Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu Attaqi Al-Laha Wa Lā Tuţi`i Al-Kāfirīna Wa Al-Munāfiqīna 'Inna Al-Laha Kāna `Alīmāan Ĥakīmāan | َ033-001 Yã kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai da munãfukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima. | يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ اتَّقِ اللَّهَ وَلاَ تُطِعِ الْكَافِرِينَ وَالْمُنَافِقِينَ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيماً حَكِيما ً |
Wa Attabi` Mā Yūĥá 'Ilayka Min Rabbika ۚ 'Inna Al-Laha Kāna Bimā Ta`malūna Khabīrāan | َ033-002 Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa. | وَاتَّبِعْ مَا يُوحَى إِلَيْكَ مِنْ رَبِّكَ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرا ً |
Wa Tawakkal `Alá Al-Lahi ۚ Wa Kafá Bil-Lahi Wa Kīlāan | َ033-003 Ka dõgara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakĩli. | وَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ ۚ وَكَفَى بِاللَّهِ وَكِيلا ً |
Mā Ja`ala Al-Lahu Lirajulin Min Qalbayni Fī Jawfihi ۚ Wa Mā Ja`ala 'Azwājakumu Al-Lā'ī Tužāhirūna Minhunna 'Ummahātikum ۚ Wa Mā Ja`ala 'Ad`iyā'akum 'Abnā'akum ۚ Dhālikum Qawlukum Bi'afwāhikum Wa ۖ Allāhu Yaqūlu Al-Ĥaqqa Wa Huwa Yahdī As-Sabīla | َ033-004 Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai. | مَا جَعَلَ اللَّهُ لِرَجُل ٍ مِنْ قَلْبَيْنِ فِي جَوْفِه ِِ ۚ وَمَا جَعَلَ أَزْوَاجَكُمُ اللاَّئِي تُظَاهِرُونَ مِنْهُنَّ أُمَّهَاتِكُمْ ۚ وَمَا جَعَلَ أَدْعِيَاءَكُمْ أَبْنَاءَكُمْ ۚ ذَلِكُمْ قَوْلُكُمْ بِأَفْوَاهِكُمْ ۖ وَاللَّهُ يَقُولُ الْحَقَّ وَهُوَ يَهْدِي السَّبِيلَ |
Ad`ūhum Li'abā'ihim Huwa 'Aqsaţu `Inda Al-Lahi ۚ Fa'in Lam Ta`lamū 'Ābā'ahum Fa'ikhwānukum Fī Ad-Dīni Wa Mawālīkum ۚ Wa Laysa `Alaykum Junāĥun Fīmā 'Akhţa'tum Bihi Wa Lakin Mā Ta`ammadat Qulūbukum ۚ Wa Kāna Al-Lahu Ghafūrāan Raĥīmāan | َ033-005 Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan'uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. | ادْعُوهُمْ لِأَبَائِهِمْ هُوَ أَقْسَطُ عِنْدَ اللَّهِ ۚ فَإِنْ لَمْ تَعْلَمُوا آبَاءَهُمْ فَإِخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ وَمَوَالِيكُمْ ۚ وَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاح ٌ فِيمَا أَخْطَأْتُمْ بِه ِِ وَلَكِنْ مَا تَعَمَّدَتْ قُلُوبُكُمْ ۚ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورا ً رَحِيما ً |
An-Nabīyu 'Awlá Bil-Mu'uminīna Min 'Anfusihim ۖ Wa 'Azwājuhu 'Ummahātuhum ۗ Wa 'Ūlū Al-'Arĥāmi Ba`đuhum 'Awlá Biba`đin Fī Kitābi Al-Lahi Mina Al-Mu'uminīna Wa Al-Muhājirīna 'Illā 'An Taf`alū 'Ilá 'Awliyā'ikum Ma`rūfāan ۚ Kāna Dhālika Fī Al-Kitābi Masţūrāan | َ033-006 Annabi ne mafi cancanta ga mũminai bisa ga su kansu, kuma mãtansa uwãyensu ne. Kuma ma'abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littãfin Allah bisa ga mũminai da Muhãjirai, fãce fa idan kun aikata wani alhẽri zuwa ga majiɓintanku. Wancan yã kasance a cikin Littafi, rubũtacce. | النَّبِيُّ أَوْلَى بِالْمُؤْمِنِينَ مِنْ أَنْفُسِهِمْ ۖ وَأَزْوَاجُهُ~ُ أُمَّهَاتُهُمْ ۗ وَأُوْلُو الأَرْحَامِ بَعْضُهُمْ أَوْلَى بِبَعْض ٍ فِي كِتَابِ اللَّهِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُهَاجِرِينَ إِلاَّ أَنْ تَفْعَلُوا إِلَى أَوْلِيَائِكُمْ مَعْرُوفا ً ۚ كَانَ ذَلِكَ فِي الْكِتَابِ مَسْطُورا ً |
Wa 'Idh 'Akhadhnā Mina An-Nabīyīna Mīthāqahum Wa Minka Wa Min Nūĥin Wa 'Ibrāhīma Wa Mūsá Wa `Īsá Abni Maryama ۖ Wa 'Akhadhnā Minhum Mīthāqāan Ghalīžāan | َ033-007 Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama,kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su. | وَإِذْ أَخَذْنَا مِنَ النَّبِيِّينَ مِيثَاقَهُمْ وَمِنْكَ وَمِنْ نُوح ٍ وَإِبْرَاهِيمَ وَمُوسَى وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ۖ وَأَخَذْنَا مِنْهُمْ مِيثَاقاً غَلِيظا ً |
Liyas'ala Aş-Şādiqīna `An Şidqihim ۚ Wa 'A`adda Lilkāfirīna `Adhābāan 'Alīmāan | َ033-008 Dõmin Ya tambayi mãsu gaskiya a kan gaskiyarsu, kuma Yã yi tattalin wata azãba mai raɗaɗi ga kãfirai. | لِيَسْأَلَ الصَّادِقِينَ عَنْ صِدْقِهِمْ ۚ وَأَعَدَّ لِلْكَافِرِينَ عَذَاباً أَلِيما ً |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Adhkurū Ni`mata Al-Lahi `Alaykum 'Idh Jā'atkum Junūdun Fa'arsalnā `Alayhim Rīĥāan Wa Junūdāan Lam Tarawhā ۚ Wa Kāna Al-Lahu Bimā Ta`malūna Başīrāan | َ033-009 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da waɗansu rundunõni suka zo muku, sai Muka aika wata iskã a kansu da waɗansu rundunõni waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Yã kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa. | يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ جَاءَتْكُمْ جُنُود ٌ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحا ً وَجُنُودا ً لَمْ تَرَوْهَا وَكَانَ ۚ اللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرا ً |
