi Mithlu  ۗ  Dhālika Fa'in 'Arādā Fişālāan `An Tarāđin Minhumā Wa Tashāwurin Falā Junāĥa  ۗ  `Alayhimā Wa 'In 'Aradtum 'An Tastarđi`ū 'Awlādakum Falā Junāĥa `Alaykum 'Idhā Sallamtum Mā 'Ātaytum  ۗ  Bil-Ma`rūfi Wa Attaqū Al-Laha Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Bimā Ta`malūna Başīrun 002-233 Kuma mãsu haifuwa (sakakku) suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne.  ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۗ   ۗ   ۗ 
Wa Al-Ladhīna Yutawaffawna Minkum Wa Yadharūna 'Azwājāan Yatarabbaşna Bi'anfusihinna 'Arba`ata 'Ash/hurin  ۖ  Wa `Ashrāan Fa'idhā Balaghna 'Ajalahunna Falā Junāĥa `Alaykum Fīmā Fa`alna Fī 'Anfusihinna  ۗ  Bil-Ma`rūfi Wa Allāhu Bimā Ta`malūna Khabīrun 002-234 Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.  ۖ   ۗ 
Wa Lā Junāĥa `Alaykum Fīmā `Arrađtum Bihi Min Khiţbati An-Nisā' 'Aw 'Aknantum Fī 'Anfusikum  ۚ  `Alima Al-Lahu 'Annakum Satadhkurūnahunna Wa Lakin Lā Tuwā`idūhunna Sirrāan 'Illā 'An Taqūlū Qawlāan Ma`rūfāan  ۚ  Wa Lā Ta`zimū `Uqdata An-Nikāĥi Ĥattá Yablugha Al-Kitābu 'Ajalahu  ۚ  Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Ya`lamu Mā Fī 'Anfusikum Fāĥdharūhu  ۚ  Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Ghafūrun Ĥalīmun 002-235 Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ 
Lā Junāĥa `Alaykum 'In Ţallaqtumu An-Nisā' Mā Lam Tamassūhunna 'Aw Tafriđū Lahunna Farīđatan  ۚ  Wa Matti`ūhunna `Alá Al-Mūsi`i Qadaruhu Wa `Alá Al-Muqtiri Qadaruhu Matā`āan Bil-Ma`rūfi  ۖ  Ĥaqqāan `Alá Al-Muĥsinīna 002-236 Kuma bãbu laifi a kanku idan kun saki mãtã matuƙar ba ku shãfe su ba, kuma ba ku yanka musu sadãki ba. Kuma ku bã su kyautar dãɗaɗãwa, a kan mawadãci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; dõmin dãɗaɗrwa, da alhẽri, wãjibi ne a kan mãsu kyautatãwa.  ۚ   ۖ 
Wa 'In Ţallaqtumūhunna Min Qabli 'An Tamassūhunna Wa Qad Farađtum Lahunna Farīđatan Fanişfu Mā Farađtum 'Illā 'An Ya`fūna 'Aw Ya`fuwa Al-Ladhī Biyadihi `Uqdatu An-Nikāĥi  ۚ  Wa 'An Ta`fū 'Aqrabu Lilttaqwá  ۚ  Wa Lā Tansaw Al-Fađla Baynakum  ۚ  'Inna Al-Laha Bimā Ta`malūna Başīrun 002-237 Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.  ۚ   ۚ   ۚ 
Ĥāfižū `Alá Aş-Şalawāti Wa Aş-Şalāati Al-Wusţá Wa Qūmū Lillahi Qānitīna 002-238 Ku tsare lõkatai a kan sallõli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai ga Allah.
Fa'in Khiftum Farijālāan 'Aw Rukbānāan  ۖ  Fa'idhā 'Amintumdhkurū Al-Laha Kamā `Allamakum Mā Lam Takūnū Ta`lamūna 002-239 To, idan kun ji tsõro, to (ku dai yi salla gwargwadon hali) da tafiya ƙasa kõ kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya nũna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba.  ۖ 
Wa Al-Ladhīna Yutawaffawna Minkum Wa Yadharūna 'Azwājāan Waşīyatan Li'zwājihim Matā`āan 'Ilá Al-Ĥawli Ghayra  ۚ  'Ikhrājin Fa'in Kharajna Falā Junāĥa `Alaykum Fī Mā Fa`alna Fī 'Anfusihinna Min  ۗ  Ma`rūfin Wa Allāhu `Azīzun Ĥakīmun 002-240 Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku, alhãli suna barin mãtan aure, wasiyya ga mãtan aurensu da dãɗaɗãwa zuwa ga shekara guda bãbu fitarwa, to, idan sun fita to bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.  ۚ   ۗ 
Wa Lilmuţallaqāti Matā`un Bil-Ma`rūfi  ۖ  Ĥaqqāan `Alá Al-Muttaqīna 002-241 Kuma waɗanda aka saki suna da dãɗaɗãwa gwargwadon hãli, wajabce a kan mãsu taƙawa .  ۖ 
Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu Lakum 'Āyātihi La`allakum Ta`qilūna 002-242 Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa; tsammãninku, kuna hankalta.
