37) Sūrat Aş-Şāffāt

Printed format

37) سُورَة الصَّافَّات

Wa Aş-Şāffāti Şaffāan َ037-001 Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi). وَالصَّافَّاتِ صَفّا ً
Fālzzājirāti Zajan َ037-002 Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi. فَالزَّاجِرَاتِ زَجْرا ً
Fālttāliyāti Dhikrāan َ037-003 Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa. فَالتَّالِيَاتِ ذِكْرا ً
'Inna 'Ilahakum Lawāĥidun َ037-004 Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne. إِنَّ إِلَهَكُمْ لَوَاحِد ٌ
Rabbu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā Wa Rabbu Al-Mashāriqi َ037-005 Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã. رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ الْمَشَارِقِ
'Innā Zayyannā As-Samā'a Ad-Dunyā Bizīnatin Al-Kawākib َ037-006 Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri. إِنَّا زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِزِينَة ٍ الْكَوَاكِب
Wa Ĥifžāan Min Kulli Shayţāninridin َ037-007 Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai. وَحِفْظا ً مِنْ كُلِّ شَيْطَان ٍ مَارِد ٍ
Lā Yassamma`ūna 'Ilá Al-Mala'i Al-'A`lá Wa Yuqdhafūna Min Kulli Jānibin َ037-008 Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe. لاَ يَسَّمَّعُونَ إِلَى الْمَلَإِ الأَعْلَى وَيُقْذَفُونَ مِنْ كُلِّ جَانِب ٍ
Duĥūrāan  ۖ  Wa Lahum `Adhābun Wa Aşibun َ037-009 Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya. دُحُورا ً  ۖ  وَلَهُمْ عَذَاب ٌ وَاصِب ٌ
'Illā Man Khaţifa Al-Khaţfata Fa'atba`ahu Shihābun Thāqibāun َ037-010 Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi. إِلاَّ مَنْ خَطِفَ الْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَه ُُ شِهَاب ٌ ثَاقِبا ٌ
Fāstaftihim 'Ahum 'Ashaddu Khalqāan 'Am Man Khalaqnā  ۚ  'Innā Khalaqnāhum Min Ţīnin Lāzibin َ037-011 Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri. فَاسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقاً أَمْ مَنْ خَلَقْنَا  ۚ  إِنَّا خَلَقْنَاهُمْ مِنْ طِين ٍ لاَزِب ٍ
Bal `Ajibta Wa Yaskharūna َ037-012 Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili. بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَ
Wa 'Idhā Dhukkirū Lā Yadhkurūna َ037-013 Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa. وَإِذَا ذُكِّرُوا لاَ يَذْكُرُونَ
Wa 'Idhā Ra'aw 'Āyatan Yastaskhirūna َ037-014 Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili. وَإِذَا رَأَوْا آيَة ً يَسْتَسْخِرُونَ
Wa Qālū 'In Hādhā 'Illā Siĥrun Mubīnun َ037-015 Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne." وَقَالُوا إِنْ هَذَا إِلاَّ سِحْر ٌ مُبِين ٌ
'A'idhā Mitnā Wa Kunnā Turābāan Wa `Ižāmāan 'A'innā Lamabthūna َ037-016 "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa,ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابا ً وَعِظَاماً أَئِنَّا لَمَبْعُوثُونَ
'Awa'ābā'uunā Al-'Awwalūna َ037-017 "Ashe kõ da ubanninmu na farko?" أَوَآبَاؤُنَا الأَوَّلُونَ
Qul Na`am Wa 'Antumkhirūna َ037-018 Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu." قُلْ نَعَمْ وَأَنْتُمْ دَاخِرُونَ
Fa'innamā Hiya Zajratun Wāĥidatun Fa'idhā Hum Yanžurūna َ037-019 Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi. فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَة ٌ وَاحِدَة ٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَ
Wa Qālū Yā Waylanā Hādhā Yawmu Ad-Dīni َ037-020 Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako." وَقَالُوا يَاوَيْلَنَا هَذَا يَوْمُ الدِّينِ
dhā Yawmu Al-Faşli Al-Ladhī Kuntum Bihi Tukadhdhibūna َ037-021 Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa. هَذَا يَوْمُ الْفَصْلِ الَّذِي كُنتُمْ بِه ِِ تُكَذِّبُونَ
Aĥshurū Al-Ladhīna Žalamū Wa 'Azwājahum Wa Mā Kānū Ya`budūna َ037-022 Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa. احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأَزْوَاجَهُمْ وَمَا كَانُوا يَعْبُدُونَ