'Idh Jā'ūkum Min Fawqikum Wa Min 'Asfala Minkum Wa 'Idh Zāghati Al-'Abşāru Wa Balaghati Al-Qulūbu Al-Ĥanājira Wa Tažunnūna Bil-Lahi Až-Žunūna | َ033-010 A lõkacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lõkacin da gannai suka karkata kuma zukãta suka kai ga maƙõsai, kuma kuka yi zaton zace-zace, game da Allah. | إِذْ جَاءُوكُمْ مِنْ فَوْقِكُمْ وَمِنْ أَسْفَلَ مِنْكُمْ وَإِذْ زَاغَتِ الأَبْصَارُ وَبَلَغَتِ الْقُلُوبُ الْحَنَاجِرَ وَتَظُنُّونَ بِاللَّهِ الظُّنُونَ |
Hunālika Abtuliya Al-Mu'uminūna Wa Zulzilū Zilzālāan Shadīdāan | َ033-011 A can aka jarrabi mũminai, kuma aka yi girgiza da su, girgiza mai tsanani. | هُنَالِكَ ابْتُلِيَ الْمُؤْمِنُونَ وَزُلْزِلُوا زِلْزَالا ً شَدِيدا ً |
Wa 'Idh Yaqūlu Al-Munāfiqūna Wa Al-Ladhīna Fī Qulūbihim Marađun Mā Wa`adanā Al-Lahu Wa Rasūluhu 'Illā Ghurūrāan | َ033-012 Kuma a lõkacin da munafukai da waɗanda akwai cũta a cikin zukãtansu ke cẽwa, Allah da ManzonSa, "Ba su yi mana wa'adin kõme ba, fãce rũɗi." | وَإِذْ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ مَرَض ٌ مَا وَعَدَنَا اللَّهُ وَرَسُولُهُ~ُ إِلاَّ غُرُورا ً |
Wa 'Idh Qālat Ţā'ifatun Minhum Yā 'Ahla Yathriba Lā Muqāma Lakum Fārji`ū ۚ Wa Yasta'dhinu Farīqun Minhumu An-Nabīya Yaqūlūna 'Inna Buyūtanā `Awratun Wa Mā Hiya Bi`awratin ۖ 'In Yurīdūna 'Illā Firārāan | َ033-013 Kuma a lõkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, "Ya mutãnen Yasriba! Bã ku da wani matsayi, sabõda haka ku kõma." Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman izni ga Annabi sunãcẽwa, "Lalle gidãjenmu kuranye suke," alhãli kuwa bã kuranye suke ba, bã su da nufin kome fãce gudu. | وَإِذْ قَالَتْ طَائِفَة ٌ مِنْهُمْ يَاأَهْلَ يَثْرِبَ لاَ مُقَامَ لَكُمْ فَارْجِعُوا وَيَسْتَأْذِنُ ۚ فَرِيق ٌ مِنْهُمُ النَّبِيَّ يَقُولُونَ إِنَّ بُيُوتَنَا عَوْرَة ٌ وَمَا هِيَ بِعَوْرَة ٍ إِنْ ۖ يُرِيدُونَ إِلاَّ فِرَارا ً |
Wa Law Dukhilat `Alayhim Min 'Aqţārihā Thumma Su'ilū Al-Fitnata La'ātawhā Wa Mā Talabbathū Bihā 'Illā Yasīrāan | َ033-014 Kuma dã an shige ta (Madĩna) a kansu, daga sasanninta, sa'an nan aka tambaye su fitina (kãfirci), lalle dã sun jẽ mata, kuma dã ba su zauna a cikinta (Madĩna) ba fãce kaɗan. | وَلَوْ دُخِلَتْ عَلَيْهِمْ مِنْ أَقْطَارِهَا ثُمَّ سُئِلُوا الْفِتْنَةَ لَآتَوْهَا وَمَا تَلَبَّثُوا بِهَا إِلاَّ يَسِيرا ً |
Wa Laqad Kānū `Āhadū Al-Laha Min Qablu Lā Yuwallūna Al-'Adbāra ۚ Wa Kāna `Ahdu Al-Lahi Mas'ūlāan | َ033-015 Kuma lalle haƙĩƙa, sun kasance sunã yi wa Allah alkawari, a gabãnin wannan; Bã zã su jũya dõmin gudu ba, kuma alkawarin Allah ya kasance abin tambaya. | وَلَقَدْ كَانُوا عَاهَدُوا اللَّهَ مِنْ قَبْلُ لاَ يُوَلُّونَ الأَدْبَارَ ۚ وَكَانَ عَهْدُ اللَّهِ مَسْئُولا ً |
Qul Lan Yanfa`akumu Al-Firāru 'In Farartum Mina Al-Mawti 'Awi Al-Qatli Wa 'Idhāan Lā Tumatta`ūna 'Illā Qalīlāan | َ033-016 Ka ce: "Gudun nan bã zai amfãne ku ba daga mutuwa ko kisa. Kuma har in kun gudu, bã zã a jĩshe ku dãɗĩ ba fãce kaɗan." | قُلْ لَنْ يَنْفَعَكُمُ الْفِرَارُ إِنْ فَرَرْتُمْ مِنَ الْمَوْتِ أَوِ الْقَتْلِ وَإِذا ً لاَ تُمَتَّعُونَ إِلاَّ قَلِيلا ً |
Qul Man Dhā Al-Ladhī Ya`şimukum Mina Al-Lahi 'In 'Arāda Bikum Sū'āan 'Aw 'Arāda Bikum Raĥmatan ۚ Wa Lā Yajidūna Lahum Min Dūni Al-Lahi Walīyāan Wa Lā Naşīrāan | َ033-017 Ka ce: "Wãne ne wanda yake tsare ku daga Allah, idan Yã yi nufin wata cũta game da ku?" Kuma bã zã su sãmar wa kansu wani majiɓinci ba, banda Allah, kuma bã zã su sãmar wa kansu wani mataimaki ba. | قُلْ مَنْ ذَا الَّذِي يَعْصِمُكُمْ مِنَ اللَّهِ إِنْ أَرَادَ بِكُمْ سُوءاً أَوْ أَرَادَ بِكُمْ رَحْمَة ً ۚ وَلاَ يَجِدُونَ لَهُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ وَلِيّا ً وَلاَ نَصِيرا ً |
Qad Ya`lamu Al-Lahu Al-Mu`awwiqīna Minkum Wa Al-Qā'ilīna Li'ikhwānihim Halumma 'Ilaynā ۖ Wa Lā Ya'tūna Al-Ba'sa 'Illā Qalīlāan | َ033-018 Lalle Allah Ya san mãsu hana mutãne fita daga cikinku, da mãsu cẽwa ga 'yan'uwansu,"Ku zo nan a wurinmu." Kuma bã zã su shiga yãƙi ba fãce kaɗan. | قَدْ يَعْلَمُ اللَّهُ الْمُعَوِّقِينَ مِنْكُمْ وَالْقَائِلِينَ لِإخْوَانِهِمْ هَلُمَّ إِلَيْنَا ۖ وَلاَ يَأْتُونَ الْبَأْسَ إِلاَّ قَلِيلا ً |
'Ashiĥĥatan `Alaykum ۖ Fa'idhā Jā'a Al-Khawfu Ra'aytahum Yanžurūna 'Ilayka Tadūru 'A`yunuhum Kālladhī Yughshá `Alayhi Mina Al-Mawti ۖ Fa'idhā Dhahaba Al-Khawfu Salaqūkum Bi'alsinatin Ĥidādin 'Ashiĥĥatan `Alá Al-Khayri ۚ 'Ūlā'ika Lam Yu'uminū Fa'aĥbaţa Al-Lahu 'A`mālahum ۚ Wa Kāna Dhālika `Alá Al-Lahi Yasīrāan | َ033-019 Suna mãsu rõwa gare ku, sa'an nan idan tsõro ya zo, sai ka gan su sunã kallo zuwa gare ka, idãnunsu sunã kẽwaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa sabõda mutuwa. Sa'an nan idan tsõron ya tafi,sai su yi muku miyãgun maganganu da harussa mãsu kaifi, sunã mãsu rõwa a kan dũkiya. Waɗannan, ba su yi ĩmani ba, sabõda hakaAllah Ya ɓãta ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah. | أَشِحَّةً عَلَيْكُمْ ۖ فَإِذَا جَاءَ الْخَوْفُ رَأَيْتَهُمْ يَنْظُرُونَ إِلَيْكَ تَدُورُ أَعْيُنُهُمْ كَالَّذِي يُغْشَى عَلَيْهِ مِنَ الْمَوْتِ ۖ فَإِذَا ذَهَبَ الْخَوْفُ سَلَقُوكُمْ بِأَلْسِنَةٍ حِدَادٍ أَشِحَّةً عَلَى الْخَيْرِ ۚ أُوْلَائِكَ لَمْ يُؤْمِنُوا فَأَحْبَطَ اللَّهُ أَعْمَالَهُمْ ۚ وَكَانَ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرا ً |