'Alam Tara 'Ilá Al-Ladhīna Kharajū Min Diyārihim Wa Hum 'Ulūfun Ĥadhara Al-Mawti Faqāla Lahumu Al-Lahu Mūtū Thumma 'Aĥyāhum  ۚ  'Inna Al-Laha Ladhū Fađlin `Alá An-Nāsi Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Yashkurūna 002-243 Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa.  ۚ 
Wa Qātilū Fī Sabīli Al-Lahi Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Samī`un `Alīmun 002-244 Kuma ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mai jĩ ne, Masani.
Man Dhā Al-Ladhī Yuqriđu Al-Laha Qarđāan Ĥasanāan Fayuđā`ifahu Lahu 'Ađ`āfāan Kathīratan Wa  ۚ  Allāhu Yaqbiđu Wa Yabsuţu Wa 'Ilayhi Turja`ūna 002-245 Wãne ne wanda zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku. ~  ۚ 
'Alam Tara 'Ilá Al-Mala'i Min Banī 'Isrā'īla Min Ba`di Mūsá 'Idh Qālū Linabīyin Lahum Ab`ath Lanā Malikāan Nuqātil Fī Sabīli Al-Lahi  ۖ  Qāla Hal `Asaytum 'In Kutiba `Alaykumu Al-Qitālu 'Allā Tuqātilū  ۖ  Qālū Wa Mā Lanā 'Allā Nuqātila Fī Sabīli Al-Lahi Wa Qad 'Ukhrijnā Min Diyārinā Wa 'Abnā'inā  ۖ  Falammā Kutiba `Alayhimu Al-Qitālu Tawallaw 'Illā Qalīlāan Minhum Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Biž-Žālimīna 002-246 Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: "Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba?" Suka ce: "Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu?" To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.  ۖ   ۖ   ۖ   ۗ 
Wa Qāla Lahum Nabīyuhum 'Inna Al-Laha Qad Ba`atha Lakum Ţālūta Malikāan  ۚ  Qālū 'Anná Yakūnu Lahu Al-Mulku `Alaynā Wa Naĥnu 'Aĥaqqu Bil-Mulki Minhu Wa Lam Yu'uta Sa`atan Mina Al-Māli  ۚ  Qāla 'Inna Al-Laha Aşţafāhu `Alaykum Wa Zādahu Basţatan Al-`Ilmi Wa Al-Jismi Wa  ۖ  Allāhu Yu'utī Mulkahu Man Yashā'u Wa  ۚ  Allāhu Wāsi`un `Alīmun 002-247 Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne, Allah ya naɗa muku ãlũta ya zama sarki." Suka ce: "Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya?" Ya ce: "Lalle ne, Allah Yã zãɓe shi a kanku, kuma Ya ƙãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani.  ۚ   ۚ   ۖ   ۚ 
Wa Qāla Lahum Nabīyuhum 'Inna 'Āyata Mulkihi 'An Ya'tiyakumu At-Tābūtu Fīhi Sakīnatun Min Rabbikum Wa Baqīyatun Mimmā Taraka 'Ālu Mūsá Wa 'Ālu Hārūna Taĥmiluhu Al-Malā'ikatu  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Lakum 'In Kuntum Mu'uminīna 002-248 Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku (ta naɗin ãlũta daga Allah ne) idan kun kasance mãsu ĩmãni." ~  ۚ 
Falammā Faşala Ţālūtu Bil-Junūdi Qāla 'Inna Al-Laha Mubtalīkum Binaharin Faman Shariba Minhu Falaysa Minnī Wa Man Lam Yaţ`amhu Fa'innahu Minnī 'Illā Mani Aghtarafa Ghurfatan Biyadihi  ۚ  Fasharibū Minhu 'Illā Qalīlāan Minhum  ۚ  Falammā Jāwazahu Huwa Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Ma`ahu Qālū Lā Ţāqata Lanā Al-Yawma Bijālūta Wa Junūdihi  ۚ  Qāla Al-Ladhīna Yažunnūna 'Annahum Mulāqū Al-Lahi Kam Min Fi'atin Qalīlatin Ghalabat Fi'atan Kathīratan Bi'idhni Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu Ma`a Aş-Şābirīna 002-249 A lõkacin da ãlũta ya fita da rundunõnin, ya ce: "Lalle ne Allah Mai jarrabarku ne da wani kõgi. To, wanda ya sha daga gare shi, to, ba shi daga gare ni, kuma wanda bai ɗanɗane shi ba to lalle ne shi, yana daga gare ni, fãce, wanda ya kamfata, kamfata guda da hannunsa." Sai suka sha daga gare shi, fãce kaɗan daga gare su. To, a lõkacin da (ãlũta) ya ƙẽtare shi, shi da waɗanda suka yi ĩmani tãre da shi, (sai waɗanda suka sha) suka ce: "Babu ĩko a gare mu yau game da Jãlũta da rundunõninsa."Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle sũ mãsu gamuwa ne da Allah, suka ce: "Da yawa ƙungiya kaɗan ta rinjayi wata ƙungiya mai yawa da iznin Allah, kuma Allah Yana tãre da mãsu haƙuri."  ۚ   ۚ   ۚ   ۗ 
Wa Lammā Barazū Lijālūta Wa Junūdihi Qālū Rabbanā 'Afrigh `Alaynā Şabrāan Wa Thabbit 'Aqdāmanā Wa Anşurnā `Alá Al-Qawmi Al-Kāfirīna 002-250 Kuma a lõkacin da suka bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."
Fahazamūhum Bi'idhni Al-Lahi Wa Qatala Dāwūdu Jālūta Wa 'Ātāhu Al-Lahu Al-Mulka Wa Al-Ĥikmata Wa `Allamahu Mimmā Yashā'u  ۗ  Wa Lawlā Daf`u Al-Lahi An-Nāsa Ba`đahum Biba`đin Lafasadati Al-'Arđu Wa Lakinna Al-Laha Dhū Fađlin `Alá Al-`Ālamīna 002-251 Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dãwudu ya kashe Jãlũta, kuma Allah Ya bã shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma bã dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne sãshensu da sãshe ba lalle ne dã ƙasa tã ɓãci; kuma amma Allah Ma'abũcin falala ne a kan tãlikai.  ۗ 
Tilka 'Āyātu Al-Lahi Natlūhā `Alayka Bil-Ĥaqqi  ۚ  Wa 'Innaka Lamina Al-Mursalīna 002-252 Waɗancan ayõyin Allah ne: Muna karanta su a kanka da gaskiya: Kuma lalle ne kai, hakĩka, kana daga manzanni.  ۚ 
Tilka Ar-Rusulu Fađđalnā Ba`đahum `Alá Ba`đin  ۘ  Minhum Man Kallama Al-Lahu  ۖ  Wa Rafa`a Ba`đahum Darajātin  ۚ  Wa 'Ātaynā `Īsá Abna Maryama Al-Bayyināti Wa 'Ayyadnāhu Birūĥi Al-Qudusi  ۗ  Wa Law Shā'a Al-Lahu Mā Aqtatala Al-Ladhīna Min Ba`dihim Min Ba`di Mā Jā'at/humu Al-Bayyinātu Wa Lakini Akhtalafū Faminhum Man 'Āmana Wa Minhum Man Kafara  ۚ  Wa Law Shā'a Al-Lahu Mā Aqtatalū Wa Lakinna Al-Laha Yaf`alu Mā Yurīdu 002-253 Waɗancan manzannin Mun fĩfĩta sãshensu a kan sãshe: Daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya ɗaukaka sãshensu da darajõji; kuma Muka bai wa Ĩsã dan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafã shi da Rũhi mai tsarki. Kuma dã Allah Yã so dã waɗanda suke daga bãyansu, bã zã su yi yãƙi ba, daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun sãɓa wa jũna, sabõda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni, kuma daga cikin su akwai wanda ya kãfirta. Kuma dã Allah Yã so dã bã zã su yãƙi jũna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi.  ۘ   ۖ   ۚ   ۗ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Anfiqū Mimmā Razaqnākum Min Qabli 'An Ya'tiya Yawmun Lā Bay`un Fīhi Wa Lā Khullatun Wa Lā Shafā`atun Wa  ۗ  Al-Kāfirūna Humu Až-Žālimūna 002-254 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabãnin wani yini ya zo bãbu ciniki a cikinsa kuma bãbu abũta, kuma bãbu cẽto, kuma kãfirai sũ ne azzãlumai.  ۗ 
Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Al-Ĥayyu Al-Qayyūmu  ۚ  Lā Ta'khudhuhu Sinatun Wa Lā Nawmun  ۚ  Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۗ  Man Dhā Al-Ladhī Yashfa`u `Indahu 'Illā Bi'idhnihi  ۚ  Ya`lamu Mā Bayna 'Aydīhim Wa Mā Khalfahum  ۖ  Wa Lā Yuĥīţūna Bishay'in Min `Ilmihi 'Illā Bimā Shā'a  ۚ  Wasi`a Kursīyuhu As-Samāwāti Wa Al-'Arđa  ۖ  Wa Lā Ya'ūduhu Ĥifžuhumā  ۚ  Wa Huwa Al-`Alīyu Al-`Ažīmu 002-255 Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma. ~  ۚ   ۚ   ۗ  ~  ۚ   ۖ  ~  ۚ   ۖ   ۚ 
Lā 'Ikrāha Fī Ad-Dīni  ۖ  Qad Tabayyana Ar-Rushdu Mina Al-Ghayyi  ۚ  Faman Yakfur Biţ-Ţāghūti Wa Yu'umin Bil-Lahi Faqadi Astamsaka Bil-`Urwati Al-Wuthqá Lā Anfişāma Lahā Wa  ۗ  Allāhu Samī`un `Alīmun 002-256 Bãbu tĩlastãwa a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.  ۖ   ۚ   ۗ 
Al-Lahu Wa Līyu Al-Ladhīna 'Āmanū Yukhrijuhum Mina Až-Žulumāti 'Ilá An-Nūr Wa  ۖ  Al-Ladhīna Kafarū 'Awliyā'uuhumu Aţ-Ţāghūtu Yukhrijūnahum Mina An-Nūr 'Ilá Až-Žulumāti  ۗ  'Ūlā'ika 'Aşĥābu An-Nāri  ۖ  Hum Fīhā Khālidūna 002-257 Allah Shi ne Masõyin waɗanda suka yi ĩmãni; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kãfirta, masõyansu ãgũtu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.  ۖ   ۗ   ۖ 
'Alam Tara 'Ilá Al-Ladhī Ĥājja 'Ibrāhīma Fī Rabbihi 'An 'Ātāhu Al-Lahu Al-Mulka 'Idh Qāla 'Ibrāhīmu Rabbī Al-Ladhī Yuĥyī Wa Yumītu Qāla 'Anā 'Uĥyī Wa 'Umītu  ۖ  Qāla 'Ibrāhīmu Fa'inna Al-Laha Ya'tī Bish-Shamsi Mina Al-Mashriqi Fa'ti Bihā Mina Al-Maghribi Fabuhita Al-Ladhī Kafara Wa  ۗ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna 002-258 Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai. ~  ۖ   ۗ 
'Aw Kālladhī Marra `Alá Qaryatin Wa Hiya Khāwiyatun `Alá `Urūshihā Qāla 'Anná Yuĥyī Hadhihi Al-Lahu Ba`da Mawtihā  ۖ  Fa'amātahu Al-Lahu Miā'ata `Āmin Thumma Ba`athahu  ۖ  Qāla Kam Labithta  ۖ  Qāla Labithtu Yawmāan 'Aw Ba`đa Yawmin  ۖ  Qāla Bal Labithta Miā'ata `Āminnžur 'Ilá Ţa`āmika Wa Sharābika Lam Yatasannah  ۖ  Wa Anžur 'Ilá Ĥimārika Wa Linaj`alaka 'Āyatan Lilnnāsi  ۖ  Wa Anžur 'Ilá Al-`Ižāmi Kayfa Nunshizuhā Thumma Naksūhā Laĥmāan  ۚ  Falammā Tabayyana Lahu Qāla 'A`lamu 'Anna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 002-259 Kõ kuwa wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne."  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۚ 
Wa 'Idh Qāla 'Ibrāhīmu Rabbi 'Arinī Kayfa Tuĥyī Al-Mawtá  ۖ  Qāla 'Awalam Tu'umin  ۖ  Qāla Balá Wa Lakin Liyaţma'inna Qalbī  ۖ  Qāla Fakhudh 'Arba`atan Mina Aţ-Ţayri Faşurhunna 'Ilayka Thumma Aj`al `Alá Kulli Jabalin Minhunna Juz'āan Thumma Ad`uhunna Ya'tīnaka Sa`yāan  ۚ  Wa A`lam 'Anna Al-Laha `Azīzun Ĥakīmun 002-260 Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani."  ۖ   ۖ   ۖ   ۚ 
Mathalu Al-Ladhīna Yunfiqūna 'Amwālahum Fī Sabīli Al-Lahi Kamathali Ĥabbatin 'Anbatat Sab`a Sanābila Fī Kulli Sunbulatin Miā'atu Ĥabbatin Wa  ۗ  Allāhu Yuđā`ifu Liman Yashā'u Wa  ۗ  Allāhu Wāsi`un `Alīmun 002-261 Sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, kamar sifar ƙwãyã ce wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kõwace zangarniya akwai ƙwãya ɗari. Kuma Allah Yana riɓinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani.  ۗ   ۗ 