Min Dūni Al-Lahi Fāhdūhum 'Ilá Şirāţi Al-Jaĥīmi َ037-023 Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm. مِنْ دُونِ اللَّهِ فَاهْدُوهُمْ إِلَى صِرَاطِ الْجَحِيمِ
Wa Qifūhum  ۖ  'Innahum Mas'ūlūna َ037-024 Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne. وَقِفُوهُمْ  ۖ  إِنَّهُمْ مَسْئُولُونَ
Mā Lakum Lā Tanāşarūna َ037-025 Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna? مَا لَكُمْ لاَ تَنَاصَرُونَ
Bal Humu Al-Yawma Mustaslimūna َ037-026 Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne. بَلْ هُمُ الْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَ
Wa 'Aqbala Ba`đuhum `Alá Ba`đin Yatasā'alūna َ037-027 Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna. وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْض ٍ يَتَسَاءَلُونَ
Qālū 'Innakum Kuntum Ta'tūnanā `Ani Al-Yamīni َ037-028 Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)." قَالُوا إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ الْيَمِينِ
Qālū Bal Lam Takūnū Mu'uminīna َ037-029 Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba. قَالُوا بَلْ لَمْ تَكُونُوا مُؤْمِنِينَ
Wa Mā Kāna Lanā `Alaykum Min Sulţānin  ۖ  Bal Kuntum Qawmāan Ţāghīna َ037-030 "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka." وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُمْ مِنْ سُلْطَان ٍ  ۖ  بَلْ كُنتُمْ قَوْما ً طَاغِينَ
Faĥaqqa `Alaynā Qawlu Rabbinā  ۖ  'Innā Ladhā'iqūna َ037-031 "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne." فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَا  ۖ  إِنَّا لَذَائِقُونَ
Fa'aghwaynākum 'Innā Kunnā Ghāwīna َ037-032 "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu." فَأَغْوَيْنَاكُمْ إِنَّا كُنَّا غَاوِينَ
Fa'innahum Yawma'idhin Al-`Adhābi Mushtarikūna َ037-033 To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar. فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذ ٍ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ
'Innā Kadhālika Naf`alu Bil-Mujrimīna َ037-034 Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi. إِنَّا كَذَلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ
'Innahum Kānū 'Idhā Qīla Lahum Lā 'Ilāha 'Illā Al-Lahu Yastakbirūna َ037-035 Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai. إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ
Wa Yaqūlūna 'A'innā Latārikū 'Ālihatinā Lishā`irin Majnūnin َ037-036 Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci? وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوا آلِهَتِنَا لِشَاعِر ٍ مَجْنُون ٍ
Bal Jā'a Bil-Ĥaqqi Wa Şaddaqa Al-Mursalīna َ037-037 Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni. بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَ
'Innakum Ladhā'iqū Al-`Adhābi Al-'Alīmi َ037-038 Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne. إِنَّكُمْ لَذَائِقُو الْعَذَابِ الأَلِيمِ
Wa Mā Tujzawna 'Illā Mā Kuntum Ta`malūna َ037-039 Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. وَمَا تُجْزَوْنَ إِلاَّ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
'Illā `Ibāda Al-Lahi Al-Mukhlaşīna َ037-040 Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. إِلاَّ عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ
'Ūlā'ika Lahum Rizqun Ma`lūmun َ037-041 Waɗannan sunã da abinci sananne. أُوْلَائِكَ لَهُمْ رِزْق ٌ مَعْلُوم ٌ
Fawākihu  ۖ  Wa Hum Mukramūna َ037-042 'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa. فَوَاكِه ُُ  ۖ  وَهُمْ مُكْرَمُونَ
Fī Jannāti An-Na`īmi َ037-043 A cikin gidãjen Aljannar ni'ima. فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ
`Alá Sururin Mutaqābilīna َ037-044 A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna. عَلَى سُرُر ٍ مُتَقَابِلِينَ
Yuţāfu `Alayhim Bika'sin Min Ma`īnin َ037-045 Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari. يُطَافُ عَلَيْهِمْ بِكَأْس ٍ مِنْ مَعِين ٍ
Bayđā'a Ladhdhatin Lilshshāribīna َ037-046 Farã mai dãɗi ga mashãyan. بَيْضَاءَ لَذَّة ٍ لِلشَّارِبِينَ
Lā Fīhā Ghawlun Wa Lā Hum `Anhā Yunzafūna َ037-047 A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba, لاَ فِيهَا غَوْل ٌ وَلاَ هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَ
Wa `Indahum Qāşirātu Aţ-Ţarfi `Īnun َ037-048 Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu. وَعِنْدَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ عِين ٌ
Ka'annahunna Bayđun Maknūnun َ037-049 Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye. كَأَنَّهُنَّ بَيْض ٌ مَكْنُون ٌ
Fa'aqbala Ba`đuhum `Alá Ba`đin Yatasā'alūna َ037-050 Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna. فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْض ٍ يَتَسَاءَلُونَ
Qāla Qā'ilun Minhum 'Innī Kāna Lī Qarīnun َ037-051 Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)." قَالَ قَائِل ٌ مِنْهُمْ إِنِّي كَانَ لِي قَرِين ٌ
Yaqūlu 'A'innaka Lamina Al-Muşaddiqīna َ037-052 Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?" يَقُولُ أَئِنَّكَ لَمِنَ الْمُصَدِّقِينَ
'A'idhā Mitnā Wa Kunnā Turābāan Wa `Ižāmāan 'A'innā Lamadīnūna َ037-053 "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?" أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابا ً وَعِظَاماً أَئِنَّا لَمَدِينُونَ
Qāla Hal 'Antum Muţţali`ūna َ037-054 (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?" قَالَ هَلْ أَنْتُمْ مُطَّلِعُونَ
Fāţţala`a Fara'āhu Fī Sawā'i Al-Jaĥīmi َ037-055 Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim. فَاطَّلَعَ فَرَآهُ فِي سَوَاءِ الْجَحِيمِ
Qāla Ta-Allāhi 'In Kidta Laturdīni َ037-056 Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni." قَالَ تَاللَّهِ إِنْ كِدْتَ لَتُرْدِينِ
Wa Lawlā Ni`matu Rabbī Lakuntu Mina Al-Muĥđarīna َ037-057 "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)." وَلَوْلاَ نِعْمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ الْمُحْضَرِينَ
'Afamā Naĥnu Bimayyitīna َ037-058 "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba." أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ
'Illā Mawtatanā Al-'Ūlá Wa Mā Naĥnu Bimu`adhdhabīna َ037-059 "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?" إِلاَّ مَوْتَتَنَا الأُولَى وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ
'Inna Hādhā Lahuwa Al-Fawzu Al-`Ažīmu َ037-060 Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma. إِنَّ هَذَا لَهُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Limithli Hādhā Falya`mali Al-`Āmilūna َ037-061 Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa. لِمِثْلِ هَذَا فَلْيَعْمَلِ الْعَامِلُونَ
'Adhalika Khayrun Nuzulāan 'Am Shajaratu Az-Zaqqūmi َ037-062 Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm? أَذَلِكَ خَيْر ٌ نُزُلاً أَمْ شَجَرَةُ الزَّقُّومِ
'Innā Ja`alnāhā Fitnatan Lilžžālimīna َ037-063 Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai. إِنَّا جَعَلْنَاهَا فِتْنَة ً لِلظَّالِمِينَ
'Innahā Shajaratun Takhruju Fī 'Aşli Al-Jaĥīmi َ037-064 Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm. إِنَّهَا شَجَرَة ٌ تَخْرُجُ فِي أَصْلِ الْجَحِيمِ
Ţal`uhā Ka'annahu Ru'ūsu Ash-Shayāţīni َ037-065 Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne. طَلْعُهَا كَأَنَّه ُُ رُءُوسُ الشَّيَاطِينِ
Fa'innahum La'ākilūna Minhā Famāli'ūna Minhā Al-Buţūna َ037-066 To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta. فَإِنَّهُمْ لَآكِلُونَ مِنْهَا فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ
Thumma 'Inna Lahum `Alayhā Lashawbāan Min Ĥamīmin َ037-067 Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi. ثُمَّ إِنَّ لَهُمْ عَلَيْهَا لَشَوْبا ً مِنْ حَمِيم ٍ
Thumma 'Inna Marji`ahum La'ilá Al-Jaĥīmi َ037-068 Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take. ثُمَّ إِنَّ مَرْجِعَهُمْ لَإِلَى الْجَحِيمِ
'Innahum 'Alfaw 'Ābā'ahum Đāllīna َ037-069 Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu. إِنَّهُمْ أَلْفَوْا آبَاءَهُمْ ضَالِّينَ
Fahum `Alá 'Āthārihim Yuhra`ūna َ037-070 Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa. فَهُمْ عَلَى آثَارِهِمْ يُهْرَعُونَ
Wa Laqad Đalla Qablahum 'Aktharu Al-'Awwalīna َ037-071 Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu. وَلَقَدْ ضَلَّ قَبْلَهُمْ أَكْثَرُ الأَوَّلِينَ
Wa Laqad 'Arsalnā Fīhim Mundhirīna َ037-072 Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا فِيهِمْ مُنذِرِينَ
nžur Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mundharīna َ037-073 Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance. فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُنذَرِينَ
'Illā `Ibāda Al-Lahi Al-Mukhlaşīna َ037-074 Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. إِلاَّ عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ
Wa Laqad Nādānā Nūĥun Falani`ma Al-Mujībūna َ037-075 Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu. وَلَقَدْ نَادَانَا نُوح ٌ فَلَنِعْمَ الْمُجِيبُونَ
Wa Najjaynāhu Wa 'Ahlahu Mina Al-Karbi Al-`Ažīmi َ037-076 Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba. وَنَجَّيْنَاه ُُ وَأَهْلَه ُُ مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ
Wa Ja`alnā Dhurrīyatahu Humu Al-Bāqīna َ037-077 Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa. وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَه ُُ هُمُ الْبَاقِينَ
Wa Taraknā `Alayhi Fī Al-'Ākhirīna َ037-078 Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe. وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الآخِرِينَ
Salāmun `Alá Nūĥin Al-`Ālamīna َ037-079 Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu. سَلاَمٌ عَلَى نُوح ٍ فِي الْعَالَمِينَ
'Innā Kadhālika Naj Al-Muĥsinīna َ037-080 Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
'Innahu Min `Ibādinā Al-Mu'uminīna َ037-081 Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai. إِنَّه ُُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ
Thumma 'Aghraq Al-'Ākharīna َ037-082 Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu. ثُمَّ أَغْرَقْنَا الآخَرِينَ
Wa 'Inna Min Shī`atihi La'ibrāhīma َ037-083 Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake. وَإِنَّ مِنْ شِيعَتِه ِِ لَإِبْرَاهِيمَ
'Idh Jā'a Rabbahu Biqalbin Salīmin َ037-084 A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya. إِذْ جَاءَ رَبَّه ُُ بِقَلْب ٍ سَلِيم ٍ
'Idh Qāla Li'abīhi Wa Qawmihi Mādhā Ta`budūna َ037-085 A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?" إِذْ قَالَ لِأَبِيه ِِ وَقَوْمِه ِِ مَاذَا تَعْبُدُونَ
'A'ifkāan 'Ālihatan Dūna Al-Lahi Turīdūna َ037-086 "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?" أَئِفْكا ً آلِهَة ً دُونَ اللَّهِ تُرِيدُونَ
Famā Žannukum Birabbi Al-`Ālamīna َ037-087 "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?" فَمَا ظَنُّكُمْ بِرَبِّ الْعَالَمِينَ
Fanažara Nažratan An-Nujūmi َ037-088 Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri. فَنَظَرَ نَظْرَة ً فِي النُّجُومِ
Faqāla 'Innī Saqīmun َ037-089 Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." فَقَالَ إِنِّي سَقِيم ٌ
Fatawallaw `Anhu Mudbirīna َ037-090 Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. فَتَوَلَّوْا عَنْهُ مُدْبِرِينَ
Farāgha 'Ilá 'Ālihatihim Faqāla 'Alā Ta'kulūna َ037-091 Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba? فَرَاغَ إِلَى آلِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلاَ تَأْكُلُونَ