Yaĥsabūna Al-'Aĥzāba Lam Yadh/habū ۖ Wa 'In Ya'ti Al-'Aĥzābu Yawaddū Law 'Annahum Bādūna Fī Al-'A`rābi Yas'alūna `An 'Anbā'ikum ۖ Wa Law Kānū Fīkum Mā Qātalū 'Illā Qalīlāan | َ033-020 Sunã zaton ƙungiyõyin kãfirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyõyin kãfirai sun zo, sunã gũrin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyãwa, sunã tambayar lãbãranku. Kuma kõ dã sun kasance a cikinku, bã zã su yi yãƙi ba, fãce kaɗan. | يَحْسَبُونَ الأَحْزَابَ لَمْ يَذْهَبُوا ۖ وَإِنْ يَأْتِ الأَحْزَابُ يَوَدُّوا لَوْ أَنَّهُمْ بَادُونَ فِي الأَعْرَابِ يَسْأَلُونَ عَنْ أَنْبَائِكُمْ ۖ وَلَوْ كَانُوا فِيكُمْ مَا قَاتَلُوا إِلاَّ قَلِيلا ً |
Laqad Kāna Lakum Fī Rasūli Al-Lahi 'Uswatun Ĥasanatun Liman Kāna Yarjū Al-Laha Wa Al-Yawma Al-'Ākhira Wa Dhakara Al-Laha Kathīrāan | َ033-021 Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa. | لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَة ٌ لِمَنْ كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الآخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرا ً |
Wa Lammā Ra'á Al-Mu'uminūna Al-'Aĥzāba Qālū Hādhā Mā Wa`adanā Al-Lahu Wa Rasūluhu Wa Şadaqa Al-Lahu Wa Rasūluhu ۚ Wa Mā Zādahum 'Illā 'Īmānāan Wa Taslīmāan | َ033-022 Kuma a lõkacin da mũminai suka ga ƙungiyõyin kãfirai, sai suka ce, "Wannan ne abin da Allah da ManzonSa suka yi mana wa'adi, Allah da ManzonSa sunyi gaskiya." Kuma wannan bai ƙãra musu kõme ba fãce ĩmãni da sallamãwa. | وَلَمَّا رَأَى الْمُؤْمِنُونَ الأَحْزَابَ قَالُوا هَذَا مَا وَعَدَنَا اللَّهُ وَرَسُولُه ُُ وَصَدَقَ اللَّهُ وَرَسُولُه ُُ ۚ وَمَا زَادَهُمْ إِلاَّ إِيمَانا ً وَتَسْلِيما ً |
Mina Al-Mu'uminīna Rijālun Şadaqū Mā `Āhadū Al-Laha `Alayhi ۖ Faminhum Man Qađá Naĥbahu Wa Minhum Man Yantažiru ۖ Wa Mā Baddalū Tabdīlāan | َ033-023 Daga mũminai akwai waɗansu mazãje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukãtarsa, kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa. | مِنَ الْمُؤْمِنِينَ رِجَال ٌ صَدَقُوا مَا عَاهَدُوا اللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْهُمْ مَنْ قَضَى نَحْبَه ُُ وَمِنْهُمْ مَنْ يَنْتَظِرُ ۖ وَمَا بَدَّلُوا تَبْدِيلا ً |
Liyajziya Al-Lahu Aş-Şādiqīna Bişidqihim Wa Yu`adhdhiba Al-Munāfiqīna 'In Shā'a 'Aw Yatūba `Alayhim ۚ 'Inna Al-Laha Kāna Ghafūrāan Raĥīmāan | َ033-024 Dõmin Allah Ya sãka wa masu gaskiya da gakiyarsu, kuma Ya azabtar da munafukai idan Ya so, ko Ya karɓi tũba a kansu. Lalle, Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. | لِيَجْزِيَ اللَّهُ الصَّادِقِينَ بِصِدْقِهِمْ وَيُعَذِّبَ الْمُنَافِقِينَ إِنْ شَاءَ أَوْ يَتُوبَ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورا ً رَحِيما ً |
Waradda Al-Lahu Al-Ladhīna Kafarū Bighayžihim Lam Yanālū Khayrāan ۚ Wa Kafá Al-Lahu Al-Mu'uminīna Al-Qitāla ۚ Wa Kāna Al-Lahu Qawīyāan `Azīzāan | َ033-025 Kuma Allah Yã mayar da waɗanda suka kãfirta da fushinsu, ba su sãmi wani alhẽri ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yãƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwãyi. | وَرَدَّ اللَّهُ الَّذِينَ كَفَرُوا بِغَيْظِهِمْ لَمْ يَنَالُوا خَيْرا ً ۚ وَكَفَى اللَّهُ الْمُؤْمِنِينَ الْقِتَالَ ۚ وَكَانَ اللَّهُ قَوِيّاً عَزِيزا ً |
Wa 'Anzala Al-Ladhīna Žāharūhum Min 'Ahli Al-Kitābi Min Şayāşīhim Wa Qadhafa Fī Qulūbihimu Ar-Ru`ba Farīqāan Taqtulūna Wa Ta'sirūna Farīqāan | َ033-026 Kuma Ya saukar da waɗannan da suka taimake su daga mazõwa Littãfi, daga birãnensu, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kunã kashẽwa, kuma kunã kãma wata ƙungiyar. | وَأَنْزَلَ الَّذِينَ ظَاهَرُوهُمْ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ مِنْ صَيَاصِيهِمْ وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ الرُّعْبَ فَرِيقا ً تَقْتُلُونَ وَتَأْسِرُونَ فَرِيقا ً |
Wa 'Awrathakum 'Arđahum Wa Diyārahum Wa 'Amwālahum Wa 'Arđāan Lam Taţa'ūhā ۚ Wa Kāna Al-Lahu `Alá Kulli Shay'in Qadīrāan | َ033-027 Kuma Ya gãdar da ku gõnakinsu da gidãjensu da dũkiyõyinsu, da wata ƙasa wadda ba ku taɓa tãkarta bã. Kuma Allah ya kasance Mai ĩkon yi ne a kan kõme. | وَأَوْرَثَكُمْ أَرْضَهُمْ وَدِيَارَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ وَأَرْضا ً لَمْ تَطَئُوهَا ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِيرا ً |
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu Qul Li'zwājika 'In Kuntunna Turidna Al-Ĥayā Ata Ad-Dunyā Wa Zīnatahā Fata`ālayna 'Umatti`kunna Wa 'Usarriĥkunna Sarāĥāan Jamīlāan | َ033-028 Yã kai Annabi! Ka ce wa matanka, "Idan kun kasance kunã nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwãna kuma in sake ku, saki mai kyau." | يَاأَيُّهَا النَّبِيُّ قُلْ لِأزْوَاجِكَ إِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا فَتَعَالَيْنَ أُمَتِّعْكُنَّ وَأُسَرِّحْكُنَّ سَرَاحا ً جَمِيلا ً |