Al-Ladhīna Yunfiqūna 'Amwālahum Fī Sabīli Al-Lahi Thumma Lā Yutbi`ūna Mā 'Anfaqū Mannāan Wa Lā 'Adháan  ۙ  Lahum 'Ajruhum `Inda Rabbihim Wa Lā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 002-262 Waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, sa'an nan kuma bã su biyar wa abin da suka ciyar ɗin da gõri, ko cũta, suna da sakamakonsu a wurin ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.  ۙ 
Qawlun Ma`rūfun Wa Maghfiratun Khayrun Min Şadaqatin Yatba`uhā 'Adháan Wa  ۗ  Allāhu Ghanīyun Ĥalīmun 002-263 Magana mai kyau da gãfartawa su ne mafi alhẽri daga sadaka wadda wata cũtarwa take biyar ta. Kuma Allah Wadatacce ne, Mai haƙuri.  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tubţilū Şadaqātikum Bil-Manni Wa Al-'Adhá Kālladhī Yunfiqu Mālahu Ri'ā'a An-Nāsi Wa Lā Yu'uminu Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri  ۖ  Famathaluhu Kamathali Şafwānin `Alayhi Turābun Fa'aşābahu Wa Abilun Fatarakahu Şaldāan  ۖ  Lā Yaqdirūna `Alá Shay'in Mimmā Kasabū Wa  ۗ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Al-Kāfirīna 002-264 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ɓãta sadakõkinku da gõri da cũtarwa, kamar wanda yake ciyar da dũkiyarsa dõmin nũna wa mutãne, kuma bã ya yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. To, abin da yake misãlinsa, kamar falalen dũtse ne, a kansa akwai turɓãya, sai wãbilin hadari ya sãme shi, sai ya bar shi ƙanƙara. Bã su iya amfani da kõme daga abin da suka sanã'anta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.  ۖ   ۖ   ۗ 
Wa Mathalu Al-Ladhīna Yunfiqūna 'Amwālahumu Abtighā'a Marđāati Al-Lahi Wa Tathbītāan Min 'Anfusihim Kamathali Jannatin Birabwatin 'Aşābahā Wa Abilun Fa'ātat 'Ukulahā Đi`fayni Fa'in Lam Yuşibhā Wa Abilun Faţallun Wa  ۗ  Allāhu Bimā Ta`malūna Başīrun 002-265 Kuma sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyarsu dõmin nẽman yardõjin Allah, kuma da tabbatarwa daga kansu, kamar misãlin lambu ne a jigãwa wadda wãbilin hadari ya sãmu, sai ta bãyar da amfãninta ninki biyu To, idan wãbili bai sãme ta ba, sai yayyafi (ya ishe ta). Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne.  ۗ 
'Ayawaddu 'Aĥadukum 'An Takūna Lahu Jannatun Min Nakhīlin Wa 'A`nābin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Lahu Fīhā Min Kulli Ath-Thamarāti Wa 'Aşābahu Al-Kibaru Wa Lahu Dhurrīyatun Đu`afā'u Fa'aşābahā 'I`şārun Fīhi Nārun Fāĥtaraqat  ۗ  Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu Lakumu Al-'Āyāti La`allakum Tatafakkarūna 002-266 Shin ɗayanku nã son cẽwa wani lambu ya kasance a gare shi daga dabĩnai da inabõbi' marẽmari suna gudãna daga ƙarƙashinsa, yana da, a cikinsa daga kõwane 'ya'yan itãce, kuma tsũfa ya sãme shi, alhãli kuwa yana da zũriyya masu rauni sai gũguwa wadda take a cikinta akwai wuta, ta sãme shi, har ta ƙõne? Kamar wancan ne Allah Yana bayyanãwar ãyõyi a gare ku, tsammãninku kuna tunãni.  