Mā Lakum Lā Tanţiqūna َ037-092 "Me ya sãme ku, bã ku magana?" مَا لَكُمْ لاَ تَنطِقُونَ
Farāgha `Alayhim Đarbāan Bil-Yamīni َ037-093 Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma. فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبا ً بِالْيَمِينِ
Fa'aqbalū 'Ilayhi Yaziffūna َ037-094 Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa. فَأَقْبَلُوا إِلَيْهِ يَزِفُّونَ
Qāla 'Ata`budūna Mā Tanĥitūna َ037-095 Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa, قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ
Wa Allāhu Khalaqakum Wa Mā Ta`malūna َ037-096 "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?" وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ
Qālū Abnū Lahu Bunyānāan Fa'alqūhu Fī Al-Jaĥīmi َ037-097 Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm." قَالُوا ابْنُوا لَه ُُ بُنْيَانا ً فَأَلْقُوه ُُ فِي الْجَحِيمِ
Fa'arādū Bihi Kaydāan Faja`alnāhumu Al-'Asfalīna َ037-098 Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci. فَأَرَادُوا بِه ِِ كَيْدا ً فَجَعَلْنَاهُمُ الأَسْفَلِينَ
Wa Qāla 'Innī Dhāhibun 'Ilá Rabbī Sayahdīni َ037-099 Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni." وَقَالَ إِنِّي ذَاهِب ٌ إِلَى رَبِّي سَيَهْدِينِ
Rabbi Hab Lī Mina Aş-Şāliĥīna َ037-100 "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne." رَبِّ هَبْ لِي مِنَ الصَّالِحِينَ
Fabashsharnāhu Bighulāmin Ĥalīmin َ037-101 Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri. فَبَشَّرْنَاه ُُ بِغُلاَمٍ حَلِيم ٍ
Falammā Balagha Ma`ahu As-Sa`ya Qāla Yā Bunayya 'Innī 'Ará Fī Al-Manāmi 'Annī 'Adhbaĥuka Fānžur Mādhā Tará  ۚ  Qāla Yā 'Abati Af`al Mā Tu'umaru  ۖ  Satajidunī 'In Shā'a Al-Lahu Mina Aş-Şābirīna َ037-102 To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri." فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ السَّعْيَ قَالَ يَابُنَيَّ إِنِّي أَرَى فِي الْمَنَامِ أَنِّي أَذْبَحُكَ فَانظُرْ مَاذَا تَرَى قَالَ  ۚ  يَا أَبَتِ افْعَلْ مَا تُؤْمَرُ سَتَجِدُنِي  ۖ  إِنْ شَاءَ اللَّهُ مِنَ الصَّابِرِينَ
Falammā 'Aslamā Wa Tallahu Liljabīni َ037-103 To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa. فَلَمَّا أَسْلَمَا وَتَلَّه ُُ لِلْجَبِينِ
Wa Nādaynāhu 'An Yā 'Ibrāhīmu َ037-104 Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!" وَنَادَيْنَاهُ~ُ أَنْ يَا إِبْرَاهِيمُ
Qad Şaddaqta Ar-Ru'uyā  ۚ  'Innā Kadhālika Naj Al-Muĥsinīna َ037-105 "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. قَد صَدَّقْتَ الرُّؤْيَا  ۚ  إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
'Inna Hādhā Lahuwa Al-Balā'u Al-Mubīnu َ037-106 Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna. إِنَّ هَذَا لَهُوَ الْبَلاَءُ الْمُبِينُ
Wa Fadaynāhu Bidhibĥin `Ažīmin َ037-107 Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma. وَفَدَيْنَاه ُُ بِذِبْحٍ عَظِيم ٍ
Wa Taraknā `Alayhi Fī Al-'Ākhirīna َ037-108 Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe. وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الآخِرِينَ
Salāmun `Alá 'Ibrāhīma َ037-109 Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm. سَلاَمٌ عَلَى إِبْرَاهِيمَ
Kadhālika Naj Al-Muĥsinīna َ037-110 Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
'Innahu Min `Ibādinā Al-Mu'uminīna َ037-111 Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. إِنَّه ُُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ
Wa Bashsharnāhu Bi'isĥāqa Nabīyāan Mina Aş-Şāliĥīna َ037-112 Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. وَبَشَّرْنَاه ُُ بِإِسْحَاقَ نَبِيّا ً مِنَ الصَّالِحِينَ