Wa 'In Kuntunna Turidna Al-Laha Wa Rasūlahu Wa Ad-Dāra Al-'Ākhirata Fa'inna Al-Laha 'A`adda Lilmuĥsināti Minkunna 'Ajrāan `Ažīmāan | َ033-029 "Kuma idan kun kasance kunã nufin Allah da Manzonsa da gidan Lãhria, to, lalle, Allah Yã yi tattalin wani sakamako mai girma ga mãsu kyautatãwa daga gare ku." | وَإِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ وَالدَّارَ الآخِرَةَ فَإِنَّ اللَّهَ أَعَدَّ لِلْمُحْسِنَاتِ مِنْكُنَّ أَجْراً عَظِيما ً |
Yā Nisā'a An-Nabīyi Man Ya'ti Minkunna Bifāĥishatin Mubayyinatin Yuđā`af Lahā Al-`Adhābu Đi`fayni ۚ Wa Kāna Dhālika `Alá Al-Lahi Yasīrāan | َ033-030 Yã mãtan Annabi! Wadda ta zo da alfãsha bayyananna daga cikinku zã a ninka mata azãba ninki biyu. Kuma wancan yã kasance mai sauƙi ga Allah. | يَانِسَاءَ النَّبِيِّ مَنْ يَأْتِ مِنْكُنَّ بِفَاحِشَة ٍ مُبَيِّنَة ٍ يُضَاعَفْ لَهَا الْعَذَابُ ضِعْفَيْنِ وَكَانَ ۚ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرا ً |
Wa Man Yaqnut Minkunna Lillahi Wa Rasūlihi Wa Ta`mal Şāliĥāan Nu'utihā 'Ajrahā Marratayni Wa 'A`tadnā Lahā Rizqāan Karīmāan | َ033-031 Kuma wadda ta yi tawãli'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki na ƙwarai, zã Mu bã ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki ma karimci. | وَمَنْ يَقْنُتْ مِنْكُنَّ لِلَّهِ وَرَسُولِه ِِ وَتَعْمَلْ صَالِحا ً نُؤْتِهَا أَجْرَهَا مَرَّتَيْنِ وَأَعْتَدْنَا لَهَا رِزْقا ً كَرِيما ً |
Yā Nisā'a An-Nabīyi Lastunna Ka'aĥadin Mina An-Nisā' ۚ 'Ini Attaqaytunna Falā Takhđa`na Bil-Qawli Fayaţma`a Al-Ladhī Fī Qalbihi Marađun Wa Qulna Qawlāan Ma`rūfāan | َ033-032 Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri. | يَانِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَد ٍ مِنَ النِسَاء إِنِ ۚ اتَّقَيْتُنَّ فَلاَ تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِه ِِ مَرَض ٌ وَقُلْنَ قَوْلا ً مَعْرُوفا ً |
Wa Qarna Fī Buyūtikunna Wa Lā Tabarrajna Tabarruja Al-Jāhilīyati Al-'Ūlá ۖ Wa 'Aqimna Aş-Şalāata Wa 'Ātīna Az-Zakāata Wa 'Aţi`na Al-Laha Wa Rasūlahu ۚ 'Innamā Yurīdu Al-Lahu Liyudh/hiba `Ankumu Ar-Rijsa 'Ahla Al-Bayti Wa Yuţahhirakum Taţhīrāan | َ033-033 Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku, kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar gãye-gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku bãyar da zakka, ku yi ɗã,ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa. | وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلاَ تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الأُولَى ۖ وَأَقِمْنَ الصَّلاَةَ وَآتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ~ُ ۚ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرا ً |
Wa Adhkurna Mā Yutlá Fī Buyūtikunna Min 'Āyāti Al-Lahi Wa Al-Ĥikmati ۚ 'Inna Al-Laha Kāna Laţīfāan Khabīrāan | َ033-034 Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin ɗãkunanku daga ãyõyin Allah da hukunci. Lalle Allah Yã kasance Mai tausasãwa Mai labartawa. | وَاذْكُرْنَ مَا يُتْلَى فِي بُيُوتِكُنَّ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ وَالْحِكْمَةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ لَطِيفاً خَبِيرا ً |
'Inna Al-Muslimīna Wa Al-Muslimāti Wa Al-Mu'uminīna Wa Al-Mu'umināti Wa Al-Qānitīna Wa Al-Qānitāti Wa Aş-Şādiqīna Wa Aş-Şādiqāti Wa Aş-Şābirīna Wa Aş-Şābirāti Wa Al-Khāshi`īna Wa Al-Khāshi`āti Wa Al-Mutaşaddiqīna Wa Al-Mutaşaddiqāti Wa Aş-Şā'imīna Wa Aş-Şā'imāti Wa Al-Ĥāfižīna Furūjahum Wa Al-Ĥāfižāti Wa Adh-Dhākirīna Al-Laha Kathīrāan Wa Adh-Dhākirāti 'A`adda Al-Lahu Lahum Maghfiratan Wa 'Ajrāan `Ažīmāan | َ033-035 Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli'u maza da mãsu tawãlĩu mãtãda mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma. | إِنَّ الْمُسْلِمِينَ وَالْمُسْلِمَاتِ وَالْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَالْقَانِتِينَ وَالْقَانِتَاتِ وَالصَّادِقِينَ وَالصَّادِقَاتِ وَالصَّابِرِينَ وَالصَّابِرَاتِ وَالْخَاشِعِينَ وَالْخَاشِعَاتِ وَالْمُتَصَدِّقِينَ وَالْمُتَصَدِّقَاتِ وَالصَّائِمِينَ وَالصَّائِمَاتِ وَالْحَافِظِينَ فُرُوجَهُمْ وَالْحَافِظَاتِ وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرا ً وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُمْ مَغْفِرَة ً وَأَجْراً عَظِيما ً |
Wa Mā Kāna Limu'uminin Wa Lā Mu'uminatin 'Idhā Qađá Al-Lahu Wa Rasūluhu 'Amrāan 'An Yakūna Lahumu Al-Khiyaratu Min 'Amrihim ۗ Wa Man Ya`şi Al-Laha Wa Rasūlahu Faqad Đalla Đalālāan Mubīnāan | َ033-036 Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna. | وَمَا كَانَ لِمُؤْمِن ٍ وَلاَ مُؤْمِنَة ٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ~ُ أَمْراً أَنْ يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ ۗ وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلاَلا ً مُبِينا ً |