ۗ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Anfiqū Min Ţayyibāti Mā Kasabtum Wa Mimmā 'Akhrajnā Lakum Mina Al-'Arđi  ۖ  Wa Lā Tayammamū Al-Khabītha Minhu Tunfiqūna Wa Lastum Bi'ākhidhīhi 'Illā 'An Tughmiđū Fīhi  ۚ  Wa A`lamū 'Anna Al-Laha Ghanīyun Ĥamīdun 002-267 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sanã'anta, kuma daga abin da Muka fitar sabõda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhãli kuwa ba ku zama mãsu karɓarsa ba fãce kun runtse ido a cikinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mawadãci ne, Gõdadde.  ۖ  ~  ۚ 
Ash-Shayţānu Ya`idukumu Al-Faqra Wa Ya'murukum Bil-Faĥshā'i Wa  ۖ  Allāhu Ya`idukum Maghfiratan Minhu Wa Fađlāan Wa  ۗ  Allāhu Wāsi`un `Alīmun 002-268 Shaiɗan yana yi muku alƙawarin talauci, kuma yana umurnin ku da alfasha, kuma Allah Yana yi muku alƙawarin gãfara daga gare shi da ƙãri, kuma Allah Mawadãci ne, Masani.  ۖ   ۗ 
Yu'utī Al-Ĥikmata Man Yashā'u  ۚ  Wa Man Yu'uta Al-Ĥikmata Faqad 'Ūtiya Khayrāan Kathīrāan  ۗ  Wa Mā Yadhdhakkaru 'Illā 'Ū Al-'Albābi 002-269 Yana bãyar da hikima (ga fahimtar gaskiyar abubuwa) ga wanda Yake so. Kuma wanda aka bai wa hikima to lalle ne an bã shi alhẽri mai yawa. Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abuta hankula.  ۚ   ۗ 
Wa Mā 'Anfaqtum Min Nafaqatin 'Aw Nadhartum Min Nadhrin Fa'inna Al-Laha Ya`lamuhu  ۗ  Wa Mā Lilžžālimīna Min 'Anşārin 002-270 Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, kõ kuka cika alwãshi daga wani bãkance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzãlumai bã su da wasu mataimaka.  ۗ 
'In Tub Aş-Şadaqāti Fani`immā Hiya  ۖ  Wa 'In Tukhfūhā Wa Tu'utūhā Al-Fuqarā'a Fahuwa Khayrun Lakum  ۚ  Wa Yukaffiru `Ankum Min Sayyi'ātikum Wa  ۗ  Allāhu Bimā Ta`malūna Khabīrun 002-271 Idan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.  ۖ   ۚ   ۗ 
Laysa `Alayka Hudāhum Wa Lakinna Al-Laha Yahdī Man Yashā'u  ۗ  Wa Mā Tunfiqū Min Khayrin Fali'anfusikum  ۚ  Wa Mā Tunfiqūna 'Illā Abtighā'a Wajhi Al-Lahi Wa Mā  ۚ  Tunfiqū Min Khayrin Yuwaffa 'Ilaykum Wa 'Antum Lā Tužlamūna 002-272 Shiryar da su bã ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, dõmin kanku ne, kuma bã ku ciyarwa, fãce dõmin nẽman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alhẽri zã a cika lãdarsa zuwa gare ku, alhãli kuwa kũ bã a zãluntarku.  ۗ   ۚ   ۚ 
Lilfuqarā'i Al-Ladhīna 'Uĥşirū Fī Sabīli Al-Lahi Lā Yastaţī`ūna Đarbāan Al-'Arđi Yaĥsabuhumu Al-Jāhilu 'Aghniyā'a Mina At-Ta`affufi Ta`rifuhum Bisīmāhum Lā Yas'alūna An-Nāsa 'Ilĥāfāan  ۗ  Wa Mā Tunfiqū Min Khayrin Fa'inna Al-Laha Bihi `Alīmun 002-273 (Ciyarwar a yĩ ta) ga matalautan nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne.  ۗ 
Al-Ladhīna Yunfiqūna 'Amwālahum Bil-Layli Wa An-Nahāri Sirrāan Wa `Alāniyatan Falahum 'Ajruhum `Inda Rabbihim Wa Lā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 002-274 Waɗanda suke ciyar da dukiyõyinsu, a dare da yini, ɓõye da bayyane, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu. Kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.