Wa Bāraknā `Alayhi Wa `Alá 'Isĥāqa  ۚ  Wa Min Dhurrīyatihimā Muĥsinun Wa Žālimun Linafsihi Mubīnun َ037-113 Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin). وَبَارَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَى إِسْحَاقَ  ۚ  وَمِنْ ذُرِّيَّتِهِمَا مُحْسِن ٌ وَظَالِم ٌ لِنَفْسِه ِِ مُبِين ٌ
Wa Laqad Manannā `Alá Mūsá Wa Hārūna َ037-114 Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna. وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَى مُوسَى وَهَارُونَ
Wa Najjaynāhumā Wa Qawmahumā Mina Al-Karbi Al-`Ažīmi َ037-115 Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma. وَنَجَّيْنَاهُمَا وَقَوْمَهُمَا مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ
Wa Naşarnāhum Fakānū Humu Al-Ghālibīna َ037-116 Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya. وَنَصَرْنَاهُمْ فَكَانُوا هُمُ الْغَالِبِينَ
Wa 'Ātaynāhumā Al-Kitāba Al-Mustabīna َ037-117 Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni. وَآتَيْنَاهُمَا الْكِتَابَ الْمُسْتَبِينَ
Wa Hadaynāhumā Aş-Şirāţa Al-Mustaqīma َ037-118 Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya. وَهَدَيْنَاهُمَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ
Wa Taraknā `Alayhimā Fī Al-'Ākhirīna َ037-119 Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe. وَتَرَكْنَا عَلَيْهِمَا فِي الآخِرِينَ
Salāmun `Alá Mūsá Wa Hārūna َ037-120 Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna. سَلاَمٌ عَلَى مُوسَى وَهَارُونَ
'Innā Kadhālika Naj Al-Muĥsinīna َ037-121 Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
'Innahumā Min `Ibādinā Al-Mu'uminīna َ037-122 Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai. إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ
Wa 'Inna 'Ilyāsa Lamina Al-Mursalīna َ037-123 Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ
'Idh Qāla Liqawmihi 'Alā Tattaqūna َ037-124 A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?" إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ~ِ أَلاَ تَتَّقُونَ
'Atad`ūna Ba`lāan Wa Tadharūna 'Aĥsana Al-Khāliqīna َ037-125 "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?" أَتَدْعُونَ بَعْلا ً وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ الْخَالِقِينَ
Al-Laha Rabbakum Wa Rabba 'Ābā'ikumu Al-'Awwalīna َ037-126 "Allah Ubangijinku,kuma Ubangijin ubanninku farko?" اللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ آبَائِكُمُ الأَوَّلِينَ
Fakadhdhabūhu Fa'innahum Lamuĥđarūna َ037-127 Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã). فَكَذَّبُوه ُُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ
'Illā `Ibāda Al-Lahi Al-Mukhlaşīna َ037-128 Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. إِلاَّ عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ
Wa Taraknā `Alayhi Fī Al-'Ākhirīna َ037-129 Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe. وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الآخِرِينَ
Salāmun `Alá 'Il Yā -Sīn َ037-130 Aminci ya tabbata ga Ilyãs. سَلاَمٌ عَلَى إِلْ يَا-سِين
'Innā Kadhālika Naj Al-Muĥsinīna َ037-131 Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
'Innahu Min `Ibādinā Al-Mu'uminīna َ037-132 Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. إِنَّه ُُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ
Wa 'Inna Lūţāan Lamina Al-Mursalīna َ037-133 Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. وَإِنَّ لُوطا ً لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ
'Idh Najjaynāhu Wa 'Ahlahu 'Ajma`īna َ037-134 A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya. إِذْ نَجَّيْنَاه ُُ وَأَهْلَهُ~ُ أَجْمَعِينَ
'Illā `Ajūzāan Al-Ghābirīna َ037-135 Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba). إِلاَّ عَجُوزا ً فِي الْغَابِرِينَ
Thumma Dammarnā Al-'Ākharīna َ037-136 Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen. ثُمَّ دَمَّرْنَا الآخَرِينَ