Wa 'Idh Taqūlu Lilladhī 'An`ama Al-Lahu `Alayhi Wa 'An`amta `Alayhi 'Amsik `Alayka Zawjaka Wa Attaqi Al-Laha Wa Tukhfī Fī Nafsika Mā Al-Lahu Mubdīhi Wa Takhshá An-Nāsa Wa Allāhu 'Aĥaqqu 'An Takhshāhu ۖ Falammā Qađá Zaydun Minhā Waţarāan Zawwajnākahā Likay Lā Yakūna `Alá Al-Mu'uminīna Ĥarajun Fī 'Azwāji 'Ad`iyā'ihim 'Idhā Qađaw Minhunna Waţarāan ۚ Wa Kāna 'Amru Al-Lahi Maf`ūlāan | َ033-037 Kuma a lõkacin da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kanã tsõron mutãne, alhãli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin (auren mãtan) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa. | وَإِذْ تَقُولُ لِلَّذِي أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِ وَأَنْعَمْتَ عَلَيْهِ أَمْسِكْ عَلَيْكَ زَوْجَكَ وَاتَّقِ اللَّهَ وَتُخْفِي فِي نَفْسِكَ مَا اللَّهُ مُبْدِيه ِِ وَتَخْشَى النَّاسَ وَاللَّهُ أَحَقُّ أَنْ تَخْشَاه ُُ ۖ فَلَمَّا قَضَى زَيْد ٌ مِنْهَا وَطَرا ً زَوَّجْنَاكَهَا لِكَيْ لاَ يَكُونَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ حَرَج ٌ فِي أَزْوَاجِ أَدْعِيَائِهِمْ إِذَا قَضَوْا مِنْهُنَّ وَطَرا ً ۚ وَكَانَ أَمْرُ اللَّهِ مَفْعُولا ً |
Mā Kāna `Alá An-Nabīyi Min Ĥarajin Fīmā Farađa Al-Lahu Lahu ۖ Sunnata Al-Lahi Fī Al-Ladhīna Khalaw Min Qablu ۚ Wa Kāna 'Amru Al-Lahi Qadarāan Maqdūrāan | َ033-038 Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a kan ƙã'idar, Allah a cikin (Annabãwa )waɗanda suka shige daga gabãninsa. Kuma umurnin Allah yã kasance abin ƙaddarãwa tabbatacce. | مَا كَانَ عَلَى النَّبِيِّ مِنْ حَرَج ٍ فِيمَا فَرَضَ اللَّهُ لَه ُُ ۖ سُنَّةَ اللَّهِ فِي الَّذِينَ خَلَوْا مِنْ قَبْلُ ۚ وَكَانَ أَمْرُ اللَّهِ قَدَرا ً مَقْدُورا ً |
Al-Ladhīna Yuballighūna Risālāti Al-Lahi Wa Yakhshawnahu Wa Lā Yakhshawna 'Aĥadāan 'Illā Al-Laha ۗ Wa Kafá Bil-Lahi Ĥasībāan | َ033-039 Waɗanda ke iyar da Manzancin Allah, kuma sunã tsõronSa, kuma bã su tsõron kõwa fãce Allah, Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi. | الَّذِينَ يُبَلِّغُونَ رِسَالاَتِ اللَّهِ وَيَخْشَوْنَه ُُ وَلاَ يَخْشَوْنَ أَحَدا ً إِلاَّ اللَّهَ ۗ وَكَفَى بِاللَّهِ حَسِيبا ً |
Mā Kāna Muĥammadun 'Abā 'Aĥadin Min Rijālikum Wa Lakin Rasūla Al-Lahi Wa Khātama An-Nabīyīna ۗ Wa Kāna Al-Lahu Bikulli Shay'in `Alīmāan | َ033-040 Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme. | مَا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَا أَحَد ٍ مِنْ رِجَالِكُمْ وَلَكِنْ رَسُولَ اللَّهِ وَخَاتَمَ النَّبِيِّينَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيما ً |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Adhkurū Al-Laha Dhikrāan Kathīrāan | َ033-041 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa. | يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرا ً كَثِيرا ً |
Wa Sabbiĥūhu Bukratan Wa 'Aşīlāan | َ033-042 Kuma ku tsarkake shi, a sãfiya da maraice. | وَسَبِّحُوه ُُ بُكْرَة ً وَأَصِيلا ً |
Huwa Al-Ladhī Yuşallī `Alaykum Wa Malā'ikatuhu Liyukhrijakum Mina Až-Žulumāti 'Ilá An-Nūri ۚ Wa Kāna Bil-Mu'uminīna Raĥīmāan | َ033-043 (Allah) Shĩ ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikunSa (sunã yi muku addu'a), dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma (Allah) Yã kasance Mai Jĩn ƙai ga mũminai. | هُوَ الَّذِي يُصَلِّي عَلَيْكُمْ وَمَلاَئِكَتُه ُُ لِيُخْرِجَكُمْ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ ۚ وَكَانَ بِالْمُؤْمِنِينَ رَحِيما ً |
Taĥīyatuhum Yawma Yalqawnahu Salāmun ۚ Wa 'A`adda Lahum 'Ajrāan Karīmāan | َ033-044 Gaisuwarsu a rãnar da suke haɗuwa da shi "Salãm", kuma Yã yi musu tattalin wani sakamako na karimci. | تَحِيَّتُهُمْ يَوْمَ يَلْقَوْنَه ُُ سَلاَم ٌ ۚ وَأَعَدَّ لَهُمْ أَجْرا ً كَرِيما ً |
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu 'Innā 'Arsalnāka Shāhidāan Wa Mubashshirāan Wa Nadhīrāan | َ033-045 Yã kai Annabi! Lalle Mũ Mun aike ka kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. | يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ شَاهِدا ً وَمُبَشِّرا ً وَنَذِيرا ً |
Wa Dā`īāan 'Ilá Al-Lahi Bi'idhnihi Wa Sirājāan Munīrāan | َ033-046 Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakãwa. | وَدَاعِيا ً إِلَى اللَّهِ بِإِذْنِه ِِ وَسِرَاجا ً مُنِيرا ً |
Wa Bashshiri Al-Mu'uminīna Bi'anna Lahum Mina Al-Lahi Fađlāan Kabīrāan | َ033-047 Kuma ka yi bushãra ga mũminai cẽwa, sũnã da falalamai girma daga Allah. | وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ بِأَنَّ لَهُمْ مِنَ اللَّهِ فَضْلا ً كَبِيرا ً |