Al-Ladhīna Ya'kulūna Ar-Ribā Lā Yaqūmūna 'Illā Kamā Yaqūmu Al-Ladhī Yatakhabbaţuhu Ash-Shayţānu Mina Al-Massi  ۚ  Dhālika Bi'annahum Qālū 'Innamā Al-Bay`u Mithlu Ar-Ribā  ۗ  Wa 'Aĥalla Al-Lahu Al-Bay`a Wa Ĥarrama Ar-Ribā  ۚ  Faman Jā'ahu Maw`ižatun Min Rabbihi Fāntahá Falahu Mā Salafa Wa 'Amruhu 'Ilá Al-Lahi  ۖ  Wa Man `Āda Fa'ūlā'ika 'Aşĥābu An-Nāri  ۖ  Hum Fīhā Khālidūna 002-275 Wadanda suke cin ribã ba su tashi, fãce kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: "Ciniki kamar riba yake."Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah.Kuma wanda ya kõma,to,waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.  ۚ   ۗ   ۚ  ~  ۖ   ۖ 
Yamĥaqu Al-Lahu Ar-Ribā Wa Yurbī Aş-Şadaqāti Wa  ۗ  Allāhu Lā Yuĥibbu Kulla Kaffārin 'Athīmin 002-276 Allah Yana shãfe albarkar riba, kuma Yana ƙãra sadakõki. Kuma Allah bã Ya son dukan mai yawan kãfirci, mai zunubi.  ۗ 
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Wa 'Aqāmū Aş-Şalāata Wa 'Ātaw Az-Zakāata Lahum 'Ajruhum `Inda Rabbihim Wa Lā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna 002-277 Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Attaqū Al-Laha Wa Dharū Mā Baqiya Mina Ar-Ribā 'In Kuntum Mu'uminīna 002-278 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance mãsu ĩmãni.
Fa'in Lam Taf`alū Fa'dhanū Biĥarbin Mina Al-Lahi Wa Rasūlihi  ۖ  Wa 'In Tubtum Falakum Ru'ūsu 'Amwālikum Lā Tažlimūna Wa Lā Tužlamūna 002-279 To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yãƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tũba to kuna da asalin dũkiyõyinku, bã ku zãlunta, kuma bã a zãluntar ku.  ۖ 
Wa 'In Kāna Dhū `Usratin Fanažiratun 'Ilá Maysaratin  ۚ  Wa 'An Taşaddaqū Khayrun Lakum  ۖ  'In Kuntum Ta`lamūna 002-280 Kuma idan ma'abucin wahala ya kasance (mawahalci) to, jinkirtãwa ake yi zuwa ga sauƙin al'amarinsa, kuma dã kun yi sadaka, shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kuna sani.  ۚ   ۖ 
Wa Attaqū Yawmāan Turja`ūna Fīhi 'Ilá Al-Lahi  ۖ  Thumma Tuwaffá Kullu Nafsin Mā Kasabat Wa Hum Lā Yužlamūna 002-281 Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su. ~  ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Tadāyantum Bidaynin 'Ilá 'Ajalin Musammáan Fāktubūhu  ۚ  Wa Līaktub Baynakum Kātibun Bil-`Adli  ۚ  Wa Lā Ya'ba Kātibun 'An Yaktuba Kamā `Allamahu Al-Lahu  ۚ  Falyaktub Wa Līumlili Al-Ladhī `Alayhi Al-Ĥaqqu Wa Līattaqi Al-Laha Rabbahu Wa Lā Yabkhas Minhu Shay'āan  ۚ  Fa'in Kāna Al-Ladhī `Alayhi Al-Ĥaqqu Safīhāan 'Aw Đa`īfāan 'Aw Lā Yastaţī`u 'An Yumilla Huwa Falyumlil Walīyuhu Bil-`Adli  ۚ  Wa Astash/hidū Shahīdayni Min Rijālikum  ۖ  Fa'in Lam Yakūnā Rajulayni Farajulun Wa Amra'atāni Mimman Tarđawna Mina Ash-Shuhadā'i 'An Tađilla 'Iĥdāhumā Fatudhakkira 'Iĥdāhumā Al-'Ukhrá  ۚ  Wa Lā Ya'ba Ash-Shuhadā'u 'Idhā Mā Du`ū  ۚ  Wa Lā Tas'amū 'An Taktubūhu Şaghīrāan 'Aw Kabīrāan 'Ilá 'Ajalihi  ۚ  Dhālikum 'Aqsaţu `Inda Al-Lahi Wa 'Aqwamu Lilshshahādati Wa 'Adná 'Allā Tartābū  ۖ  'Illā 'An Takūna Tijāratan Ĥāđiratan Tudīrūnahā Baynakum Falaysa `Alaykum Junāĥun 'Allā Taktubūhā  ۗ  Wa 'Ash/hidū 'Idhā Tabāya`tum  ۚ  Wa Lā Yuđārra Kātibun Wa Lā Shahīdun  ۚ  Wa 'In Taf`alū Fa'innahu Fusūqun Bikum  ۗ  Wa Attaqū Al-Laha  ۖ  Wa