Wa 'Innakum Latamurrūna `Alayhim Muşbiĥīna َ037-137 Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci. وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِمْ مُصْبِحِينَ
Wa Bil-Layli  ۗ  'Afalā Ta`qilūna َ037-138 Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba? وَبِاللَّيْلِ  ۗ  أَفَلاَ تَعْقِلُونَ
Wa 'Inna Yūnis Lamina Al-Mursalīna َ037-139 Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. وَإِنَّ يُونِس لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ
'Idh 'Abaqa 'Ilá Al-Fulki Al-Mashĥūni َ037-140 A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi. إِذْ أَبَقَ إِلَى الْفُلْكِ الْمَشْحُونِ
Fasāhama Fakāna Mina Al-Mudĥađīna َ037-141 Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya. فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ الْمُدْحَضِينَ
Fāltaqamahu Al-Ĥūtu Wa Huwa Mulīmun َ037-142 Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. فَالْتَقَمَهُ الْحُوتُ وَهُوَ مُلِيم ٌ
Falawlā 'Annahu Kāna Mina Al-Musabbiĥīna َ037-143 To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba, فَلَوْلاَ أَنَّه ُُ كَانَ مِنَ الْمُسَبِّحِينَ
Lalabitha Fī Baţnihi 'Ilá Yawmi Yub`athūna َ037-144 Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su. لَلَبِثَ فِي بَطْنِهِ~ِ إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Fanabadhnāhu Bil-`Arā'i Wa Huwa Saqīmun َ037-145 Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya. فَنَبَذْنَاه ُُ بِالْعَرَاءِ وَهُوَ سَقِيم ٌ
Wa 'Anbatnā `Alayhi Shajaratan Min Yaqţīnin َ037-146 Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi. وَأَنْبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَة ً مِنْ يَقْطِين ٍ
Wa 'Arsalnāhu 'Ilá Miā'ati 'Alfin 'Aw Yazīdūna َ037-147 Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka). وَأَرْسَلْنَاهُ~ُ إِلَى مِائَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَ
Fa'āmanū Famatta`nāhum 'Ilá Ĥīnin َ037-148 Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci. فَآمَنُوا فَمَتَّعْنَاهُمْ إِلَى حِين ٍ
Fāstaftihim 'Alirabbika Al-Banātu Wa Lahumu Al-Banūna َ037-149 Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?" فَاسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ الْبَنَاتُ وَلَهُمُ الْبَنُونَ
'Am Khalaq Al-Malā'ikata 'Ināthāan Wa Hum Shāhidūna َ037-150 Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce? أَمْ خَلَقْنَا الْمَلاَئِكَةَ إِنَاثا ً وَهُمْ شَاهِدُونَ
'Alā 'Innahum Min 'Ifkihim Layaqūlūna َ037-151 To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa. أَلاَ إِنَّهُمْ مِنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَ
Walada Al-Lahu Wa 'Innahum Lakādhibūna َ037-152 "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne. وَلَدَ اللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ
'Āşţafá Al-Banāti `Alá Al-Banīna َ037-153 Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza? أَاصْطَفَى الْبَنَاتِ عَلَى الْبَنِينَ
Mā Lakum Kayfa Taĥkumūna َ037-154 Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)? مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ
'Afalā Tadhakkarūn َ037-155 Shin, bã ku tunãni? أَفَلاَ تَذَكَّرُون
'Am Lakum Sulţānun Mubīnun َ037-156 Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne? أَمْ لَكُمْ سُلْطَان ٌ مُبِين ٌ
Fa'tū Bikitābikum 'In Kuntum Şādiqīna َ037-157 To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya. فَأْتُوا بِكِتَابِكُمْ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ
Wa Ja`alū Baynahu Wa Bayna Al-Jinnati Nasabāan  ۚ  Wa Laqad `Alimati Al-Jinnatu 'Innahum Lamuĥđarūna َ037-158 Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)" وَجَعَلُوا بَيْنَه ُُ وَبَيْنَ الْجِنَّةِ نَسَبا ً  ۚ  وَلَقَدْ عَلِمَتِ الْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ
Subĥāna Al-Lahi `Ammā Yaşifūna َ037-159 Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa. سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
'Illā `Ibāda Al-Lahi Al-Mukhlaşīna َ037-160 Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. إِلاَّ عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ
Fa'innakum Wa Mā Ta`budūna َ037-161 To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa, فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ
Mā 'Antum `Alayhi Bifātinīna َ037-162 Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi. مَا أَنْتُمْ عَلَيْهِ بِفَاتِنِينَ
'Illā Man Huwa Şālī Al-Jaĥīmi َ037-163 Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm. إِلاَّ مَنْ هُوَ صَالِي الْجَحِيمِ
Wa Mā Minnā 'Illā Lahu Maqāmun Ma`lūmun َ037-164 "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne." وَمَا مِنَّا إِلاَّ لَه ُُ مَقَام ٌ مَعْلُوم ٌ
Wa 'Innā Lanaĥnu Aş-Şāffūna َ037-165 "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)." وَإِنَّا لَنَحْنُ الصَّافُّونَ
Wa 'Innā Lanaĥnu Al-Musabbiĥūna َ037-166 "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi." وَإِنَّا لَنَحْنُ الْمُسَبِّحُونَ
Wa 'In Kānū Layaqūlūna َ037-167 Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa, وَإِنْ كَانُوا لَيَقُولُونَ
Law 'Anna `Indanā Dhikrāan Mina Al-'Awwalīna َ037-168 "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko." لَوْ أَنَّ عِنْدَنَا ذِكْرا ً مِنَ الأَوَّلِينَ
Lakunnā `Ibāda Al-Lahi Al-Mukhlaşīna َ037-169 "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake." لَكُنَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ
Fakafarū Bihi  ۖ  Fasawfa Ya`lamūna َ037-170 Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani. فَكَفَرُوا بِه ِِ  ۖ  فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Wa Laqad Sabaqat Kalimatunā Li`ibādinā Al-Mursalīn َ037-171 Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni. وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا الْمُرْسَلِين
'Innahum Lahumu Al-Manşūrūna َ037-172 Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako. إِنَّهُمْ لَهُمُ الْمَنصُورُونَ
Wa 'Inna Jundanā Lahumu Al-Ghālibūna َ037-173 Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya. وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ الْغَالِبُونَ
Fatawalla `Anhum Ĥattá Ĥīnin َ037-174 Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci. فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّى حِين ٍ
Wa 'Abşirhum Fasawfa Yubşirūna َ037-175 Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani. وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ
'Afabi`adhābinā Yasta`jilūna َ037-176 Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa? أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ
Fa'idhā Nazala Bisāĥatihim Fasā'a Şabāĥu Al-Mundharīna َ037-177 To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana. فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَاءَ صَبَاحُ الْمُنذَرِينَ
Wa Tawalla `Anhum Ĥattá Ĥīnin َ037-178 Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci. وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّى حِين ٍ
Wa 'Abşir Fasawfa Yubşirūna َ037-179 Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa. وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ
Subĥāna Rabbika Rabbi Al-`Izzati `Ammā Yaşifūna َ037-180 Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa. سُبْحَانَ رَبِّكَ رَبِّ الْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ
Wa Salāmun `Alá Al-Mursalīna َ037-181 Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. وَسَلاَمٌ عَلَى الْمُرْسَلِينَ
Wa Al-Ĥamdu Lillahi Rabbi Al-`Ālamīna َ037-182 Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. وَالْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Next Sūrah