Wa Lā Tuţi`i Al-Kāfirīna Wa Al-Munāfiqīna Wa Da` 'Adhāhum Wa Tawakkal `Alá Al-Lahi ۚ Wa Kafá Bil-Lahi Wa Kīlāan | َ033-048 Kuma kada ka yi ɗã'a ga kãfirai da munãfukai, kuma ka ƙyã1e cũtarsu (gare ka), kuma ka dõgara ga Allah. Allah Yã isa zama wakĩli. | وَلاَ تُطِعِ الْكَافِرِينَ وَالْمُنَافِقِينَ وَدَعْ أَذَاهُمْ وَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ ۚ وَكَفَى بِاللَّهِ وَكِيلا ً |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Nakaĥtumu Al-Mu'umināti Thumma Ţallaqtumūhunna Min Qabli 'An Tamassūhunna Famā Lakum `Alayhinna Min `Iddatin Ta`taddūnahā ۖ Famatti`ūhunna Wa Sarriĥūhunna Sarāĥāan Jamīlāan | َ033-049 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun auri mũminai mãtã, sa'an nan kuka sake su a gabãnin ku shãfe su, to, bã ku da wata idda da zã ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin dãɗi kuma ku sake su saki mai kyau. | يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَكَحْتُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِنْ قَبْلِ أَنْ تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمْ عَلَيْهِنَّ مِنْ عِدَّة ٍ تَعْتَدُّونَهَا ۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحا ً جَمِيلا ً |
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu 'Innā 'Aĥlalnā Laka 'Azwājaka Al-Lātī 'Ātayta 'Ujūrahunna Wa Mā Malakat Yamīnuka Mimmā 'Afā'a Al-Lahu `Alayka Wa Banāti `Ammika Wa Banāti `Ammātika Wa Banāti Khālika Wa Banāti Khālātika Al-Lātī Hājarna Ma`aka Wa Amra'atan Mu'uminatan 'In Wahabat Nafsahā Lilnnabīyi 'In 'Arāda An-Nabīyu 'An Yastankiĥahā Khālişatan Laka Min Dūni Al-Mu'uminīna ۗ Qad `Alimnā Mā Farađnā `Alayhim Fī 'Azwājihim Wa Mā Malakat 'Aymānuhum Likaylā Yakūna `Alayka Ĥarajun ۗ Wa Kāna Al-Lahu Ghafūrāan Raĥīmāan | َ033-050 Yã kai Annabi! Lalle Mũ, Mun halatta maka mãtanka waɗanda ka bai wa sadãkõkinsu da abin da hannun dãmanka ya mallaka daga abin da Allah Ya bã ka na ganĩma, da 'yã'yan baffanka,da 'ya'yan goggonninka da 'yã'yan kãwunka da 'yã'yan innõninka waɗanda suka yi hijira tãre da kai, da wata mace mũmina idan ta bãyar da kanta ga Annabi, idan shi Annabi yanã nufin ya aure ta (hãlin wannan hukunci) kẽɓe yake gare ka,banda gamũminai. Lalle Mun san abin da Muka faralta a kansu (smũminai) game da mãtansuda abin da hannayensu suka mallaka. Do min kada wani ƙunci ya kasance a kanka, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. | يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِنَّا أَحْلَلْنَا لَكَ أَزْوَاجَكَ اللاَّتِي آتَيْتَ أُجُورَهُنَّ وَمَا مَلَكَتْ يَمِينُكَ مِمَّا أَفَاءَ اللَّهُ عَلَيْكَ وَبَنَاتِ عَمِّكَ وَبَنَاتِ عَمَّاتِكَ وَبَنَاتِ خَالِكَ وَبَنَاتِ خَالاَتِكَ اللاَّتِي هَاجَرْنَ مَعَكَ وَامْرَأَة ً مُؤْمِنَة ً إِنْ وَهَبَتْ نَفْسَهَا لِلنَّبِيِّ إِنْ أَرَادَ النَّبِيُّ أَنْ يَسْتَنكِحَهَا خَالِصَة ً لَكَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ ۗ قَدْ عَلِمْنَا مَا فَرَضْنَا عَلَيْهِمْ فِي أَزْوَاجِهِمْ وَمَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ لِكَيْلاَ يَكُونَ عَلَيْكَ حَرَج ٌ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورا ً رَحِيما ً |
Turjī Man Tashā'u Minhunna Wa Tu'uwī 'Ilayka Man Tashā'u ۖ Wa Mani Abtaghayta Mimman `Azalta Falā Junāĥa `Alayka ۚ Dhālika 'Adná 'An Taqarra 'A`yunuhunna Wa Lā Yaĥzanna Wa Yarđayna Bimā 'Ātaytahunna Kulluhunna Wa ۚ Allāhu Ya`lamu Mā Fī Qulūbikum ۚ Wa Kāna Al-Lahu `Alīmāan Ĥalīmāan | َ033-051 Kanã iya jinkirtar da wadda ka ga dãmã daga gare su, kuma kanã tãro wadda kake so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nẽma daga waɗanda ka nĩsantar, to, bãbu laifi agare ka. Wannan yã fi kusantar da sanyaya idãnunsu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba, kuma su yarda da abin da ka bã su, sũ duka. Kuma Allah Yanã sane da abin da yake a cikin zukãtanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri. | تُرْجِي مَنْ تَشَاءُ مِنْهُنَّ وَتُؤْوِي إِلَيْكَ مَنْ تَشَاءُ ۖ وَمَنِ ابْتَغَيْتَ مِمَّنْ عَزَلْتَ فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْكَ ۚ ذَلِكَ أَدْنَى أَنْ تَقَرَّ أَعْيُنُهُنَّ وَلاَ يَحْزَنَّ وَيَرْضَيْنَ بِمَا آتَيْتَهُنَّ كُلُّهُنَّ ۚ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا فِي قُلُوبِكُمْ ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيماً حَلِيما ً |
Lā Yaĥillu Laka An-Nisā' Min Ba`du Wa Lā 'An Tabaddala Bihinna Min 'Azwājin Wa Law 'A`jabaka Ĥusnuhunna 'Illā Mā Malakat Yamīnuka ۗ Wa Kāna Al-Lahu `Alá Kulli Shay'in Raqībāan | َ033-052 Waɗansu mãtã bã su halatta a gare ka a bãyan haka, kuma ba zã ka musanya su da mãtan aure ba, kuma kõ kyaunsu yã bã ka sha'awa, fãce dai abin da hannun dãmanka ya mallaka. Kuma Allah Yã kasance Mai tsaro ga dukan kõme. | لاَ يَحِلُّ لَكَ النِسَاء مِنْ بَعْدُ وَلاَ أَنْ تَبَدَّلَ بِهِنَّ مِنْ أَزْوَاج ٍ وَلَوْ أَعْجَبَكَ حُسْنُهُنَّ إِلاَّ مَا مَلَكَتْ يَمِينُكَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ رَقِيبا ً |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tadkhulū Buyūta An-Nabīyi 'Illā 'An Yu'udhana Lakum 'Ilá Ţa`āmin Ghayra Nāžirīna 'Ināhu Wa Lakin 'Idhā Du`ītum Fādkhulū Fa'idhā Ţa`imtum Fāntashirū Wa Lā Musta'nisīna Liĥadīthin ۚ 'Inna Dhālikum Kāna Yu'udhī An-Nabīya Fayastaĥyi Minkum Wa ۖ Allāhu Lā Yastaĥyi Mina Al-Ĥaqqi ۚ Wa 'Idhā Sa'altumūhunna Matā`āan Fās'alūhunna Min Warā'i Ĥijābin ۚ Dhālikum 'Aţharu Liqulūbikum Wa Qulūbihinna ۚ Wa Mā Kāna Lakum 'An Tu'udhū Rasūla Al-Lahi Wa Lā 'An Tankiĥū 'Azwājahu Min Ba`dihi 'Abadāan ۚ 'Inna