Yu`allimukumu Al-Lahu Wa  ۗ  Allāhu Bikulli Shay'in `Alīmun 002-282 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta. Kuma wanda bãshin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsõron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bãshin yake a kansa yã kasance wãwã ne kõ kuwa rarrauna, kõ kuwa shi bã ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da ãdalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mãtã biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun dõmin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazãkũtar da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙõsa ga rubũta shi, ƙarami ya kasance kõ babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi ãdalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gẽwayarwa da shi hannu da hannu a tsakãninku to bãbu laifi a kanku, ya zama ba ku rubũta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fãsiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kõme Masani ne.  ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۚ   ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۖ   ۗ   ۚ   ۚ   ۗ   ۖ   ۗ 
Wa 'In Kuntum `Alá Safarin Wa Lam Tjidū Kātibāan Farihānun Maqbūđatun  ۖ  Fa'in 'Amina Ba`đukum Ba`đāan Falyu'uaddi Al-Ladhī A'utumina 'Amānatahu Wa Līattaqi Al-Laha Rabbahu  ۗ  Wa Lā Taktumū Ash-Shahādata  ۚ  Wa Man Yaktumhā Fa'innahu 'Āthimun Qalbuhu Wa  ۗ  Allāhu Bimā Ta`malūna `Alīmun 002-283 Kuma idan kun kasance a kan tafiya, kuma ba ku sami marubũci ba, to, a bãyar da jingina karɓaɓɓiya (ga hannu). To, idan sãshenku ya amince wa sãshe, to, wanda aka amincẽ wannan sai ya bãyar da amãnarsa, kuma ya bi Allah, Ubangijinsa, da taƙawa. Kuma kada ku ɓõye shaida, kuma wanda ya ɓõye ta, to, shi mai zunubin zũciyarsa ne. KumaAllah ga abin da kuke aikatãwa Masani ne.  ۖ   ۗ   ۚ   ۗ 
Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۗ  Wa 'In Tubdū Mā Fī 'Anfusikum 'Aw Tukhfūhu Yuĥāsibkum Bihi Al-Lahu  ۖ  Fayaghfiru Liman Yashā'u Wa Yu`adhdhibu Man Yashā'u Wa  ۗ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun 002-284 Allah ne, da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma idan kun bayyana abin da yake a cikin zukatanku (na shaida), ko kuka ɓõye shi, Allah zai bincike ku da shi, sa'an nan Ya yi gãfara ga wanda Yake so, kuma Ya azabta wanda Yake so. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.  ۗ   ۖ   ۗ 
'Āmana Ar-Rasūlu Bimā 'Unzila 'Ilayhi Min Rabbihi Wa Al-Mu'uminūna  ۚ  Kullun 'Āmana Bil-Lahi Wa Malā'ikatihi Wa Kutubihi Wa Rusulihi Lā Nufarriqu Bayna 'Aĥadin Min Rusulihi  ۚ  Wa Qālū Sami`nā Wa 'Aţa`nā  ۖ  Ghufrānaka Rabbanā Wa 'Ilayka Al-Maşīru 002-285 Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take "  ۚ   ۚ   ۖ 
Lā Yukallifu Al-Lahu Nafsāan 'Illā Wus`ahā  ۚ  Lahā Mā Kasabat Wa `Alayhā Mā Aktasabat  ۗ  Rabbanā Lā Tu'uākhidhnā 'In Nasīnā 'Aw 'Akhţa'nā  ۚ  Rabbanā Wa Lā Taĥmil `Alaynā 'Işrāan Kamā Ĥamaltahu `Alá Al-Ladhīna Min Qablinā  ۚ  Rabbanā Wa Lā Tuĥammilnā Mā Lā Ţāqata Lanā Bihi  ۖ  Wa A`fu `Annā Wa Aghfir Lanā Wa Arĥamnā  ۚ  'Anta Mawlānā Fānşurnā `Alá Al-Qawmi Al-Kāfirīna 002-286 Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."  ۚ   ۗ   ۚ   ۚ   ۖ   ۚ 
Next Sūrah