Dhālikum Kāna `Inda Al-Lahi `Ažīmāan | َ033-053 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da kun tsaya kunã masu hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi, to, yanã jin kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bã ya halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle wannan a gare ku yã kasance babban abu a wurin Allah. | يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لاَ تَدْخُلُوا بُيُوتَ النَّبِيِّ إِلاَّ أَنْ يُؤْذَنَ لَكُمْ إِلَى طَعَامٍ غَيْرَ نَاظِرِينَ إِنَاه ُُ وَلَكِنْ إِذَا دُعِيتُمْ فَادْخُلُوا فَإِذَا طَعِمْتُمْ فَانْتَشِرُوا وَلاَ مُسْتَأْنِسِينَ لِحَدِيث ٍ ۚ إِنَّ ذَلِكُمْ كَانَ يُؤْذِي النَّبِيَّ فَيَسْتَحْيِ مِنْكُمْ ۖ وَاللَّهُ لاَ يَسْتَحْيِ مِنَ الْحَقِّ ۚ وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَاعا ً فَاسْأَلُوهُنَّ مِنْ وَرَاءِ حِجَاب ٍ ۚ ذَلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ ۚ وَمَا كَانَ لَكُمْ أَنْ تُؤْذُوا رَسُولَ اللَّهِ وَلاَ أَنْ تَنْكِحُوا أَزْوَاجَه ُُ مِنْ بَعْدِهِ~ِ أَبَدا ً ۚ إِنَّ ذَلِكُمْ كَانَ عِنْدَ اللَّهِ عَظِيما ً |
'In Tubdū Shay'āan 'Aw Tukhfūhu Fa'inna Al-Laha Kāna Bikulli Shay'in `Alīmāan | َ033-054 Idan kun bayyana wani abu, kõ kuma kuka ɓõye shi, to, lalle Allah Ya kasance Masani ga kõme. | إِنْ تُبْدُوا شَيْئاً أَوْ تُخْفُوه ُُ فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيما ً |
Lā Junāĥa `Alayhinna Fī 'Ābā'ihinna Wa Lā 'Abnā'ihinna Wa Lā 'Ikhwānihinna Wa Lā 'Abnā'i 'Ikhwānihinna Wa Lā 'Abnā'i 'Akhawātihinna Wa Lā Nisā'ihinna Wa Lā Mā Malakat 'Aymānuhunna ۗ Wa Attaqīna Al-Laha ۚ 'Inna Al-Laha Kāna `Alá Kulli Shay'in Shahīdāan | َ033-055 Bãbu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma bãbu game da ɗiyansu, kuma bãbu game da 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kuma bãbu game da mãtan mũminai, kuma bãbu game da abin da hannãyensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Yã kasance Mahalarci a kan kõme. | لاَ جُنَاحَ عَلَيْهِنَّ فِي آبَائِهِنَّ وَلاَ أَبْنَائِهِنَّ وَلاَ إِخْوَانِهِنَّ وَلاَ أَبْنَاءِ إِخْوَانِهِنَّ وَلاَ أَبْنَاءِ أَخَوَاتِهِنَّ وَلاَ نِسَائِهِنَّ وَلاَ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ ۗ وَاتَّقِينَ اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ شَهِيدا ً |
'Inna Al-Laha Wa Malā'ikatahu Yuşallūna `Alá An-Nabīyi ۚ Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Şallū `Alayhi Wa Sallimū Taslīmāan | َ033-056 Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni!Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi. | إِنَّ اللَّهَ وَمَلاَئِكَتَه ُُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ ۚ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيما ً |
'Inna Al-Ladhīna Yu'udhūna Al-Laha Wa Rasūlahu La`anahumu Al-Lahu Fī Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati Wa 'A`adda Lahum `Adhābāan Muhīnāan | َ033-057 Lalle waɗanda ke cũtar Allah da MauzonSa Allah Yã la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma Yã yi musu tattalin azãba mai wulãkantarwa. | إِنَّ الَّذِينَ يُؤْذُونَ اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ لَعَنَهُمُ اللَّهُ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَأَعَدَّ لَهُمْ عَذَابا ً مُهِينا ً |
Wa Al-Ladhīna Yu'udhūna Al-Mu'uminīna Wa Al-Mu'umināti Bighayri Mā Aktasabū Faqadi Aĥtamalū Buhtānāan Wa 'Ithmāan Mubīnāan | َ033-058 Kuma waɗanda suke cũtar mũminai maza dã muminai mãtã, bã da wani abu da suka aikata ba to, lalle sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne. | وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ بِغَيْرِ مَا اكْتَسَبُوا فَقَدِ احْتَمَلُوا بُهْتَانا ً وَإِثْما ً مُبِينا ً |
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu Qul Li'zwājika Wa Banātika Wa Nisā'i Al-Mu'uminīna Yudnīna `Alayhinna Min Jalābībihinna ۚ Dhālika 'Adná 'An Yu`rafna Falā Yu'udhayna ۗ Wa Kāna Al-Lahu Ghafūrāan Raĥīmāan | َ033-059 Yã kai Annabi! Ka ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai. | يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُلْ لِأزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِنْ جَلاَبِيبِهِنَّ ۚ ذَلِكَ أَدْنَى أَنْ يُعْرَفْنَ فَلاَ يُؤْذَيْنَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورا ً رَحِيما ً |
La'in Lam Yantahi Al-Munāfiqūna Wa Al-Ladhīna Fī Qulūbihim Marađun Wa Al-Murjifūna Fī Al-Madīnati Lanughriyannaka Bihim Thumma Lā Yujāwirūnaka Fīhā 'Illā Qalīlāan | َ033-060 Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hãlãyensu), lalle, zã Mu shũshũta ka a gare su, sa'an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan. | لَئِنْ لَمْ يَنْتَهِ الْمُنَافِقُونَ وَالَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ مَرَض ٌ وَالْمُرْجِفُونَ فِي الْمَدِينَةِ لَنُغْرِيَنَّكَ بِهِمْ ثُمَّ لاَ يُجَاوِرُونَكَ فِيهَا إِلاَّ قَلِيلا ً |
Mal`ūnīna ۖ 'Aynamā Thuqifū 'Ukhidhū Wa Quttilū Taqtīlāan | َ033-061 Sunã la'anannu, inda duka aka sãme su a kãmã su, kuma a karkashe su karkashẽwa. | مَلْعُونِينَ ۖ أَيْنَمَا ثُقِفُوا أُخِذُوا وَقُتِّلُوا تَقْتِيلا ً |
Sunnata Al-Lahi Fī Al-Ladhīna Khalaw Min Qablu ۖ Wa Lan Tajida Lisunnati Al-Lahi Tabdīlāan | َ033-062 A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin waɗanda suka shũɗe gabãninka, kuma bã zã ka sãmi musanyãwa ba ga hanyar Allah. | سُنَّةَ اللَّهِ فِي الَّذِينَ خَلَوْا مِنْ قَبْلُ ۖ وَلَنْ تَجِدَ لِسُنَّةِ اللَّهِ تَبْدِيلا ً |
Yas'aluka An-Nāsu `Ani As-Sā`ati ۖ Qul 'Innamā `Ilmuhā `Inda Al-Lahi ۚ Wa Mā Yudrīka La`alla As-Sā`ata Takūnu Qarībāan | َ033-063 Sunã tambayar ka ga Sã'a. Ka ce: "Saninta yanã wurin Allah kawai." Kuma me yã sanar da kai cẽwa anã tsammãnin sa'a ta kasance kusa? | يَسْأَلُكَ النَّاسُ عَنِ السَّاعَةِ ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِنْدَ اللَّهِ ۚ وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّ السَّاعَةَ تَكُونُ قَرِيبا ً |
'Inna Al-Laha La`ana Al-Kāfirīna Wa 'A`adda Lahum Sa`īrāan | َ033-064 Lalle Allah Yã la'ani kãfirai, kuma Yã yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna. | إِنَّ اللَّهَ لَعَنَ الْكَافِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمْ سَعِيرا ً |
Khālidīna Fīhā 'Abadāan ۖ Lā Yajidūna Walīyāan Wa Lā Naşīrāan | َ033-065 Sunã madawwama a cikinta har abada, bã su sãmun majiɓinci, kuma bã su sãmun mataimaki. | خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدا ً ۖ لاَ يَجِدُونَ وَلِيّا ً وَلاَ نَصِيرا ً |
Yawma Tuqallabu Wujūhuhum Fī An-Nāri Yaqūlūna Yā Laytanā 'Aţa`nā Al-Laha Wa 'Aţa`nā Ar-Rasūlā | َ033-066 Rãnar da ake jũya fuskõkinsu a cikin wuta sunã cẽwa, "Kaitonmu, sabõda,rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo!" | يَوْمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ يَقُولُونَ يَا لَيْتَنَا أَطَعْنَا اللَّهَ وَأَطَعْنَا الرَّسُولَا |
Wa Qālū Rabbanā 'Innā 'Aţa`nā Sādatanā Wa Kubarā'anā Fa'ađallūnā As-Sabīlā | َ033-067 Kuma suka ce: "Yã Ubangijinmu! Lalle mũ mun bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya! | وَقَالُوا رَبَّنَا إِنَّا أَطَعْنَا سَادَتَنَا وَكُبَرَاءَنَا فَأَضَلُّونَا السَّبِيلَا |
Rabbanā 'Ātihim Đi`fayni Mina Al-`Adhābi Wa Al-`Anhum La`nāan Kabīrāan | َ033-068 "Yã Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azãba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma." | رَبَّنَا آتِهِمْ ضِعْفَيْنِ مِنَ الْعَذَابِ وَالْعَنْهُمْ لَعْنا ً كَبِيرا ً |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Takūnū Kālladhīna 'Ādhaw Mūsá Fabarra'ahu Al-Lahu Mimmā Qālū ۚ Wa Kāna `Inda Al-Lahi Wajīhāan | َ033-069 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci Mũsã sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah. | يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لاَ تَكُونُوا كَالَّذِينَ آذَوْا مُوسَى فَبَرَّأَهُ اللَّهُ مِمَّا قَالُوا ۚ وَكَانَ عِنْدَ اللَّهِ وَجِيها ً |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Attaqū Al-Laha Wa Qūlū Qawlāan Sadīdāan | َ033-070 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya. | يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلا ً سَدِيدا ً |
Yuşliĥ Lakum 'A`mālakum Wa Yaghfir Lakum Dhunūbakum ۗ Wa Man Yuţi`i Al-Laha Wa Rasūlahu Faqad Fāza Fawzāan `Ažīmāan | َ033-071 Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gãfarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, lalle, yã rabbanta, babban rabo mai girma. | يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ ۗ وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ فَقَدْ فَازَ فَوْزاً عَظِيما ً |
'Innā `Arađnā Al-'Amānata `Alá As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Al-Jibāli Fa'abayna 'An Yaĥmilnahā Wa 'Ashfaqna Minhā Wa Ĥamalahā Al-'Insānu ۖ 'Innahu Kāna Žalūmāan Jahūlāan | َ033-072 Lalle Mũ, Mun gitta amãna ga sammai da ƙasã da duwãtsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsõro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ (mutum) ya kasance mai yawan zãlunci, mai yawan jãhilci. | إِنَّا عَرَضْنَا الأَمَانَةَ عَلَى السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَالْجِبَالِ فَأَبَيْنَ أَنْ يَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الإِنْسَانُ ۖ إِنَّه ُُ كَانَ ظَلُوما ً جَهُولا ً |
Liyu`adhdhiba Al-Lahu Al-Munāfiqīna Wa Al-Munāfiqāti Wa Al-Mushrikīna Wa Al-Mushrikāti Wa Yatūba Al-Lahu `Alá Al-Mu'uminīna Wa Al-Mu'umināti ۗ Wa Kāna Al-Lahu Ghafūrāan Raĥīmāan | َ033-073 Dõmin Allah Ya azabta munãfukai maza da munãfukai mãtã, da mushirikai maza da mushirikai mãtã, kuma Allah Yã karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mãtã. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. | لِيُعَذِّبَ اللَّهُ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْمُشْرِكِينَ وَالْمُشْرِكَاتِ وَيَتُوبَ اللَّهُ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورا ً رَحِيما ً |